Showing 129001 words to 132000 words out of 194140 words

Chapter 44 - BABU SO Book Complete by Maman shakur.doc

kamar bata fahimci komai ba, fuskarta da murmushi ta mi?e tana faWin,  Aunty ku zauna Please bara na kawo muku ruwa . Bata jira cewarsu ba ta nufi kitchen.
? ??  Babbar b*r* uba kai. Wai wannan yarinyar tana nufin bama tajin mi muke faWa ko mi? .
?? Fadwa da batace komaiba tun shigowarsu tana kuma daga tsaye dan bata zauna ba tace,  Hummm! Tana jin komai sarai iskanci ne kawai fa Aunty. Ni dama kun barta dan ALLAH kawai....
? ? ? ? Harara Hajiya Luba ta zuba mata. Shigowar Shareff a bazata ta saka Fadwa haWiye abinda zata faWa babu shiri da risinar da kanta ?asa, wani yawu mai kauri ya wuce mu?ut a ma?oshinta ?irjinta na bugawa.
? ? ? ? Idanunsa ya janye a kanta da ?arasowa cikin falon hannayensa duk biyu a cikin aljihun wandonsa.
??  Oh dama kana gidan? .
Aunty Sakina ta faWa tana hararsa.
Duk da sarai ya jita sai bai amsa ba, sai da yakai zaune cikin kujera da Wora ?afa Waya kan Waya sannan ya dubesu.  Barkanku da safiya aunty kune a gidan namu? .
? ?? Sosai ransu ya sosu da salon rainin wayonsa su duka. Sai dai kafin wani yace wani abu a cikinsu Anaam ta fito Wauke da tray sha?e da kayan ciye-ciye da ruwa da lemo. Itama dai ta Wanji wani iri na ganin nasa, amma saita fiske abinta ta ajiye tray Win a gabansu tana murmushi.  Aunty ga ruwa to....
? ? ? ? A matu?ar harzi?e Hajiya Luba ta tura tray Win da ?afarta tana ballama Anaam harara.  Tunda shine ya kawomu ba, k ki kama kanki wadda ta haifeki ma a tafin hanunmu take balle ke kanki...
? ??  Juwairiyya bani lap-top dana bari a Wakinki . Shareff ya katse hargowar Hajiya Luba tamkar bai ji mima take faWa ba. Tsamm Anaam ta mi?e batare da tace uffan ba, ba kuma ta kalli sashen da Shareff Win yake ba balle Fadwa ta Wauka wayarta ta wuce bedroom.
? ? ? ??  Oh ke ko ga mahaukata suna magana dole ka sata aika. K! Fadwa sha?omin ?ar iskar yarinyar can na nuna mata wacece ni dan ubanta .
? ?? Mu?utt Fadwa ta haWiyi yawu da ?yar a karo na biyu domin jin umarnin Aunty Sakina tamkar saukar aradu bisa kai. Ta Wan saci kallon inda Shareff ke zaune a harWe har yanzu kai kace baima san wainar da ake toyawa a falon ba. Kanta ta girgiza a hankali, so take tayi magana amma ta kasa motsa lips Winta sai kawai ta juya da sauri ta bar falon ma gaba Waya. (Tabbas Fadwa nada kurari da haya?i, amma kuma tanada tsoro bata cika iya jure hatsaniyar faWa ba. Idan mai karatu bai manta ba kokuma ya lura da ?yau zai fahimci Anaam ta fita tsiwa, saboda a lokuta da dama takan takaleta faWa amma a ?arshe Anaam Win ke tsigeta itako sai tai la?was. Tabbas a cikin raunanan halayanta wannan yana ciki rashin juriyar hatsaniya, a wani fannin kuma zamu iya kiransa ha?uri=??).
? ? ? Daga aunty Sakina har Hajiya Luba baki suka saki uwa sakatar sakarai dan al'ajabin Fadwa.  Oh ni Sakina ato lallai Fadwa kema kin cika asararriyar yarinya, to kodai ba Al-Mustapha Win kawai aka shanye ba harda ke Win kema? .
? ?? Maimakon samun amsa daga Fadwa data fice sai Hajiya Luba ce ta amsawa Aunty Sakinar.  A to ga halama kin gani kuwa Sakina. ?an?anuwar yarinya ke juya gida miji da kishiya duka a tafin hanunta.
? ? ?? ?ololuwar Sacin rai kam Aunty Sakina takai, musamman biris da su da Shareff yayi. Tsabar wula?anci ma sai latsa wayarsa yake yana Wan girgiza ?afarsa da yay crossing. Anaam dake danne dariyarta da jinjina tsaurin idon mutumin nan ta ?araso Wauke da lap-top Win a hannu. Gabansa gab ta matsa, ta mi?a masa harda takardun data haWo da su. Idanunsa dake akan wayar ya Wago yana kallonta, ta Wan tura baki gaba tana son dangwarar da kayan bisa cinyarsa ya ri?o hanunta. Fuska ta Wan narke da ?ya?y?yafta idanu tai ?o?arin janye hanunta.........
'



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? [11/11, 7:37 PM] Marsy=??: *_Typing=???_*




*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_54_*




.........?ara ri?o hanun yay da ?yau idanunsa masu kaifi na saukar mata da kasalar data mantar da ita wanzuwar su aunty Sakina a falon. Dama haka yake bu?ata, ta manta da wanzuwar tasu ya samu damar isar da gargaWinsa garesu batare daya samu wani tangarda daga gareta ba.
? ??  Dama haka ake bama miji abu? .
? Ya faWi maganar a salon daya nema Wauke numfashin Anaam na wucin gadi, dan muryar da yay mata magana da ita muryace da zata iya rantsuwa bata taSa ji daga garesa ba. Da ?yar ta iya ?wato kanta, tai ?o?arin ajiye masa kayan a hanun kujerar da janye nata idanun daya sargafe a nasa dan ta gama yanke shawarar barin wajen kafin a samu matsala yaga rauninta. Tana daga kafa ya ri?o hanunta tare da jawota sai gata Waram a cinyarsa tamkar wal?iya. Kafin tunanin wani abu ya risketa har ya yimata zobe da hanunsa ta hanyar Worawa a saman cikinta ya manne bayanta da ?irjinsa kansa bisa wuyanta yana shinshina da fara magana cikin kunenta da wani salon daya saka tsigar jikinta tashi..  A haka ake bama miji abu ba'a tsaye ba .
? ? ? Saukar wata mulmulalliyar ashariya cikin kunnuwansu ta tilastata ?an?amesa babu shiri dan da gaske ta tsorata dama gata a tsakkiyar wani firgicin. Harga ALLAH ta manta da su a falon, saSanin shi da duk abinda yakeyi domin su Winne dama. A firgice ta Waga ido zata kallesu ya hana hakan, dan kuwa hanunsa ya tura cikin rigarta sai dai akan cikinta ya tsaya.. ?an matsawar da yay ta sata saki ?arar ruWewa dan a bazata abin yazo mata kuma taji zafi......
? ? ? Rige-rigen fita aka farayi tsakanin Hajiya Luba da Aunty Sakina, saboda ?arar Anaam Win fassara daban suka bata. Aunty Sakina ma harda gwara kai a jikin garu lokacin da suke turereniyar ficewa.
? ? ? ? ? Hanunsa da taketa faman kaima mintsini ya janye, ta mike zumbur daga cinyar tasa idanunta taf kunya. Ri?ota ya sake yi fuskarsa Wauke da murmushin ?eta.  Malama nace na gama n....
? ? Hararar data wulla masa ce ta hanashi ?arasa faWa ya saki dariyar data ?ara ?ular da ita tana jin zafinsa har cikin ma?oshinta. Sake fisgota yay ta dawo saman cinyar tasa. Ya haWe hannayenta duk biyu dake son turesa ya danne akan cikinta.  Idan idanunki suka cigaba da harararta daga yau sai na miki haWiyar Wan sululu a gidan nan fitsararriya . Mutsu-mutsunta ta cigaba dayi na son ?wacewa ya?i bata dama. Saima lan?wansota yay ta kwano jikinsa ya kai goshinsa kan nata ya haWe. Yawu ta fara kokawar haWiyewa da sauri-sauri ganin yana daidaita lips Winsu.
? ??  Please Yaya dan ALLAH kar kayi bana so .
? ? Gira ya Waga mata da kashe ido Waya,  Fitinanniyar yarinya minace zanyi to? .
? Bakinta da take faman karewa da hannu tatura gaba da ?o?arin kauda fuskarta ya tare da hannunsa, tare da janye nata hanun ya manne lips Winsu. So take ta turesa, amma tasirin abinda yake matan a cikin jini yana barazanar hanata kowanne irin yun?uri, daWin daWawa ya ri?e hanunta ta yanda bazata iya ko motsashi ba. A karon farko ta fara maida masa murtani a yau dan tasirin salon nasa jinin jikinta ya fara amsarsa da ?arfin gwiwa da wani sirrin Soye dake can ?asan zuciyarta da ita kanta har yanzu bata san da zamansa ba tattare da ita. Hakan tamkar ?ara zugane a garesa da dukkan ha?urinsa, dan kai tsaye zuciyarsa ta fara ingizasa ga kaiwa inda bai gama shirya kai kansa ba. Ring na wayarsa ne ya dawo dasu duniyar da suka jima da yin nisan barin cikinta da lissafi irin na masu hankali. Sakinta yay, zaram ta mi?e kamar wadda take a tsinin allura. Da sassarfa ta bar falon ko waiwayensa ta?i tayi. Da kallo ya bita yana sakin kakkauran numfashi da murmushi, a hankali yakai bayansa jikin makarin kujera ya kwantar yana mai lumshe idanunsa da sake sakin ajiyar zuciya a jajjere yana kai hanunsa ya shapo lips? Winsa....

? ?? Tun fitowarsu take faman kaikawo a harabar gidan, dan ko sashen Fadwar sun gagara komawa tsabar mamaki da jinjina ?warewar iskancin Shareff Win a yau. Yaron da ko ido bai cika Wagawa ya kalla mutane ba shine yay musu wannan ba?in iskancin. Ina bazata iya ha?uri har sai sunje gida ba, dole ne ta kira Mommy kam ai. Takai wayar kunenta tana faman kaWa ?afafu da jijjiga jiki na tsantsar bala'i. Cikin sa'a aka Waga mata gab da zata tsinke.
? ? ?  Sakina har kun isa gidanne? .
Mommy ta faWa tunkan aunty Sakinar tace wani abu. Aiko cikin matu?ar Wacin murya ta tare numfashin Mommy din da faWin,  A dole Mustapha kam yafi karfinki wlhy Yaya Nafi! Dan tabbas babu makawa an wanke an basa ya sha.
? ?? ?irjin Mommy ya buga da ?arfi, sai dai kafin tace wani abu Aunty Sakina ta cigaba da bata labarin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Ta ?are da faWin,  Zama dai kam bai gammu ba dan wannan yarinyar tafi uwarta hatsabibanci. Nan gaba babu makawa zaima iya cewa kwanciyar aure zaiyi da ita a gabanki saboda ya tabbatarma duniya shi Win tantirine na gask...... ?itt!! Wayar ta yanke. Tai saurin cirota a kunenta tana kallo a tunaninta ko kuWine suka ?are. ?o?arin siya tai ta banki ta ?ara kiran Mommy Win. Sai dai kuma number busy ake nuna mata alamar waya take ko kiran wani.....

? ? ?? Ring Win wayarsa ne ya sake sashi buWe idanunsa da har yanzu ke'a rufe. Ya kafe fuskar wayar da kallo tamkar mai tsoron Wauka ganin sunan First Luv ru?u-ru?u na yawo. Rabon da suyi koda waya ne harya manta, ya kuma tabbatar gargaWin da yayma su Aunty Sakina ya risketa ne matsayin sa?o. Bazai iya ?in Waga kiranta ba koda yana jin tsoron dukkan wani furuci daga bakinta, kimarta da girmanta sun wuce a musalta a cikin idanunsa da zuciyarsa. Hannu ya kai ya Waga tana gab da tsinkewa, yakai kunen nasa cikin ?arfafa kai....
? ??  First luv barka da safiya .
 First ubanka ba first luv ba. Al-Mustapha wlhy ina gab da jamaka kalmar ALLAH ya i.....
? ? ??  Please First luv, abeg kar kice haka dan girman ALLAH.
 Idan ka sake kirana da sunannan ALLAH sai naci ubanka. Kuma kazo ina nemanka idan ba hakaba ka bari na tako ?afata gidanka da kaina yarinyar nan na a ciki wlhy wlhy wlhy kadaiji na rantse ko! Sai na jamaka ALLAH ya isa da manyan ba?i no-no na daka sha dan bakai kaWai na haifa ba balle ka Wauramin hawan jini .
? ? ?? Harshensa har sar?ewa yake wajen faWin,  Shi... Shike nan naji zanyi, zan zo, amma kimun alfarma Mommy dan ALLAH sai gob.......
? ??  Alfarma ubanka, Al-Mustapha ni kake son tozartawa a idon ma?iyana dai ko? Kana nunama duniya mace ta fini daraja da kima a idonka? . Ta faWa tana fashe masa da kuka. Idanunsa ya rumtse da ?arfi, ya girgiza kai tamkar yana a gabanta.  Mommy wlhy babu wata mace da darajarta zata ko kama ?afarki a wajena. Dan ALLAH ki fahimceni Mommy ina a tsaka mai wuya......
? ? ? A fusace ta yun?uro zatai magana Gwaggo ta fisge wayar.  Nafisa wai kin rasa hankalinki ne halan?! A tunaninki wannan butsutsun naki akan Mustapha shine mafita ta ?arshe da zakibi wajen raba auren?!!......
? ? ? ?? Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da lumshe idanunsa ya saki wayar a jikinsa batare daya ?arasa jin abinda Gwaggon ke faWa ba. Dan kuwa tabbas a wannan gaSar ta taimakesa taimako irin wanda bakinsa bazai iya maimaita faWa ba, sosai al'amarin Mommy ke daWa tayar masa da hankali, ya rasa ta inda zai kama domin shawo kanta akan wannan aure. Har yanzu yarasa gane minene takamaimai laifin su Abie a gareta da take musu irin wannan ?iyayyar (Niko nace Shareff a haka ta tashi, tun tana ?aramarta an riga an cusa mata ?insu. Haka Wan adam yake, a duk lokacin daka koyar da shi wani abu ?ya?y?yawa ko mummuna yakanzo ya fika iyawa. Iyaye tabbas muna kuskure, kuskuren da shike saka ?an ubanci a zukatan ?a?anmu tsakaninsu da ?an uwansu. A kullum baki da aiki saina aibanta kishiyarki gaban ?a?anki, baki da aiki sai na zaginta da nuna cutarki take zaluntarki take bata sonki, bata ?aunarki, ma?iyarki ce kuma a gaban ?a?anki. Tayaya kike tunanin bazasu tsaneta su tsani ?a?anta fiye da yanda kike tsanarta ba, saboda ke ra'ayin ?inta ya shigekine da girmanki da hankalinki, idan kin so zaki iya ya?arsa, suko kin raini zukatansu ne akan wannan ?iyayyar, dolene su dawwama da ?inta da ?in duk wani abinda ya shafeta koda bata aikata musu komai ba na ?i Win. ALLAH ka gafarta mana ka gana damu gaskiya koda bazata mana daWi ko zuwa dai-dai da son zukatanmu ba).
? ? ? ? Anan falon yabar lap-top Win da takardun ya fice, koda ya fito su Aunty Samira sun wuce dan baiga motarsu ba. Motar ya shiga shima ya fita a gidan, dan yana bu?atar yin nesa da su har zuciyarsa ta huce. Haka yake baya son yanke hukunci cikin fushi, ya gwammaci yin nesa da abu a duk lokacin da zuciyarsa ta harzu?a. Asibiti ya nufa wajen Dr Jamal, sai da ya shigo cikin asibitin sannan ya kira wayarsa..
? ?? Daga can Dr Jamal yace,  Ka shigo mana, ni kaWaine ma a office .
?? ?ar ?aramar ajiyar zuciya ya Wan sauke da yanke wayar, bai cika san buWe cikinsa ga kowa ba. Amma dai mutane biyunnan sun wuce abokai kawai a garesa aminaine na gaskiya. Daga Dr Jamal har Fharhan abokansa ne tunna ?uruciya, koda yabar ?asar kuma basu yarda juna ba. Basu da abokin shawara sama da shi, duk da shi yakan jima basuji nasa cikin ba saboda yanada zurfin ciki matu?a. Na ukunsu kuwa shine Khaleel, duk da kasancewarsa ?ani a garesa hankalin yaron da nutsuwarsa kansa ya kallesa tamkar aboki, sannan shima Khaleel Win bashi da wani amini sama da shi duk da yana amsa sunan yayansa ne.
? ? ? Sai da yay knocking aka bashi izinin shiga sannan ya shiga. Dr Jamal na zaune a kujerarsa ya amsa masa sallamar da yay fuskarsa da murmushi. Cikin danne kishin rashin Anaam yace,  Ango kasha ?amshi . Harararsa ya Wanyi ya Wauke kai, ya zube cikin kukerar dake gaban desk Win Dr Jamal Win yana furzar da iska mai nauyi. Dr Jamal dake binsa da kallo danya fahimci damuwa a fuskar abokin nasa ya mi?a masa hannu sukai musabaha.
? ??  Wai yana ganka haka kamar mara lafiya? Ko jikinne har yanzun? .
Kai ya girgiza masa, sai dai baice komai ba. Dr Jamal ya tsura masa ido na wasu sakanni, sai kuma ya mi?e ya Wakko masa ruwa. Baiyi musu ba ya amsa, murfin ya Salle ya kai bakinsa. Tass ya shanyesa yana dire robar da lumshe idanu ya sake lafewa a kujerar yana sauke numfashi. Kusan mintuna uku suna zaune a haka shiru, kafin ya buWe idanunsa da gaba Waya launinsu ya canja ya kalla Dr Jamal daya tsura masa ido...
? ? ?  Kai kurwana da Waci irin wannan kallo haka .
Dariya Dr Jamal ya kwashe da shi.  ?an wulakanci, inda ni maye ne ALLAH kamun kaWan a ci Wan iska kawai .
? ?? Murmushi yay a karon farko da gyara zamansa.  To zama mayen mana kaga idan zan ciwu a wajenka mara mutunci .
? ? ?? Dr Jamal yay dariya kawai. Sai kuma ya mi?e daga kujerar zamansa ya dawo inda Shareff Win ke zauna shima ya zauna suna facing juna.  Mike faruwa? Damuwa ta kasa Soyuwa a kan fuskarka my Dude . Nannauyan numfashi ya sauke da Wan Wage kafaWa,  Bani da wata damuwa kawai dai nace bari in gaisheka . Idanu Dr Jamal ya tsura masa fuskarsa na canjawa zuwa jin haushi........
'


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?



*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_55_*



............ To na gode da gaisuwa . Ya faWa da mi?ewa zai bar wajen. Ri?osa Shareff yay ya maida ya zaunar.
? ?  Wai haushi kaji? .
?  Mizaisa naji haushi? .
Murmushi Shareff yayi da cike lips. Sai kuma yace,  Manta kawai .
??  Ka gwammace ka cigaba da ri?e damuwarka kenan. Look Musty! Idan kasan zaka iya shanyewa miyasa zakazo min nan to?. ALLAH kana bani matu?ar mamaki. A yanda muka ri?eka sam kai ba haka baneba, ban saniba ko baka yarda damu bane har yanzu oho. Well koma dai minene matsalarkace, mudai har gobe da jibi bazamu daina kallonka matsayi mai girmaba insha ALLAH....
? ? ?  Humm Jamal .
 Miye wani Humm Jamal. Na jima da fahimtarka ai Shareff kai har yanzu matsayin abokai gama gari muke a wajenka. Mune dai kawai ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login