Showing 1 words to 1767 words out of 1767 words
Chapter 1 - KUNDIN TSATSUBA 4 by Abdul'aziz Sani Madakin Gini.docx
KUNDIN TSATSUBA
BOOK 4 COMPLETE
Writing by
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
07032707179
Daga can sai Yelisa ta sake matsawa kusa da shi ta hade rai ta ce "Ina dalilin wannan dariyar ta ka?"
Boka Jinshan ya murtuke fuska sannan ya ce "Ya ke 'yata, ki yi sani cewa ba komai ba ne ya sani dariya face ganin yadda kuke son ku yi aikin manya a matsayinku na yara. Ni a tawa shawarar ku ba ni Kundin Tsatsuba ku bar komai a hannuna, ni zan aika aje a kawo mini kubar Muftahul Zarbil a cikin kwanaki kadan. A gaban idanunku zan bude wannan littafi na karanta shi tare da ku."
Sa'adda Boka Jinshan ya zo nan a zancensa, sai Yelisa ta bushe da dariya ta ce "Haba abbana, na san kai ka haife ni, amma ka sani cewa ba fa zaka iya yi mini wayo ba a yanzu, domin kaina ya waye fiye da yadda baka zato. Mu yanzu abin da mu ke so da kai kawai shi ne ka sanar da mu dokokin da za mu kiyaye yayin da muka shiga jejin Kalkim don dauko takobin maridi Magulus. In kai mana wannan ka gama biya mana bukata, sauran wahalar ka bar mu da ita."
Sa'adda Boka Jinshan ya ji haka, sai yayi shiru yana tunani, a zuciyarsa ya ce 'A gaskiya abin kunya ne a gare ni na kwace Kudin Tsatsuba daga hannun yaran nan, tunda dai ban san yadda a kai suka samo shi ba. Kuma idan nayi haka kimata zata ragu a idanun 'yata.'
"Shike nan na yarda zan sanar da ku dokokin da za ku bi yayin da kuka shiga jejin Kalkim, amma bisa sharadi guda. Sharadin shi ne zan hada ku da wani bawana ya tafi tare da ku. Ba wani ba ne wannan bawa face aljani Nargaz. Ku yi sani cewa shi Nargaz sadauki ne na gasket, zai zama kariya a gareku daga sharrin mugayen aljanu, kuma ya kasance mai sauri five da naku aljanin wato Gulzum. Haka
kuma idan Gulzum ya gaji da tafiya, Nargaz zai iya daukarku ku duka ukun ya ci gaba da tafiya da ku."
Bayan da Yelisa da Jafar suka ji wannan batu, sai suka dubi juna suka yi shiru. Daga can sai Jafar ya dubi Boka Jinshan cikin biyayya ya ce "Ya shugabana mun ji sharadinka, kuma mun amince, amma muna so kayi mana uzuri zuwa gobe domin mu yi shawara."
Boka Jinshan yayi dariya ya ce "Shi kenamy na amince ku tafi sai gobe warhaka ku dawo mini da shawarar da kuka yanke."
Nan take Yelisa da Jafar suka mike suka fita daga cikin fadar rike da Kundin Tsatsuba. Fitarsu ke da wuya Boka Jinshan ya kira sunan aljani Nargaz sau uku. Nan take ya bayyana gabansa ya risina cikin ladabi Ya ce "Ga ni gareka ya shugabana, me kake bukata da ni?? hung
Aljani Nargaz katon gaské ne, domin kuwa girmansa ya nunka na aljani Gulzum sau goma. Kakkarfan gaske ne. kuma a halin yanzu yana kan tsakiyar gajiyarsa ta samartaka. Ko kadan bai san wani abu wai shi tsoro ba.
Boka Jinshan ya dubi Nargaz cikin nutsuwa ya ce "Ban kiraka dan komai ba, sai dan ka yi shiri ina son zan hada ka da 'yata tare da Jafar dan Ruziyal ku tafi izuwa jejin Kalkim, don ku dauko takobin maridi Magulus. Ka sani cewa za ku yi wannan tafiya tare da Gulzum, na hore ka da ka taimaka musu a duk lokacin da bukatar taimakon ta taso. Bayan kun sami nasarar dauko takobin za ku wuce izuwa birnin Teheren ku shiga kurkukun sarki Lu'umanu da ke Karkashin kasa, ku sare kwadon da aka rufe bakin akwatun nan wanda aka sa aljani Markahul Sabus à ciki. Lallai da
wannan takobi Sarjis zaku sare kwadon. Da zarar kun bude akwatin za ku iske wata battar Karfe a ciki. Ka da ku kuskura ku bude battar, lallai ku zo mini da ita a rufe. Idan kuwa kuka yi gangancin bude battar, aljani Markahul Sabus zai fito ya hallaka ku gaba daya."
Yayin da aljani Nargaz ya ji wannan bayani na ubangijinsa, sai ya kawo gwauron numfashi ya ce "Ya shugabana, ka sani cewa ban san dokokin da zan kiyaye ba yayin da muka shiga jejin Kalkim, haka kuma shiga birnin Teheren ba na karamin shiryayye ba ne, bare ma har mu sami ikon shiga kurkukun sarki Lu'umanu da ke karkashin kasa
Ko da jin wannan batu, sai Boka Jinshan ya bushe da dariya, sannan ya ce "Kar ka damu zan sanar da ku komai gobe warhaka. Yanzu na sallame ka ka tafi sai goben ka dawo a daidai irin wannan lokacin.
shugabana. Aljani Nargaz ya risina ya ce "An gama ya
Nan take ya bace, shi kuma Jinshan sai ya murza daya daga cikin zobunan hannunsa, take shi ma ya baсе.
A daidai nan ne Boka Sulbaini ya sake núna allon tsafinsa da sandar nan da ke hannunsa, sai komai ya washe, su Gimbiya Sima suka daina ganin hoton komai a kai.
To yanzu kun ga komai da idanunku, saboda haka babu abin da ya kamace ku face ku bi bayan wadannan yara, duk inda za su je kuma ku je, kuma duk abin da za su yi, su yi a gabanku. Da zarar kun ga sun mallaki kubar Muftahul Zarbil sai ku yake su ku kwace Kundin Tsatsuba da Muftahul Zarbil a lokaci guda.
Sa'adda Boka Sulbaini ya zo nan a zancensa, sai waziri Kuddaru ya ce "Kai sarkin bokaye ka sani cewa daga nan zuwa birnin Sin, tafiya ce ta shekara dari da goma bisa rakumi ba tare da ya da zango ba. Yanzu ta yaya zamu isa zuwa wannan gari kafin su Yelisa su tafi jejin Kalkim, kuma ta yaya zamu bi sawunsu sau da kafa?"
Ko da jin wannan tambaya, sai Boka Sulbaini ya tuntsire da dariya, sannan ya ce "Ai wannan mai sauki ne, yanzu zan hada ku da wani aljani daga cikin aljanuna, wanda nake matukar takama da shi. Sunan wannan aljani Durfas. Ku sani cewa Durfasu ya linka aljani Nargaz arba in a komai, haka kuma yana da wani sihiri na musamman wanda in ya so yana iya bacewa ko dan uwansa aljani bai isa ya iya ganin sa ba, duk wanda ke zaune a kansa ma zai bace tare da shi, idanun bil' adama ko na aljan ba zai gan shi ba. Yana da tsananin gudu da sauri yayin tafiya a cikin sararin samaniya kamar tauraruwa mai wutsiya. Aljani Markahul Sabus ne kadai ya fi shi sauri,"
Kafin Gimbiya Sima da Kuddaru su kara fadin wani abu, tuni Boka Sulbaini ya shafi wani mummulallen karfin tsafi, sai ga aljani Durfus ya ratso ta cikin dutsen kogon ya durkusa bisa guiwoyinsa a gaban Sulbaini ya ce ia ni gareka ya shugabana, fadi kowacce irin bukata yanzun nan na aiwatar da ita."
Boka Sulbaini yai murmushi ya ce "Maza ka dauki Gimbiya tare da wazirinta ka kai su birnin Sin, don ku bi bayan su aljani Nargaz izuwa jejin Kalkim. Ina son ka kasance tare da su har izuwa lokacin da za'a mallaki kubar Muftahul Zarbil. Da zarar hakan ta faru, sai ka yaki su aljani
Nargaz ka kwato Kundin Tsatsuba da kubar Muftahul Zarbil ku taho nan gaba daya gare ni.
Ko da jin wannan umarni, sai aljani Durfus ya sa hannu guda ya suri Gimbiya Sima da Kaddaru ya aza su a bayansa, sannan ya yunkura da niyar tashi, sai Sima ta ce "Ka dakata sarkin hanzari, akwai sakon da zan bayar a waje ga jama'ata.
Ko da jin haka sai Boka Sulbaini ya ce "Kar ki damu ya shugabata, ai mun san sakon naki. Kina so ne ki bar amanar kasa a hannun galadima. Ki tafi abinki, za mu isar da wannan sako, kuma mu ma za mu zuba ido akan harkar mulkin don ka da ayi wani abu ba daidai ba yayin da ba kwa nan.
Sulbaini na gama rufe baki. Durfas ya bude fukafukansa ya zama haske, su ma su gimbiya Sima da ke zaune akansa ai suka zama hasken, take hasken ya ratsa ta saman ginin kogon dutsen ya fice izuwa sararin samaniya, kuma ya бaсe.
Al'amarin Yelisa da Jafar kuwa bayan sun baro fadar Boka Jinshan, sai Gulzum ya dauke su ya mai da su cikin kogon nan na Yelisa da ke can bayan gari, anan su ka zauna kowa yai shiru yana tunanin mafitar wannan al'amari.
Jafar ne ya fara magana, ya dubi Yelisa ya ce "Anya kuwa ba kya tsammanin cewa mahaifinki ya shirya mana tuggun da zai raba mu da Kundin Tsatsuba? Ni kam hankalina bai kwanta ba da batun wannan aljani nasa da zai hada mu da shi.'
Yelisa tayi ajiyar zuciya ta ce "Abokina, ni kaina ban yarda da shi ba, to amma ka san cewa a halin yanzu ba mu da wani zabi wanda ya fi mu bi umarninsa."
Haka ne sai dai ai dabara bata karewa mai nema, kar ki damu tuni nayi wani shiri a zuciyata, lallai babu wanda ya isa ya raba mu da Kundin Tsatsuba har sai mun gama karance shi tsaf daga farkonsa zuwa karshe."
Ko da jin haka sai Yelisa ta dubi Jafar cikin mamaki ta ce "Kar kuwa wane irin shiri ne ka yi mana, wanda tunanina da hikimata ba su kai kansa ba?"
Jafar yayi dariya ya ce "Haba kawata, ai gadon tsafi kika fi ni, amma ba gadon hikima ba lomin kin san cewa mahafina cikakken masani ne kuma mai cikakkiyar basira. Ke dai kawai ki zuba ido ki sha kallo. Shin kin mata da kirari na ne? Ni ne fa hatsabibin yaro mai ta adin tsiya. Mugun tsuntsu nake mai sheka dubu, bai zama waje daya don gudun tsautsayi. Ni da tsoro mun raba gari
Da jin haka Yelisa ta kyalkyale da dariya ta ce "A'a gyara maganarka, ai akan batun tsoro kayi karya. Ashe ba kai ba ne ka yi arba da zakin mahaifina ka firgice ba?"
Jafar yayi murmushi ya ce "Ai jin tsoro take ba tsoro ba ne. abin da nake nufi anan shi ne ba na jin tsoron abin da ban gani ba. Kin sani cewa ko da za'a gaya mint cewa akwai mutuwa a cikin rijiya, ba fa zan ji tsoron shiga ba, sai dai idan na shigan na sadu da ita."
Yelisa tayi murmushi ta ce "Kwarai ni ma na shaida da wannan, kuma na jinjina maka. Bari ni ma nai maka nawa kirarin. Sunnu Jafar gogan Yelisa, kura kake ga tsoro kuma ga ban tsoro. A fagen gaba baka san gudu ba, gaishe ka