Showing 1 words to 3000 words out of 10342 words

Chapter 1 - FAHIMAH Book 2 Writing by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

 Da kyar ta iya mikewa ta soma dafa bango, tana mikewar jini na tsinke mata. Daga nan sai
wani duhu ya mamayi ganinta, ganinta ya dauke gaba daya ji ka ke yif! Ta fada a kan Fahimah
da ke jan minshari sabida dadin A.C.
A firgice ta farka, ta janye Amrah daga kan kafafunta tana salati. Ta mike jiki na rawa ta
kunna kwan lantarki. Nan ta ga jini na fita a jikin Amrah, kuma ko motsi ba ta yi. Fahimah
saboda gigicewa a guje ta fita dakin Ammi tana kwala mata kira tun daga falo.
Hatta Baba Talatu da ke baskwata sai da ta jiyo kiran Ammi da Fahimah ke yi. Babban
tsoronta kada a ce ta kashe matar Uwais. Cikin barci Ammi ke jiyo ihun Fahimah yana doso
dakinta, don haka a bakin kofa suka ci karo. Fahimah ta hada hannayenta waje guda kasan
habarta kamar mai roko. Ta ce, “Ki taimaka Ammi, Amrah za ta mutu a dakina, wallahi ban mata komai ba. Kawai tashi nayi
na ganta a kaina jini na zuba. Na shiga uku Ammi…”.
Ammi ta ce, “Ke da Allah can shashasha, haihuwa ce”.
Ta ture ta ta wuce dakin nata. Daidai lokacin da Baba Talatu ma ta karaso. A tare suka shiga
dakin suna ganin halin da Amrah ke ciki suka gane wannan haihuwa ta zo da tangarda.
Ammi ta ce da Talatu maza dauko min wayata da mukullin mota”.
Talatu da gudu ta juya ta dauko. Ammi da Talatu suka ciccibi Amrah suka yi waje. Ammi na
cewa, Fahimah ta dauko jakar da Amrah ta zo da ita gaba daya ba za a rasa kayan jariri ba. Ta
biyo su.

Asibitin Standard suka wuce don komai dare ba a rasa likita, suna zuwa aka karbe ta da
gaggawa. Dubawa ta farko likita ta ce,
“Amrah ba za ta iya haihuwa da kanta ba an samu matsala mai girma, sannan babyn a
breach yake, abu mai sauki shine CS kawai don su ceceta ko babyn, amma ita ko babyn dole a
rasa guda.
Sabida tsananin rudewa Ammi kalmar shahada ta ke ja. Fahimah kuwa sai mazari ta ke daga
tsaye. Likita ya ce maza mijinta ko mahaifinta su zo su sanya hannu don lokaci ya kure babu
wani taimako da za su iya yi mata bayan CS.

Talatu ce mai karfin halin ce da Fahimah,
“Ba ni wayar Ammi da ke hannunki bayan kin latso min uban dakina”.
Haka Fahima ta yi, ita mantawa shaf ta yi da wayar Ammi na hannunta don a gida ta baro
tata. Ta lalubo lambar Uwais hannunta na karkarwa ta bai wa Talatu.
Bugu daya Uwais ya dauka don yana can kamar mai nakudar shima, yana jiran abin da zai
biyo baya, me ya kawo Amrah gidansu har dakin Fahimah cikin dare haka, kuma ina Fahimar ta
ke da ta barta ta daukar mata waya tsakar dare? Ya tabbata sha’ani ya lalace kam, da ya ji
shawarar mahaifiyarshi tun farko da haka ba ta faru ba. Yanzu da wane yare zai yi wa Amrah bayanin da za ta fahimce shi? Kuma me za ta dauki
Fahimah? Ba za ta kara yarda da ita ba duk son da ta ke mata yau zai koma kiyayyah.
Talatu na kira yana dagawa, a nitse ta gaya masa halin da ake ciki da bayanin da likita ya yi.
Uwais ji ya yi kamar kwarankwatsa ta fado a kansa, ya ji kamar ya yi fiffike ya ganshi a Nijeriya.
Babynsa! Gudan jininsa da ya kwallafa wa rai yau ga kuskurensa zai yi sanadinsa.
“Ba ni likitar”.

Kawai ya ce cikin tashin hankali.

Ya gaya mata ba ya kasar, sannan iyayenta ba sa gari, ya amince a yi mata CS din da duk
wani taimako da ya dace. Ya kara da cewa,
“Likita ki taimake ni kada in rasa kowanne a cikin su. Don dukkansu ina so, and they mean a
lot me. Kuma na yi mata laifi ina so in nemi gafarar ta… idan ta mutu a wannan halin bazan
taba yafewa kaina ba.....".
Gaba daya muryarsa ta karye kamar ba Uwais ba. Bolded and courageous a komai. Likita
bata tsaya doguwar magana dashi ba don ta lura ba'a hayyacin sa yake ba, suka shirya Amrah
zuwa dakin tiyata.

******

"It’s a baby boy, amma bai zo da rai ba. The mother is still unconscious, za ta dawo
hayyacinta in the next two hours in allurar barci (anaesthesia) ta sake ta, sai ku shiga ku
ganta".

Siririyar nurse din ta fadawa Ammi, a lokaci guda ta mika mata jaririn nannade cikin farin
shawul. Ammi hannu da jiki na rawa ta amshe shi ta bude fuskarsa su duka ukun suka zuba
masa ido. Uwais sak! Fari sol bai debo komai a jikin Amrah ba. Hatta farcen yaron irin na Uwais
ne. Fahimah jin wata irin soyayyar jaririn ta yi, ko don kamanninsa da Uwais, ta kifa kai jikin
Ammi tana kuka. Uwais na ta kira babu wadda ta iya amsa wayar sa. Ammi ta ce, Fahimah ta
zauna ita da Talatu za su tafi da jaririn maigadi ya kira makwabta a yi masa sutura.
Ba su jima da tafiya ba aka gungura Amrah zuwa aminity. Da sauri Fahimah ta bi bayansu
suka kwantar da Amraha kan gado suka yi mata duk abin da ya dace sanan suka fita.

Fahimah ta ja kujera daidai kan Amrah ta zauna. Tana karanta addu’a tana tofa mata. Ga
karin jini ga na ruwa, tana da son haihuwa matuka, musamman da Uwais ya ce zai so ‘ya’yansu
ne fiye da son da yake yi wa kansa.... Amma in haka haihuwar ta ke lala - lala ta hakura. Lallai
wannan shi ne kafa daya a duniya, kafa daya a lahira. Ta tuno uban jinin da ta ga Amrah na zubarwa, wani matsanancin tsoro ya kara kamata.
Tunda dai Allah ya taimake ta ba ta yi cikin ba, to ba za ta kara yarda ta yi abin yin cikin ba. Ta
barwa Amrah Uwais su yi ta haihuwa, tarewar ma ta fasa ba za ta yi ba. Zata cigaba da zama
da Ammin ta.
Wajejen karfe goma na safe Amrah ta bude idonta a hankali. Kafin idanunta su washe a
dakin su sauka a kan jinin da ake kara mata. A lokacin ne ta fahimci a kan gadon asibiti ta ke.
To me ya kawo ta asibiti ita da ta kwanta a gadon Fahimah za ta yi barci?

“Masha Allah, kin tashi Aunty Amrah? Bari in kira likita”. Ta ji muryar Fahimah a gefenta.
Muryar da ta tado mata da ainahin dalilin zuwanta asibiti. Da sauri ta kai hannu kan cikinta ta
ji wayam! Da azama ta yunkura za ta mike, daidai lokacin da likitan ya shigo, Fahima na biye da

shi. Da sauri ya maida ita kwance, ya ce, “Be careful Madam, akwai aiki a jikinki”. Sannan ya
tambaye ta,
“Are you alright?”
Kai kawai ta gyada masa. Ta runtse ido da Fahimah ta zagayo gefen fuskarta, tana tambayar
likita ko za a iya ba ta tea ta sha? Doctor ya ce, ta bari sai an jima, Nurse za ta zo ta ba ta da
magani.
Tunda Amrah ta rufe ido ba ta kara budewa ba. Don ba ta son ganin Fahimah, ba kuma barci
ta ke yi ba. Har zuwa lokacin da su Ammi suka dawo.
Ammi bata san Amrah ta farka ba ta tsaya tana gaya wa Fahimah har an binne yaron. Allah
ya ba su wani mai albarka, Ya bai wa iyayensa dangana. Shi ma Uwais din yana hanya gobe
duk da bai gama abin da ya kai shi ba.
Wasu dumammun hawaye suka biyo ta gefen idanun Amrah, Dan ta ya koma, duk wannan
wahalar da ta ci akan rainon cikin, duk a dalilin bakin cikin Fahimah da Uwais? Ko Uwaisu ne
autan maza ta hakura da shi yau, in ba haka ba bakin cikinsa shi zai yi ajalin ta.
Ta soma tunanin hanyar da za ta bi ta tsere kafin Uwais ya zo ya tadda ita. To amma da
wanne ido za ta koma wa iyayen ta???

Wannan tunanin ya sa Amrah fashewa kuka wiwi a fili. Su ba su san idonta biyu ba, kuma
sun dauka kukan na rashin dan ta ne da ta yi. Su basu san abubuwan sun ma zuciyar ta yawa
ba. Da wanne zata ji?
Ammi ta karasa ta kama hannunta tana ba ta baki. Ta ce, “Ki yi hakuri Amrah, insha Allahu
mai ceton mu ne. Ba ki ganshi ba kamar Uwais ya yi khaki. Allah ya yi wa iyayen da suka rasa
‘ya’yansu suna kanana babban tanadi a ranar gobe. Kada ki yi bakin ciki, ki yi addu’ar Allah ya
bada rayayye mai albarka, kin ji”. Amrah ko kallon Ammi ba ta yi ba, ta ci gaba da gunza kukanta. A ranta ta ce, duk abin da
Uwais da Fahimah ke yi da sanin Ammi tunda ai a gabanta suke, and she is educated enough
da za su yi irin wannan danyen aikin ba da saninta ba.
Me kuma za ta ce mata yanzu? Ai ta bar mata danta ke nan har abada ta aura wa farkarsa,
ko su ci gaba da watsewar su.
Gaba daya sun kasa gane kan Amrah, tunda ta farko ta ki ci ta ki sha, sai kuka, sannan ta ki
karbar lallashin Ammi.
Har dare suna tsaye a kanta suna lallami, amma ko uffan ba ta ce musu ba. Sai da Ammi ta
koma ta kira babban likita ta ce ya bincike ta ko da wani abu da ke damunta daban, kada jininta
ya hau.

Likita ya shigo, ya ce duk su ba shi wuri zai yi magana da Amrah. Ya ja kujera a gabanta ya
zauna, ya ce, “Madam, may I know your problem? Na dauka ke musulma ce, kin san mutuwa
tana kan kowa babba da yaro? Na dauka za ki yi tawakkali ki yi masa addu’a, ki roki Allah ya
sake ba ki wani cikin gaggawa?” Amrah na kuka ta ce, “Doctor ni farin ciki nake da Dan ya koma. Ko bakomai zai dandani irin
bakin cikin da ya kunsa min. Tunda gashi nan a dalilin cin amanar da yayi min shima ya rasa
abinda ya kallafawa rai.
Damuwata yanzu kawai yadda zan je Abuja. Ka taimaka min ka sallame ni a yau, kuma ka ba

ni aron wayarka in kira direbana ya zo ya dauke ni”.
Doctor ya ce, “Babbar magana. Ba zan iya sallamarki ba sai jibi, a ka’ida in aka yi wa mutum
aiki sai bayan kwana uku ake iya sallamarsa shi ma in an tabbatar babu wata matsala da za ta
biyo baya. Advisably ki bar ni in yi wa Mamanki bayani cewa kina son tafiya Abujan da zarar an
sallame ki, na tabbata za ta fahimta ta kai ki da kanta…”. Da sauri Amrah ta ce, “Doctor ba abin da ya hada ni da su, kuma in ba za ka taimaka min ba
wallahi ko a kan iska sai na tafi".

Ta ci gaba da rusa kuka. Doctor ya rasa ya zai yi da ita, da ma kuma yana da lambar Uwais
da suke magana wadda waccan likitar data karbi Amrah ta bashi da za su yi handing over, sai
ya koma ofis ya kira shi, ya yi masa bayanin halin da matarsa ke ciki.

Uwais ya rasa inda zai tsoma ransa ya ji sanyi, ga booking dinsa ma an ce ba zai samu ba a
goben sai bayan kwana uku, na goben bai yiwuwa saboda hazo. Da kyar ya iya ce da Doctor ya
kula sosai kada ya barta ta fita, har zuwa kwana ukun, wato ranar sallamar ta, zai turo matar
Yayanta ta tafi da ita, ya tabbata za ta yarda ta bi ta. Daga nan ya kira Jabeer, a yadda Jabeer ya ji muryar Uwais ya tabbata ba lafiya ba. Ya ce,
“Jabeer, I donno from where to start, don ko kai ba za ka yi min uzuri ba balle Amrah. Amma
wallahi ka yarda da ni ina da niyyar gaya mata ne da zarar na dawo, don in samu ta haihu
lafiya. Sai kaddara ta riga fata. Yau ga kuskurena da rashin jin shawarar mahaifiya sun jawo na
yi asarar babyna”.
Jabeer ya ce, “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, me ya faru haka Uwais?”
Uwais ya share zufar da ke yankowa daga goshinsa, ya kwashe komai ya gaya wa Jabeer,
ya kare zancensa da cewa, “I never take it serious, (auren sa da Fahimah), kuma tunda na
mallaki Amrah ban kara waiwayar zancen Fahimah ba.
Na yi duk iya kokarina a kan Amrah ta fahimce ni ban iya rayuwa babu macen aure, ta dawo
B.U.K mu ci gaba da rayuwarmu. Amrah ta ki fahimtata da gangan, ta sa kafa ta yi tafiyarta
Malaysia ta bar ni. As a man like me na san za ka fahimci halin da na kasance kuma na san ina
da wata matar. Amma wallahi Jabeer ban taba tunanin auren zai je ko’ina ba shi ya sa na dauki lokaci ban
gaya wa Amrah ba, sai kuma ga ciki ta samu mai matsaloli, sai na kara jinkirtawa da niyyar
zuwa ta sauka.
Ban san ya aka yi Amrah ta zo gidanmu ba, har dakin Fahimah, har wayar Fahimah ta je
hannunta. Daga nan komai ya lalace wanda I’m sure shi ne sanadin nakudarta.
I’m sorry Jabeer, wallahi ban yi da niyya ba, haka Allah ya nufa. Jabeer babyna da na kallafa
wa rai ya zo ba rai, sannan Amrah na can ta tubure musu Abuja za ta koma. Bayan already na
yi booking ina tafe in three days”.
Jabeer ma ransa ya baci sosai, amma sai ya yi hali na dattaku, ya ce, “Ka yi babban kuskure
Uwais, kuma magabatanka ma sun yi kuskure tun a wajen neman auren Amrah ya kamata ku
gabatar da wannan maganar, in ya so in yin yin, in barin-barin. Amma yanzu ka bata goma daya
ba ta gyaru ba. Don ka san Daddy ba wai yana farin ciki da aurenku ba ne don dai ya ga Amrah
na so ne ya hakura.
Don haka ni ban isa in rike Amrah a gidana ba tare da iyayen mu sun ji zancen nan ba, don

Murjanatu ba ta taba haihuwa ba, ba ta san ya za ta yi da Amrah ba. Don haka in an sallame ta
zan je in dauke ta a asibitin mu wuce Abuja”.
A sautin muryar jabeer Uwais ya tsinkayi bacin rai sosai, don dai yana kokarin dannewa ne.
Babban bacin ran Jabeer wai a ce har shi bai gaya wa yana da wata matar bayan Amrah ba?
Duk yadda suke da shi, ai zai iya gaya masa ma tun lokacin auren in ya so ya roke shi ya rufa
asiri. Wannan itace abota ta hakika. Amma ina? A lokacin idon Uwais ya rufe da son mallakar
Amrah anyhow.
Don haka yanzu kam yana bayan kowanne hukunci Amrah za ta yanke wa aurenta da Uwais
don tana matukar sonsa, kuma ya yi betraying dinta a magana ta gaskiya.
Shi ya sa har kullum mota suke kuka da maza a kan rashin amanar soyayya, da gaske ne su
maza ba su da tabbas in dai a kan mace ne. Amma why Uwais? Mutumin da ya ke yi wa kallon
wanda ya fi kowa son Amrah? (in kina tunanin namiji na da tabbas a kanki to ki daina- Takori).
A yadda suka yi sallama da Jabeer a wayar ma duk da yana kokarin dannewa ya fahimci
ransa ya baci sosai a matsayinsa na shakikin Amrah. To ina ga iyayenta da ita kanta?
Bai dora neman aurensa a bisa tafarki na gaskiya ba tun farko don haka he must try to be a
man, ya yi dammarar facing every challenge da zai biyo baya kawai.

Duk maganganun da suke yi a kunnen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login