Showing 1 words to 3000 words out of 8928 words

Chapter 1 - Rijiya Gaba Dubu Book 1 by Madakin Gini.pdf

RIJIYA GABA DUBU 1
Saurayin gudu yake iya karfinsa acikin dajin domin ya ceci rayuwarsa,yana gudu yana waigen
bayansa cikin tsananin tsoro,amma baya ganin komai kuma baya jin sautin komai face na
masifaffun karnukan dake biye dashi.
Su dai wadan nan karnuka sun kai guda saba in da doriya kuma sun kasance jibga jibga tamkar
ba karnuka bane kai kace kurayene sabo da girmansu da kwarjininsu gami da ban
tsoro,musamman aka kiwata wadan nan karnukan kuma aka basu horo na musamman domin
suyi gadin babban kurkuku na birnin Kisra. A tarihin birnin na kisra tunda aka gina kurkukun tsawon shekaru arba in ba ataba samun
fursuna da ya taba guduwa daga cikin sa ba sabo da karfin tsaron da ke cikinsa sai wannan
saurayi wanda ake kira IMHAL IBN IMZANU,sabo da tsananin karfin gudun Imhal ne ya baiwa
karnukan tazara ta kimanin taku sittin amma sabo da nacin karnukan da mugun horon da suka
samu sai gashi sun fara hango shi,nan fa suka kara kaimi,nan fa Imhal ya kara kaimin gudunsa
alokacin da ya waigo ya hango su yaci gaba da falfala azababben gudu ta cikin kwazazzabai da
sarkakiya,sabo da karfin gudun ma har tashi sama yake yana tsallake duwatsu da karyayyun
bishiyoyin da suka fadi kasa.
Shi dai Imhal gudun kawai yake yi acikin dajin amma baisan inda yake dosa ba,sabo da baisan
ma a inda yake ba bare ma yasan hanyar da ya kamata yabi, a duk sanda ya tuno da bakar
wahalar da ya sha kafin ya sami nasarar guduwa daga kurkukun sai ya kara kaimin gudun nasa
yana mai ayyanawa a ransa da dai a kamasa a raye a mai dashi cikin kurkukun gwara a sami
gawarsa sabo da azabar da take cikin kurkukun ta wuce tunanin mai tunani.
Asalin Imhal bin Imzanu mutumin birnin misira ne kuma shi ba dan kowa bane kuma bai aikata
laifin komai ba,mahaifinsa wani makiyayi ne mai kiwon dabbobi a daji,don haka rayuwar Imhal
gaba daya a cikin daji take,sai dai a karshen kowane sati ranar Lahadi sukan shiga cikin gari
suyi dan siye-siyen su sannan su koma daji inda suka gina bukkarsu. Imhal ya taso da Jarumtaka juriya da iya farauta,sanan komai yawan dabbobi idan ya tafi kiwo
dasu yana iya sarrafa su.
Lokacin da Imhal ya fara girma ya cika shekaru goma sha shida ne ya tambayi mahaifinsa
tsoho Imzanu yace ya kai Abbana me yasa baka taba bani labarin mahaifiyata ba?ban santa ba
kuma bansan yanda akayi ta mutu ba kullum sai kace dani kawai mutuwa tayi,kayi sani cewa
yanzu ni ba yaro bane karami na mallaki hankalin kaina yakamata ka sanar dani gaskiyar al
amari,koda tsoho Imzanu yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yayi shiru yana
mai sunkui da kansa kasa,kawai sai idanunsa suka ciko da kwalla hawaye ya fara zubowa kas,
a sannan ne ya dago kai ya dubi Imhal yace yakai dana kasani yau ka tambayeni wani sirri
wanda dama nayi alkawarin bazan sanar dakai ba sai bayan ka mallaki hankalinka,don kada
hankalinka ya dugunzuma kwakwalwarka ta kasa daukar al amarin, koda imzanu yazo nan a
zancensa sai ya sake yin shiru kamar bazai ia cewa komai ba,da kyar ya ake dago kai ya dubi
Imhal muryarsa na rawa yace ka gafarceni yakai dana bisa abinda zaka ji daga bakina yanzu
domin zakayi matukar mamaki kuma zai iya girgiza ka,maganar gaskiya ita ce ni ba mahaifinka
bane na jini,koda jin wannan batu sai zuciyar Imhal ta buga da karfi,nan take idanunsa suka
kada sukayi jawur,bai san sanda hawaye ya zubo masa ba yace yanzu idan ba kaine mahifina
ba to wanene? Bansan kowa ba a rayuwata sai dai kai kadai,kaine kasan cina da shana
tundaga kuruciyata har izuwa yanzu,me yasa uban nawa ya gujeni ya barni a wajanka cikin daji

inda babu jin dadi da tsaro?lallai kuwa ashe babu soyayya tsakani na da uban nawa tunda bai
damu da rayuwata ba.
TO JAMA'A KUYI MIN AFUWA SAI NA HUTA ZAN CIGABA.
RIJIYA GABA DUBU 1 Cigaba1
Koda Imhal yazo nan a zancensa sai tsoho ya zubar da hawaye sannan yace Ni kaina bansan
waye mahaifinka ba,ka saurara dakyau kaji labarin da zan baka yanzu,wata kila idan kaji labarin
zuciyarka tayi sanyi ka rungumi kaddara a bisa halin da ka tsinci kanka a ciki.
Wata rana da safe na fito kiwo acikin dajin nan ina kada dabbobi na sai kawai na hango wasu
mutane bisa keken doki sanye da bakaken tufafi kuma sun rufe fuskokinsu su biyu sun nufi
bakin wani katon rami mai zurfi da fadin gaske,cikin hanzari na kada dabbobina izuwa cikin
duhuwar bishiyoyi nima na sami wuri na buya,dama wadannan mutane basu ganni ba,ina nan
labe cikin duhuwa sai naga wadannan mutane sun fiddo gawar wata mace daga cikin keken
dokin sun cillata cikin wannan ramin,kawai sai suka shiga cikin keken dokinsu da sauri suka fice
daga cikin dajin gaba daya,sai da na tabbatar da cewa sunyi nisa da tafiya kuma babu alamar
cewa zasu dawo sannan na ruga izuwa bakin wannan ramin na leka cikinsa kawai sai naga
ashe wata kyakkyawar mace ce aka yanka ta har a sannan jini na bulbulowa daga cikin
makogwaronta kuma tana dauke da tsohon juna biyu,nan take naji na kamu da tsananin
tausayinta,don haka sai na yanke shawarar na shiga cikin ramin na dauko gawar wannan mata
domin na suturta ta sosai na haka kabari mai kyau na binne ta,idan ma na barta acikin ramin
zata rube ne warinta ya dameni tunda ramin yana kusa da inda bukkata take,nan fa na fara
tunanin dabarar da zanyi na iya shiga cikin wannan rami har na iya dauko gawar,sai da nayi
tunani na tsawon 'yan dakiku sannan dabara ta fado mini,kawai sai na ruga da gudu izuwa cikin
bukkata,na dauko igiya mai tsawo sannan na dawo bakin ramin,na daura igiyar a jikin wata
bishiya na wurgata cikin ramin sannan na kama igiyar ina binta ina shiga ramin,sannu a hankali
na isa kasan ramin,koda naje kan gawar na duba ta sai naga ashe da ranta bata mutu ba domin
numfashinta na fita kadan-kadan,cikin gaggawa na sunkuci wannan mace na goya ta a bayana
na daureta tamau,na sake kama igiyar nayi iya kokarina na fito daga cikin ramin goye da matar
a baya na,hankalina a dugunzume,sauri nake kawai na jarraba ceto rayuwarta,ina fita daga
cikin ramin na ruga da ita izuwa cikin bukkata,na shimfide ta a kasa sannan nayi sauri na dauko
allura da zarin dinke fata na dinke raunin wuyanta sannan na shafa magani akan raunin,A
sannan ne na kara hancina a dai dai hancin matar don naji ko tana yin numfashi,amma sai naji
shiru alamar babu rai a jikinta,nan fa bakin ciki ya lullube ni naji kamar na fashe da kuka sabo
da takaici,gashi nasaa wahalar dauko ta daga cikin wannan ramin mai zurfi har ma tafin
hannuwana sun dade saboda kama igiya,cikin sanyin jiki na mike na sunkuya da nufin daukar
gawar na fita da ita waje inda zan binne ta,kawai sai naji tayi tari,numfashinta ya dawo,nan take
murna ta kamani na ruga na dauko wani ruwan magani na dura mata a baki dakyar tasha
mukurwa uku,jin kadan sai idanunta suka bude dakyar,koda tayi arba dani sai naga ta firgita ta
yunkura zata tashi amma sai na danne kafadunta na hana ta tashi,matar ta budi baki da nufin
tayi magana sai ta kasa,kawai sai naga tana dariya,wani lokacin kuma sai ta hade fuska ta
kama kuka tana fisge-fisge,nan fa na gane lallai wannan mata ta samu tabin hankali,al'amarin
da yayi matukar bakanta raina kenan domin naso ace ta iya yin magana acikin hankalinta,domin
na tambayeta ko ita wacece da kuma wadannan mutane da suka kawo ta dajin acikin keken
doki a matsayin gawa,abinda zuciyata ta aiyana min shine in ma basu bane to sun san wanda

ya kasheta,kuma akwai wani boyayyen al'amari akan kisan nata,daga wannan rana naci gaba
da jinyar wannan mata har tsawon kwana ashirin da daya,A tsawon wadannan kwanaki kullum
a kwance take kuma koda tayi yunkurin mikewa zaune sai ta kasa sabo da raunin da yake
makogwaronta,haka kuma bata taba yin magana ba sai fisge-fisge da dariya irinta
mahaukata,abinci kuwa sai dai na dura mata abaki tana ci tana kuka sabo da ciwo,da yake
naga tana dauke da juna biyu sai na dinga yawan bata madarar shanu gami da abincin da yake
gina jiki domin abinda ke cikinta ya samu cikakkiyar lafiya,a kwana a tashi har wannan mata ta
shafe wata uku cur a wajena,a sannan ne raunin makogwaronta ya warke sumul har ya zamana
cewa tana iya magana sosai,amma a koda yaushe babu magana ta hankali da nutsuwa a tare
da ita sai maganganu irin na mahaukata,nayi iya kokarina akan ta gayamin ko ita wacece,daga
inda take da kuma yadda akayi ta shiga wannan hali sai tayi ta kyalkyala mini dariya,ganin
hakane yasa tausayinta ya karu a zuciyata,sau bakwai ina nemo masana ilimin maganin
mahaukata,wato likitocin mahaukata suna zuwa su dubata kuma su bata magani,amma duk a
banza lafiya taki samuwa,sau tari matar takan sulale ta nausa cikin daji bansani ba,sai nasha
wahalar nemota,bisa wannan dalilin ne ma duk sanda zan fita kiwo ko farauta sai na tafi tare da
ita,wato na daina barinta a gida.
TO JAMA'A AYIMIN AFUWA SAI NA HUTA ZAN CI GABA
RIJIYA GABA DUBU1 CIGABA 2
Lokacin da cikinta ya tsufa sai tafiya da ita kiwo ko farauta ya gagara,don haka nima sai na
hakura da zuwa ko ina,na tanadi abincina da na dabbobi na mai yawa wanda zai kai tsawon
kwana arba in,Ai kuwa adaren kwana na talatin da bakwai nakuda ta kama wannan mata acikin
tsakiyar dare.Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalina kenan tunda babu halin in ruga
cikin gari in nemo ungozoma,Da yake na taba shiga irin wannan hali da nake tare da matata
wacce ta rasu a wajen haihuwa abinda ta haifa ma yazo a mace,sai na shiga taimakon wannan
mata,nine na yankewa jaririn cibiya,na wanke shi sannan na kimtsa mahaifiyar tasa,matar taci
gaba da rainon jaririnta tana shayar dashi ni kuma ina cigaba da fita farauta da kiwona ina
barinsu a gida,har tsawon shekara daya da wata bakwai muna tare sannan yaron ya fara tafiya
da kafafunsa.
Kwatsam wata rana naje kiwo na dawo sai na nemi wannan mata sama da kasa na rasa,kuma
ga dannan ta bar shi acikin bukka a zaune shi kadai yana ta tsala kuka,cikin dimaucewa na
dauki yaron na gaya shi a bayana sannan na bazama neman wannan mata wacce ko sunanta
ban saniba bare na dinga kwalla mata kira,Abu kamar wasa sai da na shekara daya da wata
tara ina nemanta amma ko alamunta ban gani ba acikin wannan daji.A tsawon wannan lokacin
ni nake kula da wannan yaro da ta haifa dare da rana,ya zama cewa na shaku dashi ainun
shima haka
.Kwatsam wata rana da yammaci ina wasa da yaron a kofar bukkata kawai sai na hango
wannan mata daga can nesa ta durfafo bukkata,cikin alamun tsananin mamaki na mike tsaye
na zuba mata idanu,matar ta rame matuka,kuma duk rigar jikinta ta yayyage,sannan tayi baki
sabo da wahala da kazanta,koda ta iso daf dani ta dubeni sai ta fashe da kuka ta durkusa kasa
bisa gwiwoyinta tana mai neman gafarata tamkar mai cikakken hankali,nan take naji na kamu
da tsananin tausayinta don haka sai na kama kafadunta na tasheta tsaye kuma na rungumeta a
kirjina a karon farko tun haduwa ta da ita,ita kuma sai ta kankame ni ta da da fashewa da
kuka,kawai sai na janye jikina daga nata na dubeta nace me yasa kika gudu kika barmu?shin

kin manta ne cewa kin bar danki a hannu na?koda jin haka sai matar ta dubi dan nata ta girgiza
kai tace ai ni kananin yaro na bar maka bai kai wanan girma ba,da jin haka sai nayi dariya nace
to ai kullum mutum dada girma yake har yanzu baki gaya min inda kika tafi ba kika barmu,Matar
ta bushe da dariya sannan ta hade fuska tace shan iska na tafi na sake dawowa.Cikin tsananin
damuwa nace yau shekara hudu kenan muna tare baki taba gaya min sunanki ba kuma baki
gaya min sunan garinku ba bare nasan asalinki da danginki shin bakya tausayin wannan yaron
da kika haifa ne?Koda jin wannan tambaya sai matar ta sake bushewa da dariya tace bansan
kaina ba kuma bansan kowa ba sai kai,tana gama fadin haka ta juya ta shige cikin bukka taje ta
kwanta ta kama bacci,tun daga wannan rana muka ci gaba da zama tare,amma ko kadan
wannan da nata bai dameta ba,kuma bata yi masa komai sai dai ni nayi masa,wani lokaci sai
naga kamar hankalinta ya dawo tana magana a nutse,amma da zarar na fara tambayarta
asalinta da garinsu sai ta birkice ta koma hauka.
Wata biyu da kwana uku mukayi tare ranar kwana na ukun ne matar ta wayi gari da tsananin
rashin lafiya wadda bansan sanadinta ba,cikin rudewa na shiga hada mata magunguna iri-iri ina
bata tana sha amma duk a banza tamkar kara mata ciwon akeyi,kawai sai naga idanunta sun
fara lumshewa kuma numfashinta na sarkewa,Al amarin da ya dugunzuma hankalina kenan na
fara zubar da hawaye,na shiga yi mata tambayoyi akan ta sanar dani asalinta,matar na kokarin
bude baki tayi magana amma sai ta kasa,nan take jikinta ya sandare,idanunta suka kafe ta
daina motsi.koda naga haka sai na rungumeta na fara kuka,ganin ina kuka ne dannata wannan
yaro dan shekara kusan hudu ya rugo izuwa kaina shima ya fashe da kuka.Hakika wanan rana
nayi kuka mai yawa sabo da shakuwar da nayi da matar nan sai da nayi kwana ashirin da daya
bana iya cin abinci sosai,amma koda yaushe hankalina yana kan wannan yaron ina kula da
lafiyarsa sosai.
Koda tsoho Imzanu yazo nan a zancensa sai Imhal ya tari numfashinsa suka dubi juna a lokacin
da kowannensu yake zubar da hawaye yace yakai Abbana na gane cewa wannan yaro da
mahaukaciya ta haifa ba wani bane face ni dinnan,tabbas yanzu na tabbatar da cewa ni
marayane wanda bashi da uwa bashi da uba kuma wanda baisan asalinsa ba,koda Imhal yazo
nan zancensa sai tsoho Imzanu ya rungumesa suka fashe da kuka tare,can sai Imhal ya janye
jikinsa suka fuskanci juna ya dubi Imzanu yace Bazan taba yarda bani d uba ba amma ni kai na
sani a matsayin ubana,ina son nayi maka wata tambaya guda daya menene dalilin da yasa
kake kirana da suna IMHAL?
TO JAMA'A NIMA NA GAJI IDAN NA HUTA ZAN CIGABA DAGA MAI SON NISHADANTAR
DAKU COMBATANT33
RIJIYA GABA DUBU1>CIGABA3
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa tsoho Imzanu yace Abinda yasa nasa maka
suna Imhal shine a iya zama na da mahaifiyarka har ta mutu ban taba jin ta ambaci sunan wani
mahaluki ba face IMHAL,A kullum duk sanda za taci abinci sai naji tana kiran sunansa tana
cewa yazo suci abincin tare,abinda na fahimta shine,koma wanene wannan Imhal din lallai ya
kasance babban masoyi a gareta,zai iya kasancewa mijinta ne ko dan uwanta ne ko
mahaifinta,Abu na biyu da nake zargi shine,duk yadda akayi mahaifiyarka ta fito daga babban
gida domin a ranar da na tsince ta acikin wannan katon ramin mai zurfi sutturar dake jikinta mai
matukar tsada ce,babu mai sanya irinta face sarakai da manyan attajirai,babban bakin cikina
shine babu wata shaida a tare da mahaifiyarka wadda zata iya sawa a gano asalinta,koda tsoho

Imzanu yazo nan a zancensa sai suka sake rungume juna,daga can sai Imhal ya dubi tsoho
Imzanu yace,Lallai zan rike sunana a zuciyata da bakina,lallai wata rana wannan suna zai
taimakeni na gano asalina.
Tun daga wannan rana Imhal da tsoho Imzanu suka cigaba da rayuwarsu acikin daji kamar
yadda suka saba,amma sai ya zamana cewa kullum sai Imhal ya shiga cikin garin Kisra kuma
duk inda yaje si ya tambayi mai suna Imhal,idan aka tambayeshi wane Imhal yake nema sai ya
kasa bayani domin baisan wata inkiya ba ta Imhal din da yake nema,hakane yasa suka dinga
yiwa Imhal dariya suna cewa dashi Bagidaje mutumin daji,saboda ganin yanayin shigarsa ta
makiyaya.
Wata rana Imhal yazo giftawa ta kofar gidan sarkin kisra akayi sa a kuwa a lokacin sarki ya fito
daga cikin gidan sarautar zai fita rangadi kwatsam sai yayi arba da sarki,Abinka da wanda
baisan yadda ka idar sarauta take ba sai kawai ya kurawa sarki idanu,maimakon ya zube kasa
gabansa ya kwashi gaisuwa,ai kuwa sai dakarun sarki suka afkawa Imhal da duka har suka kai
shi kasa,cikin fushi ya yunkura ya watsar dasu duka duk da cewar sunkai su ashirin,nan take
shima ya rufesu da duka,duk wanda yayi wa naushi daya sai ya baje a kasa sumamme,koda
ganin haka sai ragowar dakarun sarki suka zare takubbansu sukayi caa akan Imhal zasu
sassara shi,amma sai sarki ya daka musu tsawa suka saurara,nan take sarkin kisra ya sauko
daga kan dokinsa yazo daf da Imhal yadda har suna iya jin numfashin juna,sannan ya dubeshi
cikin murmushi yace,A duniya babu abinda yake birgeni sama da jarumtaka,tabbas na yarda kai
jarumi ne amma ina son na gwada jarumtaka ta akan taka,nasan baka san koni waye ba to nine
Sarkin garin nan,koda jin haka sai Imhal ya zube kasa bisa gwiwoyinsa yana mai sunkui da
kansa kasa yace ka gafarceni ya shugabana,kasan cewa ni rayuwata gaba daya cikin daji nayi
ta,sau daya a sati muke shigowa cikin garinnan,yau ne ranar farko da na fara ganinka a
rayuwata,ya shugabana kayi min afuwa domin bazan iya fada da kai ba,Koda jin wannan batun
sai sarki ya bushe da dariya ,lokaci guda kuma ya hade rai ya dubi Imhal cikin nutsuwa yace,ya
kai wannan saurayi ma abocin jarumtaka kayi sani cewa nahiyar nan gaba daya babu wani
jarumi ko mayaki mai karfi da iya yaki kamata,yau shekara talatin kenan ina gwagwarmaya da
gumurzu kuma sau arba in da uku ina lashe GASAR JARUMTAKA a kasashe arba in da uku
dake cikin wannan nahiya tamu ko sau daya ba a taba samun jarumin da ya lakuci jikina ba
bare ya kaini kasa,naga jarumtakar jarumai da yawa a rayuwata,amma ban taba ganin jarumi
mai zafin nama da karfin naushi kamarka ba,ina

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login