Showing 6001 words to 8928 words out of 8928 words
Chapter 3 - Rijiya Gaba Dubu Book 1 by Madakin Gini.pdf
rijiyar zaka samu hanya wadda zata kaika har izuwa kogon Ishmal dake can bayan
gari,daga nan sai ka nausa daji kayi kokarin ficewa daga nahiyar nan gaba daya,kada ka
kuskura ka dawo garinnan sai bayan anyi gasar Jarumta a birnin misra koda gama fadin haka
sai matar ta juya da baya,cikin sauri Imhal ya ruko hannunta,ta waigo ta dube shi cikin mamaki
yace mata mene sunanki? Matar yai murmushi tace mishi sunana ZUMAIRA IBINI IMHAL.Koda
jin wannan suna sai idanun Imhal suka zazzaro ya kasa sakin hannunta kuma a sannan ne
suka ji anbugo kofar gidan da karfi ta fadi rikica gaba daya,koda ganin haka sai matar tasa
kafarta ta doki kirjin imhal ya fada da baya cikin rijiyar,kawai sai ya nutse izuwa karkashinta,cikin
hanzari matar ta juya ta koma baya da gudu.Tana isowa falonta ta iske tsoho Imzanu zaune
akan teburin cin abinci yana shan ruwan Inibi kuma har ya sauya tufafin jikinsa,kuma ya sauya
kamanninsa domin ya shafe gemunsa da sajensa da shuni kamar bashi ba,wadansu karti
kimanin su arba'in na tsaye a gabansa daya daga cikinsu nayi masa tambayoyi,kawai sai
Zumaira ta dakawa kartin tsawa ta dube su tace,su waye ku akan wane dalili zaku karya mana
kofar gidanmu ku shigo?koda jin haka sai Dakarun suka waigo izuwa kan zumaira suna muzurai
kamar saci babu har sun zare takubbansu zasu afka mata sai daya daga cikinsu ya daga musu
hannu suka dakata sannan ya matsa daf da Zumaira ya dubeta a fusace yace muna neman
wani saurayi da wani tsoho mai furfura a gemunsa ki gaya mana gaskiya idan sun ahigo
gidannan kun boye su domin idan kuka yi mana karya kuma mukayi bincike muka gansu sai
mun kasheku,koda jin haka sai Muzaira tayi guntun murmushi tace ai sai ku duba ku gani,nan
take katti suka bzama ko ina amma basu ga kowa ba,sannan suka fice daga gidan gaba daya.
To jama'a kuyi min afuwa zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU1 CIGABA 8
Muzaira ta dubi tsoho Imzanu kawai sai taji ya fashe da kuka,al amarin da ya karya zuciyarta
kenan ta kamu da tsananin tausayinsa don haka sai ta dube shi tace Ya kai Imzanu ka kasance
mai gaskiya da juriya acikin duk irin yanayin da ka tsinci kanka aciki,koda jin haka sai Imzanu ya
dago kai ya dubeta cikin mamaki yace Ya akai kika san sunana?yayin da muzaira taji wannan
tambaya,sai nan take idanunta suka ciko da kwallah sannan ta dubi Imzanu tace Mahaukaciyar
da kayi jinya acikin daji har ta haifi wannan saurayi da kuke tare yayata ce uwarmu daya
ubanmu daya,kuma ita ce babba a wajen mahifinmu wanda shine sarkin kisra na da,kafin
azzalumin sarkinmu na yanzu ya kashe shi ya hau kan karagar mulkinsa.Gaba daya zuri armu
sai da sarki GURZALU ya kashe su,nice kadai nayi saura,nima albarkacin karfin sihirin tsafin da
nake dashine yasa na tsira da rayuwata,Ba wani abune yasa yar uwata ta haukace ba face a
gabab idanunta aka kashe mijinta Imhal aka yi masa yankan rago,sannan aka yanka iyayenmu
da dukkan zuri'armu,tana ganin wannan al'amari ne ta haukace nan take,amma duk da haka sai
da aka yi mata yankan rago akasa dakaru sukayi badda kama suka dauki gawarta suka kai daji
suka yar,Abinda yasa aka dauki gawarta aka kaita daji shine,Ramin da aka haka aka saka
gawar mijinta da ta sauran zuri'armu ya cika.Duk abinda ya faru da yar'uwata Shulaira na gani a
madubin tsafina,kuma duk naga irin dawiniyar da ka sha da ita shi yasa yanzu na taimake ku na
kubutar da Imhal,ina mai tabbatar maka da cewa Imhal ya kubuta daga sharrin sarki Gurzalu
domin zai fice daga cikin garin nan gaba daya ta cikin wata rijiya dake cikin gidannan.koda
Muzaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imzanu ya cika da tsananin mamaki gami da tsananin
bakin ciki,daga can kuma sai ya dubi Muzaira cikin alamun damuwa yace Ke kuwa mai yasa tun
yar'uwarki na raye a wajena a daji baki ziyarce ta ba,kuma me yasa yanzu baki gayawa Imhal
cewar ke kanwar mahaifitarsa bace?Muzaira tayi ajiyar zuciya tace Ai ina fita daga cikin
garinnan sihirin tsafina zai karye sarki Gurzalu ya gano inda nake ya turo a kashe ni,dalilin da
yasa ban sanar da Imhal ni uwace a garshiba shine,idan na gaya masa bazai tafi ba yanzu
kuma idan yaki tafiya ni dashi halaka zamuyi,koda jin haka sai hankalin tsoho Imzanu ya tashi
fiye da ko yaushe ya rasa abinda ke masa dadi a duniya.
Lokacin da Imhal ya nutse izuwa cikin karkashin wannan rijiya ya isa can kasanta sai ya kama
laluben hanya,nan da nan ya fara fita daga hayyacinsa sakamakon rashin numfashi,amma cikin
sa a sai yaga wani kifi yas shigo cikin rijiyar ta cikin wata kofa,cikin sauri ya kunna kai cikin kofar
sai ya ganshi akarkashin wani katon kogi,ciin sauri ya taso sama domin ya shaki
numfashi,aikuwa yana dagowa sama yaji an gabza masa duka da kulki a fuska,take jini yayi
feshi daga cikin bakinsa da hancinsa nan take ya baje a saman ruwa sumamme.
To jama'a ayimin afuwa wlh cajina ya kare zan cibaga ba da dadewa ba
RIJIYA GABA DUBU1 CIGABA9
Sa'adda Imhal ya farfado sai ya tsinci kansa acikin wani matsatstsen daki kwance a
kas,gefensa ga wani garjejen saurayi a zaune ya kura masa idanu,cikin dimaucewa da mamaki
imhal ya mike zaune zumbur ya karewa dakin kallo tsaf,sannan ya dubi garjejen katon saurayin
dake gabansa yace,Ina ne nan?Yaya akayi nazo nan?koda jin wannan tambaya sai katon ya
bushe da dariyar mugunta,maimakon ya baiwa Imhal amsar tambayarsa sai ya mike tsaye ya
damki makoshin Imhal da hannu daya ya daga shi sama tamkar ya daga sillan kara,sai gashi
Imhal ya fara kakarin mutuwa,kawai sai garjejen katon yaci gaba da kyalkala dariyar mugunta
sannan ya daga kansa sama yana duban Imhal yace,Kai yaro yau ka shigo kurkukun darul
maut na birnin kisra,kurkukun da ba a fita sai dai gawa ta fita kuma gashi kayi rashin sa a ka
shigo dakin dodon kowa a gidannan ZAUWADU,a dai dai wannan lokacine sauran fursunonin
dake cikin sauran dakunan gidan suka kama lekowa dakin Zauwadu domin suga mai karar
kwanan da aka kawo,ashe duk fursunan da aka kaishi dakin Zauwadu kawai so akeyi a kashe
shi,Ba zato ba tsammani kawai sai Zauwadu yaji Imhal ya gabza masa mugun duka a fuska da
kafarsa guda,Sabo da karfin dukan sai da Zauwadu yaga taurarin wuya bai san sanda ya
dimauce ba ya saki wuyan Imhal ya fado kasa yana tari,koda Zauwadu ya shafa fuskarsa yaji
jini sai ya fusata ainun ya juya bayansa inda Imhal ke kwance yana mai yin kururuwa kuma
yakai masa mugun taku da kafa,cikin bakin zafin nama Imhal ya goce ya mirgina can gefe daya
ya shammaci Zauwadu ya buga masa kafa akan marenansa,take Zauwadu ya sulale kasa
sumamme,koda ganin abinda ya faru sai gaba daya fursunonin gidan suka daina shewa da
dariya suka kame kamar gumaka sabo da tsananin mamaki,Ba komai ne ya jefa fursunonin
cikin tsananinb mamaki ba face ganin yadda aka samu jarumin da ya sumar da Zauwadu.Gaba
daya fursunonin dake cikin kurkukun suna tsananin tsoron Zauwadu,kai ba ma fursunoninba su
kansu dakarun dakaru dake tsaron fursunonin shakkarsa suke domin mutum goma basa iya
ladaftar dashi sai dai ashirinb zuwa sama,duk da cewa dakarun kartine majiya karfin gaske
wanda sai da aka zabo su,ko ya ya wani abu ya hada fursuna da Zauwadu to fa sai dai a sanya
sunansa acikin matattu don ansan cewa Zauwadu ya kashe shi sabo da zaluncinsa,karfinsa da
rashin imaninsa.Lokacin da Zauwadu ya farfado daga dogon suman da yayi yaga Imhal a zaune
acan gefe daya kan shimfidarsa ya harde kafafu tamkarma ba fada sukayi ba sai ya fusata
ainun musamman da ya waiga baya yaga gaba daya sauran fursunonin dake cikin sauran
dakuna sun zubo idanu suna kallonsa,nan take zauwadu ya yunkura zai sake afkawa Imhal
kawai sai gani yayi Imhal ya daka tsalle sama kamar dan biri ya dirga akan wuyansa ya shake
shi,duk da tsananin karfi irin na Zauwadu sai gashi ya kasa kwacewa kuma idaninsa sunyi
bulu-bulu sunyi jawur sai gashi yana dukushewa kasa yana kakarin mutuwa.Koda Imhal yaga
Zauwadu na neman mutuwa sai ya sake shi ya zube kasa magashiyan yana numfashi
sama-sama,take imhal ya nuna Zauwadu da dan yatsa ya dubeshi yace idan ka kara kawo miki
wargi a karo na uku sai na kashe ka,Tun daga wannan rana Imhal ya zama shugaban
fursunonin gidan gaba daya ya zamana cewa kowa yana shakkarsa ana yi masa ladabi da
biyayya.A bangaren shugaban dakarun dake dake tsaron kurkukun kuwa,sai ya dauki kiyayyar
duniya ya dora aka Imhal ya zamana cewa haka kawai sai yasa a kama Imhal a daureshi a
tsaye da sarkoki ai ta dukansa da itatuwa har sai ya suma kamar gawa sai dai fursunoni su zo
su dauke shi suyi masa magani,wani lokacin kuma ai ta gana masa bakar azaba iri-iri wacce
duk fursunan da akayiwa ita sai ta zama sanadin ajalinsa amma sai gashi imhal yana jureta,duk
da tsananin juriya irin ta Imhal sai da ya dinga ramewa yana yawan ramewa yana yawan rashin
lafiya sabo da tsananin wahalar da yake sha,kai in ba don ma fursunonin suna matukar
kaunarsa ba kuma suna gadin rayuwarsa ba,da tuni dakarun gidan sun kashe Imhal,komai
rashin tausayin mutum idan yaga irin halin da imhal ya shiga sai ya tausaya masa,ba komai ne
yasa fursunonin gidan suke matukar kaunar jarumi Imhal ba face zuwansa ya kawo adalci a
tsakaninsu ya zamana cewa mai karfi ya daina zalunta mara karfi,a da,ko abinci fursuna ya
karbo ya zauna zaici sai kaga wanda ya fishi karfi yazo ya kwace ya hada da nasa sai dai
wancan ya kwana da yunwa,haka kuma akwai fursunoni masau mugayen dabi'u na yin luwadi
ga wadan da sukafi karfi amma duk sai da Imhal ya hana yin wadannan mugayen
abubuwa,Zauwadu da ya kasance babban makiyin Imhal sai da ya zamo babban amininsa
kuma abokin shawararsa.
To jama'a ayi min afuwa idan na huta zan cigaba.
RIJIYA GABA DUBU1 CIGABA 10
Wata rana bayan an kama Imhal an kai shi wani daki na musamman inda ake yiwa fursunoni
azaba,anyi masa dukan kawo wuka,sai aka dawo dashi dakin su aka warbar dashi a kasa
jina-jina yana numfashi sama-sama kamar zai mutu,cikin dimaucewa Zauwadu ya shiga yi masa
magani,da kyar ya samu ya tsayar da jinin da yake zuba a jikinsa,koda Imhal ya farfado ya
dawo cikin hayyacinsa sai ya bude idanunsa dakyar ya dubi zauwadu yace Gobe idan na samu
karfin jikina da cikin dare zan gudu daga cikin kurkukun nan,idan zaka iya bi na kazo mu gudu
tare mu tsira tare,koda jin wannan batu sai idanun Zauwadu suka zazzaro ya kamu da tsananin
tsoro ya dubi Imhal cikin damuwa yace Ya kai abokina kayi sani cewa tunda aka gina kurkukun
nan tsawon shekaru arba'in a baya ba'a taba samun fursunan da ya samu damar guduwa ba
daga cikinsa,ta ya ya kake tsammanin kai zaka iya?ka dubi katangar gidannan wacce ta
kasance mai tsananin tsawo da kauri,Ta ya ya zaka iya haurata ko fasata ba tare da anzo an
kamaka ba?ka dubi yawan dakarun dake rangadi a harabar gidan nan a duk dare da
rana,sannan ka dubi mugayen karnukan da suke gadin ko ina wadan da suka kasance manya
tamkar kuraye sannan gashi sun samu da horo na musamman na iya kama mai laifi gami da
tsananin karfin gudu gami da juriyar su.Idan baka sani ba to ka sani cewa gaba dayan kurkukun
nan akan tsibiri yake,kuma shi tsibirin akan tsakiyar teku yake,idan ma ka samu nasarar fita
daga cikin kurkukun nan ta yaya zaka iya ketare wannan teku har ka tsira da rayuwarka?Ai
dabbobin dake cikin tekun nan ma kadai da sanyin teku sun isa su hallaka ka.Tabbas wannan
kurkukun yaci sunansa DARULMAUT wato gidan mutuwa,duk fursunan da ya shigo gidan nan
ya san cewa ya shigo gidan ajalinsa.Lokacin da Zauwadu yazo nan a zancen sa sai kawai yaji
Imhal ya bushe da dariya al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan ya kura masa idanu
kawai ya kasa cewa komai,daga can sai Imkal ya nutsu ya dube shi yace Babu wani abu da
bazai yiwu ba a doron kasa,kawai abinda nakeso dakai shine ka nemo mana kudade masu
yawa wadan da zamu iya siyan ma'aikatan gidan nan,babu abinda kudi ba~ai iya yi ba.Koda jin
wannn batu sai jikin ZauwadU yayi sanyi ya sunkui da kansa kas ya fada kogin tunani,Daga can
sai ya dago kai(ya dubi Imhal yace Ya kai abokina ko na bika ko ban bika ba mutuwa zanyi
acikin gidan nan don haKa gwara ma na bika din tunda babu wanda yasan abinda zai faru
gobe,naga misali akan ha$uwa ta dakai,ban taba zaton za'a iya0samun furcunan da zai zo
gidan nan ba har ya iya kainé kas sai gashi ma kai ka kaini kas har da sumar dani clhalil babu
wan "DA" mai karfina kowa tsorona yake,dukkan fursunoni da ma'aikata amma sai gashh
andawo andaina tsorona oai ake tsoro ana yi maka ladabi da biyayya.Ko da jin wannan batu sai
farin ciki ya lullube Imhal ya rungume Zauwadu suka busHe da dariyar murna tare.Daca can sai
Zauwadu ya janye jikinsa dag` cikin na Imhal ya dufe shi cikin nutsuwa a karo na biyu yace Ya
kai abokina kayi sani cewa da dangari akan ci gari,a matsayina na fursuna da ya shekara
ashirin da uku a cikin gidan nan nafi kowa sanin sirrin kurkukun nan acikin fursunoni domin
babu wajda yayi dadewata kuma nafi kowa sanin irin ma'aikAtan da ya kamata mu hada kai
dasu wajen samun nasarar wannan gagarumin aiki da m}keyi,Ina nufin dole ne mu zubo
ma'aikatan da na tabbatar da cewa suna da kwadayin abun duniya,to amma inda íatsalar take
shine ta yaya zamu iya samo kudaden da zamu biya ma'aikatan su`bamu hadin kai?Abu
na biyu shine,har0yanzu bakq gaya min yadda zamu iya ketare tekun da ya zagaye gidannan
bayan mun sami nasarar fita wajensa bc?Sa'afda Imhal ya ji wannan tambayoyi sai yayi
murmushi yace abinda nakeso dakai shine ka bini!a sannu zamuyi komai dakm-daki da
idanunka zaka ga amsoshin duk wadannan tambayoyin da kayi min yanzu.
tO JAMA'A AYIMIN AFUWA YANZU ZAKU DINGA JINA aKAI-AKAI ZAN DINGA POSTN DE
WURI DON HAKA IDAN NA HUTA ZAN CIGABA!DAGA MAI SON NISHADANPAR DAKU
COMBATANT33
RIJIYA GABA DUBU1 CIGABA 11
Abu na farko da nakeso mu farayi shine ina so mu hada baki da masu dafa abincin gidan
nan,su zuba banju acikin abincin dakarun da suke gadin dakin shugaban dakarun gidan
nan,domin mu samu damar shiga mu balle akwatin da yake ajiye kudin hidimar gidannan
aciki,na sani cewa akalla baza mu rasa dinare dubu dari ba acikin wannan akwatin wadannan
kudade sun isa mu siye duk mutanen da mukeso suyi mana aiki,Zauwadu ya gyada kai yace
tabbas zasu ishe mu,amma ta yaya zamu samu amincewar ma'aikatan da suke dafa abinci su
zuba banju acikin abincin?Imhal yace baza mu iya yin wannan aiki mu biyu kacal ba,dole sai
mun nemi hadin kan yan'uwan mu fursunoni akalla mutum goma,cikin tsananin firgici Zauwadu
yace idan muka gayyato mutane cikin wannan aiki namu za a iya samun rashin sirri a ciki,acikin
mu za a iya samun munafikin da zai zagaye ya tona asirin mu,Imhal ya gyada kai yace ai ba
kowa zamu tabo ba sai wanda mukasan ya gari da zaman gidannan kuma yana da taurin rai
gami da sai da rai,haka kuma duk wanda ya shigo cikinmu zamu gaya masa idan har ya tona
mana asiri aka kamamu hukuncin kisa ne akan sa,koda jin wannan batu sai Zauwadu yayi
murmushi yace hakika kwakwalwarka tana aiki sosai to idan muka samu mataimakan ta yaya
zamu samu hadin kan masu dafa abincin?Imhal ya sake murmushi a karo na biyu yace ka sani
cewa masu dafa abincinnan fursunoni ne yan'uwanmu dole ne mu firgita su mu kashe daya
daga cikinsu a gaban idanunsu sannan mu umarce su da abinda muke bukata kuma mu
gargadesu cewa duk wanda ya tona asirinmu acikin su shima mutuwa zai yi,koda jin haka sai
Zauwadu yayi dariyar farin ciki yace tabbas indai mukayi haka komai zai tafi dai-dai to amma fa
kasani idan muka debo wadannan kudaden acikin sa'a daya asirinmu zai tonu don a sannan ne
shugaban dakarun zai dawo,koda jin haka sai Imhal yayi tsaki ya mike tsaye zumbur a fusace
ya dakawa ALZauwadu tsawa yace kada ka sake yimin tambayar komai har sai bayan mu samu
nasararr fita daga gidannan.Gama fadin haka ke da wuya sai suka ji an kada kararrawar zuwa
cin abinci nan take dakaru suka fara bude kofofin dakunan fursunonin,ana bude dakin su Imhal
sai suka wuce da sauri suka zama akan gaba suka riga kowa zuwa inda masu dafa abinci suke
suka shige har cikin dakin girkin ba tare da dakaru sunga lokacin da suka shiga ba,suna shiga
suka iske masu dafa abincin akan aikinsu kawai sai Zauwadu ya kama kan daya daga cikin su
ya murde ya yar da gawrsa a kasa,cikin tsananin tsoro sauran ma'aikatan suka zube a kasa
suna rokon su ayi musu rai kawai sai Imhal ya dube su yace idan kuna so ku tsira da rayuwarku
ayau ku zuba banju acikin abincin da za a kaiwa masu gadin shugaban dakarun gidannan idan
kuma kuka gayawa wani wannan sirrin duk sai kun mutu lallai kuyi wannan aikin cikin dakiku
kadan,koda gama fadin haka sai Imhal da Zauwadu suka fice daga cikin dakin suna fita kuwa
suka yi arba da wani babban badakare akayi kallon-kallo nan take jikin badakaren ya bashi
cewar da akwai abinda suke shiryawa.
TO JAMA'A ANAN NAZO KARSHEN LITTAFI NA DAYA IDAN NA HUTA ZAN CIGABA DA
LITTAFI NA BIYU DAGA MAI SON NISHADANTAR DAKU COMBATANT33