Showing 30001 words to 33000 words out of 65935 words
Chapter 11 - Auren Huce Haushi Book 2 by Maman fatima.pdf
lalubo shi Dan wallahi bazanga bakin cikin da
ze hanani barci ba.
Duk iya kokarin sahura na taga magaji abun ya gagara wayar zilan ma an rufe ta, ko Kuma
network yaki bada hadin Kai.
Wata dabara ta fadowa sahura, da sauri ta nufi gurin Bala driver tana fatan samun mafita a
gurinsa saboda Bata fatan ta rasa abinda Mama ta kwadaita Mata zata Bata.
Yana aikin goge mota da alama fita zasuyi da Abba, sallama tayi Masa suka gaisa sannna tace
Masa.
"Dan Allah malam Bala ko zaka taimaka ka kwatanta min gidan da yarinyar Nan zahra suka
koma naji ance sun tashi daga Nan hayin banki,Kuma na nemi duka lambobinsu ban samu ba".
Ta fada tana fatan samun abinda take so.
Tunda ta fara Kora bayani malam Bala ya dakata da aikin da yakeyi Yana kallon ta Saida ta Kai
aya sannan yace Mata.
"Haba sahura yaushe Zan dunga bin diddigin yarinyar da take gidan mijinta, ai wannan rashin
lissafi nema ma wallahi ai da kunya ki fito neman gidan Zahra a Nan gurin mu alhalin ga uwarta
can a cikin gida, to ke me zakiyi a can Wanda Baki son uwarta ta sani".
Cikin rashin yarda da Kai ta Fara fadin.
" A'a wallahi kasan wani abun alherin idan mutum zeyi baya son a gani sai dai shi yaron ya
fadawa uwar tasa daga baya".
"To shiga ciki ki nemi bayani dole"
Ya juya yaci gaba da aikinsa ya bawa banza ajiyar ta, it's Kuma ta koma ciki da ledarta a hannu,
mita yake shi kadai.
"Haba mutane sai halin tsiya, Nan gaba kadan wallahi wannan mijin nata ze shayar da mutane
mamaki Dan naji Alhaji Yana wani furuci jiya bansan dai dawa yake waya ba Amma Ina ganin
da bincken da yake yi akan yaron Nan Kuma jiya Wanda ya saka shi ya dawo Masa da amsa".
Shi kadai yaci Baga da Yan maganganunsa.
Duk iya dabara Mama tayi Amma babu wani cigaba dole ta nufi bangaren Ammah.
Cikin iya makirci Mama tayi knocking a kofar falon Ammah.
Autane ya taso ya bude mata kofar, parlourn yasha gyara sosai sai kamshi ke tashi da sallama
ta shiga, duk sai ta Raina nata dakin Dan babu karya ko yanayin gyaran da banbanci.
"Mama Ina yini".
ba zato Mama taji muryar magaji yana gaisheta daga bayanta.
Da sauri ta juya tana fadin.
" A'a Magaji! Daman kana gidan Nan tun dazu nake nemanka na rasa, Dan Allah tashi ka
taimaka ka raka sahura gidan Zahra akwai wasu Kaya Dana saka a kawo Mata Amma shiru
basuzo ba sai yau da safe shine nake son a Kai Mata su banso ko Ammah ma ta sani ba, sai
dai zahrar ta Bata labari, to anje ance Wai basa gidan". Zama magajin ya gyara, Yana kallon Mama Ido cikin Ido.
"Wai Mama kina maganar zahra ne?".
"A'a to da maganar wa nake maka".
"To ai Bata garin nan tun jiya suka wuce Kano, kinsa mijin nata baya kasar suna tare da Baba
malam a India, to yafi son ta zauna a ca gaskiya, kin San manya Basu fiye son zaman gefe ba
gara gurin da yake da kyakykyawan tsaro"
Rasa abin fada tayi, ta rasa zancen wa zata Kama na magaji Kona zilai data ce Bata San
unguwar da suke ba, kenan ba'a garin Nan ba kenan take nufi,ai da mamaki Daman Ace Wai
zilai Bata San sunan unguwa a garin Nan ba, to Wai waye ma babban da taji magaji ya fada shi
yaron ko Kuma waye?. Tunda magaji ya Gama fada Mata abinda zahra ta fada masa ya koma yayi kwanciyarsa, yaci
gaba da latsa wayarsa.
Fita tayi daga parlourn ta koma nata part din duk dabara takwance mata Kuma Bata taba zaton
wankin hula ze kaita dare ba sai yanzu, tana fita Ammah na shigowa.
Magaji Ammah ta kalla tana fadin.
"Waye ya fita yanzu?"
Tashi zaune sosai magaji yayi haka Musaddiq ma matsowa yayi tana fadin.
"Ammah Wai Ya magaji yaje ya raka sahura gidan Adda Zahra".
Gyara Zama magaji yayi sosai Yana fuskantar Ammah.
Kinsan wani Abu Ammah Anya zahra Bata San wani abu ba game da maganar zuwan da
sahura ba zatayi ba? saboda ina zaune Zahra ta kirani ta kada min warning akan kada na
kuskura na kawo sahura inda take, tace min na fada mata Bata Nan sun koma Kano, to yanzu
magamar ce ta kawo ta wai na dauki sahura na kaita gidan zahra zata kai Mata sako shine
nace Mata ai sun koma Kano".
Jinjina Kai kawai Ammah tayi tace.
"Allah ya kyautata".
A binda ta iya fada Kenan tayi gaba abin ta, ita lamarin Mama har ya daina ma Bata mamaki
tausayi take Bata hassada ai mugun ciwo ce.
*
Sai kusan Sha biyu na agogn kasar India Habib ya tashi, yayi mamakin yanda lokaci yayi gudu
haka, da sauri ya nufi toilet Yana yiwa Kansa fadan me kenan yayi shida ya biyo marar lafiya
Amma ya bige da dogon barci irin haka, "ko Yaya Baba malam din yake?" Ya yiwa Kansa da
Kansa tambaya.
A gaggauce yayi wanka ya fito, Bai wani Bata lokaci ba ya shirya ya fito yana ayyana Allah yasa
Mahmud ya dawo Dan jiya sun Dade suna dakon zuwansa Amma shiru dole suka hakura suka
kwanta.
A parlour ya iske mahmud Yana ta faman aiki a cikin computer desktop wadda take girke a
parlourn, daga gefe Kuma wasu indiyawa ne su biyu Yana musu magana da harahen indianci
suna amsa masa, da alama Kamar Umarnin wani Abu yake basu, har Inda yake zaune Habib
ya Karasa yayi Masa sallama ga mamakinsa sai yaji gaba Daya sun amsa masa, Shima
Mahmud barin abinda yake yayi ya juyo Yana sakin murmushi ya mikawa mahmud hannu
sukayi musabaha, sannan ya mikawa bakin mahmud suka gaisa, ganin Kamar Habib na
dari-dari dashi dan Yana kula da yanda yake tsare shi da ido, sai idan yaga zasu hada Ido yayi
saurin janye nashi, tashi muhmud yayi daga Kan computer ya riko hannun Habib Suma sauran
biyun suka rufo musu baya.
"Bakon india, nasan ka gajine shi yasa na Hana Abubakar tashinka nace ya barka kayi barcin
gajiya tunda ka gaji da yawa".
Ya fada suna Zama a kujera two seater,
"Bari kawai ni kaina nayi mamakin barcin da nayi, Ina Abubakar ne?".
"Sun fita da Mr Ajey kasuwa, inaga sun kusa dawowa ma yanzu, ga abinci nan kaci idan ka
gama zaku fita dasu Mr Salman zasu rakaka kuje a Sami kayan sakawa tun dazu suke jiran ka
fito ku tafi baka tashi ba, ga abincin can ka duba Wanda zaka iyaci sai ku wuce, nima Zan shiga
naga doctors din dake kula da Baba malam yanzu suka nemi ganina tunda tun jiya suka shiga
dashi dakin bincike na musamman sai gobe za'a fito dashi, kasan tsare-tsaren Asibitocin su da
banbanci da namu na Nigeria"..
ATM mahmud ya mikowa Habib na bankiya juya Kuma yayiwa su Mr Salman maganar da Habib
besan me aka fada ba, ya wuce ciki Yana fadin.
"Kada ka dauko kaya kadan Dan bamu San how long samu zauna a Nan ba sai yanda Hali
yayi".
Shi dai Habib kasa cewa komai yayi Dan ya gama Shan ruwan mamaki ba kadan ba, Mahmud
din da suke kwana su tashi tare ne wannan? ko a mafarki be taba kawo haka ba".
Cikin abinda be wuce minti latatin ba Mahmud ya fito cikin kananun Kaya yayi fresh dashi ya
fice daga gidan, har lokacin su Abubakar Basu dawo ba, da kanshi yake driving din, da Dan
hanzari yake tafiya saboda gaba Daya hankalinsa yayi Asibiti.
Lokacin Daya shiga direct office din consultant din ya nufa, be same shi a office ba Yana cikin
ward inda yake duba patient dinsa, baifi zaman minti goma ba doctor din ya dawo da zugar
wasu dalibai a bayansa Yana ganin mahmud ya gane shi, tunda yaji yana Jin yaransu yake Nan
Nan dashi. A cikin office din wasu hotuna ya dauko ya aje a Kan table dinsa yace mahmud da sauran
daliban su matso.Dalla Dalla ya shiga Yi musu bayanin yanda ciwon yake da yanda yake yiwa
mutum illah idan har ba'a Farga an kawo mutum Inda za'ayi Masa aikin gaggawa ba saboda
yanda spinal cord din ta matse to komai ze iya faruwa za'a iya rasa kafa da amfanin kasan Jiki
na har abada, Dan haka daga Nan zuwa Kwana uku za'ayi wannan aikin, Amma dole charges
zasu karu tunda sun Kara gani karaya a kashin hakarkarinsa na hagu guda biyu sai kashin
mukamikinsa Daya goce".
Take a Nan mahmud ya nemi a bashi bill na Karin charges din da aka samu, yaje ya biya komai
ba damar ganin Baba malam haka dokar take,yana tafiya a Kan barandar Asibitin Yana sauri ya
Karasa gurin Daya aje mota yaji daga bayansa ance.
"Waye nake gani Kamar Mahmud Dange".
Da sauri ya juya Yana mamakin waye wannan yayi Masa farin sani haka.
Faisal ya gani kanin Aunty Surayya matar uncle Mustaphan zasuyi sa'anni da mahmud din,
cikin fara'a Mahmud ya Fara fadin.
"Faisal bungudu Long time, Daman talaka Yana ganinku?".
"Kaji ka da wani magana Kai ganin ku ai sai Mai sa'ar gaske, Nigeria kun Mata tawaye ma
kwata-kwata yaushe ake ganinku, meya kawo ka Nan ne haka ko patient gareka".
"Eh wallahi wani Babana ne ya samu spinal cord injury muka kawo shi Nan, Kai Kuma meya
kawoka?"
"Wallahi Alhajin mu ne ya samu accident tun kusan wata hudu da suka wuce, karaya ya samu a
cinya, anyi gyara har sau uku abun yaki shine, wani doctor da muke gani a wani private
orthopedic hospital a Sokoto yayi Mana hanya mukazo nan, kaga jiya uncle Mustapha ya bar
Nan kasar tunda shine ya kawo mu sai da ya Gama Mana koma".
Jinjina Kai Mahmud yake kafin yace.
"Allah ya bashi lafiya, ga jikin girma ga lalura muje na ganshi na duba shi".
Tare suka juya Faisal din Yana fadin.
"Wallahi Rabon mu hadu ne nace Bari na koma masaukina nayi wanka na huta tunda ba wata
damuwa a tare dashi sunce sai Nan da sati uku zasuyi Masa aiki sai sunyi treating din gurin da
infection ya Kama sannan zasu sake Masa aiki"
"Allah yasa ayi aikin cikin sa'a yasa da nasara yasa a dace.
"Allahumma Amin" Faisal ya fada.
Lokacin da suka shiga Alhajin Yana zaune a gadonsa Yana lazimi da casbaha dinsa.
Ganin Faisal ya dawo da wani yasa ya maida hanklinsa a Kansu, har suka karaso yana
kallonsu.
Sallama Mahmud yayi masa ya amsa sannan Mahmud din ya gaishe shi da jiki.
Faisal ne ya yiwa mahaifansa bayanin Mahmud, cikin nuna Jin Dadi mahaifan na Faisal ya
shiga jorowa mahmud godiyar abinda akayi masa, Basu jima ba Mahmud ya aje Masa Dala
dubu yayi masa sallama, Mahmud yasha shi Albarka Kamar ze Bari Baki gurin godiya.
Shima Faisal godiyar ya dunga jerawa Mahmud Kamar me, shiya dauki Faisal ya Kai shi har
masaukinsu sannan Shima ya hada shi da dala dari biyar yayi gaba, wani irin shauki ke dibarsa
akan yaje gidanta tunda gari ya waye yaji ba abinda yakeso irin yaje ya ganta ita da yaran,
amma wata zuciyar na fada Masa kada kaje akwai k'ura Kuma wannan match din bazaka iya
playing dinsa yanzu ba, kwabarka ce zatayi ruwa, dole ya karkata Kan motar ya dauke daga
direction din da ze Kai shi gidanta, Amma fa dole yaje gareta duk rintsi Dan yanzu ma yasan
Yana zuwa wani labarin za'ayi ba wannan ba Dan dole ballin ya tashi.
__
Har dare Zahra Bata Jin dadin jikinta Sam da mahmud ma ya Kira Basu Dade ba yace Yana da
wani uzurin da zeyi sukayi sallama.
Wurin karfe biyu da rabi ta farka sai taji Kamar an Zuba Mata ruwa, da sauri ta yunkura ta tashi
zaune abunda ta gani ya sakata tashin hankali ta sauko a zabure tana sallallami jikinta sai rawa
yakeyi, period ne yazo abinda Bata taba yiba kenan ai sai kowa yasan da zuwansa Amma
wannan sai ganin Abu tayi da wata irin Zuba ta tashin hankali. "Na shiga Tara mezan gani haka?".
Toilet ta nufa tana cikin rudu ba kadan ba data shiga ta cire nighty din ta sakarwa kanta Ruwa ta
wanka Yana bin kafarta Zuba yake sosai har da guda guda, ganin abin bana hankali bane yasa
ta fashe da kuka, da kyar ta samu ya Dan tsagaita da Zuba ta hada pad biyu ta saka ta fito ta
kunna wutar dakin yanda taga Kan bed din sai hankalinta ya Kara tashi cire bedsheet din tayi
tana share hawaye.
Cikin washing machine ta saka bedsheet din ta fito da towel a bucket da detergent ta Fara aikin
gurin tana cikin aikin tayi wata irin Zuba wadda har Saida ya biyo kafarta saboda yawa hannu ta
Dora a ka ta fasa kuka tana fadin.
"Na shigesu shikenan mutuwa zanyi".
Wayarta da dauko ta lalubo number Muhmud ta Kira ba tayi tunanin ko karfe nawa bane a can.
Yana zaune yana aiki a laptop dinsa yaji Kiran ta ya shigo agogon dake parlourn ya duba yasan
yanzu a Nigeria tsakar dare ne to lafiya yasan ba gwanar chart din dare bace bare yayi tunanin
kiransa tayi suyi Hira.
Yana dauka yaji shashshekar kukanta.
Cikin kidima ya tambayeta.
"Menene? Meya faru? Keda waye a dakin?" Kiyi min magana Mana ".
Duk ya jero Mata wadannan tambayoyin, Bata bashi amsa ba sai faman fadin ta shigesu take.
"Wai precious so kike Nima na fasa kukan ne? na tambaye ki kinyi min banza kina ta kuka, ko
wani ne ya mutu aka fada Miki kike wannan kukan ko wani Abu yake damunki ne?"
Ya fada Yana kwantar da murya Dan so yake tadan samu nutsuwar da zatayi masa bayanin
damuwar data saka tayi masa Kiran tsakar dare.
"Pls precious tall me menene Mana?".
Cikin karaya da sallamawa ta bude bakinta da kyar tana shashsheka.
"Wallahi me Amor jinane ze Kare bleeding nake kagan shi Nan sai Zuba yake duk na Bata
bedroom din Nan Ni dai ka yafe min nasan mutuwa zanyi ta fada wani kukan Yana kwace mata.
Jin abinda take fada ya daga Masa hankali sosai, saima ya rasa Yaya zeyi Mata wani tunani
yayi, saiya aro jarunta ya yafa yace mata.
" Pls haba my angel ki nutsu babu abinda ze sameki kinji maza kirawo Matar nan tazo ki hadani
da ita.
Kai kawai ta gyada Kamar Yana kallonta, Kiran number Aunty zilan tayi, tana cikin barci taji Kira
figigit ta tashi ta dauka sunan Zahra ta gani da sauri ta dauka cikin kuka Zahra tace Mata.
"Kizo Aunty zilai zan mutu".
"Innailaihi wa innailaihi raji'un! Na zilai na shiga uku meya sameki?".
Shiru tayi mata, da gudu-gudu zilan ta karasa bedroom din Zahra abinda ta gani ya daga Mata
hankali.
"Na shiga uku Ni zalaihatu meya sameki wannan ai Bari ne, tun yaushe Kika Fara zubar da jinin
nan? Bari na fadawa Mai gadi ya kaimu Asibiti wannan ai ba abun Wasa bane, Kiran Mahmud
ne ya shigo Aunty zilai ta mikawa wayar.
Jin muryar Mahmud yasa Aunty zilai Kara risunawa tamkar yana gabanta, magana ya Fara Dan
ko gaisuwar da take masa Sam beji ba.
"Dan Allah ki taimaka Mata ta gyara jikinta ga zayyan can Yana jiranku zaku wuca Asibiti.
A&E sukaje anyi Mata tambayi daga karshe sukace sai nayi scanning da safe zasu tantance
Dan Zahra ta kafe ita ba miscarriage tayi ba su Kuma sunce babu abinda ze kawo Mata irin
wannan heavy bleeding din Sai shi, suna Asibitin mahmud ya sake Kiran zayyan ya tambaye
shi me sukace ya sameta. Yace Masa ance miscarriage tayi Amma da safe zasuyi hoto su duba.
Jim Mahmud yayi Yana tunanin meya hada zahra da barin ciki Kuma? Sai dai wani abun na
daban gaskiya.
Sunyi mata duk abinda ya kamata Kuma Alhamdulillahi zubar tayi sauki, wurin karfe hudu da
rabi suka dawo gida sai da safe zasu koma za'a Mata scanning a ga menene mu"assasa na
kawo zubar jini kuma ayi Mata pcv.
Bayan daqowarsu mahmud ya kirata yafi sau biyar Yana tambayarta ya jikin? Ba wata matsala?
Meke mata ciwo?.
Haka yayi tayi ita har Saida ya koma Bata tausayi ma ya fita shiga damuwa ita keda Matsalar
Amma ya fita shiga tashin hankali nesa ba kusa ba, ya fada Mata yayi Dana sanin tahowa ya
barta,Amma dole yasan abinyi tunda akwai matsala.
[2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318: *AUREN HUCE HAUSHI*
08055362975
Or
09061432330
My WhatsApp number.
AISHAT ISAH MUSA (Aunty Uwani)
Naman Fateemah.
Page 64.
.............Sun koma asibitin sunga consultant g
Gynecology doctor sabuwar ce tazo daga federal medical center Birnin kudu, Dr Hajara yqrinya
ce karama Amma tasan aikinta, so sai ta duba zahra ta turata ayi Mata special scanning saboda
taga history na ciwonta a cikin file dinta.
Basu Dade a gurin scanning din ba suka dawo, tunda doctor din ta bude take jinjina Kai abun
yayi matukar Bata mamaki, Saida ta aje result na scanning din sannan ta cire eye glasses din
idonta.
"Dan Allah sister me ki kayi amfani dashi akan matsalarki ta fibroid? Ma'ana kin Sha wani
magani na hausa Kona Islamic chemist haka akan matsalarki?".
Kai zahra ta gyada mata alamar eh.
"Pls my friend talk to me".
Ta fada tana murmushi.
"Eh nayi amfani da wani magani Amma Ina ganin black pepper ne kawai da kakata ta bani tace
na ringa Sha da ruwan zafi Amma sai yayi twenty minutes Zan tace na Sha safe da yamma tace
ze narke basai an yanka an cire ba, tace ma Yana maganin haihuwa Wanda baya haihuwa idan
Yana amfani dashi eggs dinsa zeyi producing a samu haihuwa, tace min Yana magani sosai a
bangaren ciwuwwukan Mata da suka shafi mahaifa,