Showing 1 words to 3000 words out of 10415 words
Chapter 1 - Rijiya Gaba Dubu Book 3 by Abdulaziz Sani Madakin Gini.pdf
RIJIYA GABA DUBU 3
Lokacin da jarumi Imhal da sadauki Darwaz suka ruguntsume da azababben yaki a tsakiyar filin
fadar birnin misra wanda yan kallo sama da mutane miliyan dari suka kewaye, sai filin ya cika
da ihu da shewar jama'a, nan fa kowa ya cika da mamakin yadda Imhal ke iya kare hare-haren
sadauki Darwaz har yake mai da martani, sai da aka day lokaci mai tsawo ana wannan artabu,
daya daga cikin jaruman biyu bai samu nasarar Koda kwarzanar jikin daya ba,Al'amarin da yasa
jikin sarki taryan yayi Dan sanyi kenan, kuma ransa ya baci, bai San sanda ya mike tsaye ba
daga kan karagar sa ta mulki ya fara yiwa jarumin sa kirari, abinda sarki taryan bai taba yiba
kenan a tarihin gasa da ake yi tsawon shekaru, Koda sadauki Darwaz ya ga sarkin sa ya mike
tsaye Daga kan karagar sa yana Koda shi,sai ya fusata ainun ya kara zage damtse iya karfin sa
ya dinga kaiwa Imhal Sara da suka da dukkan karfin sa,cikin wata irin sabuwar jarumtaka mai
tsananin zafin nama ta BAZATO, Nan fa shima Imhal ya dinga yin iya kokarin sa don kare
kansa,amma sai ya zamana cewa dakyar yake iya kare hare-haren, kuma baya iya mai da
martani, Koda ganin haka sai murna ta kama sarki taryan ya dinga shewa, Ai kuwa sai jama'ar
gari suma suka dinga taya shi,ya zamana cewa babu mai yiwa jarumi Imhal jinjina a filin, Duk
abinda yake faruwa sarki gurzalu yayi shiru yana guntun murmushi kawai don yasan wanene
Imhal, A gaba dayan filin gasar babu wanda hankalin sa ya dugunzuma ainun bisa ganin halin
da jarumi Imhal ya shiga sama da Gimbiya Shumaira, domin duk sanda taga an kai masa wani
mugun gari sai kaga ta kai da kai kamar ita ake kaiwa, wani lokacin ma har mikewa take yi
tsaye zumbur! kamar zata kwalla ihu,ita kuwa Gimbiya lamirat kawai tana kallon fadan ne,ba ta
ma San jarumin da take so ba acikin ranta, amma kuma sanda ta tuno da bayanin da mahaifin
ta sarki gurzalu ya gaya mata cewar idan Imhal ya samu nasarar lashe wannan gasar
JARUMTA sai ya ga bayansu sai ta ji ta tsani Imhal fiye da komai a duniya, domin babu abinda
take so sama da sarki gurzalu da mahaifiyarta, ana cikin haka ne sadauki Darwaz ya kara
kuntata Imhal har ya matse shi a waje daya ya hana shi matsawa, kuma ya cigaba da kai masa
Sara da suka na hauka ba sassauci, ai kuwa sai ya samu nasarar dankara masa Sara a saman
kirjin sa,take Imhal ya kwalla ihu ya fadi kasa a lokacin da jini yayi tsartuwa daga kirjin nasa,
Koda Darwaz yaga Imhal ya fadi kasa sai ya kai masa suka da takobi a ciki, Cikin zafin nama
Imhal ya goce ya doki marainansa da kafa, kawai sai ji akayi Darwaz ya kurma uban ihu ya fadi
can gefe daya, a sannan ne Imhal ya mike tsaye dakyar jini na zuba kirjin sa yana yin layi,Cikin
sauri ya cire wani yanki dake daure a goshin sa ya daure raunin don ya rage zubar jinin, a
sannan ne Darwaz ya mike tsaye zumbur! ya kwarara uban ihu bisa ganin ya samu nasarar
yiwa Imhal rauni, A sannan ne fa sarki taryan ya cigaba dakyakyata dariyar mugunta, Koda
suka had a idanu da sarki gurzalu sai gurzalu yayi masa murmushin mugunta ba tare da nuna
karayar zuciya ba,Al'amarin da yasa jikin sarki taryan yayi Dan sanyi, kuma ya daina kyalkyala
wannan dariyar muguntar,A wannan lokacin Imhal ba karamin kokari yayi ba ya tsaya bisa
kafafunsa, don jiri ne yake dibarsa sakamakon jinin da ke zuba daga kirjin sa kuma idanunsa
suna lumshewa yana gani dishi-dishi,Koda Darwaz ya lura da irin halin da Imhal ke ciki sai ya
bushe da dariyar mugunta don yasan cewa yanzu ne zai gama da Imhal farat daya.
zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU 3 CIGABA 1
Kawai sai Darwaz ya gyara tsayuwarsa, sannan sannan ya sake zaro wata sharbebiyar adda a
bayansa wato ya hada makamai guda biyu a hannun sa yana mai gyara tsayuwarsa gami da
fuskantar Imhal, A sannan ne fa filin gasar ya rude da shewar jama'a, Attajiran da suke yin caca
akan gasar suka dinga yiwa junansu kirari, Kaso bakwai cikin kaso goma na 'yana cacar duk
sadauki Darwaz suka zaba a matsayin jarumin su,kaso uku ne kacal suka yi kundunbala suka
zabi Imhal, tun da ake yin caca a wannan gasar ba a taba zuba kudade masu yawa ba irin na
bana,Da yawa Daga cikin attajiran da suka shiga wannan caca idan ba jarumin su ne yaci gasar
ba karayar arziki tazo musu kenan.
Lokacin da jaruman biyu suka fuskanci juna, sai filin gasar yayi tsit! aka zuba Ido don ya ga
wanda zai yi nasara, saboda ansan cewa wannan gamon da za ayi na karshe ne, Koda Darwaz
ya ga shima Imhal cike yake da burin neman sa'a, sai ya budi baki ya karanta wadansu
Dalasumai na tsafi guda biyu, kawai sai Imhal yaga wata irin gagarumar iska ta kanannadeshi
tasa ya kasa Koda daga hannun sa,ko matsawa daga inda yake, kuma sai Darwaz ya rugo
izuwa kansa yana mai daga makamansa sama yana ihu, Abin al'ajabi shine, babu wanda yaga
wannan guguwa wacce ta kanannade jarumi Imhal face sarki gurzalu, domin shine kadai yake
da karfin ganin sihirin tsafin Darwaz,Imhal yayi iya kokarin sa akan ya kaucewa guguwar ya
kasa,Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sa ke nan yana ganin mutuwa muraran, Koda sarki
gurzalu yaga abin da ke shirin faruwa sai yayi nuni da hannun sa izuwa kan guguwar da ta
kanannade Imhal don ya kawar da ita ,amma sai nasa sihirin tsafin ya ki yin tasiri, Take ya tuna
cewar ai Yau ya manta bai dauro gurunsa na tsafi ba ya barshi a can cikin wata akwati a dakin
da aka sauke shi,nan take bakin ciki ya rufe shi ya sunkuyar da kansa kas yana mai rufe
fuskarsa don baya son Darwaz ya samu nasarar kashe Imhal, A dai-dai wannan lokaci ne
hankalin Shumaira ya dugunzuma ainun bisa ganin za a hallaka jarumin da taji ta kamu da
tsananin sonsa a Yau dinnan kuma farat daya,kawai sai ji tayi hawayen bakin ciki ya zubo
mata.Gaba daya attajiran da suka zabi Imhal a matsayin jarumin su suka zuba kudin su na caca
akansa sai jikinsu yayi sanyi, suka ayyana cewar asara tazo musu tunda gashi suna gani an
durfafoshi da gudu za a sare shi,amma ko motsi ya kasa yi,Koda ya rage bai fi taki uku ba kacal
Darwaz ya iso kan Imhal ba sai ya daka tsalle sama da nufin ya sare kan Imhal da makaman
dake hannun sa,wato takobi da adda, Kwatsam!ba zato ba tsammani sai Imhal yaji guguwar da
ta kanannadeshi ta sake shi ta bace bat!t take ya samu damar sunkuyawa ya kaucewa harin da
Darwaz ya kawo masa ,makaman Darwaz din suka sari iska, kafin Darwaz ya juyo da baya tuni
Imhal ya soka masa takobi a gadon baya, takobi ta burma gadon baya ta fito ta cikin sa ,Darwaz
ya kwarara ihu saboda tsananin zugin sukan da akayi masa ,sannan ya fado kasa yana
shure-shuren mutuwa, Ai kuwa sai attajiran da suka zabi Imhal a matsayin jarumin cacar su
suka kaure da ihu gami da shewar farin ciki, Gimbiya Shumaira kuwa bata San sanda ta daka
tsalle ba sama don murna ta kama kyalkyala dariya, amma tana hada ido da sarki taryan sai
taga ya kame, saboda tsananin mamaki da takaici, fuskarsa ta murtuke babu alamar annuri ko
kadan, Sarki gurzalu da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT kuwa, suma sai farin ciki ya lullube su suka
kama yiwa Imhal tafi. Sauran 'yan kallo kuwa kamewa suka yi kamar gumaka saboda tsananin
mamaki bisa ganin yadda aka gama dajarumi Darwaz farat!daya, duk da cewar babu kamar sa
a karfin damtse da karfin sihirin tsafi a garin,shi kuwa jarumi Imhal yayi matukar mamaki yadda
akayi ya tsira daga sharrin wannan guguwar tsafin, Haka ma sarki gurzalu yayi wannan
mamaki, kuma hankalin sa ya Tashi, ya fara tunanin cewa lallai akwai wani ma'abocin tsafi da
ya taimaki Imhal daga cikin'yankallo,don haka ya zama wajibi yayi bincike don ya gano ko
wanene, nan take ya ayyana a ransa cewar yana komawa turakar da aka sauke su zai daura
gurun tsafin sa don yayi binciken.Ana cikin wannan halin ne aka ga jarumi Imhal ya yanke jiki ya
fadi kasa,Koda ganin haka sai Gimbiya Shumaira ta yunkura za ta ruga izuwa cikin filin inda
Imhal yake, amma sai sarki taryan ya ruko hannun ta yana mai daka mata harara, take ta shiga
taitayinta ta sunkui da Kanta kasa cikin alamun kunya. ZAN CIGABA.
RIJIYA GABA DUBU 3 CIGABA 2
A wannan lokaci ne sarki taryan ya umarci likitansa yaje ya ceci rayuwar Imhal, a guje likita ya
isa filin gasar ya kama aikin sa na ceton rayuwar Imhal tare da dinke masa saran da Darwaz
yayi masa,nan take aka dauke gawar sadauki Darwaz Daga filin gasar sai sarki taryan ya ba
'yarsa Gimbiya Shumaira izuwa cikin gidan sarautar, Al'amarin da yasa filin gasar ya watse
kenan, kowa ya kama gaban sa,shi kuwa sarki gurzalu da Gimbiya LAMIRAT sai suka wuce
izuwa masaukin sarki gurzalu, shi kuwa jarumi Imhal bayan likita ya gama dinke raunin da ke
kirjin sa yasa masa magani sai aka dauke shi aka kai Shi izuwa cikin wannan daki mai kama da
kurkuku aka kulle shi.
Lokacin da sarki gurzalu suka isa cikin masaukinsu suka zauna, sai wata kuyanga ta kawo
musu ruwan inibi suka Sha,a lokacin da fuskar sarki ta cika da annuri yana ta farin ciki amma
sai yaga gimbiya lamirat tayi shiru tana mai sunkui da Kanta kasa cikin alamun damuwa,
Gurzalu ya dubi LAMIRAT yace, Yake 'yata,ina dalilin wannan damuwa taki? Koda jin wannan
sai lamirat ta kawo gwauron numfashi ta ajiye sannan ta dube shi cikin alamun tsananin
damuwa ta ce,Ya kai Abbana akan wane dalili kake farin ciki alhalin babban makiyin mune ya
samu nasara a wannan gasa? sabo dame kake son lallai kayi wannan gasa da jarumi Imhal
alhalin na gani da idanunka cewar shi mutum ne mai tsananin sa'a? shin baka tunanin cewa
kana neman kayi ganganci ne da rayuwarka akan jarumi Imhal? maimakon kai ceci rayuwar sa
kamata yayi kasa a kashe shi,ko a sirrance ne kai bani dama a daren Yau nayi baddakama naje
har dakin da aka kulleshi na kashe shi.Kafin lamirat ta gama rufe bakin ta tuni sarki gurzalu ya
daka mata tsawa har ta firgita taji hantar cikinta ta kada,ta Dan na da baya kadan Daga kusa
dashi, Koda yaga ta firgita sai ya bushe da dariya, sannan ya dubeta cikin nutsuwa da
murmushi yace,Haba yake 'yata, shin kin manta da ko ni waye ne? NINE FA MURUCIN KAN
DUTSE,WANDA BAN FITO BA SAI DA NA SHIRYA! NINE SA GUDU, MAGANIN KI GUDU!
KUMA NINE BAKIN TAKOBI MAI RABA MASOYA! Ina mai tabbatar miki da cewar na gama yin
bincike a cikin halwar tsafi na gano cewa idan har ba ta hanyar wannan gasar jarumtaka
ba,bazan samu damar hallaka shi ba,duk da cewar na gwada jarumtaka ta da tashi,naga karfin
mu yazo daya, ai yanzu zanyi amfani ne da karfin sihiri na,na hallaka shi a yayin da muke yin
wannan gasa,ni yanzu Abu daya ne ya shige min duhu, kuma ba komai bane na fuskanci cewar
akwai wanda ya taimaki Imhal da sihirin tsafi a Yau lokacin da ake wannan gasa,kuma bansan
ko waye ba, amma yanzun nan zan bincike na gane ko waye.Koda gama fadin hakan sai sarki
gurzalu ya mike tsaye ya shige cikin kuryar dakin da ya kwana inda akwatinsa ta ke,da Isarsa
gaban akwatin wacce ta kasance katuwar gaske mai nauyi, kuma wacce ke datse da katon
kwado,sai ya kurma uban ihu, Cikin firgita lamirat da dakarun sa dake can kofar turakar suka
rugo izuwa cikin dakin, A dimauce LAMIRAT ta dubeshi tace,Me ya faru ya kai Abbana kai
kurma uban ihu haka? maimakon ya bata amsar tambayarta sai ya juyo a fusace ya fuskanci
wadannan dakaru nasa masu tsaron dakin yace, Bayan mun tafi filin gasar JARUMTA waye ya
shigo cikin dakin nan? Shugaban Dakarun ya risina yace, Ya shugabana babu wanda ya shigo,
in baka manta ba kai da kanka na kulle dakin da mukulli da zaka fita ,kuma yanzu ma da kai
dawo kai ka bude shi da hannun ka... Kafin badakaren ya rufe bakinsa tuni Sarki gurzalu ya
sare takobinsa cikin bakin zafin nama ya fille masa kai, sai ga jini yana tsiri izuwa saman dakin
ta cikin jijiyoyin wuyan badakaren, sannan kuma sai gangar jikin ta fadi kasa rub da ciki,Faruwar
hakan ke da wuya sai ragowar dakarun suka firgita ainun suka dauke gawar dan'uwansu da
sauri suka fice da ita,A sannan ne sarki gurzalu ya dubi lamirat a lokacin da idanunsa suka kada
suka yi jawur yace,Wani yazo ya sace min gurun tsafina, maza ki tafi neman wannan barawo a
cikin garin nan,shine wanda ya taimaki Imhal a filin gasa. Da jin haka sai LAMIRAT ta juya da
sauri ta tafi izuwa can bangaren da turakar sarki taryan take domin ta sanar dashi abinda ya
faru kuma ta nemi izininsa akan tafiya cikin gari don farautar barawon mahaifinta.
to jama'a zan cigaba idan na huta.
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 3
Lokacin da sarki taryan ya tafi da Gimbiya Shumaira izuwa cikin turakarsa, bayan Angama
wannan gasar JARUMTA, sai ya tunkude ta ta fada kan wata doguwar kujera, ya dubeta cikin
fushi har muryarsa na rawa yace,akan me Zaki so jarumin da yake fada da nawa jarumin?sabo
dame Zaki nuna soyayyar ki a fili gaban jama'a ki zubar da kimarki da mutuncin gidan nan?Shin
kinsan irin makudan kudaden da nayi asara a wannan gasa bisa kudin da na zuba a cacar da
mukayi ni da sarki gurzalu? Lokacin da sarki taryan yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Shumaira
ta sunkui da Kanta kasa cikin biyayya tace,ka gafarceni ya kai Abbana, ka sani cewa a
rayuwata ban taba son wani da namiji ba a rayuwata ba face wannan bakon jarumi, kai da
kanka kayi mini tayin 'ya'yan sarakai guda ashirin da uku a wannan nahiya amma nace akai
kasuwa, idan baka manta ba na gaya maka cewar, bazan yi aure ba face na samu jarumi mai
tsananin sa'a da JARUMTA, kaga kuwa lallai babu wanda ya dace dani face wannan bakon
jarumi tunda gashi sa'arsa ta bayyana a fili, tunda gashi ya kashe jarumin da babu kamarsa,
alhalin a zahiri bai isa ya iya da shi ba.Yayin da sarki taryan ya ji wannan batu sai jikinsa yayi
sanyi, kuma hankalin sa ya dugunzuma yayi shiru ya kasa cewa komai, kwatsam! sai ga wani
babban hadimansa ya shigo cikin turakar sa,hadimin ya risina ga sarki taryan yace,ya
shugabana Gimbiya LAMIRAT 'yar sarki gurzalu tazo yanzu, tace tana son ganinka cikin
gaggawa, Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki taryan tare da Gimbiya Shumaira
suka dubi juna sannan ya dubi hadimin yace, he ka kace ta shigo,nan take hadimin ya fita sai
ga gimbiya LAMIRAT ta shigo fuskar ta a murtuke babu annuri, kai da gani kasan cewa tana
cikin tashin hankali, LAMIRAT ta risina ga sarki taryan tace,Ranka ya dade barawo ne ya shiga
cikin masaukin Abbana ya sace masa wani Abu mai darajar gaske.Koda jin wannan batu sai
mamaki ya turnuke sarki taryan da Gimbiya Shumaira, sarki taryan ya dubi lamirat yace, Tun da
aka gina gidan sarautar nan tsawon shekaru dari da goma Sha daya ba a taba yin sata ba a
cikin sa sai Yau,lallai ko wane ne yayi wannan sata ya cika hatsabibin gaske, domin nasan irin
tsaron da yake gidan nan yafi gaban misali, ko sarkin barayin aljanu yana shakkar yazo yayi
sata a nan, wai shin mene ne abinda aka satar muku? lallai zan sa a tsananta bincike har a
kamo wannan barawo, kuma ki gayawa mahaifin ki cewar komai kimar abinda aka sace masa
zan biya shi.lokacin da gimbiya lamirat taji wannan batu sai ta gyada kai cikin alamun takaici
tace,Inda zaka cika gidan sarautar nan taka da darhami, baza ka iya siyan abinda aka sacewa
ubana ba,ni yanzu abinda ya kawo ni gareka shine, ka bani izinin shiga cikin gari don farautar
wannan barawo, kuma ka bani dakarun ka wadanda za suyi mini rakiya, wadanda suka San
sirrin birnin ka sosai, in yaso kayi naka binciken daga baya, Koda jin wannan batu sai sarki
taryan ya sake kamuwa da tsananin mamaki, kuma hankalin sa ya dugunzuma ainun, nan take
ya tura aka kirawo masa wani badakare mai suna DARHUS, ya dubeta shi yace, maza ka debi
jama'arka mutum dubu uku Ku tafi tare da Gimbiya lamirat izuwa cikin gari, lallai ina son Ku
bincika gida-gida,lungu-lungu da duk wani sako da ke cikin garin nan domin Ku gano barawon
da yayi wa mahaifin ta sata har cikin masaukin da na bashi, kada Ku dawo gareni face kun
kamo wannan barawo, idan bakwa son Ku fuskanci fushi na.nan take DARHUS ya risina yace,
Angama, kawai sai ya juya da sauri ya fice daga cikin turakar, Gimbiya lamirat ta bishi da sauri.
A wannan rana dai sai da hankalin gaba daya mutanen birnin misra ya tashi, domin sama da
dakaru dubu arba'in DARHUS ya diba bisa jagorancin gimbiya LAMIRAT suka dinga shiga
gida-gida,unguwanni da kasuwanni suna dukan mutane suna caje kayayyakin su ana neman
abinda aka sacewa sarki gurzalu. Zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 4
Duk gidan da aka shiga sai an tarwatsa kayan ciki anyi filla-filla da su kin a duk Inda aka riski
bako tasa ta same shi domin anfi tsananta bincike a kansa saboda sai anfara yi masa dukan
tsiya anyi laga-laga da shi sannan ma za a fara tuhumarsa, Tun safe aka fara wannan bincike
amma har dare ya raba ba a ga abinda ake nema ba,kuma ba a ga wanda ya dauke abin
ba,Bisa dole su Gimbiya lamirat suka hakura suka koma gidan sarautar suka sanar da sarki
gurzalu da sarki taryan abinda