Showing 30001 words to 31290 words out of 31290 words
Chapter 11 - Rayuwar Raihana Part 2 Hausa Novels by Takori Kabara.pdf
hakika shine ka so uwa tare da dan ta. Sai ga Asma’u na gayar da Mansur Takai kullum, har in ba ta ganshi ba ta hau tambayar
Khalisa yau Baban Khalipha bai zo bane? Khalisa kan ce, ya zo ya sumbace shi ya ba shi
chaculates ya tafi. Sai Asma’u ta yi murmushi har ta kai Khalipha London a bisa shawarar
Mansur a haka suke.
Mansur shi ya lalubo mata makarantar kasancewar ya zauna England kafin Ireland inda ya yi
karatun share fagen shiga jami’a. Ya fita sanin UK da Islamic Schools masu yawa dake cikin ta.
Sai kuma aka koma kawance har cin abinci take gayyatarsa gidansu wajen Uncle da Dr. Aasiya.
Ta kai ta kawo duk wani wanda ya rabi Asma’u, to ya saba da Mansur mai yi mata son
kan-uwa-da-wabi, wato sonta yake tare da dukkan ahalinta da duk wanda take tare da shi.
Tare suke zuwa London dubo Khalipha duk wata. Lokacin komawar Mansur gida ya cika, amma
ya kara neman visar aiki ya shantake ya ki tafiya saboda Asma’u. Su kuwa gwamnatin Dublin ai
gaba ta kai su don dama irin Mansur din suke so su suke gudunsu domin kishin kasa
(Patriotism). Irin na ‘yan bokon nijeriyar jiya ba na yau ba. Sai suka shiga jika shi da kudi, gida cikin gidajen malaman Jami’ar Trinity da Insurance,
accommodation and allowances. Da Hakimi ya bi ba’asin fasa dawowar tasa bai boye masa ba,
“He cannot live without Asma’uuuuu!!!”
“Wace ce ita?”
Hakimi ya tambaya.
Bai boye komai ba ya warware masa zare da abawa. Satin bai cinye ba, sai ga Hakimi
Abdulkadir Balarabe Sardauna da mai dakinsa Kareema a Dublin. Suka karbi auren Asma’u da
amincewarta hannun Yohan, suka danganata da dakin mijinta da alkawarin suma din su koma
gida. Suka yi musu alkawarin hakan, wato da zarar ita Asma’un ta kare Khalipha ya gama
primary.
Mansur da Asma’u cinye junansu ne kawai basu yi ba, saboda so da kauna, a shekararsu ta
biyu da aure ne ta haifi IBRAHEEM. Ba ta kara haihuwa ba, ba kuma dalilin tsarin iyali ba, Allah
ne bai bata ba, don in ta Asma’u da Mansur ne, duk shekara su haife, suna da halin da za su
kula da abinsu, kuma suna so, kamar su hadiye su. Sanda Khalipha ya gama primary, Ibraheem na primary 3 a Al-Falah Islamic Children School in
London. Asma’u ta karbi kwalinta suka tattaro suka dawo gida Nigeria da ‘ya’yansu biyu maza,
baki da fari duk kyawawa, kowanne da irin kyan shi mai daukar hankali.
Tun kan su zauna sosai su huta federal ta karbesu aka cillasu asibitin koyarwa na UNILAG Dr.
Mansur na aiki yana kuma koyar da medical student. Basu kara haihuwa ba har aka mai dasu
Ibadan Teaching Hospital duka tare suke aikin shi da Asma’u.
A can ne Allah ya basu Jawahir, aka mai dasu Jos suka haifi Abida a can bayan shekaru uku.
Daga nan haihuwa ta kara dauke mata dif! Har suka dawo Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya,
shi ya dauki kujerar kwamishinan lafiya ya baiwa Dr. Mansur a dalilin wani aiki na koyarwar
sa-kai (voluntary) da ya yiwa jami’ar Abdullahi Bayero, wanda shi gwamnan ya neme shi da ya
yi.
Wannan ne mafarin zamansu a gidan da suke ciki yanzu a Lamido Crescent, Gwamnatin ce ta
bashi ya zauna har ya yi kokarin da ya mallake shi bayan barinsu Gwamnati da komawarsu
bakin aiki. A nan ne kuma ta haifi auta Azizah.
Shima Uncle Yohan ya baro Dublin tuni da iyalinsa suna zaune a Jos. Shakuwar dake tsakanin
Khalipha da Uncle Yohan ta wuce tunani, don haka yau abin da ta gani ya tabbatar mata da
sanya hannun Yohan Khalipha ya nemo dangin ubansa har ya auro jininsa ba da izininta ba.
Ta riga ta yi fushi mai tsanani da dangin Mukhlis shi yasa ko da wasa ba ta taba gaya masa
cewa ba Dacta Mansur ne ya haife shi ba kada ya ce zai je ya nemo su. Da ta kawo nan a
tunanin da take yi a tsaye a bakin kofa sai hawaye suka tsinke mata.
Yohan da Baba Dacta basu kyauta mata ba, ta fassara hakan da cewa Baba Dacta ya yi hakan
ne don ya rama abinda ta yi masa na hana Khalipha auren gallafirar ‘yarsa, me ta yi da zafi, da
ta cancanci hakan???!
****
MURFIN LITTAFI NA BIYU!
Tana shirin juyawa ta fita ta ji hannayensu sun rungumeta, sun hanata fitar. Khalipha da
Mimtaaz, ke hawayen suma, suna rokonta ta shigo gidansu, ta sa musu albarka, in sun bata
mata ne abisa rashin sani ta yafe musu. Domin dukkansu sun tsorata da dogon tunanin da ta
afka a tsaye a bakin kofa. Mimtaaz hannun Radhiyyah ta kamo suka shigo dasu cikin falon.. Ita dai Radhiyyah jikinta ya yi sanyi, musamman da Mimtaz ta soma hidimar kawo wannan kawo
wancan tana lallaminsu su ci. Tambayar kanta take mececedin Khalipha wannan? Khalipha
bedroom ya shiga ya sako cikakkiyar suttura a jikinshi ya dawo.
A baki yake baiwa Mami abinci. Mimtaz na hidimar zuzzubawa. Sai ta ji tausayinsu dukkansu su
biyun ya kamata. Hawaye sosai take yi da ta tuna Mukhlis haka yake wannan hidimar da ita
wajen cin abinci yadda Mimtaaz ke yi yanzu.
Kawai sai ta rungume Khalipha tana bashi hakuri tana yiwa Mukhlis addu’a. Sai ya jawo
Mimtaaz ya kara mata ita cikin hannuwanta. Sun dau lokaci a hakan kafin Mami ta ce,
“Ga Radhiyyah, amma wallahi na daina shishshigi a al’amarin Ubangiji. Na baka zabi ka zauna
da ita ko ka sahale mata in baka so tun iddah ba ta hau kanta ba. Babu ruwana, kana naka
Allah na nashi, kuma nashin shine gaskiya”.
Ta kai gefen mayafinta tana share ido. Tambayar kanta take tana mamaki wa ya nunawa
Khalipha danginsa har suka yi masa aure? Ita kanta duk dadewarta a duniya in za’a kashe ta
bata san hanyar Hurghadah ba. Ya ce,
“Na sake ta Mami, Mimtaaz ‘yar uwata kuma kanwata ta isheni, Allah ya bata miji na gari, ba
zan iya yin adalci ba.”.
A daren Mami da Radhiyyah suka juyo Kano ko gidanta ba ta shiga ba, sai da ta kai Radhiyyah
gaban iyayenta. Ta kawo takardar saki da Khalipha ya rubuta ta bayar. Babu tsoro babu shakka
ta gayawa Dr. Halima aure ya kare, Khalipha baya so.
Sai abin ya zama fadi-in-fada a tsakaninsu, aka soma maidawa juna magana ana tonawa juna
asiri.
Mami ta ce, “Ai na gane kokari kike ki tarwatsa min gida, ki aure min miji, ko kin dauka ban san
kuna neman Dacta har ofishinsa ba tunda naki mijin hoto ne baya amfanuwa, in takurawa Da na
ya tsane ni, in kuntata masa ke ki farantawa taki?
Ko kin dauka ban san asirin da kike jifana da shi ba? Ba Rayhanah ba, ko uwarta ce yaje ya
auro min zan zauna lafiya da ita, so kike ki fiddani daga addinina kina tura min shaidanu cikin
kaina, to ta Allah ba taki ba. Ga ‘yarki nan Umma ta gai da Assha, gobe kuje ku kwashe
tarkacenku Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi, amin”.
Ta mike ta nufi kofa Dr. Halima na gyada kai tana fadin
“Za ki gani, in dai Dr. Mansur ne da kike takama da shi haka za ki barshi wutsiya a zage.
Tsohuwar arniya tubabba”.
Mami ta ce, a sanda ta murda kofar falon zata fita batareda ta juyo ba
“Na fi wadanda aka haifa cikin Musuluncin, tunda bana zina balle kwartanci”. Da haka ta fice.
Mu Hadu a RAYUWAR RAYHANAH 3&4.