Showing 1 words to 3000 words out of 23627 words
MAI DAKI...
4
NA
HAJ. HAFSAT C. SODANGI
(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai)
1
GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take, Masanin yau
da gobe, mai kowa mai komai, Gwani mai hikima
wanda yayi halitta tasa duka bibiyu, ya kuma halicci
mutum da Aljan don su bautata mishi.
Tsira da Aminci su tabbata ga cikamakin
Annabawa shugaban Manzanni, Annabin Rarshe
Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa da
wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa
ranar Alkiyama, amin.
Godiya mai yawa gare ku makaranta litattafaina,
na kusa da na nesa, Ubangiji ya saka da alheri ya
kuma kara karfafa zumuncin da ke tsakani, na gode.
SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin ta Iyayena ce, Alhaji Chindo
Muhammad Sodangi da Hajiya Fatima Musa
Sodangi, Ubangiji ya saka muku da alheri ya kuma
Rara muku lafiya amin.
2
TUKUICI
Tukuicin littafin naki ne:
KHADIJA CHINDO SODANGI (Mrs Nasiru Idris)
JINJINA
Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya laifi
(Maman Umar) Zuhuriyya Ibrahim (Mrs Lawal
Chindo Sodangi), Ubangiji ya raya Umar da imani.
FATAN ALHERI GARE KU
Fatima Abdulkadir Kazaure
Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi
Khadija Usman Nasarawa
Nafisatu Ibrahim Muhammad
Fatima Ahmad Shehu Kaduna
Maryam Muhammad Gusau, Zamfara
Umaima Abubakar Umar
Maijidda Uba Magaji
Na gode, Ubangiji ya saka da alheri, amin.
KUNA RAINA
Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassan
Hajiya Jamila Ibrahim Na Bature
Hajiya A'isha Balarabe (Jazan)
UbangiJ1 ya bar zumunci amin.
3
LITTATTAFAN SODANGI:
Uwar miji
Naga ta kaina
Rabon kwado...
Cikar alkawart
Wayyo duniya
Yi wa wani...
Abu naka...
Mata ma su duniya
Nufin Allah
Kifin na ganinka..
Daga Kin gaskiya...
Da kamar wuya...
Mai uwa..
Duk daya...
Mata da kicin dinsu
Wacece ni?
Wata fuskar...
Mijin ta ce
Garin banza...
Ga ni gare ka
Biyan bukatar rai
Shamaki
Hattara
Kyautata
4
Ayi dai mu gani..
Tabbataccen al'amari
In kunne ya ji..
Halin rayuwa
Mai daki...
Littattafan ba sa nufin yi da wani ko
habaici ga kowa, sai dai an rubuta su ne
don fadakarwa da nishadantarwa, ana
neman afuwa ga duk wanda yaga wani abu
yayi kamar abinda ya shafe shi, ba da shi
ake ba dace ne kawai.
5
MAI DAKI...4
Sai da Babana ya dawo ne magana taso ta
lalace, don kuwa cewa yayi ba zai karbi
kayan Ahmad ba.
Shiru nayi a daki cikin wani yanayi, yayi ta
fada dalilin da yasa Umma ta bari aka sauke.
Itama dai bata ce komai ba, Yaya Auwalu
ya kira yace ya nemo mota a mayar da kayan
ba ya so. Ganin haka ne yasa Baba Ladi
diddingisawa ta same shi ta ce wai wannan
fadan da kake yi na meyene?
Na jin haushin yayi wa Mahaifiyarshi
biyayya ya saki Maijidda iye? Ina
tambayarka?"
Ya ce, "Subhanallahi Haj..." ta ce, "Kada
ka ce min komai, idan ba haka ba to menene?
Na ce me yayi maka?
Ai bai yi maka komai ba in baya ga hakan.
Haba! Wane irin abu ne haka, ka sa a mayar
mishi da kaya kayi abin kunya ka tonawa
kanka asiri ya gane abinda yayi ya bata maka
rai kai ka sani." Wai! Shiru Babana yayi ya
koma daki, ni kuma na dan ji dadi don kuwa
har a yau bana jin haushin Ahmad. Gagarumin
6
biki muka yi, cikin wadata don kuwa abinci
kala-kala aka yi, fate, shinkafa fara da miya,
dafa duka, alala, tuwon semo da shinkafa da
miyoyi daban-daban.
Ga kuma masa, kowa yana cin abinda yaga
dama ne.
Ta bangarena kuwa kwalliya nayi bana
wasa ba, don kuwa dinkunan da Ahmad ya
aiko min da su na saka, sun kuma amshi jikina
tsaf.
A gidan da Yaya Auwalu ya karba haya aka
saka Amarya wanda yake daf da namu.
An kuma watse biki lafiya, kowa ya tafi in
banda Baba Ladi wacce take zaune saboda
asibitin da zata fara zuwa, saboda ciwon kafa
da ke damunta.
Hakan yayi mun dadi ba kadan ba, don
kuwa katifata na dauko na dawo da ita dakin
Baba Ladi.
Wani lokaci sai mu kai karfe sha biyun dare
muna hira tana bani labarin mijinta da ya rasu.
Mahaifin Babana da irin gwagwarmayar da
ta sha da kishiyoyinta da a yanzu suka zame
mata 'yan uwa.
7
A duk sanda ta bani labarin su sai na ce oh,
amma dube ku Baba Ladi kamar ba ayi irin
wannan zaman ba.
Sai tayi murmushi ta ce, eh to wanda ya
hada ma ai ya raba tunda ina yake?
Bana shekaru ashirin kenan dukkanmu
kuma muna nan, ko wace ce zata fara bin shi a
cikinmu? Sanin gaibu sai lillahi.
Na ce, amma fa ni sai nake gani kamar gara
mun matsalar kishiya a kan ta uwar miji.
Baba Ladi ta waiwayo tana murmushi ta
kalle ni ta ce, saboda matsalar uwar miji ce da
ke ko?
Amma in ban da haka ai matsala bata wuce
kishiya ba. Sai dai idan kawaiba ka da
fitinanniya.
Ba zan yi musu da Baba Ladi ba da na gaya
mata cewa ita kishiya duk fitinarta ai ba za ta
saka mijinka a gaba ta ba shi umarnin sakinka
ya kuma sake ka din ba, kenan dai da
bambanci.
Kwanci tashi babu wuya sai dai kawai idan
Allah bai kaddara maka ganin gobe ba.
8
An wayi gari ne a yau na gama Iddah ta. A
karo na Rarshe kuma da nayi nufin fuskantar
gaskiya game da maganata da Ahmad ta kare.
A daren jiya kuma na kwana ne ina tunanin
abin da ya kamata nayi shi ne, komawata
Makaranta wanda nasan da wuyar gaske
Babana ya bar ni.
Umma dai ina ta yi mata maganar cikin
dabara nake 6ullo mata da kuma muhimmancin
karatun 'ya mace da kawayena irin su Sadiya
Tanimu.
Wacce a yanzu take aiki a babban asibiti, ta
gama karatunta na aikin jinya.
Umma ta ce, eh hakan yana da kyau amma
ai kuma naga bai kai darajar aure ba.
To gaskiya Umma ta fada, don kuwa ko ba
komai ai gani da Abulkhairi da ke can tare da
Babanshi.
Yanzu shekarunshi hudu ne har da watanni.
Idan da na haihu a gidan Ahmad da yanzu
abinda na haifa yayi wayo.
Tuna abinda ya faru da ni da cikina a
lokacin yasa zuciyata tayi mun wani iri.
9
Amma har yanzu Sadiya tana nan bata y
auren ba tukunna.
Ganin yadda Ummata ki maganar
makarantata yasa jikina yayi sanyi da yawa.
Anya Babana zai yarda kuwa? A wancan
karon ma ga yadda muka yi da Babana to
ballantana kuma yanzu. To amma duk da haka
Makarantar ita ce mafita a gare ni, tunda dai
karatu ba ya hana aure.
Sai dai ta ya ya zan bullo mishi?
Muna zaune da Baba Ladi a tsakar gida
hantsi muke sha, yayinda nake shafe mata
kafarta da wani mai da aka bata a asibiti.
Muna kuma 'yar hirar mu mai dadi. Umma
ce a kicin, kokarin damawa Baba Ladi kunun
tsamiya take yi.
Saboda wai bakinta da baya mata dandano.
Wayata tayi kara, na dauka.
Ahmad ne sai dai jikina a sanyaye na dauka
na shiga daki don kada Umma taji ta gane da
shi nake magana.
Bata hana ni magana da shi ba sai da kuma
a yanzu da na gama Iddah menene alakata da
shi?
10
Wannan ita ce tambayar. Har ta gama
kararta ina rike da ita a hannuna ban dauka ba.
Ta sake fara wani sabon rurin kamar kada
na dauka amma kuma sai na kasa.
Sallama na fara yi mishi tare da gaishe shi,
sannan muka yi shiru kamar dai ba kudi ne ke
tafiya ba. Shirun ne yayi yawa na ce ya
kasuwa?
Ya ce, Lafiya Hauwa'u, na kira ki ne naji
lafiyarki." Na ce, To na gode.
Na ajiye wayar ina jin haushin abinda yasa
na dauka.
Shiryawa nayi da daddare na nufi gidan
Yaya Auwalu, don nayi mishi magana kan
Makarantata.
Don nasan idan ya nunawa Babanmu yana
da ra'ayi a kan karatuna babu mamaki nayi
nasara ya sassauto.
Matarshi na samu Samahatu tana ta hidimna
dashi tana kokarin hada mishi abincin dare.
Sha'awarsu ta kama ni.
Yaya Auwalu yayi sa'ar mata nitsattsiyar
yarinya, ga kunya da kirki. Cikin girmamawa
ta gaishe ni ta juya tana hado wani abincin.
11
Kasancewar kicin din ta falo yasa Yaya
Auwalu ya ce idan Hauwa'u za ki hadowa
abinci bar shi zamu ci a nan.
Ta ce, To don haka ta miko min cokali na
saka a plate din Yaya Auwalu muna ci tare.
Sai da muka gama cin abinci sannan na ce
Yaya wurinka nazo. Dukkan nutsuwarshi ya
tattaro ya zuba mun ido ya ce lafiya dai ko?
Na ce, Lafiya kalau, ya ceTo
Alhamdulillahi muje waje. Na ce, A'a zamu
iya yin magana a nan babu komai ai.
Duk da haka sai da Samahatu ta shiga daki
har da ce matan da nayi tayi zamanta kawai.
Na dan yi mishi 'yan bayanan da zan yi
mishi kan bukatata ta komawa Makaranta, da
kuma muhimmancin hakan a wurina idan an
bar ni.
Karshe nayi mishi bayani mai gamsarwa
kan hakan ba zai hana ni aure ba idan damar
hakan ya samu.
Ya dan yi shiru ya ce, "To ai matsalar a
wajen Baba ne da kyar zai yarda don ba ma zai
kalli abin ta wannan bangaren ba.
12
Kuma ni nasan yana da gaskiya don kuwa
karatu tuntuni ba a yishi ba sai yanzu ne za a
tsiri yi Hauwa'u zai yiwu?
Na ce zai yiwu Yaya, ai komai sa kai ne
1dan mutum yayi niyyar yi. Ya ce, To haka ne.
Muka fito da Yaya Auwalu yana rakoni
gida muna 'yar hirarmu.
Kwata-kwata ban kula na ganshi ba,
Abdussamad ne. sai da naji suna gaisawa
Yaya Auwalu.
Na daga kai na hango shi tsaye kofar
gidansu, hannayenshi zube cikin aljihun
wandonshi.
Duk da dare ne bai hana ni gane cikar da
yayi ba. Ban ce mishi komai ba gida kawai na
shige ina tuna rabona da ganin Abdussamad
tun kafin aurena da Alhaji Ahmad.
Kwanaki biyu ne bayan nan ya shigo
dakinmu ya same mu muna hira da Baba Ladi,
ya zauna.
Mun jima muna hirar dashi sai da ya fara
shirin tafiya ya ce, to ke idan aka ce an bar ki
ki koma makarantar daga ina za ki faro?
13
Cikin sauri na kalle shi na ce, Yaya Baban
ya bari ne? ya ce, eh ya yarda amma kin san ba
ki da takardar Secondary school ko?
Na ce, eh. Ai niyyata na koma daga inda da
ma na tsaya, wato SS 2. Ya dan yi shiru ya ce,
To amma me yasa ba za ki yi ertra moral
classes ba sai ayi miki register ki rubuta
(WAEC) da (NEC0).
Yayi min register gaba daya har da kuma
reciept na biyan extra moral classes.
Na tsaya bayanin murnar da nayi ma batawa
ne kawai. Haka nan shi kanshi Yaya Auwalu
yayi ne don naji dadi.
Tunda ba wani kudi ne da shi ba, dawainiya
tayi mishi yawa, a yanzu mafi akasarin hidimar
gidanmu a kanshi take, ga kuma na gidanshi.
Ban san dalili ba sai kawai naji tamfar an
yaye min dukkanin matsalata. Ban wani bata
lokaci ba a washegarin ranar ne kawai na fara
zuwa daukar karatuna don fara shirin zana
jarrabawar shaidar gama Secondary school.
Kwanaki kadan da fara zuwana karatu na
dawo da yamma ina shan furar da na samu
Baba Ladi ta ajiyc mun.
14
Sai kawai ga dan aika wai ana sallama da ni
a waje. Mamaki ya matukar kama ni.
A sanina dai ban taba kula wani ba tun
gama Iddah ta, na ce ma dan aiken waye ne?
Baba Ladi ta ce, mu ki ke tambaya ko shi da
aka aiko? Yarinya tayi aure ta zauna a dakinta
wani sanabe wai zata yi karatun da da can ba a
yi ba.
Nayi lullubi na fito na bar Baba Ladi tanata
sababinta.
Hango wata dalleliyar mota nayi sai kashe
ido take yi, sai dai tun. daga nesa mamaki ya
kama ni, Ishak ne.
Na kama baki ina mamaki tare da murmushi
a raina dai ina cewa to wane irin kudi wannan
mutumin ya samu haka?
Na karasa inda yake na ce, To ya ba ka
karaso ba ku gaisa da su Umma. Ya dan yi
murmushi ya ce, Hajiya Hauwa'u kenan ai sai
na samu fuska a wurinki tukunna kada nayi
karanbani.
Komawa nayi na sanar da Umma zuwan
Ishak, na jawo tabarma nayi mishi shimfida
tare da ajiye mishi ruwa.
15
Suka gaisa da Baba Ladi da Umma, sannan
ya koma motarshi ya zauna.
Nima can na sake binshi. Na tambaye shi
Yaya da yaran duka, Ya ce suna nan kalau.
Satin can ma ina Kaduna tare da su na ma
sanar da su cewa zan zo, Yaya ta ce na gaishe
ki sosai.
Na dan yi murmushi don kuwa raina yana
Son Yaya. Ya dan kalle ni ya ce, Jininku ya
hadu da na Yaya.
Na ce, To ya harkoki da iyali?
Ya ce, "To harkoki kam mun gode Allah,
amma iyali kam ai kema kin dai tambaya ne
kawai don jin baki?
Ban ja zancen ba a nan na bar shi don ba
doguwar magana nake nema ba.
Bai wani jima ba ya sa hannu a aljihun mota
ya dauko kudi masu auki ya miko min.
Na kalli kudin na kalle shi na dan girgiza
kai na ce a'a na gode.
Ya zuba min ido yana kallona ya ce ba za ki
kar6a ba saboda me?
Na ce, saboda ba ni da buRatar su. Take
yanayinshi ya canza alamar ranshi ya sosu, ya
16
Ce to amma ai ko ba ki da bukata da sai ki
karba don na gane ina da mutunci a wurinki.
Ba na ba ki ki ki karba ba, tunda nima ban
ce kina da bukatar su ba, kyauta ce nayi niyya.
Nasa hannu na karba tare da cewa, Na gode.
A tsakar gida na samu Umma da Baba Ladi
suna 'yar hirarsu da alama kuma kan zuwan da
Ishak yayi ne.
Baba Ladi ta ce, To ina tabbatar muku dai
wannan mutumi idan ko me yazo yake nema ta
tattara a kuma daura mata aure da shi ta koma
ta rike danta.
Tunda ma da alama a gidanshi nata arzikin
yake, ba gashi shi wannan da ta aura ba 'yan
rabuwarsu bata haihu ba.
Sannan shi mutumin da yayi saki ya dawo
yake neman a komai ai alama ne na zai gyara
kuskurenshi na baya.
Ina jinsu ban ce musu komai ba haka nan
ban ma nuna musu kudin ba, don kuwa nasan
halin Umma.
Da daddare bayan mun idar da sallar Isha'i,
hira muke yi da Baba Ladi ta kara sako mun
zancen Ishak da zuwan da yayi.
17
Na ce, kai Baba Ladi kenan, kuma kawai
daga mutum yazo ba ki san abinda ya kawo shi
ba sai ki ce a bishi a sasanta.
Saboda zamana ya ishe ki ba kya son ganina
ko ya ya? Ta ce, a'a ba fa haka nake nufi ba,
zato nake ko maganar komawarki ce ta kawo
shi?
Na ce, To ba haka ba ne, ranar da yazo a
kan maganar ko-men zan kawo shi wurinki.
Ni kaina nasan zamana a gida baya yiwa
mahaifana dadi, to amma lalura idan ta samuu
mutum hakuri yake yi da ita, ya jira lokacin da
Ubangiji zai warware mishi ita.
Wannan yana daga cikin dalilin da yasa na
dukufa wajen ganin na dage na samu nasara a
kan karatuna.
Kyakkyawan shiga nake yi ta mutunci a duk
lokacin da zan tafi Makaranta.
Dogon hijabi nake sakawa, haka nan ko a
Makaranta bana shiga harkar kowa.
Karatuna kuma nake yi bil hakki da
gaskiya. Yau ma fitowa nayi zan tafi
Makaranta cikin kyakkyawan shiga.
18
Har na hauro saman layinmu, daga kan da
zan yi sai muka hada ido da Abdussamad da ke
tsaye kofar shagon askin unguwar.
Shima ni yake kallo, ban tsaya ko tunanin
gaishe shi ba wucewa ta kawai nayi. Sai dai a
raina tunani nake yi abinda ya dawo da shi
cikin ranakun aiki.
Tunda a sanin da nayi yana zaune ne a
Abuja inda yake aiki a Ma'aikatar Sufuri.
Tun a wancan karon da yaro yayi mun
rashin mutunci ya fita mun a ka, don haka a
yanzu ma babu ruwana da sh1.
Sati guda cif da zuwan Ishak, sai kawai
gashi ya dawo abinda a take ya fassara min
abinda yake nufi.
Ko da dai bai budi baki ya furta ba. Nima
kuma ban ce mishi komai ba, baya ga fitan da
nayi ya gama maganganunshi ya sauke min
kayan masarufi iri-iri.
Na shiga gida bayan tafiyar shi. Tun daga
shigana jikina yayi sanyi saboda yanayin
kallon da Umma take yi mun.
Daga nesa kadan na nemi wuri na zauna,
amma na kasa sukuni.
19
Bata ce min komai ba, aikace-aikacenta take
tayi. Bayan ta gama ta shiga daki ne naji ta kira
ni.
Har a lokacin fuskarta bata washe ba. Ta
zuba min ido a durkushen da nake ta ce "Za ki
koma gidan shi ne?
Tambayar tayi mun wani iri, cikin sauri na
dago kaina na kalli Umma da itama ni take
kallo.
Idan za ki koma gidan shi ne ki fada saboda
na sanar da Babanku tun kafin ki karasa zubar
ma mutane da mutunci.
Cikin sauri na ce, "Umma kiyi hakuri ba
izinina yake nema yake zuwa ba, ganinshi
kawai nake yi.
Ganin shi kawai ki ke yi shi mahaukaci ne?
kina nufin idan da bai ga fuska a wurinki ba za
ki ganshi?
Tunda ki ke abubuwan da ki ke yi a gidan
nan ban taba ce miki komai ba, amma ki kwan
da sanin cewa a wannan karon kada ki sake
fitowa ki dawo gidannan ki zauna.
Hakan yana nufin sabon aure ne ko kuwa
ko-me don abin ya ishe ni haka, sannan na baki
20
kwanaki kadan mutumin nan ya daina zuwa
gidan nan ko kuma na shaidawa Babanku don
ya sani."
Dawowa daki nayi na zauna ina