Showing 27001 words to 30000 words out of 31290 words

Chapter 10 - Rayuwar Raihana Part 2 Hausa Novels by Takori Kabara.pdf

ci gaba da jiran ango, a
karbe shi da soyayya marar misali, da aka tanadar masa.
****
A TAKAI
A Takai, Rayhanah ta wayi gari a gidan Hakimi matsayin daya daga cikin surukan gidan, yadda
Haj. Karima da Hakimi ke kula da tarairayarta basa yiwa ‘ya’yan da suka haifa su Nabilah. Ga
wani girma na musamman da barorin gidan ke bata.
Su Zinaru sun koma gidajensu. Juma kawai aka bar mata, Hakimi ya ce ta rufo gidanta
kwata-kwata ta zauna da jikarta a duk inda Allah ya kaita zaman aure. Tunda bata da miji, ba
Da, ba jika. Don dadi Rayhanah kuka ta saki ta rungume Inna Juma tana yiwa Hakimi godiya.
Ya ce, “Babu komai Rayhanah, yadda zamu kula da ‘ya’yan cikinmu, haka muke kula da
surukanmu. A kalla kina bukatar budar ido ki ga jininki ko yaushe a kusa dake. Allah ya ji kan
Malam Rashidu, na zauna da shi cikin amana don haka Rayhanah ke amanar Allah ce a
hannunmu”. Tunda aka daura auren nan Nabilah ke ta kuka, ta hana uwarta sakat da jama’ar gidan baki
daya. Kowa na da masaniyar cewa ta zauna ta kai shekaru talatin a gida ne cikin jiran dawowar
Ya Himu, ta kori duk masoyanta amma ba a duba hakan ba, mahaifinta da mahaifiyarta sune
ja-gaba wajen aurawa Ibraheem din da ta kallafawa rai wata bare ‘yar talakawa ba ita ba. Duk mai tausayi dole ya tausayawa Nabilah a bisa yadda ta mai da kanta kamar matar mamaci,
balle kuma iyayen da suka haifeta.
Haj. Karima mutum ce mai tsananin kawaici da zuciyar mai da nata ba nata bane, da kuma
biyayya ga mijinta. Tabbas tana tausayin Nabilah amma ita a ganinta gara haka, gara da hakan
ta faru da Nabilah ta yi auren da ba za a ga kimar ta ba, tunda ita ce mai son, wanda ake son
bai san tana yi ba. Tabbas kulluwar aure a tsakaninsu zai iya kawo babbar baraka cikin zumuncin iyayensu da
suka budi ido suka gansu tare ba a taba jin kansu ba (Dr. Mansur da Hakimin Takai Abdulkadir
Balarabe Sardauna).
Ta kuma yi la’akari da cewa, Dr. Mansur ya san da zaman Nabilah, amma ya kawo baren ya ce
ita ya zabawa dansa. To nacin na mene ne? Dama ita ta maida kanta tsohuwa, amma manema
wane iri ne Nabilah bata gani ba? ‘Yan boko, attajirai, masarauta babu irin wadanda basu nemi
auren ta ba amma ta ki. Yanzu da hakan ta faru a ganin Haj. Karima, sai ta nutsu, ta san tudun dafawa (in fa har tana da
hankali). Ibrahim ba shine autan maza ba, ta yiwa kanta suttura kamar yadda Hibbah ta yi, gata
can da ‘ya’yanta dugwi-dugwi dasu har uku. Soyayya daban, aure daban. Aure ana yin shi ne
don Ibada, ba don son zuciya ba, soyayya ba ita ce aure ba. Sai ayi soyayya kamar a cinye juna shekaru aru-aru, amma idan Allah ya kawo aure, sai a yi shi

cikin kwana uku. Masana a ilmin halayyar dan Adam sunyi ‘analysis’ a kan soyayya sun gano
cewa, majority (akasari) long-dating (doguwar soyayya) ba a yin nasarar yin aure da ita, iska
take bi, kamar ba a yi ta ba.
Sai ayi aure ba a san juna ba kuma a zauna lafiya, a hankali sai so ya shiga. Shi wannan son
ba irin na soyayyar iska bane, so ne na halitta wanda gamayyar jiki (physical relationship) ke
haifar da shi. Yana da karfin da soyayya bata da shi, yana da tasirin da soyayya bata da shi,
yana da tubalin da dan Adam bai iya hako tushensa wanda shine tsakanin Adamu da Hauwa’u,
sune kuma suka haifemu, Allah ne ke sanya shi ba long-dating ba.
Don haka ita Haj. Karima addu’a take yiwa autarta Allah ya yi mata zabin miji mafi alheri, wanda
zai so ta fiye da yadda take son shi, amma ba bahaguwar soyayyar da take yiwa Ibraheem ba.
Gara ka auri wanda ke sonka a kan ka auri wanda kake so!!!
****
[12/24/2019, 21:48] Takori: Mukhlis Abu-Arab, shi ya musuluntar da ita a Jos, ba da sanin
yayanta Yohan ba, wanda yake rike da ita a lokacin bayan mutuwar iyayensu. Mukhlis abokin
cinikin Yohan ne, yana kawo kaya daga Egypt su Yohan na saye su zuba a shagunansu a
babbar kasuwar Jos. Galibi gayan yara ne (Children wears and accessories) a lokacin duniya
na kwance, kasuwanci yanada albarka. Sai Allah ya hada Yohan da Mukhlis duk da bambancin
addini sakamakon son da yake yiwa tilon kanwarshi.
Shi Yohan bai taba haihuwa ba da matarshi Marye, shi yasa yake son kanwarshi Anita kamar
shi ya haifeta, gata da hazaka a makaranta, ita ma Marye tana son Anita saboda yarinya ce
kyakkyawa mai shiga rai. Har yau Yohan bai musulunta ba, sai dai ya bar Anita (Asma’u) ta yi
addinin da ta zaba shi kam banda shi. Kuma fa Hausawa ne, Hausa rangadadau a bakinsu kamar jakan Kano, amma basu yarda da
addini ba, Neither Islam nor Christianity, Budduism, Hinduism, Jainism, Sikhism Paganism,
Rastafari, Taosim ko kowanne ma.
Ta wannan kasuwancin Mukhlis da Yohan suka yi kudi na ban mamaki. Mukhlis ya sayi gida a
Jos, kawai don Yohan ya yarda ya aura masa Anita. Suka ci gaba da kasuwancinsu Anita na
girma. Mukhlis ya sayi kadarori da yawa a Jos don a nan yake son kafa tubalin iyalinsa.
A lokacin kasar Egypt na fama da matsin durkushewar tattalin arziki kamar Sudan. Larabawan
Egypt da yawa sun warwatsu a duniya don neman halalinsu. Garin Hurghada a can matsin yafi
yawa. A Larabce ana kiran Hurghada da El-Ghardaqah).
Da yawa sun shigo cikin Cairo suna leburanci masu ilimi sun tsallaka kasashe irin Saudiyyah,
Dubai, Bahrain, Kuwait, Taiwan, Dammam Qatar da sauransu. Wasu sunyo Africa irin su
Mukhlis kenan.
Duk dimbin iliminsa a kan Geography ya fi ganewa kasuwanci, kuma Allah ya sanya mishi
albarka a ciki. Har ya soma tsallakawa kasashen da suka ci gaba yana kawo kayan daga can,
musamman Saudiyyah, akwai wani shago a Madina wai shi Majma’al Qimmah da ya shahara
wajen kayan yara, Mukhlis na daya daga cikin manyan dilolinsu. Sanda Anita ta shiga aji shida na sakandire shekarunta goma sha biyar, sai tsahon kafa kawai.
A lokacin ne ya nemi Yohan da bukatarsa na neman iri a wajensa.
A lokacin shi Yohan yana shirye-shiryen komawa kasar Ireland shi da Marye, inda harkokinsa
suka fi yawa. Shi abin ma dariya ya bashi, wai Mukhlis ya yiwa Anita tsufa duk da bai taba aure
ba. Sai dai shi kansa ya san bai isa ya hana Mukhlis Anita ba, ba don su basu da addini ba su,

sai don shakuwar da ke tsakaninsu ta tsayin shekaru masu yawa.
Tun Anita na ‘yar shekara biyar Mukhlis yake kula da ita da daukar nauyoyin rayuwarta. Da dora
ta a kan hanyar tarbiyya kamar diyar Musulmi. Ya dora Asma’u a kan turbar yin shigar da ba ta
fidda tsaraici ba, sun sha yin sallah shi da ita a boye.
Haka ya taka rawa wajen kara mata karfin gwiwa a kan ilimin zamani. Har abada Asma’u ba za
ta manta da Mukhlis ba, har abada hoton wannan ranar ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba.
Wato ranar da Mukhlis ya danka sadakinta a hannun Yayanta Yohan, ‘yan’uwa da abokan arziki
suka shaida. Bai kuma taba ta a ranar ba sai da ya lakana mata LA’ILAHA ILALLAHU,
MUHAMMADUR-RASULULLAHI a bisa ra’ayi da yardarta. Don zuwa lokacin Anita ta yarda su
dabbobi ne kawai sakamakon cakudo da musulmi a makarantu da take yi da kuma tarayyarta
da Mukhlis, tana ganin yadda yake tafiyar da ibadar addininshi yana burgeta, su haka nan suke
kara zube, kamar katakwaye da duwatsu. Babu direction.
Mukhlis shi ya sanya mata suna Asma’u, sunan mahaifiyarsa bayan yin shahadarta. Wata da
watanni Mukhlis na koyar da Asma’u hukunce-hukuncen addinin gaskiya. A karatun Alkur’ani da
yake koya mata sun zo izfi ashirin ya kuma dauketa ya sanya a Islamiyya, kasancewar shi ba
mazauni ba. Sai da ya tabbatar ta ilmantu ta zama cikakkiyar Musulma sannan ya fara mu’amalar aure da
ita. Rayuwar auren Asma’u da Mukhlis rayuwa ce mai dadi amma takaitacciya. A lokacin Yohan
da Marye suna Ireland sun tafi sun barta da mijinta, wanda ke tattara komai nasa a Nigeria cikin
nutsuwa domin ya koma gida tare da matarsa. Allah ya aiko da mummunan hatsarin jirgin
‘Egypt Air’ wanda ya taso daga Cairo zuwa Nigeria har da Mukhlis a ciki.
Asma’u dai sakamakon wannan labari sai nakuda ta tashi, ciki wata takwas sai fedeta aka yi
don ta kasa haihuwa. Aka fidda yaro namiji mai kama da ita, amma kalar mahaifinsa.
Bayan takaba da zuwan dangin Mukhlis suka sai da duk wata kadara tasa suka auna suka yi
gaba, sun ki sauraren kowa a kan matar da Dan. A lokacin Yohan na Ireland kuma babu
hanyoyin sadarwa irin na yanzu.
Asma’u gidan Yohan ta koma ita kadai ta ci gaba da rainon yaronta wanda take yiwa wani irin
masifaffen so kamar yadda take son Mukhlis Abu-Arab, tana amfani da ajiyarta ta banki da
Mukhlis ke zuba mata duk wata tun aurensu da sunan asusun ajiyar ko-ta-kwana.
Yau da gobe ba ta bar komai ba, kudin banki suka kare. Ko kudin da za a saiwa yaro madara
babu, saboda tana da karancin ruwan nono. Haka nan ta yi ta fadi-tashi har da wanke-wanke da
shara gidan masu akwai don kawai ta samu abin da za ta sanyawa Abdullahi a baki. Ba ta
damu da kanta ba, she only want to save his life..... Asma’u har kosai da fanke ta sayar, a kofar
gidansu take soyawa safe da yamma da kuruciyarta da komai, duk saboda Khalipha. Khalipha
na da shekara daya Allah ya jefo Yohan gida.
Kuka na duniya Yohan ya yi shi da ganin yadda tilon kanwarsa wanke-hannu ka taba ta koma
rufe hannunka sannan ka taba. Amma fa yaronta bul-bul very energetic, diety.
Ita dai ce cikin tsummokara, amma danta tsaf cikin napkin mai tsafta da riga mai kyau har
kamshi yake. Rasuwar Mukhlis da abin da danginsa suka yiwa Asma’u da danta ya taba zuciyar
Yohan. Abin da ya kai shi ga yin alkawarin har Khalipha ya mutu ba zai kai musu shi ba, zai rike.
A satin suka daga Dublin. Abin da Yohan ya fara yi domin inganta rayuwar Asma’u da danta shine samar mata gurbi a

Jami’ar Trinity, ta fara karatun medicine cikin himma. Ba ta yi nisa da karatu ba Khalipha ya
soma wani rashin lafiya, sai hankalinta ya rabu biyu, don ma Marye tana taimaka mata da
hidimarsa.
Zama a Turai bai sa Asma’u ta canza daga addinin da ta karba da zuciya daya ba, ba ta son
barin danta hannun Marye don ta san ba ta da tsarki. Ta fi so ta kula da danta da kanta, ko ina
zata tura shi take cikin keken zaman yara, sai dai dole lokutan daukar darasi take barinsa da
Marye. Likitoci sun sha bincike a kan dalilin da ya hana yaro Khalipha barci kullum cikin dare sai kuka,
inda suka gano cewa ciwon hanta ne (Hypertitis B). Allah ne ya yi kawai Khalipha rayayye ne ba
maganin asibiti da kwakule-kwakulen likitoci ba.
Asma’u ta ji jiki ta sha wahala da danta Khalipha, Yohan da Marye sun taimaka. Ta yi ta yi su
Musulunta sun ki. Rashin lafiyar Khalipha ne yasa ta dauki bangaren likitancin yara paedatric
don kawai ta kula da lafiyar Khaliphanta.

Haduwarta da Mansur Balarabe Sardauna, ta samo asali ne a matsayinsa na daya daga cikin
malamansu, a lokacin shi ya yi graduating yana aikin da ya zamewa duk wani foreigner dole
bayan kammala karatu kamin ya koma kasarsu.
Ya lura in ana darasi tana yawan fita ta je ta shayar da baby a hannun wata dattijiyar
Balarabiya da take aikin leburanci a Jami’ar, take rike mata dan saboda Allah, don ta lura
Asma’u ce kadai Musulma a bangaren da take kula da shi. Amma abinda yake daukar hankalin
Mansur da Khalisah (dattijuwar), basu taba ganin uban dan ba, ga shi Balarabe ziryan ita kuma
da ganinta ka ga ‘yar Nigeria.
A al’ada irin ta Bature, mace mai aure kusan koyaushe tare take da mijinta duk inda za su je,
balle idan akwai karamin yaro kusan uban ne ke da wannan alhaki na kula da yaron a lokacin
zirga-zirga, shi zai tura shi zai dauka, basa barin matansu su sha wahala.
Hazakarta a karatu na ba shi mamaki yadda take yin zarra da manyan maki (marks) a cikin
Turawa. Ya damu da al’amarin ta, gata yarinya karama da ko ashirin ba ta rufa ba. Idan yana
lacca kusan rabin hankalinsa a kanta yake, idan tambaya ce ita yake jefawa, ba ta yin kasa a
gwiwa wajen farke masa zare da abawa. Tafi-tafi Mansur ya kasa sukuni da tunanin Asma’u da begenta dare da rana. Uncle Yohan shi
yake daukar nauyin karatun Asma’u, ba yadda bai yi ba don ya samo mata Nanny din da za ta
dinga kula mata da Khalipha a gida ta je ta dawo tunda ba ta son shi a hannun Marye. Asma’u
ta ki. Ya ce, zai dinga kai shi gidan raino na Turawa shima ta ki. Don haka ya yi fushi ya rabu da ita
kamar akan ta aka soma haihuwa. Ga shi Allah ya jarrabi zuciyarsa da son Khalipha
kasancewar shi Allah bai ba shi haihuwa ba.
Daga shi har Marye kyamarsu take, ko abincinsu ba kowanne take ci ba. Don a Jos Marye
murde kan kaza take da ranta ta cizge ta cillar ta fige ta dafa. Ire-iren wadannan yasa Asma’u ta
gwammace Yohan ya ba ta kudi ta sayi ‘halaal’ ta dafa da kanta ko ta yi take away daga
makaranta a wajen larabawa musulmi ko Pakistani mazauna turai. Asma’u bata takurawa Yohan da cewa lallai sai ya Musulunta ba, don ta lura tana tufka ne
Marye na warware mata, ko yaso ya saduda zigar Marye ke hana shi. Tana nuna masa cewa
addinin Musulunci addini ne na takurawa kawai, sannan Musulmin da ya zama kasurgumin

Musulmi shine yake zama terrorist (dan ta-adda).
To Allah shi ke hukunta al’amura yadda yaso, idan ya so bawanshi da shiriya ruwa da iska basu
isa su hana ba. Marye ta yi mutuwar wulakanci a Dublin inda wani ginin bene ya rubza da ita da
jama’a masu dimbin yawa, ko gawarta sai part-part aka tattara, sauran namanta ya zama na
ungulu da tsuntsaye. Asma’u ta ja dan’uwanta a jiki, dare da rana, yini da safiya tana kwadaita masa dadin addini
musamman na Islam. Ta kan ce, “Shi Musulunci haske ne kuma guidance ne, wanda zai sada
dan Adam ga nutsuwa da kwanciyar hankali, hanya ce kawai dake nuna maka yadda za ka rayu
a kan tafarki madaidaici. Tsani ne mai mika mutum kusa da Ubangijinsa yaje ya iske sakamakon
abin da ya shuka a rayuwarsa ta duniya.
Ba abin da addinin musulunci bai koya mana ba, hatta shiga bandaki, tsarki, wanka, cin abinci
duk Islam ya kawo su a kan hanya sahihiya (to the heaven)” Haka dai, yau da gobe har Allah ya
taimaketa ta yi galaba a kan Yohan, ta kai shi wajen Limamai suka musuluntar da shi ya mai da
sunanshi Yahya. Hakan bai hana har yau jama’ar da suka san shi kiranshi da Yohan ba. Yohan (Yahya) ya shiga Islam ne da zuciya daya. A wannan lokacin Yohan ya yi karfi na ban
mamaki cikin kasuwancin da yake yi tsakanin Ireland da Nigeria. Ta hanyar Asma’u ya auri wata
mutuniyar Somali zaunannun Dublin wai ita Aasiya. Ba ta taba yin aure ba amma ta manyanta
domin cikakkiyar likitar mata ce. Shekara ba ta kai ga fita ba Dr. Aasiya ta haihu da namiji. Ashe matsalar daga Marye ne ita din
ta sani likitoci sun gaya mata, wannan ne yasa ta san duk hanyar da ta bi ta hana Yohan zuwa
asibiti a bincike su sai karyar bari (miscarriage) take masa.
Har lokacin Asma’u na jinyar Khalipha dake fama da hypertitis B. Zuwan Aasiya gidansu ya
kawo sauki mai yawa cikin rayuwarta duk da ita ma Aasiyar ma’aikaciya ce a babban asibitin
kasa amma tana taimaka mata sosai wajen rainon Khalipha har Allah ya raya shi, ta kai shi
wata Islamic school a London (Al-Muntada Islamic Pri. Sch.) boarding, ita kuma ta koma Dublin.
Duka cikin aljihun Uncle Yohan.
A shekarar Dr. Aasiya ta kara haihuwar diya mace, a wannan lokacin shekarun da Mansur zai yi
yana aikin wucin-gadi da jami’ar Trinity sun kusa cika, zuwa lokacin ya yi duk binciken da zai iya
a kan Asma’u, ya tadda komai, wato ba ta da aure, uban dan ya rasu.
A matsayinshi na Bahaushe Ba-Kano kuma wanda ya fito daga jinin sarautar Takai abin ya zo a
karkace, saurayi da auren bazawara mai da. Duk da addininmu bai hana ba, karewa ma hakan
sunnah ce, kuma ya san yayansa Abdulkadir ba zai taba ki ba. Shi a kaunar da yakewa Asma’u
ma, ko kantin kwari ta haife zai rike mata, kuma in ta amince zai aureta. Kai tsaye bai doshi Asma’u ba, domin ba fuska, kullum suturce take cikin yalwatacciyar suttura
da karamin hijabi iya kafadunta. Sai ya bi ta hanyar da kowacce UWA ba za ta iya kaucewa ba.
Wato yaje ya yi kawance da dattijuwar lebura Khalisa, yake tayata hidimar Khalipha kafin
Mamanshi ta kai shi makarantar kwana. In ba shi da lacca wajen Khalipha da Khalisa yake
lalacewa. Siyo wannan, siyo wancan duk na Khalipha.
Har Asma’u ta fara mamaki saboda ta san ko shi wane ne a Trinity da tarin iliminsa. A hankali
suka soma gaisawa, tunda an ce mai Da wawa. Wani irin so Mansur kewa Khalipha wanda ko
shi ya haife shi sai haka, ba kuma don komi ba sai don kamanninsa da mahaifiyarsa. So na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login