Showing 6001 words to 9000 words out of 10342 words

Chapter 3 - FAHIMAH Book 2 Writing by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf


mahaifiyarsa ce ta tursasa shi ya auri waccan din. Na tabbata zai kasance mai adalci a
tsakaninsu".
Alhaji Umar Dikko bai san sanda ya kwada wa Jabeer ashariya ba, har yana zaburowa daga
cikin kujerar sa, ya ce, “kun ci kaza-kazan ku kai da Uwaisun naka ku raba. Ya rike adalcinsa, ni
ma in rike ‘ya ta. Ni za a raina wa hankali?
Nan wannan Balaraben kawun nasa kamar mutumin arziki da ya zo nema masa auren me ya
sa bai gaya min gaskiya ba? Nawa Amrah ta ke da za a hada ta da kishiya ko ashirin fa ba ta
kai ba, uwarta sai da ta shekara ashirin tare da ni na yi mata kishiya, balle a yi wa tawa ranar

nata auren.
Da ma auren ba wai ya gamshe ni ba ne. Na ga amrah na so ne, shiyasa na hakura aka yi.
Amma ya yi da Umar Dikko dan Adamawa”.
Ya fiddo wayarsa a take ya kira Uwais amma ba ta shiga, ya yi ya yi ya kasa samunsa. Sai ya
juya ga Jabeer,
“Ba ni shi almuri a lambar da ku ke magana”.
Jabeer ya soma bada hakuri, wata tsawa da ya daka masa ba shiri ya latso Uwais ya mika
masa.

Uwais ya dauka Jabeer ne, don haka with much respect irin na wanda ya san ya yi laifi ya
amsa. Sai muryar Babansu ya ji yana magana a matukar hasale.
“Kana magana da Umar Dikko Baban Amrah. Ina mai gargadinka da kada ka sake ka tako
min gida, ka rubuta takardar sakin ‘yata ka ba wa Jabeer ya kawo min, ka ji na gaya maka. In
ba haka ba kuwa kotu ce za ta raba ni da kai, na rantse daga nan har kotun kolin Najeriya”.
Ya kashe wayarsa ba tare da ya saurari Uwais ba, shima da ma bai da abin cewa, amma a fili
ya sauke wayar sa, ya ce,
“Me ya yi zafi???”
Don so yana son Amrah har gobe, don she’s his first love. Wadda ya fara mallaka wa
ragamar zuciyarsa ya ba ta dukkan so da kauna. Amma duk abun mutuncin da zai hada da cin
zarafi, to fa Uwais ba ya daukarsa.
Ya yanke shawarar rabuwa da Amrah cikin wani hali na kaka-ni-kayi. Kafin Alh. Dikko ya kai
ga taba mutuncin sa. Ya gama gane iyayen Amrah ba su son aurensu kaddara da rabo ne
kawai ya kaddara auren. Ita ma Amran fama yake da ita a kan karan-kanta don ba ta dauke shi
a bakin komai ba. Hakkokinsa na aure kuwa a gantale suke yawo. Ammi ta yi gaskiya da ta ce, kyal-kyal banza ya daina dibanka. Halin mutum shi ne yake sa
wa a so shi ba nasaba ko zubin halitta ba. Amrah ga nasaba ga zubin halitta, amma ta rasa
iyaye masu dattaku, nasaba da asali ba ta yi amfani ba anan.

‘FAH-HIMAH!’.
Sunanta ya fado a ransa yana daga kwance. Ya wani irin lumshe idanunsa.
“Ita ko kara ya saka ya ce kada ta tsallaka ba za ta ko doshi hanyar ba. Ga iya soyayya in
stylish. Komai cikin class da sanyin rai hadi da girmamawa. Ba ta da wayewa kamar Amrah,
amma ta fi daidai da rayuwarsa. Tunda kuwa idan ya yi umarni za a bi shi, idan ya yi hukunci shi
ne abin bi. Me kuma yake nema a diya mace wanda bai samu a Fah-himah ba? Ya yarda Fahimah
kyautar mahaifiya ce, kuma kyautar Allah a gare shi. Amrah kuma iznah ce kuma jarrabi a gare
shi, duk son da yake mata da ita ma wanda ta ke masa rabuwarsu ita ce mafi alkhairi, domin
zukata sun riga sun baci, ko an koma za a yi ta ganin juna da tsohon tabo ne. Sannan upbringing na gidan su Amrah bai yi daidai da wanda yake fata wa ‘ya’yansa ba.
Fahimah ita ce daidai da shi, daidai da komai nasa.
Sun samu tarbiyyah iri daya, raino da upbringing iri daya, wanda yake fatan ‘ya’yansa ma su
taso a cikinsa…...
A bisa wadannan dalilan da ma wasu da dama, Uwais ya yanke shawarar rubuta wa Amrah

saki ba tare da ya yi shawara da kowa ba, daga Ammi har Fahimah don ya san cikinsu babu
wadda za ta goyi bayan haka.
Bai baro Switzerland ba sai da rubutacciyar takardar sakin Amrah a cikin takardunsa.

****


Yau Uwais zai sauka a Kanon Dabo, don haka Ammi, Fahimah da Talatu kowacce tana tsaye
a kan kafafunta tun safe. Yau kwanaki uku ke nan Ammi ba ta komai sai gyaran Fahimah da
kayan mata masu inganci wanda a baya ba ta samu damar hakan ba.
Musamman ta yi wa Hajiya Asabe waya, ta ce ta kawo gudunmawa, gobe ‘yarta za ta tare.
Hajiya Asabe a ranar ta zo da babban shirinta har da dafaffiyar kazarta cikin romon maganinsu
na Sokotawan usli.
Tun jiya Ammi ke ciyar da Fahimah nau’i-nau’in abin da zai kara ni’imtata, ya bambanta da
sauran mata a wurin Uwais ko ya daina yo mata kwashe-kwashen ‘ya’yan masu kudi (ta
bakinta), wadanda ba su san mutunci ba.
Fahimah ba ta san amfanin abubuwan da Ammi ke ta dirka mata ba, amma tunda dadi gare
su a baki ba ta da matsala da su. Sai a daren ranar ana i gobe zai dawo ne da ta shiga toilet
don yin wanka kafin ta kwanta, ta ji jikinta gaba daya ya sauya, tafi-tafi ta ji ba wanda ta ke son
bude ido ta gani sai Uwais domin gaba daya Ammi da Hajiya Asabe sun rikita hormones dinta. Don haka tana fitowa daga wanka yau tun kafin lokacin hirarsu ya yi ita ta kira shi da kanta,
Uwais na dauka ya ce,
“Anything special for Uwais?”
Ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce, “Ya Uwais, yaushe za ka dawo ne?”
“Gaya min tukunna, mene ne damuwar?”
Nan Fahimah ta hau kame-kame, “Ba wani abu fa Uwaisu- Uwaisunmu ni da yayata Amrah…
I just want to see you, it is almost 70days ban sanya ka a idanuna”.
Uwais ya ce, “Kin ma fadi gaskiya za ki yi bayani dalla-dallah in na iso domin Fahimah na
tara da yawa.... only Fahimah can treat my unnamed illness”.
Fahimah ta kai tafukanta ta rufe fuska tamkar Uwais yana ganinta. Da sauri ta kashe wayarta
bayan ta ce, “Ya Uwais I’m not a doctor”. Ba ta karasa jin me yake cewa ba ta kashe sabida
yadda muryarsa ta saukar mata da wata irin kasala.
Sallamarsu ta daren jiya ke nan.

Kafin su gama aikin abinci ita da Talatu, Ammi ta yi kiranta. Tana zuwa dakinta ta ce, “Bar
aikin nan wa Talatu, ki zo ki yi wanka da ruwan turaren nan, in kin fito ki zo ki yi tsugunno a kan
wannan turaren, sannan ki saka kayanki”.
Fahimah ta bi umarnin Ammi. Da ta gama ita da kanta sunsuna kanta ta hau yi sabida dadin
kamshin da jikinta ke mata. Ta rasa ina Ammi ta samo wadannan mayatattun traditional
turarukan.
Fahimah ta shirya cikin wani pink voyel wanda aka yi wa aikin dutse mai matukar kyau da
tsari, babbar riga ce Senegales, Ammi ta ce ita za ta je ta dauko Uwais daga airport anjima, ita
ba ta jin dadi, ba za ta iya tuki ba.

Duk da hannunta ba wai ya fada da tukin ba ne, wani zubin Ammi tana ba ta sai ta makala
mata learner.
A shagwabe Fahimah ta ce, “Ammi gaskiya ni ba zan iya zuwa dauko Yaya Uwais ba, wallahi
Ammi kunya nake ji”.
Ammi ta yi banza da ita ta ci gaba da shan shayinta, daga bisani ta ce, “To a barshi a can,
kada a dauko shin, asarar wa? In don ta Safeeyyah-Basudaniyyah ne tana da ‘yarta, wata ce za
ta yi asarar miji”.
Dariya fahimah ta yi don in Ammi ta so raha kamar kakarta ta ke komawa.

Ta dade a gaban madubi (dressing mirrow) tana kalmasa daurin kallabi, ta yi ta kwance ta
sake daurawa, ta rasa wanne za ta bar wa Ya Uwais ya gani ya san cewa kwalliyar yau
musamman don shi aka yi. Sai da Ammi ta kwala mata kira cewa lokaci ya kure, sannan ta
hakura ta fita, bayan ta feshe jikinta da turaren oud midnight ta cakuda da (cerruti) ta yafa
yalwataccen gyalen da ya shiga lightly da kayan jikinta, sannan ta fito.
“Na fito Ammi sai mun dawo”.
“Sai ki hanzarta, it’s almost past 8 now”.

Fahimah tuki ta ke a hankali ba ta gudu, sannan ba ta hawa tsakiyar titi da gani dai za ka san
‘yar koyo ce.
Tun daga ‘Yankaba har airport sabida lattin da ta yi tuni jirgin su Uwais ya yi landing suna can
suna kokarin fitar da kayayyakinsu.
Ta tsaya daga can gefe, idanunta a kan kofar fitowarsu, yadda duk mai fitowa sai ta ga
fuskarsa. Ba ta yi tsayuwar mintuna ashirin ba ta hango shi yana tahowa sabe da jakarsa. Ya
maka bakin glass (GUCCI) a idanunsa.
Ba don ta yi masa farin sani ba, sama da shekaru sha takwas da ko kusa ba za ta gane shi
ba. Domin kyawun da ilhamar sun ninka na baya, kasar Switzerland ga dukkan alamu ta gama
karbarsa. Farar fatar nan ta yi luf! Sassalkar gashi ya kwanta a gefe da gefen fuskar wanda a
baya ba ya barinsa bai aske ba. Sai ya koma Balarabensa sak da sirkin rayuwar kasar sanyi. Ta gabanta ya gifta ba tare da ya gane ta ba. Sai kawai ta bi shi a baya. Har suka fita daga
reception. Ya duba agogon (swatch - blustery) da ke daure a damtsen hannunsa yana kallon
hanyar da jama’a ke bi. Kamar daga sama ya ji muryar Fahimah a bayansa.
“Maraba, lale, Ya Uwais!
Na kara baki ko akan nawa, shi ya sa ba ka gane ni ba?”
Da sauri ya juyo cikin wani irin yanayi, “Fah-himah, ke ce da kanki ki ka zo daukana? Wow!
Lucky me’. Ya sa hanun damansa ya janyo ta barin damansa, daya hannun rike da bakar
jakarsa. Kunya ta kama Fahimah, ta soma kokarin zamewa don ga mutane nan birjik suna
wucewa, wasu suna shigowa. Ya ki ba ta damar hakan, domin kuwa ya rike ta gam-gam, suka
zama kamar madara da bombita (black & white) suna taku tamkar ba su so, zuwa inda ta ajiye
motar Ammi.
Ya bude booth ya sanya jakar hannunsa, sannan ya ce, “Ba ni makullin, ban shirya mutuwa
yanzu ba da zan hau tukin ki. Ban dauki bakaken ‘ya’yana ba masu yi min addu’a? Ammi wane
ganganci ya sa ta ba ki mota? Anyway, ni ta taimake ni cikin dimbin alfarmominta da ba sa
karewa a gare ni”.

Ya karbi mukullin daga hannun Fahimah, ya bude mata gidan gaba ta fara shiga, sannan ya
zagaya ya shiga ya zauna. Yadda yake treating dinta like a queen wajen shiga motar kadai
abun ka tsaya ka kalla ne.
Maimakon ta ga sun dauki hanyar ‘Yankaba sai ta ga Uwais ya karkata kan motar ya dauki
hanyar Sultan Road. Suna tafe a motar yana satar kallonta yana fadin, “Fah-himah kin kara yin
baki, amma kin kara yin fresh, in ji dai ba aikin wahala ki ke yi ba? Kodayake ko zirga-zirgar
makaranta cikin ranar kasar Nigeria ya isa ya sa dalibi duhu”. Fahimah ta ce, “Umh, ina muka nufa ne Ya Uwais?”
Ya ce, “Inda ya kamata masoya kuma ma’aurata su samu privacy, kafin mu je ana kulle min
mata ana saka min ka’idodi”.
Fahimah ta gintse fuska ta ce, “Da wa ka ke kenan? Ammin?”
Ya ce, “Akwai mai rike min mata ne bayan ita da zan kyale shi yana abin da ya ga dama idan
ba ita ba?”
Fahimah ta marairaice fuska tace, “Ni dai babu ruwana Ya Uwais, mu wuce gida don Allah.
Ammi na can na jira, ta tanadar maka abinci, in ta ga mun dade me za mu ce mata?”
Uwais ya wani irin juyo ya dube ta yana shigar da sexy eyes dinsa can ciki, ya ce, “Akwai
abincin da ya kai black wife dina dadi ne? Ki bar ni in mori kuruciyata kafin furfura ta zo ‘ya’ya
su cika gida su hana ni sakewa”.
Ya karasa fada ta hanyar sanya hannun damansa ya rungumo ta gaba daya, saura kadan
sitiyarin motar ya kufce masa. Fahimah ta zaro ido tana fadin.
“Ya Uwais kada ka zubar da mu ba mu ajiye wa Ammi ‘ya’yan da ta ke buri ba”.
Maganar Fahimah ba karamin dadi ta yi wa Uwais ba. Ya kara kankame ta da hannu guda
yana tuki da dayan cikin gwaninta har suka zo gidan sa.

Maigadi yana nan don Uwais ba ya wasa da hakkinsa da extra ihsani. Suna zuwa ya zo da
gudu ya bude musu yana ta faman sannu da zuwa wa Uwais, Fahimah ta yi gingirin a cikin
mota ta ki ko motsi bayan Uwais ya kashe motar ya bude mata kofa.
“Fito mana my sweet 16? Ko sai an ja min ajin ne yadda aka saba? Kiyi a hankali kada ya
tsinke don na kusa hango ta uku”
Fahimah ta tsuke baki ta tattare gira ta ce, “Ya Uwais! Ba zan shigar wa Amrah gida don ba
ta nan ba, Ammi ta ce kowa da gidanta, ta ya ya za ka kawo ni gidanta?”
Uwais ya kankance ido cikin mamaki.
“Gidanta ko gidana? Nawa muka hada ni da ita muka sayi gidan? Tun muna shaidar juna ki
fito, ko ki ga abun mamaki a cikin motar nan”.
Amon muryarsa kadai Fahimah ta ji ta gane asalin Uwais dinta ne rigimamme, mara karbar
uzuri kuma mara ragowa ta wannan bangaren. He will go far beyond abin da ya ce din in ta
sake ta ki bin umarninsa, to kuwa maigadi zai sha kallo daga inda yake zaune. Motar Ammi
farin gilashi kal gare ta. Kafa a mace ta zuro ta kasa ta sauko tana turo baki tana kunkuni, “Haka kawai daga
zuwanka sai rigima? Ba za ka bari mu gama gaisawa ba?”
Uwais ya sanya mukulli yana bude falon gidansa, ya ce.
“Akwai gaisuwar da ta fi wannan ma’ana ne?”
Ya karasa fadi ta hanyar janyo ta cikin falon da wata irin azama. Kamar yadda ta yi tsammani

farkon love making din Uwais hot and deep kisses ne a kullum, amma na yau ya fi na kullum
domin a urunce yake sumabatarta a ko’ina, kusfa-kusfa yana yi yana kiran sunanta. Abin har sai
da ya koma ba ta tsoro, domin ba ta taba ganinsa a cikin kwatankwacin irin wannan bukatuwar
ba. Tamkar bai taba kusantarta ba sai yau… ya ba ta dukkan soyayyarsa, ya ba ta dukkan
amanarsa da sirrikansa wanda daga ita sai Ubangijinta sai shi suka sani. Wani hidden side ne
na Uwais da ko Amrah ba ta taba gani ba don ba ya jin tsananin urge din da yake ji akan Amrah
kamar a kan Fahimah.... wadda ta zo cikin takaitaccen lokaci ta gigita duniyarsa, ta canza ta, ta
fahimtar da shi a baya ba soyayya yake ba, sha’awa ce ta kyawun halitta.
Duk da haka har gobe yana son Amrah, amma yana ganin rabuwar tasu ita ce mafi alkhairi a
gare su baki daya. He will miss Amrah, amma yana da yakinin yanzu zai iya rayuwa ko babu ita.
Infatuation dinsa a kanta kullum kara raguwa yake yi, anya haka Ammi ta barshi? Wane irin sirri
ne haka tattare da Fahimarta? Uwais ya kasa shiru, a bisa doguwar kujerar falonshi suke yana kanannade jikin Fahimah
domin ta yi rantsuwa ba za ta hau gadon Amrah ba, dakinsa ma ba za ta shiga ba tunda kuwa
Ammi ta raba tuntuni, duk wani hali na Ammi na tsayuwa a kan magana daya ya lura Fahimah
ta dauke shi tsaf. Don haka ne ya sa shi ma ya hakura ya kyale ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login