Showing 3001 words to 6000 words out of 8928 words

Chapter 2 - Rijiya Gaba Dubu Book 1 by Madakin Gini.pdf

da tabbacin cewa idan muka fafata sai na sami
nasara akan ka duk da cewar na yaba da karfinka,ka sani cewa kana da zabi guda biyu kodai
ka yakeni ko kuma yanzun nan nasa tagobi na sare maka kai,koda jin wannan batu sai hankalin
Imhal ya dugunzuma ya mike tsaye cikin sanyin jiki,abu na farko da ya fado masa a rai shine,Ai
bai kamata ya mutu yanzu ba har sai ya gano asalinsa,koda gama aiyana hakan acikin
zuciyarsa sai ya mikawa wani badakare hannu yace bani tagobinka,ba tare da gardama ba
kuwa ya mikawa Imhal tagobinsa ya karba,koda ganin haka sai murna ta kama sarki,shima ya
zare tagobinsa,a lokacinne dakaru suka buda suka yi musu da ira aka sa su a tsakiya,nan fa
sarki da Imhal suka fara zagaya juna suna kallo-kallo.
TO JAMA'A KUYI MIN AFUWA IDAN NA HUTA ZAN CI GABA DAGA MAI SON
NISHADANTAR DAKU IBRAHIM S COMBATANT
RIJIYA GABA DUBU1 CIGABA 4
Lokaci guda kowannensu ya daga tagobinsa sama suka ruga izuwa kan juna,suka ruguntsume

da azababben yaki ya zamana suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya
da bajinta ta ban al'ajabi,sai da suka shafe sa a guda suna wannan bakin artabun amma
dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar mutum daya ba,Al'amarin da ya fusata sarki kenan
kuma ya cika da tsananin mamakin yadda akayi wannan mutumin dajin ya samu gagarumin
horon yaki haka,nan take sarki ya canza salon yaki,ya dinga tsalle-tsalle da
kwance-kwance,kawai sai yaga Imhal ya iya duk irin abinda yake yi tamkar tare aka koya musu
yaki babu wani banbanci,koda ganin haka sai sarki ya ja da baya taku biyar,shima Imhal sai
yayi hakan amma shi taku uku yayi,duk su biyun suka kurawa juna idanu na tsawon yan dakiku
kadan,kawai sai sarki ya rugo da gudu izuwa kansa,shima sai ya ruga gareshi,kafin su hadu sai
kowannensu ya daka wawan tsalle sama ya kai hari cikin mugun nufi,Acikin tsananin zafin
nama kowannensu ya kaucewa harin takubbansu suka sari iska,amma kafin su duro kasa sun
gwarawa juna fuska,ai kuwa sai hancin kowannensu ya fashe,a saman sai suka sake kaiwa
juna hari,sai sarki ya sami nasarar yankar Imhal a saman cibiyarsa,Shi kuma ya sami nasarar
yankar sarki a gefen wuyansa,kowannensu jini yayi tsartuwa daga jikinsa suka rikito kasa a
matukar galabaice,A guje Dakaru suka ruga aka baiwa Sarki rawani ya daure wuyansa da
jini,take likitan Sarki yayi masa magani,Kawai sai Dakaru suka ruga izuwa kan Imhal wanda
yake kwance a kasa ya dafe raunin don tsaida jini zasu halaka shi,Sarki ya daka musu tsawa
suka fasa,kawai sai sarki ya dubi likitansa yace Idan ka gama dani kaje kayiwa wannan
saurayin magani,Cikin gaggawa kuwa likita ya gama yiwa sarki magani sannan yaje yayiwa
Imhal,Sa ar da Sarki da Imhal sukayi raunikan basuyi zurfi ba a jikin su,Tunda Likitan ya fara
yiwa sarki magani sai zuciyar Sarki ta fara tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki
da takaici bisa ganin yadda a yau wannan bakon saurayi ya karya alkadarinsa na jarumin dake
rike da KAMBUN JARUMTAKA na nahiyar gaba daya,Bayan angama yiwa Imhal magani ya
mike tsaye sai yazo gaban Sarki ya risina yayi godiya,Sarki ya dube shi cikin yake yace Tabbas
ka cika jarumi abin kwatance amma ka saurari ranar da zamu sake haduwa a filin gasar
JARUMTAKA wacce za ayi a birnin MISIRA nan da cikar wata uku,ko kana so ko baka so sai ka
shiga wannan gasa kuma ina tabbatar maka da cewar sai na sami nasara akan ka na kasheka
murus har Lahira,yin hakane kadai zai sa na huce bisa takaici da bakin cikin da ka jefani a
ciki,Koda ya gama fadin hakan sai Sarkin Kisra ya dubi wani babban Badakare nasa yayi masa
rada a kunne sannan ya juya ya kama dokinsa ya hau ya kada linzaminsa yayi gaba,sauran
dakarun gaba daya suka rufa masa baya.Shi kuwa jarumi Imhal sai ya tsaya cak yabi sarkin
kisra da kallo cikin tsananin mamaki,Imhal ya tambayi kansa cikin zuciyarsa yace WAI SHIN
MENENE YAYI ZAFI HAKA,HAR DA SARKI YACE ZAI KASHENI MURUS HAR LAHIRA
ALHALIN MA BASU TABA GANIN JUNA BA SAI YAU?AKAN WANE DALILI ZAI TSANANTA
GABA A TSAKANINMU HAKA?koda Imhal ya kasa baiwa kansa amsa sai ya juya ya falfala da
gudu ya nufi hanyar da zata kaishi daji.
To jama'a ayimin afuwa zan cigaba idan na huta daga mai son nishadantar daku IBRAHIM S
COMBATANT
RIJIYA GABA DUBU 1 CIGABA 5
Imhal ya ci gaba da gudu har sai da ya iso dajin da bukkarsu take,yana cikin gudu ne ya hango
tsoho Imzanu ya goyo jakarsa ta tafiya yana dogara sanda ya baro bukkar acan baya,cikin
kaduwa da matukar mamaki Imhal ya karasa wajen Imzanu da gudu ya tareshi yana mai rike
kafadunsa ya dube shi yace Ya kai abbana lafiya kuwa?ina zaka je naga ka dauko jakarka ka

nufi hanyar cikin gari?Koda tsoho Imzanu yaga Imhal a tsaye gabansa sai fuskarsa ta fadada
da murmushin farin ciki,har ya budi baki zai ce wani abu sai idanunsa suka kai kan raunin dake
kan kasan cibiyar Imhal,cikin firgici Imzanu ya dube shi yace yaya akayi ka samu wannan
raunin?koda jin wannan tambayar sai Imhal ya kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da
sarki Kisra ya zayyana masa ba tare da boye masa komai ba,koda jin wannan labarin sai
hankalin tsoho Imzanu ya dugunzuma ainun har idanunsa ya ciko da kwallah ya dubi Imhal
yace ya kai dana ina so ka sani cewa kamar yadda ka kasance maraya a garin nan haka nima
nake,iyayena da kakannina duk sun mutu,matata ta mutu tare da dan da ta haifa kamar yadda
na baka labari,A halin yanzu bani da kowa face kai wane irin hali kake tsammanin zan shiga
idan na rasaka?ina mai tabbatar maka da cewa idan har ka halacci gasar jarumtakar da za ayi
nan da cikar wata uku a birnin Misira sai ka rasa rayuwarka domin tabbas sai sarkin garinnan ya
kashe ka,domin zai je yayi gagarumin shiri ne yayi amfani da karfin sihirin tsafi wanda dole sai
ya samu nasara akan ka,A halin yanzu bamu da wani zabi wanda ya wuce mu sulale mu bar
Nahiyar nan gaba daya,indai muka isa wata nahiyar daban shikenan mun tsira daga sharrin
sarkin kisra,duk inda muka tsinci kanmu sai mu fara sabuwar rayuwa,duk da cewa ni tsufa ya
kamani ina da sauran buri guda daya a duniya,wannan burin ba na komai bane face nason
ganin aurenka,koda tsoho Imzanu yazo nan a zancensa sai Imhal ya rungume shi suka fashe
da kuka tare tsawon yan dakiku suna manne da juna sai daga can Imhal ya janye jikinsa daga
cikin nasa ya dube shi yace Ya kai Abbana kayi sani bazan yi maka gardama ba bisa wannan
shawara da kazo min da ita,sabo da nasan cewa ni bansan abinda kasani ba,domin duk wanda
ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi,yanzu sai mu koma bukkarmu mu debo kayanmu gaba
daya,Imzanu ya gyada kai yace Ai na debo mana dukkan kudadenmu idan mun shiga cikin gari
mayi guzuri,cikin alamun tsananin damuwa Imhal ya dubi imzanu a lokacin da idanunsa suka
ciko da kwallah yace Haba ya kai Abbana ko ba komai na koma da baya ka nuna inda ka binne
mahaifiya ta nayi mata bankwana tunda rabona da ita tun ina kankani,koda jin wannan batu sai
hawaye ya zubowa Imzanu ya dubi Imhal yace ka gafarceni ya kai dana hakika naso nayi
babban kuskure,zo muje na nuna maka kabarin mahifiyarka,ko da gama fadin haka sai tsoho
Imzanu ya juya da baya suka koma izuwa can gaban bukkarsa suka cigaba da nausawa cikin
daji suna bin wata hanya mai sarkakiya da yawa wacce shi kanshi Imhal a iya tasowar shi acikin
daji bai taba sanin akwai wannan hanya ba,kawai sai tsintar kansa yayi acikin wadansu
dogayen bishiyoyi masu manyan ganyaye wadan da suka sa dajin gaba daya yayi duhu,bisa
dole suka kunna wuta a jikin itace don haska hanya,Imzanu ya cigaba da yiwa Imhal jagora sai
gasu a bakin kofar wani kogon dutse mai girman gaske,da isowarsu bakin kofar kogon sai
Imzanu ya haska cikin kogon yaga lafiyarsa sannan ya juyo ya dubi Imhal ya mika masa wutar
itacen yace acikin wannan kogon na binne mahaifiyarka,ka shiga ciki zaka ga kabarinta sai kayi
mata bankwana ni kam bazan iya sake kallon kabarin ta ba domin idan na gan shi zan tuno
baya,kuma hakan zai iya jefani cikin mugun hali,cikin matukar sanyin jiki Imhal ya karbi wutar
icen sannan uya kunna kai cikin kogon dutsen yana shiga kuwa ya hango kabarin na
mahaifiyarsa,kai tsaye ya tukari inda kabarin yake da isarsa gaban kabarin sai ya durkusa a
gabansa ya kifa kansa akan kabarin sannan ya fashe da matsanancin kuka tsawon yan dakiku
yana cikin wannan hali sannan ya dago ya kurawa kabarin idanu yace YAKE MAHAIFIYATA
SABO DAME ZAKI TAFI KI BARNI LKACIN DA NAFI BUKATARKI FIYE DA KOMAI?ME YASA
KIKA TAFI BAKI FADI KO WAYE UBANA BA?SHIN HAKA KIKE SO RAYUWATA TA KARE

ACIKIN KADAICI, MARAICI GAMI DA TAKAICI KAMAR YADDA TAKI TA KARE?WANENE
IMHAL?SUNAN DA KIKE AMBATA AKO DA YAUSHE?IDAN HAR BAZA KI IYA BUDAR BAKI
KI GAYA MIKI AMSAR TAMBAYOYINA BA YANZU ZAN KASANCE MAI SAURARON
FATALWARKI KODA ACIKN BARCINA,BAZAN TABA SAMUN SUKUNI DA KWANCIYAR
HANKALI BA A RAYUWATA HAR SAI NA GANO ASALINA.
Koda gama fadin hakan sai Imhal ya sake kifa fuskarsa akan kabarin ya dada fashewa da kuka
bakin ciki.
To jama a ayimin afuwa idan na huta zanci gaba
RIJIYA GABA DUBU 1 CIGABA 6
Sai da ya jima yana kukan sannan ya mike tsaye ya fice daga cikin kogon dutsen yana waigen
kabarin yana zubar da hawaye,har ya isa bakin kofar kogon zai fita sai ya waigo ya dubi kabarin
yace Yake ummata nayi miki alkawarin zan rayu acikin wannan duniya komai RINTSI DA
TSANANI har izuwa lokacin da zan gano asalina na dawo har nan na sanar dake,koda gama
fadin haka sai ya juya ya fice daga cikin kogon yana fitowa ya iske tsoho Imzanu a zaune ya
kishingida da jikin kogon har ya fara bacci sabo da gajiyar yaar tafiyar da yayi,motsin takun
sawun Imhal ne yasa ya farka daga baccin cikin yanayin damuwa,Imzanu ya dubi Imhal yace
yakai dana kayi sani cewa na gaji ainun kuma gashi tsufa yana tabani ina ganin cewa yanzu
bazan iya takawa da kafafuna ba yanzu sai dai mubarwa gobe da safe amma yin hakan yana
da hadari,domin ina ji a jikina cewar sarki zai iya turowa a kamaka domin ya tsareka a
kurkukunsa,don kada ka gudu kabar garin,kafin tsoho Imzanu ya gama rufe bakinsa sai suka
jiyo sautin takun sawu daga can nesa,alamar takun sawu ne ta mutane da yawa kuma inda
suke aka durfafo,koda jin haka sai Imhal yayi wuf ya suri tsoho Imzanu ya goyashi a bayan sa
ya daure shi tamau,sannan ya ruga izuwa kan wata bishiya mai tsawon tsiya wacce can
karshenta ganyayene manya manya masu duhuwa,kamar kadangare na hawa bango haka
Imhal ya dinga hawa kan bishiyar da gudu kai kace ba sama yake hawa ba,cikin dakiku kadan
ya isa karshen bishiyar yayi lambo akan wani reashe,shi kansa Imhal idan ya leko kasa baya
iya jiyo motsin komai sabo da nisa,A dai dai wannan lokaci ne dakaru acikin bakaken kaya
kimanin su dubu suka iso dai dai kofar kogon dutsen da gudu,dukkanninsu suna rike da tagobi
tsirara kuma sun rufe fuskokinsu,koda tsoho Imzanu ya hango wadannan dakaru sai ya sai
zuciyarsa ta buga da karfin gaske ya firgita ainun ya fara kokarin tuno da wani al amari wanda
ya faru a shekarun baya,amma sai kwakwalwar tasa ta kasa tuno komai.Dakarun masu
bakaken tufafi na isowa suka tsaya cirko cirko suna kallo kallo da waige waige,nan dai
shugabansu ya rarraba su izuwa gabar da yamma kudu da arewa,suka bazama neman inda su
Imhal suke,har cikin kogon dutsen inda kabarin mahaifiyar Imhal yake sai da suka shiga.A dai
dai wannan lokacine Imhal yayi kundunbala ya sallamo kasa daga kan doguwar bishiyar,karar
dirar kafafunsa kasa ne yasa dakarun suka farga suka baro inda suke da gudu,amma kafin su
iso inda suka bari tuni Imhal ya falfala da azababben gudu goye da tsoho Imzanu,Wohoho!kafa
me naci ban bakiba?idan zan ta tarar da muje mu sai abinda hali yayi,duk tsananin gudu irin na
Imhal sai gashi wadannan dakaru suna rufa masa baya har ma suna nema su cimmasa amma
sun kasa,koda dakaru suka ga an shafe dakiku masu yawa sun kasa cimma Imhal duk da
tsananin nacinsu gami da horon da suka samu na juriya sai suka fara zaro kibiya suna danawa
akan baka suna harbawa Imhal,Imhal na cikin gudu sai yaji kibiyoyi suna wucewa ta samansa
da gefensa,har ma sai da wata kibiya ta karci gefen kunnensa jini yayi tsartuwa,al amarin da

yayi matukar girgiza hankalinsa kenan ya kara karfin gudunsa,amma abinda ya kara tayar masa
da hankali shine,tunowa da tsoho Imzanu wanda ke goye a bayansa wanda ako da yaushe bisa
tsautsayi kibiya zata iya zuwa ta soke shi,koda ya aiyana hakan sai yasa hannayensa ya juyo
da tsoho Imzanu daga bayansa ya dawo dashi gabansa ya ci gaba da falfala gudun da
haka,kaico!Tsautsayi ba a yi masa barci!Imhal na cikin wannan azababben gudu ne kibiya tazo
ta soke shi a duga duginsa na kafar hagu take kibiyar ta ta nutse ta hudo waje,Imhal ya kwarara
uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji,yayi taga taga kamar zai kife kasa amma sai
ya yunkura cikin zafin nama da tsananin juriya ya take kafar a haka tana zubar da jini yaci gaba
da gudu.Naci damben kuturu!koda dakarun nan suka ga Imhal yaki faduwa kasa yaci gaba da
gudu duk da cewar kibiyar ta soke shi a kafa sai suma suka ci gaba da falfala gudu suka dada
zubo masa ruwan kibbau ba sassauci,Har Imhal ya iso daf da kafar cikin gari dakarun basu
cimmasa ba kuma babu wata kibiya data soke shi amma fa yana jin mugun zugi acikin kafarsa
tamkar ya sare kafar da hannunsa ya yar da ita.koda dakaru suka ga an iso cikin gari sai suka
samu lokuna suka shiga suka buya suka sauya tufafin jikinsu suka sa irin na mutanen gari suka
bude fuskokinsu,sannan suka rarrabu suna masu dada ci gaba da farautar Imhal.Imhal na
shigowa cikin birnin kisra goye da Imzanu sai ya fara sarewa yana jan kafa da kyar,cikin
hanzari ya doki kofar wani gida dake rufe da hannunsa guda, take kofar ta balle ya kunna kai
ciki ya yunkura zai kwance Imzanu daga jikinsa sai yaga ashe ya suma sakamakon wata kibiya
data soke shi a gefen wuyansa,cikin tsananin dimaucewa Imhal ya sauke Imzanu kasa ya
wangame baki zai rusa ihu don a zatonsa Imzanu ya mutune,sai kawai yaga wata tsaleliyar
mata ta rugo da gudu daka can cikin gidan ta dube shi tana mai yi masa inkiyar yayi shiru.
TO ZAN HUTA ANAN SAI KUNSAKE JINA
RIJIYA GABA DUBU1 CIGABA7
Sai da tazo daf da shi sannan tayi masa rada a kunne tace tsohonka bai mutu ba,zan iya ceto
rayuwarsa ni likita ce,bari nayi sauri naje na batar da shaidar da zata sa a gane ka shigo
nan,maza ka shigar da tsohon can cikin dakina ka kwantar dashi kada ka taba shi,tana gama
fadin haka sai ta dauki wani tsumma ta ruga waje,cikin sauri Tsaleliyar matar taje ta goge duk
jinin kafarsa,daya zuzzuba a kofar gidan,sannan ta sake rugawa izuwa cikin gidan ta mai da
kofa ta saka sakata.Faruwar haka ke da wuya sai ga wadannan dakaru da suka biyo Imhal sun
iso wajen da gudu,gaba dayansu sai suka tsaya suna yin duru duru suna waige waige da hange
hange,suna jiran karasowar shugabansu domin ya basu umarni bisa abinda za suyi
Al'amarin Imhal kuwa,lokacin da ya kinkimi tsoho Imzanu ya shige dashi izuwa dakin wannan
tsaleliyar mata a dimauce sai ya shimfide shi akan wani babban teburi na katako,a sannan ne
ya dubi ko ina a cikin dakin nan take ya gamsu cewa daki ne na likita,don babu komai acikinsa
face tarkacen kayan likitoci,kawai sai ga matar ta shigo cikin dakin da gudu,ko kallon Imhal
batayi ba ta ruga izuwa kan tsoho Imzanu ta shiga yi masa aiki,nan take ta cire kibiyar dake
wuyan nasa,ta zuba wani garin magani akan raunin nan take jini ya daina zuba,duk wannan abu
da take Imhal yana tsaye a gefe daya ya zuba mata idanu kawai cikin tsananin mamaki,domin
bai san dalilin da yasa ta taimake shi ba alhalin gashi ma yayi mata laifi ya karya mata kofar
gida da karfin tsiya,kuma gashi bata taba ganin shi ba sai yau,Bayan gama shudewar dakiku
dari da ashirin da gama yiwa Imzanu magani sai ya farfado ya bude idanunsa,koda ganin haka
sai farin ciki ya lullube Imhal ya kama yiwa matar godiya,A dai dai wannan lokaci ne suka ji ana
kwankwaso kofar gidan da karfi,Al'amarin da ya tayar da hankalin Imhal ya yunkura zai zare

tagobinsa,sai matar tayi masa nuni da kada ya zare tagobin,ta dube shi tace ka bani yardarka
ina mai tabbatar maka da cewa komai dadewa zaka dawo ka iske mahaifinka a cikin koshin
lafiya,maza kayi sallama da tsohon naka zan nuna maka hanyar da zaka bi ka fice daga cikin
gidan nan ba tare da wani ya ganka ba,cikin tsananin mamaki Imhal ya dubeta yace wacece ke
kuma sabo dame kika ce ci rayuwarmu nida wannan tsohon nawa?matar tayi murmushi mai
taushi ga Imhal tace Ni na sanku fiye da shekaru bakwai baya,kune baku san ni ba,kuma na
dade ina bibiyarku a duk sanda kuka shigo garinnan,tana gama fadin haka ne suka ji anci gaba
da buga kofar gidan da karfin gaske,A guje matar ta kama hannun Imhal ta jashi izuwa cikin
wani dakin daban yana waigen tsoho Imzanu yana hawaye,shima Imzanu ya bishi da kallo yana
zubar da hawaye,domin duk su biyun sun san cewa abu ne mai wuyar gaske idan har zasu
sake saduwa da junansu,da shiga su Imhal cikin wannan daki na biyu sai sukayi arba da wata
rijiya a bude wacce ta ciko da ruwa har baki,kai sai matar ta dube shi tace kayi nitso izuwa can
kasan

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login