Showing 36001 words to 39000 words out of 69924 words

Chapter 13 - KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf



"Fadi kanka tsaye yallabai,ai dukka kunnuwana suna tare da kai"

"To shikenan yallabiya" ya furta cikin dan salon tsokana,yaza hannu ya tura hularsa baya
sannan yace

"Zuwa yanzu wasila ina gani lokaci yayi da zamu maida alaqarmu ta ainihin gaske,tunda iya
fahimtar juna mun yishi tsahon shekarun da muke tare,ina so ki shaidawa umma,ta yiwa su
kawu magana in sha Allah qarshen watan nan zan aiko da kudin aurenmu hade da kudin sa
rana,kuma banason duka a wuce wata hudu in sha Allah ba'a yi bikin ba" tunda ya fara zancan
ta zuba masa ido gabanta yana faduwa. Bata shirya auren isma'il ba bata kuma son ta rasashi
tun yanzu,tafison koda zai tafi sai idan FAISAL ko wani kaman faisal din ya kawo mata kudin
aurenta tasan ta kama dahir

"Kudin aure kuma isma'il ka gama ginin ne?" Ta fada tana dubansa. Dan nazarinta yayi kadan

"A'ah,yanzu ba magana ake ta gama gini ba,gini na yana da buqatar a zuba masa kudade da
yawa,inason nayi abu me kyau me tsari,wanda duk wanda ya kalla zai san na mori nemana"
Fuska tadan bata tana girgiza kai

"Gaskiya nidai nafi buqatar ka kammala tukunna"

"Wasila" ya kira sunanta kai tsaye a maimakon seela da yakan kirata da shi,abinda yasa itama
tayi hanzarin daga kai tana dubansa

"Ni na shirya aure magana ta gaskiya,sanann hajiya kanta kullum maganarta kenan nayi aure
taga 'ya'yana kafin ta Allah ta kasance a kanta tunda ban rasa komai ba,hankalina nima yanzu
ya karkata ga hakan,in sha Allah bazan wuce wannan lokacin ba tare da nayi aure ba,idan kin
shirya nima na shirya"
"Idan ban shirya ba fa?" Ta fadi a qasan ranta tana dan satar kallonsa gabanta yana sake
tsananta faduwa. Isma'il shine saurayi kusan na biyar da haka ta taba faruwa a tsakaninsu.
Abdullahi,abubakar,nasir da sagir ga kuma isma'il. Dukkansu sun tafi ne saboda samun masu
kudin da take muradi a irin wannan lokacin,kamar hadin baki dukkansu sai zance ya fara nisa a
tsakaninsu sai masu kudin da take buri su bayyana saisu rushe gwamnatinsu,sai bayan ta
sallamesu ne saboda ganin wadan nan sai suma daga baya su fece su barta ba wan ba qanin.
Tayi qunan rai a sannan ba dan kadan ba,tun daga lokacin ta yanke hukuncin ta daina sallamar
standby din har sai ta tabbatar ta kama wadancan din,yanxu gashi ana neman kwatawa
(Yan mata!,yan mata!,wallahi wallahi wallahi kuyi hankali,ku yiwa kanku karatun ta nutsu,a irin
wannan yanayin da ake ciki babban arziqi ne ma ki samu wanda zaice yau so nake muyi
aure,da yawansu ba aure bane a ransu,saidai suzo su hole da ke kamar uwa su ta haifa musu
ke,da yawan 'yammata ba mijin aure suka rasa ba, a'ah.......MIJIN BURI MIJIN MAFARKI suke
jira ko ince suke nema,kibar wahalar da kanki kina namena lallai saikin auri me kudi,wallahi
wannan din da kika raina qila shine me kudin da kike burin amma kika wulaqantashi,Allah ya
rubuta sai ya aureki zakuyi arziqin tare amma kika bijire saboda idanunki sun kulle, ba'a ce ki
auri namijin da bazai iya kula dake ba,namijin d a baikai ajinki ba,tunda ko a musulunci akwai
KAFAA'A wato dacewa da juna,amma ta yaya a gidanku ana kulawa dake da kwatankwacin
kudin da sukakai dubu dari kice ke wanda zai kula dake da million d'ari kike nema?wanne irin
buri ne wannan?. A qa'ida dai ba'a son ana kula dake a dubu dari ki auri wanda saidai ya kula
dake da dubu goma,ko ina anason aga mace gidan mijinta yafi gidansu ci gaba,AMMA
FA ba tarin dukiya ba. Albishirinku!!!!,akwai tarin dimbin matan da zaki gani cikin leshi
na kece alfarma,motar hawa ta isa da qasaita,gold kowanne corners na jikinta bodyguard da
sauransu,amma billahillazi la'ilaha illa huwa da zata bude miki cikinta saikin kwana kina sallah
kina godewa Allah da ya barki a inda kike,shi aure bawai mutum me DUKIYA kadai ake nema
ba,Inaaaaaa........'yar uwa nemi MAI ZUCIYA wanda ko matar da take Jin mijinta wani ne idan
kuka jera da ita zatasan lallai kinfi qarfin raini,nemi mijin dake KISHINKI wanda bai yarda
matarsa ta rasa komai ba,wanda bai yarda a raina matarsa ba,wanda zai maidake SHALELE
kifi qarfin rainin kowacce mace,mijin da zai kula da lafiyarki sai inda qarfinsa ya qare,wanda ya
damu da damuwarki me tsare miki mutuncinki da dukkan qarfi da iyawarsa,wanda zai dauki
iyayenki tamkar nasa ya basu girma na musamman.ba mai tarin dukiyar da baki da tabbas din
zaki cita cikin kwanciyar hankali ma kuwa?. Da yawan 'yammata basu shiga gidan aure sunsan
meye ainihin ma'anar miji ME DUKIYA ba dame ZUCIYA wannan shike rudarsu. Akwai wani jin
dadin da duk girmansa kome miji yake baki koda kullum million hamsin ce wallahil azeem idan
yana miki wasu halayen ba zaki taba jin dandanonsu ba,saikin gwammace naira dubu goma
yake baki yake mua"amalantarki cikin nuna qauna tausayi da girmamawa,don Allah qannena
yayyena da sa'annina YAMMATA ku farka,KU FARKA,KU DAINA KORE MAZAJEN AURENKU
SABODA HANGE DA NEMAN WANDA YA FISHI,Allah ya shiga lamuran rayuwarmu gaba daya



*HUGUMA*

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 17



Tana tsaka da wannan nazarin akayi sallama qofar soron,isma'il ya miqe a nutse ya
karbo saqon ya dawo ya zauna yana ajjiyewa gabanta

"Kada ki damu,amma kije kiyi nazari,saidai am sorry to say....koda baki shirya aure ba in sha
Allah zanyi aure a wannan lokacin,don haka kiyi tunani a hankali kina da sati daya cif,duk
abinda kikaji zuciyarki bata kwanta da shi ba kada ki yanke shi,ki zabi abinda kikaji kinfi aminta
dashi,zaman aure zamuyi wanda muke saka ran mutu ka raba,bawai aje a dawo ba" da wadan
nan maganganun yayi mata sallama ta dauki ledar takeaway dinta ta wuce gida.

Da farko jikinta yayi sanyi sosai,har ma ta dinga juya lamarin,wata salihar zuciya daga
qirjinta tana gaya mata

"Me zaki jira?,kin cika shekara talatin fa kenan wasila,ki yarda da isma'il kiyi aurenki ki
huta,tunda bazai barki da yunwa ko a wulaqance ba" zuciyar dake da gamayya da shedan na
tuna mata

"Shi kuma faisal ya zakiyi dashi?,idan kika amincewa isma'il shi kuma faisal yana da niyyar
aikowa kinga kin yiwa kanki asara,yanasonki Faisal yanason kuyi aure,akwai jifan da ake miki
ne ansan da arziqi a jikinsa ba'a so ki shiga gidan hutu shi yasa,amma da tuni kin jima da zama
matarsa" kai ta jinjina tafi yarda da shawara ta biyu. Su masu jifan nata qila an duba musu
sunga wahala zatasha a gidan isma'il shi yasa basu maida hankali su rabasu ba,sun hango
arziqi jikin faisal wannan dalilinne yasa sukafi maida hankali a kansa.

"Bari kiga" ta fada ita kadai tana janyo wayarta,wata number dake dauke da sunan MALAM ta
lalubo ta dannan masa kira.

Sai data kusa katsewa ya daga,suka gaisa da kakkaurar muryarsa sannan ta fara
masa bayani

"Isma'il ya matsa malam,yanzu haka zancen turowa yakeyi,ni kuma tun kafin ma ka shaidamin
babu alkhairi tsakanina da shi nafison faisal gaskiya,don Allah malam a taimaka asa faisal ya

turo ko yayi maganar kafin isma'il ya dawo" kai ya jinjina,yanzun haka a buqace yake da kudi

"To ai shi kansa faisal din ba maganar aure a ransa kwata kwata,saidai zamu bullo masa ta
bayan gida,bazai wuce wata guda ba tare da ya aiko din ba"

"To na gode sosai malam Allah ya saka maka da alkhairi"

"Ameen........yanzuuuu ......akwai turare da zamu siya,daga Syria ake kawo wannan turaren,sai
wasu duwatsu daga misra a cikin ruwa ake samo ire irensu"

"Kamar nawa kenan ane buqata malam?" Dan shuru yayi sannan yace

"To,ai wasila ke abar tausayi ce,dole me imani ya tausaya miki saboda irin jifa dake jikinki Allah
yayi yawa dashi,ki bayar da dubu ashirin,abinda bai cika ba na cika miki cikin aljihu na" Taji dadi
sosai,godiya ta dinga yi masa kamar ta durqusa,sukayi sallama ta kashe wayar.

Ranta fes ta soma cin takeaway dinta,a yanzu tunaninta inda zata hada kudinne
kawai,don ba komai takeson gayawa umma ba,wani abun sai ta doje akai,tafison kome zatayi
tayi abinta kai tsaye ba'a kawo mata cikas ba.

Wayarta ta jawo sai tayi tunanin tayi kiran faisal(sau tari dama wasu 'yammatan suna
qarewa ne da kiransu,kafin ya kirasu sau daya sun kira biyar). Duka yau basuyi waya da shi
ba,amma takan bashi uzurin cewa harkokinsa ne sukayi masa yawa.

Har ta katse bai daga ba,sai data qara kira bugu biyu ya dauka. Ranta fes ta
shagwabe masa,shima ya biye mata suka bata kusan awa biyu suna waya,don leqowar umma
biyu amma bata gama wayar ba.

Suna tsaka da wayar dai dai lokacin da tasan yafison hira da ita ta katse wayar,sai
bayan minti kusan biyu ta kunna ta kirashi

"Nayita trying kuma naji a kashe"

"Uhmmm wallahi,qawata ce ta shigo,bikinta ya kusa,ta kawomin anko amma nikam gaskiya na
gaji da yin ankonnan,nima burina yanzu ace yau nice na fitar da nawa ankon kamar kowa?"

"Nawa ne kudin ankon?" Ya fada yana share maganarta ta biyu

"Dawainiya baby?"

"No,kada ki damu abinda kakeso kake wahaltawa ai ko"

"Gaskiya ne" ta fada da wata siriryar shu'umar muryarta cikin son sake shigar da kanta

zuciyarsa

"Lace ne 20k,sai atamfa 10k"

"Alright,to ba damuwa,zan saka miki 40k harda kudin dinki"

"Wow.....Allah ya biya, godiya nake" a cikin ranta tana jin ta samu kudin da zata biya malam
harda riba.

Wannan abun da ya faru a ranta sai ta sake jin me zatayi da isma'il?,mutumin da
qarshen kyautar bajintar da zaiyi mata itace 10k,itama sai bisa abu me amfani tare kuma da
qwaqwqwaran dalili. Tun a daren ta yankewa kanta shawarar sallamar isma'il,indai aikin malam
yayi kyau Faisal yana magana zatace a saka wata biyu ma,tasan daga umma har yayunta duk
a shirye suke mijin dama kawai ake jira.

********Tun da tayi sallar asuba bata koma ba ta wuce kitchen don hada abincin yara da nasu da
wanda za'a kaiwa zainab asibiti.

Shima saleem din da ya dawo daga masallaci zama yayi saman abun sallah yayi
lazumi da karatu kamar yadda ya saba,bayan ya kammala bacci yadan daukeshi.

Koda zai farka ta kusa gama sallamarsu,don uniform kawai suke sakawa,ya shiga
dakin ya iskesu kowa yana saka uniform dinsa. Alhassan ya gama iftee yake sakawa socks. Su
alhassan suka fara gaidashi,ganin haka kuma sun hada ido da haneefa sai itama ta matso tana
gaidashi.
Gefe ya koma yana karantar kowa. Tare ya canza musu uniform da komai na
makaranta,amma idan kaga nasu haneefan zakayi tunanin sai da suka shekara biyu sannan
aka dinka nasu alhassan,a haka ma kuma wai a wanke suke. Yana daya daga cikin abinda yasa
daraja da martabar ruqayya ke qaruwa a idanunsa,sau tari idan zai canza musu abu takance
yabar nasu alhassan din tunda nasu baiyi komai ba, musamman idan ta fuskanci baya da kudi
sosai a hannunsa. Saidai karamcinta yakan sanya bayan wani lokaci itama yayi mata kyautar
wani abun da yake kaman madadi na wannan sadaukarwar da tayi (hakan yana da kyau,bawai
kice don an yiwa kishiyarki ba koda miji yadan shiga yanayi kema ko a mutu ko ayi rai sai an
miki ba ke ba ruwanki,a'ah.....zuciya fa tanason me kyautata mata,sannan duk abinda ke faruwa
namiji yana ankare,saidai ba kowane zai nuna ba amma a qasan zuciyarsa yasan da hakan.
Bugu da qari ke kanki idanma ba zaki iya haqura ba,akwai hanyar da hankali kwance zaki
fanshe kudin ba tare daya ankara ba,kema kuma baki rasa wannan darajar ba cikin wayo
hikima da dabara).

Da dukka lunch box dinsu ta shigi,tuni haneefa ta biyewa khalil suka dinga doka tsalle
bayan sun bude sunga meye a ciki. Rabon da suje da sabon girki har sun manta,sannan koda
zasuje da shi dinma ina yaga dadi da haduwar wannan. Dubansa ya maida kanta ta duqa

kadan daga tsaye tana gyarawa iftee hijabinta. Yadan lumshe ido,ko yaushe abinda zai sanya
yaga kyanta cikin idanunsa takeyi. Rigar baccin jikinta me wani irin taushi da sulbi sabuwa ce,
gray color me wani irin daukan idanu,tabi tattausar chocolate color din skin dinta ta kwanta
sosai. Baya taba gajiya da kasancewa tare da ita,koda komai bazai hadasu ba ta jingina da
jikinsa kadai yana shaqar daddadan qamshinta yana shafar soft skin nata kadai yana sakashi
nishadi. Hular kanta tadan zame bata,gashinta duk da baikai tsahon na Zainab ba amma yafi na
Zainab bashi sha'awa da qayatar dashi. Don kafin ta karba girki shekaran jiya taje aka wanke
mata shi fes aka mata stretching don ba kasafai ta fiya ma sanya relaxer ba. Qamshin hair mist
kawai yakeyi da hair oil.

"Zauna ki huta" ya fadi yana amsar agogon iftee da take shirin daura mata. Dagowa tayi sai
suka hada ido,ta sakar masa murmushi ganin yadda yake faman qare mata kallo,har
albarkatunta dake cikin riga idanunsa sai da sukakai kai

"Na gode" ta fada a tausashe taja baya tana zama. Dan murmushi ya saki,qamshin kanunfari na
fita daga bakinta,sai zainab ta fado masa,ya tabbatar da itace tayi masa magana a irin wannan
lokacin saidai ya kauda kai.

Da kansa ya kadasu farfajiyar gidan wajen driver,sai da ya tabbatar sun fice sannan ya
dawo gidan da dan sassarfa,don ta riga data tsomoshi.

Tana qarasa gyaran falon ya sameta tsaye gaban tv. Ta bayanta ya tsaya ya
rungumota jikinsa yana cewa

"Aiba wani aiki,aiki kuma ya qare,aji da dan hajiya malam saleem" qaramar dariya ta qwace
mata,don ya tuna mata da tsohon sunan da ake kiransa shekarun baya

"Haba malam saleem,da safen nan?"

"To me zan jira?,bayan jiya qwalele kikayimin,wai ina isowa na tarar kinyi bacci ko tausayina ma
bakiji" ya fadi yana shafa kafadarta har zuwa tsintsiyar hannunta. Tsigar jikinta ce ta zuba
wannan ya sanyata noqe kafada

"Kuma kika saka wannan rigar don kawai daukan alhaki ko?" Ya sake fada yana juyo da ita tare
da saka hannunsa ya fara balle bottom na rigar. Shigewa jikinsa tayi wannan ya bashi damar
riqeta sosai suka wuce bedroom dinta dake a gyare fes don dama ba ciki suka kwana ba.
Yanayin bedroom din ya sake qara masa shauqi qwarai da gaske,ya tsumu da turaren wuta
qwarai,hakanan bata gajiya da yiwa bedsheets pillow case da blanket dinta kabbasa.

(Ko da magani sai da tsafta,ko da gyaran HQ saida gyaran tukunya,gyaran lafazin baki iya
mu'amala da gyaran muhalli. Koda wadannan sai kina updating yanayin position na
auratayyarku,ba ko yaushe ki shirgice ki jibge kaman kayan wanki ba,KINSAN AMFANIN DIRTY
TALK?KINA MASA KO SAIDAI 'YAMMATA A WAJE SUYI MASA KINA ZAUNE?IDAN KIKA GA

KUMA AN MASA KICE WANE YA ZAMA DAN ISKA MAZINACI?,BAYAN KEMA KIN TAKA
RAWA?,TURQASHI.....nauyinku nakeji amma zan bincina muku kadan cikin littafin nan ta
hanyar data kamata idan na samu chance,ragowa kuma zai shige a littafin GUDUN
ƘADDARA 2024 in sha in sha Allah.
*HUGUMA*
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 18
________________________________
https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39


*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA
HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU
QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA
MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har
zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________




Ita ta fara ankara bayan komai ya kammala,ta tureshi tana sauka a gaggauce daga
gadon

"Lokaci yana wucewa fa, za'a kaiwa maman haneefa breakfast" da kallo ya bita yana dan bata
rai cikin sigar zolaya

"Shine kuma zaki tureni?"

"Yi haquri,kai dinne....."ta fadi tana qyalqyale masa da dariya sannan ta tura toilet din ta shige.
Har ga Allah batasan abinda yasa yake sake maqale mata ba duk kwanan duniya,abu guda
daya ta sani,duk da maganin gyara ingantattu da take hadawa kanta ko da ta siya gurin
amintattun da tasan su waye?,zuciyarsu kuma a tsarkake take......bayan wadannan ta naqalci
abubuwa masu yawa dake tafi da zuciyar saleem din. Ba ruwanta da abinda ke tafi da zukatan
maza,ABINDA KE TAFIYAR DA ZUCIYAR SALEEM ne kawai a gabanta (maza sun

banbanta,me yiwuwa abinda ke burge wancan ba shine abinda yake burge mijinki ba,ki karanci
mijinki a karan kansa,saiki tsara yadda zaki tafi dashi).

Yana lalace a gurin yana tuna yadda ruqayyan ke bashi gamsuwa ta kowanne bangare
tare da hasaso matsayin Zainab a duk lokaci irin wannan. Zai iya rantsuwa koda ya samu
zainab din a matse,amma baya samun nutsuwa da gamsuwar da ruqayya ke bashi. Ruqayya
kawai yake kaiwa ziyara ya samu hanyarta ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login