Showing 9001 words to 10342 words out of 10342 words

Chapter 4 - FAHIMAH Book 2 Writing by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

suka sha soyayyarsu anan
falon shi kamar babu gobe… a karshe Uwais bai yi mamaki ba da ya ji damshi a idanunsa,
‘Hawaye yake yi ba tare da ya sani ba'. Fahimah ko a aljannah yana fatan a bar masa ita kadai
a matsayin hurul eeninsa. Ya yafe 'yammatan aljannah.

“Ki yafe min Fahimah, hakika na yi kuskure a baya wanda yake hunting dina har gobe. Da
zan iya da na maida bara-bana, na gyara all those inconveniences da na wanzar a tsakaninmu.
Dana hadiye kalamai na na baya marasa dadi akan ki.
Watakila har in koma ga Ubangijina ba zan daina nadamar abin da na yi miki a baya ba. Ni
dai na san a halin yanzu hukunta ni Ubangiji ke yi da hakkin ki, soyayyar ki nema ta ke ta kashe
ni…”.
Fahimah ta kai tausasan yatsunta ta toshe masa bakitana girgiza kai, cikin wata irin tattausar
murya ta ke magana.
“Tashi mu tafi wajen Ammi haka Ya Uwais, ko ta ganka ta ji dadi a ranta itama. Na ga Uwais
after 70days, na kasance cikin alfarmar Uwais after 70days ....in a way and manner da na
tabbata wata diya mace ‘yar uwata ba ta taba samu ba.
Idan na rike Uwais a raina bayan duka wannan ni’imar da Allah ya yi min ta mallaka min shi
matsayin mijina uban 'ya'ya na, na zama mara godiyar Ubangiji.
Besides, an ce so hana ganin laifi Ya Uwais, ni fa ban taba jin haushinka ba, karewa ma
komai ka ke yi burge ni ka ke yi. Rana daya ce na ji haushinka a rayuwata, ranar nan a
Sudan…”.
Da sauri shi ma ya toshe mata baki yana girgiza kai, "Kada ki tono abin da ya riga ya wuce,
domin na tabbata alhakin wannan ranar ba nawa ba ne, naki ne. And i sincerely repented, so ni
da ke duka masu laifi ne kuma tare za mu ke istigfari”.
Let’s go for another ......…” Ya rada mata sauran maganar cikin kunnuwanta.
“Umh…” Fahimah ta iya cewa domin dadin bakin Uwais in yana son abin da yake so yawa
gare shi, ba ta da ikon musantawa don bai ba ta damar hakan ba ma.

Ammi ba ta gansu ba sai karfe sha daya na dare. Fahimah sai baya-baya ta ke yi daga bayan
Uwais da ganin ta ka ga mara gaskiya. Shi ko Uwais ko a jikinsa, karasawa ya yi da sassarfa ya
rungume Ammi ya sumbaci goshinta. Da wannan damar Fahimah ta yi amfani ta gudu dakinta,
ta barsu suna tasu soyayyar ta da da mahaifi. Har wata ajiyar zuciya ce ta kwace mata da ta
ganta a dakinta. Ba tare da ta karbi query daga Ammi ba.
Ammi kuwa ba ta bi ta kan wannan ba, farin cikin ganin Uwais ya ishe ta. Sun gaisa sun sake
gaisawa har da musabaha irin ta larabawa. Ta ce, “Uwais kamar ba kai ba, Switzerland ta
amshe ka, ina fatan an yi nasarar duk abin da aka je nema?”
Uwais ya ce, “Nasara kam an same ta Ammi alhamdu lillah, ga sabon albishir da nake son yi
muku, World Bank da muka je yin course dasu sun ba ni aiki tare da su a yanzu haka, na bar
GT idan na dawo. Yanzun ban karasa ba saura sati 3 mu gama gabadaya, na ga cewa ya zama
dole in zo in saita al’amuran gidana”. Ammi ta ce, “Ina yi maka ta’aziyya Uwais, Allah ya sanyaya, Allah ya ba mu rayayye. Sannan
sai ka kai zuciya nesa ka yi hakuri da Amrah, don kuwa laifi kan laifi ka yi mata. Don haka ka
jure duk abin da za ka gani ko za ka ji daga gare ta ko iyayenta, tunda kai ne mai laifi”.
Uwais ya yi murmushi kawai ya mike, bai gaya wa Ammi abin da Alhaji Umar Dikko ya ce ba,
na cewa in bai sako masa Amrah ba zai kai shi kotun koli. Da kuma hukuncin da zuciya ta
kwashe shi ya yanke tun a lokacin ta sakin Ammi, yanzu haka takardar tana cikin kayansa, jira
yake zuwa jibi in ya kara hutawa ya runtse ido ya kai wa Jabeer. Yana addu’ar Allah ya sa kada rabuwarshi da Amrah ta yanke kyakkyawar alakar da ke
tsakaninshi da Jabeer Dikko.
Wanka ya sake yi sannan ya sa farar shirt (Hilfiger) da wandon jeans dark blue ya fito falon
jaye da akwatuna guda biyu.
Ya samu Ammi tana marking takardun dalibanta da medical glass a idanunta. Ta daga
kyawawan idanunta ta dube shi tana murmushi.
“Sai ina kuma? Na ganka ka dau wanka ka janyo akwatuna? Ko bikon za a tafi cikin daren
nan?”
Murmushi Uwais ya yi ya zauna a gefenta yana bude akwatunan, ya ce,
“Ammi bikon lafiya? Laifin me na yi da zan je biko? Na dauka bayan Amrah da Fahimah ina
da damar kara guda biyu ba tare da na yi wa Ubangijina laifi ba?”
Ammi ta ce, “Haka ne, amma a al’adance ka yi laifi ba a addinance ba. Ni dai ban yi wa kowa
cikinku laifi ba daga kai har Amrah domin kuwa auren Fahimah na sa aka fara daurawa, ban
kuma ce wani cikinku ya boye zancen ba, don haka can ta matse muku kai da Amrahn. Amma
ina so ka yi hakuri ka dauki girma ka amsa laifinka, sannan ka bada hakuri ta dawo dakinta.
Kowa ta zauna a gidanta, ban yarda da hada muhalli ba”.
Uwais bai ce komai ba, ya rika fidda tsala-tsalan atamfofi, shaddodi da lesuka yana tulewa a
gaban Ammi, ya ce, “Ammi ga tsarabarku. Sai ki zaba wa Fahhimah wanda zai dace da ita, I
don’t know her favourite colours yet, kuma ban yi azancin tambayarta ba”.
Ammi farin cikinta ya fi gaban misali, “Allah ya albarkaci rayuwa Uwais. Amma ni tsohuwa me
zan yi da wadannan kayan gayun? Na bar wa Fahimah bakidaya tunda tarewa za ta yi, ta je ta
yi ta yi maka kwalliya da su’.
Murmushi ya yi ta sake cewa, “Ina na Amrah?”

Kamar ya ce mata, “She’s no longer Mrs Shagari now”. Ya tuno halin Ammi na dattaku ba za
ta bar shi ya bada takardar nan ba ko da za su kai shi kotun.
“Zan kai mata jibi in za ni, don gobe tun safe har dare in na fita ba zan dawo ba, zan maida
hankali a kammala komai na gidan Fahhimah ta tare jibi, don tare za mu koma Switzerland
tunda sun yi hutu, wata daya ne na gama gaba daya don a reshensu na Najeriya za'a ajiye mu.
Kuma a garin Abuja ne, don haka zan nema wa Fahimah transfer zuwa (BAZE) tunda ta gama
year 1”.
Ammi ta ce, “Hakan shi ne daidai, ni bana bayan miji na wani gari matarsa tana wani saboda
kananan dalilai. Duk abin da zai zama dole ba a barshi a nemi alternative a zauna tare a nemi
lahira. Tunda duk wani buri na duniya an gama samunshi, ilmi, career da aure na hakikah.
Yanzu sai shirin tarbar abokai da kawayen Ammi.
Sannan Uwais na aika takardar murabus daga aiki, idan kun dawo daga Switzerland kun
nabba’a a permanent sabon muhallinku, ni kuma zan koma SUDAN gaba daya, a can zan
karasa rayuwata. In kun haifa ku kai min Khartoum zan rike muku”.

Mu hadu a book 3 na karshe

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login