Showing 1 words to 3000 words out of 24534 words

Chapter 1 - GIRMA YA FADI 2 Hausa Novels Complete By Takori .pdf

[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: GIRMA YA FADI 2
Cikin su ya duri ruwa, idanunsu ya raina fata suka yi jigum-jigum. Ba sai ga Imran da kan
wayoyi har uku ba? Har cikin dakin barcinmu ya shigo yake tambayar ina Zaynab? Da fari sun
tsorata sun dauka zancen jiya ne ya kawo shi, don haka a tsorace suka ce tana toilet tana
brush. Ya ce, “To madallah, ga tsarabar ku, saura in ji ana kiran ‘ya’yan banza”. Ni dai sai ihun
su Azizah na jiyo don wayoyi ne ya kawo mana ‘yan uban su duk iri daya (Nokia), sai dai duka
ba layi nawa ne kadai ya sanya layin ‘glo’. Ni dai tunda na karba na jefa kasan filona ban kara
tunawa da ita ba, don ba ita ce a gabana ba jarabawar da nake yi ne.
Yau da muka fito paper din ‘geography’ Mr. Segun ya biyo mu, tun farkon zuwan su yake min
nacin na tsaya na saurare shi na ki, an turo shi invigilating ne daga Minna jami’in NECO ne, ga
tsagun nan na Nufawa rankacau cike da fuskar shi, amma shi tsakanin shi da Allah sona yake
yi da aure kuwa ba da wasa ba. Su Iftihal dariya yake basu, idan kuma ya rubuto masu amsa su karbe su kwafe babu ko tsoron
Allah, su koma bayan idon shi suna dariyar shi. Ga mamakin su yau tsayawa na yi da Mr.
Segun ina jin wadda ya zo da ita, wato yana so in kwatanta mishi gidanmu ya zo, yana so in
mun kare jarabawa zai aure ni, kar in damu da matarshi da ‘ya’yansa ba zai hada mu gida daya
ba.
Na ce masa, “To”. Ya ce, “Wane gari nake son zama? Minna ko Sokoto?” Na ce, “Duk inda ya fi
maka sauki”. Dadi ya kama shi sai washe baki yake. Daga can gefe kuma GG ne zaune a benci
yana kallon mu fuskarsa a hade. Mr. Segun ya tambayi nambar wayata na ce da shi ban rike ba
tukunna yau aka bani wayar, amma gobe zan kawo mishi. Ya rasa inda zai sa kanshi don dadi,
muka yi sallama kamar ya goye ni ya gudu dani.
Ina yin taku biyar don cimma su Azizah sai ganin GG na yi a gabana kamar an jefo shi, tsulum!
Ya ce, “Wato don wulakanci Zaynab don kin ga na damu dake kike yi min duk abin da kike yi
min?” Na ce, “Ba wulakanci bane GG na ga irinmu fitina ne a bayan kasa, shine nake jiye maka
haduwa da fitinar mai narka-narkan mazauna”. Ya fashe da dariya, daga nan inda nake ina iya jiyo mugun doyin da bakin shi ke yi. Ya ce, “Don
Allah don Annabi Zaynab ki yafe min ki bar TUNA BAYA….., wallahi tun a lokacin son ki ne ya yi
min yawa nake kuma neman hanyar da za ki kula ni na rasa……”
Na dan juya don gano su Azizah, na hango su duk a nutse cikin motar Ya Im suna ta jirana, shi
kuma yana jingine jikin kofar motar wadda take a bude, ya dage kafarsa ta hagu ya jingineta
jikin motar ya harde hannuwanshi a kirji, manyan idanun shi fes a kanmu. Ban bari ya fahimci
na san da tsayuwar shi ba, da na kakaro wani lallausar murmushi na kwarawa GG bai san
sanda ya sanya hannu a aljihunsa ya rarako duk abin da ke ciki ya miko min ba, ni ko sai na ce,
“Mai da abinka muje ku gaisa da Yayana ga shi can, dama ya ce yana son yin abota da kai tun
sanda ka sani wankin toilet, shine waliyi na a wajen shi za ka karbi aure”.
Da GG ya hanga ya dubi Ya Im, kayan jikinshi da irin motar da yake tsaye a jiki, duk da ba a
gano kwayar idanunshi ya saya ta da bakin gilashi (blackmail) sai ya rikice, ya ce, “A’a, ayi haka
Zaynab? In ce ko ba gatsen da na yi miki a kan a koreni daga aiki kika dauka da gaske ba? Ki yi
hakuri don Allah ki yi mun arziki, wannan aikin da shi nake ci, nake sha ni da iyalina da
gyatumata. Kuma wallahi karya nake bani da wata gonar gado wani busasshen kango ne kawai
a kauyen mu”.
Na yi mai murmushin kwantar da hankali na ce, “Kai dai tunda na ce ka zo muje, to ka zo muje,

baka san alheri irin na Yayana ba, cewa fa ya yi zai sa a mai da kai principal dinmu”.
Ai jin haka GG ya gyara hula tare da gyara zaman kwalar rigar shi, ina tafe yana biye dani
kamar wani mai take min baya. Shi kuma Ya Im ganin mun nufo shi sai ya shiga mazaunin shi
ya zauna, garam ya rufe kofa ya danna wani abu a jikin hannun motar tintics suka rufe mana ido
rufe bakake sidik, kan in ce me! Ya ja motarshi aguje ya bude mu da kura muka yi futuk ni da
GG, amma GG bai damu da kansa ba sai sannu yake min, na tabbata da da hali ma da ya
karkade min kurar da ta bata fararen uniform dina.
Wata matsiyaciyar kunya ce ta kama ni, domin bayan GG akwai sauran malamai da dalibai da
dama da suka ga faruwar al’amarin da basu ga dalilin shi ba. Ban ko bi ta kan GG ba na yi gate
ina share hawayen wannan wulakancin da Imran ya yi mani a bainar jama’a, wata zuciyar kuwa
sai ta ce dani baya da laifi, ai ba ubanki ne ya saya masa motar ba. Achaba na tara ya dawo dani gida har cikin gate, lokacin Imran na tsaye tare da wani abokin shi
Jabir suna magana. Gaba daya suka juyo suka zubo min ido ina lalubo kudi a jakata don bai wa
mai babur, ya kara kuluwa iyaka da ya ganni na dare a bayan mai mashin, ya kuta ya kada kai
ya mai da hankalin shi ga Jabir yana ta yi masa magana amma shi hankalinshi da attention din
shi duk yana kaina. Sai da na wuce cikin gida sannan Jabir ya ce (yana nuna hanyar da na bi
na kule) da dan alinsa, “Wannan (fresh baben) fa Imran? Yanzu dama kuna da irin wadannan a
gida ka barni ina bin kadangarun bariki karmasassu?”
Imran ya wani irin juyo ya lafta mishi harara, kamar ya yi aman zuciyarshi don takaici, ya ce,
“Idan za ka yi iskancinka ka san a inda za ka yi shi, me kake nufi? Kannen nawa ma basu tsira
ba? To ahir dinka, kuma in gaya maka ba a nan gidan ba, kuma wallahi ka yi kadan ka lalata
min kanne J.B, su basu san irin wannan rayuwar ba yara ne, kada ka sake ko da wasa ka kula
su, ka ga hanya sai mun hadu…..”
Yadda ya fitittike yana ta fada ko idanunshi baya iya budewa, duk sai ya ba Jabir dariya, ya kara
kular da shi da cewa, “Kanwar ka? Ta ina kuma? Wannan Balarabiyar haka? Na san Iftihal da
Azizah amma wannan kam ba ‘yar gidan nan ba ce, don haka ina kamu babban Yaya, kuma ka
yi hakuri ni ba da manufar da ka fassarani ba nake son ta, ina nufin…. da aure!” Wayyo Allah! Karshen ta dai Imran sai shigewa ya yi gida ya barshi a nan don ya san muddin ya
ci gaba da sauraron shi, za ayi batacciya, amintar shekara da shekaru ta zama tarihi.
Su Azizah me za su yi da gani na ba dariya ba. Nima dariyar ce kuma ta kama ni na taya su
muka yi ta yi sai da muka yi mai isar mu. Na ce, “Ni yau na ga abin da ya fi karfina, kunyar
duniya yau kam na gama jin ta, kin ganni kuwa goye a bayan acaba? Sai ka ce wata karuwa,
kai Allah ka yafe mini”. Mama ta shigo tun daga falo take cewa, “Meye dalilin tahowa a bar Zaynab ta hawo acaba?
Kuna tunanin in Abba ya ji daga ku har Yayan ku za ku iya kwanan dadi a gidan nan?” Suka yi
tsit, na yi saurin cewa, “A’a, Mama wallahi ba laifin su bane, na bi wata kawata ne cikin kwatas
din malamai zan amso (past question pepers) sai basu ganni ba suka taho”. Ta ce, “Rufe min
baki, ai dama kullum ke a wurin ki basa laifi, in ban da iskanci a jira ki man ko a nemo ki, sai a
taho a rabu dake? Ni kam ba da ni ba, Allah wannan Abba zai yi hukuncin sa, don Zaynab ‘yar
aman ce a hannu na. in kuma da wani mugun abu ne ya same ki fa a cikin makarantar shima
haka za a taho a rabu dake?”
Ganin ranta ya baci ba da wasa ba, gaba daya muka shiga ba ta hakuri kar ta gayawa Abba har
da hawayena, ta ce, “To gaya min gaskiyar dalilin tahowar a barta, in ba haka ba, ba makawa

wallahi sai na gayawa Abba”. Na ce, “Wallahi laifi na yi masa”. Ta ce, “Shi waye?” a sanyaye na
ce, “Ya Im”. Ta zaro mana ido ta ce, “Laifin me?” Hantar cikina ta kada, wani fitsari ya kulle min
mara ban san takamaiman abin da zan ce ba.
“……. Ai laifin da Zaynab ta yi mun Mama kema in kika ji sai kin hukuntata”. Gaba daya muka
juya muka dube shi, yana bakin kofar bai shigo ba, hannunsa na dama dafe da kofar fuskarshi
babu alamun wasa. Ya ce, “Mama Zaynab ce mai rubuta jarrabawa su Iftihal su kwafa, da na yi
magana suka mai dani shashasha, har wata gadara suke wai ai malaman duka samarin ta ne
ba abin da za su yi masu. Yanzu kamar ‘ya’yan V.C a ce suna aikata examination malpractice,
wai kuma har suna gaya mun har bencinsu malaman suke rubuto musu su kawo musu. Shine
yau na ce bari dai in je in genewa ido na me ake a makarantar nan?
Wallahi Mama a kan ido na Zaynab zance da maza har layi ake a kanta, in wannan malami ya
wuce sai wannan malamin ya zo. Wani kuma har da kwaso kudi a aljihu wai zai ba ta. Sun fi
rabin awa a tsaye duk ina tsaye ina kallon ikon Allah, can kuma ba sai na ga an nufo ni ba, ko
me za a ce min oho, na ga wannan rainin hankali da ake min ya yi yawa, ko ba ta sanni ba ai
gaba nake da ita, ya dace ta nuna ta san girmana amma wallahi yarinyar nan kamar wani
direban ta ne ya zo, kamar ba ta san da tsayuwata a wurin ba, kawai sai na ja mota na barta a
nan, don wallahi da na biyewa zuciyata a lokacin dukan ta zan yi”.
Mama ta samu kujera ta zauna tana kallon mu tana gyada kai cikin mamaki, duk muka yi
tsuru-tsuru, ba ya ni da cikina ke ta kartawa, na soma kukan da nasani da haushin Imran.
Mama ta ce, “Da gaske ne Zaynab abin da nake ji? Ke da nake yabon ki sallah za ki biye ma
wadannan shashahun ki kasa alwala”. Ni dai ba abin da na ce sai “Ki yi hakuri don Allah Mama”. Ta ce, “Ai ba zancen in yi hakuri
bane, zance ne na hukuma. Baban ku malamin makaranta ne, wadanda suka sa dokar duk
wanda aka kama da (malpractice) a kulle shi shekara biyar da tara mai tsanani. Su kuwa
malaman naku ko in ce samarin naku kora ne daga gwamnati. Ku sani Bindawa Proffessor ne
da bai wasa a kan harkar ilimi da ci gaban sa, ku bar ganin ku ‘ya’yan cikinsa, wallahi daure ku
zai yi har sai igiya tai rara…”
Idon kowacce ya raina fata, ya yi narai-narai kiris ya rage hawaye su zubo. Cikin tashin hankali
na soma yi mata rantsuwar wallahi, ban taba kwafar abin da suke bamu ba, su Ifty ne. su kuma
suka ce wallahi ba su ake kawowa ba ni ce, karba suke don su miko min amma ba don su
kwafa ba. Imran ya juya mana baya yana ta dariya, ta ce, “Sai magana ta biyu, tunda duk aure kuke so, to
ku yin hakuri ku karasa jarabawar, yaya sunan shi mai son Zaynab din da suke rabin awa suna
magana?”
Ta juya ga Ya Im, ya ce, “Na ji suna cewa GG”. Ta ce, “In ma G&G ne babu laifi, zamu tura
masa ya fito da zarar kun ka re karatun sai mu sha biki. Ke kuma Iftihal dama ba tun yau ba
Shehu yake son ki tun kina karama….., auren naku shi zai fiye min kwanciyar hankali….” Ni da
Iftihal muka soma share hawaye kamar mu mutu don bakin ciki. Ta dawo ga Azizah ta ce, “Saura ke, ‘yar kwalisa, Lawal wannan yaron na gidan Malam dan
dakin Inna Rakiya, na yaba da hankalinsa, gashi da hakuri, na tabbata zai iya hakuri da iyayin
ki, don haka zan yiwa Abba magana da daddare in ya shigo ya sanar da Malam din duka a
hada ku a aurar, in ce ko shi kenan?” Ta mike tana shirin fita, Ya Im na take mata baya yana kara zugata wai hakan da ta yi shine

dai-dai, gaba daya muka bita muka rungume muna kukan da bamu shirya ba. Na ce, “Wayyo
Allah Mama ki yi min rai, wallahi yau ne kawai na taba sauraron GG a rayuwata, wallahi ki je
makarantar ma ki tambaya”.
Da kyar da sidin goshi Mama ta fasa niyyar ta na fadawa Abba, amma ta gargademu ta ja
kunnen mu, suka rantse mata ba za su sake kwafar amsa ba, ni kuma na rantse ba zan kara
kula GG ba sannan ta kyale mu. Amma kam a ranar mun dandana kudar mu, mun ga tashin
hankalin da bamu taba gani ba. Barin ni da na tsani a zo a ce da Abba BABA SA’IDU ga laifina. Cikin dare duk su Azizah sun yi barci, amma ni kwance nake bisa filo ina ta bitar littafina. Ba sai
na ji filona na wata irin girgiza ba (vibrating), sam ni na manta da wani abu wai shi waya da na
tusa a cikin folona, na wancakalar da littafin na yi zaune dirshen a tsakiyar gado na ina ta raba
ido don fahimtar ta inda karar ke fitowa, kamin in nutsu in fahimci daga cikin folona ne. A sannan ne na tuna da wayar da Ya Im ya raba mana da safe. Na mika hannu cikin sanyin jiki
na zaro ta, an boye nambar mai kiran bayan ma ni ban shigar da sunan kowa ba. Cikin
gajiyayyar murya na ce, “Yello!”
Sassanyar ajiyar zuciya ya yi ta cikin wayar kawai amma bai yi magana ba, na sake cewa,
“Yello!” Wannan karon a dan zafafe, nan ma shiru kama babu kowa a kan layin, wani haushi ya
taso min, ina niyyar kashewa na ji ya ce, “Zaynab kema baki yi barci ba?”
Magana yake kamar baya so, ko ko an tilasta mishi yinta. Na ce a raina, “Yau na ji ikon Allah, ka
kira ni ina zaman-zamana sannan ka yi mun iko?” A fusace na ce, “Wai waye ne?” Murmushi ya
yi, duk da ban ganshi ba na jiyo sautin murmushin nasa har cikin zuciyata, muryarsa kamar na
mai fama da mura ya ce, “Plzzzzzzzz, ki yi hakuri da abin da ya faru dazu, komi da na yi na yi
ne sbaoda KISHIN KI, in san kuma baka kishi sai a kan abin da KAKE SO…”
Tsaki na yi da ya katse shi gabanin idasa tatsuniyar shi, amma hakika na yi mamaki. Ji na yi
kamar ma ba dai-dai kunnuwa na suka jiyo min ba anya Imran ne?
“Ni fa har yanzu ban san wa yake magana ba, saboda a sanina ban bawa kowa nambata ba,
sannan me aka yi min ake bani hakuri? Da kyar idan ba wrong number ka kira ba”.
Cikin zafi ya ce, “Sanin cewa baki baiwa kowa no din bane zai sa ki san da wa kike magana. Na
yi mamaki da yawa a kanki Zaynab tun dawowa ta, na kuma ci gaba da yi a yanzu. Na ga
sauyin abubuwa da yawa cikin kwayar idanun ki, wadanda a da ba sune ba. Na ga sauyuka da
dama wadanda a da ba sune a tare da ke ba. Ban san yaushe kika koyi wasu bakin halaye
masu kama da wulakanci ba wadana a gaskiya ni ba zan iya jurar su ba. Idan kuma kin ce haka
za ki ci gaba, to wallahi zan fito fili in fadawa kowa a gidan nan abin da muke ciki….”
Na yi murmushi mara sauti na ce, “Malam kuke ciki kai da wa? Ni na ji sunana radam a bakin ka
amma ni har yanzu ban san da wa nake magana ba, kuma Hausar ka bana fahimtar ta, don
Allah ka je ka koyo Hausa”. Daga haka na kashe wayar na yi tsaki, amma a zuciyata ina jinjina
namijin kokari na. Da safe da na bude wayar (txt msg) na fara cin karo da shi daga gare shi.

“Rashin sauraro na da ki kai a daren jiya, shi ya nuna kin fara sanin kanki”.

Na yi tsaki na ce a raina, “Lallai ma Ya Im din nan ya ga wallena da yawa, har yanzu bai san
wace ce Zaynabu-Abu ba, bai san wace ce Abun Faruq-Abun Baba Sa’idu ba. Bai san wace ce
Kyautar Allah, Kyautar Inna Rabi ba”.

Ko da wasa washegari bai yi gigin binmu makaranta ba, na fassara hakan da rashin son
haduwa da su GG. Yammacin ranar mun dawo kamar kullum a gajiye, na ga wata bakuwar
mota mai tsananin kyau a kofar gidan. Nice na fara shigewa cikin gida saboda sun tsaya amsar
sakon Mama a hannun maigadi. Ashe da rabon zan yi mugun ganin da ban taba yi ba a
rayuwata.
Nasa kai a corridor din da ke tsakanin cikin gida da baskwata, wani lafiyayyen kamshi ke ta
dukan hancina tun daga soron farko, ina iya jiyo shesshekar kukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login