Showing 18001 words to 21000 words out of 24534 words

Chapter 7 - GIRMA YA FADI 2 Hausa Novels Complete By Takori .pdf

jefa Innata na taraddadin inda take, da halin data ke ciki
tsayin shekaru goma sha takwas har ta mutu da shi a zuciyarta. Sai na daukarwa kaina fansar
rabani da duk wani farin cikin rayuwa da ta yi, sai na dauki fansar dan uwana Imran a kanta…..
​ Ban san sanda na soma sheshshekar kuka ba, tun inayi a hankali har ya fito cikin motar
mutanen motar suka ji shi, su a tsammanin su har yanzu tunanin abinda 'yan fashinnan suka yi
min nake, shine har ya sani kuka. Wannan dattijuwar tace "yarinya ai kin auka arziki, ki godewa
Allah ba kuka zaki yi ba. Keta haddin da akewa al'ummar mu a wannan hanyar a shekarun
baya, ai ba zaki so ki ji shi ba, banda yanzu da muke cikin gwamnatin “mace tamkar da maza
Hajiya Nuratu Mainasara”, ai da wannan tallafin da kika samu baki same shi ba.
A gaba dayan gwamnatocin da mukayi a baya, bamu samu gwamnatin da tayi tsaye akan
harkar tsaro da yaki da miyagun dabi'u kamar ta Mainasara ba. Ruwa ya wadace mu, wuta
kuwa bamu da matsalarta, idan kuwa aka koma ta fannin lafiya a garuruwan kasar Nijer baki
daya ba zaki samu nagartattun asibitocin gwamnati kamar namu ba, duk a cikin shekaru ukun
da Mainasara tayi tana aikinta.
Ta fannin ilimi kuwa, fensir wannan bamu san nawa ake sayawa 'ya'yan mu ba, duk ita ce take
basu har littafin rubutu. In kuma aka koma ta fannin albashin ma'aikata da malam makaranta,

duka Nuratu ta ninkashi. Farin rashin abincin da akayi kuwa akasar nan shekarar baya, mu
mutanen Dagamaram bamu san da shi ba.
Ta yi mana ayyukan da maza da dama, suka kasa, ta cika dukkan alkawurran data daukar
mana, ta cikawa jihar mu burinta na shekara da shekaru. Don haka kuri'armu duk na wannan
karon ma mun tabbatar mata nata ne, mu al’ummar Damagaram! Tunda ai munyi Gwamnatin
mazan shekara da shekaru bamu ga me suka kulla mana ba, sai zalinci, sata, cin hanci, da
rashawa, amma a gwamnatin MAINASARA babu wannan".
​ Daga can gidan gaba wani magidanci ya karBe, “kin manta da inganta tituna da
hanyoyin sadarwa, kafin Nuratu, ina muka samu wannan gatan?” Wani ma ya cafke, "kwarai
kuwa, ga dakakkiyar zuciya da rashin tsoro, don duk barazanar abokan adawa baya sata fasa
kudurinta na alheri. Duk girman buzu da rawaninsa baya bata tsoro, balle ya sata cin amanar
talakawan Jihar ta.
Ni kam da ana tazarce sau goma, da na cigaba da jefawa Nuratu kuri'ata har a nade birnin
Damgaran. Babu abinda zamu ce akan Mainasara sai Allah ya karya makiyanta, ya tabbatar da
kujerarta ta gaba, ya zama jagoranta a rayuwa, kada ya bawa makiya da mai nufinta da sharri
iko a kanta…." na yi murmushi, a raina nace "irin mu ke nan, amma yabin da ake miki ba zai sa
ni yin kasa a gwiwa ga fiddo musu ainahin your real colour ba, sheep in a wolf clothing.

A dai-dai lokacin da motar ta tsaya cikin babbar tashar Damagaram, kowa ya fito ya kama
gabansa, anan ne idanuna suka raina fata, don ban san inda zani ba.
Na tsaya ina ta raba ido har a cikin tashar hotunan ta ne a ko ina. Garin cike yake da hayaniyar
siyasa data kacame a lokacin da bana fahimta, domin yarurruka ne sukeyi daban-daban, ko
kuwa nawa kunnen ne, oho! Duk da cewa mafi yawa hausa suke yi amma wata irin
gurbatacciya ce da wadda na taso a cikinta. Na matsa ga wani mutum mai sai da shayi a irin dogayen butocinnan nasu masu garwashi a
kasa, nayi msa sallama, kallona kawai yake bai ce min komai ba, bai kuma amsa sallamata ba.
Na dangata hakan da rashin yarda dani sabida yanayin shigata data ban-banta data sauran
matan dake wucewa, ga nikab dana maka kamar matar limamin masallacin Makkah. Na
tambayeshi ko ina ne gidan saukar baki mafi kusa?
​ Yayi magana cikin harshe faransanci mai nuna baya jin yare na, na canza na koma
turanci, nan ma ya gyada kai, bai gane ba, to fa! Na matsa ga na kusa da shi wani mai saida
taba shima duka yarukan nawa ba jin su yake ba, dukkan su buzayene na sosai nade cikin
bakin rawani, sai idanun su da dogon karan hancin su kawai kake gani. Sai na koma kwatanta
musu gidan saukar baki (Guest House) nake nufi, sai ya yi gaba abinsa ya rabu dani, a ransa
nasan cewa yake in gaskiya ne abun naki, ki bude fuskarki mana.
Ni kuwa tun daga kan dan fashinnan, dana fahimci fuskar nan ta zaga ko'ina a Niger, ba zan
kara yin saken da zan budeta ba. Don bansan me hakan zai kuma jawomin ba. Sai na tafi bakin
hanya na tsaya ina kallon giftawar motoci akan titi jefi-jefi, don bansan wace iri ce tasi ba.
Cikina in banda kiran ciroma babu abinda yake, nayi wujiga-wujiga da yunwa, gajiya rashin
kwanciyar hankali da rashin barci. Daga baya na naji wani zazzakan horn din mota irin na YA
IM, watau mara gigita mutum, mara karar dake gundurar mai jinta. Naki juyawa na cigaba da
tafiya cikin nutsuwa, domin bana daya daga cikin mutanen da ‘horn’ din mota ke sa su waiwaya. Ya wuce ni yayi parking tsaleliyar farar motarsa mai kofa daya (hemi) can gaba da ni kadan,

kamin ya fito ya kulle ya doso inda nake tsaye. Saurayi ne ba'abzinen usli jajur da shi, mai
lallusa kuma suma nannadaddiyar suma baka wuluk kaman ya hada jinsi da larabawa.
Ganin da nai mishi cikin hasken farin wata da duhun dare, shi ya hanani gane hakan a daren
jiya. Sanye yake cikin (dark green) shadda ‘yar Mali dinkin tazarce sai daukar ido take, abinka
da farin mutum, kada ki so kiga yadda kalar shaddar ta fito da shi, kansa ba hula, wadda na lura
ba al'adar mazan garin ba ce. Matashinnan ne da muka shigo mota tare dashi daga MaradI,
ban san daga ina kuma yaje ya dauko mota cikin mintuna ashirin ba, ban san dalilin sa na son
yi min shishshigi, cikin rayuwa ba, bayan a zahiri ko fuskana bai gani ba. Sai murmushi yake
mun tun daga nesa kamar gonar auduga, daya ga ina shirin wuceshi batare da niyyar tsayawa
ba, sai ya fiddo hannunsa wanda ke cikin aljihun damansa, yana mun kwalele da sarka ta.
Nayi hanzarin kai hannu zuwa inda na ajiyeta, watau cikin ‘bra’ dina, babu ita babu dalilinta,
watau ban san sanda ta fadi ba, ba mamaki sanda dan fashinnan ya wancakalar da ni ne.
Na bude baki ina murmushin jinjinawa kokarinsa, wane ne a wannan zamanin zai tsinci zinare
(White-Gold) yayi tunanin maidawa mai shi? Sai dai-daiku, masu tsananin tsoron Allah.
Na ja burki a gaban sa, na mika hannu da nufin ya bani, sai ya maidata cikin aljihunsa ya ce
"idan kece kika tsinci abun mutum, kamin ki mika masa, ai ya kamata ki tabbatar cewa nasa
ne, ko ba nasa bane?”
Na yi murmushi "idan baka yarda cewa tawa ba ce, meye dalilinka na tsayar dani ka nuna min?”
Yace "from your voice, I guessed you are a girl in tender age, me ya kaiki yin tafiya irin wannan
cikin dare, ba tare da mijinki ko dan uwanki ba?”
Na tsuke fuska, don a fahimtar dana yi, yana son kai tsayuwar tamu da tsawo, nace "baka yi
mun kama da mutanen dake shiga abinda babu ruwansu ba, this is my personal world, don
haka in zaka bani sarkata, ka bani, in ba zaka bani ba, in kara gaba" yace a tausashe "me yayi
zafi, gyara kayanka, ba sauke mu raba bane, ina zaka? Ba zo mu tafi tare bane, don haka
maida wukar, ga sarkar ki” nayi murmushi na karBa nayi gaba ina cewa "ban taBa jin irin
wannan hausar ba. Tsaya a inda kafi wayau, kada ka shiga gonar da ba taka ba, in hausawa
suka ji sai suyi maka dariya, don kuwa ba bahaushe bane, Badamagare ne".
​ Ya sha gabana yace "a kasar nan, ni cikakken baushe ne kuwa, kamin ki samu wanda
zai miki kyakkyawar hausa haka, zaki dade. Don haka inma ki tsaya ki nemi taimakon da kike
nema daga gareni, ko kuwa kiyi gaba ki sha wuya, mutum nawa kika samu da irin tawa hausar
da kike rainawa?" A raina nace "kwarai babu” amma a zahiri sai nace "turanci na zai fidda ni a ko‘ina cikin duniyar
nan".
Dariya yayi, data fiddo jerarrnn fararen hakoransa reras kamar shi ya shiryawa kansa, yace "Mu
ba rainon Ingila ba ne, rainon Farisa ne, don haka dauki turancinki ki jefa a wannan katuwar
jakar taki data kusan janyo miki salalon tsiya, ki koma dashi inda kika fito, ki dauko faransanci,
sannan ne zaki shiga ko'ina a cikin mu. We need no your Engilish…" ban san sanda na
murmusa ba, hakannan naji ina kaunarshi, ban san dalili ba, ban jin zan gaza da sauraron
tattausar hausarshi koda zamu kwana ne a hakan kuwa. Koma wane ne, farat daya naji jini na
ya hadu da nashi. Daga fatar jikinshi, sutturarshi zuwa motar da yake ciki kadai ya isar maka
kimanta daga inda ya fito, bi ma'ana, da gani babu tambaya cewa shi wani ne, ko kuma dan
wani ne a Damagaram. Don haka nayi gaba, domin baya daga cikin ire-iren mutanen da nake
jin zan amincewa cikin garin, nafi son in nemi gidan talakawa 'yan uwana in fara sauka, in ga

kamun ludayin mazauna garin, kafin in nemi dangin Innata.
​ Bai hakura ba dai ya sake shan gabana, ya mairairairce kaman wani kan karamin yaro
yace “in kin amince ‘I would like to be your host’ (zan so zama mai masaukin ki) don na fahimci
ke bakuwa ce, baki kuma san kowa ba".
Na yi hamzarin dubansa saboda mamakin yadda yasan hakan, ya dagan kyakkyawar girarshi
yace "yes, kuma ba kowa ke karBar bakon da bai sani ba a garinnan” . Nace “shine kai zaka yi
kasadar karBar bakuncin nawa, bayan ko fuskana baka sani ba? Idan kuma dodanniya ce fa ko
aljanace?” Ya ce yana mai murmushi "na yarda na amince ta cinye ni har hanji na". ​ Tunda muka soma tafiya a motar babu wanda a kara ce da dan uwansa uffan, sanyin
A/C ne ya kara sani samun nutsuwa da warwarer gajiya, nake jin shirun namu ne bai yi masa
dadi ba, don haka ya mika hannu ya sanya kaset na faifan mawakan 'soulsquad music' sautin
na tashi a hankali har muka iso wata keBantacciyar anguwa da tafi mun kama da iri-iren
gidajennan namu na GRA, domin dukacin ginin gidajen iri daya ne, kansu daya haka tsarin su
ma daya.
Ya karya motar a kofar shiga flat na ashirin da biyu, yayi (horn) mai gadi ya bude muka shiga.
Korran (Grass Carpet) ne malale a gabadayan harabar gidan banda sauran shuke-shuke
kala-kala da suka kawata gidan saosai. ka ramin gida ne hawa daya, da aka yi gininshi da jan
dutse kaman a kasar China. Daga kofar shigowa gidan bazaka taba tsammanin haka cikin
gidan yake ba. Babban abinda yafi burge ni da tsarin wannan gida shine kacokam ginin gidan a
tsakiyar gidan yake, sannan hanyar da zaka bi zuwa cikin gidan duka (grass carpet) ne mai
taushi. Na zauna cikin motar na kasa fitowa cike da tunanin a wane matsayi zanje wajen
matarsa? In kuma babu matar aure a gidan haka zan zauna da gardin namiji, a irin wannan
gidan ihunka banza? Kai da sake, wai an baiwa mai kaza kai.

Mu kammala a littafi na 3.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Duk wasu kalami na kwantar da hankali Ya Faruq ya gaya
min su a wannan rana, tamkar yawun bakinsa ya kafe, tamkar ya fido zuciyarsa ya nuna min,
tamkar harshensa ya tsinke don tabbatar min da abinda yake fadI, jinsa kawai nake, amma
hawayena basu bar kwarara ba, wanda na tabbata har abada ba zasu daina ba, haka zuciyata
ko daya bata russuna ba ga kudirinta akan NURATU da BABA SA'IDU.
In Allah ya yarda sai sun zubar da hawaye, fiye da wanda na zubar. Fiye da wanda Inna ta
kwashe shekaru goma sha takwas tana zubarwa akan su.
​ Tare dashi muka kamo hanyar Gwarzo, cikin masiffafar motar da ya iso da ita daga
asibitin AKTH dake Kano, yana ta kara kwantar min, da hankali, da kalami masu taushi da kara
imani. Akwai inda yace “Zaynab in nine ke, babu abinda zai sa inta zubar da hawaye na har
haka, tunda da Allah yayo fitowana a hakan bai barni haka ba. Sai ya sanya matsananciyar
kaunata zuciyar iyayen nawa, yayi mun gata irin wanda baiyiwa sauran 'ya'ya irina ba.
Kina ina iyayen da suka haifi 'ya'ya kamar ki, suka kai su bola suka zubar, don gudun abin
kunya? Kina ina ake tsinto 'ya'ya irin ki ana kaisu gidan marayu, ana kyamar su ana zuwa kallon
su? Ke kuwa Babanki sonki ya ke fiye da sauran 'ya'yan da ya haifa ta hanyar auren. Son ki
yake fiye da komai na rayuwar duniya, son ki yake ta yadda da da hali, daya mallaka miki duk
abinda ya mallaka a duniya.
So yake ki zo kusa da shi, saBanin 'ya’ya irin ki da ake neman maraba da su. Kina ina uwar da

ta haifi 'ya ta irin hanyar data haifeki, ta kasheta da hannunta, ta tura ta a masai tayi ‘flushing?’
Ke kuwa na tabbata duk inda mahaifiyarki take, cike take da kaunarki da tausayinki, domin
soyayyar gaskiya ce tsakaninta da mahaifinki, illa makiya da sharrin Shaidan, gami da kaddara
da suka tarammusu. Ki godewa Allah, domin yace “in baku godewa Rahmata ba, hakika zaku godewa azabata”. Ki
yafewa iyayenki, ki taya su rokon Allah ya yafe musu, domin babu wanda yake sama da aikata
‘kuskure’ cikin rayuwarsa. Dukkan mu masu saBo ne in one way or the other, amma Ubangijin
mu hakuri yake da mu, yana yi mana afuwa har zuwa ranar da kowanen mu zai karBi
sakamakon sa, sai ki dage wajen kyautata lahirar ki, ki gani idan zaki taBe. Wannnan shi ne
gata na karshe da zakiyiwa rayuwarki, amma ba kuka ba.
Kuka babu abinda zai sa babu abinda zai hana, saidai ya kara dagula zuciya, ya raunana
imaninta. Muminai na hakika basa kuka akan komai, sai akan tsoron Allah, wannan shine lokaci
na karshe da zaki nunawa Innarki kaunar da kike ikirarin kina yi mata, ta hanyar yi mata addu'a
da nema mata gafara. Ina yi mana ta'aziyya Zaynab domin bake kadai aka yiwa mutuwa ba, mu biyu ne Zaynab, nima
nayi rashin uwa abokiyar shawara kuma mai kaunata…….." Yasa hankici ya share hawayen
idanunsa, ya miko mini da hannunsa na dama, ayayin da yayi amfani dana hagun wurin tukin
motar "maza share su Zaynab, Inna bata cancanci mu dinga yi mata kuka ba." ​ Na mika hannu na karBa, amma ban san sanda kukan ya kara subuce min ba jin
kalaman sa. Na kifa kaina a cinyoyina nayi ta yi ba kakkautawa, don ni har yanzu na kasa
amincewa raina wai Innana, ta rasu! To ni in haka ne wa nake da shi a yanzun? Zaman wa
zanyi? Ina zani? Tunda mutumin da na rika a matsayin mahaifina, an ce ba shi ya haife ni ba.
Mutumin da nake kauna fiye da kowa a duniya, nake ganin GIRMANSA da kimarsa fiye data
kowa, a yau bani da wanda na tsana a duniya tamkar shi.
A yau kam na daina ganin beken Innata, dana kwashe shekaru goma sha takwas ina gani.
Baba Sa'idu ya cuce mu, ya ci amanarta. Ya barmu da tabo da bakin cikin da har abada ba zai
gogu daga jikin mu da zuciyar mu ba.
Wai ni Zaynab ce 'yar zina? Gaskiya mana! Biri ya yi kama da mutum!! Yadda na tsinci kaina da
tsananin son aikata zina, tun 'yar ficiciyata ashe ban yar a kas ba, tsotsa nayi a nono, ba don
kariyar Ubangiji da kokarin dan uwana Imran ba. Da ashe bakin cikin yafi haka.. Da tuni nima
na aje shagen…… wayyo Allah! Inama ba'a halicce ni ba…….!!” Magana nake cikin zuciyata, ban sani ba tsabar bakin-ciki ashe a fili nake yi. Ya Faruq ya
kaashe motar a gefen titi, shima ya kifa kai akan sitiyarin ban san a halin da yake ciki ba.
​ Na sani da da hali, da ya jawo ni jikinsa yayi min lallashin da ba'a taBa yi min ba, yayi
min lallashin da wani da namiji bai taBa yiwa diya mace ba, domin nuna mata matsayin da take
dashi a zuciyarsa, da yadda damuwarta ta zamo tashi. Ya kasa ce min komai illa tsinkayar
numfashinsa da nake, wanda ke fita da sauri-da-sauri kamar na mai ciwon asma. He really lack
a word to express his feelings, his sympathy and how much he cares. Gane hakan dana yi ne
ya sani yin karfin zuciyar dagowa in share hawayena, na kuma rasa hanyar da zanbi in ganar
da shi na daina kukan domin idanunsa a rufe suke ruf.
Sai na kai hannu ga ‘horn’ din motar na danna a hankali. Ya bude idanunsa da suka kada suka
yi jawur ya dubeni very pale. Sai na samu kaina cikin wani sabon al'amari, wato abubuwa da
dama dana gano cikin kwayar idon Ya Faruq, su suka tuna mani da Imran.

​ Bai ce komai ba, ya ja motar muka ci gaba da tafiya, gab da sallar magariba muka iso
gida, sai a can bakin hanya ya kashe motar domin gabadayan unguwar babu masaka tsinke,
ana yiwa Malam Ali ta'aziyyar mai dakinsa. Zuciyata ta kara tsinkewa, hawayen suka kara
malalowa. Na tabbatar Inna ta a yau ta wuni a makwancinta. Ni kadai zan kwana a wannan
gadon karfen namu, ni kadai zan rufe da katon bargon mu, ni kadai zan cigaba da rayuwar
hakannan ni kadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login