Showing 24001 words to 27000 words out of 46889 words
Chapter 9 - KAWAR ZUCIYA PART 1 BY TAKORI KABARA.pdf
zafi, sannan
tace in ta warke kuma sai harka ta balle a
koma soyayya, nan ta shiga koya mata
salo-salo na shimfida da sauransu
baro-baro.
A matsayin ta na karamar uwarta mai
shirin kaita dakin miji, Anti Dije da
karambani irin nata taga ya kamata ta
koyar da diyar tata duk wannan. Kada ta
barta a dukunkune taje ta rasa yadda zata
yi. Don ta tabbata Safiyya banda text books
dinta na Architecture bata karanta littafan
soyayya koda na turanci ne. Kuma ta san
Ammi bazata taba yin irin wannan hirar da
itaba.
Amma ga Safiyyah diyar Ammi da Anti
Dije, maimakon hakan yayi amfanin da ake
zato, wato ya zama karin ilmi a gareta da
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
wayar da kai, sai ya zama akasin haka, duk
Aunty Dije ta hargitsa mata tunani akan
aure. Ta koma anticipating ranar first night
dinta shine kwatankwacin ranar
mutuwarta. Domin daga hudubobin Anti Dije
Safiyya ta fahimci ai wata sabuwar rayuwar
ce ke jiranta daban da wadda suke yi da
Zayyan kafin aure, Anti Dije ta yi instilling
tsoro mai yawa a Safiyyah, don sai ta kai ta
kawo ko cewa akayi Zayyan ya zo sai
gabanta ya yanke ya fadi, sai kuma taji
bacin rai wanda har a fuskarta sai ya nuna.
Tayi ta tambayar kanta ta yaya ma
za’ayi ace abubuwan da Aunty Dije ke fadi
zasu faru tsakaninta da abokinta Zayyan, ai
akwai kunya, kasancewar hirar soyayya da
kauna data karatu ce blah… blah… kawai
tafi gudana a tsakaninsu (very pure gist)
koyaushe Zayyan bai taba wuce limit dinsa
ba.
A takaice Aunty Dije ta gama nuna
mata cikin rashin hikimar zance akwai
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
muhimmin abinda ke jiranta duk ranar
data tare daga salihin mijinta dan mutanen
Rafindadi, wanda take yiwa kallon aboki,
masoyi, amini. Bayan daurin auren har
wasu magunguna ta soma bata masu dadin
ci na “Bojuwa Herbals” wato kayan gyaran
auren nan na musamman na kawarta
(Aunty Surayyah Halin Yau 08032773332)
tace rayuwa ce zasu fara wadda sai an kai
zuciya nesa, saboda nauyinta. Tace mata
wannan shine zahirin auren hakikaninsa,
asalin abinda ya saka mata tsoron tarewar
gabadaya.
Duk da Zayyan bai taba nuna mata
wani abu daban mai nuna hakan ba, tun
kafin ayi auren da bayan an daura shi,
bayan an daura ma rage zuwa yayi, amma
Anti Dije tasa mata tsorata dashi sosai
kamar mala’ikan da ke jiran ta shiga
gidansa ya dau ranta, da take gaya mata
abubuwa kuru-kuru, abinda Ammi bata
taba zama ta gaya mata ba, saboda kunya
da fulatanci irin na iyayen da, kuma ita bata
kawaye bata kuma karance-karancennan
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
na zamani da ire-irensu. Antin nata Dije
tayi mata (sensitization) ne na kai tsaye (ba
cikin hikima ba).
Kamar ace Anti Dije irin matan nan ne
masu barin zance da rashin sakaya shi cikin
hikimar harshe, har cewa take da Safiyyah
idan ta nuna bata son hirar.
“To nifa ban gane ba Safifin Ammi,
wai kina nufin shi Zayyan din bai taba nuna
miki yana bukatar komai daga gareki bane
tun daurin aurennan ko yaya ne?
To idan yazo Dandumen haka kuke
wuni baya komai a gabanki sai zuba zance
kamar lalataccen famfon I love you na fatar
baki?
Safiyyah ta dukunkuna fuska tace
“Anti meyasa kike min haka ne? ni Zayyan
bai taba yimin irin wadannan zantukan na
rashin kunya da kike min ba”. Anti Dije ta
kai mata dundu tace “nice mara kunyar? To
ko dai baida lafiya? Koda yake fa irin shi in
sun samu wuri, sun fi kowa jarabar
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
matansu, tunda Ustazi ne, to ke wai kin
dauka in kun tare ma haka zaku cigaba da
zama cikin ustazancin kamar wasu
muharraman juna ko yaya? Da zaki ce ina
miki rashin kunya, ko ba kya son lectures
din da nake miki hakkina ne in miki”. Ko tace cikin jimami “Allah Sarki
diyata Safifi, duk wannna hirar soyayyar da
ake sha a waya (is different) fa da irin
abinda nake gaya miki, duk da na fahimci
kamar Zayyan din baya da rawar kai irin
na angwayen zamani, amma zaki ce na gaya
miki irin shi sun fi kowa fitina da an shiga
gidajensu.”.
Hakan kullum kara ruda Safiyyah
yake yi duk duk tabi ta tsorace, ta kidima
kanta da auren bakidaya, don Anti Dije ta
sakata a kwana, ta jefata a tsoron masoyinta
yanzu, ya zama last person data ke son jin
sallamarsa gidansu. Da tunanin Zayyan zai canza daga
yadda ta sanshi zuwa marar ta ido, da zarar
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
ta saka kafarta a gidan shi kullum take
kwana take tashi.
Safiyyah dai irin ‘yammatannan ne
kifin rijiya, ko kawaye bata dasu, watakila
shiyasa ko kwalliya bata iya ba, gata dai a
jami’a, amma bata deviating daga abinda
ya kaita, kamar bata san wasu ‘yammata na
existing a jami’ar ba. Kannenta su Sabah ne
manyan kawayenta, sai ko Anti Dije da ta
maye mata gurbin uwar daki kuma
karamar Goggonta, 'yan ajinsu tsakaninta
dasu gaisuwar mutunci ba wata hira
makamanciyar wannan irin ta sa’o’In juna,
ita Anti Dije a wurinta abin kirki take yi,
bata san ta saka mata shakku da wani
bahagon tunani na daban ba, a kan cewa
Zayyan zai canza daga nunkufurcin sa na
ustazi zuwa devilish duk ranar data tare.
Sai ta cewa kanta ashe auren ana yinsa
ne don wata manufa, tarewarta kuma na
nufin a zubar mata da kunyarta ta diya
mace, to bazata je ba.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Har ila yau Anti Dije ta nuna mata
kamar taci wani bashi ne nasa a kanta, da
zata biya koda tsiya koda arziki da zarar ta
tare din.
Bawan Allah Zayyan yana can ABU
yana fama da akalami bai san da aika-aikar
da Anti Dije ta gama yi masa ba, bai san ta
gama jika masa garinsa ba, ta hanyar yiwa
amaryarsa famfon ilmi da wankin kai ba. Ya kammala project ya mika. Duk da
haka bai koma Katsina ba yana Zarian
yanata shirye-shiryensa na tarewar Sahibah
Sophie, bai fasa ba, sayo wannan yau sayo
wancan gobe yana kara kawata dan gidan
nasu, duk don tanadin zuwan Safiyyah. Mama da kanta take tambayar Zayyan
ya taji shiru, sai yaushe ne Safiyyar tasa
“fi-sauran mata” zata tare ne???
Rasa mai zai gayawa Mama yayi,
sabida ya biyewa son ran Safiyyah da yawa,
shi kansa ya rasa inda Safiyya tasa gaba
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
akan batun tarewarta. Yau tace ciwo, gobe
tace jarrabawa. Kuma duk tayi su ta gama.
Don haka a karshen wannan makon da
yazo Dandume, aka yi masa masauki a inda
suka saba zama wato dakin bakin Malam
na soron gidansu Safiyyah.
Safiyya ta fito ta sha Jilbab dinta
kamar ba amarya ba, kai shi hijab dinnan
fa ya fara daina burgeshi yanzu, ta
tsugunna da murmushi a gabanshi tana
zuba masa ruwan randar Ammi mai sanyi
data debo a jug a tambulan mai garai-garai. Tace "wai fa daga Zaria kazo ko?
Sannu kaji! Ka sha hanya".
Ya dubeta da kasan idanu rabin jikinsa
kwance cikin kujera one seater guda daya
dake dakin, sonta da kaunarta kullum
karuwa suke yi a ransa, musamman saboda
yawan kunyarta dinnan da har gobe taki
barinta, da kalamanta na hankali cikin
in’ina, sannan da hankalinta irinna
tarbiyyar tsoffi, daga Malam har Ammi sun
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
manyanta sosai kuma tarbiyyar manya suke
yiwa ‘ya’yansu, shiyasa kullum ya ganta
gabansa tana masa magana cikin in’inarta
da taushin murya sonta da kaunarta
karuwa suke a ransa su ninka na baya. Komai Safiyyah tayi na manyancennan
nata burgeshi take yi, amma yau jilbab da
hijabs din sun fara gimsarshi. Fisabililllahi
ace wai har bayan daurin aure matarsa ba
zai ganta cikin kwalliya ba??? Yau sai ya hade giran sama dana kasa
ya fito mata a Mr. Zayyan dinsa sak, namiji
irin kowanne, yace cikin dakewa da shanye
shakkarta, wanda kwarjininta ke sabbaba
masa a kullum har yaji ba kowanne irin
zance zai iya dosarta dashi ba. Amma yanzu fa?
Ya hadiye miyau yana kallon pinky lips
dinta da kullum suke bashi sha’awa. Yace.
“Sophie, yau daya dai a ajiye Hijab
dinnan a gabana mana, in ga “Hijabie” dita
a zahiri babu Hijabin?”
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ta yi maza ta kalle shi da mamaki, sai
ya lumshe mata ido yace cikin kwantar da
murya. “ina nufin don ki sha iska. Dubi fa
yadda yake faman saka ki zufa har a goshi,
to ina ga cikin jikinki? Duk da fankar nan
dake faman filfilwa Safiyyah gumi kikeyi?
Shi Hijabin na dauka na fita ne kawai
amma banda a cikin gida a gaban miji?".
Taji kunya da murmushi sun kamata a
lokaci guda. Ranar farko kenan da ya taba
cewa yanaso ya ganta babu hijabi, ya kuma
hada da kiranta da suna ‘Sophie’ duk don
ya tausasawa yardarta, sai taji sunan yayi
mata dadi yau fiyeda sanda ya fara fade,
saboda ba wanda ya taba kiranta da
‘Sophie’ din ta wannan sigar ta lallashi da
Zayyan ya furta yau, very loving and so
romantic daga zuciya har bakinsa, hakan
yasa Safiyyah jin kanta yayi girma, irin na
macen da miji ke lallashi kan tayi masa abu,
taji kamar sunannan da Zayyan ya lanqaya
mata yanzu, yafi na kowacce mace dadin
furtawa (Sophie).
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Duk da haka Safiyyah sai ta turo baki
gaba, sannan a shagwabe ta dubeshi cikin
marairaicewa “ai ni sam ban saba cirewa
ba, sai in a dakina nake kona Ammi.
Saboda inna cire hijab ko a gaban mata
'yan uwana nake, sai in jini kamar tsirara”. Zayyan yace a ransa “tabdijam! Akwai
aiki ja, a gabana ashe”, kafin ya samu abin
cewa Safiyyah ta kara da cewa cikin irin
zancen zucinnan da ya fito fili “kwatakwata
ni in ba a cikin gidanmu bane, a dakina
kona Ammi, bana iya cirewa. To balle kuma
a gaban katon namiji kamarka".
Abin ya bashi dariya sosai amma ya
gintse ya shanyeta yayi fuska, ya dan zamo
daga cikin kujerar da yake kwance, ya riko
hannunta dake zuba ruwa a tambulan bata
san sanda ta saki kofin ba ruwan ya bare,
jikinta ya hau rawa, Zayyan bai damu da
reaction dinta ba ya kura mata ido, so
inviting... tuni Safiyyah ta hau barin jiki,
bai damu ba ya ce a tausashe.
“Sophie, nine katon namijin???
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ni ko???”
Ya fada yana nuna kansa da dan
alinsa. Idanunsa na neman nata. Ta ji wata
irin kunya ta kamata, ta rufe ido da hannu
dayan da bai kama ba tana cewa “to da
menene? Ai kayi biyuna a girma da tsayi,
you are a giant!". Zayyan ya murmusa cikin kallonta,
Mama na yawan cewa shi kato ne amma
yau na Safiyyah yasa ya ji mazantaka ta
karu masa sosai, a hankali ya sakar mata
hannu, a sanyaye yaja baya ya koma cikin
kujerarsa sosai, ya soma kokawa da
emotions. Sai kawai zancen zucinsa ya fito
fili a lokacin.
“Baza ki san ni katon bane sai ranar
da kika bar gaban Mallam zuwa nawa
gidan. Idan na tube a gabanki kika ga
girman kwanjina da kaurin ‘muscles’ dina.
Daga ranar wannan hijabin na
Safiyyah da acan baya yake burgeni ya
daina burgeni kenan, sai dai ‘lingerie’ da
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
‘yan ‘nude nighties’ kawai nake son gani a
jikinki Sophie!".
Ya kare zancensa da wani irin lumshe
idanu kamar mai hasaso ranar kasancewar
hakan. Safiyya ta zaro ido tana dubansa a
tsorace, sannan ta bude baki, nan ya gane ta
ji zancen zucinsa. Sai ya fashe da dariyar
basarwa, ya yunkura ya tashi zaune sosai ya
dubeta cikin ido yace.
“Sophie kenan, to wai ke in tambayeki
mana? Me kike nufi damu ne?
Nufinki a haka zamu dauwama? Ai
hakan ba mai yiyuwa bane a rayuwar zahiri
tunda muma ‘yan adam ne.
In kuma a haka kike nufin zamu cigaba
da rayuwa har zuwa yanzu, rayuwa irinta
wa da kanwa, sai ince you are totally
mistaken.
Maganar gaskiya kawaici na ya fara
karewa akan mara tausayin amaryar nan
tawa Safiyyah.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Nima fa mutum ne, kuma in gaya miki
mai cikar lafiya mai bukatar kulawar
matarsa kamar kowanne namiji, amma ni
sai zabga min kebura ake cikin ruwan
sanyi. Kafin muyi aure ne nake saurayinki,
wanda bashi da kowanne hakki a kanki,
mai iyaka dake a cikin mu’amala, amma
yanzu Zayyanu ne mijin Safiyyahtu, Baban
yaranta masu zuwa nan gaba kadan in sha
Allah, kinji ko Sophie, don haka ki saki
jikinki dani haka, Allah ya halatta min in
ganki babu Hijabin. In kuma taba duk inda
nake so a jikinki don hutu jin dadi na.
So yau daya dai, daure ki cire min shi
in samu inga halittar matata Safiyyah babu
Hijabi, ko in taso yanzunnan in cire miki shi
da kaina”.
Safiyyah ta sunkuyar da kai cikin jin
nauyi da kunya da wani irin abu da ya soma
yanyame ruhin jikinta, Zayyan yace
“kinsan har suna nasaka miki kuwa a wajen
Mama, I used to call you ‘Hijabie’, duk
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
sanda na ce Hijabie Mama ta san ke nake
nufi, because these hijabs are your main
characters dana fara ankarewa dasu a tare
dake, kuma shine babban abinda ya fara
fizgata zuwa gareki bayan in’inar. Amma
daga yau su koma na fita school don Allah". Kunya sosai ta kama Safiyyah, haka ya
ci gaba da kasheta da zance yau mai narka
zuciyar mace yasa tayi laushi, har mamaki
take wai Zayyan ne, sai murmushi take tana
rufe ido in ya fadi wani abun mai nauyi, da
ya matsa da son ta cire hijabin sai ta hau
buga kafa a kasa cikin tabara tana cewa
cikin shagwaba da rigima.
“ni dai bazan iya cirewa ba, ka barni
da abina, bana so, kana bani kunya
Zayyan…”.
Zayyan wanda a lokacin duk ta kara
rikita shi da wannan salon shagwabar da
bai taba gani a tareda Safiyyah ba, har dasu
shura kafa irin na rigimammun yara, ba
shiri yace ya hakura, domin ta tabo wani
irin feeling da bai taba ji ba a kasan ransa,
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
ya daga mata hanauwansa sama cikin
saddaqarwa da bada kai, yana dariya yana
cewa “nayi saranda Sophie! Na yarda ni
Zayyan mijin Ustaziyyah ne, to yaya zanyi
da ustaziyya ta? Daina borin haka kinji! Na
hakura na bar miki abinki, ince ko shikenan
zance ya kare?".
Ita kanta Safiyyah sai da ya bata
dariya, yadda ya biye mata hadda saranda.
Ta lura da yadda jikin sa ke dan rawa a
lokacin, amma bata fassara hakan da komai
ba, amma fa Zayyan yau an shiga yanayi,
gabadaya ta lura yau Zayyan wani kallonta
yake so inviting with great admiration. Yayi
kuta yace,
“Amma ba komai kiyi lokacinki ne,
nima nawa lokacin na zuwa, kowa da
ranarsa, tawa ranar na nan tafe.
Ranar da bazan saurari wannan
shagwabar ba nima, balle in yi la’akari da
ustazancinki, kaina kawai zan taimaka.
Kaina zan so nima a ranar, zaki ce na gaya
miki.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Kiyi shagwabarki da ustazancinki ki
gama su a Dandume, tunda gidan Malam ne
ba nawa ba, don haka banida ‘say’ sai
abinda kikace kika kuma zaba mana, tunda
ni na biyo ki gidanku yanzu dole ne in bi
duk abinda kika gindaya min". Ya karasa da muryar da dole Safiyyah
taji tausayinsa.
Safiyyah ta hau dariya tana cewa "au
abin haka ne? In da kara ga Malam ai
kaima nan gidanku ne “Habiby!".
Ya ji wani irin tashin tsigar jiki, ya dai
daure yace "ba wani Habiby, tunda guduna
kike a gidanku Safiyyah, da gidana ne kin
isa ince ki cire min hijabi kice a’ah ba’ayi
yakin duniya na uku ba???” Safiyyah sai
dariya take har hakan yasa Zayyan ya
shagala cikin kallonta, ‘she looks so cute’ in
tana dariyar in’inarta.
“Mu bar zancen wasa Sophie, yau
zuwa nayi inji gaskiyar yaushe zaki tare a
gidanki? Hatta Mama ta magantu, tunda
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
har tayimin magana cikin kosawa akan
batun tarewarki.
For God’s sake kince “exams” kuma
na tabbata an gama. Safiyyah kince rashin
lafiya, kuma gashi kin murmure, for God’s
sake yaya kikeso inyi da raina da tunanin
Safiyyah tana Dandume, ni ina Zaria
nikadai, sai faman rungumar pillow da
tumurmusar katifa nake, alhalin na san
inada Safiyyah ta kuma zama mallakina?”
A yadda yayi maganar idanunsa kai
tsaye suna kallon nata saida ya bata kunya
sosai, da tausayi kuma duka a lokaci guda,
domin damuwarsa ta fito karara a sautin
nasa, sannan cikin lallashi da ban baki yake
maganar. Abinki da So, koko ince soyayyah ta
hakika mai saurin karya zuciyar mace,
Zayyan ne fa! Wani mutum guda daya da ta
fara sanin so a kansa, batare da ta san ma
menene son ba, kawai ta samu kanta da
sabo dashi farat daya, ya shige ranta sukuf!
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Duk a lokacin da bata yi tsammani ko taba
hakaitowa ba.
Itama tasan ba wai bata son Zayyan
bane, ba kuma ta daina son sa bane bayan
an daura musu aure, kawai Anti Dije ta
tsoratata da aure ne gabadaya.
Safiyyah sai ta samu kanta da yin
saranda, ta hanyar cewa “Shikenan na
daina, duk lokacin da iyaye suka sake
sakawa bazan kara musawa ba, kayi
hakuri, ka ji Habiby?”. Zayyan ya ji wani irin dadi ya ratsa har
ransa, sai kawai ya taso daga kishingidar da
yayi cikin kujera ya dawo yayi zaman
Rakuma dirshan a gabanta. Ya daga