Showing 3001 words to 6000 words out of 31405 words

Chapter 2 - Hariji Part 3 Complete By Oum Aphnan.doc

05 Dec 2025

95

ba mata ba

Da wannan tunanin yaje ya auro Nnenna Wanda take nacin sonsa kuma Account ne a wajen aikinsu,don har alaqawari tayi masa akan indai ya aureta zata musulunta.

Amma da yike batada cika alkawari da ta shigo sai ta ki musuluntan. Saima qaton plaza da ta bude tana Satan masa kudi tana dibga kaya ta saka saurayinta ,matsayin manager din wajen,ashe dama ta auresa ne saboda taji labarin yinada kudi kuma bayida banki ,don haka tabbas a gida yike ajiyan kudinsa.


Da quliya ya gane hakan ,sai ya sa aka tottone tsakiyar bed room din kowaccensu ,ya zuba mata maqudan arziki ,da yasan zai sustaining din rayuwar su Dana yaransu da suka roro koda bashi,da rai.don a gaskiya ya fara tunanin komawa saudiyya dingurgum da Zama don ya Lura matan Nigeria basuda kirki Sam,dukkansu yarigada yayi masu kudin goro,.

Kuma bai bari wata tasan wainnan tsubin kudin yina dakin er uwarta ba,yayi hakan dan su samu peace of mind a barshi ya zauna lahiya,suyi tunanin kowacce itace yardajjiyar mijinta,amma sai kuma kowacce akalanta ya koma yanda zataga bayansa don ta nade dukiyar ita daya...gane hakan yasa ya daina cin komai a gidan don yasan zasu iya zuba masa guba ,amma ya yanke lokacin rabuwarsa dasu da zaran ya aurar da yaransu ,don sune vayaso su hofinta .


...Saidai Ana cikin hakan ummi ta 6ullo rayuwarsa ,wannan ya canja masa lissafinsa Na komawa madina amma ya maida Nigeria tamkar zuwan week end

Adnan kam,shaquwarsa da quliya daga jininsu yake,saidai rashin yardarsa ne yike damunsa,musamman yanda yaga
Yana qoqarin maisheshi cook,bayida damar zaman Nigeria .

Ana cikin hakan ,tsohon su quliya shima ya rasu,don haka aka roki quliya yazo a bashi sarautar gidansu,ba tareda sanin kowaba ya tattara ya koma qasansu,saidai in gawurtaccen shari'a ya samu yazo yayi attending shari'ar ya juya. Sam ya fita sha'anin su duka,kuma duk jarabansa irin Na Arab blood ya roqi Allah ya cire masa sha'awar kowata irin diya mace.

Rayuwarsa ta fara tafiya masa smooth ,kafin tsidik sophy sukayi tafiya Kai ziyara kogon hira,A saman kogon wata balarabiya ta bata tuffa,da nufin girmamawa ,ashe akwai sinadarin guba mai tsintsinka jijiyoyi a ciki Wanda in har taci bazai fara yi mata aiki ba sai bayan awanni Sha hudu ,daga nan sai gawa,wannan kuwa makircin kishiyarta ne,cikin hukuncin Allah sai bataci tuffa din da aka bata a wajen masu kasuwancin kogon ba,saima ba wata kuyangarta tayi da taci ita yau bata muradin ci.
Sosai abun yayi touching matar,suna barin wajen ,ta Kira ta a waya ta shaida mata sophy bataci tuffa ba,kuma mutuwar kuyangar a en awanninnan daidai yike da tonuwar sirrin su

Shiru tayi cikin tunanin chanjin salo

Aikuwa suna hanyar komawa gida a saman titin gada,aka turo katafila tazo zata kutsa ta gefensu ta hankadasu qasa ,motar anan take tayi falle falle,kowa Na motar ya mutu har kuyangar,itakuma rudewa ya juyar mata da qwalwa,ta dawo ba uhm,ba um um.


Tunda wannan abun ya faru quliya sha'anin Mulki ya fice mai aka ya ajiye muqaminsa yace a ba kawunsu ,ya dawo Nigeria ,in kin gansa a madina yaje duba sophy ne...

Ta kwashe shekaru hudu tana jinya,kafin a wannan rutsutsin ta yi lafiya ,wannan shine dalilin zuwansa madina kuma...

*Afwan Na rashin update da wuri,jikina yaqi dadine,saida naje asibiti,na sake amsan sabon treatment amma ynx alhmdllh*
75&76
*Alheri writers asso.*

Ummi kam,gajiya da tunane tunanin ta ,tayi ta fara dan gyangyad'awa ,aikuwa karaf ba zato ba tsammani taji hannu dan bawanka akan cikinta ,zillo tayi ta gwale duk idon ta ,ta zuba masa su cikin alamar tsoratarwa

Shegen sama,maimakon ya tsorata kurum sai ya hau yi mata murmushi yina gyada mata Kai ,sannan yina yunqurin Kai hannunsa ,saman tudun qirjinta

Aikuwa cikin zafin nama ta fincike hannunsa tayi jifa dashi gefe sannan,kuma batayi wata wata ba ta kifesa da mari,wanda saida yaga gilmawar wasu tartsatsi ('

A gigice ya dafe wajen kafin yace "Ni kika mara??"

"Qaramin dan Tasha ,ashe kanajin Hausa ? Da ka isheni da larabci,wannan kadanma nayi maka nagaba in nayi maka saina sauya maka kamanninka,don harda mahangur6a zan hada maka"

Lumlumshe idonsa ya kamayi ,yanda take magana zafi zafi ba qaramar qara masa shauqinta yikeyi ba,komai nata abun burgewa ne,maganarta komunta sanyi sanyi
Sosai baiso ta daina tsiyan ba,don haka a jikinsa yaji inama ya qara takalota,koda zata qara kwasa masa wata Marin ,indai zatayi magana yaji sanyi a ransa?

"kina da kyau"

Ya fada cikin wani murya mai tarwatsa qwalwar en mata

"Kai kanada lafiya?" Ta fada tana zaro masa Ido

Dariya ya kwashe dashi harda tafa hannu "yes Na fada maki abunda ke raina ne,and maganar gaskiya I've much sha'awa on you"

Daura hannu aka tayi sannan tace Na shiga uku,na hadu da kwarto" duk zaton ta a sirrance tayi maganar ashe a bayyana ne.

"Ah Kar kiyi mun sharri ,nace miki bude mun tsuliyarki in tsotsa? Ko Na baki gindina nace kisha,daga nace kinada kyau?"

Wawwaige waige ta kamayi ko'ina a lullu6e da labule bamai iya ganinsu ,ga qaran kidin larabawa da ya cika motar Na tambarin gidan sarautar


"A'uzubillahi minash shaidanir rajim, Allah ya la'anci shedanin da ya hauro kanka yikeso ya sanya maka kallon lalata a matsayina Na matan dadynka"

"Haba wai ya kuke haka ne mata,Ana fa d'aukan haqqin oga shaid'an ,komai in akayi ace shaidan,no! Kawai maganar feelings ne,in kinyarda muyi abinmu cikin sirri zan tanajeki da kyakyawar masauki ,tamkar yanda kike me kyau"

Ca6e baki tayi batareda ta tamka sa ba ,lallai d ake cewa balaraben mutum yafi kowa shagala ashe da gaske ne

Hannunta ya kama ya fara murzawa a hankali

"Babae say something" a hassale ta dad'a d'aga hannu zata wankesa da mari,kurum sai sukaji tsayuwar motar su ,wancakali tayi da hannu wani hawaye Na cika mata kwamin Ido

Shikuwa da sauri ya dafe Kai alamar baiso aka kawo ba

Amma Allah ya kaimu dare zan bibiyi makwancinki,tabbas dole in dandani zumarki.


Qofarsa aka fara bude mai,saida ya gama zuba Mulki sannan ya fito ,tabbas sarauta ba qaryaa ba,a haka kamar Na Allah,amma a gefe guda tantiri ne
Cewar ummi da ta shiga rud'ani.

Itama wasu mata sukazo suka fiddo ta aka rankaya zuwa cikin tafkeken masarautar ,wanda duk dakiyar ummi er qauye ta Zama
"Shikuwa quliya me yake tsinta a Nigeria,da ya gwammace Zama a can da ya zauna a wannan gidan tattashin da tarin bayi da dukiya? Gabadaya matakalar qofar da zaikaika dakin sarauniya safiyya kuwa kwalliya akayi masa a dadda6e da zinare ,abun gwanin ban sheqi ,haka suka shiga anata lale da zuwansu har kowa ya zauna a mazauninsa ,quliya watsa idonsa yayi ya sauke akan ummi,aikuwa caraf idonsu ya sarqe,ta kuwa Galla masa harara
Matse gira yayi ,irin. Alamar tambaya lafiya dinnan
A maimakon tayi wani respond saita murguda masa baki.

Ai a fujajan yazo ya tashi Adnan dake kujeran daf da ita,ya zauna sannan ya rafka tagumi ya saka bakinsa cikin tafin hannunsa

"Zinariyata me nayi maki?"

Adnan ji yayi kamar ya shaqe quliya,don Allah ji wani son rai,gamu matasa masu jini a jika,muna buqata ku iyayenmu Ana rububida ku?...mtseww yayi tsaki a zahiri ya miqe

Hakan shi ya jawo attention din kowa Na wajen ,ciki harda quliya

"Son me ya faru ne kuma ? Banson wutan ciki?"

"Gajiya" ya bashi amsa gamida tsallake qafa yabar dakin da duk aka hadu za'aci abinci akuma tarbi su quliya ,tarba Na musamman.

D'an tsam yayi da rai kafin ya maze "zinariyata yadai ko gajiyar hanya ne?"

"Uhum kaina ke ciwo"

Gigice wa yayi nan take kamar wanda aka fada masa wani abun tsoro

Da sauri yakai hannunsa goshinta "ayyah ga zafi"


"Heyyy iynt ,ilal mustashfal aln" ya ya fito wata servant ,wai su wuce asibiti ynx


Tsam sophy ta taso tazo ta dafe kan ummi cikin kulawa "ma asa baha?"(what's wrong with her?)

Kafin yayi magana tace "eyyah seems headache,sorry ladaina d'abib ,sa atiy huna bissur'a,l a takhaf".

(Eyyah gayinan kamar ciwon kaine ma,bakomai ai muna da likita zai zo nan da sauri ,karka damu)

Ta kamo ummi suka miqe ta wuce da ita dakinta ,sosai quliya yaso a barsa da matarsa,amma Ina surukutan Hausa /Fulani ya shigesa bazai iya binsu dakin qanwarsa ba


A katafaren gadonta ta shimfideta ta rage mata kayan jikinsa,sannan ta kawo mata ruwa me sanyi da dan shayi me Zuma
Ta warware mata a.c
Da turanci tayi mata magana "ki Sha shayi kinji,sai kiyi wanka ,ki sa kaya matasa nauyi kafin likita yazo,allahu yashfik"(Allah ya baki lpy)

Gyada mata Kai kurum tayi don ba duk yaranta take jiba ,qalilan qalilan dai=??

A sanyaye ta kafa dan ficilin Kofin shayin na tangaram a bakinta,zuciyarta Na tuna mata Adnan da halayyarsa,mafarkanta dashi yina mata gizo ,ai unknowingly taji tashin ziciya

Da gudu ta dirka a gadon tana ware waren neman toilet

Zuwa tayi ta rungumeta

Me ya faru menene ?"

Ta kasa magana saboda aman da ya taho mata,da sauri ta rimtse bakinta tana mata isharan amai amai

Ai kafin sukai toilet ta fara kelaye amai ,kaf saida ta fidda madaran da Tasha a jirgi,haka take fidda numfashi sama sama tana kakari

Shafa mata baya ta shagayi bata damu da 6atata da tartsatsin aman da tayi ba


"Sannu matar yaya ,sannu kinji

Ruwa ta bata ta wanke baki ,sannan ta barta tayi wanka ,ta Kira hidimai suka gyara wajen ,nan danan ya dau qamshi kafin ma ummi ta fito wankan ,ai kwashe kayan ta da na sarauniya safiyya da ta 6ata, an bardasu gidan .wata sassauqar jallabiyya milk me jiki tattausa aka bata ta saka, ta fito da nufin ta kwanta,saidai kamshin turaren dakin Kansa tashuwar zuciya take ji


A take kanta ya buga "to meye haka daga zuwana qasan mutane zan qazantasu da laruran amai,wai ma me ya jawo min?

Falon ta ta fito da sauri ta bar bedroom din

Suna zaune da barorinta a gefenta tayi sauri ta taso ,ta kamo ta ta zo suka zauna a rungujejiyar 3 seater dinta da take ,tana Zama ta daura kanta akan cinyarta tana shafa kanta wani barci barci Na fizgarta me tsananin dad'i ,cikin abunda baifi 5 second ba kuwa barci ya sureta


Shigowar likita yasa quliya jin haqurinsa ya qare ,ganin shiru shiru basu fito ba ,yakuwa biyo bayan likitan


Yina hangen matarsa er d'agwas a cinyar qanwarsa ,tayi wani ru6u ru6u gwanin sha'awa ,tashin ta tayi ta hanyar dunga shafa mata kumatu tana kiran "kulthoom" a hankali ta bude Ido

Quliya yace "zinariyata ya jikinki"
Shiru tayi sannan tayi kwa6a kwa6a kamar zatayi kuka

"Ayyah yi haquri ga likita zai dubaki zakiji sauki "

Kya6e fuska tayi cikin shagwa6a sannan ta gyada masa Kai alamar gamsuwa

Adnan dake dab da shigowa,dakatawa yayi yina kallon wannan abun ban haushin kurum da rufaffen Ido ya juya yabar wajen ba tareda sunga zuwarsa ba,zuciyarsa Na azalzalarsa da mugun sonta ,wanda ya kasa tantance menene ,shin sha'awa ce ko qaqa? Amma tabbas inajin tsananin kishin dady akan watannan er tsanan babyn...
81&82Bonus page
*Alheri writers asso.*

Oum Aphnan
'?
*Paid book @ #200 regular ,v.i.p #400 ,via 7782217014 , Mohammed Hassana fcmb,or MTN card via 09065990265*



Resuscitation, akayiwa driver din ,shikuwa kasantuwar quliya famous mutumine da kowa ya sanshi ,nan Da nan rasuwarsa ya gama kewaye gari ,da yanar gizo .

"Allah sarki ne ,halinka Na gari ya cimmaka dadyna!" Ya fada yina rufe saman fuskarsa da mayafin asibitin da aka rufe quliyar da shi

A galabaice yaja wani irin wahalallen ajiyar zuciya ,yayi baya kamar zai fita,likitocin Na dafe dashi,kurum ba zato ,ya dawo da gudu ya qanqame gawar yina girgiza shi

"Dady me yasa kaimun haka? Kaine gatana dady why...ka fada mun abunda kace kana son ka fada mun " kawai sai ya fara dukan goshinsa akan qirjinsa, da qyar aka 6an6are adnan a kan sa...tundaga nan adnan bai kuma sanin inda kanta yikeba har danginsu Na saudiyya sukazo .

Sarkin kano shi ya Kira mai unguwa aka shaida masa mutuwar quliya ,saidai ance ayi hankali da ummi kasantuwar tanada juna biyu.

Hajjo da uwale suka tafi gidan gaisuwar,ummi Kam tunda quliya ya rasu kamar ya tafi da cutar haukan ta ,ta dawo garau ,saidai wani azababben laulayi ke dawainiya da ita kullum barci ,sai son abincin gargajiya much more fatan tsaki ,Haka umma za tayi mata yaji zogale da tantaqwashi ,ta zuba ,manshanu ko kakide.

Saidai abu daya yike bata mamaki yanda Sam ,quliya tsawon kwana 3 bai kirata a waya ba ,amma ta kasa fadawa ummah saboda kunya,su kuwa matan gidan da suka tafi gaisuwa bata damu da sanin Ina suke ba ,tunda tasan ba mazauna bane da ma.


Saida akayi sadakan uku kafin Adnan ke iya Zama Ana kar6an makoki dashi ,Sunga kara da jama'a ba adadi qasa qasa ,saidai sofy dukda kasancewarta ba bahaushiya ba ita ta kasance mace a cikin gidan .

Su hajjo kuma suka zauna a dakin ummi suma suna kar6an makoki ,in anzo nemarta sai ace itama taje gida jinya ,har yanzu batasan rasuwar ba

***
Ranar da quliya ya kwana goma da rasuwa ,a ranar dangin Adnan ,dasu hajjo suka biyo jirgi suka taho gidan su gabadaya

Ummi tana zaune a falo tana cin dan wake da yajin tafarnuwa sai zan yaji take yi a bakinta tana shan ruwa ,saiga sallamar baqi ,cak ta tsaya ganin larabawan dangin mijinta harda wanda bata sani ba ciki kuwa harda adnan

Murmushi tayi tana masu barka da zuwa da turanci ,su kuma su hajjo nan da nan suka kawo masu ruwa da lemu aka baza masu sababbin tabarmi Na auren uwale da za ayi .

Sunji dad'in tarban da akayi masu

Sofy a nutse ta saka ummi akan cinyarta tana shafa bayanta

Shiru ummi tayi amma haka kurum taji zuciyarta yina tsinkewa,ya nagansu dukkansu amma ba Mijina ?

Qyam ta tsaida idonta akan adnan da taga kamar har ya fada ,kuma yayi zuru zuru kamar firgitacce

"Adnan Ina dady??" Ta fada kamar wanda aka tursasata ,ta qwato maganar a bakinta .

Kallon kallo aka fara yi ,ba mai zarran bata amsa .

Ganin dakin yayi tawai tawai yasa zuciyarta yankewa ya fadi

"Adnan kay??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i mun shiru!" Wannan karon cike da tsawa da kakkausar lafazi tayi maganar .


Sofy da bata fahimci komai ba face Kalmar "Dady" da kuma "Adnan ".sosai ta fahimci tana tambayar adnan ne


"Ummi, Accept our condolences anty , we're sorry on behalf of late Elkabeer Ahlan musannah's Relatives and family..." Ai kafin ta qarasa maganar ta ummi ta saki wani gigitaccen qara ta miqe tana fizge fizge kafin tayi yuuu ta fadi rim sumammiya.

Tabbas ta fahimci so ake a ce mata quliya ya mutu ,to kafin a fada mata hakan gwara ta bishi .


Adnan da kansa ya miqe ya 6alle hancin

Ruwan da ke a gefensa ya kamota yina shafa mata ruwan a fuska ,wani ajiyar zuciya tayi tana sambatu "saida su Adama ,Nnenna da Abike suka kashe mun miji ,sannan hankalin su zai kwanta,Ban yafe maku ba ,kun gotarmun da gatana ,kun maida yaron cikina maraya ,Allah..allah kabi mun haqqina a kan ku!"

Umma ra6ewa tayi tana kallon innocent yarintarta tana shararar da hawaye

"Ya Isa ummi,Ba wani ya kasha dady ba ,Allah da yafimu sonsa shi ya kar6esa to ya zamuyi sai haqury mu kuma raini abunda ya bari"

"Wayyo Allah Na,adnan kace mun bai mutu ba"

"Ya Rasu!"

"Ina yike ,zan masa magana ,inaso in masa magana xakuga ya tashi bazai tafi ya barni ba..."

"Sorry ummi ,Elkabeer yina kabarinshi over 10 dayz "

"Baku fada mun ba sai yau! Saboda ni ba kowa bane a wajensa!"

Ansha artabu da ummi kafin asha wo kanta ,da ance kaza zata juya tace kaza

**
Dangin quliya da adnan suka bar Nigeria,rabon gado sai ummi ta haihu anga abun da ta Haifa ,tunda quliya ya mutu ba da ba mata sai ummi kadai,iyayensa kuma sun rasu saura en uwa ,din haka dole a jira ta haihu aga mace ne zata Haifa ko namiji


***
Ummi Sam batada nutsuwa ,abinci ta daina ci. Kullum azumi ,in an magana tace ai ko bata yi azumin ba bazata iya cin abincin ba gwara ma tayi.
Tun Ana biye mata har suka qyaleta don sun San mutuwar mijinta ke ta6a ta.


A haka bikin su uwale ya qaraso ,saidai ummi Sam ta hana en gidansu sukuni da sun shirya zasu fita yawon barikinsu zata dauko makami ta coge a qofa ,dole fita ya fasu,tunaninsu hauka ya motsa Don haka mai wada a qagauce yake ayi ayi biki ko ya samu ya ke6e da uwale don kwana biyunnan ya wujijjiga da kewarta,gashi matarsa abun sai a hankali ,a cewarsa .

Hajjo Kam sau uku Ana daidaitawa da samari kamar za ayi aure sai en Gaza gani in sunji labari su soke,yanzu hakan ta tattaro ta dawo gidansu ,don wulaqancin gidan kawunsu ya isheta ,ashe zata hadu da masifar kullen ummi , da qaryan hauka!


***
Alhmdllh duk abunda aka sanya masa rana to la shakka zai zone


A yau jumu'a tururuwan jama'a suka shaida daurin auren Alhaji maiwada da Uwale akan sadaki naira dubu saba'in ,sai dai muyi masu fatan dawwamammen zaman lafiya

Da yike aure da tarewa ne a hade ,shi yasa aka zarce da yinin biki a gidan su uwale ,en Kai kara,suka wuce jere wanda kayan gadon da set din kujerun duk Na ummi ne.

Daki Kam ya qawatu ba qarya,tunda ba kowa ma zai gane ba sababbi bane ba

Qarfe 8 Na dare akazo daukan amarya , shikam maiwada yina zaune a sitting room din sa dake kallon waje ,shida abokansa yina kallon shedanun qawayen uwale da suketa shigowa gamida cika gidan da guda, harda en daudu,wannan kuwa tawagar hajjo ne ,suka gama bidirinsu ,masu rabon samun new catchers anan suka Dane motarsu suka warwatse ,zuwa qarfe Tara da rabi kowa ya watse ,tunda bikin na bazawara ne kowa yasan ba'a kwana .


Uwale Kam suna fita ta warware kayan jikinta ta daura towel ta fito sashen ta tundaga bakin qofa ta ringa binshi da kallo tana tasbihi a ranta "oh alhmdllh ,ni uwale ashe da rabon mu ta6a ,yau nine a wannan gida ! Me haquri ke cimma rabo " saida ta kakkawar da abubuwan da aka 6ata mata ta ,qalailaye ko Ina ta feffesa room freshener ,sannan taje ta zare maganin matsin da ta saka da auduga ta wanke da ruwan dimi,ta sillo wanka a qasaitaccen toilet dinta ,ta Dada matsa Virginie cream dinta ,ta fito ta mulke jikinta da lotion me qamshi ,ta murza turaren humrah masu qamshi ta saka chewing gum me kamshi

Wata damammen fitted

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login