Showing 1 words to 3000 words out of 4616 words
Chapter 1 - PRINCE ISHMEL Complete Hausa Novels by Fauziyya Tasiu Umar .pdf
*_PRINCE ISHMEL_*
*OUM HAIRAN*
*300 via 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank*
*Or 9031307566: Fauziyya Tasiu Umar Opay bank*
*WhatsApp number 09013718241
í ½í´žFOR ADULTS ONLY
*1-2*
BuÉ—e manyan idanunsa da suka kada daga farare zuwa jajaye yayi kan TAJ, ya sauke ajiyar
zuciya tare da dashi daga kwanciyar da yake tun farkon safiya gashi har duhun magrib ya fara
shiga. Hannu yasa ya É—auke gumin da sanyi A C ya gaza tsai dashi Yace.
TAJ bansan Jenny ta buÉ—e zuciyata ta É—iga jininta ba sai bayan da abubuwa suka lalace, TAJ na
tafka kuskuren da bansan ta ina zan fara Please help me TAJ wlh a yanzu sonta nakeyi ba
sha'awarta nake ba".......
Kallon tuhuma TAJ yayi masa tare da zama kusa dashi Yace “Tun dawowarka daga England na
fahimci akwai damuwar da take cin ranka saidai tunda baka sanar dani ba banji zan tambaye ka
ba PRINCE ISHMEL meye asalin abinda yake damunka yake neman taɓa lafiyarka?" Miƙewa
yayi tsaye ya fara zagaya ɗakin yana dukan tsakiyar hannunsa yace “Itace TAJ Jenny ita ne
damuwar da take neman zautar da ruhina" rusunawa yayi gaban Taj ya riƙo hannunsa yace
“Please ka bani mafita, na rusa rayuwata da hannuna bansan Jenny rayuwata bace sai bayan
na tozarta ta na koreta daga rayuwata ina zan ganta ina zan fara neman ta ina ta tafi ta barni
Taj wanne hali take ciki ita da cikina dake jikinta? Don Allah ki dawo Jen wlh na yarda cikin
jikinki nawa ne baki taɓa sani wani namiji ba bayan Ni am believe Jennifer ki dawo Please....."
Mamaki tsoro da tunanin Abokin nasa ya zauce yasa Taj jijjigashi yace “Eshmel calm down
mana wacece ita meye yasa ta zama damuwarka ka haƙura ka manta da ita mana haba don
Allah nawa ka manta kafinta sai itane zata gagara mantuwa Ishmel wai itan me take dashi da
sauran mata basu dashi meye yasa ka saki zuciyarka har tayi maka saƙa to wai ma a ina take
da kakejin ciwonta yake damunka mace ko a daular Hindu take in mukaso sai mun amfana da
ita itan me isa ka yarda ta baka ciwon kai?"
Komawa yayi ya zauna yana jan ajiyar zuciya me ƙarfi yace ba kamar kowacce mace take ba Ni
nake faÉ—a maka wannan wlh tafisu komai duk da kasancewarta ba musulma ba inajinta saman
mata musulmi na duniya gabaÉ—aya babban tashin hankalina abinda zata faÉ—a a gaba game da
Musulmi bazai zama mai daÉ—i ba domin ba daÉ—in taji ba Taj nine musulmi É—aya tal data fara sani
a rayuwarta na shiga rayuwarta tun bataso har ta haƙura tasoni ta bani kanta don mafitar kaina
badon tata ba Taj bantaɓa mu'amalantar Jenny ranta naso ba amma takan danne tayimin duk
wani abu da zaisa na samu nutsuwa duk da wahalar da take sha wajen sex dani bata guduna
da na nuna mata alama take kawo kanta. Amma hakan baisa na ɗaga mata ƙafa ba kan
kuskure ɗaya tak da tayimin shima don kare lafiyarta ne nasani badon ta baƙantamin ba"
Taɓa ƙofar da aka fara ne ya sanyashi tashi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa Taj ne
ya sanar da Bafaden yaje yace da Mai martaba gasu nan. Hakance ta faru bayan ya fito ya
shirya cikin shigarsa ta alfarma kasancewarsa cikakken Prince mai cikakken iko tunda ya fito
ake watsa masa fure ana zuba masa kirari, tabbas isa Izza da iko da ÆŠagawa da Miskilanci ya
gama ƙarewa wajen Yarima Isma'il bayada sauƙi kuma baya shayin murje uban kowa, wannan
yasa duk sanda ya dawo hutu wannan babbar masarauta take matuƙar shiga taitayinta domin
Yanzun nan zaisa ayi maka azabar da a wannan rana tsaf zaka roƙi Allah ya ɗauki rayuwarka
ka huta.
Kai tsaye gurin da yaga an parker manyan motocin suka nufa shida Taj É—aya cikin kafuran
motor É—in suka shiga daidai lokacin aka bada umarnin tafiya suka sulali hanya cikin nutsuwa
ake tafiyar jerin gwanon motocin dukka farare sunata É—aukar idanun talakawa da haka suka isa
wani babban guri sukayi parking kowa ya fito amma banda Isma'il yana zaune ya lula duniyar
gajimare tunano farkon haÉ—uwarsa da Jenny kawai yakeyi lokaci zuwa lokaci yana fidda iska
me huci.
Shidai Taj fita yayi don wakilci kamar yanda ya umarce shi gidan marayu ne musamman da Mai
Martaba Ƙassim ya gina tun shekara goma sha biyar baya to yau ake aurar da wasu yammata
cikin marayun shine dalilin zuwansu don halartar É—aurin auren da King bazai samu halarta ba.
Sun ɗauki a ƙalla awanni uku a wannan gidan marayu sannan ne suka sami damar juyawa
domin komawa gida, tunda suka taho kansa ke cikin cinyarsa har suka isa gida a haka yake
saida Taj ya taɓashi sannan ya fita a wahalce ya nufi sashinsa an gyara masa shi kawai faɗawa
yayi gadon tare da jan bargo ya ƙudundune yana rawar sanyi komai ya ƙwace masa tabbas
dole cikin satin nan ya sake komawa England a karo na ba adadi ko Allah zaisa ya sami wani
Information game da Jen tabbas ya haƙiƙance zuwa yanzu haƙƙin marainiyar Allah ne ya fara
bibiyar rayuwarsa.
Gabansa ne ya faÉ—i wasu kalmominta suka fara dawo masa lokacin da yake fatali da kayanta
bayan ya gama zane ta da belt ta zuba masa idanunta dake tsiyayar da hawaye tace “Banida
kowa a duniya daya wucce ka kowa na shine ya damƙani a hannunka bayan ya tabbatar min
kai Musulmi ne kuma musulmi basa zalunci Eshmel ka tabbatar min da cewa Musulmi basa
zalunci kamar yanda Kenn ya sanar dani ta hanyar jin ƙai na da nunamin tausayinka gareni.
Me kake tunani game da gobe na bayan ka koreni daga sashinka a lokacin da nake tsananin
buƙatar kulawarka Ishmel farin cikina ya ta'allaka da naka ne komai damuwar da nake ciki
burina na ganka cikin farin ciki saboda ina maka kallon uwa uba kuma É—an uwa sannan ina
kallonka kallo irin na miji domin abinda na daÉ—e ina tanadin saboda miji na sallama shi gareka
burika kawai naga ka tsarkaka ka daina mu'amala da kowacce mace Ishmel saboda Future
naka ne saboda kaine duk da cewa hakan baisa nayi nasara ba amma ban fasa baka kaina a
duk sanda ka buƙata ba nidai inaji a raina ko ba komi ka rage kula mata.
Ishmel karka wofintar dani a daidai wannan lokacin wlh dani da babynka muna tsananin
buƙatarka babynka baya gajiya da ɗuminka idan ka barni na tafi ya zanyi...."
Duk da ƙarfin zuciyarsa bai hana shi fashewa da wani marayan kuka na tausayin kai ba kora na
ba adadi da yake ƙalubalantar muguwar zuciyarsa mara tagomashin ɗigon tausayi a cikinta wai
meye yasa ne anya kuwa shi mutum ne?" Sake ƙanƙame ƙirjinsa da yake masa zafi yayi ya
rushe da kuka me sauti yana faɗin Jenn! Please Jennifer help me am dead in kika ƙi dawowa
gareni wlh zan mutu babynmu zai taso irin rayuwar da kika taso Jenn meye yasa kika sallama
min komai Ni na kasa sallama miki farin ciki É—aya, kawai É—aya tal. Da nayi miki da ba anan
muke ba yanzu ina zan ganki Jenn don Allah ki tausayamin kizo gareni ko cikin mafarki ne
zakiga na canza ba Eshmel É—in da kika sani ba.
Nasan yanzu kin haifa min babyna me kama dani ki kawo shi ya ganni na gansa inason King
don Allah Jenn ki yafe min nasan zuciyarki batada juriya game dani ƙarya nake bazan kasheki
ba ki yarda dani daga yau zan fara faÉ—awa kowa nawa Inada Abraham É—ana ne na cikina daga
jikin....
Rufe masa bakin da yaji anyi ne ya sanyashi buɗe ƙananun idanunsa da suka kaɗa sukayi
jawur ya zuba su kan Queen Wato mahaifiyarsa sai kawai ya tashi ya faÉ—a jikinta ya rungumeta
yace “Please Mom kice ta dawo gareni wlh tallahi inasonta inason fetus ɗina kar ta bari ya taso
da baƙin cikina Mom zan mutu Mom zuciyata zata fashe na kasa jurewa Jenn Mom Jenifer nake
buƙata ita nakeson rayuwa da ita kiji ƙaina ki tausayamin Mom ita ce rayuwata tayimin komai ta
sallama min komai ko zata sha wahala indai zanyi farin ciki to bata ganin wahalar burinta farin
cikina Mom please kice wani abu mana ko kema kin daina sona ne...."
Numfashi ta sauke me nauyi ita dama tasan bayan tia akwai wata caca tun dawowar Ismail
daga England ta fahimci akwai wani abu dake cin ransa amma dake miskili ne yaja bakinsa ya
kulle sai rama yakeyi sai yau da abin yafi ƙarfin cikinsa sannan ne ya fita batare daya shirya
fitarwa ba.
Miƙewa tayi da nufin ficewa domin kanta ya kulle tunanin ta ya kasa hasaso mata kalmar da
zata furta akan wannan rikitaccen al'amari da Isma'il yazo mata dashi lamarin ya girmi tunaninta
dole sai ta nutsu zata samu abin faÉ—a.
Ji tayi ya riƙo hannunta ta ɗago ta zuba idanunta cikin nasa ba ƙaramin firgita tayi da saƙon
data gani a cikin idanunsa ba ta rikeshi da sauri tace.
“Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Isma'il kai meye hakan...." Kafin ta rufe bakinta yakai ƙasa ta
fasa ƙara tana cewa jama'a ku kawo min ɗauki Yarima kai kuma soyayya ce ƙaddararka jama'a
ko gidan babu kowa ne a taimaka min zan rasa shi akan mace....."
Tuni masu hidimar sashin suka cika parlourn hankalin kowa ya tashi domin iyakar saninsu
Yariman nasu ba ma'abocin yawan lalura bane hassalima bai taɓa shiga irin wannan yanayin
ba.
Fita akai dashi domin sadashi da babban asibitin dake cikin masarautar likitoci biyar ne a kansa
domin ceton rayuwarsa, daƙyar suka samu ya dawo hayyaci Dr Nazar ya fita yana sharce gumi
ya isa ga Queen dake zaune cikin damuwa yace.
“Allah ya taimake ki duk abinda ya damu Yarima gsky me girmane domin kuwa binciken farko
ya nuna mana abun ya daÉ—e yana cin zuciyarsa sannan yana tsananin soyuwa ga abin wanda
bazai iya cire shi a ransa ba kuma bazai iya control tamper É—insa akansa ba Queen indai zai
yiwu a kusantashi da abin da yake muradi ko kuma a bashi madadi da zau cire masa kewar
wancan saboda lallai zuciyarsa tana barazanar kamuwa da mugun ciwon da zai iya kaishi
ƙarshen rayuwa!....."
Cikin ɗimuwa Queen ta kama kuka tana cewa da wacce ke kusa da ita “Kinji ko? Kinji abinda
nake gudu ko Janah yanzu ina zan iya nemowa Baban karuwar da shi kansa bai san inda zai
nemota ba, shiyasa tunda na fuskanci take taken Baban yarone miskili amma fitinanne bazai iya
kare kansa daga mata ba, naketa ƙoƙarin naga yayi aure amma yaƙi kuma King ya Goya masa
baya yanzu wa gari ya waya bamu ba? Janah yaje yayi zaman dadironsa da karuwa me tayi
masa me tayi masa su suka sani wai abin takaicin har Ni Baban yake faÉ—awa yanason fetus
É—insa yanzu yasan ma ta haihu ta kawo masa Abraham kar ya taso a irin rayuwar data taso!"
Dafata Janah tayi tace “Kiyi haƙuri yaya sharrin ƙadangarun bariki Prince ya haɗu dashi yanzu
addu'a za'a dage masa da ita kawai Allah ya ƙwatoshi" kuka sosai takeyi tana cewa yanzu
Ishaq dake basa ɗasawa da King ba gashi ƙalau yake zaune ba amma Isma'il shine shan giya
shine neman mata yanzu gashi garin jaye jayensa ya janyowa kansa tsiya baki Janah taci gaba
da bata har ta samu tayi shiru.
Zuwan King ne ya sanyasu tafiya bayan likita yayi masa bayanin komai sosai King ya shiga
damuwa da jin zuciyar shalelen nasa tana neman taɓuwa ya zubansa idanu lokacin da yake
buÉ—e nasa idon ya saukesu akan King matsawa yayi ya kamo hannunsa ya zauna kusa dashi
Yace “Baban meye yasa ka cunkusawa zuciyarka damuwa da take neman ganin bayan
numfashinka haka meye ya dame ka a duniya da kakasa maganceshi kuma ka kasa faÉ—a mana
mu tayaka da addu'ar samun maganinsa?"
Kawar da kai yayi gefe tare da zame hannunsa daga na King, murmushi yayi ya miƙe yace “Ok
na fahimta kayi hƙr komai yayi tsanani maganinsa Allah zamu tayaka da addu'a" da wannan
shima King ya fice basu jima ba suka fito da likitan yan cike cikensa yayi ya bawa wani Bafade
ya fita bai jima ba ya dawo da magungunan daidai lokacin shima Ishmel ya gama shiryawa ya
riga su ficewa ma daga ɗakin ya nufi cikin gidan sarautar wani ɓangare ya nufa da yakan zauna
don Hutawa da bawa zuciyarsa damar yin tunanin abubuwa shuÉ—aÉ—É—u masu muhimmanci a
rayuwarsa ji yayi an dafashi ya sauke numfashi ƙamshin turaren kawai ya fallasa masa asirin
wanda yake tsaye a kansa ƙaninsa ne Ishaq zama yayi kusa dashi Yace “Sorry Bro sai yanzu
nake samun labari ashe Bakada lafiya amma ya jikin?" Lumshe idanunsa yayi Taj ya amsa da
cewa “To da sauƙi kenan zaace kawai yana neman kashe kansa akan wata kafura saboda
rashin mafaÉ—i....."
A fusace ya ɗagansa hannu ya miƙe yayi gaba abinsa duk maganar da sukeyi masa bai kulasu
ba saida suka isa tsakiyar ɗakin baccin nasa sannan ya juyo ya kafesa da ido yace “Yafi sauƙi
ka É—aga hannunka ka kwaÉ—amin mari da ka aibata Jenn a gabana kai ko a bayan idona bazan
yafe maka ba" É—agowa Taj yayi da sauri cikin mugun mamaki karon farko da wani mummunan
furuci ya shiga tsakaninsu kenan taɓ dole ya iya takunsa aminin nasa kuma ubangidansa da
gaske yakeyi.
Juyawa yayi ya fice ya riga ya sani a yau dai ba sake kulashi Ishmel zaiyi ba hakan ce ta bashi
ƙwarin gwiwar ficewa to shima bathroom ya shiga yayi wanka yayi sallolinsa ya ɗauki wata
zazzafar Giya ƙaramar kwalba ya ɓalle ya shanye wai ko zaiji sauƙin abinda yakeji a ransa. To
yadaiyi bacci shima me cike da mafarkai masu tada masa da hankali, zabura yayi ya miƙe
baitaɓa mafarkin da ya nemi tafiya da ransa ba saboda firgici kamar wannan ajiyar zuciya kawai
yake saki dafe da kansa da yake juya masa a haka ne kula da abincinsa ya shigo ya ishe shi ya
rusuna yace “Abinci ya kammala Allah ya taimakeka ko da wani abu da kake buƙata?" A zahiri
yana bukatar wani abu amma nauyin da harshensa yayi masa yasashi ɗagansa hannu miƙewa
yayi ya fice shi kuma ya sake gyara kwanciya ya zubawa pop na É—akin idanu abubuwa suna
dawo masa kamar yanzu suke faruwa kamar bazasu ƙare ba yau gashi cikin bala'in da bazai
taɓa iya fitar da kansa ba. Itace maganin ita kuma tayi masa nisa.
Zuffa ya share ya lumshe idanunsa farkon haÉ—uwarsa da ita tana dawo masa sabuwa kamar ya
kunna video yana kallo.......
*_PRINCE ISHMEL_*
*OUM HAIRAN*
*500 via 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank*
*Or 9031307566: Fauziyya Tasiu Umar Opay bank*
*WhatsApp number 09013718241 / 09031307566*
í ½í´žFOR ADULTS ONLY
3-4
ENGLAND
BIRMINGHAM State Yammacin ranar Lahadi ne mafiya yawan mutanen dake zaune a unguwar
ta Alum Rock suna cikin gidajensu ne saboda yau É—in ta kasance rana ce ta hutu ga daukacin
ma'aikata wadda aka ware ta don samun damar zuwa gurin ibada.
Haka yake ga Jennifer wadda tun sanyin safiya ta shirya ta tabi grave na Mahaifiyarta Helina
nan ne ta mayar gurin ibadarta a nan take bautar ta tanajin a ranta bata da wani abin bauta
daya wucce mahaifiyarta.
Tsugunne take gaban kabarin tana rera wasu yan baitoci cikin sahihin turancinta na jini domin
kuwa cikakkiyar baturiyar England ce kasancewar mahaifiyarta cikakkiyar yar ƙasa.
Miƙewa tayi tana share hawaye ta matsa daidai ƙirjin Mahaifiyar Tata ta kwanta saman tiles ɗin
tana kuka me tsuma zuciya tana cewa “Miss ur Mom na rasa komai saboda rashinki tare dani
tunda ke kinƙi dawowa gareni ki rokamin Yessu ya dawomin da ɗan uwana Kenny gareni
rayuwar kaÉ—aici tayimin wahala Harvest ne yake daukemin kewa inason mutum a kusa dani
Mom please kar kice a'a yau ma kinji!"
Murmushi tayi me ɗauke da hawaye tace “Yap naji a jikina kin amsa zaki faɗawa Masihu
damuwata zan barki kamar yanda nayi miki alƙawari bazan dawo ba sai Sunday me kikeso na
taho miki dashi?" Wata leda dake ajiye a gefe ta buɗe ta ɗauko wata flower me kyau ta saƙala
saman wani kwando dake saman grave É—in ta mike tana hawaye tana ja da baya tana É—agawa
kabarin mahaifiyar tata hannu.
Ji tayi ta daki wani abu ta baya tayi saurin juyawa tana faɗin “Ohh God bless sorry...." Wani
tsalle tayi ta maƙalƙale mutumin data gani a tsaye tana shinshina shi ta tura hannunta cikin
sumarsa ta fashe da kuka tace “Miss you bro ka tafi ka barni long time why?" Shima shigar da
ita yayi jikinsa yace “Miss ur My love" kissing kuncinta yayi yaja hannunta ta zame ta sake
tsugunnawa gaban grave ɗin tace “Double tnks My heart na daɗe ina faɗawa Masihu bai amsa
ba sai gashi kina faÉ—a ya amsa na gode ki huta" tashi tayi ta sauke idanunta kan mutumin dake
gefe da tunda ta juyo ta ganshi idanunsa a kanta amma ba tashi takeyi ba ta É—an uwanta takeyi.
Har yanzu idanunsa akanta yake tare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da Kenn ya kama
hannunta ya kamo na Ishmel ya haɗasu yace “Friend ga love sis da ka daɗe kanajin labarinta
inasonta fiye da yanda nakeson kaina itane rayuwata kuma amanata" jinjina kai yayi tare da
É—aga É—ayan hannunsa ya saka a bayanta ya janyota ya rungume wannan ba wani abu bane ga
al'ada ta Bature itan ma bata É—auke shi komai ba saidai banda Ishmel da ya tsinci duniyarsa da
ɗaukar wani shorck da baitaɓa jin irinsa a rayuwarsa ba musamman lokacin daya ɗora haɓarsa
saman gyararriyar sumarta me nauyi baƙa wulik kwanciya ta sakeyi a jikinsa ɗumin hannunsa
daya riƙe ƙugunta yana zaga ilahirin jikinta.