Showing 3001 words to 6000 words out of 65935 words
Chapter 2 - Auren Huce Haushi Book 2 by Maman fatima.pdf
daga can Azaren ne ko
Kuma kinzo nan garin ne?"
Shiru zahrar tayi kafin tace "ganin likita nazo akan wannan ciwon marar da bakeyi duk wata".
"Ikon Allah kuma ke kadai Kika taho ganin likitan kamar marar gata".
"A'a bani kadai nazo ba tare da Aunty Zilai Mai aikin Ammah mukazo tana can a Nasarawa
G.R.A".
"Ok, to mryasa baku taho tare ba Nan din".
Shiru tayi Bata ce komai ba, ganin da Yara yasa itama ummar tabar zancen.
Kafin kowa ya tashi Zahra ta tashi tana fadin "Umma Bari naje ba kwanta barci nakeji"
"To Allah ya tashemu lafiya.
Basu Dade ba Suma suka shige daki Daman duk sun gaji.
Lokacin da Ammah ta shiga dakin Abban samun Mama tayi kane -kane tana ta zuba zance da
kudi a hannunta masu Dan yawa da gani a gurin Abban ta Karba, cikin alamun rashin gaskiya
mamar ta Fara fadin. "Aina leka parlourn ki naji Shiru nayi zaton kina Nan wallahi Ashe Baki
shigo ba" Fuska ba annuri Ammah tace. "Eh ban shigo ba idan kin gama na dawo ta juya har Takai kofar
ficewa Abban yayi gyaran murya Yana fadin "dawo ki zauna Ina Kuma Zaki ita ta tashi ta tafi
tunda ta gama abinda ya kawo ta"
Jiki ba kwari Mama ta tashi tana fadin "ai Kam na Gama Allah ya tashemu lafiya nagode Allah
ya Kara arziki".
Ta nufi inda Ammah ke tsaye tana fadin "mu kwana lafiya ki tayani yiwa Abban yara godiyar
abin arzikin Daya bawa Najjahi na kudin registration".
"Masha Allah! An gode Allah ya bada sa'a".
Ta fada fuskar ta Babu walwala ko alama, da gaske ta kule Abun Yana so ya Zama rainin
hankali tayi noticing dinta duk ranar girkinta sai ta dunga Karakaina a part din Abban Amma
idan tasan wata ai Bata San wata ba.
Dawowa tayi ta zauna kusa dashi "meya Bata Miki Rai ne Kika juya Zaki bar dakin?"
"Ba komai".
Ta Bashi amsar in short.
Haka Nan yabar zancen badan ya gamsu da abinda ya fada ba.
"Neman izinika na shigo zanje Kano gobe in Sha Allah"..
Saida ya Kare Mata kallo tsab sannan yace. "me akeyi a kanon da zakije?"
Kai ta girgiza ba komai zanje barka ne na yaron nan Sameer ranar da yazo daukar su Zahra
yake fadawa magaji anyi Masa haihuwa an samu takwaran mijin Zahra".
"Kai Masha Allah, ai ban sani ba da nayi Masa barka ranar da yazo".
Tashi tayi zata fice Abban ya mayar da ita "Wai me yake faruwa ne Naga ranki a bace tun
shigowar ki".
"Ba komai zanje na dawo ne yanzu in Sha Allah".
Ta Mike ta nufi kifar ficewa, haka Nan yayi Shiru badan ya yarda da ba yasan da abinda yake
damunta taqi fada Masa ne kawai".
Ammah na shiga part dinta ta Kirawo Abdul Hakeem, lokacin Yana kofar masallaci tare da
Habib.
A parlour ya samu Ammar ta zuba tagumi.
Saida yayi sallama biyu sannan taji.
"Wa'alaika Salam".
Ta fada tana kallon Abdul Hakeem din, kusa da ita ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah Ina
sallama bakya jina?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin "yanzu ba dadewa Umman Sajida ta kirani waiga zahra taje
Mata zata kwana a can Kuma ita kadai ba tare da zilai ba, na Kira zilan tace min tun fitar safe
Basu dawo ba har dazun, ka Kira Sameer kaji shin yasan da tafiyar ko Kuma wani Abu ya faru
tayi musu yqji nasan halin kayana zatayi abinda yafi haka ma in dai zahra ce, Dan haka ka
kwana da Shirin Kano sakko zamuyi ko Abban KU ban fada Masa wannan maganar ba ina
tsoron ta fito duk da nasan ba lallai ta fito din ba amma sha'anin mace da miji sai Allah"
"Allah ya rufa asiri".
Abdul Hakeem ya fada Yana Kiran Sameer duk da lokacin ya ja Sha Daya ta gota.
Ringing Daya saneer ya daga kafin Abdul Hakeem ya Fara magana Sameer ya rigashi Dan ko
sallama Babu ya Fara fadin "Abdul Hakeem zahrar tazo Nan ne?.
"Easy my man! Tana Nan Kanon a Janbulu gidansu Sajida, yanzu Umman su sajidar ta Kira
Ammah ta fada Mata saboda hankalin ta be kwanta da ganin zahrar ba duka yaushe akayi Abu
da zata wani zo yawon ziyara tasan da wata a kasa, shine ta Kira zilai ta fada Mata tun fitar safe
baku dawo ba". Ajiyar zuciya ya sauke, sai Yanzu ya samu nutsuwa dan Yanzu suka gama wayar da mommy
akan ko akwai wani cigaba? Yace Mata Babu Kuma tun lokacin da abun ya faru yake ta kokarin
ya Sami Mahmud Abun ya faskara.
"Na gode kwarai Abdul wallahi muna nan hankalin mu a tashe tun bayan Azzahar muke Abu
Daya, Dan Allah kayi min godiya gurin Ammah, kace Kuma tayi hakuri ba sai tazo ba Dan Allah
ga mommy ta Isa tayi komai ka fada Mata laifi akayi mata amma in Sha Allah hakan baze Kara
faruwa ba wannan ma tsautsayi ne". Kai kawai Ammar ta gyadawa Abdul Hakeem ya gane me take nufi tunda handsfree ya saka
wayar".
"To ba damuwa tace ayi maka godiya da kwaramniya"
"Ba komai yiwa Kaine ka turo min da address din gidan Yanzu na gode".
Sukayi sallama ta kashe Kiran Yana Maida hankalinsa a Kan Ammah.
"Ammah lokaci yayi daya kamata a zauna da Mahmud asan who's he? Aure ba Abun Wasa
bane asan asalinsa Kinga muna tare sosai wallahi be taba fada min asalinsa ba kawai dai
nasan he's educated fiye da tunanin mu badai ya nunwa ne kawai anyway kome Kenan dai kiyi
abinda ya kamata kawai".
*** **** ***
Suna Gama waya Sameer ya lalubo Number Rukayya tana dauka yace ki fadawa mommy gani
Nan zamuje mu taho da Zahra tana janbulo gidansu friend dinta".
Bai jira tayi abinda zata fada ba ya katse Kiran ya saka jallabiya ya dauki key din motar yayi
waje.
A kofar parlour ya tarar da Rukayya da Mommy.
Fitowa yayi yana fadawa mommy Yanda sukayi da Abdul Hakeem da Ammah.
"Dan Allah ki zauna mommy muje da ya Sameer kawai ana ganin mu dake za'a San ba lafiya
ba Kinga ai itama zato takeyi kawai muce Mata ya Mahmud ne ya dawo yace muzo mu taho da
ita tinda da saura lokaci".
"To shigo mu tafi tsari mistress".
Saida suka dauki titin rijiyar zakin sannan Sameer ya mikawa Rukayya wayar da address din da
aka turo Yana fadin " duba ki gani ko kinsan laying kune masu yawo lungu da sako na garin
nan".
Dubawa tayi tana fadin " Nasan gurin layin gidan su saliha sani Musa ne tare mukayi Excel da
ita".
Cikin ikon Allah suna tsayawa a kofar gate din motar ya Abba ta shigo shida Abie dinsu sun
dawo daga kwangwalam bodar NIGER inda sukaje gaisuwar mahaifar amininsa data rasu jiya,
sun biya ta kazaure gurin wani abokin aikinsa daya kwanta a Asibiti Shima a Nan sukayi dare.
Ganin mota a kofar gidan yasa Abie yace Abba ya tsaya yaje yaji ko lafiya Yana fita Mai gadi
ma ya fito Yana ganin Abba ya karasa gurin da sauri, fitowa Sameer yayi ya tarbesu Yana Mika
musu hannu sukayi musabaha Yana fadin "Ayi hakuri munzo cikin dare ba sanarwa,Daman
munzo mu tafi da zahra ne tun Rana tazo Bata Fadi zata kwana ba sai Yanzu mijinta ya dawo
gashi ba waya a hannunta, ganin da sauran daren yasa muka biyo samunta".
,"Ok. Ba damuwa muma Yanzu shigowar kenan munje unguwa tare muke da Abie".
"To mu karasa Mana na gaishe shi ya juya yabi bayansu suka nufi gurin Abie din, Rukayya gani
tayi kamar akwai rashin kyautawa ace tana kallo aje a gaishe da babban mutum tana zaune sai
kawai ta fito ta rufa musu baya.
Cikin girmamawa Sameer ya gaishe da Abie din sai Jin muryar Rukayya sukayi daga baya tana
gaishe da Abie din, hankalin Ya Abba biyu ya kasu ga wata murya data fizgeshi lokaci Daya ga
Kuma bayanin da yake yiwa Abie.
""Ba wani Abu Bari a Kirawo Umman tasu saita fada Mata ta fito wannan ai shashanci ne ya
za'a bar yarinya ta nemi gurin kwana da mijinta da komai".
Sameer ne ya Dan shafa Kai.
"Ayi hakuri Abie mijin ne baya Nan sai yanzu ba dadewa ya shigo kasar".
Mazaunin direba Abban ya koma suka nufi ciki tunda Daman Mai gadi ya bude gate Yana jiran
su shigo.
A waya Abie ya Kira Umma har lokacin idanunta biyu da wuya tayi barci matukar tasan mijinta
baya Nan da sauri ta dauki wayar tana Masa sannu da zuwa.
"Yauwa ya amsa a takaice Yana fadin. "ki taso bakuwar da kikayi a gidan mijinta ya dawo gasu
Nan a gate". Ya kashe Yana nufar part dinsa.
Shiru tayi waye ya fada masa da bakuwar a gidan jiki ba kwari ta nufi dakin sajida, barci ta
Samu tanayi sadidan kamar Nan duniya Bata da damuwa Kota sisi dakin ta shigo tazo bakin
gadon ta tsaya tana Kiran sunan ta a hankali, tana fadin "tashi ki kimtsa ki fito ga Mai gidanki
can zaku tafi gida". Idanun tadan zaro tana fadin "wallahi bazani ba Umma kice musu bana nan
sai hawaye"..
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 43.
_______ kuka zahra keyi ba kakkautawa a hankali Umman ta zauna kusa da ita, ki daina
kukan Nan kiyi hakuri ki tashi ku tafi, kiyi ta addu'a Allah ya kawo Miki saukin ko menene
damuwar, kada ki Kara tunanin yin irin haka idan Abu ya dameki ki tafi kibar gida ba shine
maslaha ba kinji, tashi ki cire Rigar barcin ki canza suna jiranki Kinga dare ya farayi inaga tun
Rana suke bulayin nemanki sai Yanzu suka samu inda kike".
Kai ta gyada tana goge hawayenta, Bata taba tunanin yau zata koma gidan Nan ba Dan ita a
budget dinta daga Nan gaba zatayi Dan kasar tayi niyyar tsallakewa tayi gaba abunta tunda
passport dinta yana jaka, to Wai ta Yaya suka gano tana gidan Nan Wama yasan gidan a
cikinsu, to shi yaushe ya dawo? Haka zuciyarta ta dunga sake-sake.
Fita Umma tayi ta Bata guri ta canza Kayan, jiki a mace ta fito ta iske Umma da Ya Abba a
parlourn, gaishe da Ya Abban tayi ya amsa Yana fadin "wallahi kin wahalar da mutane da
wannan Daren Kika sakasu fitowa har da mace Ina jinma mijinta ne"
.ita dai zahra Shiru tayi Masa ta nufi Hanyar fita daga parlourn tana fadin "ummah na tafi Saida
safe".
Ta fada tana yin gaba "to Allah ya tashemu lafiya kiyi hakuri da safe idan Allah ya kaimu ki bude
wayar zamuyi magana".
"To Ummah in Sha Allah Zan bude". Suka fice daga Fallon. Ya Abban Yana biye da ita tun kafin
ta karaso Rukayya ta taho cikin sassarfa ta ringume Zahra tana fadin "wallahi kin dauki alhakina
da Hajiyar makwarari Kinga kukan da muka Sha yau? Tambayi Ya Sameer kiji duk kin tashi
hankalin mu". Wani sanyi ya ratsa Ya Abban Jin Rukayya ta ambaci Sameer da yayanta, daman Kuma yaga
Kama ta zahiri duk da dare ne Bai Hana shi ganin kamannin nasu ba.
Shiru zahrar tayi Mata ita sai Yanzu taji wata kunya duk ta rufeta, me kenan tayi? Shike Nan
zasu dauka fa tayi yaji ne dole ta magantu.
"Wai Dan Allah Aunty Rukayya ku kasa barina nayi kwana ko Daya ne a gurin Ummata nifa
bada wata manufa ba na taho kawai dai nasan idan nace zanzo ba Bari Oga sameer zeyi ba
zece saina nemi izinin....."
Sai tayi Shiru.
"Izinin wa za'ace ki nema?".
Gaba tayi kawai ta nufi gurin da Sameer yake tsaye jikin kofar driver, da wannan damar Ya
Abba yayi amfani ya matso kusa da Rukayya yana fadin "Ashe Aunty tasha kuka zanso Naga
kina matse hawaye".
Kallonsa tayi haka nan taji yayi Mata kwarjini.
'yar dariya tayi tana fadin "Ina yini?"
"Lafiya kalau beauty, ki saka min number ki Zan kira naji ya kukaje gida tunda sister Zahra har
wayar tayiwa tawaye".
Ya karasa Yana murmushi itama murmusawar tayi tana karbar wayar, number ta saka Masa ta
Mika Masa wayar tana fadin "bari na wuce ya Sameer Yana jirana"
Tayi gaba.
"Ok saina kira shima gurin Sameer din ya nufa sukayi sallama, ya leka ta window Yana yiwa
Zahra magana.
Tunda suka dauki hanya ba Wanda ya Kara magana sai ajiyar zuciyar Zahra ke sauka kadan-
kadan.
A hankali zahra ta bude Baki tace "Dan Allah oga sameer kayi hakuri na Bata maka Rai bada
niyya nayi ba kawai dai Ina son Naga Ummah ne Naga kuma kamar bazaka yarda naje na
kwana ba".
"Ba komai kawai, Daman Yanda su mommy suka tada hankalin su ne ya daga min hankali
nasan ba Bata zakiyi ba tunda da kafarki Kika fice".
Shiru tayi tasan magana ce ya fada Mata a kaikaice, tasan a kule yake da ita kawai dai Batasan
dalilin Daya hana yayi Mata buyaji ba, Dan taga alama ya iya tijara Yanda ya karewa Rukayya
dazu ko shi yasa taja bakinta tayi shiru Yanzu.
Sha biyu da minti goma yayiwa Mai gadin gidan horn Saida ya leko shima Sameer din ya fito
Yana ko waye sannan ya bude.
Yana shiga da motar Maimakon yaje kofar main parlourn sai taga yabi ta baya ya nufi wani gani
Mai azabar kyau ko Ina tar kamar dauko ginin akayi aka aje ga wata 'yar baranda data hade
ginin biyu an saka glass anyi kamar katanga da wasu irin flowers masu kyau a jere ana ganinsu
gurin yayi matukar kyau da burgewa a kusa da steps din da ze sadaka da Main parlour, Zahra ba tayi kokarin bude side din da take zaune ba, dan juyowa Sameer yayi
"Dan Allah kada maganar nan ta fita kawai da safe ki fada musu mun Dade a Asibitin ne yasa
Kika bamu dawo da wuri ba sun kulle, kiyi using da Nan kawai ki barsu su a can, Rukayya zata
kawo Miki kayanki da safe kiyi idan Allah ya kaimu". "To nagode".
Abinda ta iya fada kenan, ta bude ta fita Rukayya man ta fito tana fadin " Bismillah kizo muje na
rakaki".
Tare suka jera suka hau zuwa kofar, ita Kanta kofar abin kallo ce ita Yanzu zahra abin har ya
daina Bata mamaki so take taga iya gudun ruwan bayin Allah nan Kullum lamarin su ba baya
yake ba gaba yakeyi daga Nan sai can suna shiga ta Kara jinjina girman lamarin Wai shi
wannan abokin nasu wane irin kusancin ne a tsakanin su da za'a dunga sauke ta a duk inda
akayi ra'ayi. Wannan part din yafi wancan komai parlour sun Kai hudu, a cikin parlour na uku ne
suka taka steps ya Kai shida sannan suka shige want korido ko Ina tadal sai wani special
kamshi ke tashi bedrooms ne guda biyu a jere, Rukayyar ce ta Dan juyo tana murmushi "to
madam gasu Nan saiki shiga Wanda kike so ki kwanta, tunda kin samu muna yawon dare
kamar marasa gaskiya, Zan Baki shawara sai kin Zama jaruma fa a gidanki Dan Ya Mahmud
wallahi Mata rubibinsa suke, idan kikace Abu kadan Zaki fece kece ki tafi kece a kwana Dan
idan yayi wata tafiyar sai ki kwana hamsin Baki saka shi a idonki ba, pls you have to be very
strong gaskiya kada ki yarda a gano Ina kike da lapse akwai damuwa kwarai ki rike mijinki da
kyau ki mutunta shi ki girmama iyayensa zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah, zabi na rakaki
dakin na wuce barci Kuma nakeji tunda Allah yayi Mana gyadar dogo ya rabamu da kwanan
zaune to matar big bro ta Bata Ina Ni Ina barci ai sai kwana sallah".
Ta fada tana 'yar dariya.
"Ki sakani kowanne Wanda za'a sanwa ya taba cewa way gutsiri nan? Duka zaman na yau
zuwa gobe ne Dan gida zamu koma bana son wani surgery a Nan idan ma yimin din za'ayi ba
wannan Mai fuska kamar Jan karas din zatayi min ba muma muna da qualified a can Dan dai
kada nayi musu dashi ne kawai". "Kinga mu Shiga na koma dare Karayi yakeyi gara naje na kishingida".
Dakin da yake facing dinsu ta bude MashaAllah" ta fada Tana karewa dakin kallo sannan ta
juyo tana fadin mu kwana lafiya"
Kallonta Zahra keyi tana son tayi Mata tambaya Amma ta rasa ta Ina zata Fara, Dan Yanda
tasan gudan Nan da Yanda take fadar wasu abubuwan akan Mahmud ga Kuma abinda Hajiya
kakarsu ta fada Mata dazu maganganun suna kamanceceniya da juna amma Bari ta Adana
tambayoyinta da sauran lokaci. "Nagode Aunty sai da safe, Amma fa Ina Jin tsoron gurin nan fiye da can din wallahi, Kinga
Nan ba kowa. Allah mu kwana tare ko kin tafi bazan iya barci ba".
Dan Jim tayi tana tunani ita Kanta Bata San dalilin Ya sameer na kawota Nan ba, amma tasan
dole da dalilinsa nayin hakan.
"Ok ba damuwa Bari naje na dauko sleeping dress Dina da naki saina dawo"
"Ok, yauwa Aunty ki taho min da phone Dina tana cikin bedside".
Ta nufi Hanyar fita, wayarta ce ta dauki ringing number ce tasan Wanda ya Karba ne dazu a ta
daga da sallama suka Kara gaisawa ya tambaye ta ya suka zo gida ta fada masa lafiya kalau
sukayi sallama ta fice.
Kofar ta rufe ta farko tayi gaba tana fadin "kamar wata Rukayyar mahaukata na shigo wannan
part din na kwanta a can ma naki kwana ballentana a Nan yarinya Allah ya kawo mijinki ki
tarairayi kayanki kuna gefe Naga alama sai nayi Mata budedden karatu sannan zata gane mace
har Mace ta fita kunya Amma ki tsaya kina Wasa da damarki". Ta wannan barandar