Showing 3001 words to 6000 words out of 10415 words
Chapter 2 - Rijiya Gaba Dubu Book 3 by Abdulaziz Sani Madakin Gini.pdf
ake ciki, nan fa hankalin sarakunan ya kuma dugunzuma fiye da
ko yaushe, musamman ma sarki gurzalu wanda ya tabbatar da cewar duk burinsa na duniya ya
rushe idan har ba a ga wannan Abu da aka sace masa ba,nan fa sarki taryan ya sake
dimaucewa bisa ganin yadda hankalin sarki gurzalu ya Tashi ainun, don haka sai ya sake baza
dakaru izuwa cikin birni da kauye kai har izuwa cikin dazuzzuka ma yace duk inda aka ga
wadansu baki a kamo su azo dasu Koda kuwa sun kasance fatake ne masu wucewa,haka kuwa
al'amarin ya kasance aka yi ta kamo baki ana kai su kurkuku ana kullewa, har sai da babban
kurkukun birnin ya cika fal sannan aka dinga kaiwa sauran kananan gidajen maza da ke wurare
da bam.A wannan dare dai sarki gurzalu bai yi bacci ba har gari ya waye bisa tsananin tashin
hankalin da yake ciki.
Ba wani abu aka sacewa sarki gurzalu ba face gurunsa na tsafi wanda shine kadai abinda ya
dogara da shi akan cewar yana bashi sa'a a gasar jarumtakar da akeyi a birnin misra tsawon
shekaru, abinda ya fi razana shi shine, yanzu yaya zai yi da batun shiga wannan gasa,ya sani
cewa saura wasa biyar ga jarumi Imhal su hadu a filin gasa su fafata, Koda yake dai yanzu
Imhal bashi da lafiya, dole ne yayi jinya ta tsawon Koda kwana bakwai ne,kuma ya San cewa ko
babu wannan gurun tsafi a tare dashi ba ya shakkar karo da Imhal domin Idan har bai samu
nasarar kashe shi ba sai dai ayi RAGAS indai da zallan karfin damtse da kwarewar yaki za suyi
fadan, babban abin tashin hankali shine, barawon da ya sace gurun tsafin sa ba karamin sihirin
tsafi ne da shi ba tunda har ya iya shiga har cikin masaukinsa ya sace gurun ba tare da asirin
sa ya tonu ba kuma tabbas zai cigaba da taimakon Imhal a cikin wannan gasar jarumtaka da
ake yi har ya kai ga nasara.
Abinda ya fadowa sarki gurzalu a rai shine, yana da zabi guda biyu rak! Ko dai ya koma can
birnin Kisra ya shiga halwar tsafin sa yayi bincike don ya gano ko waye wannan barawo da
kuma inda yake kafin a cigaba da gasar JARUMTA, ko kuma duk yadda za ayi ya gano
barawon kafin gasar tazo kansa,nan fa sarki gurzalu ya rasa hukuncin da ya kamata ya yanke,
Babu yadda sarki taryan bai yi ba don ya San abinda aka sacewa sarki gurzalu amma abun ya
gagara, domin yaki ya gaya masa,Dama ya dameshi da tambaya sai yace dashi, Abinda aka
sace mini yafi komai da kowa daraja a idanu naka wannan duniya, tunda sarki taryan yaji
wannan batu sai yayi shiru bai kara yi masa magana ba.kashe gari kuwa tun kafin hasken rana
ya fito su Gimbiya lamirat suka sake bazama izuwa cikin gari neman barawon sarki gurzalu.
Al'amarin Gimbiya Shumaira kuwa,a wannan rana sai ts rasa sukuni, domin ta kasa zaune ko
tsaye, kuma ta kasa yin bacci, ba komai ne ya janyo hakan ba face duk sanda ta runtse
idanunta bata ganin komai face jarumi Imhal, nan take taji tunani da begensa sun addabe ta
kuma taji bata da sauran kwanciyar hankali idan bata je ta gan shi ba,domin gani take kamar
mutuwa zai yi sakamakon wannan Sara da jarumi Darwaz yayi masa a kirji, nan fa Shumaira ts
fara tunanin hanyar da zata ni taje ta ga jarumi Imhal a can inda aka tsareshi, Samun wannan
dama kuwa ba karamin aiki bane saboda babu wanda yake da ikon zuwa wannan wuri face
sarakunan biyu wato sarki taryan da sarki gurzalu domin dokar da aka kafa kenan tun jiya da
aka kai Imhal aka tsare, Koda Shumaira taga tunanin yayi mata yawa ta kasa komai sai ta fito
daga cikin turakar ta,A wannan lokaci da ko wanka ba tayi ba,kuma tana sanye ne da rigar
bacci wacce ke nuna dukkan siffofin jikinta, kawai sai ta kama kai kawo a cikin harabar turakar
ta ta inda kuyanginta ke ta kai kawo suna yi mata aiyuka iri-iri, kwatsam! sai ta hango wata
kuyanga ta taho za ta gifta ta gabanta,tana kallon fuskar kuyangar sai ta ga ai bakuwa ce domin
bata taba ganin fuskarta ba.Al'amarin da yai matukar bata mamaki kenan domin babu yadda
za'ayi a kawo bakuwar kuyanga cikin turakarta ba tare da an sanar da ita ba,Har kuyangar ta
gifta ta zata wuce sai Shumaira ta Sha gabanta da sauri suka dubi juna,tsawon 'yana dakiku
sannan Shumaira tace, Wacece ke kuma yaushe aka kawoki nan,muhallina ba tare da sani na
ba?Koda jin wannan batu sai kuyangar tayi murmushi cikin alamun takama da yarda da kai
tace,Ni ba kuyangar ki bace hanya ce ta biyo dani ta nan,bani hanya na wuce abina idan ba so
kike ranki ya baci ba, Koda jin wannan batu sai ran Gimbiya Shumaira ya baci bisa ganin cewa
tana matsayin'yar sarki amma kuyanga tayi mata rashin kunya, kawai sai ta daga hannu da
nufin ta sharawa kuyangar mari,amma sai taji hannun nata ya makale a sama ta kasa sarrafa
shi,kuma taji an matse hannun nata,wani irin mugun zugi da radadi na shigarta bata San sanda
ta fara ihu ba,Abinda ya daure mata kai shine,duk ihun da take yi babu mai jinya,asalima babu
wanda yaga abinda ke faruwa, nan take tsoro ya kama Gimbiya Shumaira ta fara tunanin
cewa,lallai wannan kuyanga da ke gabanta ba mutum bace aljanna ce.
zan cigaba.
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 5
Koda ta ayyana hakan a cikin zuciyar ta sai ta dubi bakuwar kuyangar cikin tsananin dauriya
tace,Ki gafarceni banyi dai-dai ba,kafin ta gama rufe bakinta sai taji an saki hannun ta kuma ta
daina jin zafin komai, kawai sai ta sake duban kuyangar tace,"Ya ya akayi kika sami damar
shigowa gidan nan ,alhalin babu wani aljani da ya taba shigowa tun farkon gina shi? " sanda
bakuwar kuyangar taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace,Ni ba aljana bace, mutum ce ni
kamar ke,idan har kina so kisan ko ni Wacece ki kaini cikin turakar ki mu zauna muyi wata
magana, bayan hakan ne za kisan ko ni wace ce kuma zan taimaka miki na kaiki har inda aka
tsare bakon jarumi ki ganshi ba tare da kin fuskanci wata matsala ba,Koda jin wannan batu sai
murna ta kama Shumaira nan take ta kama hannun kuyangar ta ka ta izuwa can cikin turakar
ta,da shigarsu cikin kuryar dakin kuyangar ta zauna tana mai yin hamma alamar cewa tana jin
yunwa da bacci, har Shumaira ta budi baki za tayi magana sai ta dakatar da ita da hannu
tace,Kafin muyi maganar komai sai naci na koshi, maza kisa a kawo min abin kalaci,Koda jin
haka sai gimbiya Shumaira ta kwalawa wata kuyangarta kira tace da ita,taje ta kawo mata abin
kalaci,Koda jin wannan umarni sai mamaki ya kama kuyangar mai suna SALIFAT, Salifat ta
sunkui da kai kasa tace,"ya shugabata me za kiyi da abincin kalaci yanzu alhalin dazu na kawo
miki kika ce bakya bukatar?" Shumaira ta dakawa Salifat tsawa tace,"Ina ruwan ki,yanzu nake
bukatar cin abincin, maza kije ki dauko mini kafin raina ya baci".Cikin hanzari kuyangar ta juya
da sauri ta je ta dauko abincin bisa faranti a cikin manyan kwanuka guda biyu na dinare,
kuyanga Salifat tazo ta ajiye farantin a gaban bakuwar kuyangar amma kuma ba ta ganta
ba,bata ma San cewa akwai wani mutum a cikin dakin ba face Gimbiya kadai,Koda kuyangar ta
ji kamshin abinci ya doki hancinta sai ta fado kasa Daga kan kujera ta bude kwanukan abincin
ta duma hannu a ciki ta kama ci kamar wacce ta shekara da yunwa, kafin a jima ta cinye kusan
rabin abincin dake cikin kwanukan biyu wanda a ka'ida mutum shida ne ke iya cinye shi,tana
gamawa ta dauki tambulan din ruwan ta shanye shi tas ya zama ko digo daya bata rage ba
sannan tayi wata katuwar gyatsa,kai da gani kasan cewa bata saba cin abinci mai daraja ba irin
wannan, A sannan ne bakuwar kuyanga ta mike tsaye ta koma kan kujerar ta zauna sannan ta
fuskanci Gimbiya Shumaira ta dubeta cikin nutsuwa tace,"sunana MUZAIRA, kuma ni 'yar uwar
matar sarkin Kisra ce na da,wanda sarkin yanzu ya kashe ya hau karagar mulkinsa. "Koda jin
wanne batu sai Shumaira ta mike tsaye zumbur! cikin alamun tsoro da mamaki, kuma jikinta ya
kama tsuma tana mai nuna MUZAIRA da dan yatsa bakinta na rawa tana so tace wani abu
amma sai ta kasa,Koda ganin haka sai MUZAIRA tayi murmushi tace," kwantar da hankalin ki
ya ke Gimbiya Shumaira, ban zo nan dan cutar da ke ba,sai domin na taimake ki kamar yadda
nayi alkawari,kuma kema ki taimake ni,wannan bakon jarumi da kika kamu da son sa wato
jarumi Imhal da ne a waje na,domin MAHAIFIYARSA yayata ce,uwar daya uba daya,kuma na
biyo shi ne izuwa birnin misra domin na ceci rayuwar sa a cikin GASAR JARUMTAKAR da ake
yi,Tabbas a dazu sanda ya fafata da sadauki Darwaz, in ba don na kawo masa dauki ba da tuni
Darwaz ya hallaka shi da karfin sihiri, inda kin lura za kiga cewar jarumi Imhal ya tsaya cak a
waje daya sanda Darwaz ya rugo da gudu izuwa kansa a wannan lokaci wata guguwar sihiri ya
jefo masa ta kanannadeshi ya kasa Koda motsa hannayensa,nice na kawar masa da guguwar a
lokacin da saura kiris Darwaz ya gama dashi.
Yanzu zan gaya miki wani babban sirri wanda ba ki San shi ba,kuma labarin zai girgiza
kwakwalwarki, da farko dai nice barauniyar da ake ta nema a cikin garin nan da kewayensa
wacce tayi wa sarki gurzalu sata, kuma ba wani abu na sace masa ba face wani GURU na
TSAFI indai yana tare da wannan grun tsafi babu wani mahaluki da ya isa ya samu nasara a
kansa,ko ya iya cutar dashi, yanzu gashi Gurun ya dawo hannu na, koda MUZAIRA tazo nan a
zancen ta sai ta yaye rigar da ke jikinta, take Shumaira tayi arba da gurun tsafin zagaye a
kugun MUZAIRA, MUZAIRA ta saki rigar ta rufe gurun sannan ta cigaba da cewa, Albarkacin
wannan guru ne na samu damar shigowa gidan nan ba tare da kowa ya ganni ba,kuma abinda
sarki gurzalu bai sani ba shine, tun kafin su shigo cikin garin nan na sace gurun a wani lokaci da
suka ya da zango a cikin daji ya fita daga cikin tantinsa yaje yayi wanka a wani rafi.
zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 6
Dama ina biye dasu tun daga can birnin kisra a cikin siffar wata tsuntsuwa basu sani ba,A
lokacin na shiga cikin tantin nasa,kuma nayi sa'a na iske akwatinsa a bude, ya manta bai kulle
ta ba bayan ya dauki mayafin da zai tsane ruwan jikinsa bayan yayi wankan, Bai taba mancewa
da kulle wannan akwati ba sai a wannan lokaci, don haka bayan na sace gurun tsafin sai na
datse kwadon akwatin ,shi kuwa dan mabudin kwadon akwatin dama ko da yaushe yana jikin
mazagin wandonsa.
Lokacin da ya dawo cikin tantin nasa ya iske akwatinsa a rufe bai iya tunawa cewa a bude ya
barta ba,Bayan na mallaki gurun tsafin ne jiya na shiga har cikin turakarsa na bude akwatin da
karfin sihiri, kuma na barta a bude domin nasa shi zargi cewa a nan ne aka sace Gurun.
Yanzu zan baki labarin abinda yasa na sace wannan Guru.
Nan take Zumaira ta bawa labarin duk yanda akayi aka yanka mahaifiyar Imhal aka kaita daji
aka yar ana zaton ta mutu har tsoho imzanu ya ganta ya ceci rayuwar ta kuma ta cigaba da
rayuwa a cikin hauka har izuwa sanda ta haifi jarumi Imhal, a karshe ta mutu ta barshi a hannun
tsoho imzanu ya cigaba da rainonsa har ya girma, kawo izuwa sanda sarki Gurzalu ya tura a
kashe tsoho imzanu a kamo Imhal har izuwa cikin gari inda suka fada cikin gidan ta ta taimake
su.
Koda MUZAIRA tazo dai-dai nan a labarin ta,sai taga hawaye na zuba a idanun Shumaira
sakamakon tsananin tausayi da ta ji bisa jin tarihin rayuwar Imhal da yadda aka yiwa iyayensa
kisan gillah, Nan take Shumaira taji ta tsani sarki gurzalu don jin mugun zaluncinsa, kuma ta
kudurce a ranta cewar lallai sai ta raba alakar dake tsakaninsa da mahaifinta sarki taryan, Koda
Zumaira taga Shumaira na kuka,sai itama zuciyar ta ta karaya ta fashe da kukan aka rasa
wanda zai rarrashi wani har izuwa tsawon 'yan dakiku sai daga can Shumaira ta nutsu ta daina
kuka ta dago kai ta dubeta tace,Yanzu wane irin taimako kike so nayi miki? Koda jin wannan
tambaya sai Zumaira ta nutsu tace,Ba wani taimako nake so kiyi mini ba face ki ajiye duk
abinda na fada miki sirri a cikin zuciyar ki har izuwa ranar gasar Imhal ta karshe, wato ranar da
zai fafata da sarki gurzalu domin idan kika gayawa Imhal cewar sarki gurzalu ne ya kashe
iyayensa ya hau karagar mulkin a yanzu duk shirin mu ya watse baza mu iya daukar fansa ba
akan sarki gurzalu, domin Imhal zai hau kace ne yace yanzu-yanzu zai dauki fansa,kinga kuwa
ba zai iya ba,tunda sarkin yawa yafi sarkin karfi,karfi.
Inda dai ace nasan sirrin yadda ake amfani da wannan gurun sihirin ne na sarki gurzalu da nayi
amfani dashi wajen hallaka shi, abinda zan iya yi yanzu kawai shine, nacigaba da boye wannan
gurun tsafi a waje na har izuwa ranar da zasu fafata shi da Imhal ya zamana cewa ta kowane
hali bai bar hannuna ba,domin indai gurzalu baya tare da gurun tsafin, bazai iya samun nasara
ba akan Imhal,sirri daya na sani na amfani da wannan gurun, wato sirrin bata,duk wanda yake
tare da wannan gurun da wanda ke tare dashi ba a ganinsu, kuma ba a jin muryarsu Koda kuwa
za suyi ta tsandara ihu, su kwana suna yi,yanzu sai ki tashi kiyi mini jagora izuwa inda aka tsare
Imhal domin na ganshi ko ma samu 'yar nutsuwa, amma baza muyi masa magana ba ,don ko
munyi ma bazai ji ba ,ba tare da gardamar komai ba Shumaira ta mike tsaye ta kama Zumaira
ta ka ta suka fice daga cikin gidan sarautar suna ta ratsawa ta cikin lunguna da sakuna, suna
tafe suna hira abin su,kuma gashi duk inda suka ratsa akwai dakaru a tsaitsaye suna rangadi
amma babu mai ikon ganinsu ko jin muryarsu, duk inda suka je kuma suka iske kofa a rufe basa
bukatar su bude sai dai kaga sun ratsa ta cikin karfen kofar sun wuce, tamkar yadda danshi ke
tsatstsafowa daga cikin kasa,Albarkacin wannan gurun tsafin dake daure a kugun MUZAIRA
hakan ke faruwa, A haka dai suka iso kofar dakin da aka sa jarumi Imhal a ciki. da yake kofar
dakin anyi tane da sandunan karfe sai suka ganshi kwance a kasan dakin ko shimfida babu
yana ta faman shara baccin wuya, Koda suka ga halin da yake ciki ,kuma suka ga katon raunin
dake kan kirjin sa sai suka fashe da kuka, Tabbas duk wanda ya dubi Imhal a wannan yanayin
da yake dole ne ya tausaya masa domin numfashinsa ma yana fita ne da sauri-sauri kamar ba
zai rayu ba,sai da suka dade a tsugune a wajen suna kallon sa sannan MUZAIRA ta zura Kanta
ta cikin sandunan kofar da hannun ta guda ta shafa kan Imhal, a lokacin da hawayen idanun ta
ya zubo akan kumatunsa, shafa kan nasa ke da wuya ya farka daga bacci, Koda ya ji danshi a
kumatunsa sai ya shafo shi ya duba, Koda ya fahimci cewar ba ruwa bane,hawaye ne,sai ya
mike tsaye zumbur! ya kama waige-waige amma bai ga kowa ba,A lokacin ne Shumaira tayi
sauri ta kama hannun MUZAIRA ta janye ta suka bar wajen.
zan cigaba.
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 7
Nan take Imhal yaji a jikin sa cewar lallai wata ce tazo wajen sa har tayi kuka hawayen ta ya
zuba akan kumatunsa, Amma abin tambayar shine,Shin Wacece wannan mai zubar da hawaye
saboda tausayinsa? Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan, shi dai a sanin sa bashi da kowa a
wannan duniya wacce zata zubar da hawayen ta saboda tausayinsa, nan dai jarumi Imhal ya
fada kogin tunani inda ya tuno da abokin sa MARIGAYI ZAUWADU kuma ya tuno da wasiyyar
da ya bar masa sanda ya bashi wata sarka yace dashi, lallai komai dadewa yaje unguwar
sharkas a cikin birnin kisra ya nemi masoyiyarsa SUHAILA ya bata wannan sarka, kuma ya bata
labarin rayuwar su a cikin kurkuku har izuwa lokacin da ajali ya riske shi,Koda yazo nan a
tunaninsa sai hawaye ya zubo masa yaji yana fatan ya rayu ya sake kubuta Daga sharrin sarki
gurzalu domin yaje ya sauke wannan alkawari da ya daukarwa abokinsa Zauwadu.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin Gimbiya Shumaira da Zumaira kanwar mahaifiyar jarumi
Imhal wacce itama take da burin daukar fansa akan sarki gurzalu.
Al'amarin sarki gurzalu kuwa, lokacin da su Gimbiya LAMIRAT suka sake shafe wuni guda suna
neman barawon sa a cikin birni da kauye suka dawo babu nasara, sai sarki gurzalu ya zama
kamar mahaukaci ya dinga buge-buge da iface-iface, da kyar!LAMIRAT ta shawo kansa ya
dawo hayyacinsa, sannan ta dube shi tace,Ya kai Abbana yanzu mene ne dalilin da ya hana ka
tashi na garzaya izuwa can birnin kisra domin kar shiga dakin halwar tsafin ka ka binciko wanda
ya sace maka gurun nan?Koda jin wannan tambaya sai sarki gurzalu yayi aniyar zuciya yace,
Abinda yasa naki komawa birnin kisra shine tunda nake zuwa wannan gasa tsawon shekaru
talatin baya ban taba komawa gida ba a lokacin da aka gasar ba,idan na koma mutane za su
iya cewa na tsorata ne da abokin gwamina ko kuma na karaya na koma gida don nayi sabon
shiri, kinga kenan yanzu duk zabi biyun da nake dasu akan matakin da ya kamata na dauka duk
sun rushe, muna ji muna gani kenan makiyanmu za su iya samun nasara akan mu.
Koda jin haka sai lamirat ta gyada kai tace, Haba ya kai Abbana, hanyar kashe