DIDDIGAR ƘAYA    (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid*                       *Shimfiɗa* *PAID BOOK* ƊANƊANO **Assalamu Alaikum warahmatullah, tadaaaa ga Gureenjo da sabon littafi,salo,labari me kama zuciya.. Ba zan ce wadda baku taɓa gani ba sede in ce ya sha bam-bam da wadda kuka saba gani, Mallaki naki tun kan free pages su ƙare ki sha karatu cikin kwanciyar hankali🥰** Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata, wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta. "Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali... Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba, idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!" Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa "Na yarda baba Alhj....a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina...! Ko yaya yake... Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni.." Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa. Wani mugun kallo ya watsa mata yace "ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!" Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi. Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama'ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe "Ammi! Baba Alhj basa ƙaunata Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwanana be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!" Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za'a aiwatar? Allah kaɗai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da ƴanci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? Kuɗi ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya ɗin? "Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba... Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina" Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa "Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina.... Duk ranar da aka yi Adu'ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata ɗakin sa.. Ku gafarceni Jaddah..." Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, irin muryannan na no nonsense, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta... "Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba a rayuwata, ban taɓa sauya fari zuwa baƙi ba idan har ku kuka furta Cewar farin ne, sau ɗaya dae ku dubi Allah karku tilastani yin abunda ba zan iya ba, zan iya shiga wuta aka yi min dole wannan aure saboda ba zan iya adalci tsakanin ta da Fatima ba, above all that baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa...! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina..." Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa. Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna ba tare da ya iya cewa komai ba, karon farko da wayaunshi kenan da mahaifiyarshi ta sa hannu a kanshi duk akan wannan annoban, miƙewa yayi a zuciye ya fice kaman kububuwa... "Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?" Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta. Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi. "Baki da hujja? To fitar min daga ɗaki" Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka. Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri'ar ta, idanunta ta kai kanshi yayi shiru cikin nazari da tunani, chan ya ɗago ya kalli Jaddah cikin girmamawa yace "kwarai raina a ɓace yake kuma a ƙuntace hajiya! Ban taɓa yin abunda na muzanta ba irin wannan kab tarihina zuwa matsayin da na taka a yanzu, na kan Haɗa auren maƙota ma su karɓa cikin farin ciki bare na ƴaƴan cikina.." Shiru ya ɗan yi kan ya kalli Mammi yace "Ki sanar da ɗanki daga yanzu har a ɗaura auren nan idan na saƙe jin muryarsa da sunan mujadala da auren nan na yafesa har Abada!" A razane duk suke kallon shi, kwarai ranshi ya ɓaci da wannan lamarin tunda har Baba prof ze iya furta kalma irin wannan. Miƙewa yayi ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, a maimaikon yayi sashensa se ya nufi sashen ƙaninsa Sulaiman, sama sama yake amsa sannu da matan da suke daga farfajiyar har zuwa harabar na gidan Sulaiman suke mishi har ya isa zuwa parlornshi, da sauri Baba Alhaji da yake shirin cin abinci ya miƙe tsaye yana furta "Yaya! Ai da ko a waya ka ƙirani ba se ka zo da kanka ba!" Daga tsayen hannayenshi goye a baya yace cikin natsuwarsa na tsantsan ilimin addini "Ba buƙatar hakan Sulaiman saboda ina so ka san saƙon me muhimmanci ne, ina so ka sanar da Fauziyya idan har kai ka haifeta na sake jin magana makamancin wadda ta zo dashi yanzu sashen hajiya ka yafeta wa duniya har Abada!" Da sauri ya ɗaga kai ya kalli yayan nashi zuciyarshi na bugawa, dukda maganan yayi mishi tsauri sede zasu iya kaiwa ko wani mataki domin ganin mutuncinsu be zube ba kaman yadda ƴar wajenshi ta so zubarwa, mutuncin da tun kan a auri mahaifiyarta yake wanzuwa a idanun mutane.. "Kayi hakuri yaya in shaa Allah hakan ba ze sake faruwa ba" "Allah ya sa!" Baba prof ya faɗa yana Juyawa ya fice a lokaci ɗaya yana amsa saida safen da Baba Alhajin ke yi mai. Ya jima bayan ya fita harabar gidan yana safa da marwa, kan ya nufi kofarshi bayan ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi...! ***Shin ya kuka gani? Menene hasashenku kan wannan sabon littafi? Su waye ne waennan ahali? Me yake faruwa a cikin wannan gida? Menene musababbin tsanar da suke yiwa juna? Meyasa kowa ya buɗe baki da kalmar fasiƙa yake jefan Fauxa? Wani irin zama zasu yi bayan Haɗa Wuta da Auduga inuwa guda? Akwai fa'ida a wannan aure ko babu? Za'a daura ko kuwa?*** Pls waenda suka fara biya should dm me sbd in saka su paid group. One more thing comment matters pls, ba zan zauna ina wasting energy wurin typing ku ki yin comment in ji daaɗi ba, so show some love with ur wonderful comments🙏🥰 Duk ku biyo ni a cikin wannan littafi nawa me suna DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA...    (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid*                       *Shafi Na Ɗaya* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN KARO COMMENTS ƊINKU NA DA MATUKAR MUHIMMANCI SOSSAI*** Idanunta da gabaɗaya suka jeme suka kumbure suntum har suka sauya mata kamanni ta sake saukewa kan agogon ɗakin karo na ba adadi, hasken dake ratsowa daga window ɗin ya bata damar kallon lokacin, karfe 12:30 na dare yunƙurawa tayi ta miƙe zaune tana jin kanta na mata wani irin nauyi kaman an ɗaura mata dutsen dala. Idanunta ta kai kan handbag ɗinta cikin tsananin nazari da damuwa kan ta janyoshi ta zaro wani farin gora ta gimtse cikin hannunta, ɗakin su ta bi da Kallo, ɗakin dake ɗauke da rabi da kwata daga cikin tarihin rayuwarta, duk cikin waenda suke kwance babu wacce zata ce sun yi kusa kusa duk en uwan nesa ne waenda suka zo bukin nan da bata taɓa hasashen yiwuwarsa ba seda taga wankin hula na shirin kai ta dare, kai tsaye zata iya cewa biyar daga cikin ahalinta na ɗakin suna wurin mahaifiyarsu da itama tun zancen ya tashi basu da sukuni. Ƴar uwarta kuma da suke ciki ɗaya ta ƙaura wa sashen sbd rashin son hayaniyarta, cikin dauriya ta miƙe tsaye jiri na shirin yar da ita, a saɗaɗe ta nufi kofa ta buɗe ta fice, babu kowa a tsakar gidan sede tana iya kallon haske daga sashen mahaifinta alamun idanunshi biyu har yanzu, hannunta har rawa yake wurin cire sakatar ƙaramin gate na sashen nasu ta fice tsakar babban gidan nasu dake ɗauke da sashuka masu ɗan dama. Chan baya inda haske be cika yawa ba ta je ta tsaya idanunta zube bisa farin robar da aka rubuta sniper da zanen ƙwari a jiki, hawaye masu tsananin zafi ne suka saukar mata maganganun mahaifinta na ƙarshe gareta masu kaifi da ƙuna na amsa kuwwa a kunnuwanta kaman yanzu yake yin su... "Fauziyya ban san cewa kin tabbata marar kunya fitsararra ba seda kika tsaya gaban su jadda da yaya kina ikirarin kashe kanki saboda abinda yake gata ze miki, kina Tunanin ko wasu iyaye ne zasu yardar ma ɗan su auren mace irinki? Ko ni.. (Ya nuna kanshi da hannu) da Farhan ze zo min da zancen auren mace me makamancin halayenki Fauziyya ina miki rantsuwa ba zan amintar mishi ba, in har kin haifu don Allah ki kashe kan naki in aka ɗaura, jaliha marar tunani.. Daga sadda kika kashe kanki daga sannan ni kuma na zare duk wata alaqa tsakanina dake, zan tsinewa gawarki tun kan a binneki, wanka da sallah ba de a gidana ba don ba zan taɓa yiwa kafira Adu'a ba, kaman yadda kika san hukuncin duk wadda ya kashe kanshi ya mutu kafiri... Don Allah karki faasa, fice ki bani wuri...!" Kuka take yi sossai tana jin yadda zuciyarta ke mata ciwo, meyasa kowa ya gagara fahimtarta? Meyasa se ita? Hannayenta na rawa ta buɗe roban sniper ɗin ta nufi bakinta, duka jikinta na mugun rawa gwara ta mutu ta bar musu duniyan da wannan bakin cikin, motsin da taji a bayanta yasa tayi saurin juyowa se idanunsu suka sarƙe cikin na juna. Hannunshi zube cikin wandon Fararen pajamas dake jikinshi masu sulbi da suka fitar da kirarsa na kakkarfan namiji me zaati da charisma, idanunshi masu kaifi ya fara saukewa kan hannunta kan ya ɗago ya tsura mata su na mintuna ya ɗaukesu tare da jan tsiririn tsaki, cikin takunshi na zaratan maza ya nufo ta har kaman ze goge ta kan ya ɗan ja kuta yace cikin muryarsa me rikitar da mata.. "Mutuwa se ta fi miki sauƙi da aurena! Rayuwar ƙabari se ta fi miki jin daaɗi idan kika mutu kafira da irin rayuwar da na tanadar miki muddin kika sake aka shafa Adu'ar aurena dake! Faizan be yi zina ba da yardar Allah ba ze taɓa auren mazinaciya ba, ki saka wannan a bayan thick lunatic skull na ki..." Yana kai nan ya tsirtar da miyau ya wuce abunshi ba tare da ko waiwaye ba. Fitinan da Fatima ta dasa mishi kaɗai ya ishe shi, idan ta mutu se ya fi kowa farin ciki wallahi, ihunta yaji hakan kuma be saka shi waiwayawa ba har ya shige sashen samarin gidan inda nan ɗakin shi yake tun kan yayi aure har yanzu. A kan gwiwowinta ta zube tana kuka me cin zuciya wani irin jarababbiyar kaddara ce wannan? Wadda ake yi mata murnan samun shi kenan a matsayin miji? Wadda shine ya zama duk wani silar taɓarɓarewar farin cikinta, idan da be tsoma kanshi cikin tsarin rayuwarta ba da duk hakan bata faru ba.. Da sauri ta sake kai roban bakinta tana shirin apawa taji an yi chilli da robar, da sauri ta ɗago se taji sauƙan mari bisa fuskanta dake suntume already. "Fauziyya??? Innalillahi wainna ilahi rajiun..!" Ko bata ɗago ba ta san jadda ce daga muryar, fusgo ta tayi suka zagaya zuwa kofan sashenta suka shiga, tsallake mutanen dake parlorn suka yi suka wuce kofar ɗakin Fauza dake sashen wadda shima mutanen su na Maiduguri ne ciki suka shiga ɗakin jaddar, kan gado ta ajiye ta tace "Fauziyya kina da hankali kuwa? Meyasa kike shirin kashemu tun kwanakin mu be ƙare ba? Ki bar mu muji da abu ɗaya mana! Kin kuwa san hukuncin ki daga sadda kika aikata abunda kika aikata kuwa? Wuta fa! Kin kuwa san menene dawwama a wuta na har Abada? Haba Fauziyya! Ina iliminki? Wani bala'i ne yafi na jefa kai ga halaka? Akan auren ɗan uwanki saboda laifin da ke kika janyo?" Cikin kuka sossai take girgiza kai hannayenta gabaɗaya a kanta duniyar gabaɗaya yayi mata zafi ji take kaman an rufe ta ne a cikin kurkuku me cike da tsananin duhu da zafi, bata iya magana ba Jaddah ta sake cewa "ba don naji ihun ki na fita ba da yanzu ba wannan maganan ake ba Fauziyya waye ya kawo miki wannan abu? Taya ya zo hannunki?" Seda ta daka mata tsawa kan ta faɗa cikin dasashiyar muryarta.. "Sakinah!" "Yanzu waennan ƙawayen arziki kenan Fauziyya?" Sassauta muryarta tayi tace "Fauziyya duk abubuwan nan da suke faruwa ki saka a Ranki Allah ne ya tsara hakan ba wai yin mu ba, ina me tabbatar miki kuma Faizan shine alkhairinki in har kinga an ɗaura auren nan to tun farko rubutacce ne daga sama! Wlh idan na ganki cikin wannan hali hankalina tashi yake" Tana girgiza kai saboda babu wadda ze iya hango abunda take hangowa ta fara cewa "Meyasa se Faizan? Meyasa Jaddah? Don Allah ki taimakeni Jadda, aure fa ba wai ana yinshi don gobe a fito bane a'a, ana so in ka yi shi ku kasance abadan abada har se mutuwa ta raba, taya kuke hango min farin ciki da zama na har abada daga Maƙiyi na wadda burinshi ko da yaushe ya ga hawaye bisa idanuna? Mutumin da be taɓa ƙaunata ko da na second guda ba, Jaddah idan kuka hana ni mutuwa tabbas zan gudu!" Bakinta ta buge cikin faɗa tace "Haba Fauziyya ke kam meyasa kike da taurin kai ne Haka? Auren nan se an ɗaura tunda har iyayenku sun riga sun zartar, tun farko wa ya janyo? A tarbiyarki ban taɓa Tunanin zaki aikata abunda kika aikata ba, gwara ki sakawa zuciyarki salama ki amshi wannan aure don ko gawarki ne na yarda a kai gidan Faizan da irin watsewar da zaki zauna ki mana, kuma babu uban da ze amince da aurenki in har yayi bincike akanki gwara tun wuri mu rufawa kanmu asiri, daga yanzu in kara ganinki ko da a kofar ɗakin nan ne ki gani..." Tana kai nan ta hau gado ta kwanta tare da kashe wuta, anan Fauza ta cigaba da zama lokaci lokaci tana share hawaye zuciyarta baƙi kirin har bata san sadda bacci ya sureta ba kanta bakin gado tana zaune daga ƙasa. Sam bata san an yi asuba ba don Jaddah bata tashe ta ba sanin bata sallah, don seda babanta yayi mata har gwajin ciki da HIV kan ya saduda da hana Faizan aurenta Dukda iyayenshi basu damu da duk wannan ba. Hayaniyar da take ji daga tsakar gidan da salati ya sakata farkawa Sam bata so tashi ba amma jin hayaniyar kaman tayi yawa ne ya sakata mikewa tana yamutsa fuskanta da ya jeme ya rame saboda tashin hankali ta nufi waje, a iyakar sanin ta in har kaji ana hayaniya a gidan Baba Prof to da Fauziyya ne yau kuma to me ke faruwa? Daga kofar gate na Jaddah ta ja ta tsaya tana kallon matan dake tsakar gidan wasu kuma sun fi yawa a kofar sashensu, tana shirin Juyawa don bata ga abunda ake ba se ta hangi tahowarsa da Fatima a hannu gabaɗayanshi a rikice kana ganin fuskanshi ka san al'amarin dake nufo shi baya kaunar ta ko na miskala zarratin, da ta kura idanu se taga kaman jini ne ke gangara daga jikin Fatimar alamu wannan cikin ma da ya kwallafawa rai ya tafi. Baki ta taɓe tana jin burbushin farin ciki a zuciyarta, ko yaya shima ya shiga cikin baƙin ciki kaman yadda take ciki, tana shirin Juyawa ta koma taji wata daga cikin en uwansu na cewa "khaihh na tausayawa yarinyar nan, kishiya ba karamar abu bace a wannan zamani bare ma irin kishiyar da kuka tashi tare matsayin ya da kanwa, iyayenku mata kuma suna auren miji guda" Ɗayar wacce ƴar uwar Mahaifiyar Fatiman ce tace "wannan kam son zuciya ne karara daga gani ai cusa mishi Amaryar aka yi don yadda take ta bore ya nuna komai, Allah sarki Fatima ciki na kusan biyar kenan shima be zauna ba sanadiyar wannan kadararren auren!" Juyawa tayi ta koma tana mamakin kanta, for the first time kenan da aka yiwa Fauxa Abu ta ɗauke kai ta wuce, lallai abunda ya dameta ya dameta. A kan gadon Jaddah ta sake yin masauki tare da tsunduma komar Tunaninta da ta san babu ranar gamawa, ɗagowa tayi jin alamun shigowar mutum. "Ya Fadeelah!" Ta kira sunan kawai kan ta maida idanunta ƙasa, babbar yayarta ce itace babba mace a ɗakin su, bata da wani shaƙuwa ko kusanci da kowa a gidan bayan Jaddah da Fa'iza wacce ta san a yanzu ko giyar wake fa'iza ta sha bazata zo kusa da ita ba. karasowa Fadeelah tayi ta zauna gefenta tare da rike hannunta tace "Fauxa! Kin ga yadda kika koma kuwa? Wannan anya fauxa ce kuwa? Wannan Fauzan da na sani bata taɓa zama na minti biyu shiru ba tare da ta nemi maganar wani ko faɗar wani ba? Fauxa nata ne..!" Ɗago kai tayi tana dan ɓata fuska tace "A'a yaya Fadeelah banda ɗan banza" Dariya Fadeelah ta saki ita kuma fauza ta ɗan yi murmushi duk sun tuna sadda suke tare kirarinta kenan 'Fauxa kowa naki banda ɗan banza' ta kan faɗi hakan da proud musamman idan Fatima na kusa se gashi kaddarar Allah ya Haɗa su zama inuwa ɗaya a matsayin kishiyoyi. "Bazaki tambayeni yaushe na zo ba? Ko ina yara?" Ɗago idanu ta sake yi ta kalleta cikin gajiyawa tace "Yaya stop been nice please ba haka muke ba" Rike hannunta tayi tace "I know, yanzu ina so mu fi haka.. Fauziyya ke yarinya ce har yanzu gashi Allah ya jarabceki da auren wadda kika ɗauka a matsayin Maƙiyi gabaɗaya rayuwarki ya kuma Haɗa ki da wacce tun shigowarta gidan nan matsayin agola baku taɓa kaunar juna ba a matsayin kishiya, ba Yola Zaku zauna ba bare ace akwai idanun Jaddah ko Ammi da mammi Abuja Zaku inda daga ku se ku you really need a guardian, please Fauxa ki girma and let me be a good sister I've supposed to be tun farko" Hawaye masu zafi ne suka saukar mata tana kallon Fadeelah tace "Ya Fadeelah kema kin yarda in hakura in zauna da Maƙiyina bayan kin san cewa duk mun tsani juna? Hakanan matarshi ko na minti biyu shiri be taɓa shiga tsakaninmu ba? Yaya Fadeelah wallahi wallahi ban taɓa aikata zina ba, meyasa kowa ze min wannan shedar alhali duk sharrin Faizan ne?" Fadeelah ta sake rike hannunta tace "Fauziyya kiyi Adu'a kinji? Ki sasaautawa ranki ki ɗauka cewa wannan aure shine alkhairinki kuma aljannarki karki manta abunda babba ya hango yaro fa baze hangonshi ba ko da kuwa ya hau dutse, yanzu iyayenmu duka fushi suke daku especially ma ke da kike da taurin zuciya, Fatima ta zama abar tausayi tunda tana chan kwance ta rasa cikin da ta kwallafawa rai" Tace "ya fadeela duk cikin munafurcinta ne, ni a duniya Ban taɓa ganin munafuki irin Fatima ba!" Dafe kai Fadeela tayi, Fauza ta kau da kanta, Fadyaa ce ta shigo itama suka haɗu Suka yi ta nusar da ita, ɗan banzar taurin kai ne da ita kaman arnan fari, ga kafiyar tsiya da kyar suka samu tayi wanka ta ci wani abu, Fadyaa ta fice ta barsu da fadeela tana ta kokarin cigaba da bata shawarwari. Walimar da za'a yi ranan har an yi niyyar fasawa Baba prof yace ayi tunda an yi gayyata, duk a Tunanin Faizan za'a fasa auren nan a gobe ganin abunda ya faru kuma har a yammacin da aka yi waliman Da seda mammi ta sa baki kan Amaryar ta fito Fatima na kwance a asibiti, Bayan ta farka tayi ta mishi kuka likitoci suka tabbatar mishi da jininta yayi mugun hawa duk abunda ya ɗaga mata hankali haka yayi kokarin kau dashi. Da takardar ya dawo gida a Tunanin hakan ze zame mishi wata madafa wurin gujewa wannan kadararren aure sede hasashen shi be zama gaskiya ba, a washegarin da safe jama'a masu tarin yawa daga mabanbanta garuruwa ciki harda sarakuna da ƴan siyasa tare da manyan malaman ƙasa suka shaida auren "FAIZAN IBRAHIM KAKA DA AMARYARSA FAUZIYYA SULAIMAN KAKA" kan sadaki dubu ɗari uku lakadan ba ajalan ba. Sanarwan yayi daidai da tsayuwar bugun zuƙata masu yawa sede waenda suka bayyana a fili mutum uku ne, Chak numfashin Fauza ya ɗauke ta yanke jiki ta faɗi dama tun safiyar ranar kuka take, Faizan dake zaune kaman mutum mutumi yaji wani duhu ya rufeshi tsana da kyamar auren na ƙara lulluɓe shi. Fatima da take daga cikin mota dawowar su kenan daga asibiti da mahaifiyarta ta fashe da wani matsanancin kuka me taɓa zuciya, lallai An zalunce ta kuma an ci amanar ta an nuna mata ita ɗin ba jinin GIDAN F ba ce, har Abada bazata manta wannan ba kuma tabbas an taɓa wutsiyar damisar da take bacci cikin matsanancin yunwa... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Biyu* *PAID BOOK* ƊANƊANO **Wannan shafi gabaɗayanta sadaukarwa ce gareki sister zainab Salis, hausawa suka ce yaba kyauta tukuici na ji daaɗi sossai da wannan kyauta Allah ya saka da alkhairi🥰❤️** Ba'a samu kan Fauza ba har Seda aka nemi doctor da kyar ta farfado, in ka ganta bazaka ce Fauzan Jaddah ba ce gabaɗaya ta firgice wadda hakan ya taɓa zuciyar Jaddah da Baba prof sossai. Ya sani auren dole a musulunce haramun ne, sede yana da tabbacin gata ya musu wadda har abada ba zasu mance ba, watarana kuma in sun tuna zasu yi alfahari dashi su mishi Adu'a idan har be riski lokacin da rai ba, sannan sunan gidanshi ya riga ya fara ɓaci ta silar Fauziyya har hawaye ya zubar saboda wani da ya tare shi ya faɗa mishi magana marar daaɗin ji akan ɗiyar ƙanin nashi, sannan ya san halin Fauziyya ba me chanzuwa da sauki bane muddin bata gamu da abunda ya girgiza mata kwakwalwa ba, ko ta shiryu samun mijin da zata samu farin ciki da kaunar en uwanshi ze yi matukar wahala hankalinsu baze taɓa kwanciya da tayi ta musu yawon makaranta alhali sun san da cewa ga hanyar da ta ɗauka ba. Duk zaune suke a babban parlorn nashi, in ka cire yara daga kan Fa'iza dake sa'ar Fauziyya zuwa kan auta Faazila babu wadda babu a wurin kuma tsab ya ɗauke su duka har ya bar fili me yawa saboda girman parlorn na Baba prof. Gyaran murya yayi kan ya fara nasiha me ratsa jiki akan bin umarnin iyaye da kuma kyautata musu, daga nan ya ɗaura da haƙuri da irin girmansa har a wurin Mahalicci, bayan ya gama ya kira sunan Fatima. Ɗago rinannun idanunta da suka haɗu da fuskanta suka kumbure tayi ta kalleshi kan ta maida kanta ƙasa tana bitar karatun da ba'a jima da fara ɗaura mata ba tace "Na'am Baba" Yace "ke zan fara ba haƙuri Fatima, na san mun miki ba daidai ba kina zaman zamanki mun saka mijinki aure, amma ki sani mu ɗin ma bamu isa hakan ta kasance ba idan ba da yardar Allah da sahalewarsa ba, Ke da Fauziyya ƴan uwa ne waenda kuka tashi gida ɗaya ɗaki guda kusan gabaɗaya rayuwarku tare kuka yi shi, babu halin juna da baku sani ba hakan yasa nake jan kunnen ki da ki cigaba da rike Fauziyya a matsayin ƙanwarki, kiyi haƙuri da duk wasu halayen ta kaman yadda na san ki na kuma shede ki me dumbin haƙuri da kauda kai, to ki ƙara akan hakan, Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri'a dayyaba" Kanta ƙasa hawayenta da ta kasa rikewa na ɗiga akan shinfidadden jan carpet da ya cike parlorn tass tace "in shaa Allahu Baba, ai Fauziyya ƙanwata ce kaman yadda ba zan iya cutar da Fa'iza ba haka ba zan taɓa iya cutar da Fauziyya ba, Zaku sameni me hakuri akan hakan Allah ya bamu zaman lafiya" Kowa a parlorn seda ya sa mata albarka, Fauziyya wani irin baƙin ciki ya zo mata wuya, a duniya in akwai abunda ta tsana ya biyo bayan munafurci wallahi ita bata taɓa yiwa Fatima kallon ba munafuka ba, komai nata na munafurci ne, sunanta da Baba prof ya kira ne ya katse mata bitar wasiƙar jaki. Ta ɗago fuskanta da yayi mugun chanzawa ta kalleshi. Yace "Fauziyya ba wai Bama son ki bane muka nace da lallai se an ɗaura wannan aure, ina so ki san gata ne wadda ba kowa ke samun irin wannan ba, Fauziyya ke ce shaye shaye kece club club da hotels hotels babu wani zuri'a da zasu zauna dake ba tare da sun wulakanta ki ba..." Katse shi tayi saboda yadda zuciyarta ke matukar ƙuna idan aka jefeta da waennan kalamai masu daci wadda ta san ba laifin kowa bane illa nata. Hawaye na gangaro mata ta miƙe tsaye tace "Duk nan kuna zargi na ne da zina da kuma kuma shaye shaye, lallai idan har kuna zargina ku dangi na waenda na ɗauka bani da ya su a duniya to babu wadda ze yarda dani kuma!" Katseta babanta yayi yace "Me yasa baki da kunya ne ni kam a rayuwarki Fauziyya? Kin zauna kin rufewa mutane baki ko se na zo nan nayi fata fata dake?" Baba prof ne ya dakatar dashi ya san she's too young for all this duk tauna tsakuwar da suke don kawai aya taji tsoro ne. Yace "kina nufin ki ce duk wasu videos da hotuna naki da aka turo mana ƙarya ne? Ko kuma ganinki sau biyu da Faizan yayi a mabanbanta hotels da mutanen banza cikin shigan banza da buguwa suma ƙarya ne? Ko ganinki da idanuna da nayi shima karya na miki? Ko kuma biyo cikin layin nan da kika yi a buge shima karya ne?" Girgiza kai tayi in confused tace "bani da masaniya akan wasu pictures da videos, shi kuma da ya ganni duk a wuraren na yarda ni ya gani amma na rantse da wanda raina yake hannunsa ban taɓa aikata zina ba, tun da nayi wayo na san menene zina kuma na kyamaceshi wallahi ban san duk yadda abubuwan suka zama haka ba..." "FAUZIYYA!" Yayanta Farhan ya kirata yace cikin jin zafinta "Ki dena rantsuwa akan ƙarya zaki cutar da kanki da kanki!" Shesheka ta ja me karfi tana ciccilla idanunta cikin parlorn, chan cikin sif ɗin baba prof ta hangi Alqur'ani izu sittin da gudu taje ta ɗauka tare da ɗaurawa akai a razane duk suka miƙe suna kallonta har Faizan da duk jijiyoyin jikinshi suka miƙe saboda wani irin tafasa da zuciyarshi ke yi, ji yake kaman in ya kamata da musu da rantsuwar nan ze iya kashe ta. "Na rantse da wanda ya saukar da wannan littafi ban taɓa aikata zina ba kuma ban taɓa ɗaga abun maye da hannuna cikin hayyacina na sha ba, ban san meke faruwa dani ba amma wallahi ko a mafarki ban taɓa aikata zina...." Kwace Alqur'anin da aka yi a hannunta ya sakata saurin ɗagowa se suka Haɗa idanu, yana shirin sauke mata zazzafar mari mahaifiyarshi tayi Charab ta riƙe hannunshi a kausashe tace "A kul Faizan! ban yarda ba ban amince ba, ko a bayan idanunmu ka daga hannu da sunan dukan Fauziyya ban yafe maka ba duniya da lahira!" A razane yake kallon mahaifiyar tashi kan yayi wani magana mahaifinta ya bata mari daya, Farhan ya ƙara mata har Seda bakinta ya fashe. Da sauri Amminta ta miƙe ta nufi kofa tana kuka, Baba prof ne ya dakatar da ita "Ruƙayya!" Tsayawa tayi tana jin yadda kukan ɗiyarta ke ratsa parlorn. "Dawo ki zauna" Mikewa ya yi da kanshi ya nufi Fauziyya ya riƙe hannunta suka dawo dab dashi a ƙasa ta zauna kanta ƙasa tana cigaba da kuka. Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya kan ya sauke ajiyar zuciya yace "Farhan ban yarda ba ko da bakin wasa ka sake ɗaga hannunka akan Fauziyya, bana so ka sake mata kallo a matsayin ƙanwarka ita ɗin matar yayanka ce a halin yanzu" Hannunshi na kan ta yana shafawa ya ɗaga ya kalli Faizan da da kallo guda zaka san ranshi be taɓa sosuwa irin na ranar ba, ko ɗagowa baya yi yadda mamminshi ke fifita wannan yarinyar fiye da farin cikinshi hakan na matukar ƙona ranshi, idan ya kalli matarshi da halin da ta shiga duk saboda ita se yaji ina ma ze iya kawar da ita a duniya ko ze huta. Ɗauke kai baba prof yayi shima kwarai ya san an shiga hakkin shi sede ya za'ayi shine babba dole shine Juji. "Fauziyya ki sani yanzu bakin alƙalami ya riga ya bushe, duk wannan bashi da anfani sannan Qur'ani ya wuce wasa babban hatsari ne amfani dashi wurin rantsuwa se idan har babu yadda za'a yi ne.... Ki yi haƙuri ki rungumi sabuwar rayuwar ki" Kai ta gyaɗa tace "shi ke nan Baba" Shafa kanta yayi yace "Allah ya miki albarka" Babanta yace "Ni kam ba zan ce kiyi hakuri ba, in kin ga dama kar kiyi abunda nake so ki sani shine daga ranar da kika kashe aurenki karki neme hanyar gidan nan, kije chan wurin abokanan watsewarki ku cigaba na yafe ki har Abada, in har kina son Adu'a da farin cikina gareki shi ne ki zauna da Faizan ba tare da wani matasala ba, ko a labari na ji ranar da kika saɓawa umarninshi Fauziyya ban yafe ba, tun rayuwarki baki taɓa saka ni farin ciki ba kullum da fargabar abunda ze fito daga gareki nake kwana nake tashi, sau ɗaya dae zaki yi kokarin proving Cewar ke ɗin ɗiyata ce har ki min biyayya!" Ammi ta ɗago tana Kallonshi "me yasa ne Sulaiman? Me yasa kullum ka buɗi baki alkhairi baya fita in har dae akan Fauziyya ne? Duk wannan hali da ta shiga da wadda take ciki baka taɓa tausayinta ba! Ni kam wlh ban yarda a zalunce ta ta ja baki tayi shiru ba!" Kallonta kawai jadda ke yi, wani lokacin hankalin Ruƙayya na bata mamaki ganin idanunta tana ga yadda Aisha da Prof ke ture yaronsu ba wai don basa sonshi ba se don ganin sun samawa Fauziyyan ƙima da daraja a idanun Faizan ɗin sun kuma hana shi cutar da ita saboda rashin ƙaunarta da baya yi tun tale tale, amma ji inda ta dosa ita, babu wadda ya fi dacewa yayi magana a nan na rashin adalci irin Fatima da mahaifiyarta amma they sat patiently suna sauraron baba prof ɗin. "Ruƙayya...." Ɗaga mishi hannu baba prof yayi, kan ya dubi Faizan "Faizan ga amanata na baka, ka san girman amana ka kuma san hukuncin duk wadda ya ci amana, in ka cutar da ita ina rokon Allah ya saka mata, Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya, an riga an yi mata jerenta so mutum biyu ne kawai zasu raka ta su dawo" Mammi tace "Toh ka ji, nima Amana na baka Fauziyya in ka ci ma kanka! Ka riga kayi karatu babu abunda baka sani ba, ina fata zaka wanzar da adalci a tsakaninsu su biyun" Jadda da hawaye suka zubo mata da kewar fauzin nata tace "Fauziyya kiyi haƙuri! Kiyi hakuri!! Ki ƙara haƙuri!!! Ina tabbatar miki zaki ci ribar wannan haƙuri.. Faizan ga ƙanwarka nima na damka maka amanarta, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Fatima kiyi hakuri kin ji? Haka Allah ya tsara" Kuka sossai duk su biyun suke kowa da abunda yake saƙawa cikin zuciyarsa, Fauziyya ta ƙudiri aniyar zama ɗiya ta gari for the first time ko don saboda Mammi da Baba prof, ko don babanta yayi alfahari da ita sau ɗaya dae a rayuwarta, bata taɓa saka shi farin ciki ba kap rayuwarta se bakin ciki har hawan jini yake dashi sanadiyarta, zata yi hakuri har taga yadda Allah ze yi da ita a wannan gida da yafi kabari ko wuta a gareta.... Kowa yana ta kara yi mata nasiha har suka fito a yammacin zasu tafi Abuja inda nan ne gidanshi kuma anan suke zama da Fatima, bata taɓa Tunanin zata yi wani kukan rabuwa da gidan da tafi tsana ba se yanzu da take ji yafi mata sau dubu akan inda za'a kaita a kuma barta chan bata san kowa ba se maƙiyanta, kuka sossai take yi da kyar aka cire ta ɗaga jikin jadda se ta koma na Amminta, daga nan tayi kan mammi ta sha kuka kam, daga karshe ma fa'iza da kullum se sun yi faɗa ta rungume tana kuka sossai, Fatima tuni tana mota. Cikin sassarfa ya fito daga sashensu ba tare da ya kalli ko sashen inda suke ba ya nufi mota sanye da wasu ɗanyen boyel me taushi da tsada farare sol, hulanshi light ash da fari tangaran ya zauna mishi sossai haka takalmin shi half cover ce me ainihin kyau da tsada ta bayyana Fararen digadiginshi da kaman baya taka kasa. Baba prof da ya bishi da kallo yana murmushin yadda duk yayi kicin kicin da rai yace "Faizan!" Juyowa yayi se yayi kaman yanzu ne ya kallesu alhali tun fitowarshi ya san suna wurin, nufansu yayi kanshi kasa yace "Na'am baba" Jadda, momma da Baba Alhj duk babu wadda ya fito Amminta kuma ta juya mata baya, da Yaya Fadeelah da wata ƴar uwar su Baba prof zasu tafi, Kallonsu yayi yace "ku je ku shiga mota ga mijinta ze zo da ita yanzu" Kanta ƙasa tana shesheka duk masu rakiya suna tsaye cike da tsakar gidan ana ta mata Adu'o'i. Hannunta baba prof ya riƙe ya sanya cikin hannunshi a tare suka ɗaga suka kalli baban se suka kalli juna, dukkansu suka ɗauke kai, gyalen ta baba prof ya sake ja ya rufe mata goshi yace "Allah yayi muku albarka! Allah ya tabbatar muku da farin ciki a wannan tarayya ku je kuna cikin adu'o'inmu a kullum, Fauziyya karki manta duk abunda na ce miki kinji?" Kai ta gyaɗa, hanya ya nunawa Faizan se ya juya riƙe da ita suka nufi mota, dole ya biye mata suna tafiya kaman ba zasu taka ƙasa ba don haka tafiyar ta, idanun mutane da Baba ya sanya ya saka hannu ya buɗe mata gefen ta shiga ya gyara mata kayan ta kan ya rufe kofar fatima dake gefe ɗaya ta ja tsuka me karfi, gaban motan ya shiga Farhan ya ja suka fice kan na su yaya fadeela ya biyo bayansu. Basu tsaya ko ina ba se Airport, suna parking ya fita ya shiga ciki yana waya kaman yadda tun da suka fita daga gidan waya yake, Fatima fushi take dashi kaman shine ya ɓarar mata da ciki hakan yasa itama be kula ta ba, yaya fadeela ce ta zo ta riƙeta suka shiga ciki Fatima da Ya kaka suka biyo su cikin mintuna ya gama komai, ya zo ya Mikawa kowa tickets nashi suka wuce suka yi checking suka shiga jirgi. Banda ajiyar zuciya babu abunda take saukewa, ba wannan ne karonta na farko shiga jirgi ba Dukda duk gidansu babu wadda ya sani sede tana yawan zuwa Abuja da friends nata kuma da jirgi hakan yasa bata ko nuna alamar tsoro ba, jirgin na daidaita a sama ta yaye gyalen ta sbd zafi, daga inda take tana hangar yadda Fatima ta kwanta a jikinshi yana riƙe da hannunta da alama rarrashi yake. Kau da kai tayi tare da tsaki tana kallon window ta fara Tunanin rayuwata Daki-daki....duk me ya jawo waennan abubuwa da suke faruwa? Shin wacece ita tun daga farkon fari? A take tunaninta ya daka tsalle yayi baya daga inda ta fara sanin wacece ita... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari.                🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Uku* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️** *SOME YEARS BACK* "Fauxa! Fauxa!!" Muryar ke fitowa daga tsakar wawakeken gidan yana amsa kuwwa a duk saƙo da saƙo na cikin gidan, har matsakaiciyar matar ta iso kofan ɗakin tare da yaye labulen sbd kofar dake wangale bata fasa kiran sunan ba. Turus! ta ja ta tsaya tare da wara ido Kalmar "kan uban chan!" Ya fito daga matsakaitan laɓɓanta. "Fauziyya! Ashe sunanki daaɗi yake min da zan kama in yi ta kira kina ji ki min banza? Ni sa'ar ki ce? Ko kin maida ni irin su fa'iza ne?" Kyakyawar matashiya ce me ɗauke da coffee colour skin, irin skin ɗin nan da ake kira glass skin da ake wa magana na zaune saman bed me yanayi da gadaje irin na hostel hannunta chocolate ne na bounty tana sha, a hankali ta ɗago manyan idanunta  da kwayar suke kalar Grey ta watsawa matar tare da motsa kyawawan siraran lips ɗinta wadda ya saka cikakken girarta me cike da gashi suka haɗe wuri guda cikin kunkuni tace "Ai an san inda mutum yake ba se a zo a same shi ba, sai an yi ta mishi kiran kasuwa!" Ta karasa da murguɗa baki. Wara idanu matar tayi tace "Me kike cewa?" Da karfi tace "ni ban ce komai ba, gani..!" Tayi maganan tana dirkowa ba tare da ta bi matakalar da aka tanada don hakan ba ta je gaban matar ta tsaya kerere, tsiririya ce me kananun shekaru bata da kauri da matukar wuya ta haura 16yrs karamin shape da take dashi ya haɗu da tsawon ta ya bata wani kyaun sura na musamman, manyan idanunta da dogon hancinta zuwa lips ɗin ta sun taimaka wurin fitar da ainihin kyaun da Allah yayi mata musamman in ka Haɗa da yanayin skin color ɗinta. "Ki wuce ki je ki yi min wanke wanke tunda zuwa Islamiyya ya gagareki, Fatima bata samu tayi ba sbd lokacin islamiyya da ya shiga" Baki ta turo tace "ni ba zan yi wanke wanken da ba na rana na ba fa! Me anfanin rabawar to in an san za'a zalunci mutum? Ni de! Ni de......" Ɓassss haka karar Marin da aka yiwa bakinta ya bada sauti da sauri ta ɗago don ganin waye ne ta sauke mishi tijarar ta da be bar kan kowa ba, se suka Haɗa idanu da Ya Farhan zaro mata idanunsu iri ɗaya yayi yace "fitsararriya ana magana kina yi, ki wuce ki je maza ki kama wanke wanken nan tun ban sauya miki kamanni ba.." Baki ta zumburu tana kunkuni "mugu, azzalumi..!" "Me kika ce?" Tace "cewa nayi to bari na fito" Ta Raɓa ta wuce tana ci gaba da kunkuni musamman da taji Aunty Amarya na cewa "da baka kai mata hannu ba ai Farhan, yaran ne se Adu'a yanzu" "Munafuka, guntuwa..!" Ta faɗa bayan ta sauka tana bin kan interlocks da suka zagaye sashen wadda har daga wajen karamar kofar da nake hange a buɗe su ke zube. Tsakar gidan an yi kaman roundabout na interlocks inda tsakiyar kyakyawar bishiyar Almond wacce aka fi sani da umberalla ta kawata gidan, chan gefen kitchen da store ɗinsu aka yi wurin wanke wanken dake lailaye da tile, Fatima ta riga ta gama Haɗa wanke wanken har ruwa da komai, farawa tayi tana me cin alwashin wlh ranar wanke wankenta baza tayi ba sede Fatiman tayi. Tana wanke wanken tana ta bubbuga kwanuka har Seda Ammi ta leƙo tace "ke kam lafiyanki kuwa?" Kallon farar matar tayi wacce suke ɗan yanayi ta tsawo da hanci tace "ƙalau Ammi" Girgiza kai tayi ta koma tana sauke labulen ta duk ta ji abunda suka yi da Amarya, bata mamakin halayen Fauxa don kowa ya kwana ya tashi ya san wacece Fauxa a gidan, zama tayi cikin kujerun parlorn nata tana ta tufka da warwara wadda bata rabo da shi a kullu yaumin na kwanan duniya. Har Fauxa ta gama wanke wanken ƴan islamiyya basu dawo ba, hijab ɗinta ta janyo daga saman igiya dake ɗaure a tsakar gidan ta saka tana me ficewa kar wannan guntuwar Amaryar ta Haɗa ta da aiki. Masha Allah, tsakar gida ne me matukar yalwa, shimfiɗe da interlock ƙawace da flowers kama daga koraye, jajaye, ruwan ɗoruwa da kuma farare chan gefe parking space ne, se parts babba guda ɗaya, wadda nasu ne na biyun girma se wani ƙarami a gefe, da kuma wadda be kaishi ba daga gefe. daga cikin gidan wani babban masallaci ne da yafi gidan ƙawatuwa, babban kofan ta waje ne sede akwai wasu kofofin kama daga na maza har mata ta ciki. Karamin part ɗin tayi tana shiga ta fara ambatan "Jaddah! Jaddah!!" "Maza to cire min dodon kunne Fauziyya se ki huta" Baki ta chuno wadda kaman ɗabi'ar ta ne na lura, tana shiga parlorn matar bayan ta cire takalman ta daga bakin varendern tiles dake shimfiɗe daga kasan kofan. Parlor ne madaidaici sede ya wadatu kwarai da kayan more rayuwa, cikin ɗaya daga cikin kujerun ta kalli dattijuwar wacce kamanninsu har ya ɓaci da yarinyar tace "Haba jaddaty ai ni dake Bama ƴar haka" Jaddah na jin haka ta san wani jarabar Fauxa ta kwaso, tace "Toh ina ji yanzu kuma me ke tafe dake?" Fauza na zama daga kasa ta kama mammatsa kafafun tsohuwar tace "Ban je islamiyya da karatu ba kuma kin san anjima se Baba Prof ya aiko kirana" Ta faɗa a marairaice "in ba'a yi sa'a ba se ya sa su Faisal zazzane ki" Jaddah ta karasa mata. Raurau tayi da idanu ga tsoro ga neman rigima, babu abunda take tsoro irin bulala kuma tana dakuwa kam sbd rashin jinta da neman rigimar ta babban shine rashin kunya. "Ki taimakeni jadda kar baba prof ya san lafiya ta ƙalau ƙin zuwa nayi, wlh na gaji ne kullum kullum abu ɗaya bawa baka da hutu ko kaɗan" Sallama aka fara daga ɗan harabar na jadda wadda ya sakata saurin cewa Fauza "yi maza hau kujera ki kwanta ki kuma rufe fuskanki da hijabi, maza maza" Da gudu kuwa ta haye tare da janye hijabinta ta rufe fuskan nata. "Wa'alaikumussalam waye ne kaman Farhuddeen?" Saurayin ya karaso yana sanye da blue riga da wando me taushi tare da hular taɓani kaji hadisi yace "nine Jaddah dama baba prof ne ya aikoni in kira masa Fauxa se kuma Aunty Amarya tace min yanzu ta gama wanke wanke baze wuce nan tayo ba" Jadda tace "eyyaa ai kuwa nan ta shigo zazzaɓi ya rufe ta kwab ɗaya dama wanke wanken ma da kyar ta gama shi sbd kawai Amarya ta matsa ne, ka ce mishi bata jin daaɗi" Ko rantsuwa ze yi baze yi kaffara ba lafiyar Fauxa ƙalau tsabar sonta da jadda ke yi yake sa take goya mata baya lokuta dayawa irin wannan, kwafa yayi yana hararanta kan ya juya ya fice. Seda ta tabbatar ya fita kan ta wanckalar da hijabin tana saukowa hakwaranta farare Kal da kaman jera su akayi a waje. "shiyasa nake matukar yinki tawan, shege ya Farhuddeen ina Kallonshi yana harara ta ta wuyan hijab kawai ba yadda ya iya dani ne" Hira suka cigaba da yi da jadda sbd duk jikokinta kowa ya san mutane biyu ne mafi soyuwa a wurinta se kuma aka samu akasi suka kasance WUTA DA AUDUGA. Dab magrib suka ɗauro alwala a harabar na Jaddah suka fito don zuwa masallaci, ɗabi'ar gidan dole duk me kake yi kan magrib ka tabbatar ka gama daga mazan har matan a kira sallah kana cikin massallaci ana kira kuna amsawa kaman yadda addini ya koyar daga karshe ayi Adu'ar bayan kiran sallah se a yi sallah, in an idar za'a yi azkar bayan an gama za'a yi nafila kan kowa ya ɗauki Alqur'ani daga ma'ajiyar Qur'anai na massallacin a hau karatu har zuwa lokacin da za'a kira isha a gabatar ayi nafila karfe takwas na dare kowa ze koma gida don cin abinci da sauran hidimdimu haka da asuba kiran farko dole kowa ya mike ya hau shirin massallaci har yaro ba'a bari, ɗabi'a ne da suka tashi suka tarar ana yi wadda basu san iya tsawon lokacin da aka ɗiba ana yi ba. Tun kan su isa massallacin suka hango ƴan mata wacce zata ɗara Fauxa ɗaya se kuma waenda basu kaita ba su uku se wasu guda biyu da zasu yi sa'anni da ita duk tafiyar daban dabance. Kau da kai tayi ta cigaba da hiranta da Jaddah, bayan sun shige kowa ya zazzauna chan se ga Aunty Amarya da Ammi sun shigo sanye da hijab, daga bayan su mata ne guda huɗu ras, a kallo daɗɗaya zaka iya faɗin kai tsaye biyu Fulani ne, sbd yanayin haskensu se biyu baƙaƙe waenda kuma suke da zane wato tsaga irin na kanuri. Duk gaban jadda suka duƙa suka mika gaisuwa, ta amsa da fara'arta kaman kullum, Fauza ta kalli wata babbar mace daga ciki tana da dirin jiki Dukda tsufa da ya fara bayyana mata kuma fara Kal me yawan fara'a wadda be ɓoye hakwara biyu na hajji dake bakinta ba tace "Mammi sannu, ya ciwon kafan?" Da tsantsar kulawa Mammi ta kalleta tace "sannu Fauxa, kafa da sauƙi idon ki kenan tun asuba ko?" Murmushi kawai tayi, ta juya ga sauran matan kaman dole tace "maami, umma da dada sannunku" Ba don idanun Jaddah dake kansu ba babu wacce zata amsa a cikinsu sbd haushin rainin wayaun Fauxa da a kullum kaman kara karuwa yake, gyaran muryar loudspeaker da ya karaɗe ilahirin unguwan da kiran sallah yasa duk kowa ya samu sahu ya natsu suka fara amsawa. Har zuwa na karshe wato; Laaa ilaha illallah! A lokaci ɗaya duk suka amsa da (laaa ilaha illallah Muhammadurrasulillah sallallahu alaihi wa salam, Allahumma rabba hazihida'awatit tammah, wassalatul qa'imah, aati Muhammadu Al wasilata Wal fadeelah, wa ba'athhu maqaman mahamuda Allazee wa'ad ta. Allahumma Salli ala Muhammad wa'ala aali Muhammad, kama sallaita ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed, wa barik ala Muhammad wa'ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed) "ya ke ƴar uwa shin kin san falalar amsa kiran sallah kuwa? Ko wani irin yanayi kike ko wani irin nauyi ne a gareki in har bakinki ze iya motsawa manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi ya ce 'idan kuka ji me kiran sallah to ku faɗi irin abinda yake faɗi, sannan kuyi salati gareni, domin wadda yayi salati ɗaya a gareni Allah zai yi salati goma a gareshi". Bayan an idar da isha duk gida kowa yayi anan aka fara haramar cin abincin dare, ita kam dae Fauza ko kallon inda su Fatima suke bata yi ba suma ba wadda ya mata magana saboda tuwo ne kuma miyan kuka ko shakureta ake ba ci zata yi ba. Mp wadda kowa da kowa ke dashi personal a gidan me ɗauke da memory 32Gb cikinshi karatuttuka ne na malamai daban daban da kuma riwayoyi kala kala sede fa Fauza nata harda wakoki kala daban daban na mawaka mabanbanta, memoryn take cire wa ta kai school wata friend ɗinta ta saka a wayanta su tura wakoki duk ta harhardace rabi da kwata yanzu ma wakar Auta waziri na Kewa ta saka tana ji murya chan kasa kasa, Sam bata ji shigowar shi ba se jin kiran sunanta tayi cikin kaushin murya wadda ya sakata saurin mikewa tana zare idanu zuciyarta na bugawa, yau idan waƙar nan ne ya shiga kunne Baba ta shiga uku!.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na huɗu* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️** Da wani kalar sauri ta amsa tana me miƙewa tace "Na'am Alhaji! Sannu da dawowa" Be amsa ba se idanu da ya zuba mata, duk cikin yaranshi itace yake jinta na karshe a cikin zuciyar shi, Allah ya gani babu yadda ya iya ne yake zaune da ita amma ya gaji iya gajiya da halayyarta babu randa za'a wayi gari a yini ba'a kirashi kan case ɗin Fauxa ba, a gida babu irin rashin kunyar da baya ji da kunnuwanshi tana yiwa yayyun ta, duk gidan babu wadda baya girmama na gaba dashi se Fauxa, dokarsu kuwa ba a bakin komai yake ba a gareta. "Ki je Baba Prof na kiranki" Daga haka yayi gaba sbd saƙo ne Yayan nashi ya bashi Idan ya shigo ya tura ta, mikewa tayi da hijab ɗinta dogo har ƙasa kaman ta Allah ta fice, harabar gidan tar kaman rana har ta isa babban parlorn na Baba prof dake gefe da shiga kofan sashen nashi da na matanshi, akwai hanya da ze kaika ɗakunan baccinshi kuma akwai wadda ze kaika cikin gidan nashi ta cikin parlorn. Da sallama ta shiga, babban parlor ne me ɗauke da kujerun alfarma, carpet ne me taushi da tsananin kyau malale bisa parlorn duk girman parlorn Seda ya ɗauke tsab, ga kujerun alfarma na asalin royals, chan gefe shelf ne na littatafai har ba zasu kirgu ba. A tsakiyar kujera ta ganshi zaune yana nazarin wani littafi, ta karasa kusa da kafafunshi ta zube tace "Barka da dare baba" Ya kalleta kan yace "yauwa Fauziyya" Fuskanshi ba alamun wasa yace "me ya hana ki zuwa Islamiyya yau?" Wuri wuri ta fara yi da idanu cikin in ina tace "baba... Am dama.. Dama tunda na dawo makaranta ne na fara ciwon ciki shiyasa ban je ba" Yace "kin san Allah yayi mana hani da karya? Ya kuma kwaɗaita mana riƙe gaskiya a kowanni hali? Karki kasance cikin makaryata sbd daga furucinki zan iya cewa kai tsaye ba gaskiya kike faɗi ba, me yasa baki son karatu daga na boko har na Arabi?" Kanta dake kasa ta girgiza tana forming hawaye tace "kayi hakuri" Yace "na haƙura, na san ki da tsanar karya hakan yasa farar ɗaya na gane ki, Fauziyya karatu na da wani irin muhimmanci a rayuwarmu daga boko har arabi, barin ma arabi da ya zama dole wajibi a garemu mu nema, duk girmanka da tsufanka dole ne ka cigaba da neman ilimi sbd shi ze zama haske a rayuwar duniyarka da lahirarka, Allah SWT yace ku sanni kafin ku bauta mini idan har baku sanni ba to ta yaya Zaku bauta mini? Haka kuma Ayar farko da ta fara sauka da Kalmar 'Iqra' ta fara to meyasa bazaki dage wurin gyara gobenki ba?" Nasiha ya cigaba da yi mata da misali da ayoyi da hadisai masu magana akan neman ilimi musamman Addini, tana shiru bayan ya gama ya sallameta ta miƙe ta fice ba wai don ta ɗauki ko abu guda da yace a cikin nasihohin shin ba. Ya kamata ku san wani gida ne haka? Wannan gida da mutane suka mata laƙabi kala kala wasu su ce "GIDAN F" dalili kuwa duka yaran da suke cikin wannan gida sunansu daga F ya fara. Wasu su ce "GIDAN PROF KAKA" dalili kuwa babu wadda be san waye PROF Ibrahim KAKA ba a faɗin Nijeriya da ma kasashen ketare. Dalilinshi ne ya sanya gabaɗaya unguwan tasu ta tashi daga ainihin sunanta ta koma "UNGUWAN ƳAN BORNO" Wannan unguwa na kafe ne a tsakiyar garin Yola na Adamawa state, zagaye yake da barebari Albarkacin dattijon arziki Baba Prof, asalin su ƴan garin Maiduguri ne na jahar Borno, daga uwa har uba barebari ne, a garin Borno Zulaikha wacce yara suke mata laƙabi da Jaddah ta haife su, su biyu ne rak wurin Mahaifinsu Abubakar Kaka, Baba prof wadda Asalin sunanshi Ibrahim Abubakar kaka da kuma ƙaninshi Sulaiman Abubakar Kaka. Mahaifinsu mutum ne me nagarta kuma babban malami a jahar Borno, karatu da karantarwa gadon su ne sbd abunda suka taso suka samu Mahaifinsu da shi kenan, a wurinshi suka fara karatu na addini ya basu ilimi me nagarta musamman ibarahim da kullum karfe biyun dare haka ze tashe shi ya makala mishi redio yana sauraran karatuttukan malamai tun yana gyangyaɗi yana farkawa har ya dawo daga baya idan ze kwanta da kanshi ze cewa Mahaifinsu idan lokacin karatu yayi a tashe shi fa kar a manta. Wani irin buɗewa kwakwalwanshi tayi da Alqur'ani wadda har ya iya qira'o'i da riwayoyi iri iri, a tsakanin ya shiga boko wadda be hana shi yin karatun shi ba, duba da iyayensu girma ya fara kama su gashi shine ɗan su na fari dayake Jaddah tana yawan haihuwa ne suna komawa, haka ta cigaba ko da bayan ta haifi Ibrahim ya tsaya. Shi kaɗai ya buɗi ido ya gani a gidan hakan yasa ya ci alwashin gadar Mahaifinshi, wadda karantawar tashi wata rana yake fata ta zama sadakatul jariya ga Mahaifinshi, yana da shekaru goma sha biyu ya haddace Alqur'ani, hadda marar gargada bare kame kame, be dena karatun littatafai ba har ya shiga jss3 anan ne Jadda ta sake haihuwa bayan shekaru masu yawa inda ta haifi Sulaiman. Shekarar su uku da Sulaiman ya samu scholarship sbd irin kwazo da ilimin shi da ya baza ko ina a cikin garin na Borno, har wasu state ɗin da idan be je musabaqa ba to ze je su debate, quiz, spelling bee da sauransu be kuma taɓa ɗaukan na biyu ba. Madina yayiwa tsinke inda ya dage ya maida hankali yayi degree ɗinshi na farko har kuma lokacin be dena neman ilimin addini ba, bayan shekaru huɗu ya dawo Nijeria. Alhamdulillah be bar iyayenshi haka ba ko da yake chan, ko da ya dawo ya cigaba da taimaka musu da karfinshi, yayinda Sulaiman ya fi maida hankali a boko Dukda dae ba laifi shima yana da iya nashi karatun na addini sede ba kaman Ibrahim ba. A haka ya koma Madina yayo masters fannin kasuwanci, bayan ya dawo ya tafi America yayi degree ɗinshi na uku fannin halayya, anan ne ya dawo Nijeria lokacin Mahaifinsu na cikin hali na ciwo Sulaiman yana jami'a. Wasa wasa Dr Ibrahim KAKA ya zama sananne a harkar musulunci, karantarwa da da'awa babu inda kafafunshi basu taka ba a Nijeriya, wani wurin har jifa suke sha, ruwa, rana, zafi, iska duk ya ƙare a kansu amma basu karaya ba. A haka Allah ubangiji ya karɓi ran Mahaifinsu yana me alfahari da kaɗan da Allah ya bashi masu albarka sede kuma da takaicin rashin ganin auren Ibrahim sbd har lokacin be maida hankali kan mace ba, ina ka fito karatu ina zaka karantarwa, me kaci karatu, me ka sha karatu haka Ibrahim yake. Sulaiman na Bautar ƙasa a Adamawa aka fara hare haren boko haram tashin farko kuma da matukar zafin su hakan yasa Sulaiman ya nemi Yayanshi Ibrahim da ya riga ya zame mishi uba sbd irin respect da yake bashi ya wuce na wa, akan su zo yola da Jaddah tunda apartment da shi baba prof ɗin ya kama mishi me girma ne. Be ƙi ba haka suka dawo cikin garin Yola wadda ya kasance dawowar kenan, wasa wasa Ibrahim yayi wani irin kafuwa sbd mutum ne me zafin nema Sam baya kwanciya kawai yaji daaɗi, a tafiyan su wani kauye ne na mayo belwa ya samo Aisha(Mammi) gani ɗaya ya mata yaji nan duniya itace macen da ta dace dashi ko da ya dawo kan yayi magana Sulaiman ya tare shi da zancen ya samu mata, shima nan ya faɗa musu yayi mata farin ciki wurin jadda harda hawaye. fili babba ya saya ya samu architecture ya tsara mishi yadda yake so gidansu ya kasance na dindin din kuɗi ya zube aka soma aiki, wata uku aka gama komai sashe uku ne se masallaci da islamiyya babba daga jikin gidan, a lokacin aka yi bukin su. Yadda faɗan boko haram ke tsamari a Maiduguri yasa yake ta sayan kananun Gidaje a unguwan yana saka ƴan uwa da abokan arziki kusan almost rabin unguwan shi ya mallaka musu Gidajen su kuma in har ya kiraka akan ka dawo yola to wannan gida naka ne halak malak. Wani irin buɗi yake samu sbd alkhairanshi dake da matukar yawa, basu shekara biyu da Mammi ba ta haifi Yaron su na farko da ya ci suna FAIZAN(Genorous/Me karamci ko kuma beneficence wato me aikata mai kyau), bayan wata uku da haihuwar Faizan ruqayya(Matar Sulaiman) itama ta haihu ta samu ɗiya mace wacce ta ci sunan Fadeelah(Virtuous wato tagari). Ba'a rufa shekara ba Aka sake baiwa Baba prof mata Hussaina daga Wani kauye na jalingo da ake kira Sunkani, itama Fulani ce ba'a ɓata lokaci ba aka yi bukin nasu, shekaranta ɗaya Mammi kaman yadda Faizan ke kira ta sake haihuwar ɗa namiji Faahim(me ilimi or mai fahimta). Ammi itama ta sake haihuwar Falaq(Ketowar Alfijir), Anan hankalin Ruqayya ya soma tashi, dama wani irin zama suke yi marar daaɗi da Maa wadda musabbabin abun Ruqayya ce, tunda ta saka kafa gidan ta fahimci nisan dake tsakanin Ibrahim da Sulaiman kaman nisan dake tsakanin sama da ƙasa ne, wai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau. Bata kara shiga tunani ba seda taga irin girmamawar Sulaiman ga Ibrahim kai tsaye zaka iya cewa matsayin mahaifi ya bashi don ko ratar dake tsakaninsu rata ne me girma, randa ta haihu kuwa taga Sulaiman ya ɗauki yarinyar musamman ya kaiwa Ibrahim shi ya mata huɗuba ya sa mata suna alhali ta riga ta faɗawa Sulaiman sunan da take so a sawa yarinyar, ba karamin rikici suka yi ba akan sunan Fadeelah sede Sulaiman ya fi karfinta haka ta bari, sede daga ranar maganan arziki ita da Mammi babu dama chan sama sama ne, se kuma gashi Mammi na jera maza Ita kuma tana jera mata alhali Ibrahim da Sulaiman basu bambanta dukiyar su ba. Zaman doya da manja ake yi a gidan har Amaryar baba prof itama ta haihu ta samu mace, Falusha(Haske). Bayan haihuwan Falusha Baba prof yayi tafiya Maiduguri inda ya dawo da Auren Zainab, ba karamin rikici aka yi da Hussaina ba kan ta saduda, Mammi kam fatan alkhairi kawai tayi mishi, a lokacin ma tana da tsohon ciki inda ta haifi Fahad(Damisa) ba'a ɗau lokaci ba Ammi ta sake haihuwan Fadyaa(sadaukarwa). Hussaina da yaran suke kira Maami ta sake haifan Farrah(Florence nau'in haske), har lokacin zainab bata haihu ba, Baba prof ya karo aure cikin ƴan gudun Hijira Sakinah itama barebari ce usul, a tare suka fara haihuwa da Zainab wacce su Faizan ke kira Umma, ita ta samu Faraj(cure, waraka kenan) yayinda sakina ta samu Farzan(me wayau). Daga nan dukkansu basu sake haihuwa ba seda aka ɗau lokaci Ammi kuwa ta haifi maza biyu a tsakani Farhan(farin ciki) da Faris (horseman). A lokacin Baba prof ya kara sashe a gefe da masallaci sbd matasan yaran da suka fara tasowa, Mammi ta sake haihuwar  Farida(ta musamman ko lu'ulu'u me daraja) daga nan har yau bata sake haihuwa ba. Bayan nan Sakinah (umma) ta sake haihuwan Farhuddeen(farin cikin addini). Sulaiman ya ƙara aure inda ya auri sumayya ta zo gidan da ƴarta Fatima, sumayya sun haihu tare da Ammi(ruqayya), Ammi ta haifi Fauza (triumphant wato nasara) yayinda sumayya ta haifi fa'iza (Gain, wato samu). Bayan su Fauxa, sumayya ta kara yara uku Fadiyah(me kyau), Fakiha(fruits) se Faazila(gaskiya) su kenan yaran gidan karan katakap. Mammi na da huɗu Faizan, Faahim, Fahad da farida. Maami na da biyu Falusha da Farrah. Umma na da guda biyu Faraj da Farhuddeen. Daada na da guda ɗaya Farzan. Gabaɗaya yaran na Baba prof guda 9 ne Allah ya bashi. Se Alhaji wato Sulaiman. Ammi na da shidda Fadeelah, Falaq, Fadyaa, Farhan, Faris se Fauxa. Aunty Amarya na da huɗu Fa'iza, fadhiya,Fakiha da Faazila. Gaɓadaya yaranshi 10. Gidan na da wani irin dokoki ne wadda duk tsari na addini ne, yaran kuwa akwai matukar shakuwa, tausayi da kauna irin ta ƴan uwantaka a tsakaninsu Baba prof baya wasa da tarbiyar su ko na miskala zarratin, duk kuma abunda ze shimfiɗa hannu bibbiyu Alhaji ke karɓa. Ya ƙara samun wani girma ne a unguwan sbd yadda baya banbance ƴaƴanshi da na dangin shi Dukda ba komai yake da iko akai ba sede fa ya san duka yaran don dole a islamiyya ɗinshi zasu yi karatu kuma shi da kanshi yake koyar dasu sbd dumbin falala dake cikin koyarwa da yara addini babban sadaqatul jariya ce wacce bata gushewa har se me wannan ilimi ya gushe idan kuma akwai wadda ya koya daga wurin ɗaya haka ze yi ta gudana har illa ma shaa Allah. Wannan al'ada itace zaɓarwa yara abokan zama masu nagarta, kawai ze kira ka a waya akan Zaku yi baƙo ze zo wurin wacce kaza, ko kuma wane kaza na gidan ka yaje wurin wacce kaza na gidan wane, a haka ya Haɗa wani irin bond me girma tsakanin kaɓilarsu ta barebari da suke nan unguwar, kuma duk zaɓin shi suna alfahari dashi sbd baya taɓa zaɓin banza. Mata da mazan gidanshi kan yi karatu har matakin degree ma idan har maneminki be fito ba, sbd ya san muhimmancin karatu ya kuma san karatu wani makami ne da zaka barwa yaro wadda ba ze taɓa tagayyara ba hakan ne dalilin da ya sa ko maneminki ya fito baki fara makarantar gaba da jami'a ba dole akwai yarjejeniyar ci gaban karatun ki don gudun halin rayuwa. Faizan pilot ne wato matuƙin jirgi wadda aka fi sani da Captain Faizan matashi me jini a jika, kyaun fuska da na hali, ilimi both Islamic and western, his father's favorite, the first born to the house of F, har yau Allah be yi yayi aure ba kaman ba Baba prof ne ya haife shi ba. Fadeelah tana auren wani businessman suna zama a Australia with kids. Faahim Navy ne, an aura mishi Fadyaa suna da ƴaƴa biyu. Auren da saida aka kai ruwa rana da Ammi ta saduda. Falaq har yau bata yi aure ba sbd rashin lafiya da take fama dashi. Fahad na aiki da inland revenue with a wife and a kid. Farida tayi aure some months ago with a costume officer suna zaune Lagos. Falusha and Farrah duk tare aka yi aurensu su biyun duk suna yola suna auren ma'aikatan Gomnati. Faraj, Farhan da Farzan duk suna final year of their studies a Apti American University mabanbantan courses. Farhuddeen da Faris suna SS3 Fatima na SS2 Fauxa da fa'iza na SS1 Fadhiya js1, Fakiha pri5 and Faazila pri3. Tou readers ya kuka ji GIDAN F? A tunaninku duk wani haɗin kai da kaunar juna da zaman lumana dake wakana a wannan gida me cike da addini me ɗaurewa ne har abada? Sheɗan ze iya barin ɗaurewar wannan haɗin kan da kaunar kuwa? Akwai wasu abubuwan da ban sa cikin tarihin gidan ba a hankali a hankali Zaku fahimta in shaa Allah, mu je zuwa🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Shidda* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️** "Wa'alaikumussalam warahmatullah sannu da zuwa Mammi" Cewar Fauxa tana me sakin murmushi. Jaddah ma sannu Da zuwa ta mata, Seda ta amsa na Jaddah kan tace "Fauxa ke kam ba zan amsa ba, riƙe kayan ki" Dariya suka yi duka tace "yi hakuri maa in shaa Allahu zan zo" Tace "na gaji da ji, ke kam gidan mu kaman wadda aka yiwa farraku dashi idan ba'a compound ba ko nan sashen Jaddah ba'a ganinki Sam?" Dariya kawai take yi, wlh ita tana rasa dalilin da yasa take kasa shiga sashen na Baba prof, duk matanshi ma dama banda gaisuwa Mammi ce kawai take sakewa sossai, tana son matan ba tare da ta san dalili ba. "Ina yini Jaddah? Fatan mun sameku lafiya?" Cike da so Jaddah ta amsa mata, duk cikin surukanta babu mafi soyuwa a gareta irin Aisha, matar ta dabance cikin mata, tana da kawaici sossai gata da fara'a bazaka taɓa ganinta bata murmushi ba, tana da son mutane da jan kowa a jiki bata damuwa da kai nata ne ko ba nata ba, tana da kirki fiye da zato, duk cikin matan na Baba prof babu me shiga kitchen da kanshi yayiwa Jaddah girki na musamman ya kuma tako ya kawo ya zauna suyi hira sossai irin Mammi. Dukda tana yawan fama da matsanancin ciwon kafa se ta kwana biyu uku ma bata iya tafiya idan ciwon ya tasar mata amma hakan be sa tayi kasa a gwiwa wurin kula da mijinta da surukanta ba, kuma ita da kanta take taya baba prof kula da mahaifiyar tashi mace ce da a duk lokacin da mijinta ze shigo da wani abu a Leda bazata taɓa karɓa ba se ta tambayeshi ina na Jaddah? Idan har ya manta ko be saya ba sbd ganin ta girma da abun ko wani abu haka zata sa ya koma ya sayo, tana da wani ƙima na daban a zuciyar mutanen gidan musamman mijinta da surukuwarta. "Aisha ya ciwon kafan? Fatan kin ji daaɗin maganin nan na Gamborun gala?" Tana murmushi tace "wlh na ji daaɗinshi sossai Jaddah, kafa yayi sauƙi sosai" Jaddah tace "Toh Allah ya qara afuwa" Suka amsa da Ameen. Chan cikin hiransu Jaddah tace "ni kam Aisha kina ji daga wurin wannan Miskilin nawa kuwa? Kwana biyu be kirani ba fa" Maa tace tana murmushi "eh Jaddah, ya ce min ze shiga ƙasar da bashi da simcard ɗinta idan har ze fi kwana biyu to ze saya Sim ɗin sbd mu ji lafiyar shi idan kuma ba ze wuce hakan ba in ya bar ƙasar in shaa Allah ze ƙira" Jaddah tayi tsaki tace "ba ga irin ta ba, mutum ne kullum a sama kaman tsuntsu fisabilillahi idan ya zo nan fa ya zube Sima simai se ki dauka kamfanin mtn ne, wani idan ya manta na wace kasa ce kuma be da lokacin gwadawa sede kiji katttt ya karya ta" Mammi na dariya zata yi magana kenan Fauxa ta miƙe Tsam tayi ɗakin Jaddah fuskanta babu yabo babu fallasa, da idanu duk suka bita Seda ta shige kan Jaddah ta zabga tagumi cikin jimami. Mammi tace "Jaddah Dan Allah ki dena sa damuwa a ranki sbd yaran nan kar kije wani ciwo ya kama ki, har yanzu dukkansu yara ne in Shaa Allah gaba ko ance su yi baza su yi ba" Jaddah tace "se yaushe kenan Aisha? Karki manta Faizan ya baiwa Talatin da biyar baya wannan ta fi sha shida amma ace se gaba? Wani gaban kuma bayan wannan? Wlh Allah ya gani babu abunda ke ci min tuwo a ƙwarya irin tsananin rashin jituwar yaran nan, har tsoro irin ƙin da suke yiwa juna yake bani kwata kwata ɗaya baze taɓa bada fuska ayi maganan ɗaya a gabanshi ba?" Mammi tace "ni na fi ganin laifin shi babban kwabon nasu ai, na yi faɗa har na gaji amma ya kasa fahimtata" Jaddah tace "ya Allah ka kawo mana karshen wannan abun nasu" Mammi ta amsa da Ameen suka kama wani hiran kuma se dab magrib kowa yayi alwala suka tafi masallaci a tare. Bayan kwana biyu Tunda ta tsefe kanta bata yi kitso ba gashi har yau Sunday, barta dae da neman tsokananta wadda bata rabo dashi, ita da fa'iza ce tafe suna hira sbd duk gidan babu wacce suke shiri kuma suke ƙaunar juna kaman fa'iza babu wacce kuma ta tsana irin Fatima in ka cire Faizan. Abun nata kaman jinnu, tana son fa'iza sbd haƙurin ta ta kan yi hakuri da duk wani halinta tana yawan kare ta, in kaga sun yi faɗa to akan Fatima ne, Fatima na son nuna mata uwarsu ɗaya da fa'iza ita kuma ta tsani hakan, idan kuma fa'iza tace mata kar ta biyewa Fatima su yi ai jinin dake yawo a jikinta shine yake yawo a nata jikin tunda uba suka Haɗa se ta ce ai fa'iza ta goyi bayan Fatima alhali Agola take a gidan Anan zasu yi faɗa su Rabu Toh Fauxa da zuciya se ayi kwana biyu bata huce ba hakan yasa shirin su da fa'izan yake yawan ja baya. Sashen Jaddah suka shiga tana zaune tana jan chasbi Fauxa ta zube kan kujera tace "Jaddah wainar fulawa nake son ci na manja da yaji me tafarnuwa" Jaddah tace "se ki ci ai, ni kam ban yi tunanin akwai fulawa a gidan nan ba" Fa'iza tace "kash! Ya kenan Fauxa gashi namu ma babu ya kare" Mikewa Fauxa tayi tace "mu je wurin Mammi mu yi, dama wlh tun jiya ban je na gaisheta da ciwon kafan nan nata da ya tashi ba" Ficewa suka yi Jaddah bata ce komai ba har suka fice, ko da suka isa a ɗaki suka sameta kwance a ƙasa an shimfiɗa mata bargo me taushi da pillows, ƴar yayarta da zata ɗan girme su da take hannun ta tun bayan auren farida ita ke taimaka mata tunda bata karatu. Sashukan nan basu da maraba da sashen su Fauxa, se na kitchen da akwai cikin kowanni sashe saɓanin nasu, se kuma na yawan ɗakuna wadda nan kofa biyu ke fuskantan biyu, na Mammi ne na farko wadda babban parlor ne sossai da kitchen da ɗakuna biyu, hakan ne kuma a kowanni ɗaki, sannan akwai kitchen na waje da kowacce me girki a sashen take girki ranan girkin ta, tsakar gidansu bishiyar cashew ce me ni'imtacciyar inuwa. "Fauxa yau ke ce a sashen namu? Lallai za'a yi ruwa da kankara" Fauxa na murmushi ta zube kasa tace "sannu Mammi ina yini? Ya kafa?" Mammi tace "Alhamdulillah Fauxa da sauki sossai har ɗazu ma na taka zuwa toilet" Fauxa tace "Allah ubangiji ya ƙara sauki" Da Ameen ta amsa, fai'za ma ta gaisheta. Fauxa tace "Mammikina da fulawa? Wainar fulawa nake son yi bamu da fulawa haka Jaddah ma" Ta karashe tana karya wuya Mammi tace "Ah Kice abunda ya kawo ki kenan ba zuwa na musamman da kike cewa ba" Tana dariya tace "Allah ba haka bane dama nayi niyyar zuwa" Mammi tace "ba za'a rasa fulawan nan ba ku duba a kitchen na cikin nan se kuyi, dama akwai yaji da Zuwaira(kanwar ta) ta kawo min ma jiya da alama ze yi daaɗi" Cikin jin daaɗi Fauxa ta mike, fa'iza ta bi bayanta suka yi kitchen. Anan suka kwaɓa suka fara suya se suka fara na manja sbd yadda Fauxa ta hanata sakat Seda suka yi me yawa se suka koma man gyaɗa sbd shi fa'iza ke so, suna cikin yi se Fa'iza tace "ni bani manjan ma in yi mixing kaɗan yadda ze bada wani dandano me armashi" Fauxa tace "Wallahi bazan bayar ba ka jimin wayau, kowa ya ci da plain abunda yake so" Musu suka fara, fa'iza ta kai hannu da niyyar fusgan manjan Fauxa ta ɓalle da gudu daidai kofar kitchen ɗin taji taci wani uban karo da wani broad chest me yanayi da rock, gabaɗaya manjan ya zube a jikin kayan mutumin. A hankali na kai idanuna bisa mutumin da aka kwararawa manjan Masha Allah, kyakyawar matashi ne me tsawo sossai a kamannin fuska zaka iya cewa kaman an tsaga kara da Fauxa, banbancin nasu kaɗan ne shi ɗin fari ne Kal saɓanin Fauxa, haka idanunshi wasu irin Ash ne me walƙiya.. Ko kaɗan bashi da rama wani irin tsayayyen namiji ne da yake da jikin every woman dream, daga ka ganshi zaka san cewa ma'abocin workouts ne, yana da dogon hanci sak irin nata da lips wadda suke iri daya da nata kaman an shafa musu cherries yadda suke kyalli, yana da gashin saje gyararre me kyau wadda har zuwa gemu amma be cika yawa ba, a gyare tsab baƙi sidiƙ se shining yake yi wadda ya kara fitar da ainihin kalar farin fatar shi, daga yatsunshi na hannu zuwa na kafa dogaye ne a gyare suke tsab gwanin burgewa, yana da wani irin kwarjini da farin jini sede fa ma'abocin tsare gida ne, Miskilin bugawa a jarida ne sannan yana da murɗaɗɗen hali da zama dashi se ka shirya. Sanye yake da Fararen kaya Kal Kal Jean da shirt designers kafafunshi sanye da Dior lufas masu kyau, kamshinshi a take ya baza lungu da sako na kitchen ɗin, kyawawan idanunshi na kafe kan inda manja ya zube a Rigan nashi kan a hankali cikin tsantsar natsuwa ya ɗago birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata. Wani irin faɗuwar gaba ne ya risketa ga tsoro da ya kusa sumar da ita, cikin da na sanin fara sha'awar wainar fulawa da ta yi a yau ta fara ja da baya, wannan baƙin azzalumin yanzu se ya mata abunda se ta gwammaci kiɗa da karatu, ita kanta fa'iza dake tsaye jikin gas a take ta saukar da pan ɗin sede ta kasa kashe gas ɗin se rawan tsoro jikinta ya ɗauka. Kokari yake yayi controlling ɓacin ranshi sede ganin ko sannu bare yi haƙuri ta kasa ce mai yasa ya ɗaga kafafunshi ya fara takawa zuwa gareta, a duniya ya tsani ganin yarinyar halayen ta, neman tsokananta, rashin jinta, rashin kunyarta duk ya tsana bata yi mishi don babu fuskan yi ɗin sede ya kan tsinkaya tana yiwa wasu, sannu be taɓa Haɗa su ba tana karama in har zata zo kusa dashi se ya mata mugunta tun tana zuwa har ta dena hakan ya dasa mata tsoron shi, Sam baya zama a inda take sbd hakan itama ta koyi kin zama a inda yake, idan kana son ganin ɓacin ranshi ka ce suna kama yanzu se ku samu matsala, ya kan yi mamakin yadda kowa a gidan complain ɗinshi baya wuce Fauziyya har iyayensu maza, shi yana ganin iskancinta wuri ya samu bata sami me saita ta bane, hakan ya sa ya buga Mata tambarin annoba don shi da annoba yake kiranta. Ganin da gaske nufanta yake ga fuskanshi babu ɗigon rahama yasa tayi kokarin gudu, taku ɗaya yayi ya saka mata ƙafa hantsilawa tayi zata faɗi, garin neman abunda zata dafe don gujewa kaiwa ƙasa ta ɗaura hannunta na dama bisa kan gas ɗin da yake kunne, ba wutan bane karafunan da suka riga suka jima da ɗaukan zafi sossai ne suka aika mata da wani irin raɗaɗin azaba zuwa kwakwalwanta har bata san sadda ta saki wani ƙaran azaba ba tana rike hannun. Wani mugun murmushi da ko haƙorin shi be bayyana ba ya saki kan ya juya ya fice daga kitchen ɗin, da gudu Fa'iza ta kashe gas ɗin kan tayi kanta ta kama hannunta a tsorace tana kallon fuskanta yadda hawaye ke ambaliya kaɗai zaka gani ka san tana cikin wani hali ga zufa dake aikin tsatsafo mata. "Sannu Fauxa! Sannu" Mammi ce jin ihun Fauxa yasa ta lallaɓa ta fito a hankali ta nufe su tana cewa "Subhanallah me ya same ta? Konewa tayi?" Cikin kuka Fauza tace "mammi wannan azzalumin ne ya saka min hannu akan karafunan gas, Wayyoooo hannuna!" A hankali Mammi tace "FAIZAN!" Don shi kaɗai Fauxa ke cewa Azzalumi. Da sauri Mammi ta cewa Fauxa "ɗauko akamu yi sauri gashi a chan in saka mata kar ya tashi" A hankali ta karasa gareta ta ɗaga ta tare da riƙe hannun har ya tashi gabaɗaya tafin na hannunta yayi wani kalar bororo, wani irin tausayinta ne ya rufe Maa sbd ta san zafin wuta ba daaɗi amma se ta saɓawa Faizan, ashe kaddarar ƙone wa ya kawo ta sashen nata da ta jima tana mita akan rashin zuwan nata, da kuwa ta san Faizan ma ze zo yau da bata ma bari sun yi wainar anan ba, wani irin abu ne haka? Akamun fa'iza ta kawo ta kwaɓa ta saka mata har lokacin kuka take, tayi tayi ta ci wainar da saura kaɗan ma su kammala ta ƙi tace ta koshi, cikin rashin jin daaɗi Mammi ke bin ta da ido har ta fice se ta saka fa'iza juye wainar a flask ta bita dashi su je su ci a gida don ta tabbatar ko sashen Jaddah Fauxa bazata kara zuwa ba se an tabbatar mata da baya gari. Haka kuwa aka yi da fa'iza ta kawo mata ma ƙin ci tayi, Allah ya isa kuwa ta ja mishi yayi cikin kwando, gashi Ammin ta bata nan ta tafi kauyensu jiya uncle ɗinta ya rasu, da magrib ma da kyar ta samu tayi alwala ta tako zata fito zuwa masallaci kenan ta tsaya Chak jin muryar dake tashi a speaker na masallacin, tsaki ta ja ta koma ɗaki nan tayi sallah har isha bata fita ba, a Cewar ta bazata bi sallar azzalumi ba don Allah ba karba ze yi ba. bayan tayi isha ne ta kunna speaker ɗinta iya daidai jin kunnen ta ta saka waƙa abunta anan mood ɗinta ya fara dawowa daidai. Tana ji su fai'za na cin abinci bata fita ba, idanunta a lumshe take jin Fatima na fesawa fa'iza ita duk yadda take jin karatu bata taɓa jin me natsuwa da kwantar da hankali irin na Ya Faizan ba, fa'iza na dariya tace mata "zaki ce haka ne ma tunda kina son shi" Fatima ta ce "ban gane ina son shi ba? Ko de muna son juna?" Fa'iza tace "ai ko makaho ya shafa ya san ke ce kike mahaukacin son ya Faizan shi ba take yake ba, ba ta yadda za'a yi yana son ki ne ke karan kanki kan ya miki magana ɗaya se kinyi hamsin, sannan ya tafi yayi wata da watanni ko a wayan Jaddah baze ce a baki ku gaisa ba idan ma yana jin kunyar Mammi kenan, ni wlh bana son miki kasancewa da ya Faizan ina so ki samu me son ki inda zaki ji...." Tsawa ta daka mata "dakata fa'iza! Don ina maganan soyayyata dake ba shi yake nufin ki gayamin duk wani banzan maganan da ze fito daga bakin ki ba idan ma ba kitsa miki aka yi ba don baki da wannan wayaun, to henceforth as from today kika kara min irin wannan maganan wlh se nayi mummunan saɓa miki ni ba sa'ar ki bace" Fa'iza tace "Ya Fati daga faɗar gaskiya?" "Bana son gaskiyar ki riƙeta" Daidai lokacin Fakiha ta shigo da gudu tana shelan ya Faizan ya ce a je a karɓi tsaraba yana sashen Jaddah. Da sauri duk suka tashi suka fice daga tsakar gidan. Taɓe baki Fauxa tayi, Fatima na neman magananta ta tabbatar harda shagube a zancen nata, amma ba ta ita take ba yanzu ta samu ta warke shine damuwanta kuma wlh akan Fatima zata rama abunda ya mata tunda shi azzalumin ya fi karfinta. Chan da yunwa ya fara damunta don ko abincin rana bata ci ba ta sa a zuciyarta zata ci wainar fulawa yasa ta mike ta fito a hankali ta nufi kitchen, ja tayi ta tsaya jin kuka na tashi a hankali.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Bakwa* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️** "Aunty wallahi son shi ze kasheni! Kin Reneni ne da soyayyar shi hakan ya bani karfin gwiwar kwallafa rai a kan samunshi sede gashi har yanzu shi bana gabanshi, yanzu har fa su fa'iza sun san nice me cusa kai a gareshi shi ba ta ni yake ba! Aunty kinga wulakancin da ya min a gaban su Fa'iza da kannenshi maza?" Ta karasa tana me kara rushewa da kuka. Aunty tayi saurin sa mata hannu a baki tace "Haba Fatima! Me yasa ke kam kullum rashin haƙurinki kara gaba yake? Na faɗa miki na kara jadadda miki idan har Faizan be aureki ba to wallahi ba ze auri wata ba, wannan alqawarin da na daukar wa kaina ne tun kan in shigo gidan nan, tufka nake ana warwarewa amma ba matsala ki kwantar da hankali na miki alqawari Faizan ba ze bar garin nan ba tare da an tsayar da magana tsakanin ku ba!" Wani wawan tsaki Fauxa ta ja kan ta juya ta fice daga gidan gabaɗaya, a chan gefe da sashensu inda aka yi wasu kujeru haka masu kyau na tayoyi ta zauna, tana me kallon qonannan hannunta, murmushi ta saki na jin daaɗin ba ita ba aikin gida har se ta warke, makaranta ma in ta je ba rubutu ai kuwa za'a sha neman tsokana. Bata san iya adadin lokutan da ta ɗauka a wurin ba, chan ta hangosa yana tahowa cikin tafiyar nan tasa me cike da natsuwa kaman saraki, sanye da wasu kananun kayan still farin Jean da navy blue shirt a ko yaushe Adonshi da shigar shi masu kyau ne da salo irin na burgewa. Maganan Fatima ne ya faɗo mata bata san sadda ta kwashe da wani irin dariya ba har da hawaye, wai amma Fatima tayi asara ta taɓe duniya da lahira fisabilillahi ta rasa abun so se wannan? Dariya take tayi tana sakewa wai fa har da kuka Fatima ke yi sbd shi? Ta kara kwashewa da dariya tace "Taabbb Allah ka rabani da aikin wahala" Har ya wuce tana babbaka dariyar ta kaman sabon kamu inda Allah ya taimake ta ba Kallonshi take ba don ta san in har ya san dashi take yadda ba kowan nan se na lahira ya fi ta jin daaɗi, ji fa yadda yake tafiya, ita wallahi tafiyar da yake yi ko ita mace bazata yi irin shi ba, dariyarta tasha daidai sashensu na samari ta ga ya ɗan tsaya ya waigo, daidai itama ta ɗago ta kalle shi se suka Haɗa idanu, kallon kanki ya taɓu ya watsa mata. Ko seconds biyu be yi ba ya juya ya karasa shigewa sashen, mikewa tayi tana share hawayen dariyarta kaman wacce duniya ta yiwa daaɗi ta wuce sashen Jaddah, tana shiga ta narke tana tafiya kaman marar lafiya. Jaddah tace "zo ki karbi tsarabar ki na wurin Faizan" Haɗe rai tayi, Fa'iza tace "ke kinga rikicin da aka kwasa da ya Faizan kan Jaddah ta kwasar miki chocolates ɗin nan karfi da yaji? wlh ki gode mata ta san yadda kike son chocolates shiyasa, ga su da daaɗi kaman zasu tsige kunne" Kallon chocolates ɗin tayi masu tsada ne sossai, daga gani ma maybe ba a nan Nijeria ya sayo su ba sede tunda daga hannunshi ya fito basu ba ta sha'awa ba, kau da kai tayi tace "Jaddah da baki wahalar da kanki ba don ni kam ba sha zan yi ba" Jaddah ta saki baki zata yi magana kenan Fauxa ta fara kukan hannunta na zugi, da sauri Jaddah ta karɓe hannun tana salati tace "Faozia garin yaya? Me ya sameki haka?" Ai jin tambayan Jaddah yasa ta kara narkewa tana fashewa da kuka, she's so fragile in tana abu kaman little baby, Fai'za tace cikin damuwa. "Jaddah ita da ya Faizan ne" Nan ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, Jaddah tayi ta masifa ta kuwa ci alwashin se ta saɓa mishi wani irin mugunta da bakin hali ne wannan? A kan cinyar Jaddah ta kwanta tana jin daaɗin yadda Jaddah ke ta zuba mitan abunda ya farun, ta kara da "mutum ne se baƙin miskilanci yanzun nan yasa yarinyar da yake ikirarin buduruwarshi ce kuka amma ko a kwalan riganshi" Kau da maganan Fauxa tayi don be shafe ta ba, anan ta kwana ma yau.. Washegari Monday ko aiki ɗaya bata yi ba da taje school ma babu abunda ta rubuta se surutu da neman magana, a ranar Ammi ta dawo itama Seda tayi faɗan hannun nata sede baba Alhj be ce komai ba. Bayan 2days ta ɗan samu sauki ta cigaba da aikinta, zuciyarta kuwa na kiyasta mata yadda zata rama abunda ya mata sbd ta sha wahalan qunan sossai. Yau tana kwance bisa kujerar Jaddah tana danna ƴar karamar wayar jaddahn sbd ita ba kaunar kallon tashoshin wa'azuzzuka da shi kaɗai suke dashi gabaɗaya gidan take ba, jaddah ta fito rike da tray tana kallonta tace "Fauziyya don Allah miƙawa Faizan abincin nan kinga yaran duka suna wurin Ibrahim(baba prof)" Haɗe rai tayi tace "Jaddah eyyah ki jira su in sun dawo su kai mishi" Jaddah ma rai ta ɓata tace "zan saɓa miki wlh Fauziyya, ki wuce ki tashi ki kai in dodonki ne se ya cinye ki, in kuma baza ki je bane ki gayamin" Hawaye ne ya cika idanunta, ita ba mikewa take son yi ba don ko da yaran suka je wurin baba prof da be ganta ba seda ya aiko fakiha tace mata tace tayi bacci idan kuwa bata ce haka ba se ta kirɓa ta in aka dawo sake kiranta, gashi yanzu Jaddah zata saka ta kaiwa wannan azzalumin abinci. Mikewa tayi ta ɗauki tray ɗin da Jaddahn ta dangwalar ta fito, shiru tayi tana tunani, in ta taɓa ji da kyau Jaddah ta taɓa maganan rashin son yajinshi sbd muguwar ulcer ɗinshi ko yaya ya ci yaji se ya kwanta, murmushi ta saki taje kan kujerun tayunsu ta ajiye tray ɗin da gudu ta koma gidansu taje ta fara binciken drawer ɗinta akwai wani yaji me zafi da ta daka ranar girkin Amminta sbd an yi mata dole daka yajin shinkafa da waken, kowa da wahala yaci yajin sauran ne ta kulle ta boye a sif ɗinta. Da gudu ta dawo ta buɗe miyan kubewa danyen ta juye duka, cokalin da ta biya ta ɗauko a kitchen ta saka ta juya kan ta ajiye shi a wurin, ta dauki abincin ta nufi sashensu, a gaban site ɗin ta kalli Haɗaddiyar beymach ɗinshi baƙi siɗik se ɗaukar ido yake da yayi parking a wurin, baki ta taɓe ta isa kan motar da sbd yanayin kyaunta mutum kan iya finshi tsawo ta ɗaura a kai ta juya tayi tafiyar ta. Tana nan kwance a parlorn na Jaddah har wuraren karfe tara da rabi, wayan Jaddah ne ya fara ringing ta ɗauko ganin Faizan ta taɓe baki ta mayar ta ajiye tare da lumshe idanu kaman tayi bacci, Seda ya kira sau biyu a na ukun ne Jaddah ta fito tana tambayar Fauziyya kam bacci tayi ne ana ta kira bata ji. Ganin baccin take yasa ta ɗauki wayan tare da amsawa ta kara a kunne, cikin kamillalliyar Muryarsa da se ka saurara zaka ji sbd rashin son hayaniyarsa yace "Jaddah abincin fa? I've been waiting." Jaddah ta kalli Fauza tace "ba'a kawo bane? Tun fa ɗazu na bayar a kai maka, ikon Allah.." Yace "wa kika bai wa?" Ta fara jijjiga Fauziyya sbd nauyin baccin da ta riga ta sani tace "Fauziyya! Ina abincin da na baki ki kaiwa yayanku ne?" Juya keya tayi kan tace "yana kan motanshi mana" Ba tare da yace komai ba sbd yana jin duk abunda suke yi ya katse wayan, Jaddah na ta mamakin ikon Allah akan Fauxa se kawai sallamanshi taji, juyowa tayi zata yi magana taga ya nufo su hannunshi riƙe da ruwa me sanyi wadda ya fara kankanra na kamfanin Faro babba yana tafiya ne cikin ƙasaitarshi yana me buɗe murfin. Kan Jaddah ta ankara ya fara tuttulawa fauxiyyan ruwan sanyin, a firgice ta mike zaune tana jan numfashi sbd sanyin ruwan gashi a duniya ta tsani ruwa ya taɓa ta yanzu se tayi mura gashi ya zuba sossai a kanta da fuskanta, hawaye ta fara don sossai ta firgita sanyin ruwan kuma ya ratsa ta, ko a jikinshi cikin muryarshi me taushi yace "wuce ki ɗauko!" Mikewa tayi tana share hawayenta ta fito, ko da ta ɗauko abincin don tuna muguntan da ta mishi a ciki bata san sadda murmushi ya subuce mata ba, a gabanshi ta dire ta juya ta fice ya ja tsaki kan ya buɗe ya zuba kaɗan. Spoon ya ɗauka sbd shi fa irin mutanen nan ne da ko tuwo zasu ci seda spoon, da bismillah ya kai loman abincin bakinshi Sam be kula da bala'in dake ciki ba seda ya haɗiye ya ɗaura na biyu a bakinshi. A firgice ya dawo da abincin yana sakin tari kaman ze shiɗe, da sauri Jaddah ta dauki ruwa ta mika mishi ya amsa ya sha sede ba sassauci, tari yake kaman ze mutu gabaɗaya ya Haɗa zufa, idanunshi sun rine sun zama jajazir, da kyar ya samu tarin ya lafa se kuma gefen cikinshi ya riƙe. Salati Jaddah take tayi tace "na shiga uku! Yaji ne a abincin ko me?" "Zaliha! Zaliha!!" Zaliha ta fito da gudu ta zube a ƙasa Jaddah tace "ke Zaliha kin saka attarugu a markaden kayan miyan nan ne?" Girgiza kai tayi tace "ban saka ba Jaddah ai kin ce yallaɓai Faizan baya so, wlh ko kaɗan ban saka ba" Fauxa dake daga window tana ta dariyar cin nasara, kwanciya yayi a kan kujeran duk dauriyarshi ulcer na azabtar dashi shiyasa yake mugun kiyayewa. Kaman wasa Seda Faizan yayi ciwo sossai kan ya samu sauƙi, kaman yadda itama saida tayi mura da zazzaɓi, kowa kuma Seda yayiwa Zaliha faɗan saka attarugu a abincinshi baiwar Allah gata da gaskiya sede babu yadda ta iya haka take shiru take bada hakuri. Zaune yake gaban baba prof kanshi a ƙasa, baban ya tambayeshi jiki, cikin girmamawa ya amsa da da sauki Alhamdulillah, bayan shirun seconds kan yace. "In Allah ya kaimu Laraba zan koma Abuja sbd akwai tafiyar da zamu yi da shugaban ƙasa" Murmushi baba ya saki, a ko menene ya kan yi alfahari da wannan yaron nashi, Faizan ba irin normal pilots bane, yana daga cikin manyan pilots da idan ba da su ba shugaban kasa baya tafiya ko ina, bayan nan yana da hannayen jari da kampanunnuka ba daya ba ba biyu ba, Sam be dogara da aiki ɗaya ba, yaro ne shi me tsantsan biyayya ga iyayenshi, babban ɗabi'ar shi kuma kunya yanzu ya san akwai abunda yake son faɗa mishi ne sede yana jin nauyin maganan shine yake ta kwana kwana. Baba yace "masha Allah, Toh Allah ya kaimu ya nuna mana" Yace "Ameen baba!" Baba ya kalleshi yace "akwai wani abu ne kuma? Naga kaman kana son yin magana" Kanshi ya dukar yana shafa kwantaccen Suman keyanshi yace "dama akan maganan Fatima ne" Murmushi baba ya fadada yace "masha Allah, ka shirya auren kenan.. Toh tunda har ka furta wani satin in shaa Allah zamu je wurin mahaifinta mu tambayar maka ita, ai Fatima yarinyar kirki ce ta samu tarbiya me kyau daga Mahaifiyarta Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Da Ameen Faizan ya amsa, dukda maganan magana ne da ya kamata yayi farin ciki sede ko kaɗan be wani ji daaɗin hakan har chan ba, hira suka taɓa kadan da baban har baba Alhj ya shigo suka kara tattaunawa kan ya musu sallama ya fice. Bayan ya koma aiki da kwanaki biyar aka tambayar mishi Fatima kuma an bashi sede an ja auren se ta gama secondary school in ya so se ta fara jami'a a gidanshi. **** Kwance take kan gadonta jikinta yayi tsami da bugun da ya Farhan ya mata da magrib ɗin saboda bin wata ƙawarta da tayi gida bata dawo ba se da ana kiran sallahn magrib tun karfe 1:30, da farko basu so dukanta ba sede Sam ta ƙi faɗan inda taje hakan yasa ya Farhan da Ya Faraj suka zane ta har Seda Baba prof da za shi masallaci ya karɓe ta, Allah ya isa take ta ja tana cin alwashi kala kala a kansu, fa'iza dake ɗakin tun da suka dawo daga sallar isha'in bata ce mata komai ba... Suna daga ɗakin Fatima ta shigo a wurin Aunty Amarya da Ammi dake bisa taburma a tsakar gidan suna cin Tuwon dare ta zauna, tace "waii wallahi Aunty mammi na jin jiki, ciwon kafan nan baya mata ta daaɗi ɗan zaman da na yi na awanni a wurintan nan baki ga ba, komai se an yi mata" Ammi tace "Allah sarki, Allah dae ya bata lafiya ai kafa shine komai a jikin mutum, Allah dae ya sa kaffara ne" Aunty Amarya tace "Ameen Ammi, Fatima se ki dinga zuwa kina taya Asiya (ɗiyar Yayar mammi ɗin) kula da ita" Fatima tace "In shaa Allahu Aunty ai Mammi kaman uwa take a wurina, bari na shiga na dubo su Fa'iza mu ci abinci" Mikewa tayi ta nufo ɗakin nasu, tana shiga suka Haɗa idanu da Faozia dake kallon kofan, ɗauke kai Fatima tayi yayinda Faozia tayi tsaki me karfi tace "Fa'iza kin san Allah ko?" Fa'iza tace "me aka yi kike tambayana na san shi mana" Faozia tace "Daaɗina dake baki iya cin riban zance ba, ko da shike manta ma... Dama Tambayarki zan yi da munafukin ɓoye da na bayyane don Allah wanne ya fi?" Fa'iza da bata fahimci zancen ta ba tace "ai munafunci ko ya yake sunan shi munafunci kawai dae gwara wadda ze nuna maka a bayyane ka san dashi da wadda ze nuna maka Musa a fuska fir'auna a zuciya" "sannan in zaka yi abu kayi don Allah da nufi ɗaya ni fa shiyasa bana son hulda da duk munafuki a duniya.." Fauza ta karasa Fatima da ta tsaya kikam tana Kallonsu se hawaye ya fara kwaranya a fuskanta, Aunty ce ta fara shigowa ta buge Bakin Fa'iza tana cewa "yanzu ƴar uwarki zaki Haɗa kai ana cusguna mata a gidan nan Fa'iza? Tana gayamin ina karyatata ashe da gaske ne? Fa'iza..!" Ammi da ita ma ta shigo tayi kan Fauxa zata make tana cewa "Ai ba ita zaki daka ba Auntynsu ita uwar iyayin nan zaki mara har se taga wuta.." Dira Faozia tayi ta Ɗayan gefen kan Ammi ta zagayo ta fice da gudu harda bangaje Aunty goshinta ya ƙume da kofa salati duk suka saki ita kam ko waiwaye babu tayi sashen Mammi da gudu. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA    (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid*                *Shafi Na Takwas* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️** Karshe dae Aunty bata iya bacci ba seda Baba Alhj ya danne mata goshin aka shafa man zafi, takaici ya hana shi cewa komai, ya aika a kira mishi Faozia ɗin aka tarar bata nan sede Jaddah bata ce bata nan ba kawai cewa tayi a ce tayi bacci Dukda bata san wani laifin ta sake aikatawa ba. Ita kuwa Faozia tana zuwa wurin Mammi ta shagwaɓe tana faɗamata abunda ya faru, Mammi tace "Gaskiya Farhan da Faraj basu kyauta ba ai da lafiyata ƙalau babu wadda zan bari ya taɓa ki su da suke gantalinsu akwai wadda ya hana su ne?" Cikin jin daaɗin goyon bayan da aka bata tace "ai shine" Mammi tace "Faozia am ki rage nemarwa kanki magana kin ji? Bana son yadda kowa ya buɗe baki yace Faozia, Faozia ɗin nan wallahi har raina bana jin daaɗi" Fauziyya tace "In shaa Allahu Mammi bazan sake ba" Mammi tayi murmushi Dukda ta san labarin kanzon kurege ne kullum haka take cewa baze hana gobe tana fita ta jajiɓo wani tashin hankalin ba. Ƙin zuwa wurin jadda tayi wai tana fushi a lokacin da su Farhan ke bugunta jadda bata zo ta karɓeta ba kuma ta tabbatar sarai tana ji. Asiya mammi ta kira akan ta zo ta dubo wa Fauzan abunda zata ci. Faozia tayi Charab tace "Mammi bari na shiga kitchen ɗin da kaina" Har ta fita ta dawo tace "ke fa Mammi kin ci abinci?" Tace "Ina ga Tea zan sha Faozia kubewa suka girka a gidan ni kuma ba so nake ba, je kiyi abunda zaki yi ke kam" Kitchen ta wuce, Asiya dake zaune a parlorn ta bita da harara ko Kulata Faozia bata yi ba don ta jima da sanin Asiya irin mutanen nan ne da suke bari hassadar wani ya gurɓata musu rayuwa, ba tun yau ba ta fahimci Asiya bata ƙaunar ta shiyasa itama bata shiga harkarta. Hijab ɗinta ta ajiye ta fara dube dube a kitchen ɗin Seda ta fidda duk abunda zata bukata na aikin da take son yi kan ta fara aikin, Yawan bin kawaye da take har ana dukanta duk akan girki ne tana matukar kaunar girki babu abunda yake bata nishaɗi a rayuwa irin ta ganta a katon kitchen tana girke girke, idan kaga Faozia a school ta natsu to kallon recipes take a wayan kawaye don gidansu kam ba'a abubuwan zamanin nan. Shawarma da suka yi ɗazu har sanadiyar shi aka Chasa ta tayi guda biyu na beef, banda kamshi babu abunda ke tashi a kitchen ɗin tana yin Shawarmanta kuwa tana biski ba me yawa tayi ba ɗan kaɗan ne sosai da kidney sauce, fancy plate ta ɗauka ta zuba biskin daga gefe in a stylish way kan ta zuba kidney sauce ɗin shima a gefe ta watsa parsley a kai kaɗan yadda ya bada wani garnish na burgewa. Shawarmanta guda biyu ta ɗauko suma ta saka su a plate ta ɗaura Duka a tray ta ɗauko ruwa masu rangwamen sanyi tare da daukawa kanta wani mango drinks ta nufi ɗakin Mammi, tana zuwa ta ajiye tray ɗin tace "Mammi guess what I made?" Mammi tana murmushi tace "Ina zan sani ina zaune a nan na dae ji kamshi na tashi kuma duk hasashe na na rasa gane menene.." Buɗe plate ɗin biski da kidney sauce tayi tana dariya cike da jin daaɗi tace "Tadaaa..!" Tana dariya sossai wadda ya saka Mammi murmushi tace "Masha Allah, Kice daughter na na shirin zama Chef eyee a ina kika koyi irin wannan delicious ɗin?" Shagwaɓe fuska tayi tace "ba irin su bane na bi Zee koyo a gidansu kuma da nisa shine ban dawo da wuri ba su ya Farhan suka bugeni ba..!" Mammi tace "masha Allah, am impressed gaskiya karki damu in shaa Allah na miki Alkawari da kaina zan saka ki a catering school ƴata ta zama Chef Faoza.." Murna Faozia ta fara harda tsalle, Mammi na ta dariya Faozia is such a wonderful child da zama da ita kaɗai ka iya saka ka farin ciki she's so lively in har ka san yadda zaka tafi da ita, Mammi ta matsarwa plate ɗin tace "bismillah Mammi" "thank you bitty" Spoon ta sa ta fara ci tana yabon hannun na Fauza a girki, itama Shawarmanta taci tas ta cinye ta sha mango juice ɗin kan ta tattare wurin ta fitar, da taimakonta Mammi taje toilet tayi duk wani abunda zata yi ta dawo da alwala, ita ta taimaka mata har ta kwanta... Tana shirin shiga wanka se taji sallaman Baba Prof hijab ta saka, Seda ya shigo ta gaishe shi ya amsa da kulawa kan ta fice ta bar su da Mammi, ɗakin yaya farida da babu abunda Mammi ta taɓa ciki ta shiga, akan gyara akai akai hakan yasa ta nufi toilet ɗinta tayi wanka, bayan ta fito ta duba wardrobe ɗinta ta kuwa samu kayan bacci sabo dal a Leda Dukda ya ɗan yi mata yawa haka ta saka. Seda ta ɓata lokaci mai yawa kan ta fito ta koma ɗakin Mammi ta samu Baba prof ya tafi, Har zata juya Mammi tace "Fauza" Dawowa tayi tana cewa "Na'am Mammi ko kina bukatar wani abu ne?" Mammi tace "A'a ki hau gado ki kwanta, kiyi Adu'a kin ji?" Kai ta gyaɗa tare da rage musu hasken ɗakin ta hau gadon na Mammi ta kwanta tare da jan bargo. Chan cikin dare Fauza ta tashi saboda fitsarin da ya matse ta se ta hangi Mammi zaune dafe da kai, da sauri ta mike tace "Mammi!" Mammi bata ɗago ba, sauƙa tayi ta nufe ta ta duƙa a gabanta tace "Mammi lafiya? Baki jin daaɗi ne?" Tayi maganan hawaye na cika mata idanu Mammi ta ɗago idanunta duk sun sauya tace "Na kasa bacci Fauxa kafana se harbawa yake" Hawaye ne ya zubowa Fauxa cikin tausayin Mammi, zama tayi gaban kafan tace "bari na miki Adu'a Mammi" Bismillah tayi sau Uku kan ta ɗaura da بِسْمِ الله! بسم لله!! بسم الله!!! "أَعُوذُ بِااللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شِّرِ مَا أَجِدُ وَأُهـَٰذِر" "Bismillah! Bismillah!! Bismillah!!! Auzibillahi bi qudratihi min sharri ma ajidu wa uhadhir". Kafa bakwai ta shafa mata a kafan ta kara da qulhuwa uku, falaki uku, da nasi uku. Manzon Allah yace babu wani ciwon dake damunka da zaka dafa wurin ka karanta wannan Adu'a ba tare da Allah ya yaye maka ba, walau ciwon ciki, ciwon kai, ciwon kunne ko ma wani irin ciwo ne. Cikin ikon Allah bayan ta gama yi mata ta ci gaba da massaging kafan har Mammi ta Samu bacci ya ɗauke ta, wani irin ciwon kafa ne wannan Fauxa tayi maganan a zuciyarta tana kallon tarin magungunan na Mammi, daga na Asibiti har na gargajiya zuwa na musulunci, komawa gadon da Fauxa bata yi ba kenan a nan kasa ta kwana se da Asuba taji Mammi na tashinta. Mikewa zaune tayi tace "Mammi ya kafan?" Mammi tayi murmushi tace "sannu Fauziyya! Sossai na ji daaɗin Adu'ar da kika min kwanana hudu rabona da baccin dare se gashi yau nayi harda mafarki" Murmushi Fauxa tayi tace "to bari na sake miki" Adu'ar ta fara mata yayinda ma ta zuba mata idanu tana kallo, ta rasa me take hangowa a rayuwar Fauxa wadda kowa baya hanga kowa kawai ya tashi Fauxa bata ji, Fauxa kaza Fauza kaza ita Sam banda haske babu abunda take gani a rayuwarta, yarinya ce me tarin ɓoyayyen baiwa amma influence na mutanen dake zagaye da ita ya hana shi bayyana. Jin za'a shiga sallah yasa tace "Fauza tashi je kiyi alwala ki tafi masallaci bari nima na miƙe" Da taimakon Allah ta kai kanta bayi tayo alwala yayinda tuni Fauxa ta fice masallaci, anan tayi sallah ta sake kishingiɗa tana me sake samun wani baccin saboda sauƙin kafan. Fauxa ko ɗar bata ji ba ta wuce sashensu abunta, yau itace da wanke wanke da kuma gyaran ɗakin su, Seda ta fara shara da gyara ɗakin tana cewa "Wallahi in an ga dama a wargaza kan a tafi ba ruwan Fauxa" Falaq tace "amma kin san dole a shirin su Fakiha su wargaza ɗakin nan kam ko?" Cikin kunkuni tace "suna da hannu ai, se su gyara! Ni de na san nayi" Tana kai nan ta hau sharewa ta fitar da Sharan a memakon ta kwashe se ta watsa tsakar gida alhali Fatima ta riga ta wuce nan a shararta na tsakar gida, tana watsawa ta bi ta kan tsintsiyar Fatima da ta sake baki tana kallonta tayi wurin wanke wanke ta fara yi, dama kowa ya san wanke wankenta kwanuka kam se sun bugu iya buguwa in akwai na fashewa kuwa to se ya fashe. Ammi da suke aikin kari da Fa'iza bata ce mata komai ba, don in tace zata yi magana kuka ze iya fin karfinta Fauziyya ta riga ta fi karfin duka yanzu kuma se Adu'a. Da yamma bayan sun dawo makaranta Fatima na wankin uniform na su Fakiha yayinda fa'iza ke wanke wanke, ita kuwa uwar gayyar kitchen take tana taya Aunty Amarya sa magana tunda ba aikin take ba duk abunda Aunty Amarya ta saka ta se tayi mata shirme da gangan. "Ni sumayya! Yanzu Fauziyya daka attarugu ma se kin zuzzubar a ƙasa haka? Ai ko Faazila dake karama a gidan nan karankap zata daka min kayan miya in kwashe lafiya lau ke kam babu abunda kika iya goɗe goɗe dake se sa mutane magana? Wani irin jaraba ne wannan?khaih Allah ya shirya mana in na shiryuwa ne" Kunkuni wadda Aunty Amarya bata ji ta hau yi. "Yen yen yen yen... Se ki zo ki shirya ai tunda charbi nake ko jigida" kawai se Aunty Amarya ta saki kuka. Baba Alhj da shigowar shi gidan kenan ya tarar da faɗan da Aunty Amarya ke yi kuma yana kallon lokacin da take gungunin sede gudun kar ya ce ze buge ta yanzu ya karya ta yasa ya shige parlornshi kawai. Aunty Amarya tace "tashi ki tafi bana son aikin, in har aikin da zaki sani magana ne, nayi maganan kuma ki zage ni don baki dauke ni da daraja ba tunda ba ni na haife ki ba jeki karki sake sakamin hannu a aiki" Mikewa kuwa tayi ta fito ko a jikinta, ta zo wucewa ta gaban Fatima suka Haɗa ido a saman labbanta tace "munafuka" tana ball da bucket ɗin wankin har ruwan ya kwararare. "Fauziyya!" Baba Alhj ya kirata cikin wani irin kaushin murya. Se Fatima ta fara kuka mikewa tayi ta wuce ta gaban Fauziyya ta duƙa a gaban Baba Alhj tace cikin sanyin murya "Baba Don Allah ina so kayi min izini ina so in koma wurin mahaifina haka..." Cikin tausayinta yace "Babu inda zaki koma Fatima, nima mahaifinki ne in akwai wacce tafi cancanta da ta bar min gida Fauziyya ce!" A razane Fauziyya ta ɗago ta kalleshi, Ammi ma da ta fito se idanu ta zuba mishi yana kallon Fauziyya yace "Eh kin ji abunda na faɗa! Na gaji bazaki kasheni tun kwana na be kare ba, ke kaɗai ranki guda kin zama sheɗaniy...." "A'uzubillahi Sule!" Jadda da ta shigo bikon ƴar gidanta sbd ta ƙi shiga wurinta tun jiyan nan ta faɗa tana karasowa ta kama Fauxiya da ta zama speechless tana kallon mahaifinta. "Ƴarka na cikin ka kake kira sheɗaniya Sule? Wani irin baki ne wannan? Me tayi maka da zafi haka?" Kanshi a ƙasa yace "Mama na gaji da halayyar Fauziyya, dubi goshin uwarta Sumayya yadda tayi mata jiya, babu wadda ze faɗa magana Fauziyya bata bashi amsa ba, ta sakawa yarinyar nan karan zuƙa tana mata gadara da gidan uba! Ita ɗin ai ba daga Bishiya ta faɗo ba, gwara Fatima sau dubu don bata sa uban ta da uwarta zub da hawaye ba... Wallahi wallahi Mama Fauziyya ta gama sane min cikin yarana har raina na gaji da komai nata" Ammi kuka ta fashe dashi tace "ba kinji ba Fauziyya? Wallahi ki guji duniya, uban da ya haife ki ma yace ya gaji dake to wa ze iya zama dake? Da wannan halayyar naki Fauziyya gwara ki sa wuƙa ki mana yankan rago mu huta da zafin zuciya kullum a kanki" "Ruqayya! Sulaiman!! Ya isheni haka, tunda mutuncina da ganin idanuna be sa kun kasa amayo da kalaman bakinku ba, ni kuwa ba zan tsaya in cigaba da saurara ba, karku manta yaranmu kaman kiwo suke a garemu Allah ya kan jarabceka ta hanyoyi daban daban maybe ita ɗin itace jarabawar taku, idan kuka yi hakuri a matsayinku na iyaye kuka kai zuciyarku nesa kuka cigaba da mata adu'a har zuwa sadda Zaku Rabu lafiya kila ku samu rabauta ta sanadiyar ta, yanzu da duk kuke aika mata da kalamai marasa daaɗi ta karasa lalacewa kuma haka Zaku ɓata lahirarku saboda se Allah ya tambayeku, abunda ya saura ku ce shine kawai ta fita ta bar muku gida tunda har ka fara attempting to zan tafi da ita sashena ku zuba ruwa a ƙasa ku sha" Tana kai nan ta janyo hannun Fauza da take tsaye kaman icce suka fice. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Tara* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️** Ƙurawa kanta idanu tayi a Door size mirror na ɗakin tana jin sukar kalaman iyayenta a kanta, lallai kam basu faɗi abunda ze gyara mata rayuwa ba se ma wadda ze ɓata saboda hango abubuwan da zata ke yi musamman wadda a da gudun ɓacin ran nasu yasa ta danne burinta take rayuwa yadda ta taso ta gani Dukda baya cikin tsarinta, kallon kanta take da kyau tare da lumshe idanu tana tuna maganar sakina. "Ke yadda kike da kyaun nan da sura wallahi kika fara ɗaukar wanka kika zama ƴar gayu ba karamin rububi maza zasu yi a kanki ba, kin san kuwa irin baiwar da kike dashi na fusgan hankalin mata ma ba maza kaɗai ba? Babe ki waye pls ki dena kunshe kanki cikin hijab" Ajiyar zuciya ta sauke tana tuna amsar rahama. "Ke wallahi abunda Sakinah ta faɗi gaskiya ne baki ganin yadda duk muke rayuwa cikin wayewa da aji da izza? Don Allah hakan baya burgeki? Amma ku kullum gidanku hijab hijab Ina ka fito karatu ina zaka karatu, babu babban waya, babu samari babu hangout da su party, wallahi kuna cikin duhu" Ba kalaman nasu bane ke tunzura ta sede illa irin tsarin rayuwar da take so ɗin kenan se ya haɗu da maganganun su yake tasiri a hankali a ranta sede yanzu kalaman iyayenta ya hauhawa su kaman tashin farashin man fetur, a yanzu take jin zata fara nunawa su baba prof ba irin rayuwar su take so ba, ko da zasu yanka ta su fige tane. Rahama da sakina ƴan ajinsu ne waenda suka shigo third term na SS1 ɗinsu asali a Abti suke sede rashin jinsu, da yawace yawace yasa iyayen Rahama suka cire ta suka dawo da ita Elkenemy ganin makarantar musulunci ne kila ta shiryu sede ba tare da sun sani ba sakina ma ta uzzuruwa iyayenta suka sake dawowa suka jone a ajin su Fauxa, tunda suka ganta suke admiring kyaunta da kalar idanunta suka fara nuna mata yadda zata ja hankali tare da tada hankalin maza a tiktok sede bata mai da hankali ba, iya kaci taji wakoki da wayoyinsu tayi ta kallon mata masu class a Instagram waenda har ga Allah suke burge ta. Tana matukar son gayu da class sede su gidansu ko ba hijab baka isa fita ba, a daren ta fara tsara yadda zata sauya rayuwarta zuwa ra'ayin kanta ba ra'ayin wasu ba, sallamar Faazila ya sa ta ɗago idanunta da suka sauya ta zuba mata, birkicewa yarinyar tayi don ta san sarai yanzu se Adda Fauxa ta mammake ta yadda take a harzuke ɗin nan. "Me??? Kin zo kin wani yi min kerere kina kallona?" Baya ta ja tace "Mammi ce tace in kira ki" Dauke idanunta tayi ba tare da ta amsa ba ta juya ta dauki hijab ɗinta ta saka tare da fitowa zuwa sashen Mammi, tana shirin shiga ɗakin Fatima na shirin fitowa da gayya ta bangaje ta har Seda tayi baya tana kallonta sede ko kallo bata ishi Fauxa ba ta wuce zuwa wurin Mammi tana daidaita fuskanta Gaisawa suka yi Mammi tace "Fauxa zo don Allah kiyi min tofi a kafan nan" A ladabce tace "to Mammi" A gabanta ta duƙa ta fara se Fatima ta shigo da bowl na fruits a hannunta ta ajiyewa Mammi ɗin tana cewa "Mammi Adu'a ce ake yi?" Mammi tace "eh wlh jiya da ta min baki ji yadda na ji daaɗin kafafun ba" A fakaice Fatima ta aika mata da wani kalar kallo tare da taɓe baki, ina Fauxa ta ma san tana yi, wai harara a duhu, bayan ta gama mata ta fice don bata jin magana in kuma ta zauna inuwa daya da Fatima karshe se Mammi ta raba faɗa. Washegari a class bayan an tashi break ta kalli rahama tace "am interested in ur way of life taya nima zan fara?" Rahama da sakina suka yi wani ihu tare da tafawa suka ce "welcome to the club babe" Sakinah tace "dama akwai wasu Zafafan dinkunan da zamu yi har ma mun yi placing order ɗin materials ɗin amma tunda zaki yi bari na sa dake" Fauxa tace "amma fa bani da kuɗi kun san gidanmu ba wani bada kudi ake banza banza ba" Rahama tace "don't mind dear! anything for you precious " Sakina tace "bare ma kwana biyu zaki fara rike wasu makudan kuɗin da se kin ji tsoro just chill babe" Aiko gwada ta suka yi suka turawa tailor ɗin su, nan suka fara nuna mata mahaukatan dinkunan tana kallo cike da yabawa.. Iyaye ya kamata mu san cewa duk fushin ka da yaro ba kowacce kalma ya kamata ka furtawa ɗa cikin fushi ba domin baka san irin influence da zaka yiwa yaro ba idan har Allah ya amsa. MAFARI Dukda rashin son karatun Fauxa ta kasance mace mai son karance karance, hakan yasa bata rabo da littafi ko na turanci ne, babu kalar abunda bata karantawa hakan yasa abubuwa dayawa tana da masaniyar already aikata shi a fili ne kawai bata yi ba. Wani irin kalar Juyawa rayuwar Fauxa yayi cikin lokaci kankani, idan tayi dressing se ka dauka ba Fauxan gidan baba prof bace, Fallin balaga ya buɗe rashin M ɗin ta se abunda ya karu ga rashin daukar raini, se neman tsokananta da yayi sauƙi sede fa ba shi ya hana kana ce mata Kule ta ce maka chass ba. Abunda take yi shine tunda yanzu Sam Sam ba cika zuwa part ɗinsu tayi ba se idan zata gaida Ammi don baba Alhj ma ta manta rabon da su haɗu tunda ya ce baya kaunar ganin fuskanta ta gwammaci ta dinga wasan buya dashi. Idan an tafi school daga an tashi break zata yi bribing gate man sbd su Rahama ma ba cika zuwa suke ba se once or twice in a week, zasu ɗauke ta a gate su tafi gidansu rahama inda wasu abubuwanta suke a nan zasu yi dressing ɗinsu na class su fice yawo, samari kuwa kaman kuda a kan Fauxa hakan yasa ta juya wannan ta waina wanchan ga yadda take sha musu kamshi kaman ƴar shugaban kasa, ɓarin kudi suke mata ba na wasa ba har ta mallaki iPhone 13pro na kanta kuma har gida take zuwa da abunta. Ta chanza mayukanta gabaɗaya zuwa wasu organic masu tsananin tsada, na kafa daban na gashi daban na fuska kala kala, in ta wuce ka se ka jima kana jin kamshin designers perfumes na jikinta. Aka ce akuyar ɗaure in ta samu sake Habaaa, har Sakina da half rayuwarta outside tayi wani lokacin ta kan mutu da kalar gayun Fauxa sede a gida har yanzu babu wadda yayi noticing ana getting to five months. Sau ɗaya fa'iza ta taɓa mata maganan rashin zamanta aji se da ta ja mata katoton layi tayi mata fata fata wadda har ta Haɗa da mahaifiyarta hakan yasa fa'iza dauke kai daga rayuwar ƴar uwar tata. Se dab za'a tashi school take dawowa su koma tare da ƴan gida, wayanta kuwa kullum a ɓoye yake kasancewar ɗakin da take a sashen Jaddah ita kaɗai ce, yanzu damuwanta yadda zata fara fitan dare sbd ana kawo mata cikas sossai da ganin ƙarancin wayewarta sbd rashin zuwa night parties ɗin nan. Zama tayi ta tsara yadda zata ke fita abunta bayan isha zuwa asuba, randa ta fara gwada luck ɗin ta Dukda yadda take a tsorace kuma cikin bugawar zuciya haka ta saka dogon hijab ɗinta bayan ta yi wanka ta gama duk shafe shafenta, fuskanta da ba ko Digon powder se wani ɗaukar hankali yake sbd kyaun da ta kara na musamman, wurin Jaddah ta je tace "Jaddah yau wurin Mammi zan kwana" Jaddah tace "yau kuma ni aka yiwa Hijira kenan, to se da safe" Tana murmushi tace "Allah ya bamu alkhairi" Sashen Mammi tayi ta gaisheta, tace "Mammi bari na tofa miki Adu'ar nan" Kasancewar kullum kaman ka'ida duk dare ta kan je ta tofa mata adu'o'in hakanan kan su wuce school kuma Alhamdulillah sossai Mammi take jin daaɗin kafan kaunar Fauxa sbd Allah na ninkuwa a zuciyarta, kuma duk wadda ya san Mammi se ya ji zancen Fauxa a bakinta sbd irin gudumawar da Fauxa ke bayarwa idan Mammi ɗin ba lafiya. Seda ta shafa mata adu'ar kan ta mike ta nufo hanyar gate, Allah ya taimake ta daidai lokacin baba prof yake baiwa Lawal kuɗi ya amso mishi credit, a jikin flowers ta buya har Seda ya wuce ciki daga masallacin da shi se lokacin yake fitowa, Lawal kuwa yayi waje ta fito da sauri ta fice gabanta na dukan uku uku. Wayanta ta fidda ta kira su Rahama suka zo da driver ɗinsu da shine yake yawo dasu dama suka wuce suna ihun ganinta at this time around. Shiri suka yi suka wuce birthday party ɗin wani saurayin Rahama, wuri ne na manyan yara waenda iyayensu suke da kumbar susa, ado ne kala kala zaka gani da kalar dinkunan rashin kamun kai, kuɗi kuwa ba'a maganan adadin da aka zube don wannan party din musamman. Fauxa ta ja hankalin matasa masu daloli dayawa a wurin kuma kowa so yake ta kula shi, sede fa in tana cikin ji da izzarta ko su Rahama shakkar mata magana suke, Fauxa ta riga ta zama hatsabibiya Dukda bata rabin abunda suke, su suna ɗan taɓa kayan maye hakanan su kan yi soyayyar shan minti sede ko ɗaya Fauxa bata yarda da wannan ba. A nan wurin suka yi till down, gab asuba ta sa wani ya ɗauke ta suka nufi gida, Seda ta bari an shiga sallah kan ta shige da sauri, alwala ta ɗaura kawai ta nufi masallaci dayake ta chanza dressing ɗinta zuwa yadda ta fita, Jaddah dauka tayi ta makara a wurin Mammi tunda Mammi ba koyaushe take samun zuwa masallaci ba. Ba se Fauxa ta samu abun yi ba, se ta kwana waje sau biyu ko sau uku a sati wadda hakan ya kara mata buɗewar idanu ba na wasa ba. **** "Malam kwana biyar ne kawai Don Allah ka yarje mana ka taimaka ka Haɗa wannan plan din, in ba Fauxa ba zamu taɓa jin daaɗin wannan party ɗin ba" Kallon Fauxa da tunda suka shigo bata ce komai ba yayi, yarinyar tana burgeshi tashen balaga ke dibar ta gashi Allah ya zuba mata sanyin kyau, ya jima yana bibiyarta tana wulakanta shi... "Albashinka na wata nawa kake so?" Ta watso mishi tambayar, wani fitinanniyar kallo ya watsa mata kasa kasa yace "just one night stand please Fauxa na jima da ƙishirwanki" Wani banzan kallo da ya kara kunna shi kanta ta mishi tace "am not that kind in baka sani ba ma ya kamata ka sani just say your price!" Rahama tace "Sir please just say your price Fauxa ba irin waennan cheap matayen bane...." "Before the count of three say your price or you loose the opportunity! And I must leave to Abuja" Dukkansu uku kallonta suke da tsantsar mamaki, barin ma malamin wata iriyar yarinyace wannan? Me take nufi? Ba de hatsabibancin nata take shirin sauke mishi ba! Be hankara ba ya ji ta ce "3" Tana murmushi ta danna play a wayanta se ga muryarshi yana faɗin just one night stand please Fauxa wlh na jima da ƙishirwanki... A razane yake kallonta zufa na yanko masa rahama da sakina suka saki murmushi lallai Fauxa ta ci lakabin da ake mata na "Hadari malafar duniya, punkasau babban girki, biri da gatari ajalin mai gona, jan ƙasa na bayan ɗaki kowa ya ganki ya tuna Allah. Kadangaren bakin tulu; a barki ki ɓata ruwa a taɓa ki kuma a fasa tulu. Ba a banza ba, biri ke shan duka a rani, kowacce ze hadiye gatari zamu riƙe masa Kota....." Wannan kirari ne da babu wadda be san Fauxa dashi ba kuma har yanzu idan ana son ganin fara'arta cikakke to ka yi mata wannan kirarin shiyasa yawancin ƴan korensu da hakan suke cin kuɗin ta. Cikin dage gira tace "zaka rubuta mana takarda da sunan zuwa excursion na kwana biyar kuma mu uku kaɗai aka zaɓa daga makaranta. Sannan ka sani ka yi wa kanka don ko biyar ba zaka samu ba! Ka yi abinda na ce kan a tashi or else..." Daga haka ta miƙe ta kaɗa mishi idanu ta juya ta fice suka bi bayanta suna murmushin irin zufan da yake Haɗawa.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank 09039206763 Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Goma* *PAID BOOK* *LAST FREE PAGES* Babu yadda wannan malami da ya shiga tasku ya iya haka ya rubuta don tabbas ya san ƙaramin aikinta ne playing wannan audio wa school authorities daga nan kuma ya san aikinshi gabaɗaya ya rasa, time da ta bashi na cika ta zo ta karɓa tana yi mishi murmushin wulakanci irin nata. Aiko tana isa gida Momma ta kaiwa don ta san daga momma ta amince to Baba Prof ma ya amince ta ci sa'a kuwa babu wadda ya hanata tafiyan suka shirya suka wuce akan ma Gombe ne bayan flight aka biya musu zuwa Abuja. Karfe biyar na yamma suka sauka a birnin tarayya Abuja Motoci har biyu suka zo ɗaukar su Dukda duka duka su ukun ne kuma mota ɗaya suka shiga ɗaya na take musu baya, babban masaukin baƙin da har gomnoni da kusoshin gomnati ke sauƙa matukin motar tasu ya taka birki, masaukin baƙin ba baƙon su  bane hakan yasa suka fito kowacce janye da karamar akwati mai taya suka yi ciki. A reception suka haɗe da samarin sakina da rahama suka tarbe su har zuwa masaukin su me ɗauke da parlor da kuma ɗaki daga gani ka san na manya ne, a kujera ta yada zango tana bin su sakina dake lafe jikin samarin su da sunan oyoyo da idanu kan ta taɓe  baki ta maida kanta ga wayanta tana cigaba da dannawa. "Ƙawarmu kiyi ordering duk abunda kike so za'a kawo bari mu je mu zo" Najeeb yaron ɗan majalisar tarayya kuma consultant saurayin sakina ya faɗa, kai kawai ta ɗaga musu su sakina suna daga mata hannu kan suka fice. "Wallahi rahama kawarkun nan ta cika ji da kai kamar ƴar sarki" Sakina ta taɓe baki tace "kuma ba ƴar kowa ba ba" Saurayin ta suhail wadda ɗa ne ga ministan lantarki kuma engineer yace "ya zaki ce ba ƴar kowa ba ina gidan Prof kaka ne gidansu? Waye be san su ba a Nijeriya?" Rahama tace "sani daban wayewa daban, gidan kaman rijiya haka yake don ta samu mun fito da ita shine fa ta fimu feleke, ka ga kuwa manyan guys da take Juyawa? Iskancinta na da girma wallahi" Anan suka bar maganan suka cigaba da harkokinsu na baɗala tsantsan rashin ilimin addini da rashin tarbiya suke nunawa a Filin Allah, ba kuma su damu da su su huɗu ne ɗakin ba. Basu dawo masaukin su ba se dare lokacin fita partyn, sun sameta kwance ɗaure da towel tana bacci, tashin ta suka yi kan suka fara shiri suna hiran irin ɗauke hankali da suke son yi barin ma suhail da yace Zubair din jiji da kanshi na dayawa kuma en matan da zasu je wurin are high class hakan yasa suka ƙara zakewa kowacce ta fita fesss kaman ka sure ka gudu. Wani arnen material lace aka yi mata fitted gown dashi wadda ya fitar da duk wani surarta yadda ya kamata ko numfashi me kyau bata yi amma dayake har ya fara bin jiki bata damu ba, kanta ko ɗan kwali babu se wani gyara da ta mishi jelar na reto a bayanta wani high hill shoe da inches ɗinshi ya kusa huɗu ta saka ta rike wayanta suka fito jewelrys ɗinta se dauke idanu suke. A cikin hotel ɗin ne za'a yi sede ta chan baya, ba su isa wurin ba saida aka fara da ɗan jimawa. Kwas Kwas Kwas haka karan takalmansu ya karaɗe ilahirin wurin wadda hakan ya saka celebrant ɗin da ya fara bayani cikin ƙasaita da ji da kai dakatawa. Chak ya tsayar da fitilun ganinsa bisa kanta, Grey eyes ɗinta da ya ji liner se ɗauke hankali yake, Zubair be taɓa ganin halittar da ya tafi dashi a kallo ɗaya ba sai Akan wannan, don kasa cigaba da bayanin godiyan yayi Dukda su Fauxa har sun sama wa kansu mazauni, class ɗin yarinyar ya burgeshi kwarai don har ta zauna kaman bata san ta fisgi hankalin mutane dayawa daga wurin ba. Taɓa shi da suhail yayi ya saka shi farga da ya ɓace a duniyar fauxa Dukda ko sanin ta be yi ba, bayanin ya karasa aka mishi tafi. Yana ba da mic ya koma ya zauna mazaunin shi yana kallon suhail yace "wacece wanchan? Na ganta da buduruwarka" Suhail yace "Zubair in zaka ɗauke kwalamarka kan wannan ka ɗauke sbd ta fi karfin duk yadda kake tunani" Wani banzan kallo Zubair ya yiwa suhail ze yi magana Najeeb yace "kaman yadda suhail ya faɗa nima shawaran da zan baka kenan..." A fusace yace "saboda ita ɗin ƴar waye kenan? Ta kaini? Ni da na Haɗa sarauta da mulki? Karka manta duk wata kwangila Indai daga fadar shugabar kasa ze fita hannuna yake zuwa, ina juya dala da euro so babu wannan magana, ko ka manta ni ɗin Burin kowacce macece da ta san rayuwa da abunda ya kunsa? Kalli ku ga duka en matan da suka taru anan sun yi ado da kwalliya ne sbd su burgeni har su sace zuciyata kuma kun san babu wacce babanta yake ƙaramin mutum me kuke min tsoro? har ta isa ta yarfa ni?" Suhail ya ce "ita ba ƴar kowa ba amma fa uncle ɗinta babu wadda be yi mishi tayin matsayi ba daga mulkin har sarauta ya ƙi, in kana jin Prof kaka to ƴar gidan ce, yarinya ce amma tana da kwarjinin manya daga jininsu ne" Shiru ya ɗan yi, kan ya ce "ni kuma zan baku mamaki akan yarinyar nan Dukda aurenta nake son yi amma na muku alkawari kan ta bar Abuja se na saye zuciyarta da gwagwalan laffuza da salo na" Ihu suka mai, suka yi dariya a tare yana kara cin alwashi akan Fauxa ɗin. Kowa kan shi yake serving sede Fauza bata motsa ba bare ta tashi ta ɗiba, kanta na kan waya tana kallon wani necklace da yayi mugun tafiya da ita.. "Wow wannan tayi! gashi kuwa ba ƙaramin haskata za kiyi ba da zaran ta hau wuyan ki" Ɗagowa tayi ta kalleshi ba laifi kyakyawa ne ajin karshe, magananshi kuma ya ɗan bata dariya Tace cikin basarwa "sai kuma ya kasance bana neman tayin zaɓin kowa kan abunda na san ze yi min kyau ko akasin hakan" Yayi murmushi ya ce "in kin min izini zan iya zama?" Tace "Allah sarki ai bani da hurumi da kujerun nan ɗin don nima a gayyar soɗi na zo" Yayi murmushi me kyau yace "Ai zuwanki ya fi min zuwan shugaban ƙasar Ingila don ni kaɗai na san irin farin cikin da na shiga da ganinki" Ta ɗan ɓata fuska tace "farin ciki??" Yace "yeah, farin cikin na samu matar aure" Kanta ta mayar kan wayanta kaman ba ita ce tayi tambayar ba, kaman ma bata ji amsar da ya bayar ɗin ba, shima shiru yayi yana jan class ɗinshi. Sun shafe mintuna kusan talatin kan yace "Wow! Zaki yi kyau da sarauta" Idanu ta ɗago ta watsa mai kan ta ɗaga tana kallon mutanen wurin da aka fara watsewa ana komawa cikin hadaddiyar club na hotel ɗin inda anan ne asalin chasun, nan an rage lokaci ne da ɗan abinci da snacks. Ba tare da ta ce mishi komai ba ta sake maidawa kan wayanta. "Princess let's go in its time for the real fun" Mikewa kawai tayi suka jera, yace "sunana Zubair turaki am the celebrant, dukda baki tambaya ba" Se sannan tace "oh happy birthday" Yace "thank you! Where's my gift?" Dan murmushi tayi kawai daidai lokacin suka shiga cikin club ɗin da mata suke ta rawan sanda kida na tashi sai de ba sauti sossai. "What do you want as the gift?" Tayi mishi tambayar. "Just ur heart, kina ban zuciyarki kin yi kyautar da ba zan taɓa manta ta ba" Dariya tayi gayen nan na da aiki, basu sake magana ba saboda kiɗar da aka sauya sauti har wani baya jin maganan wani ana ta rawa color bulb na Juyawa daga blue zuwa yellow zuwa red. Cikin ihu yace "Do you mind a drink??" Itama da karfi kaman yadda yayi tace "Non-alcoholic" Kallon mamaki ya mata, kan ya juya hanyar toilet da ya hango suhail yayi yace "bata shan komai?" Kai suhail da yake ba a hayyacinshi ba ya gyaɗa mai, murmushi yayi kawai ya juya ya tafi gaban bar, inda ya sa aka yi mishi mixing kalar fine wines da yake sha, ita kuma yace coke, ana tsiyaya rabi ya sa aka sa mata whiskey marar taste yadda ba zata ji ba, ya riƙo ya kawo mata tace "thanks!" Shan Nashi ya fara yana ganin yadda take rike da nata tana rausayawa a hankali, bakinta na bin waƙar dake tashin. Suuu ta tafi zata zube a sadda ta gama shan drinks ɗin yayi hanzarin sa hannunshi ya rungumo kwankwasonta cup ɗin hannunta ya faɗi ya fashe, murmushi yayi yana shafa fuskanta da Ɗayan hannun nashi yana Juyawa da ita. "Ashe jininki bashi da ƙarfi" ya faɗa a kunnenta in a whisper. Sossai ta bugu tun tana luuu luuu har ta fara ihu da ƙarfi kaman wacce ke jin daaɗin club ɗin ta fara rawa sossai yana rike da ita yana ƙare mata kallo cikin murmushi, be taɓa Tunanin birthday ɗin shin nan ze zama fun haka ba se yanzu. Sun yi rawa har sun gaji en mata dayawa sun kwashi takaicin ganin shi da ita, ita kam gabaɗaya ta rasa hankalinta. Da sauri sakina ta riƙo hannunta tana Kallonshi tace "Zubair kayan maye ka sa mata?" Sakina tace "mun shiga uku! Haba Zubair ka kuwa san me ka aikata?" Yana smirking yace "normal ne fa, am very sure zata ji daaɗin hakan idan ta dawo hayyacinta" "me nufin ka?" Suhail ya jefa mishi maganan, basu kula da surutan ba.. "Guys calm down ba fa abunda nake nufi, kuma babu abunda zan mata..! A hankali time ɗin da kuke yiwa tsoro ze zo, am very sure nan kusa da kanta zata neme ni da soyayyar abunda kuke yiwa tsoro it's just a matter of time" Ya karashe yana dariya sossai, ajiyar zuciya suka sauke sakina tace "ka bi a hankali wallahi baka san kalar haukan Fauxa bane" Riko ta yayi yana cewa "kuyi abunda ke gaban ku" Yana kai nan ya janye ta suka fice. Da sassarfa yake sauƙowa daga matakalar jirgin idanunshi kan tsadaddiyar agogon dake ɗaure a farar fatanshi, sanye yake da baƙin wando da kuma farin shirt wadda kallo daya zaka mishi ka san pilot ne, baƙin necktie ɗaure a wuyan shi, jacket da karamin brief case a hannun hagunshi. Sauƙar su kenan daga Adis Ababa, da sauri aka buɗe mai gaban wata Prado dake Parke don shi ya shige, drivern dake sanye da kaya me tambarin jirgin da ya tuƙon ya ja suka fice da gudu daga airport ɗin. "Sir ina muka nufa?" Ɗan kallon hanya yayi kan yace "transcope hotel" Saita hanya yayi saboda shirun da garin ya ɗauka yayi ta tsuga gudu bai tsaya ko ina ba se harabar na transcope, sauƙa yayi yana furta "thanks" Ciki ya nufa ba tare da ya jira amsar drivern ba, daga yadda yake tafiya zaka san wannan ɗin zakin namiji ne, fuskanshi a kame sai de be hana kyaunshi bayyana ba. Reception ya dakata ya biya room VVIP, ya karbi key ya nufi elevetor daidai lokacin su kuma sun bi ta bayanshi sun shiga, yana shirin rufuwa yayi saurin saka hannu tare da sanya kai ciki... **Tou Readers anan na kawo karshen free pages ɗin Diddigar ƙaya da Naira ɗari uku kachal zaki mallaki sauran ki sha karatu cikin kwanciyar hankali** DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 11 Sau ɗaya ya sauke ganinshi kan su ya ɗauke kai yana jan tsiririn tsaki, yana rasa me matasa suka ɗauki baɗala suka ɗaurawa kan su a yanzu, in har kana da kuɗin kama suit a hotel ɗin nan kayi sharholiya why not ka ajiye ka fara shirin aure ko mata nawa ne? Duk takaicin shiga cikin elevator ɗin ya cika shi, a hawa na sha ɗaya elevetorn ya tsaya tare da buɗewa. "Babe mu je ko?" Zubair ya faɗa yana ɗago Fauxa da gabaɗaya jikinta ke sake, ture shi tayi ya sake saurin tarota ganin tana shirin faɗuwa garin haka ne gashinta ya sunce ya rufe mata fuska daidai lokacin da Faizan ya sake waiwayowa ganin suna ɓata mai lokaci. A hannunta dake cikin na Zubair ya fara sauke idanu kan ya kai jikinta zuwa fuskar ta da gashi ya rufe kana ganinta ka san ba karamin buguwa tayi ba, Jan ta Zubair yayi ganin elevatorn na shirin rufuwa, da wani irin disgusting look yake bin su har suka fita, ita da fuskanta ke facing elvetor ɗin ta sa hannu ta gyara gashin nata daidai lokacin da elevatorn ya gama rufuwa. Gabanshi ne ya faɗi, ko tantama babu wannan fuskan ɗan gidansu ne Dukda kai tsaye baze ce wacece ba amma tabbas wannan yarinyar tana da alaka da gidansu, floor na 13 elevatorn ya kaishi haka ya fasa sauka ya sake danna na sha ɗaya, da sauri ya fito daga elevatorn yana dube dube, sai de babu su ba alamar su, ya jima tsaye yana tunani a wurin kan ya koma ɗakin da ya kama, zuciyarshi na faɗa mishi Fauziyya ce sai de taya zata bar gida ta zo har Abuja babu wadda yayi noticing kuma ta sha kayan maye? With this her young age? Kai be amince da abinda zuciyarshi ke faɗa mai ba. Bai gansu ba amma ya sha alwashin sakawa floor ɗin idanu sossai ko ze sake ganinta. Ɗaki ya koma ya watsa ruwa yayi sallar isha da shafa'i da wutiri, haka ya kwanta da tunane-tunane a ranshi sbd idan har tabbas yarinyar chan ne lallai ta tabbata annoba kuma se inda karfinshi ya kare wurin ganin an hukunta ta daidai da abunda tayi a cikin zuri'ar su. Da sassafe ya danna kiran Mammi, gama azkar ɗinta kenan tana shirin shiga kitchen sama ma mai gidanta abincin safe ta ga call nashi, ta ɗan yi mamaki kam kan ta ɗaga "Assalamu Alaikum warahmatullah mammi barka da safiya" Ta amsa tana zama bakin gado "Wa'alaikumussalam warahmatullah barka ka dae babana, ka sauƙa lafiya?" "Alhamdulillah mammi, ya ciwon kafafunki hope da sauƙi?" Ta amsa da "Alhamdulillah" Ɗan shiru yayi kan yace "mammi ni kam yarinyar nan tayi tafiya ne?" Shiru mammi tayi cikin tunani kan tace "wace yarinyar kuma?" Yace "wannan na gidan baba Alhj, marar jin." Girgiza kai mammi tayi kan tace "Fauziyyar ce baza'a ka iya faɗa ba sai ka yi ta juye juye? Eh sun tafi excursion Gombe daga makaranta" Da sauri ya miƙe tsaye kenan ba gizau idanunshi ke yi ba ita ɗin ce, yace "mammi yarinyar nan ba Gombe ta tafi ba, jiya na ganta da wani a halin maye da shigar banza!" "Faizan!" Mammi ta kirashi daga jin muryarta ya san ranta ne ya soma ɓaci. "Faizan don baka son yarinyar nan shine zaka ɗauko hanyar yi mata sharri? Buguwa fa ka ce? Sannan da namiji a hotel?" Yace "kin san ban taɓa miki ƙarya ba, kuma a kan wannan annobar ba zan fara ba. Ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba, zan kira Farhan ya je min makarantar ya bincika don bazamu lamunta ta ɓata mana sunan gida ba, Never!" Mammi tace "sunanta Fauziyya, kada ka sake ce mata annoba, sannan takarda da tambarin makaranta da kuma stamp da sa hannu ta kawo ni ta fara kawowa kuma tafiyar ba ita kaɗai ba ce, kar in sake jin irin wannan zance daga bakinka, karka manta ƙanwarka ce kuma karka manta tarbiyar gidan da ka fito" Tana kai nan ta kashe wayan, hannunta har rawa yake, ta san Faizan be taɓa yi mata karya ba, idan ba akwai abunda ya tsana karya ne, sai dae bazata taɓa yardar wa zuciyarta Fauza ya gani a hotel a Abuja ba, kila kama ce kawai. Har ta gama girki tana nazari, Farhan na shigowa gaisheta bayan sun gaisa tace "Farhan ina so ka je min makarantar yaran nan ka samu vice wadda ya sanya hannu a tafiyar su Fauza ya sake tabbatar maka da tafiyar, sannan ya kira wani a Haɗa ku kaji lafiyarta" Farhan yace "mammi wani abun kuma ya faru ne? Na san Fauza sarai yadda kike maganan nan kuma kaman kina ɓoye damuwa ne a ƙasan ranki" Tace "Babu komai Farhan, ka tabbatar kayi duk abunda nace maka" A ladabce yace "To mammi" Mikewa yayi ya fice. *** Yana sauke wayan daga kunnenshi yayi shrugging kafadanshi, a ranshi yana furta 'ina ma ruwana' Ya gyara kwanciyar shi ya fara bacci gajiya tuni ya mance ma da wata Fauza. Ita kuwa a ɓangarenta bacci take yi kaman gawa, ko Asuba bata iya ta tashi tayi ba, karfe takwas na safe wani irin amai ya tashe ta, da gudu ta nemi bayi ta fara kwararawa cikinta na Juyawa, saida ta gama tsab tana dafe da kanta dake sarawa kaman zae rabe gida biyu, a hankali ta wanke bakinta kan ta mike tsaye tana kallon bayin da take ɗin. A hankali Tunanin abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo mata. Wani irin tashin hankali ne ya bijiro mata, jarabar masifarta ta sa har bata gani da kyau, bata san sadda ta lalubo Kalmar "innalillahi wainna ilahi rajiun" ta fara ambata ba. "He drugged me!" Da sauri ta kai idanunta jikinta, tana taɓawa hankalinta in yayi dubu ya tashi. Da sauri ta fito daidai lokacin shima yake shigowa, kanta yayi yana furta "Babe kin tash...." Zazzafar Marin da ta sauke mishi hagu da dama ne ya saka magananshi ɗaukewa. Cikin ihu da masifa tace "Zubair or what so ever, who the hell did you think you are da zaka yi drugging ɗina? U even had the audacity na bani kayan maye?" Yace "am sorry babe! Am so sorry don't be mad I knew I messed up, but listen...." "Ba zan yi listening ɗin ba, get the he'll out of my way!" Ta faɗa da karfi tana nufan waje, hannunta ya riƙo ta juya ta mishi wani wawan tura da saida ya faɗi kan kujerar ɗakin, da sauri ta fice tana danne hawayenta.. Tana fita ta nufi room da aka fara kama musu, abun takaici Bacci ta samu suke yi, toilet ta faɗa ta sakarwa kanta shower kan ta fashe da kuka, abu guda ya saura mata a hanyar da ta ɗauko shima yana zuwa, tunda har ta iya ɗanɗana kalar buguwa watarana zata faɗa zina. Ta fi mintuna talatin kan ta fito, ta samu Sakina na waya, gata nan sir. "Yayanki Farhan ne yaje office na vice wai yana son Magana dake" Abun Dukda ya mata banbarakwai kuma gabanta ya faɗi haka ta sa hannu ta karbi wayan ba tare da tace komai ba. "Ina kwana ya Farhan!" Yace "kina lafiya?" Ta amsa da. "Eh" Ba wani magana suka saba ba, don haka yace "mammi ne ta matsa a zo a ji lafiyarki" Tace "Allah sarki! Ina lafiya gobe ma zamu dawo, an fasa sati Ɗayan" Duk kallonta suke, har ta kashe wayan. Se a sannan ta fitar da ɓacin ranta "am so so disappointed in u sakina nd rahama, kun san bana shan giya don Zubair ya bani na bugu na san ba laifin ku bane amma taya Zaku fara barin shi ya tafi dani na kwana gado ɗaya dashi? Me kuke tunani?" Rahama tace "kiyi hakuri muma duk sadda ya tafin daken ba a hayyacinmu muke ba bare mu hana shi tafiya dake" Sakina tace "to menene ma don ya tafi dake ɗin, ai tunda kika zabi wannan hanyar dolen dole watarana kin sha kayan maye, ita ma abunda kike yiwa gudan dole ne ya sameki so just chill ki sake jiki, ki waye pls" "tir da wayewar zina da shaye shaye, kun kuwa san azaba da fitinar dake cikin waennan abubuwa?" Kallon juna sakina da rahama suka yi kan suka washe da dariya, sakina tace "lallai ashe ƴar gidan malamai ce" Tafiya tayi gaban kayan ta ta fara Haɗawa ba tare da tace komai ba. "Haɗa kayan me kike? Cewar rahama "gidanmu zan koma." "Amma ai sati guda muka ce zamu yi" "ba zan yin ba". Tunda ta fara basu amsa a haka sun san in suka cigaba be gameta ba su samu gagarumin matsala se suka kyale ta. Knocking aka yi, Raham taje ta buɗe, samarin guda uku ne, duk suka janye en matansu suka bar ta ita da Zubair a ɗakin. Gabanta yaje ya durkusa bisa gwiwowinshi, cikin lalama yace "am very sorry! Na san ban kyauta miki ba amma wallahi ba da wani mugun nufi na baki ba, na zata kina sha a lokacin ne kawai ba kiyi niyyar sha ba shiyasa na baki don na tsokane ki, zuciyata zafi take min ina ganinki cikin wannan yanayi Fauxa, na tuba please" "leave me alone zubair" Ta faɗa calmly Dukda fuskanta a mugun haɗe yake. Kanshi ya duƙar daidai kafafunta sai digar ruwa taji. Da sauri ta ɗago, a take yayi deceiving ɗinta da crocodile tear ɗinshi yace "am sorry please Fauza" Tace "Abunda ya faru ya riga ya faru" "Kin yafe min?" Ya tambaya cikin murmushi da yayi mata kyau, kanta kawai ta mayar kan wayanta, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani box me kyau daga idanu zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba yace "accept this as my apologies dear" Ɗagowa ta sake yi ta kare mishi kallo, ba laifi Zubair kyakyawa ne, sai de kallo ɗaya zaka mishi ka san crook ne, ga kuɗi ga iskanci. Hannu ta sa ta karɓa ta buɗe, kasa ɓoye excitment ɗinta tayi tace "isn't it that necklace..?" Wadda take kallo jiya har yake cewa ze mata kyau. Murmushi ya saki ganin ta saki ranta, ta mishi godiya. Zama yayi a gefenta suna hira jefi jefi, duk yadda suka so su hanata tafiya a washegarin tace ita sam gida zata koma. Duk abunda take chan Kasar zuciyarta bakin ciki ne fal na kayan maye da ta sha, ga sallar asuba gari ya gama wayewa, se istigrafi take yi haka dae Zubair yayi ta lallaɓata yana yaudararta bata yi wani fushi mai nisa da shi ba.. Washegari da safe da kanshi ya kaisu har Airport ya mata sayayya mai yawa ya hada da kuɗi, duk da ya burgeta, sai de fa bata nuna ba. Sauri sauri ya shigo Airport ɗin don shi ze tuƙa Max Air ɗin zuwa birnin Yola daga Abuja, gashi ya so yayi letti, a cikin jirgin ya haɗu da sauran crew ɗin da kuma wadda ze taimaka mishi suka gaisa, he supposed to be a mazauninshi tunda har an soma shiga amma se ya tsaya daga bakin kofan, waya yake amsawa lokaci lokaci ya kan ɗaga idanunshin nan ya kalli masu shigowa ɗaya bayan ɗaya. Gudu gudu suka karaso don ana final announcement ne, Sakina ce a gaba sai Rahama kan ita, loggage ɗinsu bai da nauyi so kowacce na riƙe da nata ne a hannu, Sakina ce ta fara wucewa ta mika ticket ɗinta, aka bata na seat number ɗinta ta shige, rahama ma ta shigo tayi hakan sai Fauza ta sanyo kafafunta cikin jirgin.... *Toh Alhamdulillah! Free pages sun kare saura ni daku da kuka biya paid, na san kaunar da kuke yiwa labarin ne ya saka ku nuna wannan soyayya sai dai har yanzu ina kara jaddadawa ba zan san kuna kaunar littafin ba idan har baku comment, ni karan kaina ba zan ji kwarin gwiwar yi muku typing ɗin ba due to squeezing time kawai nake nake yi don ina aiki, bani da enough time na kaina, sannan typing in kun ga kun samu da rana to shikenan amma ka'ida sai dare in shaa Allah zan din ga yi don nafi samun time between magrib, isha. Looking forward for ur comments and love🥰🙏 DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 12 Daidai tana sanyo kafa shi kuma yana Juyawa, an tambayeshi wani code da se ya duba paper ɗin don be riƙe ba, har ta gama ta wuce seat ɗinta chan karshe be dawo ba. "Ke kinga wani haɗaɗɗen captain da ya tafi da ni? Wlh ya haɗu karshen haduwa ina ma zan samu ko phone number ɗinshi ne" Rahama dake kusa da ita ne ke maganan cikin koɗa kyaun wadda take magana a kai da ita bata sani ba. Tace "ni ban ga wani captaina ba, kuna da matsala ai ku kam" Ta faɗa jin sakina ma ta karɓa tana taya rahama gulman wadda bata gani ba ita kam. Har suka sauƙa yola basu daina maganan captain ɗin nan ba, Sakina Dan Tsoho hotel tayi don chan zata karasa satin da tace zatayi a gida, yayinda rahama tayi gida don duk iyayenta basa ƙasar, cab ne ya sauke ta kofar gida ta sauka tare da miƙa mishi kudinshi ta Janyo loggage ɗinta tayi ciki. Harabar gidan nasu tsabtsab ba kowa ta tabbatar yanzun haka suna school tunda kwata kwata karfe goma ne na safe, sashen jadda tayi direct a parlor ta taddata kan sallaya ta idar da walaha tana tasbihi, da gudu ta zo ta faɗa jikinta tayi shiru tana sauke numfashi. Ɗago fuskanta Jaddah tayi cikin farin cikin ganinta tace "oyoyo oyoyo! Maraba da mutanen Gombe kune da safen nan?" Kai kawai ta gyaɗa ta sake mayarwa tayi lamo, Jaddah ta ɗago ta gabaɗaya tana kallonta "lafiyan ki kuwa? Ko baki da lafiya ne kike hawaye?" Hannu ta sa ta share kwallar tare da karya wuya tace a shagwabe "kewarki nayi Jaddah na" Dariya Jaddah tayi tace "to ba gashi kin dawo ba? Ba shikenan ba? Oya tashi je kiyi wanka ki sauya kaya bari na sa zaliha ta sama miki abunda zaki ci" Mikewa tayi ta nufi ɗakinta tana cewa "ya yi yaji pls" Tana shiga ta jefar da Akwatin tare da dogon hijab da daga Airport ta sanyo shi zuwa gidan, ta shige toilet ta sakarwa kanta ruwa tana lumshe idanu, se yanzu take jin wani sukuni na rufe ta, lallai ta zalunci ahalinta tayi fatali da tarbiyar gidansu, tunda ta dawo daidai take jin rashin daaɗi a zuciyarta na abunda ta aikata amma fa wani zuciyar na kwaɗaita mata daaɗin shi. Bayan ta fito tayi shafe shafenta ta janyo tsarabar da Zubair ya Haɗa ta dashi, chocolates ne daban daban se wasu designers perfume guda biyu se, hoodie ash na kamfanin Fendi. Boyesu tayi a wardrobe ɗinta kan ta zaro riga ƙarami fari da wando navy blue ta saka, wandon a kaurinta ya tsaya ya kuma matse ta ya fitar da duk wani shape ɗinta, gashinta ta taje ta sake shi, tana shirin kwanciya Call na Zubair na shigowa wayanta, da sauri taje kofa ta rufe da key kan ta dawo ta haye gado tare da shigewa bargo ta amsa. A hankali suke waya tun bata saki jiki ba har ta sake saboda ya iya hira da sanya dariya ga kalamai, ta shagala sossai se jin bugun kofa tayi da sauri ta ce mai tana zuwa ta kashe wayar tare da boyeta cikin Rigan pillow ta dirka taje ta buɗe kofan. "Jadda tace ki fito ki ci abinci kar kiyi bacci baki ci ba" Cewar zaliha. Bayan zaliha ta bi suka fito tare, kan kujera ta zauna bayan ta ɗauki abincin daga cikin tray da zaliha ta shirya ta fara ci, Jaddah na bata labarin irin kewar ta da suka yi gidan yayi shiru sossai a kwana biyu da bata nan. "Ashe ana kewata amma in ina nan kowa ya buɗe baki Fauxa kaza Fauxa kaza!" Jadda zata yi magana wayanta ya fara ruri ta duba tace "oh kai kuma se yau ka tuna dani" Ko bata faɗa ba Fauxa ta san waye don haka ta maida kanta kan TV Dukda wa'azi ne gwara ta ji da ta ji zancen da zasu yi. Bata san ma jaddar ta kashe ba saida taji tana cewa "Fauziyya yi sauri gama ki je ki sharewa Yayanku ɗaki ki wanke mai toilet yadda kwana biyu be zon nan ba na tabbatar yayi kura kuma kin san shi da rashin son datti, yace min ya shigo garin gida ne dae ze ɗauki mintuna masu yawa kan ya karaso akwai abunda ze yi" Haɗe gabas da yamma tayi kaman zata yi kuka tace "Jaddah ina Fatima da ni zan mishi aikin ɗaki yau? Allah ya kyauta wlh kin dae san kap rayuwata ban taɓa taka kafa ɗakin shi ba haka kawai ba zan fara yau ba..." "Fitsararriya ajiye abincin nan ki wuce kan in Haɗaki da abincin in take" Cewar baba Alhj da yake shirin shigowa sallamar da ze yi ma be yi ba sbd abunda yaji Fauzar na faɗawa Jaddah. Da sauri ta miƙe tsaye "ban hanaki saka waennan kayan ba?" Da sauri ta wuce ɗaki tana tura baki seda ta shiga ta fara kunkuni, kaman zatayi kuka haka ta sanya hijab kato har ƙasa ta fito, ta samu baba Alhj na cewa Jaddah "Mama ni fa ba tsanar ta nayi ba, halayen ta ne bana so, a yadda Fauziyya ta ɗauko rayuwarta wlh bata so gamawa da duniya lafiya ba, tun da ta sanya kafa ta bar sashena bata sake zuwa ko da gaisheni bane wai dani uban ta zatayi gaba? Har Fauziyya ta bar garin nan bata iya zuwa ta min sallama ba se a bakin mamanta nake ji?" Kanta ƙasa tace "key!" Jadda tace "Kin san inda nake ajiyewa ai" Ɗakin Jaddar ta wuce ta ɗauko ta zo ta fice jin Jaddah na bashi hakuri ta kuma tabbatar mishi da ta tura ta ta mishi sallama saide kila zuwan ne bata yi ba, zata mata faɗa Adu'a da lallashi Fauza ke bukata ba faɗa da duka ba. Ita kam ta wuce abunta, ita fa a yanzu mahaifin ta bata san wani baabi ta saka shi ba, dukda tana son shi sossai da sossai saide wannan kiyayya da yake nuna mata yasa itama take jin babu ruwanta da shi (Subhanallah). Direct ɗakin Faizan ta wuce, a hankali ta tura kofan bayan ta murda key ɗin, kamshin room freshner da na turarukanshi ne suka bugeta, inda zata iya jinjina mishi kenan tsabta da kamshi, komai tsab tsab yake a ɗakin Sam babu tarkace kaman ba ɗakin namiji ba. Gado ne a ɗakin saɓanin sauran ɗakunan samarin gidan dake da katifa, daga gaban gadon akwai set na kujeru se TV manne jikin gini, daga gefe akwai ɗan corridor inda drawer ɗinshi yake se kofar toilet, bedding ta fara cirewa ta chilla cikin kwando wankin dake gefen wardrobe ɗinshi tare da ɗaukan tsintsiya ta fara aikin ɗakin, tana yi tana mita da masifa wlh ba don jadda ba da abunda zata mishi a dakin nan se ya kusa kasheta, sannan itama yanzu tana son lafiyar fatarta inda Allah ya taimake shi kenan. Tsab ta share ɗakin ta gyara tare da kunna burner ta sa turaren wutar da ta gansu kan dressing mirror ɗinshi masu kamshi irin na asalin Maiduguri, ta kunna Ac take ɗakin ya ɗau kamshi, bayi zata shiga se ta cire hijab ɗinta ta ajiye kan cushion kan ta wuce bayin, komai tsabtsab, wankewa tayi tana yi tana masifa, haka dae ta gama ta nufi fita. Tana sanyo kai ɗakin shima yana sanyowa, a kan junansu idanunsu suka fara faɗawa, wani irin disgusting look na me kike min a ɗaki ya fara watsa mata, ita kuma se ta so rikicewa don ko yaya Faizan na da wani kwarjini da babba ma se ya ji wani iri in ya zuba mai idanun nashi bare mace karama irin ta. Bata saba gaishe shi ba don haka bazata fara yau ba, wucewa Tayi ta ɗau hijab ɗinta zata sanya, se lokacin ya tuna abunda ya gani a Abuja don haka kai tsaye hannunta ya fara bi da kallo, kan ya maida idanunshi kan body shape ɗinta da ya bayyana sossai a wandon kaman yadda ya bayyana a wanchan kayan da ya gani, daga karshe ya kai kan gashin kanta daidai lokacin ta gama sa hijab tare da nufan kofa. Kai tsaye yace "Ke!" Chak ta tsaya, ya fara takowa gabanta hannunshi zube bisa aljihun wandon shi. "Ke! Sa gwiwowinki a ƙasa" Da sauri ta kalleshi kaman zata fashe da kuka tace "Amma me na y...." Ɓas haka ya buge mata baki da sauri ta dafe bakin yace "kin yi abunda nace ko se na tattaka ki?" Da sauri tayi kneeling ranta duk ya gama ɓaci wani tsanar shi na sake mamayarta. Shi bai damu da ita ba don haka be damu da ko ta gaishe shi ko bata gaishe shi ba, clearing thoughts ɗinshi kawai yake son yi.. "Me ya kaiki Abuja?".. Rassss haka gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, hannayenta suka soma rawa, bata ɗago ba don tana ɗagowa firgicin idanunta tsab ze bayyana rashin gaskiyarta. "Don't let me repeat myself... Uban me ya kaiki Abuja? Me kika je yi a Transcorp Hilton?" Gabaɗaya wani irin zafi ne ya rufe ta kaman an sanya ta cikin Kasar tukuban tsire "A...abu...ja kuma?" Be yi magana ba, tace da sauri "ni babu abunda ya kaini Abuja, ban je Abuja ba" Duk yadda ya so ya firgita ta ta faɗi gaskiya be samu nasara ba sbd ta kafe kai da fata ita bata je Abuja ba. Tsaki me karfi ya ja yace "get out of my sight" Da sauri ta miƙe tayi kofa ya sake cewa. "Ke!" Chak ta tsaya, yace "this is the last time da zan ga waennan singallin kafafun naki a ɗakina bana son harka da kazamai kin gane ko?" Kai ta gyaɗa wani irin takaici na zuwar mata wuya, duk Jaddah ce ta ja mata. Da sauri ta fice tayi sashen Jaddah kaman zata fashe don fushi da tashin hankali. Taya aka yi Ya Faizan ya ganta a Abuja? Allah ka rufa min asiri. Ta furta tana me shiga parlorn Jaddah har zata wuce jadda tace "Fauziyya" Dawowa tayi tana amsawa ganin jaddar is serious. "Fauziyya kin san girman iyaye ko? Kin kuma san saɓawa iyaye kaman saɓawa mahallicci ne ko? Sannan kina gani irin yadda mahaifanki basu saɓa mini ba meyasa kike shirin daukar wani hanyar saɓa musu alhali ban koyar dake ba?" Raurau tayi da idanu tace "me nayi kuma Jaddah?" "Meyasa zaki yi tafiya baki sanar da mahaifin ki ba? Ba wannan ba meyasa tunda kika dawo nan baki je kin gaida shi ko sau ɗaya ba? Kina son ganin haske a rayuwarki? Ya kamata ace kiyi nadama ki shiga alhini akan korar da yayi miki a sashenshi amma Fauziyya duk babu? Ko don kinga kina dani? Har fa rashin lafiya mahaifin ki yayi cikin wata biyar din nan ashe baki je kin gaishe shi ba?" Bakinta kaman ze taɓa gini tace "amma Jaddah kina ji yace ko ganina baya son yi, taya zan kai mishi fuskar da baya son gani da sunan gaisuwa?" "Fauziyya!" Jaddah ta kirata ranta na ɓaci. Hawaye saura kiris ya zuba mata, dama bata dawo ba da wannan damuwar da ta dawo ta riska kuma. "Naji jadda zan gyara yanzu kullum da safe kan in tafi makaranta zan je in gaishe shi ba shikenan ba? Kin turani ɗakin wanchan ya wulakanta ni kin huta!" Tana kai nan ta tashi ta wuce fuuuu, girgiza kai Jaddah tayi tana furta "Allah ya shirya Fauziyya" Ita kuwa tana shiga ta rufe ɗakin tare da yin wurin pillow ta dauki wayanta ta kira Zubair, shagwabewa tayi tana faɗa mishi abunda Faizan yayi mata. Lallashinta yayi tayi, dukda duk sun sha mamakin yadda aka yi ya ganta, tace ita bazata kara tafiya wani garin ba kuma amma shi Zubair ya tabbatar mata akwai hanyoyi dayawa da zasu bi ba me ganinta. Satin Faizan biyu aka sanya bukin su da Fatima nan da wata biyu, sbd har sun fara waec. A take duk bangarori aka fara shiri, ita dae Fauza kaman bata san ana yi ba harkokinta kawai take, ko da Fa'iza ta zo mata da maganan anko ma kai tsaye tace bazata yi ba, su karata chan daga Amaryar har Angon babu abunda ya Haɗata dasu.. Jadda ce ta bada kuɗin nata, Zubair ne yake shirin zuwa Dukda ta ƙi ya ki, wai yayi missing ɗinta Dukda sukan yi waya, su yi video call duka. Gabaɗaya ya lalatata da soyayyarsa, a gefe ɗaya babu abunda ya sauya daga abubuwan da take yi sai giyar da bata sake sha ba tun daga ranar da abunnan ya faru. Babanta kuwa ta kan je kullum ta gaida shi, iyaka abunda ke hadasu kenan, wurin mammi ne take girke girkenta hakan ya sa mammi fahimtar abubuwa dayawa daga gareta, har yau bata manta wayar da suka yi da Faizan ba, hakan yasa lokuta dayawa ta kan ja ta da nasihu kala daban daban wadda ya kan kashe mata jiki amma daga ta bar sashen shikenan. Faizan ya koma bakin aikinshi inda ya Haɗa Fadila da haɗe haɗen kayan aure, dukda ta ce bazata samu zuwa ba sede zata turo ta jirgi se ya karɓa. Wasa wasa buki ya ƙarato, Amarya da mahaifiyarta ana ta shiri, mutanen Maiduguri sun cika gidan kai ka ce bukin farko kenan a zuri'ar, ba karamin takura Fauza suka yi ba Dukda ta tsaya kai da fata tace babu me saukar mata a ɗaki bukin munafuka da azzalumi, hakan ko aka yi sbd gudun jarabar ta babu wadda ya sauka a ɗakin nata. Walima, saukar Qur'ani se reception wadda maza ne kawai zasu yi bayan ɗaurin aure aka shirya kaman yadda ake kowani buki a gidan. Zaune take kan dressing mirror hannunta riƙe da waya tace "ka fa san irin gidan da na fito Zubair, yanzu in bar gidan nan in same ka hotel kana Tunanin babu wadda ze fahimta?" Yace "ni dae ki san yadda zaki yi, Haba sweetheart in taso tun daga Abuja in zo har Adamawa don ke kaɗai abinda zaki saka min da shi kenan? Ganinki ma yayi min wuya?" Tace "kayi hakuri! Zan san yadda za'a yi na fito" Yace "ko ke fa, ina Green land" Tace "Toh" Tsab ta shirya cikin wando jeans crazy da wani armless shirt, ta gyara gashinta sossai ta feshe jikinta da turaruka kan ta ɗauki karamin jacket ta ɗaura saman Rigan ta zumbula hijab ta fito, duk an shiga sallar isha masallaci ga muryar Faizan na tashi cikin nataatsiyar karatunshin nan haka ta fice babu wadda ya lura. Napep ta tara tayi Jimeta, kai tsaye ɗakin da ya faɗa mata ta wuce, tayi knock ya zo ya buɗe mata tana shigowa ya rungumeta "oh my babe, I really miss you wlh" Ta zame tana furta "miss you more" A kujera ta zauna tana zare hijab ɗin jikinta, shishar da yake sha ya mastar mata dashi gabanta ba tare da yace komai ba. Ta karɓa ta ɗan zuƙa kan tace "Wow the flavor is giving.. Wanne da wanne ka Haɗa?" Ya mata bayani yana karawa da "karki damu ba wai bugarwa yake ba kawai dae zaki jiki fresh out of ko wani irin tunani na damuwa ko kunci" Tace "kaman ka san bana cikin daaɗin rai wai yarinyar nan Fatima tun fa da ta sa na bar sashenmu ban sake mata magana ba haka itama, shine yau na shiga wurin Ammi ina fitowa kawai naji tace min wai ina kwana Fauxa, ashar na lailaya mata kawai na ji rankwashe babu faɗar da Baba Alhj be min ba, harda zata bar mini gidan in jika a ruwa in sha, wlh na tsani abu da munafuki in ba don ta kalli baban ba na tabbatar haka zata goge ni mu wuce juna" Yace "Ki kwantar da hankalinki ina ce jibi ne zata bar miki gidan kowa ya huta?" Kai ta gyaɗa tace "bana fata har abada mu sake haduwa in ta tafi kai daga ita har mijin nata ma" Tana sha ne take ta wannan masifar, lallaɓata yayi tayi da kalamai, daga karshe se gata jikinshi dukda yadda take nuna mai bata so, haka yayi ta rinjayarta, da gasken gaske shedan ke shirin tasiri wurin, tayi saurin mikewa tace "bari na zo na tafi kar a kula bana gida" Yace "mu je dae mu ɗan ci abinci kan ki wuce ko?" Hijab ta dauka yayi saurin karɓa ya ajiye yace "me haka? A ganni ni Zubair turaki dake da wannan zumbuleliyar hijabin? Inaaa" Gashinta ya gyara mata ya riƙe hannunta suka fito, da gaske Fauza na da kyaun fusgan hankalin jama'a, shigar ta kuma ya sa kowa ya kalleta se ya sake kallo, kaman ba ƴar musulma ba. Restaurant suka shiga, yayi musu order har da su fine whiskey, sun yi nisa a cin abincin kaman daga sama taji wata razananniyar murya ta Furta "FAUZIYYA!!!" DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 13 Kamar yadda rugugin aradu ke sauƙa haka sunan nata ya saukar mata barin ma a sadda idanunta suka gane mata wadda ya ambaci sunan, wani irin razana da tsorata tayi har bata san ta miƙe kan kafafunta ba, sake ambatar sunan nata da yayi da irin yadda jikinta ke rawa yasa Zubair mikewa yace "wai waye wannan ɗin ne?" Takaici ya hana Faizan cewa komai, wani irin fisga yayi mata da saida ta buge da jikinshi ya janye ta suka yi waje saboda idanu dake kansu, motar shi ya karasa ya buɗe ya cillata ciki har Seda ta bugu ta saki kara, be damu ba ya sawa motar key, ya juya ya koma cikin hotel ɗin Zubair dake tsaye yana kallansu zafin ran dake kan fuskan Faizan kaɗai ya hanashi fuskantar shi Dukda kasancewar shi shima namijin ne, amma an ce wargi ma wuri yake samu. Shi kuwa Faizan wurin abokananshi ya nufa dama abunda ya kawo shi hotel ɗin kenan, abokananshi da suka zo ɗaurin aure duk a hotel ɗin ya kama musu masauki shine ya zo ya ɗan rage dare yaji kuma if they are comfortable with the suits se idanunshi suka mishi mummunar gani, don mummunar gani zai ce dama ya riga ya ɗaura alamar tambaya akan wannan yarinya don fitsararta ma kaɗai ya ishi ta fara bin maza, in ba ta san maza ba babu yadda za'a yi ta bushe idanunta akan kowa har uban da ya kawo ta duniya, amma bata yi a wurin da ya kamata ba don yau kakkanninta zata ci. Runtse idanunta tayi gam gam, gumi na tsatsafo mata na laifin da ta aikata da kuma na rufe ta a motar da yayi babu iska don be sauke window ba, dunkulewa tayi wuri guda kaman sardine ga kanta dake sarawa na abun maye da ta sha wadda ta sha ne don ya ce mata ba wani bugarwa yake yi ba. Yau dae ta san me kwatarta a gidansu se Allah, dama an ce kwana 99 na ɓarawo kwana 1 na me kaya yau dubun ta ya cika, ta maimaita innalillahi wainna ilahi rajiun ya fi cikin chasbi. Saida ya shafe mintuna sama da hamsin kan ya fito lokacin har bata iya jan numfashi me kyau don azabar zafi, wayanta ne ya fara ruri, ɗauka tayi tace "Zubair ka kasheni! Na shiga uku" Yace "Babe wanene wannan ɗin? Ya za'ayi ya barki cikin mota window a dage mota a rufe?" Se a lokacin zazzafar hawaye ya sauko mata tace "yayana ne! Kuma wallahi baya ƙaunata ko na sulen kwabo ba rufamin asiri zai yi ba, kashina ya bushe.." "Yaya zamu yi kenan babe? Ko na saka hukuma?" Ta zaro idanunta gabaɗaya tace "whattt? Ka rufamin asiri ka barni da abunda ka ja mini Zubair... Na shiga uku! Gashinan zuwa." Tana kai nan ta kashe wayar tare da makalewa a cinyoyinta. A jikin motar ya tsaya ya fara kiran Baba prof. Bayan ya ɗauka cikin ladabi yace "Baba akwai wata gagarumar matsala ce da ta tunkaro rayuwarmu wadda dole ce ta sa zan bayyana muku don idan na rufe ma na ha'inceku" Baba prof yace "Kowani bawa da kalar tashi kaddarar da jarabawar, ruwanmu ne mu karɓa ruwanmu ne kar mu karɓa amma idan muka karɓar mun cika wani sashe ne na imaninmu kaman yadda in muka saɓa ya zama kaman saɓawa ubangiji.... Menene?" Yace "baba ku zauna a parlornka ku jirani don fa idan na faɗa a waya ba lallai na gamsar da ku ba." Kashe wayan kawai baba yayi dama yana zaune da Baba Alhj da Jaddah ne, yana sauke wayar ma se ga mammi ta kawo musu tea kasancewar su akwai kaunar sha'i musamman wadda yaji kayan haɗi. "Kai da waye haka? Allah ya sa dae lafiya" Jadda tayi tambayar. Cikin nazarin abunda ze faru yace "Faizan ne kuma dae kaman ba lafiya ba" Tea ɗin Mammi ta zuzzuba ta miƙawa kowa, suka fara sha suna ɗan tattauna abunda ze iya kasancewa don duk tsumayin abunda Faizan ke tafe dashi suke. Parking motar da aka yi dab kofar baba prof ɗin shi ya sa duk suka maida hankali kan kofar gabansu na faɗi, kaman an cillo kayan wanki haka ya watso ta ta faɗi a ƙasa gashinta ya rufe mata fuska, duk tsaye suka miƙe suna kallonta. "Faizan menene hakan? Wacece wannan ɗin" Runtse idanu baba Alhj yayi ya sake buɗewa jiri na shirin yarda shi yace "Fauziyya???" Duk kallonta suka yi daidai lokacin ta miƙe tsaye tare da janye gashinta tace "Na'am" Da gudu Farhan da shigowanshi kenan ya tare Baba Alhj dake shirin faɗuwa amma ya fusge yayi kanta, ya fara dukanta yana cewa "ni kike amsawa idanu a sama don tsaurin ido? Fauziyya kasheni kike son yi ki huta? A ina ya samo ki? Kalar tarbiyar shigar da muka koya miki kenan? Innalillahi wainna ilahi rajiun..!!" Misalta irin tashin hankalin da suka shiga a sannan ɓata lokaci ne, barin ma da suka fahimci a buge take, sossai jadda ke kuka abunda ya kara ɗaga hankulansu kenan. Baba prof ne ya hana a taɓa lafiyanta, yace "Aisha kamata ku je wurinki, karki bari kowa ya fahimci halin da take ciki zamu yi zama in an watse bukin nan, amma ko kofar parlor ban yarda ta taka ba" Da kallon takaici da kyama kawai yake bin ta har Mammi ta cire hijab ɗinta ta rufe ta don se layi take yi a haka kuma duk wadda ya ganta se a ajiye alamar tambaya, ita kuma ta yafa mayafin kayan ta da ta ɗaura a kai ta rungumeta suka wuce cikin gida. Allah kaɗai ya san irin mazan da ta bi da irin surartan nan, haka dae babu daaɗin rai aka kira likita ya zo ya duba Baba Alhj da jikinshi ke neman yin tsanani ana gwadawa kuwa jininshi yayi mugun hawa. Jadda ma jininta se da ya hau bata taɓa zato ko tsammanin hakan daga Fauza ba, yarinyar karama waye yayi influencing nata haka? Rai babu daaɗi aka watse haka bukin auren ya rage armashi don abunda ya tunkaro su in basu yi da gaske ba akwai babbar matsala. Haka mammi ta saka ta a gaba bayan ta kwantar da ita tana kallo hawaye na zuba mata, wani irin tausayin rayuwar yarinyar na rufe ta, me ta nema ta rasa? Menene ya tura ta ga wannan halaka haka daga gidan mutunci? Mammi ta hana kowa kusantar ɗakinta yayinda Ko motsi Fauxa bata yi ba se washegari da rana ya gama fita, amai da ciwon kai ya tasheta. Mammi na zaune kan sallaya ta idar da wahala lokacin sha ɗaya taga tashinta da gudu zuwa bayi, da kallo ta bita har ta ɓace, yadda ta kwana bacci haka duka ahalinta suka kwana kan sallaya suna mata Adu'ar shiriya. Ko da ta fito zata sake komawa ta kwanta mammi tace "Fauziyya" Ta amsa ba tare da ta iya ɗaga idanu ta kalleta ba. "Koma ki watsa ruwan zafi" Komawa tayi bayin, bata da wani tunani kuma da zata yi tunda abunda ya faru ya riga ya faru, kafin ta fuskance su ne take jin tsananin tsoro amma yanzu da bayan Kowa ya sani kunya ne ke ɗawainiya da ita. Mammi da kanta ta aika aka ɗauko mata kaya, ta sa aka hada mata abinci aka kawo har ɗakin, sadda ta fito ta shirya mammi ta mata nuni da tray ɗin, haka ta janyo ta ci sbd yunwa dake dawainiya da ita, rama sallolin kanta tayi duk abubuwan nan bata yarda ta Haɗa idanu da mammi ba sbd kunya. Bayan ta idar ta gaida mammi tana wasa da kasan hijab ɗin nata. Mammi ta amsa kan tace "Fauziyya" "Na'am mammi" "Fauziyya kin san irin rayuwar da kika jefa kanki kuwa?" Kanta na ƙasa hawaye ya fara kwarara bisa fuskanta tace "mammi Adu'a Zaku yi min, nima ban san me yake damuna ko meyasa nake fadawa halaka bayan na sani ba, wani lokacin kasa fahimtar kaina da rayuwa ta nake, chan kasan zuciyata bana jin daaɗin hanyar da na hau sai de wani zuciyar na tirsasani ƙarbar hakan ta wani fuska..." Kuka ne ya ci karfinta. Mammi ma hawayenta na tsananin tausayin Fauzan ta share, tace "ɗauko Alqur'ani ki karanta Fauziyya" Mikewa tayi tayi yadda mammi tace, tayi karatu har azahar suka yi salla tare, kan mammi ta sa ta sake kwanciya. An yi walimar Fatima Dukda sun fahimci armashin auren ya ragu sossai sai de babu wadda ya san dalili washegari aka ɗaura aure aka yi saukar Qur'ani. Ko kofar ɗaki kaman yadda Baba prof yayi umarni Fauza bata taka ba, ta ci abinci tayi ibada se tayi bacci, duk tunani ya fara cin karfinta ita yanzu ko wayanta bata san hannun da yake ba, taji mammi na maganar Amarya zasu kai wani sati kan su tare don haka daga washegarin ɗaurin auren mutane dayawa suka watse. A daren Ammi ta zo ta sashen mammi daga bakin kofa ta tsaya tace "ke Fauziyya! Tunda ba a nan aka binne cibiyarki ba ki tashi ki wuce mu tafi, tun aka fara hidimar nan neman duniya na yi miki babu wadda ya iya buɗe baki ya ce min ga inda kike? Meyasa ne ake nema se an tauye min hakkina a matsayinki na ƴata kaman yadda aka tauye min sauran hakkokin nawa? Me kuma aka ce kinyi wannan karo?" Kanta ta ɗago tace "Ammi kiyi hakuri" Ammi ta aika mata da wani kallo tace "ban gane ba? Kinga tashi mu tafi mayi maganar kaman kowacce uwa da ƴa a ɗaki" Mammi tace "baba prof yayi umarni akan ko kofa be amince ta taka ba har se ya neme ta" Wani irin kallo Ammi ke mata "wani ta kashe ko mene?" "Wannan kuma shi zaki tambaya Ammin su" Neman tada zaune tsaye take wai baba Alhj ya ki ce mata komai, Jaddah ta ƙi ce mata komai sannan yanzu zata zauna da yarinyar ta ace ba haka ba? Akwai wadda ya haifa mata ne.. Baba prof be so hankalin kowa ya dawo kan abun ba amma saida Ammi ta janyo hakan Dukda yadda Fauza ke hanata maganan. A take kowa ya san akwai abu a ƙasa, hakan tasa ya kira meeting kawai. Kowa da kowa har da Amarya ta hallara, babu wani bare duk mutanen gidan ne. Kai tsaye ya buɗe taro da Adu'a kan ya fara magana akan jarabawar yana misalai da magabata akan dole Allah ze jarrabeka ta hanyar 'ya'yayenka wani dukiya wani mata babu yadda babu kaman yadda mahaifin Annabi Yusuf annabi yaqub yake annabi amma 'ya'yanshi suka so halaka ɗan uwansu, kaman yadda annabi nuhu yake annabin Allah amma ɗan shi ya fita yana saɓawa Allah har Allah ya halaka shi tare da sauran masu saɓo, misalai dae kala kala. Daga karshe ya ɗaura da "Ina so duka mu ɗauki Fauziyya as zakka, ba kuma wai zamu sakata a gaba da hantara da kyara da kuma duka bane, babu wadda ze ɗaura hannu a kanta da sunan duka idan har ka cika cikakken masoyinta da halakarta ka iya jefaka cikin alhini to ka tsaya mata akan sallaya ka rage mata bacci musamman iyayenta" "Menene Fauziyyar tayi?" Ammi ta jefa tambayar don ita duk waennan wa'azuzzuka sun ishe ta. Baba prof yace "mun zauna da Faizan ya faɗa min ganin da yayi mata a wani hotel a Abuja wadda kai tsaye ya faɗawa mahaifiyarshi ita kuma ta ƙi aminta sbd sanin da sa hannun makaranta aka tura Fauziyyar excursion Gombe, wannan kaɗai alamar tambaya ne don haka muka yi tattaki zuwa makarantar Allah ya sa abokina wadda shine mai makarantar ya zo musamman daga Maiduguri ɗaurin auren Faizan, anan muka tabbatar da manuplating malamin Fauziyya tayi yayi musu takardar bogi suka tafi Abuja saide be san me ya kaisu ba" Babanta yayi salati ya sallamar yace "yanzu Fauziyya a iya shekarun kin nan har kin san kiyi manuplating malami ya barki ki tafe watsewa uwa duniya? Bazaki kasheni ba Fauziyya..." Baba prof yace "Sulaiman karka manta duk abubuwan da nace kan mu fara tattaunawan nan, malamin karan kanshi na da laifi don da be yi abunda zata yi manuplating nashin ba da bata yi ba, shima nemanta ya so yi tayi recording ta juyar kanshi ga wayan da bamu san tana da shi ba hannun Faizan komai na ciki don a motar shi ta bari" Da sauri ta ɗago ta kalleshi shi kam ba ta ita yake ba, kawai yana zaune ne don ya san abun ya shafe masoyanshi da kuma gidansu amma da don ta shine wallahi ko a jikinshi, sarai ya san Zubair drug dealer ne wadda EFFC da NDLEA sun sha kama shi su sake saboda ɗaurin gindin da yake dashi, ya shata mishi katoton layi ya kuma gargadeshi a wayan na Fauza da yake ta kira akan in har yana cin ƙasa to ya kiyayi na shuri. "Fauziyya me ya kaiki Abuja?" Jadda ce tayi maganan har muryarta na rawa. Shiru tayi kanta ƙasa, wani tsawa da babanta ya daka mata yasa ta ɗago kowa idanunshi na kanta se ta nemi rikicewa.. "Mun je birthday party ne" Duka parlorn salati ya ɗauka, ga ɗiyar gidan baba prof a birthday party har Abuja. "Ke da waye" Baba ya jefa mata tambayar "ni da sakina da rahama, wlh baba duk partyn da nake zuwa a cikin garin nan ne wannan shine karo na farko da muka tafi Abuja" Salati aka sake dauka yarinyar kaman aljanu ke displaying ɗinta don ita fa idan lokacin abu yayi a yi shi, gaskiya komai dacinta fede ta take idan har ya kama ɗin. "Unbelievable! So you have been doing this for long?" Faizan ne ya jefa mata wannan tambayar. Shiru tayi. Ya sake cewa "wayan dubu ɗari uku a ina kika samu?" Tace "wan...wani ne ya sa...ya min" Farhan da su Faraj ji suke da a basu ita su yagalgalata ko zata yi bayani da kyau amma baba prof ya hana. Ido kaman ze cinyeta tace "baba wlh ni ban yi niyyar shan giya ba, Zubair ne ya munafunceni ya saka min cikin coke, shekaranjiya ma shisha ce kuma ce min yayi flavor ne ciki baya bugarwa shiyasa na sha" Rasa me magana aka yi a parlorn Amminta ne ta rufe ta da duka tana kuka tana cewa duk wani abunda ze sa ta tozarta ta idanun kishiyoyi tayi, gashi har wasu na jin daaɗi nasu shiryayyu ne ita kuma gurbatacciya, ita kam bata koya mata hakan ba sai de in a wuraren da take zama aka hore ta da hakan. Mammi ce ta kwace ta sauran matan parlorn duk babu wadda ya motsa, bakinta har yana jini ta lafe jikin mammi tayi shiru. Nasiha me tsayawa a rai Baba prof yayi musu, ya kafa mata sharaɗoɗi babu ita ba sakina da rahama, babu ita ba boko ze biya mata neco tunda an yi nisa da waec tayi shima lokacin in yayi da sa ido sossai zata yi, ko bakin gate aka sake ganinta da kanshi ze ɗauki mataki a kanta, manyan be yarda kowa ya sake dawo da abunda ya wuce ba suyi ta mata Adu'a, sadaka da saukar Alqur'ani, yaran kuma in sun yi ma sun Santa don haka kar a kawo mishi ƙarar ta in aka goge ta da magana ta rama. Rayuka dayawa ba haka suka so abun ya tsaya ba, sai de ya suka iya, haka ta koma sashen jadda da ta zage tayi ta mata nasihu batayi fushi da ita kaman babanta ba. Bayan sati ɗaya Faizan ya ɗauki matarshi suka koma Abuja dama an je an mata jere, ita kam Fauza ta zama kifin gwangwani hakan ya dawo da halin ta na da kannenta basu isa sun sake a gefenta ba, haka duk wani wadda ya gayamata magana akan rayuwarta se ta gayamai shuwaka, ana haka sakina ta shirya ta zo gidan... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 14 Daga bakin gate ta tambayi sashen Jaddah tunda ba zuwa gidan suka taɓa yi ba, mai gadi kuwa ganinta da jumbuleliyar hijab ya zata irin baƙin da jadda kan yi ne don ba'a raba ta da jama'a daga sashenta har sashen mammi, da hannu ya nuna mata sashen ya dae tabbatar mata jadda bata nan sun fita barka da sauran matan baba prof karshen layi. "Babu komai zan bada saƙo ne kawai in juyo" Da sauri tayi sashen tana shiga parlor ta fara kwala kiran Fauxa, da gudu ta fito jin muryar da ta sani ne tana ganin sakina kuwa ta rungumeta da murna. "Kina lafiya Fauxa? Ai hankalinmu duka a tashe Zubair ya ƙi tafiya Sam wai se ya tabbatar da babu abunda aka miki a gida, yanzu haka ma shi ya kawo ni yana farkon layin nan" Jan ta Fauxa tayi ɗaki tace "babu abunda aka min sakina sai de na zama matar ƙulle, kowa baya sake min fuska musamman waenda muka yi sabo dasu, har baba prof gaisuwa ta kawai yake amsawa, ke a takaice dae gabaɗaya duniyar baya min daaɗi, ba cireni school bane damuwa don makaranta be dame ni ba amma rashin fitan nan ga aiki don yanzu dole in ke komawa sashen mu ina aiki tunda babu wani aiki sashen jadda, komai fa ni nake yi tare da umarnin Baba Alhj" Sakina tace "kaiii wannan rayuwa na gidan nan Allah dae ya fidda ki, yanzu ko gate baki leƙa wa?" Na kara tabbatar mata da ko gate ba'a yarda in leƙa ba idon yayyuna duk a kaina yake, yanzu an yi min registern neco tunda an riga an gama waec ina ga shine kaɗai abunda ze sa na taka waje. Wayar ta karamar touch ta mika mata tace "gashi ki riƙe a hannunki zamu yi magana, bari naje tunda kin ce ko mu an rabaki damu wayanki kuma mugun wan ki yayi miki ajalinshi" Karɓa tayi tana mata godiya harda jajjada mata bata san irin taimakon da tayi mata ba don bata san tana son Zubair ba seda aka katangeta da sauraron muryarshi. Bata raka sakina ba don kar a gane, amma a fita saida sakina ta hadu da Fa'iza da kallo kawai fa'iza ta bita har ta fice, fasa shiga gidansu tayi tayo wurin Jaddah. Ɗakin Fauza ta tura da sauri Fauza ta boye wayan karkashin pillow. "Malama ya da shigo min ɗaki babu sallama?" "Fauza me Sakina ta zo yi a gidan nan bayan irin kashedin da aka yi miki?" Wani irin kallo Fauxa ta watsa mata "last da na bincika dae sunanki ba ruqayya ba! Uwata kenan ko? Sannan a shekaru kin san na girmeki don haka ki fita sabgata kaman yadda kike tun farkon fara sabon rayuwata babu ruwanki, in kuma kika ƙi kin san halina bani da kyau ko na sulen kobo wallahi" Idanu kawai fa'iza ta zuba mata kan ta girgiza kai tace "Allah ya shirya" A masifance Fauza tace "Ameen in da gaske kike, kema na lura yayarki kan ta tafi ta tsammiki wannan munafurci nata in ba haka ba yaushe kika yi wani buɗewar idon gayamin magana yen yen yen da fuska kaman nawa anan" Har Fa'iza ta bar parlorn tana jin masifar Fauxa. Ita kuwa fa'iza na kulewa ta fiddo wayan dake ringing, Zubair ne nan ta gayamashi duk abunda aka yi mata a gida "yanzu wani mataki kike shirin ɗauka?" Tace "ka bari tukuna in ga matakin su don na tabbatar ba shikenan ba, shurun baba prof wani abun ze kulla wadda babu wadda ze yi zato ko tunani, amma in na fara fita necon zan san yadda zan yi muke haduwa for now mu dinga wayan kawai" Haka ta kasancewa Fauxa, kullum in ta tashi asuba bazata dawo sashen jadda ba se ta gama komai na sashensu ta kan yi mamakin Amminta wacce bata rabo da maganan Fauxa kin wulakantani kin zubar da ƙima ta a idanun kishiyoyi, hakan yasa har ta gama ayyukan idan ba gaisuwa ba daga babanta, mamanta har Aunty Amarya babu wadda take sake tankawa. In ta gama na sashen ta koma sashen jadda tayi na nan da aka ware mata, kan ta karya, jadda zata sakata wucewa ta gaida duk matan gidan, bata fitowa daga sashen mammi kuwa se da nasiha me tsayawa a rai, hakan be hana ta waya da Zubair ba, sossai yake kara riritata yana hure mata kunne akan rayuwar gidansu ba rayuwa bace takura ce. Ana haka take samun labarin ɓarin da Fatima tayi, dukda babu wadda yake magana akan zaman su don haka bata san yadda suke yin ta ba amma ta tabbatar kowa se da ya shiga damuwa kan wannan bari har Fa'iza aka tura dake an gama jarabawar makaranta Hutu ne kawai za'a bada abunda ba ɗabi'ar Baba prof ba, don baya yarda wata cikin en matanshi taje gidan wata zama da ko wanni nufi kuwa. Ko a jikin Fauza kaman ma bata san me ake yi ba, bayan sati biyu da tafiyar fa'iza ta fara Neco, driver musamman aka ajiye mata shi ze kaita ya jira har ta fito ya dawo da ita, to ranan baba prof ya fita za shi unguwa da ya Faraj kenan ya hangi wata yarinya me irin uniform ɗin Fauzan a farkon layi saka Faraj parking yayi ya kira mishi ita. Ko da ta zo ya tambayi sunanta se ya gane mahaifinta mutum ne da baya ƙaunar shi don ko sallah baya zuwa masallacin shi ta bayan layi yake zuwa, murmushi kawai yayi ai ya riga ya san ba kowa ne ze so ka a duniya ba amma tunda akwai hakkin makotaka ze sauke. "Zan sanya driver da ke kai Fauziyya ya dinga biyowa yana daukar ki se kuke tafiya tare kuna dawowa tare se ya fi miki sauƙin neman abin hawa a nan wadda suke wahala" Har ƙasa ta duƙa ta mishi godiya Dukda kwarjini ne kawai da ya cika ta dashi in ba haka ba babu abunda babansu be faɗa musu akan Prof kaka ba. Haka ko aka fara, abunda ya fara ba Fauxa haushi yadda yarinyar take shigowa har su je su yi paper su dawo bata gaisheta, dukda ita ba kalar wacce ta damu da damuwar wasu bane sede haushi ya kan cika ta da al'amarin yarinyar kina cin arzikin mutanen gida kina musu gadara. Wata rana suna da papern rana tun da suka fito ma Fauxa ke wayanta da Zubair don yau din zasu haɗu a makarantar, musamman ya kawo wadda ze zauna yayi mata papern ranar a madadin ta ita kuma su fita tare. Ko da ta isa bata nufi hall ɗin ba ta zagaye bayan classes anan Zubair ya ɗauke ta suka fita, ya nuna mata yayi kewanta ta amince mishi sau ɗaya dae kan ta gama paper ta koma kulle, lallaɓa shi tayi akan tunda suna son juna ya turo magabatanshi in ya so tana gamawa baban ya ɗaura mata aure su huta, yace ze yi tunani akai haka dae suka gama yawon su ya haɗo ta da chocolates masu yawa. Ko da ta dawo kowa ya waste a school wanchan yarinyar se tsaki take ja, driver dae sanin halin Fauza yau ne kuma na biyu na farko sun hadu har dasu sakina yasa be ce komai ba. Koda ta zo bata ce musu su yi haƙurin ajiye su da tayi ba kawai ta shiga ta zauna abunta tana bare diary milk, har sun kusa unguwarsu yarinyar da ko sunanta bata sani ba tace "Fauziyya sunanki ko? Nace ya kamata kike sanin darajar mutane, don ana cin arzikin gidanku ba shi ze sa ki samu damar wulakanta mutane ba, sannan wallahi kika yi tsiya se in yi tattaki har gaban tsohon ki in sheda mishi abunda kike yi in kin fita, ko de!" Ta taɓe baki tace "na ji labarin da saninsu ma tunda arzikin na safarar yara ne ko me nasu tayi sakamako n....." Wani kalar buge mata baki da hanci da fauxa tayi da gwuiwar hannu se da yasa hancin ta da bakinta fara zubar da jini. "Da alama baki san Fauxa bane! Ina me tabbatar miki wannan gargadi ne ɗon wannan ne karo na farko ko da bakin wasa wannan kazamtacciyar bakin naki ya sake ambatar iyayena ko da Kalmar alheri ne se na gurje shi bare ta tsiya" Tana gama faɗa ta saka hijab yarinyar da already ya ɓaci da jini se yarfa hannu take tana kuka ta share bayan hannunta, don kowa ya san Fauxa er gayu da kwalliya ce, kayan ta bata yarda wani stain ya bata su. Driver ne yace "ashhha! Hajiya Fauxa ayi haƙuri ai duniya ɗan hakuri ne" Bata ce mishi komai ba sbd be saba shigar mata idanu ba wannan ne na farko kuma ta ɗaga mai kafa, yana tsayuwa yarinyar ta sauka da gudu tana kuka ta shige gidansu. Tsaki me karfi fauza ta ja tana rasa me ke damun baba prof da manna waenda basa kaunarka jiki. Ta samu fa'iza ta dawo da sha tara na arziki don sayayya me dumbin yawa Faizan yayi mata matsayin kanwarshi, kowa seda ya samu tsarabar shi kasancewar shi mutum me kyauta sossai. Washegari ko da suka tsayawa yarinyar bata fito ba Fauza tace su wuce, a makaranta ta samu yarinyar da wasu mates ɗinta don ita bata san makarantar ba tunda jarrabawa ne kawai ya kawo ta sbd gudun haduwa da su sakina yasa baba yayi mata registeration a wani makarantar. Yadda suke ta hura hanci ga yarinyar fuska a kumbura yasa Fauxa kwashewa da dariya, irin kallon da suke mata na zaki daku yau tayi musu kan tayi wucewarta, bayan sun gama paper an waste tana tahowa don zuwa wurin mota en matan huɗu suka yi mata ƙawanya. "Ke! Me kike takama dashi da zaki illatar da sukaina kuma kiyi Tunanin kin ci bulus?" Sha ka hura dake bakinta ta ciro ta ɗan lasa tana Kallonsu dariya suke bata. Ɗayan tace "don an zagi prof kaka menene? Waye be san yadda kudinshin nan dake ta hauhawa ba na Allah da annabi bane? Ko karya aka yi don an ce yana safarar mata?" Dayar tace "ai ba mata da yara kaɗai ba har abubuwan shaye shaye don duk abunda kaji ana jita jita a kai da ƙamshin gaskiya" Na farkon tace "karki kai da nisa gashi har yaran yake baiwa suke sha, waye be san wannan ƴar fitsitsiyar babu abunda bata sha ba?" Jakarta Fauxa ta sauke ta buɗe ta ciro paper ta fara naɗe sha ka hurarta na big bom, tana nadewa ta fara magana. "Kaman yadda na miki alkawari bakinki ya sake aibata iyayena se na gurje shi to yau se na gurje shi da ƙasa idan gasa miki shi ne ba'a yi da kyau ba yayin wankan haihuwa yau za'a miki gashi me kyau..." Tana kallon sauran tace "ku kuma en korenta kowaccenku sakamakonta na rubuce a goshinta, ke yatsar da kika nuna ni dashi yau se an yi miki gyara, ke kuma haƙorin ki ɗaya se kin rasa shi, ke kuma zaki komawa uwaki da karyayyen hanci kin san Karyewan cartilage? To yau zaki sani" Tana kai nan ta cire hijab ɗinta ta ninke, da gudu tayi cikinsu suka fara dambatuwa, dukda kwana biyu rabon da tayi faɗa tana acting classy yau seda ta zage tayi musu duk abunda tace don bata taɓa faɗan magana ta kauce akai ba. Tana yi tana cewa "Da kun tambaya tun farko waye Fauxa da baku shiga sabgata ba" Duk saida ta cika alkawarinta kan da kyar aka dagata kan su. Taje ta ɗauki hijab ɗinta tana haki ta saka ta ɗauki sweet ɗinta ta cigaba da tsotso tare da rataya jakanta tayi mota, ko da suka dawo gida ita har ta mance ma da abunda tayin. Chan dare tana cin Samosar da tayi bayan dawowarta da tea kawai Ya Farhan yayi sallama "Fauziyya zo mana" Dukda be saba mata irin kiran ba haka dae ta miƙe ta bishi ɗakin su taga yayi, a zuciyarta take masifan Allah ya sa ba aiki ze saka ta ba, tana sanya kafafunta a ɗakin ya maida kofan ya rufe, Faraj dake zaune da dorina yace "na lura barin ki da ake shi ya sa ko yaushe kika tashi ɗauko mana magana se ki ɗauko kalar wadda ba'a taɓa yi ba, bana Tunanin ko hanyar police station baba ya sani amma wai yau a ta sanadiyarki aka zo har wurin karantarwar shi za'a daukeshi.." Takaici ya hana farzan din cigaba da magana, Farhan yace "Fauziyya yau zan tabbatar da na huce duk takaicin da nake kwasa akanki, yau ɗaya zan saɓawa umarnin Baba na be amince kowa ya taɓa ki ba in yi miki dukan sauke takaici, wawuya wacce bata san me ke mata ciwo ba.." Dukda yadda zuciyarta yake bugawa, bata nuna a fuska ba, ta san sun fi karfinta kuma ihun duniya tayi anan babu me jiyo ta bare a zo cetonta gwara ta sallamar kawai su kashe ta in sun so. "In de akan yaran da na daka ne wallahi ko gobe suka sake maimaita abunda suka yi haka zan musu, ba police ba su kawo rundunar sojoji...." Bulalar da Farhan ya fara sauke mata cikin takaici ne ya katse mata maganar, dukan kawo wuƙa suka mata tun tana ihu har ta dena tana jiran kawai su kashe ta, har hijab ɗinta seda bulala ya yayyaga fatanta har jini yake yi.. "Tashi ki fice ko in kasheki kowa ya huta" Farhan yayi mata ihu hawaye na zuba a idanunshi, iyayenshi yake ji wa takaici, be taɓa ganin baba prof a yanayin da ya ganshi yau ba, wai har wannan yarinya ta ja ake gayamishi maganan da ya saka shi zub da hawaye dukda be yarda kowa ya gani ba amma sun san ba karamin zafi ya mishi ba. Da sauri ta fito tana layi, dishi dishi take ganin mammi tsaye tana kwala kiran sunanta, Sam bata san ma da wani a gefen mammin ba ta de ji tana cewa "kama min ita... Yi sauri kama min ita, innalillahi me zan gani haka?" Yanke jiki tayi sbd yadda duk garkuwar jikinta suka karaya suka gaza ɗaukar gangar jikinta a hannun mutum ta ji ta kan ta karasa ficewa hayyacinta. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari.                🖤Gureenjoh🖤 DƘ 15 Yana durkushe kan kafan shi ɗaya, ɗayar kuma kanta ne a kai hannunshi na patting kumatunta yana cewa "ke! Ke!!" Sede ina bata ma san yana yi ba. Mammi tace "yi sauri ɗauko ta mu tafi asibiti Faizan Farhan na da hannu a wannan abun kuma wallahi se sun ga bacin rai da basu taɓa gani ba, wani irin shashanci ne wannan?" Da sauri ya ɗauke ta yadda yaga ran mammi ya ɓaci be so ta bi su asibitin ba don yanzu suka dawo sbd kafar ta da ya matsanta mata se kuma suka tarar da wannan, haka ta ƙi shiga gida suka juya asibitin tana kiran Baba Prof a waya. Ba irin faɗan da likitoci basu yi ba, aka samu aka shawo kanta aka yi mata dressing ciwukanta, lokacin baba prof da Baba Alhj da jadda suka iso. Tana kwance kaman wata innocent, sossai Jaddah ta zub da hawaye tana zagin su Farhan inda take shiga ba ta nan take fita ba, Baba Alhj bazaka ce ya wani damu ba haka nan oga kwata kwata Faizan tunda nurses suka karɓeta ya samu wuri yayi zaman shi ba don mammi da tayi magana ba ma wayanshi yake ta operating, Baba prof ne yace Duk su koma a kawo ko zaliha ne ta kwana da ita tunda allurar da aka mata ze jima be saketa ba. Tun suna kan hanya ya kira Farhan da Faraj akan su same shi parlornshi, suna isowa duka nan suka yi, tun kan su zauna babu zato ba tsammani ya saukewa kowannensu zazzafan mari, duk a razane suke Kallonshi ranshi sossai ya ɓaci yace "baku da hankali ne? Kuna Tunanin duk rashin hankalin Fauza ya kai wadda kuka yi? Irin wannan duka ko a hannun hukuma iyaka tana mace in kuka yi mata illa fa? Ina ce seda na ce muku kar kowa ya taɓa ta sbd abunda ya faru? Kun tambayi dalilinta? Ko don tana da yawan neman tsokana se aka ce a komai ma ita ke da laifi?" Babu wadda ya taɓa ganinshi yana faɗa haka, yayi sossai da sossai sbd yadda ya ga Fauxa, jadda ma ta karɓa harda Allah ya isa tayi musu, mammi ma Seda tayi nata sossai ta kuma ɗauki fushi da dukkansu, Faizan dae da Baba Alhj en kallo suka zama se daga baya baba Alhj yayi ta ba jadda hakuri. Tace "me ya faru ɗazu ɗin?" Baba prof da ya zauna ya ɗan yi shiru yana Samarwa kanshi natsuwa kan yace a tausashe "Duk abunda ya farun laifin Fauziyya kaɗan ne Dukda dae ni shi ya fi daga min hankali ba wani faɗar da suka yi ba, da farko dae ni na janyo don na san halin Fauxa na Haɗata da wata yarinyar makota a nan farkon layin ganin kullum tana wahalan samun abun hawa, to wai Fauziyyar sau biyu bata rubuta paper ba tana fita wani ke rubuta mata a madadinta, to ranan sai bata dawo da wuri ba shine yarinyar ta fara zagin ta har ta kai kaina se fauziyyar ta fasa mata baki a mota kaman yadda driver ya bada nashi bayanin, to bayan nan ne suka haɗu da ƙawayen ta wai zasu dake ta shine tayi musu dukan kawo wuƙa iyayensu kuma suka kawo min hukuma sun kuma aibata ni sun yi min kazafi wadda na Barsu da Allah zasu bada shedar shi ranar gobe" Shiru parlorn ya ɗauka kan Jaddah da ta zabga tagumi tace "yau na shiga uku da yarinyar nan, to ina take zuwa? Da wa take fita kuma?" Baba prof ya kalli babanta da yayi shiru hawaye na shirin zuba mishi yace "kar ka yi mata kuka Sulaiman, da ni da kai duk ɗaya ne haka yaranmu don an zo kamani a madadin mahaifin Fauziyya ba'a yi kuskure ba, a yinin yau na yanke hukunci akan Fauziyya wadda nake so duk ku sheda, bana bukatar shawarar kowa bayan na mahaifiyata, na yanke nan da watanni biyu zan ɗaurawa Fauziyya Aure da Faizan..." Ɗib haka parlorn ya ɗau shiru, Faizan dae yi yayi kaman be ji ba don ya san kila karan jirgi ya fara taɓa mishi kunnen shiyasa ba ya ji da kyau, ko a imagination baze taɓa kawo wannan hadi ba bare a zahirin gaskiya. Mammi tace "Allah ya sanya Alkhairi, wannan haɗi shine daidai" Baba Alhj yace "A'a yaya, ya zaka fara wannan kwamachalar? Taya zaka fara Haɗa nitsaste kaman Faizan da fits...." "Akul Sulaiman, in dae ba kana so ka nuna min bani na haifi Fauziyya bane babu ruwanka naka idanu, Faizan na ba Fauziyya kuma ya riga ya zauna.." Ba don kar ace yayi rashin kunya ba da se ya tambayi baba wai wani Faizan ne yake referring to, kanshi gabaɗaya ya dau hayaƙi in kuwa baba yayi hakan ba karamin cutar shi yayi ba, me ze yi da sauran wasu? Me ze yi da ƴar giya? Jaddah sossai ta nuna amincewarta da shawaran a haka suka tsayar kan su Faraj suka yi ta ba baba hakuri yace ba shi zasu ba wa ba Fauza zasu ba kuma biyar da Faizan ya kashe a asibiti su tabbatar sun biya shi, a haka aka watse aka bar Faizan a zaune a wurin. Seda baba ya kula da Sam kaman baya hayyacinshi ne ya tashi yaje ya ɗibo ruwa masu sanyi ya kawo mishi "karɓi ka sha!" Ya kalli kofin kan ya ɗaga ya kalli baba da rinannun idanunshi yace "na koshi" Baba yace "karɓi mana ai ruwa rayuwa ne" Karɓa yayi ya kafa kai ya shanye tas kan ya ɗago ya sake kallon baban, murmushi shimfiɗe a fuskanshi yace "karka ɗaga hankalinka Faizan, a yadda na sanka da natsuwa, kawaici da hangen nesa kaman mahaifiyarka ina so ka cigaba a haka, na zaɓa ma Fauziyya Kaine sbd Kai ne Allah ya sha nuna min a duk istikhara na, da kai hankalina ya fi kwanciya, na san bazaka taɓa tozarta abinda na baka ba" Faizan yayi shiru kaman ruwa ya cinye shi "baba fa watana kwata kwata uku ne da aure" Yace "na sani, Fatima da mahaifiyarta masu fahimta ne na san zasu fahimta" "baba mahaifiyarta bata taɓa ƙaunata ba, ko gaisuwata bata taɓa buɗe baki ta amsa ba" Yace "na sani wannan duk ba wani abu bane ba lallai kowa ya so ka a duniya ba, daga kan Annabawa har Sahabai zuwa malamai babu wadda bashi da maƙiya" Yace "Baba Fauziyya da Fatima basu taɓa shiri ba taya zan iya haɗe kansu su zamar min tsintsiya madaurinki daya kaman yadda ka zamarwa iyalan ka?" Yace "kai ɗin jarumin namiji ne wannan me sauƙi ne a gareka, ina me tabbatar maka zaka yi alfahari da wannan haɗi watarana, ka je ka kwanta karka yawaita tunani instead ka raya daren idan ba zaɓin Allah ba ce se ka ga Allah ya musanya mata da alkhairi in kuma ka ga an ɗaura to kaddarar ku a sarƙe take da juna tun fil azaal" Mikewa yayi yace "Na gode, se da safe" A ladabce kan ya juya ya fice. Wannan dare haka ya zamarwa Faizan daren tashin hankali don ya kwana yana rokon Allah akan wannan abunda baba ke shirin tinkarar rayuwarshi dashi, duk mazan gidan a rasa wadda za'a lakabawa wannan fitananniyar yarinyar se shi? Yayi nadamar zuwa yola a ranar ya fi sau dubu kila da be zo ba baba be ganshi ba da wani ya zaɓa ya baiwa ba shi ba. Jadda da mammi dae sun kwana cikin farin ciki yayinda baba Alhj ya kwana yiwa wan shi Adu'a ya tabbatar ba don shi ba da lamarin Fauza yanzu ya kaishi ƙasa, Ammi ya kira ya mata bayani tashi ɗaya ta nuna Allah ya kasheta wallahi baza ta kara Haɗa zuri'a da Mammi ba an yi mata fin karfi a lokacin fadyaa yanzu kam babu wadda ya isa, har gwara faahim sau dubu da Faizan a gareta. Baba be kula ta ba ya yi kwanciyar shi don in yace ze biye mata se Amarya ta ji kuma yana so ya sanar da ita ta yadda zata fahimta babu cin fuska ko son kai a wannan tafiyar. Washegari zaliha ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallar asuba bata samu Fauza ba, neman duniya da nurses suka mata bata cikin asibitin ko da Baba prof da jadda da kuma Aunty Amarya suka iso ana kan nemanta ne. Alamu dae sun nuna fita tayi sede ina zata da rauni a jiki? Ita kuwa tana tashi ta mike zaune tana kallon inda suka bare mata a fatarta da take matukar tattali, ranta yayi baƙi kirin da irin wannan tozarci da yayyun nata suka mata, ta tabbata duk gidan maƙiyanta ne banda mammi da jadda da Amminta, lallai abunda suke gudu se ta sake yi in basu kasheta ba ba su cika mugaye ba. Dira tayi daga kan gadon ko hijab ɗin da ta dauka ganin yadda ya fashe yasa ta cillar, takalmin zaliha ta saka ta fice, abun hawa ta tare se gidansu sakina, ta sa me gadi yaje ya karbi kudin ya kawo mai, sossai hankalin sakina ya tashi da ganinta haka. Anan tayi wanka ta sauya kaya tayi kwanciyar ta bayan ta ci abinci, duk yadda sakina ta so tayi magana kasawa tayi da ta matsa se ta kawo kuka ta sa, hakan yasa zaliha bare wasu tabs tace "sa wannan a ƙasan harshen ki duka biyu ki barshi ya narke da kin yi bacci kin tashi bacin ranki ze kau" Sawa kuwa tayi ta kwanta, a haka tayi bacci har sha biyun rana kan ta farka abu kam ya fi karfin jininta ga shi ta bata overdose ne, tana tashi ta gayawa sakina duk abunda ya faru ta kuma ce tana so ta kunsa musu bakin cikin da zasu saka wuyan ta gabas su yanka, wayan sakina tayi anfani dashi ta kira Zubair luckily ya koma da yau abunda yake so da ta bashi. Haka ta diro ko mayafi taƙi sakawa kaman ba ɗiyar musulmi ba ta nufi fita, Sakina da kyar ta shawo kanta akan driver ya maida ta. A farkon layinsu tace ya ajiye ta don tana so kowa ya kalleta yadda su Farhan zasu kara jin haushi, aikuwa kaman ta kimta daidai. Farhan, Faizan, Faraj, Baba Alhj baba prof da polisawa ne tsaye ana batun yadda za'a samo ta shi Faizan kaman dole ce kawai aka mai na shiga case ɗin zuciyarshi na bashi wurin watsewarta tayi don mashayi daga ranshi ya ɓaci abun shaye shayenshi yake nema ya rage zafi. Yana cikin wannan tunani ya ɗan kalli hanya har ya ɗauke idanu yayi saurin sake mayarwa ya zuba mata su yana kallo, tun daga nesa zaka san a make take mankas, so yake ya janye hankalin baba Alhj sede yana juyowa yaga duk suma sun zuba mata idanu, ga bandage a jikinta ta sa wani riga da da kadan ya sauka kaurinta, hannunta duk a bayyane gashin kanta a Parke cikin loose bon, Baba Alhj ne ya tafi ze fadi, Baba prof yayi saurin tare shi yace "Menene haka Sulaiman? A kanka aka fara jarrabawa? Kana so se ka ɗaurawa yarinyar nan abunda ya fi wannan?" Su Farhan yayiwa kallon duk wa ya janyo? Ba ku ba? Kan ya saki baba Alhj ya fara tattaki zuwa gareta. Maganganu take maras kan gado tana faɗin laifin babanta ne da yayi mata baki kullum yake kiranta fitsararriya gashi fitsara ta bita, ba su Farhan sun ce zasu mata abunda bazata kara marmarin rayuwar banza ba? To gashi ta kara su sakata gabas su yanke yanzu yanzu zuwa tayi don su gani, Kaman Faizan ze yi kuka don tausayin kanshi yanzu da abunda Babanshi ze Haɗa shi kenan? Har ɗakinta ya kaita a sashen Jaddah tare da taimakon ta ta shimfiɗar da ita se bacci, duk idanu suka zuba mata. Jaddah tace cikin karfafa mishi gwiwa "Adu'ar mu baze taɓa faɗi ba professor, ka kwantar da hankalinka abunda kake shirin yi in shaa Allah shi ze zama silar warakar komai, Allah maji roko ne me jin ƙai ka fini sanin cewa baya taɓa juyar da Adu'a sai de in ya musanya da abunda ya fi alkhairi, ya kuma amsa ta hanyar da tafi kowacce daidai, sadaqa maganin masifa ne, haka kuma Qur'ani waraka ce, Adu'a kuma takobin mumini ne duk bamu daina akan Fauza ba kaga kenan muna da yakinin Allah ze karɓa ko ba daɗe ko ba jima" Yace "hakane mama, bana kokonto akan Hukuncin Allah sede a duk sadda zan ɗaga idanu na kalli yarinyar nan jikina yana bani wani abu na daban mama, gani nake ana zaluntarta amma ban san ta ya ba, tausayinta ke ratsa zuciyana har na kan zubar mata da hawayen tausayawa in na kalleta, ba ni kaɗai ba sau ba Adadi Aisha ta min magana makamancin haka akan yarinyar nan" "komai ze tafi daidai professor in shaa Allah auren da ka Haɗa ze zama sanadiyar warwarewar duk wasu al'amuran ɓoye" Mikewa yayi ya fita bayan ya tofe ta da wasu Adu'o'i, ko da ya dawo ya nemi Faizan ya rasa don barin garin yayi. Satin shi uku da komawa Fatima ta sake ɓarin cikin wata guda. Wannan karon har gida ta zo sbd yadda duk ta ɗaga mai hankali, ta kasa fahimtar komai na Allah ne. Shi kam ya ma tafi chan wata ƙasa ne hakan yasa dole ba yadda ya iya ya barta ta koma gidan, a gidan bayan mutane shiddan nan har yanzu babu wadda ya san da maganan auren na Fauza da Faizan, a fakaice Jaddah ke mata gyara ba tare da ta sani ba, asalin gyaran shuwa Arab take mata. Dayake yanzu ko parlorn Jaddah baba be yarda ta wuce ba necon tan ma karasa mata ake yi yasa bata fita rana, skin ɗinta ya kara wani irin kyau da sheki tayi fresh tayi kiba abunta, nasihohi take sha har ta gaji da jinsu amma tayiwa baba alkawarin bazata sake shan kayan Maye ba har abada. Yanzu wayanta bashi da anfani don tayi ta neman Zubair bata samu se kawai ta jefa shi kasan akwati. Ko da Fatima ta zo ma sannu be hada su ba har tayi kwana bakwai ranan ne baba ya kirata yayi mata nasihu masu yawa kan ya faɗa mata auren Faizan da Fauziyya da ya hada, ba karamin girgiza tayi da wannan zance ba, tsanar da ta yiwa Fauziyya me yawa ne matuka gashi zata aure mata masoyi ta zama suna shearing komai nashi, abunda ba zata iya amincewa dashi ba kenan. Ta dawo wurin mamanta hankali tashe cikin matsanancin kuka, Fauza ya sa aka kira mai itama ya faɗa mata, abinka da shiririta irin na fauza dariya kawai tayi ta fito abunta bata taɓa dauka serious bane seda abu ya karato dangi suka fara zuwa nan ne musababbin tashin hankalinta ya fara... Ko da ta nemi halaka kanta kawai kiran sakina tayi tace ga abunda zata sayo mata ba tare da ita sakinar ta san ita zata sha ba, ta sayo ta bi ribibin en buki ta bata... DAWOWA LABARI "FAUZIYYA!!!" ya fadila ta faɗa tana jijjiga ta da karfi, firgigit tayi tare da ɗago kai se taga babu kowa a jirgin se su uku. "Me haka? Me yayi zafi da zaki ɓata a tunani haka? Kin san tun yaushe muke tsaye akanki?". DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 16 A natse suke saukowa jirgin, Ya fadila na riƙe da hannunta da kallo ɗaya ka mata zaka san cewa wannan ɗin amarya ce, don kwalliyarta na ban mamaki, ba fa na fuska ba lafayarta kaɗai ka kalla ze tabbatar mata da ita ɗin Amaryar babban gida ce. Hannunta dake riƙe da jakanta ya bayyana lallenta me kyaun gani, chan jikin mota Faizan da Fatima ke tsaye suna jiran su har yanzu mita take mishi "habeeby ka san halin Fauza, wlh tsoro nake ta tarwatsa mana gida muna zaman lafiyanmu, ba wai ina ja da shawaran Baba bane amma raba mana gida shi ya fi alkhairi" Ya ɗan kalleta sbd tausayin da take bashi don ya san fitinar Fauza babu wadda ze shaƙa dayawa irin Fatima duk yadda kuwa yayi, yace mata cikin natsuwar shi "Na sani Fatima, amma ba mun gama maganan gida ba? Baba be lamunce min raba gida ba tunda tun tasowarku a tare kuka taso da Fauza kowaccenku kuma ba baƙuwar ɗaya ba ce, na san baki da fitina kiyi hakuri ku zauna tare har ku samu fahimta" Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗauke idanunta daga kanshi, se suka sauka kan su Fauza dake tahowa yadda take tafiya kaman ƴar sarki dole ya fusgi hankalin jama'a ga kyau tayi, abunda ta san zata nunawa Fauxa hasken fata ne kaɗai ko tsawo Fauza ta ɗara ta Dukda ta fi ta shekaru, dama kuma Hausawa sun ce tsawo rabin kyau, da sauri ta maida kallonta kan Faizan se taga su yake kallo shima. A take ranta yayi baƙi kirin, ta tabbatar ba don Fauza bata son Faizan ba da se ta saka mata hawan jini in ta gane tana mutuwar kishin shi, hannunshi ta kama ta rike wadda ya saka shi ɗauke lumsassun idanunshi daga kan su Fauzan ya maida shi kanta. "Tunda sun taho mu shiga motar habeeby kafafuna sun fara ciwo" Ya juya cikin kulawa da hakkin shi yace "so sorry, na barki a tsaye" Motar ya buɗe mata ta shiga ya rufe, motar bayan wadda na abokin shi ne Faisal shi ya nunawa ya fadila suka shiga, shi kuma ya zagaye suka zauna da Fatima wadda hakan yayi mugun yi mata daaɗi har suka isa gida tana gayamishi abubuwan da likita yace ta dinga yi a kan ɓarin da take yawan yi. Bayan sun sauƙa a tamfatsetsen gidan nashi dake maitama da kanshi ya musu jagora zuwa ciki Dukda ya fadila da ita aka zo jeren na Fauza, a bakin kofa Fauxa ta ja ta tsaya a hankali tayi ta karanto adu'o'in da Baba prof ya umurceta ta karanta kan ta shiga gidan, bayan ta gama tayi sallama tare da sa kafar dama se ta lumshe idanu, shikenan fa ita kuma wani sabon baabin qaddara ya buɗe mata, Allah kaɗai ya san abubuwan da zasu faru a cikin wannan gida kuma Allah shi kaɗai ya san ko gidan zaman ta ne ko ba gidan zamanta bane, ko a mafarki bata kawo auren mijin Fatima ba, ba ma wannan ba kuma wai Ya Faizan har yanzu kwakwalwanta be gama ɗauka ba bare zuciya da gangar jiki. Tamfatsetsen parlor ne wadda ya ɗauke set ɗin kujeru har biyu, ya ƙawatu sossai masha Allah, kofofi uku ne a parlorn daga tsakiya wani hadadden staircase ne golden color wadda ya tafi a karkace har zuwa sama, dukkansu shi suka bi zuwa madaidaicin parlorn dake saman wadda na kasa ya fishi girma sede ya fi na kasa haɗuwa, dining section ɗin ma kaɗai abun kallon ne haka TV stand ɗin daga ka ganshi zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba, console har biyu ne a parlorn ɗaya a dining section ɗaya daga tsakiyar stairs in kana haurowa, kofofi huɗu ne a saman, na farko daga dama ya fadila ta buɗe suka shige da Fauza da ya kaka. Yayinda shi kuma ya shiga na biyun yana cewa Fatima ta duba ko me aikinta ta gama abunda su ya fadilan zasu ci, ta amsa da to tana shiga nata ɗakin wadda yake next to nashi, jakanta kawai ta ajiye ta fito, ta san shi. shi mutum ne me matukar son yaga nashi a gidan shi, yana son en uwanshi har bata san yadda aka yi ya rabu dasu yake ketare kasashe da sunan aiki ba, idan yaga nashi a gidan se abunda babu ne baya saya, ya dinga tambaya kuma ko akwai abunda kake bukata ayi maka, hakan ya sa itama dole take yi don bata son ɓata mishi Sam. Kitchen na ƙasa ta je don ita kaɗai ke shiga na saman, ta samu me aikin nata ta gama duk wasu abunda ta faɗamata tayi a waya don haka a tare suka kwaso suka hauro sama dashi kwankwasa kofar tayi tare da buɗewa da sallama. Su ba baƙin juna bane don haka tun tuni ma Fauza ta yaye lafayarta tana kwance a kan tamfatsetsen gadonta tana karewa tsaruwar ɗakin nata kallo, Baba prof da jadda sun yi kokari don su suka mata komai, dukda be so jadda ta sa hannu ba amma tace auren Fauxanta guda in bata fasa asusu ba na wa zata fasa kenan. Mammi kuwa ita ta zubewa ya fadeela kuɗi akan wadda Faizan ya tura mata da umarnin Baba prof ta Haɗa mata lefe na gani na faɗa, kamshi da kyaun ɗakin kaɗai ze tabbatar maka da lallai nan ɗin na Amarya ne, akwai set ɗin kujeru akwai TV akwai kuma fridge a ɗakin, daga dan lungu window kuma akwai coffee table ɗaya da kujerun shi guda biyu masu kyau se karamin kofa da ze sadaka da madaidaicin balcony ɗinta wadda be wuce na tsayuwar mutum ɗaya ba an tare shi da wani black and gold glass. Kofan bayi kuma na daga kudu, duk yadda Fatima take Tunanin tsaruwar ɗakinta se taga na Fauza ya fi nata don ko ba'a faɗa mata kudin kayan nan ba ta san ba laga laga bane Dukda natan ma masu kyau ne amma na Fauza sun fi nata, ash ne da gold ɗakin haka labulayen gold da light ash, dressing mirror ɗin yayi mata sossai kaman ta ɗauke, idanunta kafe kan show glass na zamani wadda aka cika shi makil da wasu hadaddun turaruka wuta take rayawa a zuciyarta; lallai an nuna mata wariyar launi a nan wurin, an nuna mata kuma Fauxa ce yar gida kuma er gata. Da kyar tayiwa su yaya fadilan sannu ta ajiye abubuwan hannunta, daidai lokacin me aiki na shigo da saura tace "ya fadeela ku ci abinci, bari na ɗan sha magani don har yanzu cikina ciwo yake" Cikin tausayawa suka mata sannu ko kallonta Fauza bata yi ba har ta fice. "Fauziyya ya kamata fa a ce zuwa yanzu duk wani baƙin halinki kin baro shi chan yola kin nemi natsuwa da salama kin ɗaurawa ranki, daga Fatima har Faizan yayyunki ne suna da ikon hukunta ki da duk iskancin da zaki yi, kina ƴar fitsitsiyarki har kin san kishiya na ciwo ko sannu bazaki ce mata ba?" Faɗa sossai take mata wadda wacce ake wan ta lumshe idanunta kawai tana tunanin yadda zamanta ze kasance a gidan, ko sauraron ya kakar dake faɗan ba yi take ba. Bayan ta gama suka ci abinci wadda Fauziyya bata ci ba, bayi yaya kaka ta shiga don yin alwala yayinda ya fadeela ta ɗago Fauzan ta zaunar da ita. "Fauza kar mu fara haka dake mana? Kin manta kin ce zaki zauna lafiya dasu bazaki neme su rigima ba in har ba su suka neme ki ba?" Tace "ban manta ba, amma dae kin san tun da ba magana nake mata ba me don ta ce cikinta na ciwo zan buɗe baki in ce mata sannu bayan bata kasa dani ba? Yaya fadila don Allah ku Rabu dani in ji da abunda ya dameni, matar nan kuma ta ci darajar Jaddah wallahi" Tana kai nan ta koma ta kwanta abunta, girgiza kai ya fadila tayi tace "kina da aiki wallahi, amma ba komai duk sadda kika so zaman lafiya da samun kwanciyar hankali se ki neme ni" Daidai lokacin ya kaka ta fito, Ya fadeela ma ta shiga suka zo suka gabatar da sallah, suka ɗan kara kakkabe mata ɗakin don akwai injin shara a ciki, kuma ya fadila daman su dashi suke anfani a lokacin ne ma ta mike zaune tana kallon yadda ya fadeelan ke operating, bayan sun gama suka kara gyara mata wardrobe ɗinta da rabin shi glass ne ita kanta bata taɓa ganin ɗakin da ya burge ta irin natan ba, ta kuma sanyawa baba da jadda albarka don sun zuba kudi ba kaɗan ba a kayan nan, abunda kuwa yafi burge ta shine lefe don yadda take son gayu haka ya fadeela ta zaɓa mata isashun kayan gayu da ado. Sun gama kenan sun kara sa turaren wuta a burner ya shigo da sallama, kwanciya tayi tare da juya baya, be ma san tana yi ba don ko inda take be kalla ba, akan kujeran ɗakin ya zauna ya gaishe da ya kaka tare da mata ban gajiya, ya kuma tambayi ko akwai wani abunda suke so, suka ce babu yanzu ma shirin tafiya suke. Se lokacin Fauza tayi saurin ɗagowa "Ya fadeela yau Zaku tafi wai?" Se a lokacin ya kalleta babu ɗan kwali kanta gashinta ya sha kananun kitso irin na kanuri yiri yiri ya zuba a bayan wuyan ta wasu ta baya wasu sun sauƙa a kirjinta, doguwar riganta na Holland babba ya tattare daga sharabarta sbd irin kwanciyar da tayi. Tsaki ya kaka ta ja tace "yo to dama zama zamu yi? Yau zamu koma tunda mun kawo ki fatan dae Allah ya baku zaman lafiya" Rau Rau tayi da idanu tana jiran jin amsar yaya fadeela, shi kuwa tun kallon farko da ya mata ya ɗauke kanshi, ya fadeela tace "zamu tafi Fauxa, haka kowacce mace take hakuri a duk randa aka kawo ta ɗakinta amma ba gaki ga fadyaa ba zaku ke haduwa nima kan in koma Australia zan zo kin ji?" Kanta ta mayar kasa tana jin kewan gidansu na shiganta, duk yadda ta so tayi dauriya a sadda suka fito tayi musu rakiya kasawa tayi ta fashe da kuka tare da rungume ya fadeela, barin ta yanzu zasu yi da wannan munafukar da kuma azzalumi? Yanzu kenan kowa baya son ta? A haka zata zauna dasu su biyun su kasheta a banza? Ya fadeela ne ta kalleshi tace "Ya Faizan se fa ka tayamu riƙeta" Haɗe fuska yayi yace "ke! Ban fa son hauka me haka? Se kace wacce za'a bari a gidan yankan kai?" A zuciyar ta tace "kaman ka sani wallahi babu maraba" Ganin bazata sake fadeelan ba yasa ya taka ya sanya hannu ya zarota daga jikinta suka shiga mota driver ya ja suka fice daga gidan, suna fita ya saketa ba tare da ya ce mata ci kanki ba ya juya ya koma, don Fatima bata fito ba wai ta sha magani kuma bacci me nauyi yake sakata shine suka ce kar a tasheta ai tayi kokari ma. Ta jima tsaye a wurin tana share fuska kan ta juya ta nufi steps na parlorn tana dan kallon black rumfa da aka yiwa mashigar yayi kyau sossai ba kaman normal da ta saba gani ba, koda ta turo parlorn ta shigo babu kowa. Stairs ta nufa ta fara hawa se a lokacin ta lura da dining area na parlorn kasan da daga saman stairs kana hango shi daga sama, akwai washing hand base da console a wurin shima, se kofa wadda babu tantama na kitchen ne, ba laifi gidan ya mata kyau ya burge ta. Parlorn saman ma ba kowa se kawai ta shige ɗakinta ta maida kofa, bata kwanta kaman ɗazu ba ta hau kalle kalle da taɓe taɓe kaman ba itace ke kuka yanzu ba, babu abunda bata duba ta taɓa ba, duk da yadda take zabga kamshin humra da turaruka haka tayi ta sake fesa na kan mirror ɗinta wai tana jin kamshin su, bayan ta gama tsab ta wuce bayi nan ma tayi ta dube dubenta, ba laifi bayin ya tsaru ta kan yi mamakin toilets na hotels da suke zuwa musamman irin su transcorp sede wannan ya ci uban waenchan haɗuwa.. Ita bata san ma akwai kayan bayi ruwan gold ba se anan ɗin kusan komai ruwan gold ne Fararen kaɗan ne. Bayan ta gama tayo fitsari dama bata sallah, ta ma yi mamakin wannan period nata be zo mata da ciwon da ya saba ba ko don sbd tashin hankalin da ta shiga ne oho. Fitowa tayi ta cire Rigan jikinta don ya ishe ta ta duba leggings da vest ta saka abunta ta zauna ta ci tayi Nak kan ta hau gado tayi ɗaiɗai ta fara bacci. (Su Fauza an samu duniya) Chan cikin baccin ta me daaɗi taji ana buga kafafunta, bata da nauyin bacci hakan yasa ta mike zaune tana ɓata fuska hasken bulb da ɗakin ya dauka ya tabbatar mata da dare har ya shiga bata sani ba tana baccin da ta kwana biyu bata yi ba. Kallon Fatima da ta tashetan take yi tana jira taji me zata ce sede shiru tayi tana sake kallon Fauxan zuciyarta na hautsinewa da wani zazzafar kishin yarinyar ta ko ina. "Lafiya zaki wani tasheni ina baccina kuma ki tsaya kina kare min kallo kaman yau kika saba ganina?" Haɗe rai Fatima tayi tace "kul ki soma min rashin kunya daga shigowanki gidana, idan baki sani ba ya kamata ki sani da ba yanzu bane, a da ina kallonki ne kawai a matsayin shashasha wacce bata san me ke mata ciwo ba shiyasa nake kyaleki kike abunda kike so, amma a yanzu da kika amsa sunan kishiyata yanzu ne zaki sake yanke rago ki tabbatarwa da duniya cewa Fatima munafuka ce duk na baya wasa ne" Murmushi Fauza ta saki tace "kishiya? Mtseww ke kika san wannan, in baki sani ba ya kamata a ce na saka wannan a bayan tosheshen kwakwalwarki, ban shigo gidan nan da niyyar komai ba don daga ke har mijin naki ba kwa gabana, amma daga sadda kika bari na harzuƙa zan nuna miki cewa kin riga kin bar kari tun ran tubani, zan zame miki kadangariyar bakin tulu se kin yi nadamar fara auren mijin kaddarana. Don haka ki kiyayeni" Yunkurawa Fauza tayi zata miƙe daidai lokacin da aka turo kofa hakan ya sa Fatima yin baya baya zata faɗi cikin zafin nama yayi hanzarin isowa ya tarota yana aikawa Fauza dake tsaye tsakiyar gadon bata kai ga Sauƙar da tayi niyya ba wani irin dead look. *Yanzu wasan ya soma* DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 17 *Assalamu Alaikum warahmatullah barkanmu da warhaka, fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya? Alhamdulillah na gode sossai da adu'o'inku gareni Allah ya saka da alkhairi🥰 jiki yayi sauƙi se a ɗaura daga inda aka tsaya in shaa Allah.* A hankali ta samu wuri ta zauna akan kujeran parlorn saman chan nesa da inda suke, dukda zuciyarta a tsinke yake don har Ga Allah Faizan na daga cikin waenda take jin shakkarsu don tana tsorace dashi ne tun tana ƴar ƙaramarta, matarshi kawai ya kama suka fita daga ɗakin nata bayan ya ce ta same su a parlor. Ya ɗan yi shiru kan yace "Fauziyya kike ko?" Kai ta ɗago tana Kallonshi wai ita yake tambaya sunanta? Bata amsa ba seda yace "wai ba da ke nake magana ba? Kin san Allah ki rufawa kanki asiri ki zauna lafiya da mu tun muna sheda juna, ba zan lamunci rashin kunyarki da fitsaranki ba, ba a kaina kaɗai ba har da matata" Kallon Fatima yayi yace "Daga yau ki sallami Baaba ta dinga tsabtace gidan nan tana girka muku abunda Zaku ci da ke da ita, ba zan iya cin jagwagwalonta ba don haka ke zaki kula da nawa abincina da gyaran ɗakina" Fatima na murmushi tace "in shaa Allahu habeeby" Ya sake kallon Fauziyya yace "Daga ni har Fatima akwai wadda kika fi shekaru?" Girgiza kai tayi yace a ɗan zafafe "baki da baki ne?" A hankali tace "A'a" Yace "madalla! Saboda haka duk safe ke zaki gaisheta, karki kuskura in sake ganin abunda ya faru yau ya faru don bazaki ji da daaɗi ba Fauziyya, matata ta fi karfin wulakantarwanki, Abu na ƙarshe shine babu wani zancen rabon kwana don zaki zauna ne a matsayin ƙanwarmu.." Kallon Fatima yayi yace "ko kina da abun cewa?" Tace "ya Faizan na ga baka ja kunnenta akan shan kayan maye da kuma bin maza ba!" Wani irin kallo Fauziyyan tayi mata kan ta maida idanunta kanshi jin mai ze ce, se taga ya kauda kai da alama ita yake kallo ganin zata kalleshi ya kawar da nashi idanun, bazata ce ga expression ɗinshi ba amma da saisaitacciyar murya ya furta.. "Gate ban amince ki taka ba tare da izini na ba Fauziyya" Abunda ya faɗa kenan ya sallameta, ta mike ta wuce ɗakinta ba tare da ta tanka musu ba. Fatima tace "Abunda zaka ce kaɗai kenan?" Ya ɗan miƙe tsaye kan ya ce "me zan ce to? Babu wadda ta sani anan garin da ze shigo har gidan nan ya ruɗe ta, hakanan tun da ta sanya kafarta cikin gidan nan na yiwa gateman kasheɗin bayan ni da ke kar ya bar kowa ya fita daga gidan nan ko ya shigo idan har ba da sanina ba" Ganin ze wuce room nashi tayi saurin mikewa "amma fa kai da kanka ka ce ka ganta a nan garin kenan ai baka san ko akwai wasu bad friends ɗinta a nan ba..." Ya dakata tare da juyowa ya kalleta na seconds kan ya juya kawai ya wuce ɗakin shi, zama tayi kan kujeran dabas tana sake sake, ta so ya gayawa Fauziyya maganan da ze hana ta bacci wlh akan shaye shaye da yawace yawace da take yi amma ba komai da ita take zancen. Itama mikewa tayi ta wuce ɗakinta don shiryawa ta dawo turaka. Samun wuri tayi kan kujera ta zauna tare da ɗaga throw pillow ta ɗaura kan cinyar ta ta zabga tagumi, wai haka zata yi wannan zaman? In aiki ne be dameta ba don horon da ta sha kwanakin nan a gidansu na aiki ba kaɗan bane har ma ta saba, amma bata da waya ba abokin hira, shiru haka ze yiwu kenan? Chan ƙasan ranta kuma maganan Fatima ba ƙaramin kuna yayi mata ba amma ba komai zata yi lokacinta. TV ta kunna ta rage daren da kalle kalle daaɗi sossai ta ji da ta ga ba wa'azu zuƙa bane, se karfe sha ɗaya ta kwanta don ma ita ba gwanar ci ba ce da dole se ta fita ta nemi abinda zata ci. Buga kofan ta da aka yi da karfi shi ya tasheta a ɗan firgice, dalll haka aka kunna mata bulbs ɗin ɗakin duka Fararen waenda suke da matukar haske, da sauri ta sanya hannu ta rufe idanunta, duniya ta tsani a kunna mata wuta daga tashi daga bacci. "Malama tashi ki sama min abunda zan ci karfe bakwai nake da lectures" Dukda yadda ranta yayi mugun ɓaci bata tanka ba, haka kuma bata ɗaga idanu ta kalleta ba. "Da ke fa nake magana malama!" Har lokacin bata yi magana ba tana calming kanta ne, bayan ta gama Adu'ar tashi daga bacci ta sauka kawai ta shige toilet bata ce komai ba. Se hakan ya kular da Fatiman, a fili ta furta "kammm ni zaki mannawa hauka? Wato ga mahaukaciya tana magana?" Kwafa tayi ta fito ta je ta zauna a parlorn saman ta ɗaura ɗaya kan ɗaya tana girgizawa, time ta dibar mata in bata fito ba kuma wlh se ta kai karata wurinshi. Ita kuwa Fauziyya watsa ruwa tayi ta fito ta ɗan shafa mai da turare kadan ta saka cotton bubu ta fito, a kan kujera ta wuceta ta nufi hanyar kitchen ba tare da ta ko kalleta bane. "Ke! Ina zaki je? Ba'a shiga min kitchen kije na ƙasa wannan ɗin abincin mijina kaɗai nake dafawa a ciki gudun barbaɗe" Juyawa kawai tayi ta nufi ƙasa ba tare da tace komai ba. Dankali ta fere me yawa ta zuba gishiri tuli guda kan ta soye shi yayi kararau ta juye a warmers ta ɗauka ta je ta ajiye kan dining kan ta wuce ta haura. Har zata wuce ɗakinta Fatima ta ce "Fauziyya..!" Juyawa tayi ta nufi dining ɗin saman, ganinshi a ciki yasa ta ce "Ina kwana" Kaman yadda yayi mata umarni "lfy" Shine abunda ya amsa da kan ya cigaba da cin abincinshi. Kallon kiran me kika min kawai take yiwa Fatiman, ita kuma se tayi shiru na seconds kan tace "tunda ni ba zaki gaisheni ba, ina kwana? Fatan kin tashi lafiya?" Wani irin kallo Fauza ke mata na kina kure haƙurina, ɗaga idanu yayi ya kalleta se tacewa Fatiman "Ina kwana" Fatima tace "lafiya ƙalau ya kwanan bakunta?" Bata amsa ba hakan ya sa Fatima cewa "yauwa kin gama abincin ba?" Kaɗan ya saura zuciyar Fauza ya zo wuya tace "uhm" "yana ina to?" "Kasa" "ka ji ki, ai anan ne muke karyawa, je ki ɗauko mana" Seda ta lumshe idanu ta buɗe kan ta juya ta nufi sauka, shi karan kanshi da kallon mamaki ya bita a sanin halinta bazata bi umarnin Fatima kai tsaye haka shiru ba, ko ta fara sauyawa ne... Kafadan shi yayi shrugging kan ya cigaba da cin abincin shi. Bata jima ba se gata da food flask ta zo ta ajiye kan dining ɗin ta juya zata tafi "ke bazaki ci bane Fauza?" Juyawa tayi ta kalleta kawai kan ta juya ta wuce ciki. Tana shiga ta faɗa kan kujera tana ji kaman ta fashe da kuka sbd yadda ranta yayi mugun ɓaci gashi bata fitar da abunda ke ciki ba, ita kuma haka take in har bata rama abunda aka mata ba ranta yayi ta zafi kenan da kuna. Kakari taji me ƙarfi se kuma taji ana kiran "ke! Ke!!" Ta san ita kaɗai yake kira da ke hakan be sa ta amsa ba, tana kwance kan three seater taji ya turo kofan ya shigo. "Ke! Bakya ji ina kiranki ne? Ko yadda kwakwalwanki yake a toshe haka kunnuwanki?" Miƙewa zaune tayi tare da fara kunkuni "to ai ni sunana ba ke ba...." Ɗallin bakinta da taji an yi ne ya sakata sakin ƙara tana dafe bakin sbd azabar zafin da ya ratsa ta, hawaye ne ya cika idanunta ta ɗago tana Kallonshi. Kau da kai yayi yace "kashe min mata zaki yi? Wani irin jagwalgwalon girki ne kika yin nan? Baki san tana da BP bata cin gishiri bane? Tashi ki wuce mu je" Mikewa tayi ya sako ta gaba suka fito, Fatima na kwance kan kujera sama sama take numfashi sbd yadda take jin kaman zata mutu, murmushi me kyau ta saki ganinta hakan sarai ta ji yadda ake ta maganan jininta na hawa sossai sbd damuwar da ta sawa kanta na ɓarin da take tayi hakan yasa aka hanata cin gishiri, da gangan tayi labtawar da ko loma ɗaya tayi se ta ji a jikinta. Da sauri itama ta karasa gabanta ta duka tana cewa "Ya fati sannu! Me ya sameki haka?" Harara ta zabga mata kan ta cigaba da numfashin ta hannunta dafe da kai. Rufeta da faɗa yayi sossai kaman ze daketa, raurau tayi bayan ya gama idanunta na zub da hawaye tace "Yaya Don Allah kayi haƙuri, ni ban iya bane, ban kuma san tana da hawan jini ba... Jiya jiya fa na zo" Lumshe idanunshi yayi se ya sauke ajiyar zuciya kawai ya wuce ɗakin Fatima don ɗauko mata hijab su tafi asibiti. "Na san ba haka kika so ba ko? To mu zuba da ni dake ɗan halak ka fasa, in makirci ne ke jiya kika soma amma Fauza kam ta jima a ajin don ina ga har ta gama ma ta fita da sakamako me kyau" Jin motsin kaman yana dawowa ne yasa tayi saurin karasawa tana ɗagota tace "I'm so sorry ya fati" Hijab ɗinta ya miƙawa Fauza ta saka mata, sakawar ma na mugunta ta mata don seda ta karɓa da kanta ta karasa a hankali. "Karki ci abincin nan, ki nemi wani ki ci bari na kaita asibiti.." Kanta kasa tana zub da hawaye ta ɗan ɗaga, har ya kama Fatima a jikinshi sun nufi stairs ya ɗan dakata tare da waigowa kaman ya zamar mishi dole yace "kukan nan kuma ya isa haka" Yana kai nan suka fara sauƙa. Wani kalar dariya Fauxa tayi tace "gobe zaki maimaita abunda kika min munafuka kawai" Dining taje ta samu abincin shin ma be gama ci ba ya tashi, ta kara akai ta ci tayi Nak ta tattare wurin kan ta zo ta fara kimtsa parlorn da ba wani datti sbd rashin mutane dayawa a gidan. Bayan ta gama ta koma ɗaki tayi kwanciyarta cikin kewan jaddanta kan bacci ya sure ta. Chan cikin baccin ta taji ana taɓa gefen hannun kujeran da tayi matashi dashi, yadda ta saba yiwa jadda in bacci be ishe ta ba ta tura baki ta mike cikin kunkuni tana kaikaya idanu haka tayi, a hankali ta buɗe idanun nata se suka faɗa cikin nashi, yana tsaye hannunshi ɗaya a aljihu ɗaya na riƙe da Wayanshi, har kaman ze mata faɗan kwanciya bisa kujera se ya fasa. "Riƙe Jaddah ke son Magana dake" Ya faɗa yana miƙa mata wayan. Da sauri ta karɓa "Jaddah na!" Tayi maganan tana karya wuya se hawaye.. "Haba Fauza, ke da nake miki kallon jaruma ashe ke ɗin raguwa ce kukan ma menene to? Yayyun naki suna miki wani abu ne?" Yadda ya kakkafeta da idanu yana jiran jin me zata cewa jaddan yasa tace "babu komai Jaddah kawai nayi kewanku ne" Tace "nima anan hankalina da tunanina duk yana wurinki Fauziyya fatan babu komai ko? In akwai wani abu ki gayamin" Tace "ba komai, ina mammi ya kafafunta? Allah sarki yanzu wa ze dinga mata Adu'a oho" Ta faɗa cikin alhini. Murmushi Jaddah tayi tace "tana yiwa kanta amma na san tayi kewanki itama, fadyaa zasu taho ranar Laraba me kike so a kawo miki?" Zata yi magana ya zare Wayanshi ya sa a kunne tare da Juyawa ya nufi fita yana cewa "Zaku ƙarar min da credit, me zata buƙata kuwa yarinyar da ta zo jiya in ba ke ba ma Jaddah" Zata fara mishi nasihun da suka kashe mai jiki da niyyar da yayi a kan yarinyar yayi saurin kashe wayan, daga Jaddah, Babanshi da mammi duk in sun kira ko ya kira su maganan ɗaya ne kar ya sa yarinyar nan kuka kanwarshi ce wacce ko ba aure shi me share mata hawaye ne, hakanan bata da kowa a Abuja in ya cuceta don ba idanunsu Allah na gani kuma ze saka mata. Yana zama kan kujera se ga call na baba prof suka gaisa kan ya ce "na manta ne ban maka maganan karatun yarinyar nan ba, ka san ko bare na aurarwa ɗiyata akwai sharadin yin karatu to akan Fauziyya ma ba zai sauya zani ba, idan Neco ɗinta ya fito zaka nema mata university of Abuja su cigaba da zuwa da yayarta" Idanunshi na kan TV ya ɗan fesar da iska yana shafa kai yace "Baba ba za'a bar maganan makarantar yarinyar nan mu ga kamun ludayin ba tukun? Ba wai ina nufin ba zata yi bane sede ina tsoron komawarta halin da ta shiga a baya ne wadda yanzu se ya fi zunubi da da, tunda yanzu tana da aure" "in shaa Allahu yanzu bani da shakka akan Fauziyya zata maida hankali tayi abunda ake so, mu cigaba da Adu'a dae kar mu gajiya sannan ka riƙe ta amana kaman yadda ba zaka cutar da farida ba karka cutar da ita Faizan" Ajiyar zuciya me nauyi ya saki yana sake shafa kanshi Fatima ta fito ta zauna kusa dashi tana cewa "ya aka yi ne?" Ya ce "Fauziyya...! Kowa ya tashi amana amana duk sun ɗaure ni da jijiyoyin jikina wallahi" Bakinta ta taɓe kan tace "amma yaya ka san yarinyar nan da gangan ta so cutar dani ɗazu? Ai ko bata san ina da BP ba ta iya girki me yasa bata yi me kyau ba?" Yace "Meyasa ne kike son dawo da abunda ya riga ya wuce Fatima? Yarinyar nan ta baki haƙuri ba shikenan ba? Kina ji dae ina faɗa miki yadda ake bani amanarta kina so ne in yi ta jan matsala tsakaninmu har iyayemu su yi fushi damu?" Girgiza kai tayi ranta na zafi, wai ina duk tsanar da yake cewa yana yiwa Fauziyyan? Duk a kwana ɗaya baya bata wani wuta wuta kaman ma lallaɓata yake akan wani dalili? Idan ta bar zaman nan ya cigaba a haka akwai matsala dole zata nemi wani hanyar wargaza tsakaninsu. Da sauri ta miƙe ta ɗauki wayanta dake kan table ta nufi ɗakinta don neman shawarar abin yi... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 18 Bata san me ya hau kan Fatiman ba ta dena shiga mata sabga girki ma idan ita zatayi bazata ci ba, se ta koma dafa nata ita kaɗai ita Fatiman nayi musu su biyu. Tsakanin ta da shi kowani asuba ze tasheta sallah, anan take gaishe shi ba zasu sake haɗuwa ba se wani asuban sbd bata fita a sadda taji motsin su a parlor, babu ruwanshi da komai nata tunda bata rasa ci da sha ba don be katangeta ta harkar abinci ba kullum kawo abubuwa ake a loda a fridge se abunda taga daman dafawa. Iyakaci ta ci ta sha ta kwanta, a sati biyu da suka yi tayi wani irin kara girma fatanta ya sake yin fresh sbd zama wuri ɗaya, kaɗaici duk ya dameta gashi bata da waya bare ta ji mutanen gida. Yau bata nemi abinci ba sbd wani series da ake yi a Star life da ya ɗauke mata hankali bata kula da lokaci ba kawai taga magrib yayi ko da tayi sallah bata tashi ba har tayi isha kan ta mike ta ninke hijab ɗin ta ajiye, sanye take da wani half gown wadda iyakanshi kaurinta purple ya zauna mata das a jiki, gyale ne yake dashi se ta mishi ɗaurin da ya fitar da jelar gashinta yana reto, ɗan kunne fashion purple ne a kunnenta haka ta buɗe kofan ta ta fito. Dasu ta ci karo yana zaune hannunshi da remote Fatima kuma na kwance a kan cinyar shi cikinta gwanda ne a bowl da ta yanka kanana tana ci a hankali, jin motsin ta yasa duk suka ɗaga idanu suka zuba mata kowa da abunda yake saƙawa a ranshi.. Kaman bazata yi magana ba se tace "Sannunku" Be amsa ba ya maida kai TV haka Fatima ma bata amsa ba, a wuya yarinyar ta tsaya mata barin ma yadda take kara murjewa tana kyau kaman ka sure ta, ba don umarnin da aka bata na ta ɗauke kai a kanta zuwa ɗan wani lokaci ba da bata barta tana morewa zamanta gidan ba. Kwafa ta ja a ranta tana cewa 'Fauza kema maganin ki' Daga haka ta nufi ƙasa abunta, kitchen ta je ta fara Haɗa macoroni salad ɗan daidai na cikinta, bayan ta gama tayi smoothie na ayaba da madara ta zuba a cup, kyuiyar haurawa taji dashi don se ta sake fito da kwanukan bata iya bari a ɗakinta don haka dining kawai ta karasa ta zauna ta fara cin abincinta. Da ma ze yiwu da ta ce a dawo mata da kayan ɗakinta ɗakin ƙasan tana rayuwanta hankali kwance, da kyar ta gama ɗan abincin taje ta dauraye plate da cup ɗin ta mayar ta kara kimtsa kitchen ɗin don tsabtar gidan banda dakunan masu gidan har yau bata dena ba. Haurawa ta nufi yi yanayin da ta iske su ne yasa tayi saurin ɗauke kanta ta nufi ɗakinta Dukda sun riga sun Haɗa idanu dashi, janyewa yayi wadda hakan ya sa Fatima Juyawa se ta ganta tana kokarin shiga ɗakinta, tana ji Fatima na tsaki sede bata juyo ba Dukda kuwa so take tayi waya da su jadda kaman me. Haka dae ta kwanta tana ta juye juyen kewa kan bacci ya sure ta, washegari da asuba da ya shigo ɗakin ya jima tsaye yana kallon yadda ta kwanta ɗin a matukar takure irin kaman mutum na kaɗaici haka, se ta ɗan bashi tausayi bubbuga gefen pillown yayi tayi miƙa wadda ya saka shi saurin ɗauke idanu daga kanta kan ta miƙe zaune bakinta na motsin Adu'a kaman yadda ta saba tana gamawa tace "Ina kwana" Ya amsa "lafiya" Ɗan tsayawa yayi be fita kaman yadda ya saba ba yana tunawa da Fa'iza ta zo gidan basa barin ta tayi mintuna arba'in ɗaki dole zasu zauna da ita su yi hira a ci abinci ayi kallo duka, amma in ba jiya ba ya manta rabon da ya ganta tana tafiya zata kitchen ko wani abu Sam basa haduwa se a ɗakinta in ya zo da asuba ba dole ta takure wuri guda ba! "Kina da wani matsala ne?" Ya tambaya. "A'a amma don Allah ina so zan yi waya da su Jaddah yau sati biyu kenan rabon da in ji muryarta" Ta karashe tana Kallonshi da idanun baccin ta waenda suka kara girma da haske ba kaman na normal wasu mutanen ba da in sun tashi idanunsu yayi ja. Wayanshi ɗaya ya fitar daga aljihunshi fara sol design ne da bata taɓa gani ba don ba iPhone bane ba kuma dangin su tekno bane. "Yanzu yayi sassafe da ƙira, anjima se ki ƙira su" Hannu tasa garin saurin karɓa hannayensu suka shafi na juna, duk ɗaga kai suka yi suna kallon junansu kan ya ɗauke nashi yana furta "saura ki kira waenda basu dace ba ki ga ikon Allah" Yana kai nan ya juya ya fice. Baki ta karkace tana tuna su waye ne basu dace ba? Kwafa tayi su sakina ne kilan yake nufi, ajiye wayan tayi taje tayi alwala ta zo tayi sallah. Bayan ta idar ta koma ta kwanta se seven ta tashi ta fara gyaran ɗakinta tana gamawa taje tayi wanka ta shirya cikin wani Hot red top da black wando ta ɗaura black ɗan kwali, bakinta ta sanyawa red lipstick se tayi wani irin kyau, kwalli ta zana a idanunta kan ta ɗauko wayan ta zo kan kujera ta zauna. Sliding tayi se wani hotonshi hadadde ya bayyana, sanye yake da kayan aikinshi cikakke yayi wani irin kyau gashin kanshi na sheki yana dariya ne tsaye a matakalar jirgi aka ɗauke shi, kurawa hoton idanu tayi na mintuna masu yawa kan ta sauke ajiyar zuciya tana shiga call logs. Bata san da me yayi saving number ɗin jadda ba se kawai ta shigar da numbobin tunda tana dasu a kai. "Jaddah na" Ta faɗa bayan an ɗaga wayan ko sallama bata yi ba. Jidda da ita ma muryarta ya bayyana jin daaɗin ta da jin muryar Fauzan tace "Na'am Fauza ta ya kike? Ya gidanki?" Shagwabewa tayi tana cewa "shine ko kewata baki yi ba ko Jaddah" Jaddah tace "na isa ban yi kewar baki abun magana ba? Ai ba karamin kewanki nayi ba babu me sakani magana da shari'a, babu me nemo faɗa in tare, babu wacce kullum ke sakani kumbiya kumbiya idan professor ya aiko nemanta" Dariya Fauxa tayi tana jin tayi missing old life ɗinta, rayuwa fa kenan! Waye ze yarda yanzu Fauxa tayi sati biyu bata nemi faɗa ba, ai da a da ɗinta ne ko Fatima bata nemeta ba wallahi ita se tayi yadda tayi ta nemeta faɗa, amma gani take yanzu ta wuce level ɗin sede in an nemeta a samu. "Jaddah to meyasa bakya nemana?" Ta faɗa tana tura baki. "Kullum sede wannan me katon kan yace min baya gida ko kin yi bacci..." Hannunta ɗaya ta ɗan sa baki tare da zaro idanu tace "khaihh Jaddah Ya Faizan ɗinne me katon kai? Wlh kanshi daidai ne" Salati Jaddah ta ɗauka muryarta cike da farin ciki da dariya tace "innalillahi.. Fauziyya yau ke kike karbawa Faizan faɗa? Azzalumin?" Da sauri ta katse wayan kunyar duniya na kamata, me ya kaita? Wlh ta ma rasa ya aka yi tayi wannan subutar bakin, ai se ta shiga bakin duniya in dae Jaddah ce. Jaddah kuwa a ɓangarenta har sujada tayi na jin daaɗi, ko basu zama kaman yadda take so ba alamu sun nuna lamuransu akwai haske, da Faizan na cutar da ita ta tabbatar ita ce ma zata fara kawo sukarshi yau wace rana! Sake kiran layin tayi da kyar Fauziyya ta ɗauka.. "Eyyaa Jaddah kewa!" Ta fara kawo maganan dake ranta. "Ina jin kaɗaici da kewa sossai, babu inda nake zuwa babu wadda ke zuwa guna banda waya bare in dinga jin muryarku, jadda ko Ya fadyaa da kika ce zasu zo basu zo ba har yau" Jaddah tace "haka aure dama ya gada barin ma a wuri me nisa, kiyi hakuri zan mishi magana ko wayan ne se ya saya miki ai ba wani matsala kuma bayan wannan ko?" Kai ta gyaɗa tace "babu" "Ina Fatima kwana biyu itama bamu gaisa ba" Tace "Ina ga ta tafi school" Hira sossai suka yi jadda tayi ta faɗa mata abubuwan da suke faruwa a gidan, wadda ya mata ta dara wadda be mata ba ta tofa albarkacin bakinta wani kuma tayi Kwafa, barin ma su ya Farhan kam. Da kyar suka yi sallama don har katin Jaddah ya kare ta sake kira da wayan Faizan ɗin. Bayan ta sauke wayan fuskanta cike da annashuwa ta shigar da layin Mammi. "FIRST LOVE" Sunan da taga yayi saving kenan da emojis ɗin heart, murmushi ta saki tana tuna nata uwar wadda basu taɓa magana ba tunda ta zo. Bayan mammi ta ɗauka suka gaisa take tambayarta kafanta tace "Fauziyya kafafun nan se godiyar Allah amma kam da abunda yake nema" Fauziyya bata gane zancen ba tayi mata Adu'ar samun lafiya, bugan cikinta mammi tayi tayi don taji ko Faizan ɗin na mata wani abu sai de ko ɗaya bata kawo wani laifinshi ba don be matan ba, shakuwa ne dama chan babu tsakaninsu, zaluntarta da ya kan yi in ta mishi abu kuma ya daina tunda bata mishi koman ba. Daga karshe da dabarun zama da miji da kuma nasihu mammi tayi ta mata kuma tana ɗauka wannan karo kam har tana mamakin kanta. Bayan sun gama ta kira Ammi.. "Assalamu Alaikum Ammi" Fauza ta faɗa bayan Ammi ta ɗauki call ɗin. "Wa'alaikumussalam warahmatullah Fauziyya ke ce?" Shiru tayi jin muryar Ammin nata babu ɗauki sossai kaman yadda muryar jadda da mammi suka bayyana mata kewanta da suka yi tace "ni ce Ammi, kuna lafiya? Ya baba?" Ta amsa da "lafiya kalau ya gidan naki? Fatan dae baki bari ana hawa kanki kaman yadda kike da?" Meyasa kowa ke mata nasiha ta zauna lafiya da mijinta amma mahaifiyarta kuma na shirin kawo rabuwar hankalinta? "Ammi ai babu abunda suke min, muna zaune lafiya" "mene? Ashe dama karyar kiyayya kike yiwa Faizan ɗin kenan, na tabbatar shi kuma a wurinshi ba haka take ba don kiyayyar namiji bata taɓa gushewa, kuma bata sauyawa, kiyi tunani dae... Sannan ki sani mijinki ba ke kaɗai ba har ni ba ƙaunata yake ba ke hatta mahaifinki don gani yake mahaifinki kusan rabi da kwatar dukiyarshi na Mahaifinsu ne shiyasa yanzu yake saka idanu akan harkokin business na babanki fiye da yadda yake sakawa Faraj da ya fara kula da na babansu" Shiru tayi cikin dan nazari kan tace "Ammi wannan duk ba wani abu bane, kilan ba yadda kike tunani bane don na san dukkaninmu da Baba Alhj da Baba prof duk iyaye muka ɗaukesu kuma matsayin abu guda babu banbanci, sannan Ammi ai maganan yaya Faizan baya kaunarki tun da nake na san yana zuwa gaishe ki amma baki taɓa buɗe baki kin amsa ba kuma har yau har gobe kenan be tsane ki b....." "Rufe min baki, ina nuna miki gabas kina yamma... Ke kika sani" Tana kai nan ta kashe wayan.. Da idanu tabi wayan cikin mamakin Amminta, ta jima sossai tana nazari dayawa daga cikin ɗabi'un Ammin nata sede ta rasa a wani mataki ko matsayi zata ɗaura shi. Baba prof ta kira shima yayi farin cikin jin tana cikin ƙoshin lafiya ya kuma yi mata albishir da result ɗinta na neco ya fito kuma yayi kyau don har yayiwa Faizan maganan yi mata registeration na jamb. Taji daaɗi sossai tayi ta godiya da Adu'a ga baban, nasiha ya sake mata ya kuma gargadeta da Adu'a kaman yadda ya bata wani takarda da ke ɗauke da Adu'o'i masu yawa ya kuma umurceta da ta lazimcesu kuma tana yi ɗin sossai. Bayan sun gama ta kira babanta shima ya ji daaɗin jinta lafiya ƙalau Dukda kullum a tsorace yake kar ta shukawa Faizan abunda ze zama silar tsinkewar zumuncinsu, idan har ze ga wayan Faizan se gabanshi ya faɗi da Tunanin ze ce mishi Fauza ta yi wani abun sede duk be ji ba, tun yana tsoracen yanzu har ya fara sakewa. Nasiha shima yayi mata wadda be mata a lokacin barin ta gidan ba kuma ta ji daaɗi suka yi sallama tana ji matar nan na Mtn na cewa one minute remaining. Sosa kai tayi bayan ta sauke tana kallon wayan yau ƙaniyarta Faizan ze ci ta ƙarar mai da katin waya. Balcony ɗinta ta fita tana kallon harabar gidan da Gidajen unguwar da yawanci kusan irin nasu ne benaye, wayan ta sake ɗagowa ta shiga camera tare da Juyawa ya bata background ɗin unguwar Ta fara pictures style kala kala tana murmushi barin ma da taga yadda tayi kyau. Seda ta gaji ta dawo ɗakin ta zauna a coffee chair ɗin tana kallon pictures ɗinta, tana cikin scrolling taga nata sun ƙare sun shiga na wayan, bata tsaya ba ta cigaba da scrolling yawanci hotunanshi ne wasu ya sani wasu be sani ba, daga yanayin hotunanshi zaka san yana da zafin kai don kusan duk babu wadda yake cikakken dariya banda na fuskan wayan. A kan wani ta tsaya wadda aka dauke shi be sani ba shima da uniform ɗinne hannayenshi rike da abun tuka jirgin kunnenshi sanye da headphones ɗinsu ya ɗan wai go kaman ze yi magana ne aka ɗauka ba karamin kyau yayi ba. Scrolling tayi ta wuce se taga hotonshi da Fatima, Fatiman ce ta ɗauka kwance a jikinshi kaman a wani wurin shakatawa ne, se wasu a bakin ruwa wadda ba tantama Legos ne don ta san chan ne kaɗai za'a samu beach haka, yana sanye da kananun kaya tana sanye da wasu hoodies orange, baki ta taɓe zata wuce se wayan ya ɗauki ringing. 'My number' ta ga an saka, to wani number kuma? Har wayan ya kusa katsewa kan tayi kundunbala ta ɗaga "Fauziyya... Ina ta kiran Fatima bana samunta ki fita ki kama mata aiki su Faahim zasu kawo mana yini da yaran nima Ina dawowa nan ba da jimawa ba" Kusan rikicewa tayi da sauri kuma tace "Toh" Kashe wayan yayi ba tare da ya sake furta komai ba. Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke...a fili ta maimaita sunan nata "Fauziyya.." Sai de bata ji ya mata kaman yadda shi ya kira ɗin ba don har faɗar mata da gaba yayi. Tuna su Ya fadyaa ne zasu zo yasa tayi saurin mikewa ta fito parlorn saman babu motsin Fatima don haka kasa tayi, ba wai tana tsoron Fatima ne yasa bata shiga kitchen ɗin saman ba, kawai tana tsayuwa ne limits ɗinta gudun fitina da tadawa iyayenta hankali, Allah kaɗai ya san yadda zuciyarta yayi haske da taji yadda suke farin cikin da jinta ba kaman da da a duk sadda za'a kira sunanta se gabansu ya fadi ba. Abinci ta fara Haɗawa me rai da lafiya, Allah ya sa ma komai za'a kawo gidan a gyare ake kawo shi kuma cooker ɗin me kai har shidda ne a take ta Haɗa pineapple rice kamshinshi duk ya cika kitchen ɗin, bayan ta gama ta yi mishi pepper chicken, tayi grilling fish manya guda biyu se ta Haɗa zobo, karfe sha ɗaya da rabi lokacin kuma har lokacin bata ji motsin Fatima ba. A dining na sama ta shirya su kan ta shiga ɗakinta tayi wanka, ta sanya wani material lace riga da skirt yayi mata kyau sossai ta fita shar da ita, lip gloss kawai ta shafa ta ɗaura dankwali harda sarka da abubuwan hannu ta saka. Daidai lokacin take jin shigowar mota, farin ciki sossai ne ya ratsa ta yau zata kalli mutane, mutane su kalleta ko da basu wani yi shiri da ya fadyaa ba sbd rashin jinta yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya tana son ta kuma har ranta kaman yadda take jin sauran en uwanta "oyoyo" Ta faɗa tana rungume ya fadyaa, ya fadyaa ma na murmushi tace "oyoyo Fauzan jadda, masha Allah.. Kin ganki kuwa?" Da gudu yaranta biyu Asma'u(husna) da Sameer suka zo suka rungumeta suna mata oyoyo, cikin jin daaɗi ta tarbesu, tana cewa ya Faahim "sannu da zuwa yaya Faahim" Yace "uhm karki yi ya Faizan ya jiki ni yanzu ƙani nake, Aunty Fauxan Jaddah yauwa sannunki" Dariya duk suka yi ta musu iso ciki dukkansu biyu kallonta suke yadda ta sauya, a parlorn sama suka baje suka fara Gaisawa ta kawo musu ruwa da fruits. "Ina Fatima ne naji gidan shiru" Fadyaa ta tambaya. Fauxa na barewa husna lemon ɓawo tace "nima fa tun safe bamu haɗu ba kilan tana ɗaki kila kuma ta tafi school" Bayan ta bata ta dubi ya fadyaa tace "ya fadyaa tun fa wanchan sati Jaddah tace min zaku dawo shine baku zo ba har se yau" Ya Faahim yace "ba gashi mun zo ɗin ba dae, Ya Faizan ya ce ya shiga wurin Faisal ko?" Tace "eh ya de ce gashinan zuwa" Kallon juna Faahim da fadyaa suka yi suna gulma, yadda ake zaton jin hayaƙi a gidan Faizan ba haka ba, ashe igiyar aure na natsar da mutum? "Kinga muna ta shirin tafiya ne zan ga Dr shi kuma ya Faahim ze yi wani course to har yanzu visa ɗin husna ne bamu samu ba gashi ma lokaci na ta tafiya" Cewar Fadyaa "ai na ce miki mu hakura mu barta wurin su mammi kin ce za'a kara mata dawainiya ga rashin lafiya" Cewar Ya Faahim Fauza tace "to don Allah ni ku bar min ita kan ku je ku dawo Allah zata debi min kewa dama zaman kaɗaici ya isheni" Zaro idanu fadyaa tayi tace "Fauza rufa min asiri da mijinki..." "Me mijinta yayi ne?" Faizan ya faɗi yana shigowa cikin parlorn, duk ɗago idanu suka yi suna Kallonshi... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 19 "Ayya don Allah yaaaya su bar mana ita anan pls!" Yadda tayi maganar yasa dole ya kafeta da idanu yana kallonta, ta wani narke fuska se yaji wani abu ya mitsini zuciyarsa, ya lumshe idanunsa ya buɗe. "Da nan ɗin da wurinsu duk ɗaya ne tunda mu ma iyayenta ne" Ya faɗa yana zama, da kallo ta bishi babu laifi ta fahimci guy ɗin ta ko ina ya haɗu, komai nasa me kyau ne, kuma ko wani irin sutura ya sa ta kan zauna daidai da tsarin hallitarsa, ɗauke kai tayi ganin ze kalleta ta dubi husna tace "zamu zauna ko husna?" Kai yarinyar da bata wuce six years ba ta gyaɗa tana dariya. Su fadyaa ma fuskansu cike da murmushi Alhamdulillah ko gobe ne yanzu kam zasu iya tafiyar su, Gaisawa suka yi da Yayan nasu, kiran sallahn azahar ya sa mazan suka fice sallah yayinda su kuma suka shige ɗakinta bayan sun yi sallah fadyaa ta dube ta tace "Fauza ba wani matsala ko?" Fauxa ta ɗan yi kasa da kai kan ta ɗago tace "ya fadyaa dama can kin san ni da Fatima Bama shiri to dae har yanzu bata sauya zani ba, ta ɓangaren shi kam ba wani matsala, matsala ta ɗaya ne" "Uhm" Fadyaa ta faɗa jin ta ɗan yi shiru "me yasa nake jin Ammi ta sauya min daga wacce na sani? Meyasa bata so na zauna lafiya a gidan nan kaman yadda kowa ke buri? Duk yadda zan duba na kasa fahimtarta Ya fadyaa" Shiru fadyaa tayi na mintuna har saida Fauza ta sake kiran sunanta ganin fuskanta ya bayyana damuwa tace "Fauza babu abunda zan iya ce miki saide kiyi haƙuri da ita, uwa ta wuce gaban wasa amma ina me tabbatar miki ni kaina tun daga randa na amsa auren ya Faahim Ammi bata sake sakarmin fuska kaman yadda take yiwa su Fadeela ba, ban sake jin daaɗinta a matsayin uwa ba, ban sani ba ko tsanar da take yiwa Mammi da ahalinta ne ya shafemu ko yaya" Ajiyar zuciya Fauza ta sauke gaskiya halayyar Amminta na ɗazu ya dameta, jin motsin mazan yasa suka miƙe suka fito. Yana kallonta yace "Fatima fa?" Tace "bari na duba ta" Karasawa kofan ta tayi tayi sallama shiru tayi knocking sau biyu shiru, juyowa tayi ta kalleshi shima ita yake kallo kan ta murɗa kofan da nufin shiga sede a rufe yake ruff da makulli. "Baki faɗa mata sakona bane?" Tace "ban ji motsinta bane shiyasa" Wayanshi ya fiddo yana shirin kiran Fatiman yayinda ita kuma tayi dining ta fara kwaso abincin tana kawo su tsakiyar parlor, gabanshi ne ya faɗi kardae ita ce ta kwaba musu abunda zasu ci? Ai da bari ma tayi ya saya a waje tunda bata samu Fatima ba da jagwalgwalontan nan. Amma kuma ina Fatima ta tafi ba tare da ta sanar dashi ba?. Jin wayan na shiga ya sa ya tashi ya wuce ɗakin shi don kar su ji tambayar da ze yiwa Fatiman sanin ba girman shi bane taya za'a yi mace ta fita babu izinin miji? Ita kuwa bayan ta gama ta kwaso plates da spoons da forks haɗe da tissue ta kawo, babban warmer me ɗauke da pineapple rice ɗin ta buɗe a take kamshi ya cika su nan ta ɗauki plate zata fara serving kawai taji hannunsa mai azabar sanyi da taushi cikin nata. A razane ta ɗago se suka Haɗa idanu ya kauda kai yana zare serving spoon ɗin yace "kama wani let me help with this" Janyewa tayi tana jinta wani iri, basarwa yayi ya fara serving yana kawowa Faahim Hirar aikinshi da kusan akan zancen jirgi ne tunda shi Sojan sama ne. Miƙewa tayi ta sauka kasa ta samo silver tray me Adon gold ta fidda zobon da ta yi ta ɗaura a kai ta jera cups ɗin jug ɗin a gefen tray ɗin kan ta dawo ta ajiye musu fadyaa na mata sannu. Kifin ta yaye wa foil paper da ta Naɗesu dashi, shi kuma yana sanyawa kowa pepper chicken ɗin, fadyaa na kallon su da burgewa don ba karamin kyau suka mata a taren ba. Bismillah yayi duk suka sauko, zuciyarshi dae a tsinke kar su sha kunya ya ɗibo abincin a spoon ya kai bakinshi. Lumshe idanu yayi se ya buɗe a kanta maganganun su da su Faisal ɗazu a office ɗin Jafar ne ya dawo mishi. Bayan ya sauke wayanshi a sadda ya faɗa mata su fadyaa na zuwa Faisal yayi dariya yana cewa "kaga mijin mata biyu cikin wata biyar ba... Kai fa kana morewa ba'a fita a angonci ba an sake dulmiyawa sabuwa dalll me sirrin ne?" Tsaki yayi yana furta "kanku ake ji" Jafar yace "kaima za'a ji naka ne a sadda ka shiga hannun Fauza" Wani dariya yayi na baka da hankali yana dawo da kwakwalwar shi baya wurin Tunanin suffar ta da har za'a ji kanshi, a ganin da ya mata na ɗakinshi, da ganin da yayi mata randa aka kawo ta ya san kwarai tana da cikakkiyar siffa da sura, abunda kuma ke kashe shi ba ƙarya sune idanunta waenda baya jurar kallon cikinsu ba tare da yaji wani yanayi da be san menene ba, ba karya yarinya ce me cikakkiyar suffa da daradaran idanu, hotonta rungume da Zubair a elevator ne ya dawo mishi wadda ya saka shi saurin kau da Tunaninta yana sakin tsiririn tsaki. "Ya dae angon mata biyu? Yaushe ne za'a gayyacemu cin abinci ne kaga dae tun kawo Fatima kake mana haka haka, matar Faisal har ta haihu muna gari ɗaya baka bar matarka ta zo ba" Cewar Jafar "sannan ka manta Fatima tana rashin lafiya ne? Bari na zo na tafi kar baƙin mu su zo bana nan, amma karku damu kanku in shaa Allah nan kusa zan gayyaceku cin abincin ku maida kwalamarku Mayu kawai..." Yana kai nan ya nufi kofa Dariya suke yi Faisal yace "eh mun ji, wlh ko me zaka faɗa se mun zo mun kwashi gara ah to" Yana murmushin zancen ya karasa mota ya shiga ya dawo gidan. Boyeyyen ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take ta ba husna abinci a baki suna hira da dariya da yarinyar, ta bashi tsananin mamaki guda biyu a yau Na farko be taɓa kawo zata girka abincin da ya kai wannan daaɗi ba don ze iya rantsuwa bayan abincin mammi be taɓa cin abinci me daaɗin wannan ba, se kuma abu na biyu yadda ta tarbi su Faahim be taɓa zaton tana son mutane har ta ja su a jiki haka ba duba da yadda duk inda ta zauna se an samu hatsaniya da ita, kannenta karan kansu ba son zama kusa da ita suke ba don masifa da saurin hannu amma ji ta yadda take yi da su fadyaa ko don ta kwana biyu bata ga mutane bane? Har suka gama cin abincin suka cika cikinsu da zobo be Daena mamaki ba, tattare kayan suke ita da fadyaa da ta mike tana taya ta suka yi kasa suka Barsu su biyu, don yaran sun biyo bayansu, wanke wanke Fauza ke yi fadyaa na daurayewa suna ƴar hira tsakaninsu. Sun gama suna shirin haurawa saman kenan se ga Fatima, sake fuska tayi tace "ya fadyaa kune a gidan ashe?" Fadyaa tace "eh wlh Fatima mun zo kin fita" "eh na ɗan je na ga doctor na ne, Alhamdulillah kuma da sakamako me kyau na dawo" Fadyaa na murmushi tace "masha Allah, Allah ya jishe mu alkhairi" Dukda ta so Fadyan ta tambayeta menene don ciki ne da ita na sati biyu kachal amma har ta bazawa mutane tana faɗin a taya ta da Adu'a, wai ko Adu'a ne ba'a yiwa cikin yasa baya zama ga saurin conceiving da take dashi. Duk haurowa suka yi kanzil be Haɗa su da fauza ba, ta gaida Faahim ta shiga cikin su ganin Faizan be nuna komai a fuska kaman yadda ya Rufeta da faɗa a waya ba. Har suka yi la'asar a gidan still Fauza taje ta dafo musu shayi sak irin wadda mammi kan yi mishi itama kuma wurin jadda ta koya don Baba prof na matukar so kaman yadda shima yake so, be taɓa sanin ta iya something like this ba, ya sha shayin sossai don kusan abunda yake matukar kewa kenan a duk sadda aka ce yayi nisa da yola. Se dab magrib suka rako su zasu wuce Dukda Fauza ta so su zauna se dare amma akwai inda Faahim ze je kuma ze iya kai dare sossai shiyasa ba zae Barsu yaje ya dawo ba, husna kam kin bin su tayi Fauza na murmushi tace "yauwa ƴar gidana, ya fadyaa ku hado driver kawai da kayanta pls" Duk dariya suka yi ganin yadda take ta murna daga ita har husnan, sallama suka yi musu suk fice da nufin za'a aiko mata da kayanta. Tun a parlorn kasan Faizan ya dubi Fatima yace "Ashe kina fita daga gidan nan ba tare da izini na ba? A iya sanina baki da lectures yau kuma na barki kina bacci" "Yaya kayi hakuri wlh bayan fitan ka ne amai da juya ya matsa min nayi ta kiran ka kuma ban sameka ba shine na tafi ganin likita" Ta faɗa a marairaice. "Amma ya kamata ko Fauziyya ki sanarwa da zaki fita ba wai kawai ki fita kiyi tafiyar ki ba" Ta Yi saurin cewa "da ka dawo bata gaya maka ba? Na fa ce mata in ka dawo ta taimaka ta faɗa maka wallahi" Fauza da tayi nisa a kan stairs ta dakata tare da juyowa da mamakin rantsuwar da Fatiman ke yi a kan karya, ganin kallon tuhumar da yake aika mata yasa tace "kayi hakuri mancewa nayi" Daga haka bata tsaya ba tayi wucewarta, a ɗakinta suka yi sallah da husna nan suka shiririce a kallo tana kuma sauraran surutun husna don husna akwai aikin surutu. A ranar dae ba'a samu an kawo mata kayanta ba se wani shirt nata dogo ta sanya mata ya kuwa zauna mata suka je kitchen suka dafa pasta ɗan kaɗan a ƙasan suka ci kan suka hauro sama zuwa ɗakin Fauza.. Har sun yi shirin kwanciya don tana sanye da pjamas fari me layi layin baƙi me yauƙi wando da riga ya zauna mata sossai kanta ba dankwali tana kara kakkabe musu shimfiɗa ya shigo da sallama. "Oyoyo uncle" Husna ta karasa ta rungume shi "oyoyo babyn uncle" Hannunta ya kama suka zauna ya ɗan kalli Fauza da ta gama gyara gadon ta zauna daga baki tana wasa da nails ɗinta yace "kin ci abinci?" Kai ta gyaɗa tace "Aunty Fauza ta yi mana pasta me daaɗi mun ci, it was so yummy uncle kaima ka ci ka ji ko?" Girgiza kai yayi yace "ban ci ba baby husny amma zan ci" "babu wata matsala ko?" Ya jefa tambayar ga Fauza. Kai ta girgiza tace "babu" Sakin hannun husna yayi yace "OK, baby go nd sleep karki manta da Adu'a" Tace "ok uncle" Da gudu taje ta hau gadon ta zauna tare da Haɗa hannayenta wai tana Adu'a, murmushi duk suka yi na wayon yarinyar. Miƙewa yayi ya sanya hannunshi duka biyu cikin aljihu yace "madam ina wayata?" Tace "oh, yi hakuri ina ta zuci zucin baka na mance" Tahowa tayi wurin kujerun ta ɗauka a inda ya tashi ta san ya gani ko me ya hana shi ɗauka se ya sakata zuwa ɗauka ta mika mai hanu da hanu oho mishi. Karɓa kawai yayi ya juya, kaman tace mishi saida safe amma tana tsoron dizginshi har ya fice ta rage wutan ta dawo ta hau gadon ta kwanta tare da lumshe idanu tana tuna yinin ta na yau, se kuma ta tuna bata goge hotunan da ta ɗauka ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da taɓe baki ta gyara kwanciyarta. Shi kuwa yana komawa ɗakinshi Fatima na shiga da shirin bacci, farin takarda ta mika mai tana murmushi, karɓa yayi ya buɗe a take shima fuskanshi ta cika da murmushi Dukda be kwallafa rai ba sanin cikinta baya zama amma shima yana son ganin gudan jininshi kaman yadda kannenshi kusan duk suke da nasu. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ya sa wannan me zama ne fatee" Tace "in shaa Allahu Ameen" Nan ta zauna tana gayamishi yadda Dr yace ta kula da cikin don kar a samu matsala, bayan ya gama sauraron ta ta kwanta shi kuma ya zauna tare da jingina bayanshi da gadon airpod ne a kunnenshi take ya shiga wani wuri a wayan yayi connecting ya sake komawa wani wuri ya fara duba voice recording guda biyar da ya gani. Ba wai yana ghosting ɗinta bane, kawai natsuwarshi har yanzu be kama a kanta ba yana tsoron halinta na baya sossai shiyasa ya zame mishi dole saka idanu a duk al'amuranta. Wayansu da jadda ya fara saurara, sossai yayi murmushi jin yadda suka drama a kanshi, yadda Fauzan ta zage take ta bada jawabi akan duk abunda jadda ta faɗa mata an yi a gidan yayi ta bashi dariya, bayan ya gama ya saurari nata da mammi, kaɗan yaji darajarta a zuciyarshi jin duk ta yadda mammi ta so taji laifinshi daga gareta ta tare. "Ashe tana da hankali" Fatima da ta fara bacci tace "Na'am?" Yace "no yi baccinki maman baby" Murmushi tayi kan ta sake runtse idanu cikin jin daaɗin sunan da ya kirata dashi. Shi kuwa cigaba da sauraron Hirar ta yayi da Baba prof,, ya san tunda baba prof yace hakan dole ze fara mata shirye shiryen makarantar babu yadda ya iya. Hiran ta da Ammi ne na karshe da yaji shi ya saka shi yin shiru ya tafi nazari, duk yadda yake Tunanin Ammin na ƙin shi ya wuce nan, kuma shi tun tashin shi ba ze ce ga abunda ya taɓa yi mata har ta tsane shi ba, akwai shakuwa me yawa tsakanin shi da fadeela sbd da kaɗan ya girmeta, yana sonta sossai matsayin kanwarshi ya kan je sashen Ammin a lokacin don wasa da fadeela saide yana iya tunawa vividly yadda baya barin sashen se da kuka, har ya girma yayi wayau Ammi bata taɓa kaunar shi ba, gashi yanzu ya auri ƴarta. Fita yayi yana shirin kashe wayan hannunshi ya danna gallery, Jan kalar riganta ne ya saka shi sake kallon hotunan da suke jeren, hannu ya sa ya danna ɗaya, dariya ne ya kama shi ganin yadda ta tura baki wai ita nan tana style amma tayi kyau ba laifi, kallon hotunan yake yana dariya marar sauti daga karshe bayan ya gama ya girgiza kai yace "this girl is crazy" Ajiye wayan yayi ya kwanta tare da lumshe idanu bacci ya sureshi. Washegari da safe aka kawowa husna kayanta, duk inda zata Fauza zata ajiye kafa husna na biye da ita, ga surutu tun tana amsawa har ta gaji, yamma likis husna tace se sun yi game. "Toh faɗi wadda kike so se ayi" Fauza ta faɗa don ta addabe ta da maganan game ɗin nan Husna tace "muyi wasan ɓuya Aunty" Dankwalinta ta cire ta daurewa husnar suka hau wasan ɓuya duk sun cika ɗakin da hargowa Dukda su biyu ne kachal, bayan husna ta kamata da rigima da satar kallo itama aka ɗaura mata ta fara laluben husna.. Sam bata ji sallamarshi ba se jin mutum tayi da hanzari ta cabki hannunshi tana cewa "yeeeeeyyyy wa na kama...?" Dib dariyar ta ya ɗauke jin taushi da sanyin hannun ba na husna bane, da sauri ta zare kyallen dankwalin tana Kallonshi kaman yadda shima yake kallonta... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 20 Ihun da husna ta sa na yeeey an kama uncle shine ya dawo dasu daga wata duniyar da suka tafi, da sauri ta matsa baya tana saukar da kanta ƙasa, shi kam basarwa yayi ya riƙe husna dake cewa shima a ɗaura mishi yayi tunda an kama shi yace "A'a husny zan yi amma Ba yau ba, baki ga yanzu na dawo ba?" Tace cikin yarantarta "eh uncle, ina tsarabata?" Ya kalli Fauxa yace "Auntynki ta zo ta karɓa miki" Yana kai nan ya juya ya fice. Husna taje da gudu wurin Fauza tace "Aunty fauza uncle wai ki je ki karɓa min tsarabata" Fauza tace "Toh husna" Husna tace "Aunty in kallo MBC kan ki dawo?" Kai kawai Fauza ta ɗaga, kan ta ɗauki hijab ɗin sallarta ta zura tare da fitowa, baya parlorn don haka ɗakinshi ta wuce tayi knocking aka bata izinin shiga. Ta tura a hankali ta shiga, this is the first Time da ta shigo ɗakin, tsaruwa da haduwar ɗakin ya tafi da ita kasancewar shi me son fari hakan yasa komai na ɗakin fari ne, sossai tsarin rashin hayaniyar ɗakin yayi mata kyau, a kan kujera yake zaune ya tankwashe kafa, hannunshi wani daily trust ne yana dubawa. Ta ɗan rusuna tace "ga ni yaya" Da hannu ya mata nuni da ledojin da suke kan table wadda Fatima ce ta ajiye ta je kuma ɗauko plates da sauran abubuwan da zasu yi anfani dashi ne, yace "Ki dauka muku ɗaya" Tace "An gode Allah ya saka da alkhairi" Se a lokacin ya ɗago yana kallon face ɗinta da ya fito fess a onion hijab ɗin nata, daidai lokacin kuma Fatima ta shigo ɗakina gabanta ne yayi wani irin faɗuwa wadda seda cikinta ya nemi kullewa, a makogoronta taji wani abu ya tiƙe ta me take yi a ɗakin nan? Ta tambayi kanta kan ta karasa daidai lokacin ita kuma Fauza ta ɗauka ta juyo. Da wani irin banzan kallo Fatima ke bin ta, ta san duk sbd wannan Husnan nan ne har Fauzan ta samu shigowa ɗakin mijinta, daga yarinyar har Fauza ji take kaman taje ta sa musu wuta a ɗakin su mutu, sbd yanzu bayan shigan asuban shi duk in ya dawo se ya shiga, gashi Faizan mutum ne da babu fuskan kawo mai wargi ko tace zata hana shi abunda yayi niyya, gaskiya bazata iya hakuri ba kaman yadda take aika mata da harara haka itama ta rama tare da jan tsiririn tsaki wadda ya sake hasala Fatima har bata san ta furta "kan uba!" Ɗagowa Faizan yayi yace "lafiya?" "Baby yarinyar nan wai ta buge ni kuma ko sannu babu tayi wucewarta?" Yace "Fauza?" Haushin kiran sunan tan ma ya sake mamaye ta tace "ita fa" Shi har ya manta da ainihin halinta don yanzu yana ganin babu shiru shiru irin ta, sannan ga saurin bada hakuri wadda wannan na daga cikin abunda yasa tunda ta zo gidan faɗa me tsayi be taɓa hada su ba don duk ɓacin ranshi da zaran ka ce mishi yi hakuri shikenan, fauza bata san shi ba bare ta san lagon shi. "Tunda har ta fita bata sani bane na san da ta baki haƙuri, yunwa nake ji zo yi serving ɗina" Wani haushi ne ya sake turnike Fatima, yau Faizan ke kare Fauza? A kufule tayi serving ɗinshi ta mike yana tambayarta bazaki ci bane? Ko bata juya ba tayi ficewarta, girgiza kai yayi yana mamakin halayyar da take nuna mishi tun daga shigowanta gidan, tabbas ba don shi jajirceccen namiji bane da se abunda Fatima tace a gidan za'a yi, ita in har ba'a yi ra'ayinta ba tayi ta fushi kenan tana kumbure kumbure? Abincin shi ya ci ya koshi ya wuce toilet yayi brush da wanka ya zo ya sauya zuwa kayan bacci, kwanukan ya fitar da sauran abubuwan makulashen da ya sayon ya kai fridge ɗin kitchen, daga nan ya wuce ɗakinta ya samu wai har ta kwanta be tanka mata ba ya fito ya nufi ɗakin Fauza. Suma ya sa mu sun kwanta kuma har ma sun yi bacci, fitowa yayi kawai ya koma dakinshi ya kwanta shima don yana da flight 8 zashi Lagos amma around 9 na dare ze dawo.. Washegari yana idar da sallah yayi sauri ya watsa ruwa ya shirya kan ya fice bayan ya leƙa Fatima da bata tashi Bama, don ita wai don ze yi tafiyar sassafe ta samar mai abinci bata san wannan ba sede in yaje airport ya karya a chan kan ya wuce, be damu ba sbd dama chan haka yake yi. Tana jin fitan motan shi ta mike zaune, tare da sauka daga gadon dama tayi wanka kawai ta saka kaya ta yafa gyalen ta ta fito, tun wata biyun farkon aurensu ya koya mata mota kuma ya saya mata wata karamar Hyundai, direct kitchen na sama taje ta rufe da key, ta sauƙa kasa ma ta rufe ta haɗe keyn ta watsa jaka kan tayi ficewarta daga gidan. Bayan su Fauza sun tashi tayiwa husna wanka itama tayi suka gyara gidan tare duk bata lura kitchen a rufe ba se bayan ta gama taje ta murɗa kofan ta ji shi a rufe, kitchen na sama ta dawo taji a rufe, da mamaki take kallon kofan kan ta wuce kofan Fatima ta murɗa shima a rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta kama hannun Husna suka koma ɗakinta da Tunanin Fatima ba nisa tayi ba Dukda dae ita bata taɓa gani an rufe kitchen ɗin ba duk zamanta a gidan. Sauran kazan jiya ta turawa husna da Admiral 'A Dukda yayi sanyi sossai haka dae ta lallaɓa husnan ta ci, bata san lokacin da zasu dawo ba hakan yasa bata ci ba ita gudun kar kuma basu shigo da wuri ba husna ta sake jin yunwa. Wasa wasa har azahar babu wadda ya dawo a cikinsu gashi lokacin yunwa ya fara kama Fauza da babu abunda ta saka a cikinta, sauran kazan ta sake baiwa husna ta cinye. Tun suna kallo har taji bazata iya cigaba da kallon ba sbd yunwa da yake shirin yi mata illa, bayan sun yi la'asar ta duba jakanta ta fiddo kuɗin da Jaddah ta sanya mata ciki tun randa za'a kawo ta tare da sanya hijab ta kama hannun husna suka fito, saide me gadin wadda yoruba ne yace mata oganshi ya mishi umurni kar ya barta ta fita daga gidan ba tare da izininshi ba. Rokon shi ta fara saide tsoron rasa aikinshi yasa be kula ta ba, don Sam be san ita ɗin matar Faizan bace ba ma, haka suka hakura ganin tsayuwar baze yi musu ba suka koma ciki amma fa ganin magrib yayi ga dukkansu biyu yanzu sun jikkata don husna har ta fara kuka yasa ta sake fitowa ta roke shi ko ze kira mata ogan nashi da Wayanshi don ta san dae duk muguntar Fauzan in har ita ze iya mata to baze iya yiwa ɗiyar kaninshi ba, unfortunately layinshi baya wucewa. Haka suka sake dawowa parlorn kasan tana jin yadda ƙasan cikinta ya riƙe kam kam kaman zata mutu, daurewa take tana rarrashin husna da yanzu ta fara kiran iyayenta se tausayin yarinyar ya kama ta, fita tayi ta fara duba gidan, ba irin gidansu bane bare ta iya zamewa ta fita, ba kuma zata iya faɗawa me gadi abinci babu zata je su saya ba sbd ta san hakan kaman wani tonon asiri ne ga Faizan wadda be kamata gida kaman nashi ace babu abinci ba me gadin ma ba yarda ze yi ba. Hawaye ne ya gangaro mata ta sa hannu ta share, bata da waya bare tayi order a kawo mata har gida. Komawa sama tayi zuwa dakinshi banda sassanyar kamshi shi babu abunda yake tashi, duk irin dubawar da zata yi bata samu wayan da ya ara mata jiyan ba. Kuma Sam bata kula da lockers ɗin gefen fridge ba waenda snacks ne a ciki da su dangin cereals tunda ta san ita nata babu komai ciki. A ƙasa ta saka gwiwowinta ta ɗaura kanta a kan gadon hannunta dafe da mararta dake wani irin kugi, husna ce ta biyo ta tana kuka sossai ita tana jin yunwa, miƙewa tayi ta kama ta tace "mu je mu yi isha se mu koma ko mai gadin ze yarda mu fita" Komawa ɗakinta suka yi ta bar ɗankwalinta anan a ɗakinta suka yi sallah shima ba natsuwa, ko da suka sake fitowa neman yiwa mai gadin bayani take saide be kula ta ba, masifa zata fara mishi saide bata da karfin hakan kasancewar bata bar ko ruwa ne ya shiga cikinta ba. Rarrashin husna kawai take suna tsaye kaman marayu se suka ji horn, da sauri me gadin ya karasa ya duba ganin oganshi ne yasa yayi hanzarin wangale gate ɗin. Wutar motar shi ne ya haske mishi su yadda suke tsayen yasa gabanshi faɗuwa. "Peter, me ya kawosu bakin gate?" Peter yace "Sir tun da afternoon suke ta so su fita kuma ka ce kar in yarda in bar kowa fita bayan madame, ta sakani nayi ta kiran phone naka saide baya shiga sir" Ganin hawaye a fuskokinsu duk su biyu ya sa ya san ba lafiya ba, da hanzari ya karasa da motan tare da buɗewa ya fito yana kallon su yace "Fauziyya lafiya? Me kuke yi a nan? Ina Zaku je?" Kasa magana tayi se hawaye, da gudu husna taje ta rungume shi tana cewa "uncle yunwa muke ji, tun safe Aunty bata ci komai ba nima sauran kazan da ka sayo mana jiya tayi ta bani kuma ya kare nima na fara jin yunwa, gateman kuma ya hana mu fita mu sayi abinci... Ina ta kuka amma Aunty tana ta rarrashina dukda itama tana kukan bata so na gani" Wani irin yanayi marar misaltuwa ya shiga, yana rike da yarinyar yace "yunwa? Fauziyya?? Me ya samu kayan abincin gidan?" Kanta ƙasa tace a hankali "tun da muka tashi suke rufe" Kokarin controlling bacin ran da ya shiga yake yace "Fatima fa?" "Itama mun tashi bamu sameta ba" Ze yi magana se ga knocking na Fatima, me gadi yaje ya buɗe ta shigo tana ganin Fauzan tace ."Oh baby ashe ka dawo? Ina ta kiranka tun six bana samunka, ka ga ban dawo da wuri ba ko? Wlh na fito lectures 6 mota na ya lalace masu gyara suka ta ɓata min lokaci yanzu haka ma na bar musu ne na biyo bo....." "Fatimaaaa!" Ya daka mata tsawa muryarshi with so much anger yace "me ya rufe kitchens ɗin gidana tun safe?" Zata yi magana ya sake daka mata tsawa "don't you dare lie to me, me yasa kika rufe kitchen kika tafi da keys alhali kin san akwai mutane a gidan? Kisa kike son yi? Fatima a gidana har a yini da yunwa??" Kuka ta fashe dashi tana rasa abun faɗa don kwakwalwanta rasa irin karyar da zata yi tayi, in ina ta fara daga yadda fuskanshi yayi turning red ka san ranshi ya kai makurar ɓaci. Kallon Fauza da bata sake Kallonsu ba yayi yace "Fauziyya shiga mota muje" Wucewa Fauza tayi ta buɗe back seat ɗin motan shi ta zauna yayinda yake rike da hannun husna yana nuna Fatima da hannu wacce ta fara cewa "A'a ina zakuje? Ga fa keys ɗin na dawo dasu..." "Ki tabbatar kin tanadi furucin kare kanki a gareni kan in dawo don wallahi wallahi ranki se yayi mummunan ɓaci akan wannan abunda kika aikata, ko babu aure Fauziyya da husna sun fi karfin yunwa a gidana Fatima..." Yana kai nan ya zagaye da husna ya buɗe mata gaba ta shiga, ya dawo side ɗin driver ya ja motar ya fice da gudu. Hannu Fatima ta ɗaura a kai tace "na shiga uku!" Da gudu tayi cikin gidan don kiran Auntyn ta ta nemi mafita kan ya dawo, garin neman gira tana shirin rasa idanu, ita da ya kamata ta nisanta su gashi tana shirin kawo kusanci tsakaninsu, ina zasu je? Me zasu je suyi? Shine kawai tambayar dake ta mata kai kawo. Driving yake yana sauraron sheshekar kukan da fauza ke yi, husna ganin Fauza bazata yi shiru ba yasa itama ta fara kuka tana waigawa ta kalli Fauza da ta ɗaura fuskanta a tafin hannunta ta kuma kwantar bisa cinyar ta tace "Aunty yunwa kike ji ko? Kiyi haƙuri yanzu zamu je mu ci abinci ko uncle?" Shima Fauzan yake kallo a kai a kai ya gyaɗa kai yace "in shaa Allah Husna" Restaurant mafi kusa ya kaisu, husna na fita ya zagaye ya buɗe mata kofan. A hankali ta sanya kafa ta fito yace "kukan nan shi ze kosar dake ne?" Bata tanka shi ba suka nufi ciki tana tafiya a hankali sbd cikinta da ya kama, tea me zafi ya fara ordering Allah ya sa VIP ɗinsu room ne so in ka shiga babu me ganinka, suna shiga ta nufi zubewa yayi saurin tarota suka karasa kan lallausan shimfidun dake wurin ya ajiyeta ta zame ta kwanta, sake kiransu yayi a landline dake wurin cikin mintuna se gasu da shayi kan ya basu ordern abincin da zasu kawo musu. Da kanshi ya ɗagota ya miƙa mata shayin, kurbi biyu zuwa uku tayi se amai.. Da gudu ta karasa washing hand base dake wurin ta fara kwala amai, yana riƙe da kafadanta hannunshi ɗaya na shafa bayanta cikin tsantsar tausayi yake furta "sorry! Sannu am so sorry" Daga ka ga aman ka san na wahala da yunwa ne, bayan ta gama suka sake dawowa ya bata tea ɗin ta sha, bayan ta shanye ya matsar mata da abincin da aka kawo ɗin tuwo ne da miyar vegetable, yatsina fuska tayi tana kallon tuwon, husna har tayi nisa a cin nata. "Bakya so?" Kai ta gyaɗa don ita bata son tuwo, janyewa yayi ya sake kiransu tana ta Kallonshi da idanunta da suka kara girma, yadda duk tausayinsu ya kasa boyuwa a fuskanshi kaman ze yi kuka, tambayarta yayi tace rice and stew with plantain. Nan take ya faɗa musu suka kawo. Zama yayi yana kallon yadda take cin abincin Dukda yunwa da take ji amma cin ba wani sauri ko hargagi a natse take kaiwa bakinta, ganin zata ɗago yasa ya ɗauke kai ya fara cin tuwon da taki ci ɗin. Ba su suka dawo gidan ba don ya biya dasu sahad sun sayi abubuwa snacks masu yawa dangin su biscuit da su drinks da kayan tea su custard da oat, golden morn, coco pops ba abunda be saya ba. Don anan ma yaga laifinshi da be ajiye musu abubuwa haka a ɗaki ba, tunda daga dakinshi har na Fatima akwai snacks da drinks kuma a fridge. Pizza da shawarma spot suka je ya sake saya musu kan suka nufi dawowa gida, duk abubuwan da yake yi ɗin sede suyi hira da husna amma ita kam tak bata ce ba, tana jingine da jikin motar daga karshe ma bacci ne ya kwashe ta. Ko da suka dawo gidan a gate ya tsaya ya cewa gate man ɗin ya janye maganan da ya faɗa duk sadda Fauza ta nemi fita ya barta ta fita. Daga haka suka karasa ciki, zata ɗauki kayan yace ta bari. Haka ta wuce ta Barsu da husna, bata ko kalli Fatima dake zaune a parlorn kasan ba ta haura abunta, kayanta kawai ta sauya ta kwanta akan gado sbd wani irin bacci da take ji. Shi kam dashi da Husna suka kwashi kayan zuwa sama saida ma yayi sawu biyu, da kanshi ya shirya abubuwan inda suka kamata, kan ya kama hannun husna suka yi ɗakinshi tana cin shawarma. "Yaya..!" Fatima ta kirashi ko kallonta be yi ba, tayi saurin binshi ɗaki ya juya ya daka mata wani hargitsatsen tsawa "get out of my sight tun baki sanya ni yin abunda zamu zo duka muna dana sani ba.." Zata sake magana yace "outt!" Ya sake daka mata tsawa, da sauri ta fice tana kuka. Duk abubuwan da ya kamata yayi yayi har wanka yayi ya sauya kaya kan lokacin husna tayi bacci, ɗaukanta yayi ya fito zuwa dakin Fauza. Saida ya sauya mata kaya kan ya nufi gadon da ita ya kwantar idanunshi kan Fauza dake bacci peacefully, Adu'a yayi musu kan ya fito. A hankali ta buɗe idanunta ta bi bayanshi da kallo har ya maida kofa ya rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta gyara kwanciyarta cikin nazarin yadda zata ci uban Fatima na abunda tayi mata... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 21 Kimanin sati biyu kenan da faruwar abunda ya faru amma ta lura har yanzu ba wani shiri suke yi da Fatima ba, ya bata key ɗin kitchen na ƙasan gabaɗaya sbd rashin zamanshi don sun koma aiki ka'in da na'in, bata shiga harkar Fatima da take ji kaman ta hadiye zuciya ta mutu sbd yadda Faizan ya ɗauki fushi da ita akan abunda take ganin be taka kara ya karya ba, ita da ya kamata yanzu ya tarairayeta ya bata kulawa. Ita dae Fauza tunda tana da husna bata da matsala don yarinyar na debe mata duk wani kewa, tare suke koman su cikin hira da dariya lokuta dayawa gani take kaman husnan sa'ar ta ce in gujel gujel ne ma duk haka suke zagewa su yi kayansu. Kaman yau a parlorn ƙasa suka yi la'asar sbd cookies da suke yi kar ya ƙone, bayan sun idar suka zuba shi a tray me kyau, da Homemade pineapple juice tayi musu har zasu haura dashi se husna tace "Aunty mu je garden pls you promised fa cewa weekend nan zamu je ni kam I want to play with swing" Fauza ta kalleta tace "ke kam kina da aiki mutum baya mantuwa? To mu je" Juyawa suka yi suka fito, daga hannun hagunsu akwai wani ƙofa suka shige sun ɗan yi tafiya kaɗan se ga garden ɗin masha Allah kore sharrr, akwai lilo sbd hutawa, gefen shi akwai table da chairs, nan ta ajiye snacks ɗin, suka je suka hau Lilon suna lilawa Fauza na tsoron juwa bata so da karfi amma da gangan husna ke wullawa da karfi wadda ke saka Fauza ihun kiran sunanta ita kuma ta watse da dariya. Zaune yake a balcony ɗinshi bayan ya dawo daga sallar la'asar sanye da farar jallabiya wacce bata kai kasa ba don kana iya hangen black trouser da ya sa daga ciki, fuskanshi yayi wasai yayi wani irin kyau, dariyar su da kuma ƙarar Fauza shi ya saka shi miƙewa tsaye, chan ya hange su suna ta lilo, lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan tray ɗin dake gefensu, ba karya his tongue have been craving for the tatse of her food again barin ma tea ɗin nan da sati biyu kenan da yake so yace ta mishi yana fuskewa. Jaridar ya ɗauka ya koma ɗakinshi ya buɗe kofa ya sauƙa ƙasa, a natse yake tafiya cikin ƙasaitacciyar tafiyar shi da already ya zamar mishi jiki ya isa garden ɗin. "Husna bari! Bar lilawa hakanan jiri ze yarda ni" Ta faɗa tana runtse da idanu, husna kam ina ruwanta ta maida kafafunta baya ta cilla da karfi daidai ta buɗe idanunta ita kuma ta hantsila tana shirin faɗuwa yayi azamar tare ta duk idanu suka zubawa juna.. Da sauri kuma ta miƙe tsaye tana gyara ɗan kwalinta da ya zame ya bayyana baƙi sidik ɗin gashinta da ta tsefe kitson bukin ta ta tufke saboda ihun da husna tayi na "Uncle zo ka hau lilo tunda Aunty na tsoro.." Ta faɗa tana wangale mishi wawulonta, murmushi yayi yace "zan zo babyn uncle amma yanzu cigaba da abun ki ke kam" Ya karashe yana zama akan chairs ɗin wurin tare da crossing kafanshi, duburcewan da tayi yake kallo ƙasa ƙasa duk in yana wuri sakewarta ba sossai ba don tun sati biyu da in har yana gari ya kan shiga sau biyu ya duba su ya lura da hakan musamman idan husna ta rike shi da surutu ya ɗan jima se ta rasa natsuwa. Juyawa kawai tayi tana cewa husna "in kin gama se ki dawo ɗaki" Har ta juya ta ji sassanyar muryarshi me cike da natsuwa ya ce "Ji mana..!" Baki ta tura tace a ranta se kace wata budurwa da ake shirin tarewa a titi. Juyowa tayi bayan ta gyara bakin da ta turon tace "Na'am" Yace yana kallonta kai tsaye wadda har tsikar jikinta take jin kallon "Ni dodo ne da in na zo wuri kike guduwa?" Bakin ta sake turowa tana cewa a ranta "ai ka fi dodon ma razanarwa, in ka so kayi kirki in ka so ka tabka tsiya ko a gyalenka" A fili kuma tace "A'a kawai ina da abunda zan yi ne a cikin" Yace "ok, before then zan samu shayi?" Kai ta gyaɗa mishi kan ta juya ta fice, cookies ɗin ya ɗau ɗaya ya sa a baki yana mamakin yadda ta iya abubuwa haka masu daaɗi. Cikin mintuna da basu fi ashirin ba ta dawo da tray me ɗauke da karamin glass tea flask da cups ɗinshi a jere a gefe, a gabanshi ta ajiye tana kallon yadda yayi nisa a cin cookies ɗin nata. A ranta tace "ko tayi ba'a yiwa mutum ba ya zage ya cinye mana abunmu" Kaman kuwa ya san me take cewa yace "daina min kallon ba'a gayyaceni ba na ci, ladan kati na da kika ƙarar ranan ne" Wara idanu tayi a kanshi yana tsiyaya tea ɗin a cup bayan ya gama ya ɗago yace "yes" Ta langwabe kai tace "to Ayya in sake maka cookies ɗin ka bani in sake waya dasu? Bana jin daaɗi yadda na kwana biyu ban ji su ba" Yace "no bana son wannan, wani abu daban nake so" Ta Yi saurin cewa "menene?" "Zaki dinga dafa min wannan tea ɗin kullum" Da saurinta tace "eh na yarda" Murmushi ya saki wadda ya sakata kusan shagala da Kallonshi yace "wayan na sama in mun haura zan baki" Tsallen murna tayi tana cewa ta gode, kallon da yake mata yasa ta natsu ta juya ta wuce cikin don bazata iya zama a inuwa ɗaya dashi ba Sam bata iya sakewa. Kaman yadda yayi alkawari bayan sun hauro da Husna ya bata ta kai mata, taji daaɗi sossai amma ta ji haushi da ta duba taga ya goge hotunan da tayi a wayan kuma da gayya ne tunda ga na matarshi da nashi na ciki nata ne ya goge, a daren suka sha hira da jadda har da su fa'iza da faaazila sun gaisa sbd tayi kewarsu. Mammi ma sun jima suna waya kan ta ba husna ma ta ishe ta da surutu, bayan sun gama ta bata wayan ta maida mishi. Tun daga wannan rana kullum da safe da dare kaman ka'ida se tayi mishi tea ɗin nan, yawanci tana samun shi ko a dining ko a parlor ta ajiye mai, sadda Fatima tayi noticing kusan hauka ta saka mishi ai ba bata iya bane be ce yana so bane, shi kuwa namijin duniya kai tsaye ya ce mata na hannun Fauza yake so ba nata ba shiyasa be tambayeta ba, tayi kukan maganan nan, kudirinta da haushinta kan Fauziyya kuma ya ƙaru, dukda Auntyn ta tayi fushi me girma da ita sbd abunda tayi kwanaki tace ya so lalata musu aiki don in ta bari Faizan ya fara tausayawa Fauza so ze iya shiga idan kuma so ya shiga tabbas ze saka alamar tambaya akan son da yake yi mata ita. Ta dawo daga lectures tana haurowa suka kusa cin karo da fauza dake shirin sauƙa da kayan tea ɗinshi da yanzu kenan ya gama sha take shirin sauka dashi, tare ta Fatima tayi. Matsawa tayi zata bi ta gefe ta sake tare gefen, tana kallonta tace "Fauza me kike nufi da mijina?" Har kaman bazata amsa ba se kuma tace "me kuwa nake nufi? Last time da na bincika duniya sun sheda Cewar matan Faizan biyu ne, ko kunnuwanki sun toshe ne a sadda amsa kuwwa ke bayyana cewa an shafa Fatiha fauza ta zama ta Faizan?" Wani irin takaici ne ya zowa Fatima wuya "ke har kin kai macen da zaki yi ikirari namiji kamille irin Faizan ze so ki? Sauran wasu ce fa da sauran shaye sha...." "Shhhhhhhhh" Fauza ta faɗi tana sa mata hannu a lips ɗinta tace "wannan kuma tsakaninmu ne kin gane ko? So kiyi ta kanki gwara ni ban bi hanyoyi masu yawa da haramci wurin mallakarshi ba, ban kuma zauna na ɓata hawayena wurin kukan in ban same shi ba zan mut....." Ɗaga hannu Fatima tayi zata mareta tayi saurin tarewa wadda ya saka tray ɗin hannunta faɗuwa ya fashe tartsatsa, hannun Fatima ta cillar wadda ya sakata loosing balance ta tafi suuuu tana kwala ƙara. Razanar da tayi yasa Dukda bata faɗi kan cikinta ba cikin ya ƙulle har jini ya balle mata, Da sauri ya karaso yana ambaton innalillahi wainna ilahi rajiun, Fauza ta buɗe baki zata mishi magana ya ɗauke ta da wani irin mari wadda ya sakata yin baya kafanta na dama ya sauƙa a kan glass da ya fashe a wurin, runtse idanuta tayi da karfi tana jin zafafan maganganun da yake jefanta dasu. Bata buɗe ba har ya sauka ya kama Fatima dake kuka haikan sbd baƙin ciki don ta san wannan ciki kam se wani ikon Allah suka fice daga gidan da hanzari. Ilai kuwa Fatima ta rasa cikin tayi kuka har kaman ba gobe, likitan ya tabbatar musu da cewa mahaifanta is weak already shiyasa abu kaɗan ya iya ɓarar da cikin, haka ta saka shi a gaba tayi ta kuka wadda ya saka tausayinta kama zuciyarshi, Baba prof ya kira ya sanar mai da ɓarin. Ko da ya tambaya ta yaya hakan ya faru cewa yayi haka Allah ya tsara wadda kai tsaye Fatima ta dakatar da kukan tana kallon shi tace "Haka Allah ya tsara fa kace yaya? Ko kuma Fauza ce ta zubar min da shi?" Be so baba prof ya ji ba sede a yadda tayi maganan dole ya ji, tambayar shi yayi ya hakan ya faru? Taya Fauza zata zubar mata da ciki? A gaban jadda da Baba Alhj yake amsa wayan wadda duk hankalinsu ya koma kanshi jin wani sabon zance. Yace "Baba ban san me ya hada su ba na fito daidai lokacin da Fauziyyar ta hankaɗa hannunta wadda ya saka kafafunta gaucewa kasancewar tsaye take a kan stairs hakan ya saka ta faɗi amma bata faɗi kan cikin ba tsoratar da tayi ne ya saka cikin ɓarewa" Kuka me karfi ta saka tana cewa yana shirin baiwa Fauza kariya bayan ya gani kiri kiri ita ta turo ta ta faɗi, yadda take ta maganganu har take nema ta wuce layi yasa baba prof yace ya bata wayan amma shima bata wani saurare shi ba sbd kuka da take tayi. Allura kawai Faizan ya sa aka mata a take bacci ya ɗauke ta, Baba prof ya tambayi ina Fauza? Se a lokacin Marin da yayi mata ya dawo mai, lumshe idanunshi yayi yana ɗan sauke numfashi yace "tana gida baba" Baba yace "To ka tabbatar baka yanke hukunci cikin fushi ba, ka zauna kaji both side da yadda komai ya faru, abunda ya faru ya riga ya faru fushi ko hatsaniya ba ze dawo dashi ba, in har ka gama sulhunta gidan ka se ka Haɗani da Fauziyya ɗin" Ya amsa a ladabce. Baba Alhj yace "tayi wani abu kuma ko?" Baba prof yace "tayi, amma wannan tsakaninsu ne, ba zamu saka baki ba sbd idan muka zama masu saka idanu da yawan magana akan rayuwar gidanshi to lallai zuciyarshi zata mace, mu zuba idanu kawai ya gyara gidanshi da kanshi idan ba ya nemi mu shigan bane babu anfanin shigan" Duk sun gamsu da hakan prof mutum ne me hange sossai, sun fahimci dalilin shi na yin hakan don duk sauran yaran nashi ba idanu yake saka musu a Gidajensu ba Idan har ba sun zo gabanshi bane da matsala so na me ze saka akan su Faizan? A ta ɓangaren shi kuma ya jima zaune zuciyarshi babu daaɗi, dukda be kwallafa rai a kan cikin ba amma akwai zafi ace ka rasa gudan jininka da kake fatan gani a duniya, abunda kuma ya fi bashi haushi yadda sautin Marin da yayi mata ya kasa barin kwalwanshi a kuma ranshi yake jin zafin hakan. Mikewa yayi ya nemi izinin tafiya zuwa anjima ze dawo su kula da ita sossai pls, Dr yace ba damuwa ba ma lallai ta tashi yanzu ba don allurar ze jima yana aiki sbd bata samun cikakken hutawar ruhi dama chan. A hankali yake murza sitiyarin motar yana amsa wayan Jafar a kasalance, yana faɗa mishi matarshi na asibitinsu tayi miscarriage, tausayinshi yasa Jafar yayi ta bashi baki murmushi kawai yake ɗan yi yana furta ba komai haka Allah ya tsara. Bayan ya kashe be fi mintuna biyar ba se ga kiran Faisal wadda shi kuma lecturer ne a makarantar su Fatima, shima cikin tausayawa don a cikin abokanansu Faizan ne kaɗai be da yaro ko yarinya wacce zata kai shekaru bakwai sbd be yi aure da wuri ba, bayan yayi auren ma ga wani matsala nan na ɓarewar ciki. Shima dai nuna mishi yayi haka Allah ya tsara. A harabar gidan yayi parking ya sauka yana karewa gidan kallo kaman sabo ne a idanunshi, kofan motan kawai ya tura ya nufi ciki, a stairs na karshe ya tsaya yana kallon broken glasses dake zube a wurin, gabanshi ne ya faɗi ganin jini me yawa da har ya soma bushewa a wurin. Da idanu yabi ɗigon ɗigon da jinin ya bi se ya kare kan kofar ta, yana haurawa husna dake zaune jugum ta tashi ta zo wurinshi da gudu kaman zata yi kuka tace "uncle na tashi bacci na samu Aunty tana ta kuka daga karshe ma ta koreni tace in zo in kalli MBC waye ya daketa?" Shafa kan yarinyar yayi yace "Babu, na san ma ta daina husna je ki kalli cartoon ɗin bari na duba ta" A hankali ya buɗe kofan ɗakin nata ya sanya kai ciki, jinin ya diga har gaban gadonta, tana kwance rub da ciki kafan na daga ƙasa ɗauke da kwalba me girma jini se diga yake har lokacin amma ita kam kuka kawai take yi, ita kanta ta rasa wannan kuka da take yi don tana da taurin zuciya ta rasa yadda aka yi abunda Faizan ya mata yayi mata zafi sossai da sossai. "Subhanallah! Fauziyya?" Ya ambaci sunanta yana riƙe kafan, zare kafan tayi daga hannunshi ta maida gefe tana me cigaba da kukanta, sake riƙe kafan yayi ta sake zamewa, guwiwanshi ɗaya ya saka kan gadon ya mirginota tare da ɗaga ta zaune se ta kara sautin kukanta cewa yake "baki da hankali ne zaki zauna jininki na ta diga haka a ƙasa in ya kare fa?" Ba tare da ta kalleshi ba tace "se in mutu kowa ya huta tunda dama an tsane ni....." Cakkk magananta ya tsaya jin ya sungumeta gabaɗayanta tayi hanzarin saka hannayenta ta zagaye wuyanshi gudun kar ta faɗi.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 22 Yana kallon tsakiyar idanunta da suka kumbura don kuka yace "kika sake cewa tak zan sake ki ki faɗi se ki san ba'a sonki an tsaneki da kyau.." Haushi maganan ya bata kawai ta sake sakar mishi kuka, idanunshi ya runtse kawai ya juya da ita a hannunshi suka nufi kofa. "Baby taso ki zo" Ya kira husna, da gudu ta bisu ita ce ta buɗe mishi kofa ya sanya Fauziyyan, ta shiga baya ita kuma, ya zagaye ya shiga ya ja tare da ficewa daga gidan, minti minti yake kallonta har suka isa asibiti bata bar kukan da take yi ɗin ba. Nan ɗin ma saɓarta yayi zuwa office na Jafar husna na binshi a baya, a kan gadon office ɗin ya dire ta yana cewa "washhh Allah, mutum kaman buhu" Ɗago rinannun idanunta tayi ta zabga mishi harara ya ware mata nashi gabaɗaya alamar ni kike harara? Se tayi saurin maida kanta ƙasa, idanunshi na kan kumatunta da hannunshi ya kwanta har Jafar ya shigo daga ward. "Subhanallah kai kam yau gidanka da alama ba sa'a kuka tashi, garin yaya ta taka kwalba haka kuma kuka barshi har kafan ya kumbura ba'a zo asibiti ba Faizan?" Yana ɗauke idanu daga kanta yace "bayan mun zo da Fatima ne ta taka so saida kuma na koma na sameta hakan" Yace "sannu Amaryarmu" Kai kawai ta ɗaga mishi. Cikin sanyin muryarta tace "Ina yini" Ya amsa yana isowa da kayan aikinshi wurin gadon, se da ya gama kallon kafan kan yace za'a mata allura kan ya fara taɓa kafar, nan fa idanunta suka raina fata, duk bala'inta in aka zo fagen allura tsoron shi take. Daga yadda reaction ɗin ta ya nuna ya gane tana tsoron Allurar, har aka gama Haɗawa ya matso yana cewa ta gyara idanunta na kan allurar yayinda gogan kuma nashi ke kanta, idanunta na da kyau a kowani yanayi... Girgiza kai tayi muryarta har yana rawa tace a cire haka ba se an yi allura ba, a hankali taji shigar tattausan hannunshi cikin nata, Ɗayan kuma ya saka ya rungumo ta jikinshi, fuskanta ta binne bisa kirjinshi har yana jin hucin numfashin ta wadda a take gabaɗaya tsikar jikinshi suka tashi, har aka yi Allurar dukansu basu farga ba saida Jafar yace "Romeo and Juliet an gama Zaku iya ɗagowa" Da sauri ya saketa yana ɗan matsawa ya zabgawa Jafar harara, ita kuma ta dukar da kanta. An sha gumurzu kan aka cire kwalban tayi kuka sossai wadda har saida yaji a ƙasan ranshi be kyauta ba, bayan an gama ya ɗan Harare ta yace "taɓararriya kawai" Bakinta ta tura mishi ya kai hannu kaman ze ɗalle mata bakin tayi saurin saka duka hannunta biyu ta tare tana zare idanu wadda ya saka shi sakin murmushi yana girgiza kai, shi duk labarinta da ake bashi be ga ko ɗaya ba banda sanyin hali da tsoro kaman farar kura. Fita suka yi da Jafar zuwa masallaci suka yi sallar magrib, bayan sun dawo suka shiga wurin Fatima sun samu ta farka, dukkansu biyu da kyar ta amsa musu gaisuwar su, babu wadda ya sake magana sbd ganin yanayinta se Faizan ne ya bata umarnin tashi su wuce, haka ta mike yace taje mota ta jira shi gashinan zuwa. Ita kuwa tana zuwa motan ta buɗe baya ta shiga a dole tana fushi da shi na goyon bayan Fauza da yayi, yana isa office na Jafar ya samu ma har baccin wahala ya ɗauke ta. Haka ya sa hannu ya ɗauke ta, ta gyara kanta kan kafadanshi ta cigaba da baccin ta, husna ta biyo bayansu Jafar da ya rakosu ganin Fatima a baya ya sa hannu ya buɗe mai gaba ya sanyata. Ashar Fatima ta lailayo ta buga, da sauri ta sauko tace "Ya Faizan wai me kake nufi dani ne?" Yana gyara Fauza yace "kaman ya kuma Fatima? Duk maganan da zamu yi yanzu ki bari mu je gida pls" Tace "in bari mu je gida? Na rasa cikina sbd wannan karuwar...." "Shutt uppp Fatima!!" Ya daka mata tsawar da har saida Fauza ta tsorata tare da watsakewa daga baccin da ya cika mata idanu. Itama cikin kukan baƙin ciki tace "ba zan yi shiru ba yaya, ba zan yi shiru kayi ta zaluntata ba... Ta ɓarar min da ciki baka ce mata komai ba, asibitin ma ka zo ka ajiyeni kayi tafiyarka wurinta, ni da ya kamata ka ɗauko ka kawo mota baka ɗauko ni ba ka je ka dauko ta a hannu sbd tayi bacci, ni gani ƴar iska marar gata... To Alhamdulillah na gode Allah da baka sameni a watse kaman kofar taxi b......" Mari yake shirin sauke mata sbd yadda ranshi ya ke tafarfasa Jafar yayi saurin riƙe shi. Ita dae Fauza bata ko motsa ba banda idanu da take binsu dashi, sbd yadda idanun Fatiman ya rufe bata yi shiru ba tace "ka barshi ya mareni Jafar, ya mareni tunda ni ce karamar dangarshi me daaɗin hawa, ba se ka mareni zaka nunawa duniya cewa ni ɗin ba jininka bace, ba se ka mareni zan san cewa kana fifita wanchan karuwar ƴar shaye sha...." Marin da bata sha ɗazun ɗin ba shi ta sha yanzu saida ta kusa kaiwa ƙasa, hannun da ya nuna ta da shi har yana rawa yace "Ki kiyaye ni Fatima, ki kiyayi ganin ɓacin raina kuma ki rufe min baki ki shiga motar nan mu tafi...!" Jafar yace "Haba Faizan in ita ta rasa hankalinta tana faɗar abubuwan da basu dace ba kai be kamata ka biye mata ba, ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi har ita ta sauko kan ka nuna mata rashin kyautawar abunda tayi ɗin, zafin kishi ne kawai ke dawainiya da ita da kuma na rashi da tayi ka san dae se ta fi ka jin zafin hakan" Kallonshi Faizan yayi yace "zafin kishi? In zafin kishin ne se aka ce a rashin hankali yake zuwa?" Juyawa yayi kanta yace "I can tolerate anything but don't u dare cross ur boundaries... Ki wuce ki shiga mota mu tafi I won't repeat myself" Yana kai nan ya buɗe motar ya saka husna da har ta fara kuka, kan ya juya ga Jafar yace "zamu yi magana" Daga haka ya zagaye ya shiga motar, ya tayar idanunshi na zube kan hanya, saida yayi kaman mintuna uku da tayarwa har yana shirin jan motan yayi gaba kan Fatima dake kuka ta shiga, ita dae Fauza sannu bata ce musu ba ya tsaya restaurant ya musu takeaway kan suka kofanufi gida. Yanzu ɗin ma zagayawa yayi ya buɗe ya ɗauke ta, ko Fatiman be kalla ba ya nufi ciki, a kan gadonta ya ajiye ta har ya juya ze fice tayi saurin riƙe hannunshi wadda dukkansu saida suka ji har cikin ƙashinsu. Fuskanshi ya juyo ya kalleta cikin sanyin murya tace "I'm sorry...! Ban san hakan ze faru ba da ban biye mata ba, pls kayi hak'uri" Ta karashe tana duƙar da kanta ƙasa. Zama yayi yana ɗan murza hannunta dake cikin nashi Ɗayan kuma ya ɗaura a kan kumatunta da har yanzu yake kumbure ya ɗan shafa dukkansu suka lumshe idanu, wani sanyi ya ji a ranshi wadda be san na menene ba, ɗago idanunta tayi ta kalleshi dasu daidai shima ya buɗe nashi dake lumshe. Chan ƙasan maƙoshi yace "it's not ur fault, haka Allah ya tsara cikin ba me zama bane... Amma me ya Haɗa ku?" Tiryan Tiryan ta bashi labarin abunda ya faru bata ɓoye komai ba, yadda suke kallon juna a cikin idanu kuma ta bashi labarin ba rawar murya ko wani kame kame ya san cewa babu ƙarya a cikin labarin nata, murmushi ya saki kawai da nufin tsokanarta yace "Eyye ashe ƴar gurguwa kunnuwanta na ji da kyau tunda har ta ji sadda loudspeaker ke sanar da cewa ita ɗin ta zama matar Faizan" Da sauri ta zare hannunta tare da kare fuskanta tana murmushi shima yana murmushi yace "Haba ƴar gurguwa kunya kuma?" Baki ta turo tana cewa "ni Allah ni ba gurguwa bace" Yana miƙewa tsaye yace "Toh Ladi chogal" Ihu ta sake tana kukan shagwaɓa ya fice abunshi yana dariyar shagwaɓar tata. Se bayan ya fita ta saki murmushi ashe ya Faizan haka yake?. Abincin da ya sayo ya koma ya ɗauko, a plate ya juye takeaway biyu da ruwa ya sa kan tray ya ɗauka ya kaiwa Fauza ɗin, yanzu kam be ce mata komai ba ya ajiye mata ya baiwa husna nata kan ya juya ya fita. Na Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta dashi Dukda yadda yake jin ɓacin rai na abunda ta mishi ɗin amma be fasa zuwa ba. Tana zaune tana kuka ya shiga ɗakin, abincin ya ajiye mata kan ya juya shima yaje ya ci nashi, an riga an yi isha so ɗakinshi kawai ya shiga ya watsa ruwa yayi sallah, bayan ya idar ya mike yaje ya duba maganin Fauza ya nufi ɗakinta dashi. Samu yayi tana sallah daga zaune, toilet ɗinta ya shiga yana yabawa tsaftarta don bayin ta ba zaka ce ana anfani dashi ba ya samu roba ya tare ruwan zafi ya samu Towel ya fito. Husna tayi bacci ya ɗauke ta ya ɗaura ta kan gado ya sauya mata kaya daidai lokacin ita kuma ta idar. Da taimakon shi ta koma bakin gado, ya janyo stool ya zauna tare da ɗaukan kafan ya ɗaura kan cinyar shi. Ruwan da zafi sossai haka yayi ta danna mata tana raki tana yarfa Hannu, da muzurai da komai aka gama dannar ya bata magani ta sha, yace "dube ta..!" Baki ta turo kayan bacci yaje ya ɗauko mata ya ajiye mata gefenta kan ya dube ta yace "akwai wani abu kuma?" Kai ta girgiza yace "tohm se da safe Allah ya qara sauƙi" Tace "thank you" Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya maido mata da kofan ya rufe. Maganin Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta. Har yanzu tana kuka, zama yayi bakin gadon yace "Fatima!" Yadda ya kirata ɗin dole ya sa ta ɗaga idanu, yace tashi zaune. Mikewa tayi ta zauna, yace "menene matsalarki? Me yasa kike ganin an miki rashin adalci?" Kallon tambaya ta ma kake ta mishi, kan ta ɗauke idanunta bata ce komai ba, shima ɗauke nashi yayi yace "Ki tashi ki ci abinci ki sha magani" Yana kai nan ya ajiye mata maganin ya tashi ya fice abunshi don ta ƙi magana. Ya gaji ainun so yana kwanciya bacci ya sureshi, da asuba yana dawowa daga sallah kenan ya hangi ɓacewar mota kaman kuma ta Fatima, me gadinshi ya tambaya ya tabbatar mishi da yanzun nan Fatima ta fice. Be ce komai ba ya haura yaje yayi kwanciyar shi don yau bai da wani aiki, be tashi ba se karfe goma da rabi. Wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya fito, zaune ya same su suna kallon wani animation, zama shima yayi ta dube shi tace "Ina kwana?" Ya amsa da lafiya yana kallon kafafunta yace "ya jikin?" Ta amsa da "Alhamdulillah" Duk shiru suka yi, ta san Fatima bata nan don itama ta hangi fitanta ta window kuma bata ji alamun dawowarta ba, ta barshi da yunwa kuma be dace ba tunda sun yi girki kuma ya saura. Miƙewa tayi tana ɗan ɗingisa kafafunta ta nufi ƙasa da kallo ya bita har ta ɓace mai, sanye take da blue Indian gown da ya zauna mata sossai a jiki, be kai ƙasa ba se wandon shi da ake hangar adonshi daga gwiwar kafanta, yana da tsagu me tsayi daga gefe da gefe, ta ɗaura gyalen ɗaurin turban a kanta, ba karamin kyau tayi ba barin ma da ta gyara fuskanta ta saka lip gloss, bata jima ba ta dawo. A gabanshi ta ajiye tray ɗin da ta hauro dashi ɗin. Wani fancy bowl ta zuba kifi da yafi yanayi da soup don yayi kauri ta ɗaura kan plate ɗinshi, a idanu kaɗai abun sha'awa ne gwanin kyau bare a baki, akwai kuma warmer a gefen plates ɗin ta buɗe ta ɗaga miyan ta ajiye gefe doya da ta soya da kwai ne ya ji kwai ta zuba a plate ɗin kan ta matsar mai, ta sake miƙewa ta fice chan se gata da wani karamin tray wadda shayin shi da ta saba dafa mai ne ciki, ta zo ta ajiye mai ganin ya fara cin abincin ta tsiyaya mai da kanta. Idanunshi na kanta yana kiyasta abubuwa masu yawa a ranshi yace "thank you" Ta miƙe tana ɗan murmushi bata zauna a parlorn ba se ta nufi ɗaki. "Fauza!" Ya kirata yadda kowa ke kiranta, da sauri ta juyo yace "kin sha magani?" Kai ta gyaɗa mai yace "to dawo ki zauna" Dawowa tayi ba musu ta zauna a parlorn. Bayan ya gama cin abincin da kanshi ya tattare kwananukan amma kitchen ɗin sama ya ajiye, a tare suka yi spending time me yawa Dukda babu me magana cikinsu banda husna da ta ishe Fauza da surutu sede ta amsa da eh ko a'a, azahar da aka kira ya saka su duk mikewa. Ya fita be dawo gidan ba se yamma lis. Yanzu ma abincin ta kawo mai tuwon semo ne da miyan busashiyar kubewa sbd shi tayi tuwon don ta san yana so, ita kam indomie ta dafa ta ci, husna ma tuwon ta ci, se bayan magrib ya zauna cin tuwon gefen shi papers ne, bayan ya gama ya wanke hannu ya dube ta kan yace "Dukda ban so ki fara karatu nan kusa ba saide Baba prof ya ƙi aminta da kudiri na hakan ya sa dole na shiga nemar miki admission kuma Alhamdulillah yau gashi kin samu, ina so ki san rayuwarki na da da na yanzu ba ɗaya ba, idan da kin yi abubuwa masu yawa ganin u r free yanzu kina da aure, matsayin aure kuma ya wuce duk wani matsayi da kike tunani, duk laifin da zaki aikata yanzu ki sani ba iya ke da zuri'arki ba har mijinki da ƴaƴanki wannan image ɗin baze mantu a idanunsu ba, sannan zunubinki se ya fi na da sbd kin wulakanta sunnah, in Allah ya kaimu gobe zaki je ki ƙarasa sauran abubuwan da ban karasa ba ki fara shiga aji" Karɓan admission da ya miko mata tayi tace "na gode Allah ya saka da alkhairi in shaa Allahu zan kiyaye" Wayanshi ne ya ɗauki ringing ganin baba prof yasa ya ɗaga tare da sallama bayan sun gaisa baban yace "Faizan me ya faru? Meyasa zaka bar matarka tayi yaji kuma ta kamo hanya daga Abuja zuwa yola a mota bayan ka san ba lafiya ne da ita ba?" Yace "Yola ta tafi kenan? Hmm baba maganan nan ba na waya bane ta zauna a gidan in Allah ya sa Fauziyya ta warke zan zo" Baba yace "Assha Fauziyyan ma ba lafiya?" Yace "Eh amma da sauƙi" Baban yace ya bata, miƙa mata yayi a ladabce ta gaishe shi ya tambayi jiki take ce mishi ai ta warke ma bayan sun gama ya ba jadda da suke tare itama ta mata sannu tana tambayar me ke damunta, tace kwalba ta taka amma da sauƙi. Miƙa mishi wayan tayi tana Kallonshi, kallon lafiya kike kallo na yayi mata se tayi saurin kau da kai ta miƙe. "Gulma" Ya faɗa yana maida kanshi ga TV🤣 DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 23 "Aunty fa wai kinga kuwa yadda ya ɗauke tan ne? Be fa hukunta ta na abunda ta aikata ba, wallahi zuciyata zata bu...." Zazzafar mari Auntyn ta sauke mata tace "zuciyar ta buga Fatima, nace ta buga ɗin.." Dawowa tayi ta zauna ganganta tace "Fatima kin san irin asarar da kike shirin ja min? Kin fa san shekaru sama da goma sha wani abu nayi ina wannan tanadi meyasa se lokaci ɗaya zaki nemi watsar min da buri? Ni da nake zaune lafiya da kowa a gidan nan alhali zuciyata dankare take da haushi da tsanarsu duka ni me ya sameni? Toh wallahi ba zan ɗauka ba, bazaki zama wawuya shashasha, lusara a gidan Faizan har ki barwa Fauza shi ba..." Cikin kuka Fatima tace "Aunty fa kin san makircin Fauza, da gangan yarinyar nan ta sauya gabaɗaya ni bata min rashin kunya bare shi ballantana in ce zasu samu sabani har ya sauya mata kamanni don baya daukar rashin kunya.." Dakuwa Aunty tayi mata tace "baya ɗauka kin sani kuma kika mishi? Fatima wallahi wallahi zan iya sauya ki idan baki yi hankali ba bazan taɓa zama ki wargaje min mafarki na ba, sarai kin san tun kan na shigo gidan nan nake da buri a cikinshi, target na ba Sulaiman bane amma saboda in yi anfani dake yasa na auri Sulaiman yanzu bayan kin girma kuma ki kasa yi min komai ba, kin san wahalan da muka sha kan Faizan ya aureki" Fatima tana kuka tace "Amma Aunty ai laifin ki ne, kin sanya min soyayyar faizan tun ban san target ɗinki ba, kuma mun yi yarjejeniya a aikinki ba za ki taɓa cutar da shi ba, wlh rasa shi daidai yake da na rasa rayuwata, bala'in son da ban san adadinshi ba nake mishi shiyasa kusancinsu da fauza ke kasheni... Aunty ke kika ce aure kawai za'a ɗaura ba ze shiga lamarin ta ba sbd tsanar da yake mata amma gashi nan reshe na shirin Juyawa da mujiya... Ko ki san yadda zaki yi dani ko kuma wallahi kowa ya rasa nashi Burin..." Wara idanu Auntyn tayi tana kallon Fatima tace "Fatima? Are u threatening me?" Mikewa tayi tana share fuskan ta tace "ba threatening ɗinki nake yi ba, ina gayamiki ne ki ɗaukar min mataki akan Fauza in ba haka ba daga ni har ke dab muke da rasa burikanmu" Tana kai nan ta fice daga ɗakin. *** Kaman yadda ya faɗa washegari bayan ta gama Haɗa musu abin kari ta shirya a dining taje tayi wanka, doguwar riga marar nauyi ta saka tare da sanya hijab coffee color wadda yaje mata har ƙasa, ta shirya husna ma cikin doguwar riga da baby hijab, daidai sun fito shima ya fito murmushi ya sakarwa husna wadda ya saka Fauza daskarewa a wurin tana ganin cikakken haiba da kyaun bawan Allahn nan, daga baba prof har mammi ba wadda ya bari duk seda ya bi ya zaftare musu kyau da kwarjininsu. "Madam chogal" Ta faɗa yana kallonta da neman tsokana, ai kuwa baki ta turo tana cewa "Allah yaya ni ba chogal bace gashi ina tafiya da kyau" Ta fara tafiya tana nuna mai dariya yayi yace "ni dae idanuna chogal suka gani" Dining suka nufa tana ta tura baki, idanunshi kafe kan lips ɗin da take ta turowan ta saka pink lipstick da yayi mata kyau sossai. Bayan ta gama sa abincin ta tura mishi ta zubawa husna ta kuma zuba nata Dukda yadda take a takure a kuma sarge sbd yadda yake aika mata kallon ƙasa ƙasa haka ba yadda ta iya ta zauna a wurin ta fara ci, Seda suka gama suka yi hamdala kan ya saka hannu ya zari tissue ya miƙe. Taku biyu ya iso dab da ita har suna shaƙar numfashin juna, ƙashim jikinsu na gaurayuwa, duƙowa yayi yana rarraba idanunshi tsakanin kirjinta dake bugu da sauri har yana iya kallo da kuma idanunta da suke kashe shi, da kyar ya samu ya tsayar akan lips ɗinta da yanzu suka zama abu na biyu da baya iya gajiya da kallo a jikinta, saukar hannunshi taji da tissue ɗin ya ɗan kwashe lipstick ɗin cikin wani salo da ya saka su jin yarrrrrr gabaɗayansu. "Haka is ok" Ya faɗa chan ƙasan maƙoshi kan ya miƙe tsaye ya juya tare da cusa hannayenshi cikin aljihu ya fara takawa don fita daga wurin. Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta, 'oh ni fauza me ke faruwa ne kam?' Ta tambayi kanta sede ba amsa. Mikewa suka yi duk suka bi bayanshi, husna ta tura gaban motan ita ta shiga baya, har suka isa da shi da husna suke hiran su ita bata saka musu baki ba. Microbiology ne course da aka bata yayinda Fatima take yin biochem kusan dept ɗinsu wuri daya ne, sauka suka yi suka nufi ciki inda office ɗin Faisal yake nan biology dept, kan su isa ta Haɗa idanu da en mata sama da biyar waenda idanunsu kan Faizan kaman zasu cinye shi danye, ɗan Kallonshi tayi taga abunda suke kallo. Ash trouser ne a jikinshi me taushi se farar shirt wadda ya zauna mishi sossai ya fitar da siffanshi ta kakkarfan namiji, sajenshi ya kwanta lublub a kyakyawar farar fuskanshi ga fuskan cike da haiba Dukda ba murmushi yake ba amma be kama ba, taɓe baki tayi ta maida bisa hanya har suka karasa office ɗin. Faisal ya fi Jafar wasa haka yayi ta jan ta yana tsokanarta ita kam kanta ƙasa murmushi kawai take tana kuma jin idanun gogan nata jikinta alamu ita yake kallo, wata yarinya Faisal ya kira a waya ba'a yi mintuna biyar ba se gata a ladabce ta gaishesu yana kallonta yace "yauwa Afnan ga ƙawa nayi miki Dukda dae da hafsa ne kawancen asalin amma a nan kawar ki ce, ku je ki nuna mata wurare sannan Naga kuna da lectures 9-10 duk ku shiga tare kin ji?" Tana murmushi tace "Toh Yaya, Aunty mu je" Murmushi Fauza tayi kan ta miƙe tsaye se ta kalli Faizan da nufin neman izinin tafiya, murmushi me kyau da ya tafi da imaninta ya sakar mata kan yace "a kula, ina jiranki anan" Kai ta gyaɗa itama ta ɗan yi mishi murmushi kan ta bi bayan Afnan dake Kallonsu da burgewa tana amsa bye bye ɗin husna. "Kan uba! Kai fa ɗan iska ne Faizan so kake ka hana yarinya karatu da wannan narke narken?" Harara ya zabga mishi yace "ka manta ɗan guguwa ne.." Dariya suka yi a tare, Faisal yace "Masha Allah amma Amaryar ka na da hankali gata sweet sixteen shiyasa mana ka makale a gida ka kasa fita outside countries tunda aka kawo maka ita, Haba ai biri yayi kama da mutum" Duka Faizan ya kai mai yana cewa "ba da aljani ba?" Dariya sossai faisal yake mai, daga karshe suka saki hiran Fauza suka kama wani, don sun san Faizan mutum ne da baya so ko a junansu ne suke kawo maganganun iyalansu in har ya zamana sirrinsu ne, ya sha gayamusu girman sirri dake tsakanin miji da mata da kuma tanadin Allah ga me fallasawa walau miji walau matar, lokutta dayawa in sun zauna daga sun fara in ya dakatar dasu zasu fara mishi tsiyar social ustaz ko young sheikh ya hana dole a hanu. A ɓangaren Fauza kuwa taji daaɗin makarantar fiye da yadda ta zata, Afnan na da hankali ga saurin sabo nan da nan suka saba, a tare suka ɗan yiyyi signings da bata yi a course form ba suka kuma shiga lectures, basu dayawa don haka ba wani surutu kuma for the first time Fauza ta natsu a class har ta saurari malami ba zagi, faɗa ko neman tsokana. Bayan sun tashi ta same shi a office ɗin kaman yadda ya faɗa suka nufi gida. "Amm Faahim ya ƙira Visa ɗin husna ya fito zata bisu" Da sauri ta kalleshi idanunta na cika da hawaye sede bata ce komai ba, ya fahimci kewan husna zata yi to amma ba yadda suka iya dole ne zata koma wurin iyayenta, har suka dawo gida jikin ta a mace, juicy pasta bolognaise tayi musu sharp sharp suka ci yayi daaɗi kuwa sossai, har ya kasa shiru yace "Ni kam Fauza duk wa ya koya miki abubuwa masu daaɗi haka?" Murmushi tayi zata yi magana husna ta ɗauki pillown kujera taje bayanshi tana kare mishi tace "haka fa mommy ke yiwa Daddy idan yana cin abinci yana santi, wai kunnenshi na motsi..." Duk dariya suka saka Fauza ta kasa tsayar da nata har ya shagala da kallonta for the first time he admits it she's so cute and beautiful, da kyar ta tsagaita dariyar ganin irin kallon da yake mata tayi gyaran murya tare da cewa "Na koya wasu wurin friends ɗina though idan na biya wurin koyan kullum se na sha duka amma haka nake zuwa bcs shine abinda ke sani farin ciki time ɗin, se kuma da nayi waya nayi classes masu yawa online" Kallon tausayi ya mata yace "then me yake hana ki faɗin ga inda kika je a time ɗin? Me yasa ba zaki ce a saka ki a catering school ba?" Idanunta ta kaɗa wadda yaji har tsakiyar kwanyarshi tana ɗaga kafada tace "Taurin kai irin na Fauza" Kallonta kawai yake yana mamakin ita kuma wannan haka Allah ya yi ta ko kuwa? Tattare wurin da ta fara ne yasa ya ɗauke idanunshi kanta. A haka suka kwashe kwana bakwai curr kullum ita zata yi musu breakfast ya sauke ta makaranta ya wuce inda zashi wani lokacin kuma ya tsaya wurin Faisal in an tashi ya maida ta ko karfe nawa zata kai baze ci abinci ba ze jira har ta gama su koma ta sama musu abunda zasu ci. Be taɓa zaton rayuwa da ita in a shade ze zama haka ba, yarinyar tana da tsafta, kunya ga iya girki har ba'a magana, sau dayawa yana mamakin ina wannan kunyar nata yaje har take yawon hotels da shaye shaye, lokuta dayawa idan ya tuna hakan halin da rayuwarshi ke shiga baya mishi daaɗi hakan yasa yake ta kokarin rufe baabin ganinta da yayi a hotels da kuma irin shaye shaye da tayi. Ranar Sunday bayan ya karya yake sanar mata ze je yola amma gobe da yamma ze dawo, kaman zata yi kuka haka tayi mishi Dukda tana tsoron kwana haka baya nan amma da sauƙi tunda ga husna, Seda ya tabbatar babu abunda suke bukata kan ya wuce bayan ya bata Wayanshi da take yawan anfani dashi ɗin nan. *** "Na fahimce ki yanzu Fatima, an samu matsala ne girma da daraja irin na aure ya kunce ɗauri masu yawa akan Fauziyya ɗin hakan ne yasa kika ga halinta gabaɗaya kaman sake mata shi aka yi, sannan gidanta akwai kariya sossai amma jikinta da sauƙin kariyar, mijinki ze zo ku koma kawai ki zuba idanu kiyi kallo kaman yadda kika bar gidan haka itama zata bari ba na kwana bakwai ba ita kam na har Abada" Aunty ta sauke Ayar cikin cin alwashi. Murmushi Fatima ta saki tace "yauwa Auntyna maganin kuka na" Ko da ya iso se dare suka zauna da Baba Prof ya gayamusu duk abunda ya faru, kai tsaye Fatima ta Musa wadda ya saka baba prof kallonta cikin mamaki don tabbas ze iya cewa fauza bata yi karya ba kan yayi magana ma baba Alhj yace.. "Ko ni da ban shaku da fauza ba na san wannan ɗabi'ar tata na rashin ƙarya, ta kan faɗi gaskiya ko hakan ze ja mata dukan mutawa ne". Da sauri Fatima ta kalleshi har zata ce kenan ita ɗin an mata shedar karya kenan Aunty tayi saurin cewa "ai duk maida magana bata taso ba, na yiwa Fatima faɗa sossai akan shiga harkar Fauza tunda an samu tana zaune lafiya karta dinga shiga harkar ta idan har ba mutunci ne ze Haɗa su ba, kuma in shaa Allahu ta ɗauka" Baba prof yace "masha Allah, to yayi" Faɗa ya ɗan mata akan yadda Faizan ya mayar mai yadda take maida mishi magani ya nuna mata girman miji da matsayinshi kan ya sallame su akan gobe zasu wuce. Faizan wurin mammi ya kusa cinye daren suna hira tsakanin uwa da ɗa, amma fa kusan duk hiran na Fauza ne ita ke mishi yana ji, ta bashi labarin yadda Fauza ke kula da ita da cimarta in bata da lafiya har ta faɗa mai Adu'ar da Fauzan ke mata in kafanta ya tashi yanzu bata nan ne sede tayi da kanta Dukda bata tausan kafan yadda ya kamata. Tana bashi labarin tana kula dashi da a da ne da yanzu duk wani fara'arshi ya kau kilan ma da ya bar mata wurin amma yanzu har murmushi ya kan yi, se dare sossai ya miƙe yayi mata se da safe, har ranta ta ji daaɗin fahimtar da tayi akwai haske a lamarinsu. Yana isa ɗaki a kan three seater ya kwanta ya fiddo ainihin Wayanshi ya fara neman layin shi dake wurin Fauza ɗin. Har Seda ya kusa katsewa kan ta ɗaga "Assalamu Alaikum warahmatullah" Ta faɗa ƙasa ƙasa wadda a take muryar ya saukar mishi da kasala yaji gaɓoɓinshi a gajiye. Shima chan kasa ya amsa ta kan ya ɗora da "kin yi bacci ne?" Tace "uhm na soma kenan, ka isa lafiya? Ya ka same su?" Ya ɗan yi shiru kan yace "lafiya ƙalau duk suna lafiya, mammi na ta missing ɗinki" Tana murmushi tace "Allah sarki mammina nima nayi kewarta sossai" Yace a ƙasan maƙoshi "ɗan mammi fa?" Dariya me sauti tayi tace "Husna na ta tambayar ka, gidan shiru mu kaɗai shiyasa ma muka kwanta da wuri" Shima basarwa yayi kaman yadda ya fahimci ta basar da tambayar shi yace "in Shaa Allah gobe warhaka muna nan Kice mata kar ta damu sannan ki ce mata nayi missing ɗinku" Yana kai nan ya yanke wayan.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 24 kaman kuwa yadda ya ce ɗin karfe biyar daidai a bakin kofan gate ɗin gidan ya musu kaman kuwa sun Haɗa baki da wadda ya tuƙo motar Fatima ɗin tun asuba don suna parking shima yayi horn aka buɗe mai ya shigar, hana shi tafiya Faizan yayi yace ya shiga ya ci abinci in ya so ya sama mai wuri ya kwana se gobe ya wuce da sassafe ta tasha. Godiya sossai mutumin yayi kan suka shiga ciki a tare, parlorn ƙasan ya sha gyara se kamshin turarukan wuta masu sanyi yake zubawa, murmushi ya saki sanin aikinta ne don kamshin a wurinta ya saba ji irin wannan kam, ji yake kaman yana ɗakin mammi ko jadda sbd natsuwa da ya saukar mai. Kujera yayiwa drivern izinin zama shi kuma ya nufi sama don tuni Fatima ta jima da wucewa.. "Yaaa salaam!" Ya furta a ranshi a sadda idanunshi suka faɗa kanta, itama dakatawa tayi tana sakin murmushi da ya Karasa saukar mai da gajiya, da gudu husna taje tayi hugging nashi hakan ya dawo dashi daga wata duniyar da ya tafi, ɗauke kai yayi saide idanunshi basu koshi da kallonta ba. Tayi kyau sossai cikin wani material silk da aka yi mata doguwar riga fitted ya fitar da duk wani siffanta ta saka jewelries fashion gyale baƙi a ɗaure bisa kanta, tana murmushi tace "sannu da dawowa yaya" Sam wlh babu wadda yake kallo a parlorn bayan ita be san Fatima na parlorn ba har lokacin seda yaji ta ja wani wawan tsaki ta wuce ɗakinta tare da doko kofa. Duk kallon kofan suka yi kan suka kalli juna yace "yauwa ƙanwata! Pls zamu samu abinci? Akwai baƙo a parlor yayi tafiya me nisa" Tace "kwarai kuwa baza'a rasa abinci ba, bari na duba mishi" Kallonta yake ya ga ko zata fita a haka saide ga mamakin shi ta shiga ɗaki ta dau hijab ta saka kan ta fito ta nufi ƙasa, fuskanshi kaman gonar auduga ya bita da kallo har ta ɓace mishi. Hira suke yi da husna tana mai rigimar ina tsarabarta har ta dawo ɗauke da jug da cup ɗinshi me kyau bisa tray, a gefenshi ta tsuguna ta tsiyaya mishi tare da miƙa mai. Hannu ya sa yana karɓa sanyin abun na aika mishi da zakuwar son ɗanɗanawa Dukda be san me bane, kurbi daya yayi ya lumshe idanu yace "wannan kuma me sunanshi ƙanwata?" Husna tace "laaa uncle kunun aya ne baka sani ba?" Yace "Husna uncle be saba shan me daaɗi da kaurin wannan bane but it's so so giving wlh" Dariya suka saka mishi, Fauza tace "Yaaya ya su mammi da Jaddah? Baba prof da Baba Alhj da kowa da kowa dake gidan kowa na nan ƙalau?" Ta faɗa a marairaice. Yace "kowa na lafiya, duk sun gaida ke" Sossai tayi kewan su. Bayan ya gama sha ya mike yana ce mata bari ya kai bakon nan masauki, ze yi magrib kan ya shigo. Seda ya gama faɗa kuma se yaji wani iri sbd ba sabawa yayi ba. Tace "Allah ya tsare a dawo lafiya" Seda ya leƙa ya gayawa Fatima da ta amsa da kyar kan ya juya ya fice. Fitowa Fatima tayi tana kallon Fauza dake kwashe abubuwan da ya sha kunun ayan tace "mtseww ba girin girin ba dae tayi mai..." Fauza bata yi niyyar tanka ta ba ta sake cewa "cushe ba farin jini" Dariya Fauza ta saki sossai kan tace "Eyyaaa ai Alhamdulillah tunda ni umarnin iyaye nake bi kuma seda aka ɗaura na zama tashi kan nake cushen wata fa da ta gina komai a ƙarya?" Matsowa tayi tace "karki ga kaman kin ci galaba a kaina last week sbd cikina da kika ɓarar wlh yanzu se in nuna miki na riga ki shan iskar duniya" Fauza ta mata kallon sama da ƙasa kan tace "ko? Allah sarki abunda kuma aka koyar dake kenan? Iya shi kenan ko har da barbaɗe? Kin San Allah in da nayi niyyar shayar dake bakin ciki marar misaltuwa da nayi tuntuni ki kiyaye ni... Kaman yadda nake faɗa ki tsaya matsayarki sannan Haɗa jiki dake ai zubda aji ne, Allah sarki yayana bana so kayi tsiya, don kin san Haɗa ƙashi da kishiya miji yake janyowa tsiya.. Kuma komai lalacewar masa Fatima ai ta fi karfin kashin shanu" Tana kai nan ta wuce ɗakinta don husna tuni ta shige, a daskare Fatima take tana bin bayanta da kallo, lallai yarinyar nan ta gama raina ta, ya tana mata kallon biri ita kuma tana mata na Ayaba? Ashe dama Fauzan kura ce lulluɓe da fatar akuya? Waye yake hure mata kunne ta mamaye min gida? Ihu ta kurma kan ta nufi ɗaki tana ji kaman ta sa wa gidan wuta kowa ya huta. Bayan ya dawo ta gabatar mai da abinci Dukda bata yi niyya ba amma ganin yau suka dawo yasa ta bashi, amma gobe kam matarshi da ta iya girki ita zata cigaba da sama mai abunda ze ci dama taimako tayi. Tuwon alkama ne da miyar kuka ya ji ma shanu naman kazan nan yayi raga raga a ciki, ya ci sossai kuwa kan ya kira su duka parlor, nan yayi musu faɗa sossai akan rikici tsakaninsu ya kuma gargadesu da kar ya kara ji bare gani, daga karshe ya ɗaura da "Fatima tunda kina da mota Zaku dinga tafiya school da fauza har muga yadda za'a yi" Tace "Toh Yaya in shaa Allah" Fauza da bata so ba kuma har a fuskanta ya nuna ya kalla se tace "in shaa Allah, mun gode" Daga haka ta mike tayi ɗakinta da kallo ya bita har ta shige, sadda Fatima bata nan kusan a parlorn suke kashe lokacinsu amma yanzu tana so ta komawa halin farko da ta fara zama a gidan. Mikewa yayi ya bi bayanta, husna na kallo ya nufi wurinta don tana tsaye ne gaban wardrobe kuma in ba husna ta taso ta zo wurin ba ba ganinsu zata yi ba. Dab da ita ya tsaya har tana jin kamshin shi na cika mata ciki, yace "Bakya so ne?" Ta ɗago tace "me fa?" Bakinta yake kallo kan yace "seems like baki ji daaɗin zancen tafiya school da Zaku ke yi da Fatima ba, for now it's my only option don in aiki ya min yawa ba zan dinga iya kaiki ina ɗauko ki ba and I hate it so much in ga matata tana hawa motar haya ko bolt ne kuwa" Juyawa tayi tana kokarin buɗe wardrobe ɗin tace "ba komai, na fahimta" Har yanzu ranshi be bashi ta gamsu da hakan ba, ya rasa me yasa ya matsu kuma yake so ta fahimce shi ba don cin fuska bane yayi hakan, amma dae haka ya hakura ya fita kar ya janyowa kanshi raini a faɗar shi fa kenan. Washegari da safe ya fito tsab a shirye saide ganin Fatima tsaye a dining yasa ya san yau kam ze yi missing girkin Fauza, zama yayi tayi serving ɗinshi kaɗan ya ci ya miƙe yana duba agogo yace "zan ɗan fita wani meeting ba zan dawo yanzu ba ku kula pls" Daidai ya nufi cikin parlorn Fauza ta fito rike da hannun husna shirye cikin hijab dogo tayi kyau sossai, tace "Ina kwana yaya?" Yace "lafiya ƙalau ƙanwata" Shiru duk suka yi ya ɗan tsaya kan yace "Na fita" Tace "Allah ya tsare ya kiyaye" Dama abunda yake son ji kenan se yayi murmushi ya nufi gangarawa. Dama sun sha cereals yau a ɗaki don bata yi wani girki ba, zaman jiran Fatima tayi seda ta ga dama kan ta fito suka sauka zuwa motanta, gaba ta tura husna ta buɗe baya ta zauna. Tak be Haɗa su ba har suka isa makarantar, Fauza tayi dept ɗinta suka haɗu da Afnan suka yi lecture hall, Afnan ƙanwar matar Faisal ce Dukda basu haɗu da matar ta Faisal ba amma Afnan na yabon halinta hakan ya kwadaitar mata da son zama dasu ko zata rage kaɗaici barin ma in husna ta koma. Ko da aka tashi saida ta jira Fatima har ranta ya soma ɓaci kan ta zo suka yi gida, abinci marar nauyi ta Haɗa musu suka zauna suka ci da husna kan suka haura sama abin su. Ko da ya dawo ma abincin Fatima ya samu haka dae ya ci yana Tunanin kwaɓar da yayi da yadda ze gyarota. Washegari ma hakan ce ta kasance.. Suna zaune a ƙasan bishiya ita da Afnan da husna wurin akwai students haka dake kai kawo duba wani handout take yayinda Afnan ke kara mata bayani don an yi farkon lectures ɗin bata nan. Wani shirgegen ƙadangare taga yana saukowa daga bishiyar ita ba wai tana tsoron su chan chan bane amma bata so su zo kusa da ita ganin ya tsaya yana ta gyaɗa kai gashi marar kyaun gani yasa ta ɗan ɗaga hannu tayi shhh, ai kaman ta ce mishi ya zo yayi wani irin tahowa da gudu ta kafafunta kan ta miƙe tsaye ya shige mata hijab ƙara ta saki tana ambaton Hasbunallahu wani'imal wakeel....! *** Tsaye yake gefen Faisal yace "kwaɓa nayi faisal kuma duk tunanina na rasa yadda zan warware shi wlh" Faisal yace "Toh kai ɗin ma kenan bare mu? Wani irin kwaɓa ne haka da ya dameka?" Shafa kanshi yayi yana jan iska tare da fesarwa yace "ka gane ko? Yarinyar nan ne a sadda ta zo na ɗauka tayi kankanta da ɗawainiyar gida kuma bazata iya wani aikin a zo a gani ba bare har ta iya girkin da zan iya ci, to my biggest surprise abubuwan da ta iya ko chef da yayi ten years in profession be iya ba, ta kula da cikina tsawon lokacin da Fatima bata nan yanzu kuma Fatima ta dawo se ta sakar mata" Faisal ya kwashe da dariya yana cewa "kana raina yaran yanzu my guy... Dama baka raba musu kwana bane?" Girgiza kai yayi yace "she's too young" Shi karan kanshi da ya faɗa ɗin he's not so sure of his self bare Faisal me sauraro. "Maganan gaskiya shine ka fito ka raba musu kwana ko da bazaku kwana tare ba ya zamana ran kwanan ta bakwa tare da Fatima ta hakan ne zaka iya kwasar girkin tunda kana so" Shi ba fa hakan ne baze iya ba yanzu yadda ze fuskanci Fauza ne yace ta cigaba da girki bayan a fuskanta ya jefe ta da mugun kalamai yana cewa ba ze iya cin jagwagwalonta b..... Gigitaccen Ƙara da yaji da Hasbunallahu wani'imal wakeel shi ya saka shi saurin miƙewa daga jinginen da yake.. Muryarshi na rawa yace "Fauziyya..!" Da gudu shi da Faisal suka yi inda suka ji ƙaran tana kokarin cire hijab ɗinta yayinda wani dake daga gefe yake kokarin kai hannu da taimaka mata, cikin zafin nama Faizan ya damki hannun nashi ya cillar kan ya fusgota kaman yadda take a rude haka shima ta ruɗa shi. Fahimtar ƙadangare ne ya sa ya sure ta gabaɗaya yayi wurin motan shi yana sanyata ya zare hijab ɗin gabaɗaya ta haukace da kuka da kiran sunan Allah daidai ƙadangaren ya zo kan bayan wuyanta se ya tsaya Chak a wurin ko motsi baya yi. "Yaaaya.. Don Allah ka cire min wayyo kafafunshi na shiga min fata, da zafi sossai ka cire min don Allah" Yadda take kuka take abu kaman shafan aljanu yasa ya matse ta bisa kirjinshi yasa hannu da nufin fusge ƙadangaren sede duk iya gwada karfinshi ƙadangaren nan ya ƙi ko motsi, hankali tashe yake kallon ƙadangaren wani irin tashi tsikar jikinshi yayi da sauri ya fiddo waya ya fara kiran Baba prof. Cikin hanzari ya mishi bayanin abunda ke faruwa gashi Fauza ta dena motsi, Baba prof yayi salati ya sallamar kan yace "ku yi sauri ku je wurin prof ghali na tabbatar ze yi duk abunda ya dace yanzu yanzu Faizan karka ɓata lokaci bari na kirashi" Kofan motar ya tura ya kira Faisal tare da cila mai key don yanzu ba ze iya tuki ba gabaɗayanshi ya sauya idanunshi har sun sanja kala, Afnan da husna da har sun fara hawaye ne suka shiga gaba. A take ya ja mutane suna ta mamakin wannan abu da Allah ya kiyaye haka students suka watse. A hannu ya ɗauke ta zuwa wurin malam ɗin, already Baba Prof ya kirashi ya mishi bayani, a jikinshi ya sanya ta Tare da kwashe gashinta da ya baje Malam ghali na kallon kadangaren yace "la haula wala quwwata illa billah..." Da sauri ya janyo ruwan zamzam da wasu Adu'o'i ke ciki ya tashi ya shiga dakinshi mintuna biyu ya fito da wani Allon karfe ruwan ya zuba a Allon kan ya saka ya buge ƙadangaren yana ambaton sunan Allah. A take ƙadangaren ya fice fit daga jikinta ya faɗi ƙasa ya fara kokarin guduwa wannan ruwa malam ya diba ya fara zuba mai nan ya fara wani kalar birgima da mutsu mustu ba'a ɗauki lokaci ba ya zama baƙi kirin ya tamushe kaman wadda wuta ya babbake. Faizan na ta patting kumatunta yana cewa "Ke Fauza buɗe idanunki kiga an cire... Fauza! Fauziyya..!!" Malam yace "bazata tashi ba Faizan kwantar da ita" "malam me yasa bazata tashi ba? Don Allah kayi wani abu" Yadda yake maganan kaɗai zaka san ba karamin ruɗe wa yayi ba, me hakan ke nufi? Yau da baya school ɗinsu fa? Haka zata shiga wannan hali ita kaɗai? Malam ghali yace "wato wannan ƙadangaren ɗan aike ne, a yadda ka ganshin kila ta ambaci Allah a sadda ya nufi hawa jikinta da bata ambata ba ƙara kawai ta tsaya yi da yanzu ganinshi ma wahala ze mana don jikinta ze shiga, ko ya lahanta mata abubuwan ciki ta mutu ko kuma yayi mata illar da warakarshi se rabba" "waye ze mata hakan? Waye yake neman illatar da lafiyar ta haka? Me ta musu?" Kaman ze yi kuka yayi maganan. Malam yace "wannan mu barwa Allah, yanzu mu tsaya kan lafiyanta" Ruwan Adu'a malam ɗin ya bashi yace ya shafe ta dashi, bayan yayi ya saka shi saka mata a baki, nan ya bashi za'afaran da habba da suke dauke da Adu'a yace ya shafa mata, fuska, hannaye, gashin kanta da kafafunta nan take yayi. Ya zauna yayi shiru yana kallonta cikin jiran malam ya gama Adu'ar da yake yi, yana gamawa kuwa ya watsa mata se ta ja numfashi a kuma ruɗe tayi hanzarin mikewa tana mutsu mustu.. "Yayaaa ka ciremin... Wayyo zafi, Hasbunallahu wani'imal wakeel... Wayyo Jaddah..." Duk bata san tana wannan sambatu ba kamata yayi ya rungume a hankali ya sauke hannunshi bisa bayanta ya zagaye kan ya da matse ta a jikin shi cikin rarrashi yace "shhhh ƙanwata, yi shiru an cire baya jikinki... Shhh" Lub tayi. Malam yace "ku je a duba jikin nata in ya so ko maganin asibiti se a sake bata watakila yana da dafi, amma ga wannan ta dinga anfani dasu zamu yi magana da Mahaifin naka" Prof ghali babban malami ne don tsohon professor ne na musulunci abokin Baba prof ne, kuma dama chan Faizan kan leƙa ya gaida shi idan ya samu time. Zamewa tayi daga jikinshi kanta a ƙasa, haka suka miƙe suka fito, hijab ɗinta ya sanya mata yana kallon bayan wuyan nata da shape ɗin ƙadangaren har yanzu yake kwance yayi baƙi sidik... "Me ke shirin faruwa ne?" Yayi maganan yana sake kallon hannunta da ta gimtse a cikin nashi har yanzu yana iya jin yadda jikinta ke rawa ta ciki.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 25 Ko da suka isa asibitin Jafar ne ya duba raunin aka yi mata allura, ganin ko tsorata bata yi ba kaman yadda ta saba ba ya san har lokacin bata dawo daidai gabaɗaya ba, haka dae Jafar ya dawo dasu gida yana kallon yadda gabaɗaya Faizan ɗin Damuwa me yawa ya nuna a fuskanshi. "Ka tafi da motar na ga kaman hadari ko gobe se ka ba driver ɗinka ya dawo dashi" Cewar Faizan bayan sun sauƙa yana rike da hannunta, Afnan tayi mata Allah ya kiyaye kan suka fice daga gidan. Haurawa suka yi zuwa ɗakinta, cikin kulawa yace "bari na Haɗa miki ruwa ki watsa se ki sha magani ko?" Girgiza kai tayi idanunta tab da hawaye ta sake riƙe hannunshi da yake Shirin zarewa cikin nata. Fuskanshi cike da tausayinta yace "babu abunda ze sake faruwa yanzu kin ji? Sake ni kiga" Nan ma girgiza kai tayi se hawayen ya gangaro, babu yadda ya iya illa ya sa hannunshi ɗayan ya share mata kan ya ce ta tashi su tafi, a tare suka shiga bayin ya Haɗa mata ruwan ya zare mata hijab ɗin se ta ɗan ja baya amma bata sake shi ba, yace chan ƙasa "Toh yanzu kiyi wankan bari na fita" Cikin wani irin murya a shagwaɓe cike da sangarta tace "uhm uhm ni de don Allah karka fita ka barni ka Juya bayanka kawai" Babu yadda ya iya ya matsa daga bakin kofa ya juya mata baya, sharp sharp ta watsa ruwan tana ta kalle kalle, tana gamawa ta janyo towel ta ɗaura tana kokarin jan hijab ɗinta ta saka Bon ɗin da ta kama gashinta dashi sakwa sakwa ya kunce zuban gashin ya haɗu da ruwan dake jikinta yayi mugun firgitata ta kwalla ƙara, a hanzarce ya waigo kan yayi wani yunkuri ta faɗa jikinshi yayi saurin taro ta, yana cewa "menene kuma?" Siririn kuka ta saki tana cewa ya taimaka ya duba mata bayanta motsi taji kaman ƙadangaren ne ya dawo. Daga ita har shi jikinsu rawa ya ɗauka, zuciyarshi na bugawa da karfi karfi jin yadda take kara mannewa jikinshi hannunshi na cikin wet gashinta yana shafa bayan wuyanta zuwa bayanta, ya salaaaam ya ambata cikin ranshi jin yadda take kokarin kunce mai notikan kai gabaɗaya. Janyeta yayi suka fito daidai nan Fatima ta buɗe kofan ta shigo tare da nufo ciki gabaɗaya ai se idanunta suka mata mugun gani, baƙin kishi ne ya taso ya Rufeta idanunta har rawa suke yi.. "Me...me me zan gani haka? Me wannan?" Be tankata ba yana rike da fauza har zuwa dressing mirror saide bata zauna ba ta kara mannewa a jikinshi fuskanta cikin kirjinshi tana sauke numfashin dake gigitashi ba tare da ta san me take aikata mishi ba. "Zauna" Ya faɗa calmly. Zama tayi ya juya ga Fatima dake tsaye yace "Next time pls ki nemi izinin me wuri kan ki shigar mata, and bata da lafiya find something da zata ci don bazata bari na fita nema mata abinci ba" Har kaman zata lailayo Ashar ta maka se kuma ta fasa ta ficeee fuuu Sama sama ya shafa mata mai, kan suka tafi tare ya buɗe wardrobe ɗinta ya duba mata riga marar nauyi ta sanya, bayi suka koma suka yo alwala a tare daidai lokacin da ruwa ya tsuge sossai kaman da bakin ƙwarya Dukda daminar bata wani shiga sossai ba especially a ta north ɗin nan amma Abuja ba laifi suna samu akai akai tun last week. Shi ya ja su sallar magrib bayan sun idar ya bata Alqur'ani ta karanta, cikin tattausan muryarta ta fara karantawa wadda ya taimaka sossai wurin ƙara natsar da ita, se a sannan ya mike yaje ya duba Fatima ta kusa gama girkin ya sakata tayiwa husna wanka duka ranta a cunkushe, tunani kawai take me ya faru tsakanin fauza da Faizan da har yake riritata haka? Shi kuwa wanka yayi ya sake alwalan isha ya fito sanye da dogon wando da jallabiya, hannunshi waya ne yana magana da Baba prof da yake ta jimamin wannan abu, nema yayi da ya bata wayan shima kuma dama daidai lokacin yake isa wurinta se ya zauna daga gabanta ya miƙa mata wayan. Tana sawa a kunnenta ta fara hawaye cikin rawar murya suka gaisa da baban yake rarrashinta karta damu babu wani abu ta rike adu'o'in da ya bata sossai kuma ze kara mata wani, rikici ta sanya mishi akan ita kam zata dawo wurin jaddar ta tana jin tsoro. Da kyar ya shawo kanta zata zauna Abuja ɗin kan ya ba wa babanta wayan shima dae ya mata sannu da Allah ya kiyaye gaba haka jadda da mammi ma, bayan ta sauke wayan se ta miƙa mai ƙin ƙarba yayi. Idanunta da suka yi laushi yau ɗin gabaɗaya ta ɗaga se suka faɗa cikin nashi da ya kara lumshesu yana kallonta, a hankali tace "Yaaaya ga wayan" Ya rasa yadda take kiran nata yaayan da yake jinshi har cikin ɓargonshi ba ƙarya, a hankali yace "ba zan karɓa ba" chan ƙasa Kara marairaicewa tayi tace "Meyasa to?" "Me yasa kike son barin ɗakinki ki koma gida sbd wannan abu da be taka kara ya karya ba? Baki san kowacce mace da akwai abunda take fuskanta a nata gidan aure tana zama jaruma ne tayi over coming komai ba? Na Gaza wurin kula dake ne?" Ya karashe tambayar da wata murya da ta sakata maida kanta ƙasa kan ta girgiza tace "A'a ka yi hakuri" Yace "na hakura, tashi muyi sallah" Isha suka gabatar da kanshi ya fita ya karbo abincin don Fatima dangwalarwa tayi a dining ta wuce ɗakinta. Kasa hakuri tayi ta kira Auntyn ta take tambayarta meyasa bata fara ganin abunda tace ba, Auntyn tace mata an samu akasi amma ba shi ze sa su karaya ba, ta cigaba da zubawa sarautar Allah ido, rayuwar Fauza a gidan kaman a tafin hannunta yake. Husna ya ɗauka da tayi bacci a parlorn yayi ɗakin Fatima da ita, tana sauke wayan yana buɗe kofan da sauri ta gyara zamanta, a kan gado ya kwantar da ita yace "zata kwana wurinki yau" Juyawa yayi ya fita yana mamakin yadda Fatiman ta kasa zuwa tayiwa Fauza ko ya jiki ne, har ya taɓa handle ya dakata ya juyo fuskanshi ba yabo ba fallasa yace "kaman na ce miki Fauza bata da lafiya ko?" Tace "eh ka faɗa, me zan mata bayan girkin?" Ta faɗa cikin gatse. Yace cikin mamaki "wai dama haka zuciyarki yake ne ko yanzu ne ya koyi sabbin ɗabi'un nan? Fatima sannu bazaki iya zuwa ki mata ba? Wai me kika ɗau kishi ne?" "Me kuwa na ɗauke shi? Ni yaya meyasa kake min haka ne? Meyasa a ko yaushe abu ya Haɗa mu ni ce da laifi? Ni da nayi ɓari ko sannu ta min bare Allah ya kawo na mora? Gwara ni na mata girki ita ko ruwa ta kawo min? Duk baka ce komai ba se ni yanzu da ban san hawa ko Sauƙar ciwon munafurcinta ba zaka wani ce in je in gaisheta? Kayi hakuri ba zan iya ba" Dawowa yayi ya zauna ganganta yace "Fatima ki fahimce ni, babu wacce nake fifitawa tsakaninku illa ma ita da nake tauye ta, kina sane tunda ta zo gidan nan sati na shidda kenan nake ga ban taɓa ware kwana ɗaya tal da sunan nata ba, ban cika mata duk wani hakki na matsayin matata ba kina kallo baki taɓa ce min hakan ba daidai bane, annabi fa cewa yayi mafi darajar mace itace wacce zata taimakawa mijinta wurin bautar Allah in taga zai kauce ta dawo dashi daidai, duk na rasa wannan daga gareki..." Hawaye ta share tace "zaka ce haka ai tunda ta baka ka kwasa" Ya rasa me ke damun Tunanin Fatima, mikewa yayi ya fice tunda ta ƙi fahimta tana kan rashin daidai. Tsaye ya samu Fauza tsakiyar parlor tana ganinshi ta nufo shi yayi saurin saka hannu ya riƙe nata ganin kai tsaye jikinshi take shirin shigewa wadda illar da take mishi a yadda ya san kanshi idan be yi da gaske ba baze yi bacci ba yace "menene?" Tace "Motsi nake ji a ɗakina" Yace "Ina kin yi azkar kuma kin karanta Alqur'ani?" Kai ta gyaɗa yace "to ki yi yaƙini da hakan ki saka a ranki babu wani abu da ze iya cutar dake kinji?" Kai ta gyaɗa ya Janyeta suka yi ɗakin nata inda yace ta kwanta, zama yayi ta kwanta a kan pillow yana shafa kanta idanunta a lumshe yayinda shi kuma nashi ke kan fuskan nata yana kare mata kallo har bacci ya ɗauke ta. Fita yayi ya tabbatar da komai daidai a gidan kan ya dawo ya rage musu wuta ya cire jallabiyar tare da kwanciya da dogon wando kawai be damu da saka kayan bacci ba, har ya lumshe idanu ya tuna magungunan ta bata shafa ba. Sauka yayi ya ɗauko ya zo ya zauna tare da zuba mata idanu na mintuna kan a hankali ya fara sakawa a hannunshi ya shafa mata a kafafu, ya sake sakawa ya shafe hannayenta dashi, daga nan se gashin kanta ya shafa mata. Sauran na hannun nashi ne yake shafa mata a fuska a hankali wadda ya saka ta ɗan buɗe idanunta dake cike da bacci tana Kallonshi. 'Tsarki ya tabbata ga Allah da ya halicci wannan idanu' baze taɓa cewa ya taɓa ganin abunda har ranshi yake mishi kyau irin idanunta ba, a hankali yake shafa kumatunta idanunsu sarke da na juna se chan ta turo baki tace "bacci" cikin muryar da bacci ya ci karfi. "Yi baccinki an gama" Ya faɗa a natse kan ya miƙe ya adana magungunan ya dawo ya kwanta daga gefenta yana lumshe idanu, baya son kawo Tunanin komai a ranshi in yace ze yi tunanin wadda ya aika mata da wannan ƙadangare tabbas ze fara zato kuma ya san zunubi ne, in yace ze yi Tunaninta kuma tabbas ze iya Jawa kanshi damuwa wadda baya fata ya kasance yanzu don baze iya ɗaukar abu guda biyu ba idan abunda yake gudu ya kasance. Haka dae yayi bacci da blank thought, asubar fari ita ta fara buɗe idanu se ta ganta kwance dab dashi kansu a kan pillow ɗaya yayinda hannunta ke kwance bisa faffaɗar kirjinshi, a hankali ta kai idanunta fuskanshi da dim haske ya bayyana haske da kwarjininshi, dukda bacci yake yi but ba karamin kyau yayi ba sajenshi dake kwance lublub gwanin sha'awa. A hankali ta ɗago hannunta ta ɗan shafa sajen nashi tana mamakin yadda aka yi tun da chan bata taɓa ganin kyaun nashi ba se yanzu, karab taji ya riƙe hannun da take shafa mai fuskan, a hankali ya waigo yana kallon ta, kunya ne ya rufeta se tace "Ina kwana?" Daga haka ta zame ta sauƙa tayi toilet, murmushi ya saki kan shima ya sauƙa, zuwa yayi ya kunna Alqur'ani don da asuba sunna TV karatun Alƙur'ani mai girma suke sakawa, daga haka ya ɗauki jallabiyarshi ya fice dakinshi a chan yayi alwala ya zo ya fice masallaci. Ko da ta idar da sallah azkar tayi tare da karatun Alƙur'ani, bayan ta gama ta miƙe ta shafa magungunanta da kanta daga kai har kafa kan ta saka riga dogo marar nauyi, tana zama a cikin kujerun ɗakin yana shigowa. Ganinta haka ya sa ya sakar mata murmushi itama ta mayar mai tana sake cewa "Ina kwana?" Yace "kin tashi lafiya? Ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" Matsowa yayi kusa da ita tare da rankwafowa yana duba bayan wuyanta inda ƙadangaren ya bar tambari sede wayam babu, ajiyar zuciya ya sauke wadda numfashin a wuyanta se da ya sakata saurin kame jikinta tana ɗauke numfashi. Mikewa yayi yace bari ya ɗan kwanta, dakinshi ya wuce ita kuma ta mike ta fara gyaran ɗakinta daga nan ta sauka ta musu abin kari ita da husna, tana haurowa ta gamu da Fatima, abunda ya faru jiya ne ya dawo mata se tayi saurin kauda Tunanin Dukda gabaɗaya gidan babu wadda ya san ainihin su Fatima se ita amma bazata ce sune suka mata hakan ba tunda bata da shaida.. Har zata wuce se ta tsaya tare da waigo wa ta dube ta tace "Faɗan bayan fage na lusari ne, harara a duhu kuma baze sa in chanza rawa ba kirrr nake kallonku, wai baki yi mamakin yadda nake yawan faɗin cusa kanki kika yi wurin samun ya Faizan ba? Ko kwakwalwarki a toshe yake baya tunani? Toh duk wani sirrin ku yana tafin hannuna the next time kuka sake yi min abu makamancin haka ina me tabbatar miki za'a yi walƙiya... Karku yi gangancin tarar aradu da ka don tabbas kuka tara se kun samu, ni ɗin kafin Allah ce!" Tana kai nan ta nufi ɗakin Fatiman ta tado husna suka yi ɗakinta har lokacin Fatiman na tsaye tana juya maganan, kenan Fauza ta san suna da mission akan ahalin prof? Ta yaya? Kuma a ina ta sani? Da sauri ta nufi ɗakinta don kiran Aunty hankalinta a tashe. Fauza kam bayan tayiwa husna wanka ta zuba musu abincin da already ta hauro dashi suka fara ci, har sun yi nisa don har husna tana cewa ta koshi ya tura kofan ya shigo. A tsakiyar center rug ya samesu suna ta cin abinci, har a ranshi yaji sanyi ganin har ta iya yin girki kenan ta ji sauƙi, zama yayi husna na gaidashi.. Daidai lokacin ta gama itama ta fara tattare wurin ganin bata mishi tayi ba kuma ranshi ya riga ya biya yace "Ni baza'a bani breakfast ɗin bane?" Ɗago kai tayi ta kalleshi kan ta kauda don bazata iya faɗar abunda take son faɗa ba matukar tana kallon cikin idanunshi tace "Ni? Wani jagwalgwalon zan baka?" Kallon mamaki yake aika mata magana take shirin gaya mai ko me? Yace "Eh jagwalgwalon dae zan ci" Tace "ai wannan ba zaka iya ci ba, na tabbatar matarka da ta kware a girki ta tanadar maka hadadde ma kuwa" Kallon husna yayi yace "je parlor ki kalli cartoon" Da gudu ta tashi ta fice. Yace "Me kike nufi ne kam?" Ganin ta mike tana shirin tattare kwanukanta tace "Yaaya pls me yasa kake so se na fito na faɗa kai tsaye? Toh ina nufin ba zan iya baka ba gaskiya don jagwalgwale ne kaje wurin matarka ta baka me daaɗi.. Ko ba haka kace ba?" Tayi maganan tana kallon gefe... Mikewa yayi ganin da gaske take yayi saurin riƙe hannunta yana cewa "Toh yanzu zan cigaba da cin jagwalgwalon don raba muku girki zan yi kwana bibbiyu yadda addini ya tsara" Kai tsaye tace "ni kam ba zan yi ba" Ta karashe da murguda baƙi idanunshi gabaɗaya ya waro yace "ni kike yiwa rashin kunya da murgude murgude?" Me makon yaji haushi ma dariya take bashi ala dole fushi take yi. Tana kunkuni tace "ni dae ba zan yi ba bana so ai tun farko ba'a nuna ana so ba se yanzu! Ni de babu wani girkin da zan karɓa" Hannu ya kai ya dalli bakinta "ni kike yiwa kunkuni?" Haba ai se ta sakar mai kukan shagwaɓa har da bubbuga kafafu wai zafi... "Yaa ilahil alameeen" Ya furta akan lip ɗinshi kawai yana kallonta, yarinyar nan bazata kashe shi ba. Ganin kaman yayi fushi yasa ta dangwalar da abincin tana tura baki ta zuba mai, ba tare da ya kalleta ba yace "ɗauke kayan ki ba zan ci ba" Da sauri ta fara kokarin ɗaukewa yayi hanzarin rike hannunta suka zubawa juna idanu.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 26 "Wai da gaske ɗaukewar zaki yi?" Ya faɗa a marairaice, se ta saki ta tsuguna ta zuba mai tare da miƙa mai. Karɓa yayi yana cewa "thank you" Tana shirin magana Wayanshi ya ɗauki ringing, dubawa yayi se yaga Faisal suka gaisa yake tambayar shi me jiki, Seda ya kalleta kan ya amsa da da sauki, faɗa mishi yayi matansu zasu zo su duba ta. "Zaki iya tarban baƙi kuwa?" Ya faɗa bayan ya sauke wayan. Kai ta gyaɗa tace "Sossai ma, ni da nake so in ga mutane mutane su ganni.." Yace "families ɗin Faisal da Jafar ne wai zasu zo" Tace "Tohm Allah ya kawo su lafiya" Ya amsa da 'Ameen' Bayan ya gama ci yaje ya shirya ya zo ya tambayeta ko akwai abunda zata buƙata ta amsa da babu kan ya duba Fatima ya faɗa mata tare da umarnin ta fito suyi aikin bibbiyu sbd sauƙaƙawa, ta dae amsa yana fita ta kwanta abin ta ta fara bacci. Girki me rai da motsi Fauza tayi musu, dukda bata yi yayi yawa ba saide tayi varieties ta tsara shi kuwa yayi kyau sossai, ita da husna suka dinga jigilar kaiwa sama, bayan ta gama ta je tayi wanka. Bata shafa mai ba se ta shafa magungunan nan da prof ghali ya bata ta shirya cikin lace riga da skirt ne da dinkin yayi matukar amsarta, ga colourn lace ɗin blue da onions se ya haske fatarta, ɗan kwalin irin hular nan ne so gyara parking ɗinta kawai tayi ta sanya ta nemi jewelries da suka yi matching ta saka. Tana cikin shirya husna ya turo kofanta da sallama, ta amsa tare da ɗagowa. Gabaɗaya idanunshi ya sake a kanta yana karewa halittar Allah kallo, tambayar kanshi ya fara wai me yake ji a kan yarinyar nan ne takamamme? Ko ta ina ta cike mishi zuciya da Tunaninta, idan ya fita yana marmarin ya dawo ya ga shigarta da kwalliyarta, hancinshi ya shaki sassanyar turarukanta masu saukar da natsuwa, bakinshi a ko yaushe yana marmarin tasting abincin ta... "Yaaaya sannu da dawowa" Abunda kenan ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi. Kasa riƙe compliment ɗin yayi yace "Masha Allah kin yi kyau" Tana murmushi tace "thank you" Yana kallon husna yace "Na gama shirye shiryen tafiyar husna fa jibi ne da misalin karfe 5 na yamma jirgin su ze tashi" Da sauri ta kalleshi kaman zata yi kuka tace "Wai dama da wuri ne?" Kai ya gyaɗa yanayinta gabaɗaya se ya sauya, yace "Ki bar musu nasu ke ki haifi naki tunda dae kayan aro baya rufa asiri" Yi tayi kaman bata ji ba, se ma tace "kaman sallama ko?" Fita yayi ta bi bayanshi aiko iyalan abokanshin ne da su kansu kasancewar Saturday ne, Fauza kaman ta san su kuwa tayi musu tarba na mutunci bata bar matan anan ba ta ja su ɗakin ta bayan sun gaisa da mazan suka mata sannu da jiki. Yaran Faisal biyu mace da namiji matarshi hafsat da ciki, se na Jafar uku matarshi firdausi tana goyon na huɗu. Ruwa ta gabatar musu da fruits suka sake Gaisawa sossai hafsa ke gayamata yadda Afnan ke kai mata labarinta nan suka ɓarke da hira kaman sun jima da haɗuwa, mikewa tayi ta fita musamman ta je ɗakin Fatima ta shaida mata da zuwan baƙin amma bata ko tanka ta ba. Su ɗin sun riga sun jima suna son zuwa gidan Faizan ɗin saide Allah be yi ba ko da suka ji ya ƙara aure ma su suna team uwargidaye ne abun mamaki se suka ga Amarya ke ta ina za'a saka ina za'a aje dasu. Abincin ta gabatar musu bayan sun yi sallah suka ci suka yi nak suna cewa ita da bata da lafiya ta iya yin girki haka, tana ta murmushi kawai. Yini sur suka yi amma Fatima bata leko ba se gab zasu tafi ta fito suka gaisa kawai ta koma, Hafsat da Firdausi wayayyun mata ne kuma sun fahimci kishi irin na Fatima a take suka dau yi mata lecture da yadda zata karkatar da hankalin miji kanta ita kaɗai, kaman yadda Burin kowacce macece ace ta zama tauraruwa a gidan mijinta kuma sarauniyar birnin zuciyarsa. Ta Haɗa su da turarukan wuta kuwa ta zubawa yaran snacks masu yawa da Faizan ya saya musu suka yi ta murna, har mota suka raka su suka tafi. Juyowa Faizan yayi yana kallonta fuskanshi cike da murmushi na burgewa da jinjina yace "Allah ya miki albarka" Murmushi tayi tace "Ameen" A tare suka koma be zauna ba shi ya taya ta suka tattare gidan tsab, tana tsaye kitchen tana shirin wanke wanke kenan taji kamshinsa ya bule kitchen ɗin waigawa tayi se ta ganshi tsaye sanye da red riga marar hannu ta shan iska da ya bayyana damatsanshi da suke a murɗe se three quarter milk, hannayenshi zube a aljihun yana kallonta. Maida kanta kawai tayi ga dauraye kwanukan kan ta zuba ruwan sabulu se ta nufi drawer don ɗauko lemon fresh da ta ɗaura shi chan sama sbd husna dake yawan son wasa dashi. Hannunta ta miƙar har tana ɗagel don ɗauko wa kawai taji hannun mutum bisa nata, da sauri ta waigo se fuskanta ya kusan dukan kirjinshi sbd kusantota da yayi sossai, idanu suka zubawa juna na seconds kan yayi gyaran murya yana cewa "Amm jikinki ba wani matsala ba?" Fuskanshi na kusan kan nata sbd tsawo sossai da ya fita hakan ya sa ta kasa magana se da ya ɗan matsa baya kan ta saukar da kanta ƙasa tace "Ai na warke" Wani dogon tsaki da suka ji yasa duk suka kalli kofa, Fatima ce tsaye tana Kallonsu hawaye ne ke zuba a idanunta ta fara cewa "Wallahi Allah se ya saka min, Allah baze taɓa barinki ba Fauziyya kaman yadda kika yi min kema Allah ya miki, kin zo kin sameni gidana ina zaune lafiya da mijina kika shiga tsakaninmu kika juye hankalinshi gabaɗaya to Wallahi ban yafe miki ba" "Kai kuma" ta nuna shi. "Allah kaima se ya bi min hakki na, watana biyar a gidanka ka kara aure, a wata biyar da nayi ban taɓa yin sati ɗaya cikakke da kai ba kana chan gobe kana nan amma tun zuwan Fauziyya gidan nan baka taɓa fita daga Kasar nan ba, kai ka ce min baka iya komai a harkar kitchen ba, zan iya rantsuwa baka taɓa shiga kitchen da sunan aiki ba amma yau gashi nan kana taya ta... A haka kake cewa kana min adalci Toh wlh ban yafe ba idan ina da hakki Allah ya bi min..." Yadda take kuka duk suka tsaya suna kallo, kan Fauza ta taɓe baki ta nufi gaban kayan wanke wankenta ta fara wankewa, shi kuwa a natse ya isa gabanta ya sa hannu ya riƙe nata ya fusge ta suka fice be tsaya ko ina ba se Ɗakinta ya daka mata tsawa "wai me yake damunki ne Fatima?? Me yasa bakya so kiga an zauna lafiya? Meyasa kika kasa sakawa zuciyarki salama? Kullum ƙorafi an yi miki kaza an yi miki kaza? Yanzu da zan yi baƙi ban taka har ɗakinki na faɗa miki ba amma me kika musu? Babu. da babu Fauziyya haka zan kunyata? Ke baki san zuru ba? To karki yarda ki kai ni bango ba zan lamunci wannan ba, ki sani na raba muku kwana jiya da yau kwanan ta ne gobe ke zaki ci gaba, kaman yadda bata sa miki ido a naki ba karki saka mata a nata bana son fitina... Kin gane ko?" Kallonshi kawai take kaman bakonta tunda ta shiga gidan yau ne rana na farko da ya zage ya rufe ido yake ta mata faɗa Dukda ita har lokacin bata ga laifinta ba, son shi da take kawai yayi yawa shine laifinta, irin attention da yake ba Fauza da take so kawai shine laifinta? Kuka take yi sossai tana jin kaman tayi hauka. Lallai Mahaifiyarta bata kyauta mata ba da ta kwadaitar da ita Faizan tun bata gama sanin menene so ba, son shi yayi mata zurfi wadda bazata iya Daena ƙorafi ba in har akan wata macece. Fita kawai yayi ya kyale ta. Be koma kitchen ɗin ba se yayi ɗakinshi kawai, Fatima na da matsala abubuwa dayawa da tayi tayi a farkon aurensu se yanzu yake ganin rashin dacewarshi ko dama sbd ita kadai ce kuma he was new in the system yasa be gani ba amma yanzu duk asalin halayyar ta kishi ke hankaɗosu. Har dare ma be sake haduwa da kowaccensu ba, se da ya dawo isha ne ya shiga ɗakin Fauza itama ganin ranshi har lokacin ba'a sake ba yasa bata ce komai ba ta gabatar mai da abinci da tea ɗinshi. Yana Ci ya dube ta yace "gobe zan koma wurin Fatima pls idan tayi kwana biyu ki cigaba da naki and ki dinga ajiye mana a dining zamu ke haɗuwa muna ci mu duka that should be the policy" Tace "Toh" Yace "jibi da safe zamu tafi yiwa Husna shopping" Ta amsa "Allah ubangiji ya kaimu" Ya so ya kawo maganar waya don Jafar ya kirashi wai matarshi na son layin Fauza don sun manta basu yi exchanging ba se kuma ya fasa don har yanzu be jin ze iya saya mata waya tukuna. Ranar dae kam kowa ɗakinshi ya kwana, tayi kwanciyarta da husna. Sunday ma ya ɗan yi short tafiya kwata kwata basu haɗu ba se dare shima abinci ya ci wadda Fatima ne ta karɓa tunda yamma ya riga ya shiga, saida ya tabbatar basu da wani matsala kan ya wuce room ɗinshi Fatima ta bi bayanshi Fauza kam ko a jikinta ta kama husna suka yi ɗakinta. Washegari Fatiman ce tayi breakfast itama tayi wanka ta shirya cikin Atampha dinkin bubu, sanye da kaftan dinkin zamani ruwan ƙasa ya fito, ya haɗu har ya gaji. Itama Fauza Abaya ta saka milk and brown tayi kyau sossai barin ma ɗan face ɗinta da ya fita a Tarhan da tayi, ta gaishe shi kan ta gaida Fatima a dakile ta amsa, baki Fauza ta taɓe tare da serving husna tayi serving kanta tunda Fatima tayi serving mijinta ne kaɗai. Quitly suka ci abincin Dukda ita kam Fauza kaɗan taci ta miƙe ta koma parlor tana jiran shi. Kallon Fatima yayi yace "Am kin kuwa san yau da yamma husna zata bi iyayenta?" Kai ta girgiza tace "ban sani ba tunda babu wadda ya faɗa min" Kallonta yayi kaman ze yi magana se kuma kawai ya fasa, ya lura harshen Fatima ba a kame yake ba Sam bata san yadda zata ke mai magana ba. Mikewa yayi yana goge bakinshi da tissue hannunshi rike da husna suka fito parlorn yace "mu je ko?" Mikewa Fauza tayi Fatima tayi saurin cewa "Ina zaku? Ko ka manta kana cikin girki na ne?" Yace "don ina cikin girkin ki se aka ce ba zan fita da fauza ba? Ko ke kika ajiyeni da dole se kin san duk inda zani?" Fauza dae bata ce musu komai ba ta kama hannun husna suka nufi ƙasa. Yace "yarinyar nan husna kaman yadda take ƴa a wurin mu haka kema amma ko kallon arziki da mutunci ba zan ce ya taɓa hada ki da ita ba, ina faɗa miki zata tafi yau amma me? Kina wani bada amsa cikin gatse to in miki yaya kike so?" Yana kai nan ya nufi gangarawa abunshi. A gaba ya samu husna ita tana zaune baya ya ja motar suka fice, shopping sossai suka yi mata tana ta basu dariya da hirarrakinta, they all enjoyed the moment Har azahar don Fauza bata da lectures kan suka biya suka ci abincin rana a yadda Fatima ta gayamai bazata dawo ba se huɗu tun jiyan yasa be ma tuna wani jira ta koma ta mai girki ya ci ba. Daga nan suka yi gida Fauza ta haɗe mata kayan tsab. Sam Faizan be so ta koma ita ɗaya ba amma baze iya kaita ba don akwai tafiyar da ze yi Tuesday da safe kuma ze yi 2-3 days. Da farko ya tuna ko su je da fauza sede bata da visa, ko international passport be yi tunanin tana da shi ba, Seda suka yi la'asar kan suka fito suka tafi Airport... Suna tsaye wata cabin crew ta iso a shirye cikin irin shigar sun nan bakinta ya ji hot red lipstick se yanga take yi.. "Sir good evening" Ya amsa fuskanshi ba yabo ba fallasa yana nuna mata husna yace "she's my niece nd she will be flying with you guys pls take good care of her" Ita ce shugabar crew ɗin na yau hakan ya sa yake bata amana kuma sun san shi bashi da wasa, baya shiga harkarsu idan har ba maganan aiki bane, gasu Allah ya ɗaura musu maitarshi da kwaɗayinshi, a yangance tace "Worry not sir, we will make sure we give her all the care and attention from the boarding to departing" Yace "Good" Fauza ya kalla se yaga duk fuskanta ba fara'a kaman ɗazu, ya san duk kewar Husna zata yi, dukawa tayi tana rike da hannun husna take ce mata ta gaida kowa da kowa in ta isa. Kaman kar su Rabu haka tayi ta ɗaga musu hanu seda suka bace kan Fauza ta fara sauke hawayen da take rikewa dama bata son yin kukan ne sbd husnan. Kawai ji tayi lallausar hannunshi ya shiga cikin nata yana matsewa a hankali alamar rarrashi. Zare hannunta tayi suka nufi mota, har suka isa gida bata ce mishi komai ba kewan husna duk ya dameta, hakan ya sa suna isa ya je ya duba wayan nan ya bata akan ta kira su jadda. Ɗakinta ta shiga ta kira su kuwa sun jima suna ta waya har Amminta ta kira suka gaisa saide bayan nan bata ce komai ba ta kashe wayan, tsintar kanta tayi da gwada saka layin sakina ta kira, ringing na karshe ta dauka "Ke! Fauza ce" Ihu sakina ta saki tana cewa tana ina ne a Abujan? Sun yi ta neman layinta shiru wannan ne sabon layinta? Tace na mijinta ne. Rahama ce ta karɓa take ce mata Zubair ya kusa haukace musu akan ta kuma har yanzu be hakura da neman location ɗinta ba har fa cewa yake ze kai su baba court sbd an mata auren dole. Dariya tayi tace "Zubair kenan" Sam bata san ya shigo ba se ji tayi ya zare Wayanshi daga hannunta yana yi mata wani irin kallo kan ya juya a fusace ya fice yana buga kofan da karfi... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 27 Ba karamin tashi hankalinta yayi ba ganin yadda ya fita a mugun fusace.. "Innalillahi wainna ilahi rajiun na shiga uku! Yanzu me ze yi tunani?" Ta furta tana mikewa tsaye, bata taɓa jin buƙatuwar wani ya fahimce ta ba kab rayuwarta se yau, ta san yanzu Fatima ta riga ta shiga ɗakinshi da kyar ta iya barin wa gobe ta ga abunda hali ze yi, wlh Allah ya gani ba da wani niyya mummuna ta kira sakina ba kuma ita yanzu Zubair baya cikin rayuwar ta don har ta mance dashi ma. Haka dae tayi wanka ta zo ta kwanta ko abinci bata nema ba zuciyar ta fal tunani, washegari da safe bayan ta idar da sallah tana zaune tana azkar taji alamun tashin mota, da sauri ta miƙe taje jikin window se ta hangi motar shi na fita, ajiyar zuciya ta sauke ta dawo ta zauna da gaske fushi yayi? Ta tambayi kanta don ba zata Iya tuna sadda ya fita be gayamata ba tunda suka ɗan fara shiri. Gari yayi haske taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin jalbab ɗinta dogo har ƙasa don tana da lectures, fitowa tayi bayan ta sha cereal ta zuba chocolates masu yawa a jakan bayanta, Fatima ta gani zaune tana karyawa. Kaman ba zata mata magana ba se kuma tace "mun tashi lafiya?" Ko kallonta Fatima bata yi ba, zama tayi tana jiran ta ko don ta san tana jiran ta ne ita kuwa ta fara jan lokaci, ganin zata ɓata mata lokaci har a shiga lectures yasa ta miƙe ta fice. Mai gadi ya gaida ta yana buɗe mata gate ta taka da kafa har ta samu taxi ta ɗauki shata ta wuce school. Se karfe huɗu ta dawo gidan nan ma da taxi don bata ga Fatima ba, Seda tayi sallah ta zo ta shiga kitchen ta fara girki sanin itace yau da girkin, tuwo tayi mishi na doya da miyar ɗanyen kifi bayan ta gama taje tayi wanka tare da sallar magrib ta shirya cikin kananun kaya, ba karamin kyau tayi ba tayi isha kan ta fito ta zauna a parlorn saman Dukda bata ji motsin shi ba. Se a lokacin Fatima ta shigo basu tankawa juna ba, ita dae Fatima ganinta yasa ta san bata san mijin da ake yiwa kwainanen baya ma ƙasar ba, dariya ta sheke dashi tana cewa "lallai kuwa za'a yi jiran gawon shanu" Tana kai nan tayi wucewarta ciki, ganin har karfe tara be shigo ba yasa tayi Tunanin ko baya ƙasar, ranta dae ba daaɗi kaman yadda tun safe yake har Afnan take tambayarta tace babu komai, yau gabaɗaya abu mai nauyi be shiga cikinta ba, tuwon ta dibi ɗan kaɗan ta ci kan ta tattara taje ta adana a frigde daga nan ta haura tayi shirin kwanciya ta kwanta. Washegari bata yi breakfast ba miyan kifin ta yi microwaving ta ci da bread, yau ma bata jira Fatima ba tayi ficewarta yau ma dae haka ta kashe ranar da tunani, lectures ɗin ma bata wani fahimta.. A kwana na ukun har kuka tayi, ta rasa gabaɗaya me ke damunta da fushin shi, da a gidansu ne da yanzu in duka ne an daketa an wuce wurin amma shi ba duka ba zagi kawai ya ɓace mata ba tare da ta san inda yayi ba alhali yana fushi da ita. Hadari ne sossai ya haɗe garin har ana iska, Afnan ta riga ta wuce ita kuma tana tsaye tana neman taxi da sauri ta sanya hannu ganin motar Fatima amma ko bata tsaya ba tayi wucewarta kuma ta tabbatar ta ganta ba bata ganta ba, da kyar ta samu wani taxi Dukda ya tsula mata kuɗi bata damu ba ta shige da sauri sbd ita bata son ruwa ya taɓa ta, ko yaya ya jiƙata se tayi mugun zazzaɓi. *** Karfe shidda ya iso gidan yayi parking motan shi da dama Airport ya kan bari yayi tafiyar shi, Gaisawa suka yi da gate man kan ya wuce ciki yana kallon motar Fatima dake nuna alamun bata jima da shigowa ba. Gidan ya shiga yana jin wani kewa chan ƙasan ranshi da duk yadda yayi kokarin dannewa ya ƙi dannuwa, lumshe idanu yayi ya buɗe a sadda ya shaki sassanyar turaren wutan da ta kan yi anfani dashi wa gidan, a natse ya haura yana jin yadda aka tsuge da ruwan kaman da bakin ƙwarya. Ɗakin Fatima ya fara shiga tana ganinshi cikin farin ciki ta tare shi tana mishi sannu da dawowa, ya amsa fuskanshi a sake kan yace bari ya duba Fauza se yaje yayi wanka. Tace "Ai ina ga bata dawo ba fa..." "Bata dawo ba?" Ya watsa mata tambayar cikin mamaki. Kanta ta mayar ƙasa tace "eh bata dawo ba don ban ji shigowarta ba" Yace "ban gane ba, ina ce tare kuke tafiya ku dawo? Ya aka yi ke kike gida ita bata nan? Me ze ajiye ta a waje har an yi magrib?" Tace "ni dae wlh ban sani ba, abunda na sani dae tunda ka tafi bata sake tsayawa mun tafi tare ba taxi take fita ta hau haka dashi take dawowa Dukda nayi kokarin jan hankalinta akan baka son ɗabi'ar shine ma musababbin da yasa ka saya min mota amma taki saurare" Be tanka ba sbd yadda ya sake jin sabon ɓacin rai na rufe shi a kanta, duk yadda yake kokari akan yarinyar nan me yasa take so ta fara bashi matsala? Sau nawa ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi? Ɗakinta ya wuce kamshin ta na tashi a ɗakin wadda ya dawo mishi da sabon kewanta kaman yadda ya kashe kwanaki biyun cikin kewar nata ko abincin kirki bai iya ci. A balcony ɗinta ya tsaya dake shine ke facing gate, ya rasa hukuncin da ya kamata ya ɗauka a kanta, sheɗan ke ta wassafa mishi kila tana chan da Zubair tunda har ta fara ambatarshi, hangar taxi yayi ya sauke ta, ba lema hannunta hakan yasa cikin hanzari ta iso gate ɗin ta fara bugawa saide gate man ɗin kaman baya kusa don baya jinta, ta kai mintuna biyu tsaye cikin ruwan tana knocking da ƙarfi sede ƙaran ruwa ya hana gate man ɗin ji, ya so ya kyale ta ruwan yayi ta jiƙata se kuma ya ga baze iya ba. Da sauri ya juya ya nufi fita ganin ta juya itama ta bar gate ɗin da sauri sauri, da hanzari ya buɗe gate ɗin ya fara duba ta, chan ya hangota tana tafiya tana dube dube ko zata samu inda zata fake kan ruwan ya tsagaita.. Sam bata san da isowar mutum ba se ji tayi an ɗaura mata wani suede me kauri wadda a take ta dena jin Sauƙar ruwan jikinta, a hankali ta ɗaga kai se suka Haɗa idanu ruwan na zuba a jikinshi sossai. "Yaa..." Be bata daman magana ba ya riƙo hannunta suka juya suka yi gida, a kofan ɗakinta ya saketa ba tare da ya bi ta kan suede ɗinshi ba ya shige dakinshi. Ta ɗan jima tsaye a wurin kan ta shige ta cire suede din ta ajiye ta wuce toilet ta cire kayanta da ya jike gabaɗaya ta hada ruwa me zafi sossai tayi wanka, a ɗakin ta Haɗa tea me kauri da zafi ta sha jin jikinta ya fara rawa alamar zazzaɓi. Da kyar ta iya gabatar da sallah kan ta hau gado ta ja bargo ta shige tana rawar dari. Yayi wanka shima ya sauya kaya ya fito ya duba Fatima yace ta sama mai wani abu marar nauyi don yana jin yunwa, ranta fal farin ciki sanin yayi fushi da fauza ne tunda girkin ta ne amma ya saka ita tayi mishi. Kitchen ta shiga ta sama mai abinci yana zaune a parlor yana kallon Tvc news ta shigo ta ajiye mai, kallon kofan Fauza yayi kan ya maida kan abincinshi ya fara ci yana Tunanin me ya hanata fitowa ta nemi wani abu ta ci? Har ya gama ci suna tare da Fatima, tana ta kokarin jan hankalinshi sede idanunshi ne kawai gareta, tana tattare kwanukan ya miƙe ya nufi ɗakin Fauza ɗin. Kwance ya tarar da ita tana rawar ɗari sossai, yaye bargo yayi ya taɓa gefen wuyanta wani irin zafi jikinta yayi da har yayi saurin zare hannunshi, da kyar ta buɗe idanu ta kalleshi.. Harara ya zabga mata, kan yayi tsaki ya wuce toilet ɗinta towel ya samo da ruwa ya zo ya karasa yaye bargon yana ɗauke idanunshi daga kan santala santalan cinyoyinta da suka bayyana, ɗagota yayi ya fara saka Towel nan a ruwa yana shafa mata, wani irin numfashi take saukewa wadda ke rikirkitashi ganin ruwan baze Sauƙar mata da zazzaɓin ba gashi ta fara mishi kananun kukan fita hayyaci ya sa ya rufe ta da faɗa don abubuwa dayawa ne suka haɗu mai. Sossai yake mata faɗan abubuwan da ta aika ta ɗin, harda taurin kanta take shirin dawo mai dashi to baze ɗauka ba, shi ba lusarin namiji bane da ze ke gindaya mata sharudda tana tsallakewa he could remember vividly yadda ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi amma me ta aikata? Har tana tuna wani katon gardi ɗan shaye shaye cikin gidanshi. A hankali ta sabule daga hannunshi da yake rike da kafadunta ta faɗa jikinshi tare da kankameshi tana kuka kawai don bazata iya magana ba. Tsit haka maganan ya yanke mai, ya sanya hannu ya tarbeta, fuskanta take ta gogawa bisa kirjinshi alamar tana kara fita hayyacinta ne, da sauri ya kwantar da ita ya kashe wutan ɗakin tare da zare jallabiyar jikinshi, ya saura daga shi se boxer, Rigan jikinta ya cire mata don bata taimakon body contact kan da safe su tafi asibiti. In a romantic way ya sanya lallausar hannunshi ya ɗagota a hankali ya kwanta kan yayi mata masauki a faffaɗar kirjinshi, a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya, mannewa ta sake yi ta shige jikinshi kaman zata tsaga shi ta shiga ciki sbd sanyi da taji jikin nashi na dashi wadda hakan ya bashi daman sake kanainayeta ya cusa fuskanci tsakanin wuyanta yana sauke numfashi me nauyi, cikin wani irin salo yake shafa mata sajen nashi a hankali hankali cikin wuyanta, siririn ƙara ta sake tana kara kankameshi jin ya saka babban ɗan yatsan kafan shi yana wasa da tafin kafafunta, duk su biyun sun haukace da wannan masifaffen body contact da suke samu, shi da yayi da niyar taimako ma ya fi azabtuwa. Hmmm wani irin moment ne suka yi spending wadda baze Mantu ba, gabaɗaya seda ta gigitashi da albarkatun jikinta wadda duk ba cikin hayyacinta take hakan ba, ba jikinsu kaɗai ba a lokacin ze iya rantsuwa cewa numfashi ma guda ɗaya suke yi ba biyu ba, Seda suka shafe mintuna sama da talatin suna rabawa juna temperature ɗinsu kan ya mirginata, hancinshi yake gogawa da nata yana jin yadda su biyun duka numfashi ta hanci yayi musu kaɗan suna Haɗawa da baki, a hankali ya fara brushing lip ɗinshi kan nata, yana kokarin haɗe lip ɗinsu tayi wani miƙa da ya tabbatar da zazzaɓin ya sauka, yaraf ta dawo kan pillow a take wani wahalallen bacci ya sure ta, zamewa yayi ya kwanta daga gefenta yana jin yadda zazzaɓin tan ke shirin dawowa jikinshi. Bacci me nauyi ne ya kwasheta yayinda shi kuwa yace be san zance ba, janyo ta ya sake yi jikinshi ya rufa musu bargo sbd jikinshi wani irin rawa yake yi... Ya fi awa kwance cikin wannan yanayi Ganin in yana cigaba da barin ta haka a jikinshi komai ze iya faruwa ya sa ya miƙe dafe da marar shi ya fice a ɗakin. Kitchen ya shiga ya matsa lemon tsami a lipton ya kwankwade tunda yau ba kwanan Fatima bane bare ya rage wani abun, tunda yake be taɓa jin irin wannan sha'awa ba se yau, ɗakinshi ya shige ya zube rub da ciki bisa gadon shi yana juye juye. Ita kuwa bacci tayi sossai, chan wuraren karfe uku na dare taji kaman ana kiran sunanta, cikin gigin bacci ta buɗe idanunta se taga ɗakin gabaɗaya ya sauya mata ya koma wani irin Ƙango me cike da abubuwan razanarwa, a firgice ta miƙe sede bata iya ambaton komai ba kaman ɗaure mata baki aka yi ko numfashi da kyar take iya ja amma bakinta ya ƙi furta komai. Wasu irin abubuwa taga suna motsi daga jikin ginin ɗakin, sanyi taji me yawa a jikinta waigawar da zata yi taga wani irin hallita da bata taɓa sanin akwai irin shi ba baƙi sidik, me munin gani da razanarwa, ƙara ta saki wadda taji muryar yayi amsa kuwwa iya ɗakin, da sauri ta sauƙa jikinta na rawa ta nemi riga ta saka ta suri hijab ɗin sallarta ta saka, jakan da ta dawo dashi jiya ta zara ta fice da sauri daga ɗakin. Parlorn kasa taje chan lungun dining ta makale ta takure Kaman wacce ta rasa gata, jikinta wani irin karkarwa yake gabaɗaya bazata ce ta san me take yi ba, banda tsanar gidan da tsananin tsoronshi babu abunda take ji. Tana nan har aka kira sallar asuba fuskanta har ya kumbura da kuka, kaman wuta ake rura mata a gidan haka take ji, tana ji ya sauko da nufin tafiya masallaci, da sauri ta miƙe ta bi bayanshi yana fita itama ta fice daga gidan ko waiwaye babu.... **Ayi comment in takarkare in baku na dare😎** DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 28 Saboda rashin baccin da be samu ba jiya ya sa ko azkar da kyar ya iya yi ya mike ya dawo gidan, ɗakinshi yayi direct ya kwanta ba shi ya tashi ba se wuraren karfe goma sha ɗaya, wasai haka ya ji shi Adu'a yayi kan ya sauƙa ya wuce toilet ya watsa ruwa har a lokacin ze iya cewa yana jin tsadaddiyar jikinta cikin nashi, yana jin duk wani moment da suka yi spending a jiyan cikin ƙashi da ɓargonshi. Haka ya gama wankan ya fito ya shirya cikin kananun kaya, fitowa yayi yana baza kamshinshi me natsuwa da kwantar da hankali, ɗakin Fatima ya fara dubawa bata nan da alama ta tafi school, ɗakin Fauza ya nufa haka kawai ya tsinci kanshi da sakin murmushi. A hankali ya tura kofan saide turus ya tsaya ganin kaman an yi wasan kura a ɗakin, komai kaca kaca a wargaje abinda ba ɗabi'arta ba. Sunanta ya fara kira yana shiga ciki ciki sede bata kan gadon, bayin tura ya shiga nan ma bata nan. Saukowa yayi kasa ya je wurin Peter yake tambayar shi ya ga fitan Fauza ko tare suka fita da Fatima? Yace a'a Fatima ita kaɗai ta fita kuma shi yana kofan tun asuba be ga fitan ta ba, hankalinshi ya fara tashi da sauri ya koma saman ya fara kwala kiran sunanta saide babu ita ba alamar ta. Fitowa yayi ya shiga mota ya ja da matsiyacin gudu se makarantar su, Afnan yake ta nema ko ze gansu tare sede be ganta ba, wurin Faisal yaje yace ya kira mishi Afnan ko suna tare da fauza? Kiranta yayi tace tun jiya da suka rabu basu haɗu ba, yau basu da lecture ma da safen. Tun Faizan na ɗauka wasa sede hankalinshi yayi matukar tashi ganin da gaske bata nan ɗin, Faisal ne ya tuka shi suka je police station suka yi reporting, polisawan sun tabbatar saide in da kafafunta ta fice da sakacin me gadi in ba haka ba da shiga aka yi aka ɗauke ta se an gane bare da yace har tsakiyar dare ma suna tare. "Iyayen ku na nan garin ne?" Dpo ɗin ya tambaya. Faisal ne ya amsa da "A'a suna Adamawa" "to ko gida dae ta tafi?" Dpo ya faɗa. Faizan da ranshi ya soma ɓaci yace a tsawace "Me aka mata ɗin da zata tafi gida ba tare da sanina ba? Ni fa mijinta ne!!!" Ya faɗa cikin hargowa, Kafadanshi Faisal ya dafa yace "Calm down please Faizan ka natsu, ban san ka da hayaniya haka ba.." Yace "Kar in yi hayaniya Faisal? Matata fa na nema na rasa na kawo musu report kuma me makon su yi aikinsu sun tsaya suna faɗan wasu abubuwan da baze yiwu ba, ana tafiya gida haka kawai ne a aure?" Dpo ɗin yace "I'm so sorry, ka natsu please ka san komai na iya faruwa ne shiyasa muke maka waennan tambayoyi kila ka mata wani abin ɓacin rai da ze sa ta bar gidan ta tafi gida ba tare da saninka ba, amma tunda kace ba hakan bane yanzu zamu fita mu fara bincike ka kwantar da hankalinka komai ze tafi daidai" Fitowa suka yi sbd azahar da ake ta kira suka tsaya suka yi sallah, Faisal ya dube shi yadda gabaɗaya kamananninshi ya sauya jijiyoyinshi suka tashi suka yi raɗa raɗa yace "Faizan ko zamu kira su baba?" Kai ya girgiza yace "Ko gidan ta tafi in dae a mota ne zuwa yanzu be ci a ce ta isa ba... Amma me na mata da zata tafi gida?" Ya faɗa cikin sanyin murya. Dafa kafadanshi Faisal yayi ya bubbuga alamun rarrashi kan suka miƙe suka fito se ga Jafar shima suka haɗu suka fara yawon nemanta da polisawa, a Airport babu jirgin yola da ya tashi a ranar ma gabaɗaya ya gayamusu amma basu yarda ba seda suka je suka gama binciken su kan suka nufi tasha... *** Ita kuwa Fauza bazata ce ga takamammen Tunanin da take yi ba, Sam kaman makuwa tayi ne ko yaya haka dae ta miƙi hanya ta tafi sossai Dukda wani irin sanyi da ake zabgawa na asuba, bakin wani masallaci ta zauna ana sallar asuba limamin na karatu cikin Suratul baqara ayoyin ƙarshe, a hankali take jin natsuwa na zuwa mata, itama ta karɓa taci gaba da binshi har ya kai karshe yayi ruku'u. Da sauri ta miƙe ta shiga ciki ta samu ruwa tayi alwala kan ta gabatar da sallar itama nan fa ta ji bakinta ya iya fara ambaton Allah amma zuciyarta har lokacin baƙi kirin babu abunda ta tsana irin Abuja da gidan Faizan. Fita tayi daga masallacin ta tafi ta tari taxi yana tsayuwa tace "Park zaka kaini" Yace ta shiga, tashar Jabi ya kaita. Ta biya shi sbd akwai kuɗi a jakan, taje ta shiga mota nan da nan motar yola ya cika suka ɗauki hanya, Seda ta tabbatar sun bar yankin Abuja kan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya wani wahalallen bacci ya ɗauke ta. *** Su kuwa tashar mararraba suka fara zuwa duk motocin yola babu irin sunanta ma kuma duk yadda ya musu misalin kamanninta suka ce basu ga me irin kamannin anan ba. Daga nan Suka yi dei-dei park nan ma neman duniya da kwatance suka ce basu ganta ba, suka nufi jabi Dukda shi kam Faizan hankalinshi Sam be bashi gida ta tafi ba sbd be san abunda ya faru da zata tafi gida ba haka dae suka je, aiko first turn da aka duba list se ga sunanta, kurawa sunan idanu yayi kwarai itace ma ta rubuta da hannunta don ga rubutunta nan zarzar. Me makon yayi farin ciki ba ɓata tayi ba se wani sabon ɓacin rai ya ziyarceshi, ta ɗaga musu hankali a banza... "Karka ɗauki fushi ba tare da ka san dalilin ta ba Faizan" Faisal ya faɗa a sadda suka nufi gidan Faisal ɗin, Jafar ke tuka su da motar Faizan ɗin, sun riga sun sallami police. "Hmmm" Shine abunda kawai ya iya cewa tare da kwafa. Har suka isa gidan Faisal matarshi ta gabatar musu da abincin be iya cin na kirki ba, barin ma da ta tambayi lafiyar Fauza ji yayi kaman ya tashi ya bar gidan. Haka dae suka ta lallaɓa shi har Jafar ya maida shi gida, ɗaki kawai ya shiga ya zube yana kallon POP duk Tunanin duniya be ga abunda yayiwa yarinyar nan da ta zaɓi daga mai hankali haka ba, shine ma za'a ce ya dace yayi wannan fushi da ita tunda ta aikata mishi laifi har sau biyu, amma don ta mugun raina shi shine ta kama hanya ta tafi yola, shi kuwa ze nuna mata ɗan halak yake. *** Zaune Jaddah take ta idar da sallar magrib kenan taji sallama da murya kaman na Fauziyya, ɗaga kai tayi tana jiran a shigo parlorn kaman daga sama kuwa ta ganta tsaye daga bakin kofa tana kallonta. "Fauziyya!!" Jaddah ta kirata cike da dumbin mamaki. "Faizan be ce mana kina zuwa ba, wani irin zuwa ne haka? Baki da lafiya ne?" Da sauri ta karasa ta kwanta jikin jaddar ta fara kuka, shafa bayanta kawai Jaddah ke yi, yin duniyan nan ta ƙi tace komai. "Kin yi sallah?" Ta girgiza kai "to tashi kije kiyo alwala ki zo kiyi sallah, tare da Faizan kuke?" Girgiza kai tayi. "A motan kasuwa kika taho?" Ta gyaɗa kai. "Faizan ɗin ya sani?" Girgiza kai tayi. "To tashi je kiyi alwala" Mikewa tayi ta nufi ɗakin Jaddahn a chan tayi alwala tayi sallah a cikin ɗakin kawai ta kwanta shiru, babu abunda yake mata kai kawo a rai irin daren jiya, ya yaji da ya tashi be ganta ba? Ita dae babu abunda aka mata amma ta san ta tsani gidan da garin gabaɗaya. Har aka yi isha ta tashi ta gabatar tunaninshi kawai take yi. "Fauziyya taso ki zo kici abinci" Mikewa tayi ta fito, tun tea ɗin jiya ne cikinta kuma har yanzu bata ji tana sha'awar cin wani abun ba, ruwan zafi Jaddah ta fara bata kan ta saka mata tuwo da miyar lalo da yaji haɗi ta bata. Kaɗan kawai taci ta ture, Jaddah tace "kin koshi?" Kai ta gyaɗa. "Tashi muje iyayen ki na son ganinki" A tare da Jaddah suka nufi parlorn baba prof, Ammi, mammi, Baba prof, Baba Alhj se su ya Farhan ne zaune a ciki sauran matan gidan duka ba'a gayyace su ba. Bata kalli kowa ba ta karasa gaban baba prof dake daga kan kujeranshi ta zauna daga ƙasa kanta a ƙasa, daga babanta har yayyinta wani irin kallo suke aika mata sbd ko da Jaddah ta gaya musu zuwan Fauza duk sun ajiye wani abun tayo, ko tayiwa Faizan ɗin ya koro ta. Mammi kuwa kallon yadda ta ƙara kyau da haske take ba laifi Abujan ya karɓeta sossai alamun dae hankalinta a kwance yake kan yanzu ɗin. Baba prof yace "Fauziyya..! Se kawai mu ganki ba sanarwa? Ke da wa kuka zo?" Shiru tayi, Jaddah tace "Tun fa bayan sallama da tayi bata sake cewa komai ba professor" Ya dube ta yace "Faizan ne ko?" Ta girgiza kai "Toh Fatima ce?" Nan ma ta girgiza kai. "Ke don ƙaniyarki ana magana bazaki buɗe baki kiyi magana ba? Me ke damunki ne? Idan duka babu kowa to uban me ze sa ki bar gidanki ki kamo hanyar Abuja ba tare da kowa ya sani ba? Amma shi mijin naki ya sani?" Cewar baba Alhj cikin zafi. Kuka kawai ta fara kan ta girgiza kai. Wayanshi ya fiddo ya kira Faizan ya sa a handsfree. Yana kwance salla kawai ke ɗaga shi ko ruwa be sake sha ba, Tunanin duniyan nan yayi be san me ya saka yarinyar nan tafiya ba, ganin kiran baba Alhj ya sa ya san ta isa gidan. Ɗagawa yayi cikin muryarshi da yayi sanyi sossai yayi ƙasa kaman me jin bacci ko wadda ya tashi daga baccin. Cikin girmamawa ya gaida shi, bayan sun gama gaisuwa baba Alhj yace "Faizan kawai se muka ga Fauziyya kaman daga sama mun yi mun yi tayi magana kuma ta ƙi shine nace bari na kira ka kila kai ka san abunda ya sa ta bar gidan ta biyo hanya" A natse yace "Ko ɗaya baba, nima bani da masaniyar barinta gida jiya tayi zazzaɓi kuma har karfe ɗaya na dare na bar ɗakinta, na tashi da safe kawai na neme ta na rasa har police station mun je da su Faisal sbd ban san me yasa zata tashi kawai ta tafi gida ba tare da laifin tsaye ba bare na zaune, a chan ne cikin bincikensu muka je har tasha muka ga sunanta cikin passengers ɗin yola, time ɗin karfe kusan 2 na rana shiyasa ma ban kira ku ba" Duk kallonta suke, tana sheshekar kuka a hankali, shima kuma yana jinta. A hankali yace "Baba ku barta kilan akwai wani abunda aka yi mata anan ɗin in ta huce zata yi magana amma please ban amince kowa ya taɓamin ita ba" Ƙara karfin kukanta tayi, se a lokacin ta buɗe baki ta fara magana "Babu wadda ya min komai... Ni baba kawai na tsani gidan ne, na tsani garin...! Baba ji nayi in ban bar garin ba zan iya mutuwa... Yaya Don Allah kayi hakuri nima ban san sadda na fita ba.." Kuka ne ya ci karfinta. Baba prof ya dafa kanta yace "kiyi shiru Fauziyya, yi hakuri bar kukan nan... Kin yi wani mafarki ne? Ko wani abu ya faru kan kika ji bakya son Abujan?" Yana kwance lub yana sauraren ta, a hankali ta basu labarin abunda ya faru na tun tsakiyar dare bata yi bacci ba, bata samu natsuwa ba kuma seda ta bar garin wlh ko sunan garin bata sha'awar taji an kira. Rarrashinta baba prof yayi tayi akan ta bar kukan haka, ita damuwanta tana ta ɓata mishi rai kusan kwana huɗu kenan koyaushe ranshi a ɓace sbd ita, Baba Alhj yace "Toh me ke faruwa ne?" Kusan tambayar da kowa ke yi kenan a ranshi har Faizan, Baba prof karan kanshi a dame yake don wannan kowa ya ji ya san ba Alkhairi bane aikin asiri ne to amma wa ze mata? Sun san dae Fatima ciki da bai yarinya me natsuwa da hankali, ta taso a gidan cikin tarbiya irin na yaran gidan to Alamar tambayar tana kan waye? A hankali Faizan ya sa hannu ya yanke wayar, se ya miƙe ya nufi ɗakinta.. Ya jima tsaye yana karewa ɗakin kallo kan ya fara gyarawa a natse har ya gama tsab tsab kaman tana nan. Bayan ya saka turaren wutan da ta saba sakawa yaje kan kujera ya kwanta idanunshi na kallon sama.. Fatima ce tayi knocking ta shigo. "Abinci fa ya gama ɗazu na leƙa ka a ɗakinka na samu kana bacci!" Idanunshi ya buɗe ya zuba mata Su kawai ba tare da ya ce uffan ba. *** A yola kuwa cike da damuwa suka yi ta Rarrashinta har tayi shiru, Baba prof ya rubuta abubuwan da bashi dashi a gidan ya ba Farhan akan ya je ya samo mishi ze Haɗa mata maganin kariya. Farhan ya mike ya tafi, Ruwan zamzam ya bata wadda akwai ayoyi ciki ta sha yace taje ta kwanta ta huta kar tayi Tunanin komai. Mikewa tayi ta nufi sashen Jaddah, Amminta da tun aka fara bata ce komai ba se lokacin tayi kwafa ta mike kawai ta fice duk da kallo suka bita. Sun ɗan kara tattaunawa akan matsalar ta sede basu bada kofan zargi ba sun dae ajiye kila akwai aljanin da ya aureta ko kuwa suna so su shafeta. Farhan ya dawo da aikan baban, bawan Allah daren gabaɗaya be runtsa ba seda ya karance baqara kap a cikin ruwan zamzam da ya zuba mishi garin bagaruwa, ya cigaba da karatun ayoyi har uku kan ya gama se kawai ya hau jera nafilifili da Adu'ar Allah ya bayyana duk wani abunda ke boye akan Fauza sbd tun farkon fari dama shi hankalinshi be bashi haka kawai take ba. Kaman yadda be yi bacci ba haka Fauza da Faizan, bayan dogon tunani kusan a tare suka miƙe suka fara jela nafilfili haka jadda ma tsakiyar dare ta yanke baccinta dama tun lokacin ƙadangaren nan bata wani sakankance ba Fauza take nemawa sauƙi a wurin Allah da ko ma menene yake rayuwarta... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari.                🖤Gureenjoh🖤 DƘ 29 *BAYAN SATI ƊAYA* Yau satin ta kenan da zuwa garin yola, kuma sossai take jin daaɗin garin sbd yadda kowa ke ina za'a saka ina za'a ajiye da ita, daga mammi, Jaddah, babanta, Baba prof, su ya Farhan da su Fa'iza duk ji da ita suke kaman me sede in bata ambaci abu dayansu ya ji ba haka za'a je a nema mata, yanzu ita da kannenta ba duka ba zagi se jansu a jiki da take yawan yi, magungunan ta kuwa kullu yaumin safe da dare cikin kariya take na irin ayoyin da Baba prof ke mata anfani dashi, duk da waennan gabaɗaya a maimakon ta kara ƙiba tayi kyau ta Daena Tunanin komai se farin ciki duk hakan be yiwu ba. Ta ɗan zube kadan sbd yawan tunani, be taɓa kira ya ce a bata ba kuma wallahi bazata yi karya ba zuciyarta ta riga ta gama yaudararta akan Faizan bata san ta kamu da mahaukacin soyayyarsa ba se da suka nesanta da juna ta san yana fushi da ita abunda ke hanata walwala kenan gashi ita kuma ta kasa ɗaga waya ko na Jaddah ne ta kirashi. Tana kwance a parlorn na Jaddah a kan kujera Fa'iza ta shigo tana cewa "Fauza kin yi bacci ne?" Jaddah dake fitowa daga ɗakinta tace "Ina ita ina lafiyar baccin yamma Fa'iza?" Tana kallon fa'izan tace "Ya aka yi ne?" Fa'iza tace "dama zan fita ne chan farkon layi zan karɓi handout ɗina wurin wata friend ɗina shine nake so in ji har yanzu kina sha'awar cin farar ne? Don ba'a rasawa ta wurin" Mikewa tayi zaune tace "Jaddah Eyya bata ɗari biyu in tana dawowa ta sayo min fara" Jaddah tace "Toh" Ta fara duba gefen zaninta ta fiddo ɗari biyar, tana kallon Fauza tace "To da kwanciyar nan ko zaki bita ne Fauziyya? Tunda kika zo ko gate baki kara leƙawa ba kika ɗan fitan kema zaki ɗan ji daaɗi" Kaman zata ce bazata je ba se Fa'iza ta kama magiya akan su je tare ɗin wlh dama tana ta Tunanin tafiya ita kaɗai su faazila na islamiyya, ya Falaq kuma tace ita ba sa'ar mata rakiya bace. Mikewa tayi kawai taje ta wanke fuskanta ta ɗan gyara kan ta fito tana ji su Jaddah na maganan shiru shirunta ko ciwon ne oho. Fa'iza tace "ko tana kewar mijinta ba Jaddah?" "Zaki tashi muje ko zaki zauna gulmata in fasa rakiyar?" Ta faɗa tana maka mata harara duk dariya suka yi tuni ita tayi gaba, fa'iza ta miƙe da gudu ta bi bayanta. A natse suke tafiya tunda suka fito taga motar dake bin su, fa'iza dae bata kula ba, mai motar kuwa tun yana bin su a baya a baya har ya iso saitinsu ya musu horn. Kallo ɗaya tayi mishi ta ɗauke kai suka cigaba da tafiyar su, Fa'iza ma ba gwanar kula irin su ba ce se kawai suka maida kansu hanya, har suka isa gidan mai motan nan be bar binsu ba basu wani jima chan ba suka fito, suka tsaya suka saya fara tana lura da wasu dake gulmarta ana ta mamakin Fauziyya ce shiru shiru haka? Ita dae bata bi ta kansu ba suka ɗauki hanyar gida. Mai motar nan again ya cigaba da bin bayansu, gab sun iso farkon layinsu ganin bazasu tsaya ba gashi yana hangen gidansu yasa yayi saurin parking ya sauka ya biyo bayansu "Fauza...! Fauza!!" Fa'iza tace "ke fa mutumin nan ke yake kira" Yi tayi kaman bata ji ba kaman daga sama taga mutum a gabanta. "Fauziyya ni kike wulakantawa? Ni ne fa Zubair ɗin ki" Ya karashe yana nuna kanshi. Tana Kallonshi tace "Na gane ka mana amma bani da business kuma da kai Zubair hakan yasa ban ga anfanin kulaka ba, please ka kyaleni karka manta da Aurena" Hannun fa'iza ta kama suka fara yunkurin wuce shi ya sake shan gabanta.. "Fauza akan ki rayuwata ta shiga cikin barazana, a kan ki saida na shafe sama da watanni huɗu a prison amma sakamakon da zaki yi min kenan? Wallahi gayen chan ba son ki yake ba, na rantse miki da Allah ina son ki kuma in har ba zan sameki ba saide kowa ya rasa" Ya faɗa cikin alwashi. "Oh haka kace?" Tayi maganan tana Kallonshi. Yace "eh don ban ga maraba ta da mugun yayankin nan ba, shi yayi min cune ina tare da drugs da gomnatin Nigeria ta hana Anfani dasu ya kuma san idan har an kama ka kisa ne amma ya cuna ni ina dawowa daga Russia aka kamani, ba don connections ba da se wani ba ni ba Fauziyya duk a haka kika zaɓe shi over ni?" Tana shirin magana kenan idanunta suka faɗa cikin nashi, wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riske ta har bata san ta matse hannun fa'iza dake cikin nata ba, tsaye yake sanye da kananun kaya riga da wando daga gani ka san sun ci kuɗi hannayenshi zube a aljihu ya tsaresu da firgitattun idanunshin nan masu rikitar da ita yana kallo.. Ɓacin rai take hanga shimfide a fuskanshi me tsanani, yaushe ya zo? Ta jefawa kanta tambayar da bata san amsar shi ba, da sauri ta zagaye Zubair ta nufe shi da nufin yi mishi bayani ba abunda yake tunani bane, tana isa kawai ya sanya hannu ya fincike hannunta suka yi gida. Jan ta yake ba tare da ya damu da saurin da yake ɗin yayi mata yawa ba. Basu zame ko ina ba se room ɗinshi da karfi ya jefa ta kan kujera yana kallonta zuciyarshi kaman ya Faso kirjinshi ya fito sbd yadda yake hawa da sauƙa na bacin rai... *** Tun da ta bar garin Abuja yaji garin ya zamar mishi kaman Ƙango, baya jin daaɗin rayuwa, baya iya cikakken farin ciki, 24/7 da tunaninta yake kwana yake tashi, gabaɗaya Fatima ta kasa gane kanshi don ba wani abincin kirki yake ci ba, ko yaushe kuma yana ɗakin Fauza a kwance. Shi karan kanshi be san Son ta yayi mishi mummunar illah ba seda suka nesanta da juna, ita yake so ta fahimci darajar shi hakan yasa ya ƙi kiranta ko da a waya ne ba tare da haƙarshi ta cimma ruwa ba sbd rana tsaka kawai ya cewa Fatima ta shirya su tafi yola su dan kwana biyu se su dawo gabaɗaya, ya azabtu kwarai da Tsananin kewan girkin ta, shayin ta, rashin kunyar ta in tayi niyya wadda babu abunda ke mai kyau daga gareta irin shi, shagwaɓarta, ƙamshin ta, shigar ta da ma lallausar fatanta... Daren karshe da suka yi spending gabaɗaya ya kasa fita daga kwakwalwarshi. Ita Fatima ta zama abin kallo ne kawai illa iyaka abun ya ishe ta ta shige ɗaki ta sha kukanta, ta kira Aunty tana mata kuka akan yadda tunda Fauza ta bar gidan irin yadda suke dashi kaman an chanza shi, Auntyn ta tabbatar mata da ta kara hakuri na lokaci kaɗan ne komai ze sauya karta damu. Hakan yasa ta cire damuwar a ranta kawai kuma wai ta shirya su je yola in zasu dawo su dawo tare gabaɗaya, me yake nufi? Karfe 3 daidai na yamma jirgin su ya sauka a international Airport na Yola, Farhan da Faraj ne suka je suka ɗauko su, tun daga nesa kuma ya hangesu ita da Fa'iza a sadda suke tafiya.. Da idanu ya bi ta har motar su ta karya kwanan gidan nasu. Hakan yasa be shiga ciki ba ya samu kan mota ya zauna jiran ta, yana so yaga expression ɗinta a sadda zata ganshi, yana so yaga tayi kewar shi ne kaman yadda yayi mahaukacin kewar ta? Yana so yaga idanuntan nan da yayi kewarsu fiye da komai, ganin sun ɗan jima yasa ya dira ya fita wajen gate a chan nesa ya hangesu da wani guy, be ma gane Zubair bane seda ya matsu dab dasu... *** "Ashe Abun naki hauka ya koma ban sani ba Fauziyya?? Da Aurena a kanki kike kula wani gardi? Me wanchan Yaron yake dashi da ya fi ni Fauziyya??? Eyee?" Ya daka mata tsawa yana kallon yadda take ta murza hannunta da ya rike hawaye na zuba a idanunta. Fuskan nan a murtuke jajazir yace cikin dakakkiyar muryarshi da ya Haɗu da bacin rai.. "How could you? Oh da kin gayamin abunda kike buƙata da na banbance miki tsakanin Aya da tsakuwa... Da na nuna miki cewa wadda kika saba dashi fank....." "Don't...!" Itama tayi ihu cikin kuka tace "Karka fara jefana da wannan kalma, karka bari na tsaneka ya Faizan.." Kuka sossai take tana jin zafi sossai na yadda yake kokarin kawo abunda ba shine ba cikin rayuwar aurenta.. "Shut up!! Just shut the fucking up! Babu abunda zaki ce in yarda dashi.. Babu Fauziyya..." Zata yi magana da niyyar kare kanta ya riƙo hannunta kawai ya cillata kan gadon ɗakin. Yunkurin miƙewa take ya bita ya danne, a zafafe ya fara zare mata hijab yana faɗin maganganu da suka saka ta sakar mishi jiki ta Daena fighting kuma, tabbas zata ɗauki mummunan mataki kan wannan abu amma ba yanzu ba, se ya tabbatar ita ɗin ba shashasha bace, lusara, wacce bata san me take yi ba da zata rabe kanta a titi, se ya tabbatar ita ɗin daban take da sauran mata anan ne zata ɗauki matakin da ya dace da rayuwarsu.. A zafafe yake komai tun tana hawaye har ta soma kuka a hankali, daga karshe cikin kuka ta rike hannunshi tana bashi hakuri akan kar ya je mata a haka amma inaaa yayi nisa sossai, kan ta kara furta wani kalma ya haɗe bakinshi da nata yana bata wani irin zazzafar sumba, bakin da ya jima yana tsone mishi idanu... Saida yayi matukar nisa a tirbar da ya ɗauka kan ya fahimci wani abu da ya so gigita rayuwarshi, saide ba ze iya dakatar da kanshi a wannan yanayi ba, ba ze iya katange kanshi daga gareta ba.. Ƙara me ƙarfi da ta kwala shi ya saka shi kankameta kaman zasu shige cikin juna a take dukkaninsu jikinsu ya ɗauki wani irin mugun rawa, daga ita har shi hawaye suke zubarwa... Ya je mata ne a yadda be yi zato ba se gashi ta shayar dashi ruwan mamaki da baya Tunanin har Abada ze kau daga idanu, zuciya da gangar jikinshi.. Bayan lokaci me tsawo ya mirgina gefe tare da janyo ta ya rungume da karfi kaman wani ze kwace ta "I'm sorry..! I'm so sorry" Abunda kawai yake iya maimaitawa kenan hawaye na zuba a idanunshi.. Ita kam Sam bata san inda kanta yake ba, ba karamin wahala tasha ba, babu inda baya mata ciwo da radadi a jikinta, amma Dukda haka tayi juriya me yawa.. Sallah da yaji ake yi a masallaci na magrib ya sa ya zameta ta kwanta, bayi ya shiga ya watsa ruwa da wuri wuri, zuciyarshi cike da emotions da baze iya tantancewa ba, hawayen tausayi da kaunar ta kuwa sun kasa tsayawa a idanunshi, yarinyar nan ta sha wahala for nothing.... He never thought that. meyasa a sadda take kokarin kare kanta a sannan su kuma suka saka mata wani irin kyara da tsana? Fita yayi yayi masallaci, duk sallar da yake ɗin ba cikakken natsuwa yake ba.. Ana idarwa ya mike ya fito se ga Farida da be san zuwanta gidan ba ta nufosu da gudu.. "Yaaaya Mammi... Mammi" Da gudu shi da Farhan suka yi sashen Baba prof ma ya rufa musu baya da sauri ganin yadda duk faridar ta gigice. Yanayin da suka samu mammi se ya ruɗa su, da sauri suka kama ta suka fito da nufin shiga mota a kaita asibiti... Daidai lokacin da wani irin hayaniya da basu taɓa riska ba a gidan ya ɓarke da buge buge kaman faɗa, ko kan ɗaya daga cikinsu yayi wani yunkuri Aunty da Ammi sun iso tsakiyar harabar gidan ana cin uwar sabada.... Faizan cigaba da kokarin saka mahaifiyarshi mota yayi don be da lokacin su se ta rike hannunshi tace a sanyaye.. "Ku fara sassauta wannan bala'i da ya taso kan mu tafi asibitin Faizan" Gabaɗaya ilahirin ahalin gidan suna tsaye cirko cirko an rasa wadda ze raba se baba Alhj ne ya daka musu mummunan tsawa tare da rufe su da wani irin faɗa "Me wannan? Me kuke yin nan a gaban ƴaƴa da jikoki? Wani irin bala'i ne wannan? Shamsiyya!! Ruqayya!!!" Duk wannan be sa sun dakata ba, Ammi tace "Na jima da sanin ke ɗin makirar ɓoye ce, Algunguma, munafuka ban tabbatar ba se yau.... Ashe ke ce kike ta kokarin kashe min yarinya? Ashe kece kike ta kokarin haukatata ta bi duniya to wallahi baki isa ba... Na fi karfinki saka idanunki cikin nawa ki gani da kyau" Aunty ma shewa tayi "Ahayye nanaye... Wai kura ashe ze ce da kare maye? Duma har yana da bakin raɗan maɗaci karki ɗauka ban san ke kike ɓarar da cikin Fatima ba sbd karta haihu da Faizan.... Karki ɗauka Cewar Ban san ke da Ƴar ki Fauziyya kune silar duk wani wahala da Uwar Faizan take ba.... Ko ba ke ce kika harbe mata kafa ba? Ko ba Fauziyya ke saka mata maganin da yake karya duk wani Magani da aka bata take sha ba...????" Rassssssss haka gaban kowa ke wani irin dokawa suna kallon sabon abunda basu taɓa zato ko tsammani ba... "WHAT.....!!!" Faizan yayi exclaiming da karfi gabaɗaya alakanta komai da Fauziyya da aka yi shi ya gigitashi... Waige Waige yake se chan ya hange ta tsaye tana kuka me taɓa zuciya, da sauri ya karasa gangar ta yace "Wai da gaske? Da....gaske..ke ke kike sakawa mammi ma...ga...ni?" Kai ta gyaɗa tana cewa "Eh nice Amma......" Wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata, har tana shirin faɗuwa.... Haƙorin shi ya sa ya danne lip ɗinshi hawaye ya fara tsere bisa idanunshi, da sauri ya waiga ya nufi mammi... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari.                🖤Gureenjoh🖤 DƘ 30 **Wannan shafi sadaukarwa ce gareki Aunty hajjo *Autar Manya* Alkhairin Allah ya cimmiki a duk inda kike ina godiya kwarai🥰❤️** "innalillahi wainna ilahi rajiun....! Allahumma ajjirni fi musibatin wa akhlifnee khairan min ha.." Abunda Ammi take iya maimaitawa kenan jin numfashinta na seizing da gudu Farhan yaje ya riƙeta yana aikawa da Aunty wani irin kallo na kaskanci. "Mammi don Allah mu tafi in kaiki asibiti" Cewar Faizan, ta girgiza kai tace "kaima bazaka iya driving a yanayin kan nan ba Faizan, kaima kana bukatar ganin likita a wannan yanayi da kake ciki... Ka yi ta maimaita sunan Allah." Baya so ne yayi breaking don iyakacin jarumtar hana kanshi faɗuwa yanayi, maganan ya dake shi ne fiye da yadda yake zato ko tsammani... Baba Prof dake rike da kafadan ɗan uwanshi yana ɗan bubbugawa ganin irin yanayin da ya shiga yace "Duka wannan magana ba na nan bane, mu je parlor bana so in kara jin wani yace tak a cikinku" Ya bada umarnin tare da janye baba Alhj suka nufi parlornshi. A hankali hankali kowa ke binshi ciki Fatima na ta kuka cike da baƙin ciki yau kam kila se buzunsu kilan aurenta ya mutu kenan, ya zatayi da soyayyar Faizan? Jaddah ce ta taka ta nufi Fauza dake tsaye kanta ƙasa tana kuka a hankali, abubuwa dayawa ne suka haɗe mata da kananun shekaru, Zuciyarta, gangar jikinta da kwakwalwarta duka babu wadda yake aiki bisa daidai. Meyasa Faizan ke min haka? Meyasa a koyaushe fahimtar shi a gareni gurguwa ce? Bata da amsa, kuma a yanzu bata buƙatar sani. Jaddah da ta riƙeta ta ɗaga kai ta kalla se kawai ta sake rushewa da kuka, jadda ta tsorata ainun da kallon yanayin Fauza ɗin fuskanta ya kumbura sossai kaman wacce ta kwana biyu tana kuka. "Mu je Fauza" Ta faɗa tana kokarin jan ta suyi parlorn Baba ɗin saide ta kasa taka kafar ta sbd azabar zafin dake ratsa ta, wani kukan ta sake saki.. "Lafiya me ya sameki?" Kasa magana tayi se kuka. "Jaddah su baba, ba hijab jikina" Se a lokacin Jaddah ta lura ko dankwali babu a kanta gashinta a tufke kuma wlh ta nemi hijab ɗin nata ne bata gani ba gashi ta gigice jin hayaniyar da gidan ya ɗauka sossai. "A ina kika bar hijabin?" Kanta a ƙasa ta nuna sashen en mazan. Ajiyar zuciya Jaddah ta sauke kan ta nufi ɗakin Faizan ɗin don duba mata hijabin. Abunda ta ci karo dashi shi yayi mugun razana ta, cikin wani irin tsantsar mamaki take karewa beddings ɗin kallo, se kuma hawaye ya fara zarya a idanunta, Juyawa tayi tana kallon bayanta kaman zata ga Fauza a wurin a hankali ta furta "Allah sarki baiwar Allah!" Lallai Allah Allah ne, in ba shi ba waye ze iya wanke Fauza daga wannan zargi da aka yi ta mata aka ta shiga hakkinta akan abunda bata aikata ba a idanun dumbin jama'ar gidan nan? Bedsheets ɗin ta yaye, chan lungun gadon ta samo hijab ɗinta ta fito. Saida ta kai Bedsheets ɗin toilet ɗinta kan ta dawo ta sanyawa Fauza da har yanzu ke kuka hijab ɗin tare da rungumota "kiyi hakuri kin ji? Kiyi hakuri Allah ya miki albarka.. Lallai kina cikin masu hakuri Fauziyya sannu.. Ki daure mu karasa na san mu suke jira a parlorn" Da ƙyar take iya taka kafar da take ji kaman tana takawa ne bisa ƙayoyi, duk taku ɗaya kuwa ita kaɗai ta san zafin dake ratsa ta har cikin kwakwalwarta. Ilai kuwa sun samu parlorn tsit se kukan Ammi ke tashi, kana jin kukan zaka san na dana sani ne me yawa, ashe hassada ka iya jaza maka bala'in da baka san hawarshi ba bare Sauƙar shi? Duk da kallo suka bi Jaddah da fauza ɗin kowa na mamakin me ya sameta haka ita kam fuskanta a ɓoye jikin Jaddah ji take kowa ya kalleta ya san me ya faru, shi kam be iya ya ɗaga kai ba har suka zauna. Bismillah baba prof yayi ya fara da Adu'a kan ya fara da jan hankali akan wannan abu da ya faru a gidan nashi yau wadda ba'a taɓa samun hatsaniya haka ba, ga dae Mammi a sadda aka fitar da ita kaman zata mutu amma yanzu kuma Alhamdulillah da kanta take zaune. Ammi ya kalla yace "Ruqayya ke ce babba, don haka dake zan soma, me yake faruwa? Me Shamsiyya ke nufi da kalaman ta? Ko jikina duka kunnuwa ne ba zan taɓa aminta Cewar Fauza zata iya cutar da Aisha ba abunda kuma ba ze yiwu ba kenan so ina so ku faɗa min gaskiya me ke wakana a tsakanin ku?" Ammi cikin kuka tace "Wallahi Yaya(prof) ban taɓa sanin cewa za'a iya anfani da ƙi da kuma hassadar da nake yiwa mahaifiyar Faizan a nemi lawye ni ba, lallai duk wadda ya ɗauki hassada abun yi to yayi gaggawar tuba ya kuma kori sheɗan... Ba kowa bane ze nuna yana son ka a fili kuma har a zuciyarsa ta kasance haka, haka kuma ba kowa bane ze nuna tsanarka a fili ya kasance kuma har cikin zuciyarshi haka ɗin ne ba. Zan fara da neman gafararku ku yafemin don Allah" Duk kai kowa ya gyaɗa kwarai haka magananta hassada mugun ciwo ne, amma ba wannan tukuna suke son ji ba. "Ɗazu bayan na idar da sallah, se na duba ban ga redio na ba se na tuna ashe Shamsiyya ta ara da rana taji wani program a ABC don nata ya ɗan samu matsala har ta ba Farhan ma ya kai mata gyara.. Kaman Allah ne ya turani ina zuwa na samu tana yiwa Fatima faɗa akan tana kokarin ɓata mata aiki da tun kan ta shigo gidan nan take ginawa, na so shiga se kuma jin ta ambaci sunana a farkon fari yasa na dakata.. Ga abunda take cewa in na mata ƙarya kar Allah ubangiji yayi min gafara... 'Fatima kin san abubuwan da na aikata kuwa? Toh buɗe kunnen ki ki jini ina ga baki sani bane yasa kike min wasa da aiki, tun farkon fari Professor na so aure se kuma ya fi karfina da naje aka duba min se aka tabbatar min da Cewar babu aurenmu da professor har duniya ta nade sede ya hangi aurena da Sulaiman har da zuri'a, tun a lokacin na sa ya bincika min matar Sulaiman wato ni kenan(Ammi ta nuna kanta) tashin farko ya faɗa min cewa tana da halin saurin fushi sannan kuma ta kan ji haushin mammi ganin kaman ta fita a komai a gidan har miji, kai natse na mishi umarni da ya kulle zuciyarta, ni kuma zan koma in kashe aurena in dumfari gidan se na tabbatar duk wasu arziki nasu ya kasance cikin tafin hannuna. Kai tsaye ya samu nasara sbd shaidan dama ya riga ya darsawa Ammin hassada a ranta, Zuciyarta ya zama baya jin komai ƴaƴan da na haifa ma ban damu dasu ba bare miji da surakai..." Kuka ne yaci karfin Ammi tana tuna yadda take wasarere da rayuwar ƴaƴanta barin ma Fauza da ta fi bukatarta da kowa, Amma ta kan gode Allah dayake ba azzalumin bawa bane ya baiwa Fauza Jaddah da mammi da kuma baba prof. Auntyn ce ta ɗan sosa kanta kan tace "Ai baki faɗi komai ba ruqayya, wannan kaɗan ne daga cikin kaidi na.. Bayan na sa an rufe zuciyarki ana kuma anfani da kwakwalwarki se na zo na aure miki miji, tashin farko na fara kokarin cusa Fatima ga Faizan don na san ta hakan ne kawai zan samu abunda nake so, se bokana yace min idan dae har Mahaifiyarshi na da cikakken lafiya burina baze cika ba don ita ɗin a tsaye take a cikin gidanta kan mijinta da yaranta. Dukda ya tabbatar min da cewa ko an nakasta kafafun nata zata iya cigaba da nemawa yaranta kariya wurin rabba se na ce ya saka mata ciwo me tsanani wadda baze bar ta natsuwar lafiyar nema musu sauƙin ba, kwatsam se muka samu ciki ni da Ruqayya, da na koma ya duba min se ya tabbatar min yarinyar cikin Ruqayya masifa ce ga rayuwata don itace zata yi silar tabarbarewar duka aiki na in ban yi wasa ba, kai tsaye na nemi a ɓarar da ita ta bi rariya yace in bada kwanaki, duk wani hanya da ze bi don zub da cikin babu nasara ko da ya faɗamin nima ban zauna ba, hatta da maganin zubar da ciki na saka overdose na bata a kunu sede cikin nan ya ƙi barewa abun ba daaɗi wai mahaukaci ya ci kashi, duk inda muka buga cikin nan yaki ya lalace se ya kawo shawarar a dasawa mahaifanta tsanar ta musamman uba, suyi ta mata mugun fata ita kuma tun daga cikin za'a sa mata taurin kai na bugawa a jarida yadda zata gallabi kowa.. Hakanan destiny ɗinta a sarƙe yake da Faizan shima za'a saka mishi tsanar ta kaman yadda itama baza'a bari ta so shi ba ko na minti guda, duk a aikin mun manta da Jaddah, Baba prof da mammi a tsanar na Fauza saide mutanen duniya da iyayenta yadda za'a yi ta mata baki ta bi duniya... Hakan kuwa ta kasance don haka ta ta cimma ruwa sbd tunda Fauziyya ta fara wayau kowa ke kuka da ita. Mun kawar da hankalin baba prof kan Faizan ta yadda duk haɗe Haden auren da yake yi be bi ta kan Faizan ba, Ganin kissa ta bazata saka Faizan ya kula Fatima ba yasa na koma ma bokana da kukan damuwata, nan da nan ya ce ze yi aikin karkato hankalinshi dama already kaman yadda akwai tsana me girma tsakanin shi da fauza haka tsakanin mahaifiyar Fauza dashi, ita kuma ta fara jin haushin shi ne sbd abubuwan da yake yiwa fauziyya amma dayake bata da damar nunawa sbd akwai aiki a kanta se ya zamana ta fara tsanar shi a ranta wadda mu kuma muka kara rura wutar. Fatima ta tashi ne da tsananin son Faizan sbd shine nake kwadaitar mata a kullum as miji, ita tayi ta matsawa nayi ta shiga da fita har aka ɗaura aurensu suka tattara suka tafi, burina na lalacewar rayuwar Fauza ya cika na kuma san ko a kafa aka ɗaurawa Faizan ita se ya kunce ya yasar, sbd ta zama itace yawace yawace, shaye shaye da Zin....." Faizan da Jaddah suka Haɗa baki cikin kunan rai suka ce "Fauza bata yi zina ba.." Hawaye ne ke zubarwa Jaddah kaman yadda Fauza ke kuka marar sauti tana jin ita kuma yadda aka yi da rayuwarta tun tana cikin cikin mahaifiyarta. Cigaba Da bayani tayi.. "Kwatsam Professor ya shammaceni aka ɗaura auren Faizan da fauza duk wata hanya da zan bi wurin ganin na wargaza auren hakan be yiwu ba, na ba Fatima baki akan duk yadda zamu yi mu lalata auren se mun yi, bani da masaniyar cewa igiyar aure da girman darajarshi ya warware wasu abubuwa nawa masu dumbin yawa akan Fauza ciki har da rashin ji da saurin faɗa, rashin kunya da kuma shaye shaye, se da na koma wurin bokana yake faɗamin, Fatima taki kwantar da hankali tayi tayiwa Fauza abubuwa wadda a hankali ya kawo kusanci tsakanin Fauxa da Faizan se kuma ta dawo ta haukacemin, gashi Allah da ya fi ni dabara se ya hana cikin Fatiman zama bare in saka ran mallakar burina. Komawa nayi nace ko ta karfi ko ta tsiya a fitar da fauza daga gidan Faizan, ko kasheta ne ayi, shine aka tura mata ƙadangare da nufin kasheta amma Allah ya bata kariya, aka sake nufin haukatata sbd ranar ne muka samu dama ta kwanta da zazzaɓi bata iya tayi Adu'ar bacci ba shi kuma Faizan ya mance be yi mata ba, a son mu ne fitan tan nan ta bi duniya amma se Allah ya sake kare ta ta kawo kanta gida. Wannan shine abubuwan da na aikata ni shamsiyya...." Salati kowa yake yi, wasu na ta kuka barin ma fa'iza da ta fi wayo cikin yaranta kaman zata hadiye ranta, Farhan ne dake kusa da ita ya iya miƙa hannu yana lallashin yarinyar, Allah sarki uwar su bata duba kananun yara har uku da take dasu ba kwata kwata babu wacce ta kai secondary, ta aikata irin waennan abubuwa har gwara su kuma da Fatima da ta ɗaura a Keken ɓera wadda ya dire su a tashar dana sani. "Fauziyya me yasa kika amsa Faizan cewa kina shafawa Aisha magani?" Baba prof yayi mata tambayar, tana cikin ciwo bazata iya magana ba, abubuwa sun mata yawa kuma sun haɗe mata, Aunty da Fatima sun cutar da ita mafi munin cuta kuma bazata taɓa yafe musu ba har duniya ta tashi. Kirjinta ciwo yake mata, gabadaya ji take kaman zata mutu. Ammi ce tace "Kwarai tana shafa mata magani da wani Adu'a wadda ni na bata, maganin kuma wurin kawu na Wadda yake bada magungunan gargajiya na musulunci nake karbar mata sbd tausayin halin da take ciki wadda ba zan iya nunawa ba, Fauziyya..." Ammin ta kira sunanta, ɗagowa tayi har bata iya kallonta da kyau sbd kuka ta amsa.. "Ki yafe mana iyayen ki Fauziyya don Allah ki yafe mana mun kasa baki kariya kaman na kowa su iyaye, tun kan ki zo duniya muka yi saken da aka cutar dake barin ma ni mahaifiyarki, ki yafemin don Allah" Kai take gyaɗawa tana kuka, Baba Alhj ma dake kuka sossai yace "Fauziyya nima ki yafe min irin kalamai da tsana da na ɗaura miki, ki yafe mana don Allah kwarai bamu kasance iyaye na kwarai a gareki ba.." Girgiza kai tayi cikin muryarta da baya fita tace "Na yafe muku wallahi Ammi, ban taɓa rikeku ba, ko na riƙe ɗin Jaddah da ta zame min uwa kuma uba ta kan nusar dani har in yafe muku, tabbas ban samu gatan iyaye ba saide na samu gatar kakata wadda har Abada bazata taɓa fita cikin mutanen da suka fi kowanne daraja a rayuwata ba... Mammi kiyi hakuri da irin amsar da na bayar" Mammi tace "Fauza nima na ji ne kawai Amma ban amince ba, ko kin manta a duk sadda kika taimakamin na kan yi bacci cikin kwanciyar hankali? Wannan kaɗai ya isa shaidar cewa ba don cutar dani kike yi ba" Su ya Farhan ma yafiyar ta suka nema duk ta amsa da ta yafe musu, se a lokacin Faizan ya iya ɗaga kai ya kalleta zuciyarshi kaman ze fashe da tausayi da kuma ƙaunar ta, lallai ta ga rayuwa kuma daga yanzu yayi alkawari wa kanshi cewa har Abada baze taɓa judging mutum by cover ba, Fauza yarinya ce amma kafin Allah, ba don Allah na tare da ita ba da yanzu babu ita. Hannu ta mika ta rike na fa'iza dake wani irin kuka ta kasa kallon ko mamanta da Fatima da suma suke kukan tace "Ni kam ba zan iya neman yafiyar ki ba twin sister, na san bazaki taɓa yafe mini ba, ina ma ina ma... Ina ma zan iya chanza Aunty daga mahaifiyata in dauki mammi ko Ammi, ina ma bawa na da damar ɗauke ranshi da kanshi... Aunty kin cuceni, kin cuci kannena, kin cuci mahaifina, kin yi min illar da Har Abada baze taɓa mantuwa a raina ba... Wallahi na tsaneki, na tsani ganin mummunar fuskarki, meyasa kika haife ni meyasa aaa" Ta karashe tare da kurma ihu faɗuwa tayi, numfashinta na barazanar ɗaukewa, Faraj ne yayi hanzarin ɗaukar ta, Farhan ya rufa mishi baya suka yi asibiti don zata iya mutuwa a yadda taken nan. Allah sarki shiyasa wani lokaci in zaka yi abu kake duba bayanka, me zaka barwa ƴaƴan ka? Fatima ce ta rarrafo tana kuka har da majina ta riƙe kafafun Faizan.. "Wallahi wallahi abubuwa dayawa ban sani ba se yanzu, na rantse da Allah ban taɓa bin ta ko rakata wurin wani mushiriki ba, wallahi soyayyar da nake maka daga cikin zuciyata take don Allah karka barni, wallahi kana Rabuwa dani babu abunda ze hana ni mutuwa ka taimakeni karka bari na mutu Ya faizannn Don Allah.." Yadda take kuka seda kowa yaji a ranshi kwarai ita kam ta so Faizan.. Shi kuwa idanunshi da suka rine gabaɗaya suka sauya ya ɗaga ya zubawa Fauza ko kallon wurinsu bata yi ba, tana dae kwance a kan kafadan Jaddah hannunta na riƙe da nata har lokacin kuma hawaye kan zuba a idanunta ta sa hannu ta goge.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari.                🖤Gureenjoh🖤 DƘ 31 Tsatsareta yayi da idanunsan nan masu kaifi yana so yaga yanayinta da maganan Fatiman saide ko inda suke bata kalla ba bare ta bashi damar karantar ta, maida idanun yayi kan Fatima yana me kallonta cikin kyamata da tsana yace "kiyi haƙuri ba zan iya cigaba da zama dake ba, I never loved you. Sannan ko ba don haka ba, ba zan taɓa Haɗa wata macen da Fauza ba she had enough in her life so maganar baƙar kishiya babu shi har Abada, na sawwake miki igiyoyi biyu bisa uku dake kanki" Ihun kuka take kurmawa tana rokon su baba da su sa baki, babu wadda ya motsa sbd babu wadda ya taɓa kawo Fatima zata iya aikatawa Fauza abunda ta aikata, zama da munafuki me fuska biyu ba karamin hatsari bane don babu abunda bazata iya aikatawa ba. "Shamsiyya na sake ki saki biyu, ki je ke da Allah zaki girbi duk wani abunda kika shuka, sannan na baki nan da awanni 24 ki gama duk wata ganawar da zaki yi da yaranki ki tattare duk abunda kike buƙata ki bar min gida har abada kuma bana so in sake ganin kafafunki cikinshi" Ita kam bata yi kuka ba, se wani murmushi da take yi, lallai duk wani ƙarya tata ta ƙare saide bata karaya ba, a ganinta don ka yi farautar Burin rayuwarka ba wani abu bane, mikewa kawai tayi da nufin ɗaga kafa tayi tafiya se kafa yace be san zance ba, ihu ta kurma jin wani azababben ciwon ya tsarga mata a gabaɗaya kafofin nata, "Kaikayi koma kan mashekiya" ta furta tana kallon Mammi da wani irin hanzari. Se yanzu ta tuna boka ya ce mata duk ranar da aka san itace da hannu kan ciwon na mammi tsab ze dawo mata, se lokacin ta fara kuka jin yadda kasusuwanta ke tauna, haka wai dama Aishar ke ji? Ta tambayi kanta tana kara kure mammi da itama take kallonta da mixed emotions da kallo. Fatima take kira ta taimaka mata su fice, Fatima na kuka kaman ranta ze fita ta kamata suka fita ba wai don wani abu ba se dae tana Tunanin kila mahaifiyartata ta sama musu mafita don ta saba sama mata mafita, ita wlh bazata taɓa iya hakura da Faizan ba. Yunkurawa Fauza tayi da niyar miƙewa sbd Baba prof ya sallamesu bayan nasiha da yayi musu me ratsa jiki, duk sauran matan jikinsu yayi matukar sanyi, ganin kowa na shirin fita ne yasa itama ta yunkura saide bata kai ga miƙewa ba ta koma ta zauna tana runtse idanunta da suka kankance don azabar zafin da ya ratsa ta. Tsab yana hankalce da ita, wani irin tausayinta ne ya tsirga mishi, abunda ta guda kenan amma ta lura kusan kowa ya harbo jirgin duk kunyar Faizan be ji ko dar ba se ma murmushi da ya ɗan saki yana jin daaɗin yadda kowa ya kamata ya san Fauza ɗin ba ƴar iska bace kaman yadda aka mata tambari. Ammi bata kula ta ba sbd ta san zata samu duk kular da ya dace a wurin Jaddah ko mammi, yayinda ita kuwa ta ma kasa hada idanunta da mammin kwata kwata. Ji yake kaman yaje ya ɗauke ta chadak ya kaita har sashen na Jaddah, ya san tana wahalar tafiyan ba laifi ta wahala sossai, hannunshi ya cusa cikin kwwantanccen gashin kashi ya shafa yana sakin murmushi sanin se sun kwashi daru da ita alamar ta ya nuna ba karamin fushi take dashi ba. Ruwan zafi sossai da wasu magunguna Jaddah ta Haɗa mata akan ta shiga ta zauna, idan ya huce ta sake saka wani tayi kaman sau uku kan tayi wanka ta fito, duk yadda ta so shigar kasawa tayi tana kuka tana yarfa hannu, Seda Jaddah ta tsaya a kanta sossai kan ta iya shiga duk yadda Jaddah ta so ta dubata ko taji ciwo kiyawa tayi, haka aka yi wankan amma ta sha wahala kuma ita kam bata ji sauƙi ba, banda Allah ya saka mata babu abunda take kira. Bayan tayi wankan ta sha magani tare da rama sallolin da ake binta ta kwanta saide fa zazzaɓi me zafi ya rufeta har tana fita hayyacinta ba arziki Jaddah ta kira Faizan da shima ya sake wanka kenan bini bini se ya saki murmushi ya ɗan cije leɓe, ganin kiran Jaddah yasa da hanzari ya zura jallabiya me taushi Ash ya fice. A hannu ya ɗauko ta Jaddah na gaba ta buɗe mishi motar ya sanyata tana ta mishi faɗa, shi dae be ce komai ba ya zagaye ya shiga ya ja da gudu se asibiti, likita namiji suka samu kai tsaye yace a nemo mace don matsalar ba na namiji bane kuma baze iya hakura wani ya duba mishi mata ba. Haka ko aka nemo Dr mace, ko da ta duba ta taji ciwo kuma wurin yayi tsami dole tana bukatar ɗinki, haka ko aka yi tana kuka don ta sha baƙar wahala, bayan an gama aka sake mata allurai sbd zazzaɓin tuni wahalallen bacci ya ɗauke ta. Zuwa suka yi suka duba Fa'iza da har lokacin itama bata farfado ba, dama Jaddah ta tura musu zaliha ta taya su kwana, se kuma ga Fauza ma. Jaddah ce ta kwana da fauzar yayinda mazan suka wuce gida. Da misalin karfe goma na safiyar washegari ya fito a shirye tsab cikin wata farar ƴar uban sun yadi da aka yiwa ɗinkin zamani kwata kwata da kaɗan ya sauka cinyar shi, fuskanshin nan cike da haiba da wani irin annuri Dukda ba sake take ba, ya saka wata takalmin fata me surkin ja da brown se ya ɗaura jar jaddara a kanshi, sajenshi nan a gyare lub lub haka gashin kanshi dake sheki, agogonshi Iwatch ne wadda kallo ɗaya zaka mata ka san diamond ce sbd walwalinta, hannunshi cushe a aljihu ya nufi sashin mahaifiyar tashi yana taku cikin salon tafiyarsa na ingarman namiji me cike da kwalisa. Har cikin ɗakinta ya sameta ya ɗan rungumeta ganinta tsaye tana gyara kan dressing mirror ɗin ta, a hankali yace "Alhamdulillah Mammi lafiya ta samu Allah shine abin godiya" Tace "kwarai kuwa Son, ji nake kaman ban taɓa wani ciwo ba" Yace "Good morning mom" Ta amsa cikin kulawa, sannan ta ɗaura da "akwai abinci basket biyu a kitchen ka fita dashi ina zuwa mu wuce asibitin" Fita yayi yana murmushi ya zaku iya zakuwa wurin son ganin kyakyawar fuskar ta da idanuntan nan masu kyau da ɗauke hankali. A mota ya saka baskets ɗin yana tsaye yana jiran mammi se kuwa gata, daga nesa yake ayyana kyaun mahaifiyarshi da iya shigar ta Dukda hijab ne jikinta amma kallo ɗaya zaka mata ka san wannan ɗin ƴar gayu da ado ce, zobunan gwal guda biyu se walwali suke a hannunta na hagu, na damar na riƙe da jaka. Da kanshi ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ya zagaye ya shiga ya ja suka fice, tun asuba iyayensu mazan suka je asibitin suka dawo, da kyar baba prof ya lallaɓa fa'iza ta bar kuka me cin rai da take, ya mata nasihu sossai haka babanta, Fauza kam da kyar ta iya gaida su kunya kaman ta tsaga ƙasa ta shige. Sun so su dawo tare da Jaddah tace bata san zance ba se Mammi ta zo Farhan da yake ta zirga zirgan asibitin se ya maida ta. Da sallama suka shiga ɗakin tana kwance ne idanunta kuma biyu ba bacci take ba, har zata amsa sallamar mammin kamshin turaren shi ya cika ɗakin wadda ya tabbatar mata da tare suke da mammin hakan yasa tayi saurin rufe idanun.. Jaddah ta amsa tana mata sannu da zuwa har ƙasa ta duka ta gaida surukar tata, bayan sun gama Gaisawa ta tambayi me jiki Jaddah tace da sauƙi don har ta sha pepper soup ɗin kayan ciki da Amminta ta turo baba Alhj dashi da ruwan zafi. "Bacci ma take" Cewar mammi. "Yanzu fa muke hira ina ga baccin ya fusge ta" Shi kam da idanu yake binta, kaman ze cinye ta, fuskanta yayi fayau ya faɗa, tsab kuma ya fahimci ba bacci take ba shine bata son gani, ajiyar zuciya me sanyi ya sauke suka gaisa da Jaddah kan, Jaddah da mammi suka fita akan zasu je wurin fa'iza daga chan Jaddah zata wuce gida mammi ta dawo ɗakin. Shi cewa yayi ba yanzu ba, zama yayi ya kishingida idanunshi a lumshe yana tuna the best moment of his life, be taɓa sanin haka mata suke ba lallai fauzar tashi ta daban ce, a kan labbanshi ya furta "precious pearl" wato lu'u lu'u mai daraja. Murmushi ya saki yana gyara kishingidarshi haka ma ya gode. A hankali ta soma buɗe idanunta ta kure shi da kallo, dukda ba fuskantar ta yake ba saide tana iya hango farar fatar fuskar tashi da take cike da kwwantanccen saje da suka yi lublub, zara zaran gashin idanunshi da suka sauko sossai waenda suke taimakawa wurin maida idanunshi sexy kaman me jin bacci, gashin girarsa kaman zana mishi ita aka yi baƙi sidik, komai nashi me kyau ne da tsari. Ganin yana motsa idanun alamar ze buɗe yasa tayi saurin janye nata tana lumshewa, murmushi me sauti ya saki a jikinshi yaji tana kare mishi kallo kuma tsab ya ganta ta ƙasan idanunshi ya barta ne ta morewa kallon nashi. Miƙewa yayi Tsam ya nufi gaban gadon ya ja silver chair ya zauna dab ita cikin yanayin maganar shi yace "ya dae ƴan mata? Na miki ne?" Takaici ne ya zo mata wuya, kaman ta kurma ihu ji wani zance anan fisabilillahi. Chan ƙasa ƙasa yace bayan ya kama hannunta ya saka cikin nashi. "Precious pearl buɗe idanunki ki kalleni son ran ki, ni ɗin naki ne gabaɗaya, Mallakinki ne.. Ki kalleni har ki gaji babu mai miki hijabi" Bata motsa ba kaman ma bata san yana yi ba, murmushi ya saki Sam baze yi fushi ba don ya san yayi laifi, lallaɓata ze tayi har ta sauko. "Fauuuzaaa..!" Ya ja sunan wadda ya saka ta jin kiran har cikin jininta, tsammmm haka tsikar jikinta suka amsa. "Na san ban kyauta ba, na miki ba daidai ba amma wallahi ba da niyya bane so da kishin ki ne ya janyo, kiyi hakuri, kiyi min duk wani hukunci zan ɗauka amma banda shariyar nan please...ki taimaki bawan Allah Faizan kar zuciyarsa ta tsaya da aiki" Nan ma bata buɗe idanunta ba, se baki da ta ɗan turo, red lips ɗin nata se sheki suke Dukda babu abunda ta shafa musu, caramel skin ɗin nata yabi da kallo kaman da madara take wanka tsabar shekin da fatar tata take Dukda ba fara ba ce. Hannunshi ya kai ya zame ɗan kwalin kanta ya sanya ya fara shafa lallausar gashin kanta alamar rarrashi, ko motsi ta ƙi tayi, jin za'a shigo ne ya sanya ya miƙe ya rankwafo ya bata zazzafar peck a goshi sannan yayi pecking hannunta dake cikin nashi kan ya saki ya koma da baya ya zauna inda ya tashi. A ranta take raya wannan gayen bashi da kunya, tsaki ta ja kaman ta buɗe idanu tayi ta dukanshi ko zata huce take ji. Dr ce ta shigo, Gaisawa suka yi cikin mutunci tace "Captain, Mrs Faizan kaka ta samu sauƙi ga takardar sallamar ta nan amma please a sahirta mata har ta warke don ta sha matukar wahala" Wani irin smile yake saki yana shafa kanshi ba se ta faɗa ba ma ai yanzu shi da ya kara gangancin rabar ta ai se da amincewarta ɗari bisa ɗari. "OK Dr. Thank you and in shaa Allah za'ayi yadda kika ce" Karbar takardar yayi se ga jadda ta shigo ashe bata wuce ba, se kawai yace bari yaje ya biya bill ɗin kan sun Haɗa abunda zasu Haɗa se su wuce. Fa'iza ma an sallameta don taji sauƙi sossai, saide har yanzu bata daena share hawaye time to time ba tana tuna irin evil mom da Allah ya bata. Duk a tare suka fito, Fauzar na tafiya a hankali ko inda yake bata kallah ba, a maimakon ta shiga motar shi da ya buɗe mata se ta wuce ta buɗe na Farhan ta shiga gaba, Fatima na baya da zaliha. Jaddah da mammi ne suka shiga nashi ya ja ya tafi kan Farhan ya bi bayanshi. Dayake lafiyar motar ba ɗaya ba yasa Faizan ɗin ya tsere mishi kuma da yanayin tuƙinshi don kowa ya san yadda mutanen Abuja suke tuƙi ba kaman na sauran garuruwa ba. A hankali Farhan ya shigar da motar cikin gidan, daga chan kofar sashen jadda suka hangi Faizan na tsaye yana amsa waya, kaman an ce ta kalli chan gefen kofar su se taga motar Aunty Fatima zaune a driving seat fuskanta a kumbure suntum ta kure Faizan da kallo. Buɗe motar Fauza tayi ta fito, daidai fa'iza ma ta fito amma se suka yi sashen Mammi da zaliha don chan mammi tace ta je, yayinda Fauza kuwa ta nufi sashen Jaddah babu abunda take so irin tayi wanka ko zata sake jin daidai, Kure ta Fatima tayi da idanu tana jin tukukin bakin ciki yadda taga Faizan duk hankalinshi ya ɗauku kanta ita kuma tana tafiya kamar hawainiya. Tada motar Fatima tayi a ranta tana ayyana da ta bar wa Fauza Faizan wallahi gwara ayi biyu babu, sake motar tayi tayi kan Fauzar gadan gadan, kanta na a ƙasa Sam bata lura ba, yayinda Faizan kuma idanunshi na kanta ta ɗauke mai hankali kaman an ce ya waiga se yaga Fatima tayi kanta da mota... Wani irin hantsilar da wayan hannunshi yayi ya nufe ta da gudu yana kwala kiran sunanta a tsorace ta ɗaga kai kan ta waiwaya taji an yi sama da ita da mota, ta bugi gaban motar tare da faduwa ƙasa tana jin yadda Faizan ya sake kwala kiran sunanta idanunta suka lumshe. Da gudu Fatima ta juya kan motar ta nufi gate, se daka tsalle gateman yayi don shima saura kiris ta take shi, Farhan da shima ihun Faizan ne ya rinjayeshi ya fito daga sashensu na en maza haka muryar tashi tayi sanadiyar fito da rabin ahalin gidan, babu wadda ze ce ya taɓa jin muryarshi haka don bashi iya ɗaga murya in yana magana kaman da kanshi yake se yau. Ɗagota yayi ya sa akan kafar shi a rikice yana kiran sunanta ba kakkautawa yana cewa ta buɗe idanunta, saide inaa bata jinshi seda Farhan ne yace "Ya Faizan dauko ta mu wuce asibiti" Kan ya tuna da wani asibiti da gudu ya sabeta zuwa motarshi Farhan ya buɗe, mammi na riƙe da Fa'iza da ta sake sakin kuka itama tana jin kunar wannan abu a ranta kaman tayiwa Fauza kuka, me mutanen nan suke nema da ita? Amminta ma komawa sashensu tayi tana me share hawaye, jaddah kam driver ta sa ya ɗauke ta ta bi bayansu tana ta tsinewa Fatima da Aunty Albarka. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 32 **Assalamu Alaikum warahmatullah, fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya, kun jini kwana biyu shiru nayi tafiya ne kuma ban zauna ba har saida na dawo jiya da dare, kwata-kwata ban samu time ɗin kaina ba se yau... Ku yi hakuri kaman yadda na yi alkawari kan azumi zan karkare wannan littafi wadda be dayawa saide na tabbatar saƙon ciki me girma ne in ka fahimta.. Abu na biyu shine KE WACCE KIKA SAYI LITTAFIN NAN MUSAMMAN DON FITARWA BA ZAN CE MIKI ALLAH YA ISA BA SAIDE IN CE KIN KYAUTA KE KIKA SANI DA FITAR RANA DA FAƊUWAR SHI IN HAR INA DA HAKKI A KANKI*** Suna fita a gidan da wannan mugun gudun basu yi wani nisan kirki ba ta ruftawa wani kwalbati duk jikin ta rawa yake na abunda ta aikata, ihun Aunty ne ya farkar da ita sama sama take jin mutane na cetonsu, basu sake sanin inda kansu yake ba se kusan bayan awanni shidda, Allah ya taimaka babu wani serious ciwo suka biya kuɗin bills suka fice, ita dae Fatima takaici da bakin ciki sun hanata cewa komai, kawai machine suka tare suka nufi gidan iyayen Aunty ɗin inda a duniya bata taɓa ƙauna ba, ta tashi ne da baƙin cikin kasancewarta ƴar talakawa Dukda iyayenta nagartattun talakawa ne masu kokarin kiyaye dokokin Allah saide ita kullum a blaming ɗinsu take na kasancewar su hakan tun kan tayi wayo ta san karyar kuɗi da bin ƙawaye ƴaƴan masu kuɗi, da wasu irin banzan buri, ta auri mahaifin Fatima wadda bashi da irin kudin da take so, sbd in ta zauna babu wadda ze Santa ta zama sannaniya wacce duk inda zata shiga a ƙasar Nigeria an san da zamanta yasa ta kashe auren bayan dogon bincike akan gidan prof, shine ta aure sulaiman dukda ba hakan ta so ba saide babu yadda ta iya, gashi yanzu zata komawa rayuwar da ta fi tsana nan duniya. Da sallama suka shiga gidan nasu da rabin shi a zube an kare da buhu duk jar ƙasar gasu nan a barbaje ko ta ina, idanun Fatima ne ya fara kaiwa ga mawanki kwanuka ne a wurin da wasu irin bakaken tukwane waenda zan iya rantsuwa tunda aka saye su basu taɓa ganin ruwa da sunan wanki ba, kuma duk sbd rashin kuɗin sayan omo ne. Aunty ne ta kai idanunta kan dakunan gidan guda biyu banda jar block babu abunda ke jikin ginin ko arzikin Plaster bare fenti, kuka Fatima ta fara "Aunty kina nufin anan zamu cigaba da rayuwa?" Aunty tace "na lokaci kaɗan ne kan mu samu mafita" Tana maganan ne kaman itama zata yi kukan, kanta Sara mata yake sbd tsabar tashin hankali. Maihaifiyartace ta fito kana ganinta kaga wahala da talauci ta zuba musu idanu tana kallo.. "Yau kuma shamsiyya da mu kika tuna?" Kuka ta fara tana cewa "inna Sulaiman ya sake ni!" "Ashe muna da daraja da ƙima da har don an sake ki zaki waiwayi gidan nan? Mu da kike jin kunyar nuna mu a matsayin iyayen ki? Mu da duk yaran da kika haifa bayan wannan itama na manta shekarar da na ganta akwai wadda kika taɓa nunawa gidan nan bare mu? Shekara nawa Shamsiyya ki ci ki sha ki kwanta ba tare da mun zo ranki ko sau ɗaya ba? Aurenki na biyu fa hayan iyaye kika yi kika yi wannan aure hidimarki saide ƙawaye en karya da dangin su a haka dama kike son ganin alkhairi? Ba zamu kore ki ba ga ɗaki shiga ki zauna duniya ce ta fi bagaruwa iya jima" Wucewa suka yi suka shiga fallan ɗakin da babu komai ciki se buhu a shimfide suka zube, kowa da abunda yake sakawa ita dae Shamsiyya Tunanin ta yafi tafiya ta yadda zata dau fansar wannan wahalar da ta sha, yayinda ta wani bangare take Adu'ar Allah ya sa ma wannan fitinanniyar yarinyar da ta tsole musu idanu ta mutu ma kan su isa asibiti. **** Ta ɓangaren Fauza kuwa emergency aka yi da ita, Faizan ya kasa zama se jeka ka dawo yake yi hannunshi ɗaya dunkule yana dukan ɗaya dake ware, kusan duka en gidan zuwa yanzu sun iso har da su Prof da abun be faru a gabansu ba, saida likitoci suka share awanni sama da huɗu kan suka fito suna yarfa gumi a tsorace Faizan ke Kallonsu bakinshi ya gaza furta kalma ko guda ɗaya ne.. "Dr kayi magana mana kayi shiru?" Cewar Farhan. "Alhamdulillah mun samu mun ceto rayuwarta ba serious ciwo bane in shaa Allah, tsorata ce ta saka ta wannan doguwar sumar" Duk ajiyar zuciya suka sauke, Faizan be jira wani bayani ba kuma ya wuce likitan ko jin kiran da yake mishi be yi ba ya tura kofan ya shige. Tana kwance kan gadon ya karasa kaman ze zubda mata hawaye tsabar tausayi ya riƙe hannunta yana shafa kanta bakinshi ya buɗe a hankali ya fara magana "kiyi haƙuri precious pearl I couldn't save u from that bastard attack, am so sorry da kika kasance a haka in front of my eyes... Please be fine kin ji? Just be fine ki yafemin and I promise you a happy life that will last to end" Dukawa yayi yayi pecking goshinta yana kallon lips ɗinta da babu komai a kai se ainihin red nd black color ɗinsu da suke sarƙe cikin juna suka bada wani kala me kyau, babban yatsarshi ya sa ya shafa lip ɗin yana ta aikin kallonta a ranshi kuma yana ayyana yadda ze fara neman Fatima ya koya mata hankali don bata sha ba. Idanunshi zube a kanta ya tafi tunani, ya sani lokaci ɗaya Fauxa ta chanza akalar zuciyarshi ta sakata rusuna bisa burin da ya ɗauka nayi mata rashin mutunci a gidanshi har se ta gudu da kafafunta, ya fara gudanar da shirin ne ta hanyar Haɗata da ayyuka kala kala a gidan nashi kuma ya barta a matsayin ta na kanwarshi a tunaninshi zata kawo mishi musu ko rashin kunya yadda ze samu hujjar ladabtar da ita da kyau sede ta cinye wannan jarabawar ta hanyar haƙuri da juriya, sanyin hali da tsabta na ban mamaki wadda be taɓa zaton hakan take ba. Abu na biyu shine son da take yiwa iyayenshi kusan sune komai nashi duk me son su kuwa dole ya so shi, wannan ya taka rawar gani sossai wajen ganinta da mutunci da daraja, Sam baze ce ga sadda ya fara son ta ba saide ya san ya zuwa yanzu zuciyarshi gabaɗaya cike take da tsananin so da tausayinta.. Dafa shi da Baba Alhj yayi ne ya saka shi ɗagowa tare da waiwayawa iyayen nasu ne ciki se Jaddah. "Ka Daena zurfafa tunani haka Faizan in shaa Allahu zata samu lafiya" Kanshi ya mayar ƙasa yana zare hannun nashi cikin nata ya mike tare da basu kujera, fuskanshi Sam babu wata walwala. Kwananta biyu a asibitin don ranar da aka kaita da yamma ta farka, duk shigowar shi baze shigo hannu banza ba ze shigo da abubuwan ciye ciye kuma ya zauna ya jima suna ɗan hira da Jaddah ko ya zauna shiru rike da waya ko idanunta biyu bata taɓa gaisheshi ba Kallonshi ma ta ƙi tayi, abun na damun shi amma ya bata space ta warke tukuna. Shi aka baiwa sallamar ta, bayan ya shigo yace "zaliha Haɗa kayan ku mu wuce gida" Kasancewar su biyun ne kaɗai a ɗakin Jaddah ta je gida. Haɗa kayan tayi, fauza da fuskanta ba wani fara'a ta sauko sanye da hijab maroon har ƙasa, jerawa suka yi da zaliha tana rike da wasu kaya suka nufi motar tashi, zaliha ta zuba kayan a booth yayinda ta dawo ta buɗe baya ta shiga, Fauza ta buɗe bayan da niyyar shiga ta ji muryarshi daga bayanta "Dawo gaba ki zauna" Bata waigo ba kuma bata saki kofan ba. Idanu ya zuba mata se yanzu take son nuna mishi taurin kan nata? Ya ayyana hakan a ranshi yanzu baze iya fushi da ita ba in yace ze iya ma ya san babban karya yayi, hannu ya sa ya buɗe gaban ya zare hannunta daga baya ya sanyata a gaban tare da rufewa ya zagaye. Kamshi da sanyin motar suka ratsa ta, dukda ta san abunda take yin ba daidai bane amma dole ta nuna mishi kurenshi na laifin da ya aikata mata, har a asibiti bata bar anfani da wasu magunguna da Jaddah ta jiko su a wani katon buta ba tana tsarki Dukda ta warke se abunda ba'a rasa ba amma bata manta azabar da ta sha ba, haushin shi take ji kaman ta shake shi. A hankali yake murza stirring ɗin idanunshi zube bisa titi, babu wadda yayi magana a motan har suka isa gida, be gama parking ba ta balle murfin motar tayi sashen Jaddah, da kallo ya bita har ta ɓace mai ya sauke ajiyar zuciya yana shafa gashin kanshi. Zaliha ce ta tattare kayan sallamar tayi sashen jaddar itama. Daga ranar ta fara wasan ɓuya dashi, bata bari su haɗu ko a hanya, ze zo sashen Jaddah ya gama zaman shi ko kyallin ta baze gani ba, ya san tana avoiding ɗinshi ne gashi yana da tafiya tunda ya jima a gida dole ze koma wurin aiki and babu wadda yayi mishi maganan ya kamata su koma haka har ga Allah ya gaji matarshi yake buƙata Rigingine yake a kan kujerar Jaddah, chan yake jiyo sautinsu ita da Fa'iza tana tsokanar fa'iza akan wai sun sasanta kansu da Faraj don aiki suke daga shi har Farhan yanzu fa'izar ce ke level 1.. "Gwara ma ki bari a saka mana kusa mu sha buki, yadda zan zage na aurar da ƴar ƙanwata itama" Fa'iza na murmushin yadda Fauza bata taɓa bari ta kuntata ko ta shiga Tunanin ba, cike da jinjinawa haƙurin Fauxar ta yadda kowa ze yaɓa mata magana ko ya zage ta ko ya mata zafi babu me fahimta sbd bata nunawa tace "waye kanwar taki? Lallai ma yarinyar nan karki manta na baki kwana dai dai har talatin da ɗaya... Rainin wayau" Dariya Fauza tayi tana cewa "kin manta kwana ɗari ba ɗaya kika ba ni, ke ajiye batun wannan karki manta wadda nake aure don haka duk gidan nan karkashina kuke kuma wallahi dole ku ce min Aunty" Yadda tayi maganan ba fa'iza kaɗai ba har shi seda ya murmusa, fa'iza na shirin magana suka Haɗa idanu dashi. Da sauri tayi kasa tana gaisheshi ya amsa cike da kulawa ta wuce, yayinda Fauza ta nufi wucewa ba tare da ta ce mishi komai ba, cikin zafin nama ya miƙe ya taka biyu ya cabke hannunta, juyowa tayi se idanunsu suka sarƙe.. Kallonta yake da gabaɗaya idanunshi, a hankali cikin kasa sossai da murya yace "Fauziyya ni kike yiwa rashin kunya yanzu?" Kau da kai tayi tace "me nayi kuma?" Yace "yanzu kin ga ya dace ki wuce ni ba tare da kin gaisheni ba?" Ba tare da ta kalleshi ba tace "Good evening..!" Ta zare hannunta zata wuce ya sake janyo ta, "Fine and why are you avoiding me?" Ya faɗa yana riƙe da kafadar ta. Kanshi ta maida idanunta tace "Gaskiya kake son sani? Toh ina kaucewa ganinka ne sbd bana so idanunka su cigaba da kallon wannan mashayiyar kuma mazinaciyar fuskar t...." Bakinta da ya buge ne ya saka ta maida kanta ƙasa hawaye ya fara zuba a fuskanta.. "Baki da hankali ne kike danganta kanki da waennan kalamai?" "Au wai har ka manta? Ba ni ce na dangata kaina da hakan ba Kaine ka jefe ni da waennan kalamai, akwai saura ma ai cewa kayi bazaka iya cigaba da zama da me bin maza ba.... Nima kuma ba zan iya cigaba da zama da me saurin fushi da zargi ba don haka kaman yadda na yiwa su Baba biyayya a auren nan yanzu ya zama wajibi a dubi lamura na a raba wannan aure Ka sake n...." Rufff ya rufe bakinta da nashi tare da matsota gabaɗaya ta shige cikin kirjinshi, baze iya cigaba da ɗaukan kalaman ta ba, tayi babban zunubi da kunnuwanshi bazasu juri ji ba bare har ya wassafa aiwatuwarshi.. Takarkarewa tayi ta ture shi da iya karfin ta, jikinshi a mace yake don haka kujera kawai ya zube yana dafe goshi a hankali har muryarshi na cracking yace "Am so sorry... Pls karki sake faɗar irin wanchan Kalmar yayi min girma zuciyata bazata iya daukarta ba.." Kuka ta fashe dashi kawai ta juya da gudu tayi ɗakinta, a gado ta zube ta sha kukanta ta more kan ta miƙe ta faɗa toilet tayi wanka ta san kilan ya zuwa yanzu fa'iza ta gaji da jiran ta a ɗakin Jaddah ta wuce... Fita tayi ga mamakin ta har lokacin yana kwance cikin kujeran parlorn idanunshi a lumshe hannunshi kwance bisa kirjinshi, daga yadda yake karkada kafa zaka san ba bacci yake ba. Idanun da suka yi laushi ya buɗe ya kure ta da kallo, baki ta taɓe ta wuce ta fice daga sashen gabaɗaya. Bayan isha tana kwance kan cinyar Amminta dake taje mata kai a hankali Falaq tace "ji wani sabon iyayi yanzu Fauxa Ammin ce zata miki taza?" Bakinta ta murguda tace "Ina ruwan wani? Amminki ko Ammina?" Tahowa tayi da nufin gwabe mata baki Ammi tayi saurin riƙe hannunta "Ke Falaq Rabu min da yarinya akan me zaki daketa bayan kece kika fara tsokananta?" "Laaa Ammi yau bayan Fauzar kike bi? Lallai ma Ammi" Ammi tace "eh na bi ɗin" Ficewa tayi fuu sbd yadda Fauxa ke mata dariya Ammi na murmushi tace "Auta tashi mu yi magana" Mikewa zaune tayi tana fuskantar Ammin tace "Toh Ammina" "Kowa a gidan nan ya fahimci tsakaninku da Faizan babu daaɗi har ma mahaifinki ya so ajiye ki se kuma baba prof ya hana, nima shawara zan baki a matsayina na mahaifiyarki, ko menene Faizan ya miki kiyi hakuri ki bishi ku koma yana da aiki amma yake ta faking excuses duk sbd ke, ya samu baba prof akan a bashi ke ku koma baba prof kuma ya ce in har ba ke kika shirya komawa ba babu ruwanshi, kin ga dae irin karamci da soyayyar da iyayenshi ke miki ko don wannan zaki duba mafi soyuwar ɗan su ki kyautata mishi sbd su ma su ji daaɗi..." Fuskanta tayi kicin kicin dashi har hawaye na shirin zuba tace "Ammi fa zar..." Ɗaga mata hannu Ammi tayi tace "bana son jin komai in dae har don abunda ya Haɗa ku ne, shawara ce kawai na baki kiyi tunani" "ni dae Ammi ba zan iya komawa ba, baya sona nima haka kuma yanzu duk abunda ke boye ya riga ya bayyana kowa ya kama gabanshi kawai.." Kallonta kawai Ammi ke yi, zata yi magana kenan suka ji an shigo da sallama... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ 33 "Sannu da dawowa baba" Fauza ta faɗa tana ɗaukan dankwalin dogon Rigan jikinta tana ɗaurawa a kanta, Ammi ma sannu da zuwa ta mishi ta mike don kawo mishi ruwa, Fauza bata motsa ba don ta san ko ta tashi Ammi cewa zatayi ta dawo ta zauna kar ta hanata samun ladarta. Gaisawa suka yi da baban Dukda sun gaisa da safe shima cikin hikima yayi mata hannunka me sanda Dukda be fito kai tsaye yace maganansu da Faizan bane sede ya nuna mata rama Alkhairi da Alkhairi abu ne me kyau, kuma Hausawa sun ce ka gaida me gaisheka ko da kuwa baze amsa ba, shigowar Ammi ne ya katse su. Abinci da ruwa ta kawo mishi, Fauza ce ta zuba mai yace ta matso su ci rana na farko kenan tun wayaunta ta sanya hannu suka ci abinci kwano ɗaya da mahaifinta Ammi na zaune daga gefe suna hira jefi jefi ranar har kuka tayi, Aunty ba karamin cutar ta tayi ba ta hana mata wananan shakuwa da soyayyar na tsakanin iyaye da 'ya'yayensu, se da taji bacci kan ta sallamesu bayan tayi waya da husna a wayan Ammi tana ta shagwaɓa akan ita kam zata dawo gidan Fauza, da wayan ta fita parlor ta Haɗa conference da Ya fadeela take ba su labarin abunda ya faru. Sbd duk bata yi natsuwar magana da yayyun nata ba se yanzu, duk seda suka zub da hawayen jimami, suka yi mata barka sannan suma duk sun roketa ta koma gidan Faizan Dukda sun fahimci haushin abunda ya mata har lokacin yana ranta sede ta ƙi nunawa ne kawai har fadyaa ke rantsuwar ita tun randa suka je gidan ma ita da Ya Faahim seda suka yi gulmar soyayyar da suke yiwa juna a ɓoye. Ita dae fadeela se dariya take yayinda Fauza ta shagwabe akan lallai lallai ita ba haka bane tana Haɗa ya Fadyaa da Ya fadeelah, sun sha hira kan suka yi sallama don ma what'sapp call ne da ta tabbatar ko biyar baze saura a wayan Ammin ba. Anan kan stand ta bar mata ta wuce sashen Jaddah, kan ta shige ta hangi fitowanshi daga mota yana waya a natse yake tafiya yayi sashensu na ƴan maza, ta jima tsaye tana Kallonshi seda ya wuce kan ta juya itama ta shiga sashen, ɗakin Jaddah ta shiga suka ɗan yi hira kan taje ta kwanta bayan ta rufe kofan ta. Washegari da safe ko karyawa bata yi ba ta dae yi wanka ta sanya wani cotton blue shiffon shirt da straight skirt baƙi se ta ɗaura black dan kwali a kanta, se kamshin khumras na sabon gyaran da Jaddah ke mata take zubawa, fitowa tayi ta shiga kitchen ta samu zaliha na yin kosai da koko, baki ta taɓe ta warware gyalen da ta ɗaura a kanta se ta yafa ta fice daga sashen. Har ta nufi sashensu se ta juya ta nufi na mammi don tun shekaranjiya rabon da su haɗu ta aiko mata da kifi dafaffe ma da rana bata je godiya ba kuma kila abunda ta dafa se ya fi na jaddar nan daaɗi. Da sallama ta shiga parlorn, Mammi na zaune tana karyawa itama maraba tayi mata fuskanta cike da fara'ar ganin surukar tata, zama tayi suka gaisa sossai kan mammi ta mata umarni ta isa akwai abincin a dining ta ci abin ta. Tsam ta mike tayi dining ɗin ta diba kuwa me ɗan yawa ta fara ci a hankali. Sam bata san mammi har ta gama ta mike ba ma, fitinannen kamshinshi da ya cika wurin ne ya sakata saurin ɗagowa se suka Haɗa idanu, da sauri ta ɗauke kanta ta mayar kan abincin ta da idanu ya bi abincin na seconds kan ya samu wuri ya zauna ya miƙe kafafunshi ya zuba mata idanu yana kallo. Kasa cigaba da cin abincin tayi, se kawai ta miƙe da niyyar barin wurin kafa ya sa mata tayi gaba zata faɗi yayi hanzarin janyo hannunta se gata bisa kirjinshi, rungumeta yayi da kyau a cikin kunnenta ya raɗa.. "Ke kam baki san haƙuri bane Fauza? Pls kiyi hakuri mu koma gidan mu hakanan wallahi na miki alkawari ba zan ƙara yi miki komai ba idan har ba da yardar ki ba, am so sorry bisa duk abunda suka faru ki yafewa mijinki kin ji?" Bata ce komai ba se kokarin tashi da take, ya kara matse ta cike da masifa ta fincike bata ce komai ba ta juya zata fita, she's killing him da wannan shirun wallahi.. "I'm hungry ki sama min wani abu please" Bata juya ba ta fice, sashensu taje suka gaisa da mammi kan ta koma sashen Jaddah, Jaddah na zaune a parlor ta mika mata wani cup da wani haɗi ciki karɓa tayi sbd yadda yaji madara da zuma ta zauna ta shanye tass ta ajiye kofin, Jaddah tace "Fauza ki shiga kitchen ki sama ma mai gidanki wani abu duk abunda aka yi a sashukan biyu ba ci yake ba shima" Baki ta tura tace "me zaliha ke yi Jaddah?" Jaddah ta mata dakuwa tana cewa "zaki ci ƙaniyarki fa Fauziyya wai aka gayamiki zuba miki idanu da aka yi tsoron ki ake? Ki zauna kina Jawa mijinki aji mijin ma irin Faizan dake da matukar wahalar samu, wata macen na kyalla idanu ta kwace shi tsab ki zo kina min kuka wlh se na lahira ya fiki jin daaɗi, a kanki aka fara samun irin wanchan matsalar a da da se an dauko mu a ka a kaiwa miji a kullo kofa, to karki kiyaye ni kiga.." Bakinta kaman ze taɓa gini ta miƙe ta wuce fuu zuwa kitchen girkin take sede ba da wani armashi ba, da gangan sbd ta san be son yaji kwata kwata tayi girkin da zallar attarugu ta saka a plate ta ɗaura a tray bayan ta rufe ta ɗauko ta fito ta ajiyewa Jaddah "To wa ze kai mishi? Kin dae san Zaliha ta wuce kasuwa" Sake ɗauka tayi Jaddah na kallonta har ta fice kan ta taɓe baki tace "Zaku ji dashi dukkanku biyu wlh" Don shi ya zo ya roki Jaddah da ta saka ta yi mishi girki please Allah yayi kewar taste ɗin abincin ta. Da sallama ta tura ɗakinshi fitowanshi daga wanka kenan se lokacin ta tuna haduwar da suka yi a sashen Mammi da kananun kayan shan iska ne wando three quarter me taushi da kuma riga marar nauyi, ɗaure yake da towel iya kugu, saurin ɗauke kai tayi ta karasa gaban center table ta ajiye tray ɗin zata juya.. Sam baya so ta fice da sauri yace "serve me please" Dawowa tayi ta buɗe plate ɗin kawai ta sanya mishi spoon don ba'a wani coolar ta saka ba, ta wuce frigde ta dibo ruwa ta zo ta ajiye mishi daidai lokacin ya zauna ba tare da ya damu ya saka kaya ba Dukda Acn da yayi yawa a ɗakin zafi yake ji kasancewar damina kilan a samu ruwa zuwa jimawa don zafin yayi yawa. Se ta tsinci kanta da kasa tafiya ta tsaya tana kallon abincin gabanta na faɗuwa, don ta san yadda yaji yake wahalar dashi. "Yaaa...ya" Da sauri ya ɗaga kai ya kalleta tace "Karka ci" Ta matso tana shirin ɗauke plate ɗin ya riƙe hannun ya kalleta sossai kan ya kalli abincin se ya lumshe idanu kan ya kai baki, wani irin radadin yajin da ya ziyarci kwanyarshi ne ya saka shi saurin kallonta ita kuma ta runtse idanu tana jin wani tashin hankali na bijiro mata. "Idan har wannan shine hukunci na precious pearl na karɓa, zan ci har se kin ji hukuncin ya miki daidai da muradinki" Yana kai nan ya cigaba da ci abunshi Dukda yadda yake jin kaman harshen shi ze tsinke, idanunshi a take suka rine jijiyoyinshi suka tattashi, a hannunta take jin yadda jikinshi ya ɗauki rawa don Allah yayi shi yaji ba abunshi ba gashi yana da masifaffen ulcer.. Ze kai cokali na uku tari ya sarƙe shi, numfashin shi na fita babu daaɗi hakan kuma ya sake diba ze ci da sauri ta buge spoon ɗin tana zub da hawaye... Kokarin ɗaukar spoon ɗin yake tayi saurin jan gabaɗaya table ɗin ta maye gurbin table ɗin gwiwowinta a ƙasa ta ɗauko ruwa ta mika mishi a rikice tana cewa ya sha yana ture hannunta. Tuna yadda suke tafe cikin ruwa ya yafa mata designer suede ɗinshi yana kare mata ruwa shi kuma ruwan na dukanshi amma kaman be damu ba har zuwa cikin gida tayi, ta kuma tuna yadda ya kula da ita a sadda bata da lafiya Dukda a lokacin ranshi a ɓace yake da ita, ta tuna yadda a duk sadda take neman taimako shine mutum na farko dake kawo mata ɗauki he's her life savior, meyasa don ya mata laifi cikin rashin sani zata azabtar dashi ta wannan hanya, shin shi kaɗai ne yayi mata irin wannan zargi cikin rashin sani? Meyasa bata hukunta kowa ba se shi... Faɗawa jikinshi tayi tana kuka tana cewa wlh ta hakura ta yafe mai yayi haƙuri, kankameta yayi idanunshi a runtse ganin har lokacin ruwan yaki ya dawo dashi daidai kawai tayi saurin haɗe bakinsu, kaman jira yake ya cabke yana jin his life depend on that yana saketa yaji ze ji, sanyin tongue ɗinta na ratsa dukkan sassan jikinshi a hankali ya fara dawowa hayyacinshi... **** Kwano me ɗauke da tuwon datsan masara da wani bakin miyan kuka banda daddawa da gishiri babu abunda ke ciki da aka dangwalar musu ya saka Fatima rushewa da kuka tana kallon Aunty da fuskanta ke a kumbure sbd ciwon kai da ya matsanta mata tunda aka yi wannan hatsari tana cewa "Wallahi na gaji Aunty, na gaji da wannan cimar dube ni fa, dubi yadda jikina ya fara komawa tsabar yunwa da talauci, ni dae Allah ki san yadda zaki yi dani ki kwatanta min inda zan je na samu maganin damuwata..." "Fatima gwara dake kina iya cin abincin dube ni, babu abunda ke shiga cikina, bakya tausayina? Dubi yadda fuskata ta kumbure baki maganan muje asibiti a duba ni se wani maganan Faizan chan..." Aunty ta faɗa a wahalce "ni duk babu ruwana da wannan, ko ki nema min mafita ko in koma gidan mahaifina nima in barki ki fama da naki iyayen... Ba zan iya ba wallahi" Da kyar Aunty ta sakata amincewa zasu je su ga likita, suka shirya da kafa suka je wani asibitin gomnati, sun sha wulakanci kam su da suna zuwa asibiti za'a karɓe su hannu bibbiyu se gashi cleaner ma na asibitin na zagin su, test aka bata bayan sun yi, tashin hankalin da ya ziyarcesu a sadda suka ji sakamakon result ɗin Allah ne kaɗai ya sani. Ciwon daji ashe take dashi gashi an mata allurai a sadda tayi hatsari shine mafarin hauhawar ciwon. Tashin hankali wacce ba'a sanya mishi rana... *** Jin yana shirin zarcewa wani babin ya sakata janye jikinta idanunta a ƙasa, hannunta dake cikin nashi take shirin zamewa yayi saurin sake gimtsewa a hankali ya buɗe idanunshi da suka birkice yace "Fauzaaaa...!" Ya kira sunan murya a sarƙe, bata iya ta kalleshi ba ta amsa a hankali, yace "kin yafewa yayanki? Kin huce?" Shiru tayi kan ta ɗaga kai a hankali, mikewa yayi ya taka ɗaya ya haɗe kirjinshi da bayanta ya sanya hannu ya zagaye kirjinta a kunnenta ya raɗa mata "thank you wifey! Thank you so much... I LOVE YOU" Shiru suka yi a haka na sama da mintuna biyar kan a hankali ya saketa, bata iya Kallonshi ba ta fice da sauri tana jinshi yana cewa ta shirya gobe da safe zasu wuce.. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 https://chat.whatsapp.com/BjpWJdHnjtpKNK4iCeqNwh DƘ 34 Washegari Kaman yadda ya faɗa da safe ya fito a shirye, sashen Ammi ya fara zuwa suka gaisa sbd weekend ne su baba ma suna gida, ya jima sossai anan kan ya musu sallama ya nufi sashen iyayenshi suma duk ya musu sallama akan zasu wuce yau, duk Kallonshi suke da mamaki saide basu ce komai ba se farin ciki dake shimfide bisa fuskokinsu aka ce tsakanin mata da miji se Allah to shine suke kallo. Daga nan sashen Jaddah ya wuce, a parlor ya sameta suka gaisa tace "Ba dae tafiya ba? Na ganka shirye tsab kaman sabon ango" Tsadaddiyar Murmushi yayi yana kallon jikinshi don be ga wani sabon shiga da ba sabonshi bane, sanye yake da wani ɗanyen bowel sky blue an mishi dinkin boda ya zauna mishi sossai, hula zanna a kanshi ya murza ta da kyau se agogo da wayoyinshi dake a hannunshi banda kamshinshi dake baza parlorn babu abunda kake ji. "Kika sani ko zan mai dake ɗakinki a yau ɗin?" Ya bata amsa cike da tsokana, haɓa ta rike tace "zancen kake nema ai ni na jima da raba gari da kai bana auren nan, ina ni ina zama da miskilin miji ka fi mahaukaci ban haushi? Barni in lallaɓa da su Fahad yauwa...!" Yana murmushi yace "ni fito mun da matata mu wuce" "wai ina Zaku wuce?" "Dama daga ina muka fito Jaddah? Na kula na zauna jiran ki se mun yi missing flight" Tsam ya mike ya nufi ɗakin Fauza da kallo baki sake Jaddah ta bishi kan ta fara gyaɗa kai tana jiran ganin ikon Allah. Tsaye take a gaban madubi sanye da zani da riga na wata Tsadaddiyar super, kanta ba dankwali tayi loose parking wadda ya fitar da wasu daga jikin gashinta ya sassakesu bisa wuyanta da fuskanta, tsayawa yayi Chak hannayenshi zube a aljihu yana kallonta cike da so da ƙauna, ji yake kaman ya tsaga kirjinshi ya sakata ya huta da azababbiyar kaunarta. Takawa yayi a hankali ya nufe ta ganin yadda take kokawa da zip, bata ji zuwanshi ba se jin hannayenshi masu taushi tayi cikin nata, lumshe idanu tayi sbd yadda sanyinsu suka ratsa har ɓargonta ta shaki kamshi me cike da natsuwa wadda ba tantama daga gareshi ne sbd ita bata taɓa jin irin turarenshi wurin kowa ba, haka suke ne ko combination da yake na musamman ne suka bada wannan sassanyar kamshin bata sani ba. A hankali ta buɗe idanun ta sauke su tarrr bisa kamilalliyar fuskar shi ta mirror ɗin.. "May I?" Yayi tambayar yana nuna zip ɗin da idanu, kai ta gyaɗa tare da ɗan murmushi. Zip ɗin yake ja mata idanunshi kafe a fatar bayantan, bayan ya gama se ya kara taku ɗaya ya haɗe gab ɗin dake tsakaninsu ya sanya hannu ya zagaye ta tare da ɗaura haɓarshi bisa kafadar ta ajiyar zuciya duk su biyun suka sauke. "Good morning yaya" Seda ya ɗan juya idanu kan yace "morning but the Yaya is not accepted, bana so a bani wani sunan precious" Murmushi kawai tayi, yace "an gama da zip, then what?" Ba tare da ta ce komai ba ta nuna mishi sarka dama ta saka dankunne, hannunshi kawai ya miƙa ya ɗauko gashin da suka zazzame yake ɗan tattarewa da hannunshi yana mai dasu sama kan ya fara saka mata sarkar idanunshi kan wani baƙin tawadar Allah dake ɗige daga ƙasan kunnenta, Sam bata ankara ba taji saukar peck a daidai wurin, bugun zuciyarta seda ya so tsayawa. Sake komawa jikinta yayi yace chan ƙasan maƙoshi da idanunshi da suka fara sauyawa "am done baby, sai me?" Tace a hankali itama "sauran ba lallai ka iya ba, let me finish" Be saketa ba ta dauki wani silk black rowsleeke ta mishi ɗaurin Zahra buhari, yana ta kallonta, da idanu ta nuna mishi blue and black embroid lafayarta dake ajiye bisa gado, da kanshi yaje ya ɗauko zata karɓa yace "let me do it for you sweetheart" Ta ɗan wara idanu tace "in ba kana so in je in faɗi bane Yaya bani kayana in ɗaura" Ɗan dariyar maganar yayi yace "Haba yarinya tsawon rayuwata tun fa da na tashi nake ganin Jaddah da mammi na ɗaurawa in har ban ɗauka yadda ake ba kenan kwakwalwar kifi gareni" Dariya sossai ya bata wadda seda ta dara, gyara tsayuwar ta tayi tana jiran ganin ikon Allah, tsab kuwa ya ɗaura mata lafayar ya zagayeta dashi, ba karamin kyau tayi ba. Kallon madubi tayi tana murmushi kan ta ɗaga mishi hannu alamar jinjinawa ya taɓe baki irin ba na faɗa mikin nan ba, bangles ta saka ta ɗauko black handbag da black shoe ta saka, hannunta ya riƙe yana kare mata kallo. "Kin yi kyau kaman Fure precious pearl" Tayi murmushi tace "thank you yaya, and kaima ka yi kyau" Murmushi suka sakarwa juna kan suka fito, Jaddah baki sake take Kallonsu, Fauza ta kasa ce mata komai se shine ya sallameta, har suka fice bata ce komai ba seda suka fita ta saki murmushi, lallai a gaida yaran zamani. Daga mota ya jirata ta shiga wurin Ammi sama sama, tayi ta saka mata albarka kan ta wuce wurin mammi itama albarka ta sha, ta shiga wurin sauran matan a tsai tsaye daga nan ta yada zango wurin iyayenta a parlorn baba prof, nasiha suka mata kan suka sallameta. Fitowa yayi musamman ya buɗe mata gidan baya ta shiga ta zauna, kan ya zagaye ya shiga shima bayan ya zauna tare da sanya hannunshi cikin nata, kan kafadar shi ta kwantar da kanta tana kallon gidan tana tuna irin rayuwar da tayi cikinshi zuwa yanzu, Farhan ne ke tuka su har zuwa Airport kan suka yi sallama. Ko da suka isa ma be barta ta gyara gidan da yayi kura ita kaɗai ba, a tare suka yi aikin tsab suka kamalla suka yi girki marar nauyi kan kowa ya wuce yaje yayi wanka, kusan a tare suka fito ta shirya musu abincin a ƙasa suka zauna suka ci, bayan ta tattare wurin ta nufi komawa ɗaki ya sanya hannu ya dawo da ita jikinshi yana gyara kwanciyarshi yadda itama tayi lub bisa kirjinshi yace "Babe zan yi tafiya gobe it's been a while da na ba aikina hankali hakan kuma yana so ya samar min matsala" Ya karasa yana shafa gashin kanta. Da sauri ta ɗago kai tana Kallonshi Rau rau tayi da idanu, ya san me take tunani ko bata furta ba, shafa kumatunta yake a hankali kan yace "da haka kowacce mace ta saba, nan ɗin gidanki ne babu abunda ze kama ki kinji? Sannan u have to catch up with ur studies, zan samar miki driver kan na koya miki driving ɗin" Ajiyar zuciya ta sauke tana me komawa ta kwantar da kanta, a hankali tace "is it outside country?" Yace "yeah..." Ganin zata sa mishi kuka ya saka shi kara bakinshi bisa kunnenta ya fara zuba mata kalamai da suka kusa sakata sakin murmushi ba tare da ta shiryawa hakan ba. Da yamma likis suka fita tare yayi mata sayayya har da sabuwar waya ya saya mata me dankaren tsada tayi ta murna kuwa. Washegari da sassafe ta tashi ta Haɗa mishi breakfast bayan ta gama taje ta watsa ruwa tana mamakin yadda be takura ta ba da ta tuna mishi da alkawarin da ya ɗauka na baze nemeta ba se in ita ta amince. Sanye da doguwar riga orange nd black na kanti ta fito, tayi kyau sossai tana shirin knocking mai kofa ya fito sanye cikin uniform ɗinshi da yayi mugun amsarshi, kan ta motsa yayi hanzarin rungumarta yana me bata peck a kumatu yace "Good morning my moonlight" Tace "morning yaya, breakfast ɗinka na dining" Murmushi ya sakar mata yana rike hannunta suka nufi fita yace "am already late dear, in na ce zan tsaya karyawa zan ɓata lokaci" Hannunta ta zame tare da turbune fuska tana juya mishi baya. "OMG baby ba dae kin yi fushi ba? Believe me zan karya a Airport I promise" A hankali ta waigo ya kara tabbatar mata tace "Toh ko tea bazaka sha ba?" Yace "uhm uhm ni me daaɗi nake so" Dariya ta ɗan yi tace "tea ɗin akwai me daaɗi akwai marar daaɗi ne?" Kai ya gyaɗa mata yana murmushi Tace "Toh ai me daaɗin ne mu je kaji" Matsota yayi ya manna ta da jikinshi tare da rankwafowa ya haɗe bakinsu saida yayi son ranshi kan ya ɗago yana murmushi yace "this is sweeter, bye take care" Yana kai nan ya juya da nufin tafiya, tayi saurin riƙe hannunshi a hankali tace "bani minti biyu please" Da sauri ta shiga kitchen ta Haɗa mishi abincin a box me kyau yana tsaye yana duba time ta fito, ita ta mishi rakiya har mota ta saka mishi abincin a gefen baya ta inda yake kan ta sakar mishi murmushi tana mishi Allah ya tsare, cike da farin ciki da ƙaunarta me tsanani ya tafi. Kaman yadda ya faɗa karfe takwas se ga driver ta shirya ta wuce school sun haɗu da Afnan suka yi ta murnan ganin juna nan da nan ta hau ɗaura mata abunda ya wuce ta a makarantar. Se yamma lis ta dawo gidan ta ɗan samarwa kanta abun ci kan ta watsa ruwa tana shirin sa kaya se taji wayanta na ringing, dubawa tayi se ta saki murmushi ganin shine ke kiranta, ɗagawa tayi nan fa suka fara hira, jin ta sake sossai ya saka shi ce mata ta kunna data. Kunnawa tayi se ga video Call Sam ta mance ma towel ne jikinta tayi picking, daga chan ya kura mata idanu yana kallo she's morethan beautiful ya ayyana hakan a ranshi. "Ka ci abinci yaya?" Ya karkata kai kaman ɗan yaro yace "wa ze bani precious?" Puppy face tayi tace "Toh ka je ka saya mana yaya?" Yace "ni uhm uhm se an chanza min wannan sunan kan zan ci abinci yau" Dariya sossai ta saki yana ta kallonta yana murmushi, tace "tohm faɗamin wani suna kake so?" Yace "ko ma wani iri ni dae a chanza min yayan nan" Tana dariyar abunda zata faɗa tace "Toh Uncle? Ko mai gida?" Dariya ya saki yana cewa "kuttt lallai yarinyar nan Allah karki sake na kama ki, me wani uncle?" Tace "tohm am sorry mi carazon suna dae se ka gaji dasu in shaa Allah, now please go and eat" Yace "yes my queen, take care of yourself zamu yi magana anjima right?" Kai ta gyaɗa, yana kallonta yace "I love you...u are the story that I never want to end" Tayi murmushi kawai tare da hanging up, ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi he hopes ta so shi watarana. Haka rayuwa ta cigaba, don seda yayi kusan 2weeks be dawo Abuja ba, tana fama da karatu ita kuma a gefe ɗaya yana kasheta da soyayyarsa me tsayawa a rai, zasu yi voice call, su yi chat su yi video call duka, dukda har yanzu in ze mata kalamai na so da kauna ta kan yi murmushi ne kawai ba tare da ta bashi amsa ba amma in ta hira da shagwaɓa ne haka zata saki jiki tayi ta zuba mai, kusan duk abunda ya faru a rana haka da dare se ta bashi labari. Shi kuwa ta bangarenshi ko da awa ɗaya baya iya yi idan har be ji daga gareta ba. "Kin yi sallah? Kin ci abinci? Kar fa ki fita ba hijab, ya lectures kun gama? Ki tabbatar kin yi Adu'a kan ki yi bacci baby, Allah ya miki albarka" Kusan sune kalamai mafi tsada a gareta wadda ba'a kai dare be yi mata waennan tambayoyi na kulawa ba, wani lokacin in tace suna da CA haka sede ta ga text ɗinshi "kin yi karatu? Kiyi karatu bana so wanna CA ya wahalar min da ke" Misalta irin yadda yake kula da ita Dukda distance dake tsakaninsu ɓata baki ne, ta gefe ɗaya matar Faisal ta haihu ya saka driver ya kaita suna da sha tara na arziki don seda ta biya shopping abunda yayi ta bata mamaki sadda ta dawo daga sunan kasa hakuri tayi ta koma ɗakin nashi inda ya ce ta ɗauki kuɗi ɗazu ta je shopping. Wayan ta ɗauko tana Juyawa a hannunta wannan wayanta ne wadda ta taɓa bari a motarshi, to me yake yi dashi? Ta tambayi kanta Kunnawa tayi se taga akwai chaji alamu ana yawan yin chargynshi dubawa tayi babu sim, mayarwa tayi ta ajiye bayan ta kashe ta mike ta bar ɗakin, hirarrakin matan abokanshi ke dawo mata har ta isa ɗaki. Dukda bata sa musu baki ba sede ta ɗauki abubuwa masu yawa ciki, wadda dole zata yi anfani da wasu, ita ɗin idan ta duba se taga kaman tana cikin masifa da tsinuwar mala'iku tunda dae gashi ta hanashi abunda ake kira da auren gabaɗaya sbd wani laifi da yayi mata da har ta mance ma, dukda ba haushinshi take ji ba tsoro take ji, tsoron abun ya riga ya mata tasiri, bayan haka shi matafiyi ne yana shiga wurare daban daban yana ganin mata kala kala in ya faɗa halaka sbd ita fa? Tuna cabin crew na ranan tayi da irin shigar su se taji hankalinta ya tashi, yanzu fa da su yake yawo duk inda zashi, kuka ta fashe dashi tana jin zafin kishi na huda kirjinta. Kaman kuwa yaji a jikinshi se ga video Call daga gareshi, ɗagawa tayi bayan ta share hawayenta. Idanu ya zuba mata na seconds kan ya miƙe zaune yana jefar da pillown hannunshi yace "what happened? Meyasa kika yi kuka?" Kawai se ta sake sakar mishi kukan. "OMG darling please! Menene? Me ya faru?" Ganin tana shirin ɗaga mai hankali ne ya saka ta tsagaita kukan tace cikin wata kalar murya. "I miss you 😩 please ka dawo haka..!" Ajiyar zuciya ya sauke shima cikin kasalalliyar murya yace "kukan duk na kewata ne pretty?" Kai ta gyaɗa tana sake matso hawaye.. "Ya rabb! I wanna hug you so tide right now...but you are too far I also miss you so bad dear.. amma me aka tanadar min da ake so in dawo?" Yayi maganan yana kwanciya kan pillow ta saki murmushi tace "Duk abunda kake so" Yana dage gira yace "really? Duk abunda nake so? U promised? Zaki bani vitamin K, H da L?" "Me kuma hakan mi carazon?(My heart in Spanish). "Lalala baki san vitamin K,H da L ba?" Ya faɗa harda kama baki. Ta gyaɗa kai yace "tohm lemme educate you, vitamin K stands for kiss, H stands for Hug and L stands for love.. Zaki bani?" Kai ta gyaɗa tace "everything..!" "Kar fa ki sa in kamo hanya yanzu?" Dariya ta saki yana murmushi yace "soon zaki ganni kinji? Don't cry again please" Kai ta gyaɗa mai, nan ta sake suka fara labarin gidan suna da kyaun babyn, jin ya kamo zancen saura nata ne yasa ta sallameshi ta gudu. Washegari a gajiye ta dawo daga school ko abinci bata iya yi ba ta sha tea bayan tayi wanka ta saka light black shirt da iyakarshi cinyarta tare da zubewa kan gado bayan ta yi sallar isha. Har bacci ya fara shirin daukarta kawai taji tsayuwar mota, da sauri ta miƙe tana leƙa window se ta hangeshi ya fito sanye da kananun kaya baƙaƙe wadda suka mugun amsar farar fatar shi yayi fresh yayi wani irin kyau, da mamaki take Kallonshi har ya ɓace da alama ciki yayi shine ko ya gayamata yana zuwa? A take farin ciki ya cika fuskar ta, da ɗan gudunta ta buɗe kofa zata nufi sauƙa se suka yi kicibus a parlorn saman, fadawa jikinshi tayi tana murnan ganinshi shima ya rungumeta tsamm yana shakar kamshin ta me daaɗi, daga haka ya nemi zarce mata nan fa tsoro ya bayyana kiri kiri a fuskar ta, janyewa tayi ya tsaya yana kallonta. "Mu je kayi wanka bari na samo maka abunda zaka ci" Tana shirin wucewa ya dawo da ita jikinshi yace "ke kin ƙoshi?" Kai ta gyaɗa yace "fine" Yana faɗar haka ya ɗauke ta chadak se ɗakinshi, tana ta zillewa haka ya ribaceta duk da irin tsoratar da tayi ya lallaɓata kuma ya bita a hankali ya cika ta da soyayyarsa me tsayawa a rai, tayi ta mishi raki da shagwaɓa... Wannan dare na daga cikin daren da bazasu taɓa mancewa dashi ba. Sossai ya buɗe musu wani sabon baabin soyayya, har mancewa da karatu take bare ma da ya ɗan kwana biyu be sake tafiya ba, komai da komai tare suke yi, da yamma su fita koyon tuƙi ana yi ana shan love, a cikin kwanakin duk wadda ze gansu se sun bashi sha'awa, kana ganinsu zaka san akwai tsananin soyayya da shakuwa tsakaninsu. Kwance take kan doguwar kujera a parlorn tana kallon wani series film yayi sallama ya shigo, da sauri ta miƙe ta tare shi suka rungume juna ya bata peck a kumatu tace "sannu da dawowa Noor" Yace "yauwa my queen, je bedside ki ɗauko min 50k zan sallami driver ɗin nan tunda my queen hannu ya faɗa" Tayi murmushi tare da Juyawa ta nufi ɗakinshi ta buɗe se ta sake cin karo da wayanta, a hannu ta ɗauko bayan ta ɗauko kuɗin Dukda ya ga wayan sede be ce komai ba ya karɓi kudin ya sauka. Bayan ya dawo ya zauna ta kawo mishi ruwa da lemu ya sha, ta dubi wayan tace "Yaaya a bedside ɗinka na ga wayan nan" Yana kallonta yace "uhmm" Se ta rasa me zata ce, kawai se ta mike don mayarwa yayi hanzarin riƙo ta yace "you wanna know me nake yi dashi ko?" Kai ta gyaɗa tana Kallonshi ya janyo ta ta zauna gefen shi yace "bude ki shiga gallery" Ta buɗe tayi yadda yace Hotunan ta ne masu yawa ciki kasancewar ta me yawan son ɗaukan pics, ta kalleshi ya ɗaga mata gira yace "su nake kallo a ko da yaushe, ban san taya ba ban san yaushe ba na dae tsinci kaina tsundum cikin ƙaunarki wadda a ko yaushe bani da wani aiki se na kallon hotunanki, na kan yi chargyn wayan musamman don in kallesu, kusan babu wadda ban haddace kalar kayan, tsayuwar da kuma yanayin hoton ba... Believe me I loved you tun kan na san menene so" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke idanunta cike da hawaye ta rungumeshi tace "our lives are one even though we are in two different bodies, I love you too" Shima sake shigar da ita jikinshi yayi a hankali tace "sweetheart! Meyasa Zubair yace ka mishi mugunta?" Da sauri ya ɗago ta, tayi hanzarin Kallonshi gabanta na faɗuwa kar fa ya ɗauka da wata manufa ta mishi wannan tambayar.. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DƘ ƘARSHE "why do you care to know?" Ya tambaya fuskanshi ba cikakken fara'a. Mikewa tayi tace "am sorry" Ɗakinshi ta shiga ta Haɗa mishi ruwan wanka ta fito tace "ruwan wankan ka is ready" Mikewa yayi ya wuce ta ba tare da yace komai ba ya shiga toilet ɗin yayi wanka, ko da ya fito akwai kayanshi marasa nauyi da ta fesa wa turare ta ajiye bisa gadon, dauka yayi ya saka bayan ya shafe jikinshi da mai da turarukan shi, fitowa yayi ya tsaya yana kallonta tana karasa gyara dining ɗin. Takawa yayi ya rungumeta ta baya a kunnenta ya raɗa mata "I just hate him tun daga sadda na ganki dashi a Abuja, wanchan ganin ya hana mini natsatsen bacci ba tare da na san dalili ba, a sadda na sake ganinku a hotel na ja mishi federal warning amma be daddara ba wai shine har da raba ki da school kina neco at that time ya zo min iya wuya, kuma na san shi dama farin sani sbd miyagun kwayoyi da yake yawan yawo dasu akan kama shi sau da dama a Airport kwana biyu a sake shi, so bayan ya dawo ya tafi Russia, that time nima Ina chan kuma ni zan tuƙo jirgin da ze dawo daga chan zuwa Nijeriya, I clearly saw him with the drugs again.. I then reported him Dukda na so hukunci me tsanani ya hau kanshi sede sun yi anfani da hanya da kuma kuɗi wurin kubutar dashi Dukda ko da ya dawo already you are mine, shiyasa ban kara bi ta kanshi ba" Kai ta gyaɗa tace "ga abinci" Bata so Sam ta nuna interest ɗinta kan labarin kar ya ɗauka da wata manufa sanin yadda yake da zafin kishi a kanta, a tare suke cin abincin cikin plate guda, bayan sun gama ta tattare kwanukan. "Are you OK" Ya tambaya yana janyo ta jikinshi. Kai ta gyaɗa tana ɗan murmushi yace "menene?" Ta girgiza kai, da yayi insisting se tace Kawo kunnenka kaji yana mika mata ta d’an cije shi kad’an tare da Mikewa ta kwasa da gudu da gudu ya bi ta yana kokarin kamata tana zillewa. Haka suka ta zagaye tana ta mishi dariya da gwalo daga karshe yayi nasarar kamata suka zube kan kujera yana mata jakulkuli da tambayar wa ya kama tana dariya sossai har da hawaye. Bayan kwana biyu.. Karfe shidda ta fito lectures ta nufi motarshi ta shiga tana cewa "washhh Allah na, hubby na gaji dayawa" Yace yana riƙo hannunta "sorry dear, mu je mu sayi abinci sannan mu wuce gida kiyi wanka se in miki tausa" Murmushi ta saki, suna ƴar hira har suka isa restaurant bata shiga ba shi ya shiga ya fito daga nan suka yi gida. Da kanshi ya ɗauko plates da spoons da ruwa ganin da gasken gaske ta gaji ɗin, don tunda ta zube kan kujera bata mike ba, Seda ya gama ajiye komai kan ta miƙe zauna buɗe ledar yayi tare da Fiddo takeaway ɗin yana buɗe psoup na kifin tayi hanzarin toshe hancin ta. Kallonta yayi kan yayi magana ta mike da gudu tayi wurin dining sbd ɗaki ya mata nisa, a take ta fara kwara amai cikinta na murɗawa, a ruɗe ya riƙeta yana mata sannu ruwa ne kawai cikinta don tun safe da ta ci cips bata kara sha'awar komai ba, ta jigata sossai kan ya riƙo ta suka dawo tana kallon kifin ta sake fara kokarin amai cikin muryar kuka tace "Don Allah yaya ka ɗauke kifin chan bata son gani" Taimaka mata yayi ta zauna ya karasa ya ɗauke kifin zuwa kitchen yana mamaki. Hannunta ya riƙe yace "baki da lafiya ne shine baki faɗamin ba? Tun yaushe? Me ke damunki?" Tace "lafiya ta ƙalau kawai gajiya ce se kuma kifin nan bana son warin" Yace "wari kuma? Amma I thought kifi da nama na daga cikin abubuwan da kike so?" Kai ta gyaɗa, yana ta kallonta se kuma yace "wait..! Fauza" Da sauri ta kalleshi, rabon da ya kirata da sunanta tun a yola, tace "Na'am" "when last kika ga jininki?" Idanunta na kanshi ta tafi tunani, da sauri ta sanya hannu a kan cikinta tana cewa "could it be possible?" Yace "sure, When last kika yi period?" A hankali tace "tun kan in bar nan in tafi yola, satin da ya kamata na fara kuka je kai da Fatima" Ai da wuri ya tafi ya ɗauko mata hijab ya zo ya kama hannunta suka yi asibiti, bayan dogon gwaje gwaje Jafar ya musu albishir da ciki na tsawon wata uku bata taɓa sani ba se ranar, farin cikin da suka shiga baya misaltuwa barin ma shi da har Seda yayi hawaye, ze kira gida tayi saurin kwashe wayar tana shagwaɓewa. "Eyyaaa yaya karka gayamusu don Allah" Yace "Meyasa bayan abun farin ciki ne ya same mu love?" Tace "Ai to ba zasu san abunda aka yi ba, ni dae bana so" Dariya sossai ya saki, Fauza har yanzu taɓara irin na yara na damunta. "Fine my baby mama, ba zan faɗa ba" Daga asibiti yawon neman abunda zata ci suka fara, a wani tsadadden restaurant suka yada zango a gabansu aka ajiye abun gashi yana gasa mata nama tana ci, ta ci sossai kan aka kawo mata milkshake ta jingina da jikinshi. Kwanciya tayi jikinshi tare da kai mishi cup d’in bakinshi yayi sipping ta dawor dashi nata ta sha tana sake murmushi. Rayuwa ta sake yi musu daaɗi sossai, a week after suka fara exams ya ɗan yi tafiya bayan ya dawo lokacin ta gama ya shirya musu tafiya, Allah ya sa cikin nata ba wani laulayi me wahalarwa, ƙasar Greece suka tafi suka baje kolin soyayyarsu a chan, sati uku suka yi a chan kan suka wuce Australia se ganinsu Ya fadeela tayi. Sun matukar burge ta soyayyarsu ya tafi da ita ga wani kyau da kowannensu ya kara da girma alamar hankalinsu kwance yake, daga nan suka wuce wurin Ya fadyaa husna tayi ta murnan ganinsu suma kwana biyu suka musu suka tattara suka dawo sbd hutun ta ya kare. BAYAN WATA HUƊU A hankali take sauƙowa daga jirgin sbd yadda cikinta yayi wani mugun girma Dukda kwata kwata wata bakwai kenan, kafafunta da kyar take ɗaga su sanye da wani bubu Abaya me stones ta yafa gyalen, yana rike da jakanta a hannu daya yana rike da ita suka nufi farhan dake ta zabga murmushin ganinsu. Se kallonta ake sbd Fauza fa ciki be hanata gayunta ba, wani lokacin in su firdausi na tsokanarta ta kan ce ciki ne fa da ita ba hauka ta soma ba, suyi ta mata dariya, shi karan kanshi ya kan yaba kokarin ta Dukda kankantar shekarunta bata taɓa gazawa a kanshi ba daga cimarshi, tsabtarshi da hakkinshi babu abunda ta dena ga karatu. Gidan cike yake da mutane sbd yaune ake walimar Fa'iza da Faraj se Falaq da itama se yanzu lokacin yayi, a haka suka ratso mutane duk yadda take sunne kai shi kam ko a jikinshi se kara mannata da jikinshi yake har parlorn Jaddah. Farin ciki ne ya cika ta fall ko a hira basu san da cikin ba se ganin abu kawai suka yi, daga Amminta har mammi ba karamin farin cikin ganinta haka suka yi ba hankali kwance, kar iyayenta mazan su ji labari. Duk yadda ta ci Burin bukin se gashi ita a zaune tayi komai sbd kafafunta da suka ƙi, har aka sada su da gidajensu jama'a suka watse. Tana kwance kan gadon Amminta hannunta waya ne tana dubawa taga saƙonshi. Mikewa tayi zaune ta dubi Ammi tace "Ammi akwai abinci kuwa a sashen nan?" Ammi tace "eh a kawo miki ne?" "A'a Yaya za'a Haɗawa faazila ta bini dashi na tabbatar be ci komai ba" seda ta faɗa kuma kunya ya kamata, Ammin murmushi kawai tayi tare da miƙewa ta hado ta ba faazila tuni Fauza kam ta lallaɓa ta wuce. Tun daga kofa ya tarbeta ya ɗan rungumeta "Sannu baby mama... Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya miki albarka". Kusan kalaman da ta saba ji kenan daga gareshi tunda cikinta ya fara girma "Ameen Daddyn baby thank you" Zama suka yi yana nuna mata wasu gadajen yara masu kyau sossai wai ta zaɓa order ɗinshi zasu zo wani sati, tace "yanzu duk waenda muka yi ta jida a Abuja be isa ba hubby?" Yana murmushi yace "ko duka shagunan Abuja muka saye ni dae be min ba... Uhmm na fa ba da aikin ɗakin nan da muka yi magana" Ɗakin Fatima ne ya sa aka fidda komai za'a gyarawa baby, tayi murmushi kawai se ga faazila da abinci, shi ya karɓa suka ci tare sbd ya Santa idan ba shi yake bata ba bata wani ci me yawa. Duk yadda ya so tafiyarsu tare haka ya hakura ya barta sbd ya san yanzu tana bukatar babba kusa da ita, sede suna manne a waya. Watanta ɗaya da sati biyu a gida ranar ta tashi da nakuda me tsanani, yana kwance tun dare yake ta juye juye bayan mafarkin ta da yayi, ya kirata bata yi picking ba. Hankalinshi gabaɗaya ya tafi yola, haka dae da yaga baccin ba ze yiwu ba ya tashi ya fara nafilfili yana rokar mata sauka lafiya. Bayan ya dawo sallar asuba ya danna kiran Jaddah, ta ɗaga daga yadda yaji muryarta ya rikice yana tambayar lafiya? Ta sanar mishi Fauza ke labor. Hmm Allah ne kadai ya kaishi Airport lafiya don ma akwai available flight karfe takwas haka yayi ta safa da marwa a Airport ɗin hankalinshi duk a tashe. Har ya isa yola ya isa asibitin bata haihu ba, kuma wai ta kwana a haka, ai be jira wani jawabi ba ya banka kofar ya shige, duk ta galabaita kaman jira nakudar ya sake taso mata. A jikinshi ya sanyata yana mata Adu'a, wani riƙo da ta mishi seda ya runtse idanu be buɗe ba se da kukan jariri ya cika kunnuwanshi, Alhamdulillah! Yake ta nanatawa yana mata sannu a lokaci ɗaya yana shafa kanta. Wani Sabon nakuda ne ya sake tasar mata, ba bata lokaci ta sake sulbiyo wani babyn. Shikam Sam hankalinshi na kanta irin wahalar da ta sha se zufa take yi yana share mata. Mika mishi yaran aka yi bayan an tsaftace su. Ya rungumesu hawaye na zubar mishi.. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!!" Lallai Allah me kyauta da ƙari shine yau rungume da ɗan shi ba ma guda ɗaya ba har biyu, wani irin godiya ze yiwa ubangiji? Fitowa yayi dasu su Jaddah kowa farin ciki a take Fa'iza da tun asuba ta iso asibitin ta ɗaukesu hoto ta turawa su ya fadila kowa murna mata ne Duka kaman babansu yayi khaki ya tofar har hasken fatar. Wani irin so da kauna da Faizan yayi ta nuna mata a asibitin sede ita ta ji kunya shi kam ko a gyalenshi, Kwananta ɗaya aka sallameta, Faizan ya kusa cika parlorn Jaddah da saye saye, duk.abunda aka ce ya dace me jego ta ci se ya je ya sayo, kan saniya har uku ya kawo ga manyan bindi yace ayi ta mata psoup tana sha. Ranar suna yara suka ci sunan Jaddah da mammi, fa'iza ce ta musu inkiyar Arwa da marwa, me jego ta samu kyaututtuka masu dumbin yawa, ta shiga ta fita a wanka da ado kam masha Allah, shima angon karni ba'a barshi a baya ba suka dinga chanza dressing ana daukar su hotuna take suka baza ko ina latest parents of the month ba, kyautar tsaleliyar mota me rai da motsi Faizan yayi mata da wani set ɗin gold me tsada tukuicin kyautar da ta mishi. Sanye da doguwar hijabi har ƙasa ta shigo gidan, idan ba ka mata farin sani ba bazaka gane ta ba, tayi baƙi sossai ta rame kaman ba Fatima ba, kai tsaye inda aka yi decorating don taron sunan ta karasa, a gaban Fauziyya kawai ta zube tare da kama kafafunta ta fashe da wani irin kuka da ya ja hankalin mutane masu yawa. Faizan yayi saurin mikewa yana kallonta, Fauza ta ganeta tayi saurin tare shi ganin ze taɓa ta don rabata da jikinta. "Fatima???" Kowa sunan ya maimaita yana kallonta da mamakin yadda ta koma "Don darajar Allah ku yafemana Fauziyya, ke da Ammi da mammi ku dubi Allah ku yafe mana ko zamu ga da kyau, Don Allah ku yafewa Auntyna ta tafi tana rokar gafararku sede babu halin zuwa nan ɗin..." "Ta rasu??" Fa'iza tayi tambayar idanunta duka waje Kuka me ciwo Fatima ta cigaba da yi wadda ya saka su jin tausayinta. "Ta rasu Fa'iza, ta ce don Allah in ce kuma ku yafe mata, ku rokar mata Allah gafara, ta kamu da cutar dajin kwakwalwa ba tare da mun sani ba aka mata allura, tayi jinya me tsawo wadda kan ta rasu seda kamannin fuskanta ya sauya, fatar fuskanta da naman haka suke zazzagowa suna zub....." Kuka ne ya kwace mata, fa'iza ma nayi. Fauza seda ta zub da hawaye jin irin wahalar da Aunty ta sha kan mutuwa lallai wadda yace ruwan wani baze tafasa ba nashi ko zafi baze yi ba, yanzu wa gari ya waya? Arziki, kuɗi babu abunda baya jawowa.. Allah ya tsarremu da son zuciya. Sun ce sun yafe sauran ita da ubangijinta, Fatima tayi ta godiya ko da Baba prof ya tambayi ina take zaune ita nan ta gaya musu ai Aunty ɓoye iyayenta tayi suna fama da baƙar rayuwa, kilan da ta taimaka musu sun zama wasu abu kan barinta gidan Sulaiman ɗin da sun iya sun Haɗa mata kudin aikin da ya gagara har ta mutu da azabar ciwon cancer. Ta sheda musu itama zata koma gidan nata mahaifin dama Aunty ne taki sam ta bari su wani shaku sbd burinta a gidan prof ɗin.. Kyauta me yawa suka mata, Faizan dae be ce komai ba, se Kallonshi take da yaranshi rungume kirjinshi tana jin yadda azabar sonshi ke huda zuciyarta sede ya ta iya ba komai kake so kake samu ba. *** Yau suke gama wanka, ita da su faazila suka fita zagayen arba'in sun zazzaga wuraren en uwa da abokan arziki, sun zo ta wurin gidansu Sakina tayi parking motar ta sauka tana tambayar me gadi mutanen gidan. Yace ai iyayen sakina sun rasu se ita kaɗai da masu aiki, itama ta tafi islamiyya ne. "Islamiyya" Fauza ta maimaita. Bata gama rufe baki ba se ga Sakina ta taho ita da wani a gefenta kanta ƙasa hannunta rungume da Alqur'ani. Ɗaga kan da zata yi se taga Fauza da sauri suka rungume juna sakina na fashewa da kuka sossai, Gaisawa suka yi da mutumin nan kan ta cewa su Faazila su karasa ciki. Sakina ta cika musu gaba da abun motsa baki kan ta zauna tana ta kallon su Arwa yaran bul bul gwanin sha'awa kaman yaran labarawa. "Sakina ina rahama?" Ta tambaya, Sakina na kuka tace "Fauzaa na ji tsoron Allah naji tsoron rayuwa, na rasa iyayena a hatsarin jirgin ruwa hakan me makon ya saka min natsuwa Dukda kaɗaici da rashin wani dangi yasa na sake samun duniya yadda na so nake yi, Fauziyya mun tafi Gombe kusan mu shidda muna dawowa muka haɗu da wani mummunan hatsari, da idanu na na ga mutuwa Fauziyya, kowa ya mutu a gabana har rahama... Tun daga sannan tsoron Allah ya saukarmin na fara tuba. Kaɗaici ya min yawa, se masu aikin gidanmu da da nake wulakantawa suka zama en uwana, su suka sa na shiga islamiyya yanzu haka wadda kuka gaisa dashi malami na ne kuma shi zan aura" Ajiyar zuciya me nauyi Fauza ta sauki, Sakina ta nemi yafiyar ta bisa hanyar da suka jefa ta a baya, tace ta yafe kuma in shaa Allah auren ya tashi zata halarta. kaman kar su Rabu bayan sun yi exchanging numbers Fauza ta wuce gida, sati ɗaya bayan nan ya zo ya ɗaukesu da wata da Jaddah ta sama mata me taya ta renon yara suka wuce Abuja. Maternity leave ɗinta ya riga ya kare so makaranta kawai ta koma, tana kuma kula da yaranta da mijinta a gefe guda. *** Bayan tsawon lokaci. Cikin bacci yaji barinta jikinshi ya zata ma bayi zata shiga se yaga ta nufi kofa ta buɗe ta fice. Mikewa yayi yabi bayanta, ƙasa gabaɗaya ta sauƙa a dining ta zauna bayan ta ɗauko ruwa ta zare bowl ta Haɗa cornflakes ta fara sha. Daga saman stairs ya tsaya yana kallonta da mamaki karfe biyun dare? Zuwa yayi ya zauna gefenta tare da d’aura hannunshi d’aya kan ha’barshi zuwa bakinshi ya karkace sossai yana kallonta ba tare da ta sani ba. Tayi nisa wurin shan cornflakes d’inta sbd yunwar da take ji d’aga kan da zatayi kawai ta ganshi bazata hakan ya mugun Bata tsoro tayi Baya luuuu zata fad’i daga ita har kujeran yayi azamar tarbota tare da kurawa firgitattun idanunta ido, a hankali ya mayar kan lips d’inta da suke d’an bud’e kad’an sbd tsorata. Daidaitata yayi yana cewa "Easy precious ni ne" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke ta shagwaɓe tace "Abban twins ka tsorata ni wlh" Yace "sorrie! Ina mamakin yadda daaɗin cornflakes ya sa kika kasa jin zuwana ma gabaɗaya" Cigaba da shan kayanta tayi ba tare da tace komai ba, ya jira ta gama kan suka koma seda suka leƙa yaransu da yanzu suke shekara da wata shidda babu abunda basa ci babu kuma inda basa zuwa kan suka koma ɗaki. Da asuba kan tayi sallah seda ta sake shan cornflakes shi dae be ce komai ba, suna breakfast ita cornflakes take sha. "Anya lafiya Fauza?" Tace "me ka gani?" Yace "shan cornflakes ɗin nan haka kawai nake jin ba ƙalau ba" Gabanta ne ya faɗi, ita dama ta ɗauko Ammi ne in tana shayarwa bata period to haka itama bata taɓa yi ba tun samun cikin su, goyo me tsafta ake cewa ko, to amma kwata kwata en biyu yaushe suka girma? Gashi karatun ta ya ɗauko gangara yanzu duk bata da wani lokaci na kanta. Bata ce komai ba, bayan ta sallami su twins ta fito da niyar wucewa school ta biya asibiti, abunda take tsoro ne ya tabbata ciki take dashi na tsawon sati biyar. Kasa zuwa school ɗin tayi ta komo gida ta shige ɗaki ta fara kuka, yana tsaye balcony ɗinshi ya ga shigowar motan ta shiru shiru ya dauka mantuwa tayi sede be ga fitar ta ba ya sa ya fita ya nufi ɗakinta. Hankalinshi ya tashi ganin tana kuka ya hau lallaɓata da kyar ta ce mishi wai wani ciki ne da ita. Da tsantsar mamaki yake kallonta "saboda kina da ciki shine kike kuka Fauziyya?" "Yaya ka kuwa san wahalar renon ciki da nakudar? Kwata kwata yaushe na haifi twins? Ga school ni dae wlh ba zan iya b...." "Kul Fauziyya!!" Ya daka mata tsawa. "Karki kuskura wlh karki fara kawo koma menene yake ranki ki binne shi, ciki ne ya riga ya shiga don haka se kin haife shi" Yana kai nan ya miƙe ya fice yana banko mata kofar. Sossai tayi kuka kan bacci ya ɗauke ta. Gabaɗaya ranar ta fita harkar su twins ɗin da baban ko fita daga ɗakinta ta ƙi yi, tana ji yadda suke kiran "mommy! Mommy!!" Bata ko kula su ba seda daddyn nasu ya fita daga nashi ɗakin ya ɗaukesu yayi nashi dasu. Wasa wasa seda suka kwana uku a haka, bata shiga harkarsu banda kuncin rai da ta sawa kanta ko makarantar bata zuwa, bata taɓa kai hannu jikin yaran ba amma a tsakanin seda ta make Arwa wadda ya sake saka matsala tsaninsu seda yayi kaman itama ze daketa. Jafar yake faɗawa matsalar tashi don basu taɓa samun damuwa haka ba, wlh ko bacci baya iya yi tunda suka raba makwanci, Jafar ya kirata a waya ya mata nasiha sede be wani shige ta ba. Da Faizan ya gaji ya kira baba Alhj ya faɗa mishi, aiko kaman ze bar yola ya zo Abuja ya daka ta don faɗa seda baba prof ne ya dakatar dasu ya kirata ya mata nasiha sossai da kuma nuna mata kyauta ce daga Allah wasu na nema ido rufe basu samu ba, kan ta sassauto be bar Faizan ɗin ba ma ya mishi faɗa shima ya nuna mishi Fauza har yanzu yarinya ce, kwata kwata yanzu ne take shirin yin 19 ga albarkan yara Allah ya bata idan be bita da lallami ba kenan ba anfanin tarin shekarun da ya bata. Wayanshi da ta gama jin nasihar mammi ta mike ta nufi ɗakinshi Shiga d’akin tayi don bashi wayanshi ta samu har bacci ya d’aukeshi, a gefen hannunshi ta zauna tare da kura mishi ido na seconds yadda lashes d’inshi suka kawata fuskanshi zuwa sajenshi da yafi komai d’auke mata hankali lumshe ido tayi ta bud’e kan pink lips d’inshi da ya d’an bud’e kad’an, murmushi me kyau ta saki he looks so damn cute kaman d’an baby, d’an buge goshinta tayi tare da mikewa da sauri bata d’aga kafanta ba taji ya rike hannunta tare da fisgo ta ta fad’a kan gadon kanta ya sauka akan hannunshi da ya Mikar cikin wani irin yanayi ya bud’e idanunshi da suke cike da bacci da tsananin kewanta ya zubasu cikin nata yana lumshewa a hankali. Wani abu taji daga tsakiyar kanta har zuwa babban yatsanta ya tafi zirrrrr, runtse ido tayi tare da d’an juya kanta kad’an zuwa kan hannunshi hakan ya bawa gashinta daman zubowa saman fuskanta, hannunshi d’aya ya sa ya maidashi a hankali zuwa bayan kunnenta, tare da maida hannun cikin hannuta dake tsakiyarsu ya fara shafawa a hankali. "I badly missed you hayatee...if am left alone without you how am I supposed to live?" In a whisper tace "I missed you more Hubby am so sorry, na yi kuskure, forgive ur wife" Peck yayi mata a goshi kan a ƙasan maƙoshi yace "u are pardoned, I love you" Ta rungumeshi tana mishi raɗa a kunne "I didn't fall in love with you because I was lonely or lost, I fell in love with you because after getting to know you, I wanted to make you a parmanent part of my lif..." Bakinsu ya haɗe sbd kasa hakura da yayi a take suka fara nunawa juna zallar so da kauna me tarin yawa wadda baki yayi kaɗan ya misalta ko ya furta. FIVE YEARS LATER Da gudu suka hauro saman suna rige rige, dukkansu uku sanye da uniform na makarantar boko "mommyyyy! Daddyyyyy we are back yeyyyyy" Fauziyya dake daga tsaye tana serving Faizan Abinci ta haɗe fuska tamau tana gyara tsayuwar ta da ya bayyana cikin jikinta da ya soma girma tace "Arwa, Marwa, Alaya me na faɗa muku akan sallama?" Chak suka tsaya se suka juya sum sum suka koma da baya suka doka sallama daga karshen stairs seda ta amsa ta musu izini kan suka hauro har lokacin bata sake fuska ba. "Sorry mommy mun manta ne" Arwa ta faɗa tana kama kunne. Marwa ma tace "sorry mommy" Alaya da taci Sunan Ammi tace "we're sorry mammy" Faizan yace "my princesses are sorry daga yanzu bazaku sake shiga wuri ba sallama ba ko?" Da sauri suka gyaɗa kai Alaya tace "Allah mommy in mun sake punish us" Dariya Fauza tayi wai wani punish them ko me za'a yi punishing ɗin oho, "oya kuje Mamu ta muku wanka ku zo ku ci abinci kar kuyi lattin islamiyya" Da gudu suka wuce ɗakin su.. Faizan ya dube ta yace "mommy please a taimakeni da soldiers nima in samu friends" Murmushi kawai tayi, da dare suna kallon news ake sanar da mutuwar ɗan dan majalisa wadda ya shigar da kwaya wata kasar da ba'a shiga da kwaya kwata kwata suka kama shi ya jima a prison ɗinsu kan ya mutu, Zubair ta gani rayuwa fa kenan in kana takamar kuɗi da hanya akwai inda zaka je ka zama bawa ko almajiri don a komai wani ya fi wani ne..Wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta. **** ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN NA DIDDIGAR ƘAYA ME WUYAR TSINCEWA, ABUNDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH YA BAMU LADA WADDA KUMA MUKAYI KUSKURE ALLAH UBANGIJI YA YAFE MANA. WAENDA SUKA SAYA INA MATUKAR GODIYA DA KAUNA KUMA INA ALFAHARI DA KU A DUK INDA KUKE, KU KUMA DA KUKA FITAR MIN DA LITTAFI KU KUKA SANI DA ALLAH, AKWAI FULL DOCUMENT ƊINSHI IDAN DA WANNAN PAGE KIKA FARA CIN KARO MAZA BIYA KI MALLAKI NAKI KI SHA KARATU KI KWASHI ILIMI.. ALLAH YA SADA MU A WANI LITTAFIN NA GABA🥰🥰❤️‍🔥 DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤