Showing 24001 words to 24534 words out of 24534 words

Chapter 9 - GIRMA YA FADI 2 Hausa Novels Complete By Takori .pdf

a halin
yanzu da ya wuce Baba Sa'idu?
​ Wani farin ciki ya ziyarci zuciyata, ban san sanda fatar bakina ta suBule da murmushi
ba, naji kamar an dauke min wani nauyayyan dutse ne aka. To amma ina da tabbacin in sun
san ta hanyar da 'yar tasu ta haifeni, zasu yarda su karBeni a matsayin JININ SU har su bari in
zauna a cikin su? Inada tabbacin in sun san cewa ita kanta 'yar tasu, gudu tayi ta barni, tun
ranar data haifeni don tsira da mutuncinta, zasu yarda su karBeni?
Wata zuciyar tace " na Allah basa karewa Zaynab, a ko'ina ba'a rasa na Allah, irinsu Ya Faruq
da Yaya Halima, wadanda tunanin su ya sha banban dana sauran mutane, ra'ayin su ya
banbanta dana sauran al'umma. Su irin wadannan mutanen kamar wasu mala'ikun Rahma ne
da Allah ke saukarwa bayinsa masu matsala irin nawa. ‘They are just like angels in the midst of
people' wadanda suke a shirye da sadaukar da kansu domin farin cikin wani.
​ Wannan ne ya kara sani dubar rubutun da nayi shekara daya da wata daya da ya wuce,
daga bakin Inna ta;
​ "Kyauta mu ba baroroji bane, sune 'yan kasarmu dake daji, mu 'yan kasar Nijar ne, 'yan
usulin wani gari Damagaram, amma iyayen mu da 'yan uwan mu a babban birni Yamai
(Niamey) suke zaune, har yanzu suna can”.

“In kika shiga Niamey, kika ce kina neman wani daya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko
yaro kankani ya san wannan sunan.."
​ Don haka na cusa littafin cikin jakata, na kishingida ina jiran garin Allah ya waye in kama
hanyar kasar Nijar neman dangin Innata, in gaya masu rasuwar ta, in rokesu alfarmar su barni
in zauna tare dasu, ta hanyar cewa ni ‘yar ta ce. Kamin a hankali in nemo Imran, inyi masa aure
da Adda Mami, daga nan nasan ina da Uban da zai rikeni ya kuma cigaba da yi min addu'a ko
bayan raina. Wato in zauna tare da shi da iyalinsa muddin rayuwata.
​ Na dauko wasikar da na rubutawa Ya Faruq, na sake binta a nutse, ko akwai wani gyara
a ciki? Na tabbatar, babu. Ga abinda na rubutawa dan uwana rabin jiki UMAR FARUQ;

"Ya Faruq .
​ Zuciyata ta kasa amincewa da wai in cigaba da zama da Yaya Halima, bayan sanin ko ni
wace ce?
Gangar jikina ta kasa amincewa da kai wai a matsayin miji, domin tana ganin baka cancanci
hada jiki da kazamtacciya kamata ba;
You are pure as a clean glass, and I'm a green, but rotten leaf. Har ila yau, zuciyar ta takasa
yafewa Nuratu da V.C Sa'idu, don ni ba zan taBa kuma kiran sa ‘Baba’ ba, ba zan taBa iya
kiranta ‘Inna’ ba. Don haka na tafi, inda a hankali nake tunanin zan samu labarinta.
In tambayeta dalilin shegantani da tayi, ta kuma nemo min dan uwana a duk inda yake cikin
duniya a dalilin bakin cikinta. ‘I know it will hurt, but you donno how deeply it hurts the victim’.
Faruq ka yafe mani, ka yi mun godiya ga Innarmu, ina nufin (Inna Dubu).
​ Ina fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa".

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login