Showing 6001 words to 9000 words out of 25000 words

Chapter 3 - Rayuwar Raihana Part 3 By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

ba!
Bayan fitar Inna kira ya sake shigowa, Rayhanah ta daga, duk da ta ce ba za ta kara dagawa
ba, zuciyar da gangar jikin sun ki amincewa, cewa suke;

“........ ba zamu samu sauki ba in bamu ji shi ba, ba zamu barki ki zauna lafiya ba sai mun ji
ko shine IBRAHEEM!!!
[12/25/2019, 15:42] Takori: Ya tabbata ta amsa kiran, amma ba ta yi magana ba.
Ya dade shima bai ce komin ba, sai da ya saisaita kansa ta hanyar yin ajiyar zuciya akai-akai,
sannan a sanyaye ya ce,
“Am now not to ask for Doctor, (yanzun ba Dr. Zan tambaya ba) don haka don Allah kar ki
kashe min waya.
I want to know more about you..., Concerning you. ...”
Ta ce, “You can ask me anything (za ka iya yi min kowacce tambaya) insha Allahu ba zan
kashe ba”.
Ta fada da muryar da ta kara kassara Ibraheem.
Ya ce, “Meye alakarki da Doctor Mansur?”
“Likita da mai taimaka masa”.
Ta amsa kai tsaye.
“Wannan matsayin da kike ikirari bai yi isar da zai sa ya baki wayarsa ba. Don Allah!Ke wace

ce dinsa???”
Tunda ya ce ALLAH! Sai ta ji ba za ta iya yi mishi karya ba. Kuma jikinta yayi wani irin sanyi,
da wata muryar again da Ibrahim ba zai taba mantawa ba, ta ce,
“Kafin in amsa maka, nima ina so in tambayeka don ALLAH! Ko kai ne IBRAHIM.....???”

Shiruuuu! Ya bakunci kunnenta. Da ta duba sai ta ga cajin wayar ne ya mutu. Don haushi sai
raunanniyar zuciyarta ta ce da ita,

“Ki rushe da kuka........”

Shi din kuwa ta shiga yi mai yawa, sai da ta yi ya isheta. Wannan mutumin da take waya da
shi, da matsayin da zuciya da gangar jikinta suka baiwa muryarsa, suka kuma karbeta, da
tasirin muryar cikin gangar jikinta da kwakwalwarta, da wata tsoka guda daya dake tsakiyar
kirjinta (zuciya) ya fi gaban na wani mutum kawai, wanda yin waya da shi kawai zai haifar da
wadannan emotions. He must be the HUSBAND.
Ba ta tantama ko shakkar cewa shine mijinta IBRAHEEM MANSUR TAKAI....
Zazzabin na karuwa, sanyin da take ji na daduwa. Har Azahar ba ta fito ba kuma ta ki bude
kofarta kada Inna Juma ta dameta sai ta ci alkubus.
Ita yau ko naman Dawisu (Peacock) aka gasa aka kyafe mata aka ce ta ci da gida da mota
(in return), baza ta iya ci ba.
Muryar Ibraheem kawai take son sake ji, da son ganinsa a zahiri. Wata murya data haifar da
wasu bakin abubuwa agareta da bata taba ji ba a rayuwarta, ba kuma zata iya fassarasu ko
fasaltasu ba da kowacce irin siga don wani ya gane ko ya fahimta.
Zazzabin kuma sai ta ji yana sauka a hankali, a saboda lallashin da zuciyarta ke mata da
cewa,
“Watakila shine angon Rayhanah! Amma anya Rayhanah baki kamfato da yawa ba?
Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki?
Idan kuma ba shi bane hatta wannan tunanin da kike da bari da kike muryarshi na tasiri a
gangar jikinki da zuciyarki, kina aikata haramun ne fa, a matsayinki na matar aure!!!
“Astagfirullah!”
Rayhah ta fada a hankali. Ta debo kuzari da karfi ta zubawa jikinta, ta mike cikin zafin nama,
ta bude bed-side fridge dinta ta dauko gorar ruwan FARO mara sanyi ta soma kwankwanda. Sai
da ta sha rabin doguwar robar sannan ta ajiye.
Ba ta mantawa wannan horon Mami ne, ba ta bari su karya kumallo sai sun sha fresh water
sun koshi. Sannan ta adanawa Daddy wayarsa, ta bude kofa ta nufi falo wajen Inna.
Ba ta falon, don haka ta wuce dakin da ya zan mallakin Innar a kasan benenta.
Sanda ta shiga Inna na sallar Azahar, sai ta shiga bayin Innar ita ma ta yi alwalar ta fito ta
tada sallah.
Ko da Inna ta idar ba ta kulata ba laziminta ta ci gaba da yi kasancewarta mai son ibada, ba
ta zama haka kawai, inda abokin hira ayi hira ayi dariya, in babu a yiwa Ubangiji tazbihi ayiwa
Annabi salati.
Ta gane lamarin na Inna yau har da fushi a cikinsa. Ko don ta rufe kofa ne ko don ta ki cin
Alkubus ita ba ta sani ba. Sai ta ji ranta ba dadi, ta gurgusa ta kwantar da kai a cinyoyinta, cikin

murya mai ban tausayi ta ce,
“Inna idan laifi na yi miki don Allah ki yi hakuri”.
Girgiza kai Inna ta yi alamar a’a. Sai da ta kai laziminta ta ja addu’a ta shafa ta shafawa
Raihanan, sannan ta ce,
“Ni baki yi min laifin komai ba, auren nan ne dai nake so a kawo karshensa in ba mai nasara
bane”.
Rayhanah ba ta gane abinda Inna ke nufi ba, cikin mamaki ta ce,
“Inna kamar ya ya idan ba mai nasara bane?”
Inna ta ce, “Eh, idan ba mai nasara bane, abin nufi idan yaron baya so, ba zan zuba ido ki
kare kuruciyarki a haka ba har jinnu su soma kokarin auren ki.
Daga yau daki daya zamu dinga kwana. Bari Baba Likita ya zo, wannan zaman jiran
tsammanin warabbuka ya ishe ni”.

Fushi ne sosai ya bayyana cikin idanun Rayhanah, ba ta san sanda ta dagawa Inna sauti ba.
“Ko zaman shekaru ashirin ne Daddy ya ce in yi zaman auren dansa, kuma dan baya sona,
ba jinnu ba, ko ifritai ne za su aure ni ba zan taba ce da shi ya kawo karshen auren ba. Tunda
daurawa ce tashi, amma igiyar aure ba a hannunsa take ba balle ya tsinka ta.
Sama da wannan ni abin ikonsa ce sai yadda ya ga dama dani, don na san ba zai taba yin
abu don ya cutar dani ba. Shi ya mai dani -MUTUM....... Wani kwayar halitta guda daya da ya
tsaya ya maidani MUTUM!!! (Cewar Rahma Abdulmajid ). Ba don shi ba ban san ya ya
rayuwata ta baya za ta kasance ba, a lokacin da na budi ido babu kowa nawa a duniya. Don haka Inna don Allah kada ki yi masa wannan maganar hankalinsa zai tashi, ni na ce
na-ji-na-gani INA SON IBRAHEEM.......!!!
Ina darajja igiyoyin aurensa da suke kaina, ko da baya sona. Koda har abada bazan ganshi
ba, balle mu zauna tare.
Baku sani bane, baku san rawar da Daddy ya taka a rayuwata ba. Kun budi ido ne kawai kun
ganmu tare. He is someone I cherish and respect most! Ko me zan yi masa ba zan iya biyansa
hidimar da ya yi dani da rayuwata ba. Inna gaya miki ne ban taba yi ba, amma har nakasa nayi;
babu ji dungurungum!” Ta yi shiru tana share hawaye cikin TUNA BAYA. .....sannan ta ci gaba da cewa,
“Shi ya nema min magani na warke, da lafiyarsa, da iliminsa da lokacinsa da aljihunsa. Shi
ya bani ilimi irin wanda ya baiwa ‘ya’yan da ya haifa dama wanda bai basu ba.
Duk wannan bai isa ba, ya dauke ni ya aurawa dan da ya fi so cikin ‘ya’yansa. A lokacin da
aka so rayuwata ta tozarta Don na fito daga karamin asali, na taba yin cuta.
Sai kawai don yaron ban yi masa ba ya ki zuwa sai ki ce Daddy ya raba ni da auren dansa?
A’a, Inna kada ki fara, na zabi in mutu, in kare kuruciyata da rayuwata gaba daya da igiyar
auren Ibraheem, ina mai darajjata da kare martabarta. Don haka don Allah Inna kada ki kara
tada wannan magana za ta tada hankalin Daddy”.
“Sai na yi!”
Abin da Inna ta ce kenan.
“Fito fili kawai ki yi mana gori, bamu tallafi rayuwarki ba kina karama, a nan kam bani da
bakin musa miki. Amma ina da shi a wajen Allah, wannan kyautayi da alherin da ya yi ai
sakayyarsa na gurin Allah.

Ba zai zama hujjar cewa sai kin biyashi da tauye kuruciya ba, babu inda musulunci ya yarda
da wannan, sai in dama ya yi ne ba don Allah ba sai don ya aurawa dansa wanda baya so.
Mene ne dole? Babu dole!”
Amsar Rayhanah cikin rurin kuka ta bata mamaki.
“Inna in dai kin gaji da tayani zaman jiran Ibrahim ne..... kina iya komawa Takai ni in zauna ni
kadai. Babu abinda zai cinyeni cikin gidannan da yardar Ubangiji....,In har ba za ki taimaka min
in yiwa Daddyna biyayya ba.......!’’
Sai Inna ta mike a hasale tana fadin
“Haka kika ce ko? To shi kenan”.
Ta soma ciro kayanta daga cikin kwaba tana dannawa a (Ghana Must Go) din da suka zo a
ciki.
Kan ta gama kukan tuni Inna ta gama cika jakarta ta yi lullubi ta kinkima ta daura a kanta ta yi
waje.
Kamar an yiwa Rayha allura haka ta bita da gudu, ba ta cimmata ba sai a kofar fita daga
falon, ta kama jakar ta kankame tana kuka kamar na fitar rai. Inna na ja Rahane na ja, a haka
Allah ya kawo Dr. Mansur, saboda bacin ran junansu ko karar shigowar motarshi basu ji ba.
“Subhanallahi-Subhanallahi!”
Abin da yake fada kawai kenan. Inna Juma ba ta ko kalli kwayar idanunsa ba don ita kanta
ya yi mata kwarjini. Sai ta kasa cewa komai ta sunkuyar da kanta kasa, ya yin da Rayha ta
dauki jakar da kyar sabida nauyin ta, ta maida ita ciki.
Tana ji yana bai wa Inna hakuri da lallami da lallashi cikin girmamawa, sai haushin Inna Juma
ya kara kamata, da kyar ya lallabata suka koma falo.
Ya zauna a kan kujera yana fuskantar tsohuwa Juma, wadda ke zaune kasa kan kilishi ta
rasa daga inda za ta dauko masa zaren bayanin da ya bukata, wanda ya sata yin fushi haka,
har za ta iya tafiya ba tare da ta neme shi ba,.
Ko me Rayhanah ta yi mata ai yarinya ce, shi ya kamata ta jira ya zo in na fada ne ya yiwa
Raihan, in na tsawatarwa ne ya tsawatar mata. Yara yanzu ai ka haifesu ne kawai amma ba ka
biye musu sai ku taru ku zama yaran dukkanninku.
Inna ta yi shiru dai-dai lokacin da Rayha ta iso da tray shake da jus da ‘ya’yan inibi, peach da
pear ta ja karamin tebur din dake gefen kujerar da Daddy ke zaune ta dora ta matsar dasu
gabansa.
Hankalinsa kwance ya soma cin kayan marmarin yana sa mata albarka kamar ba shi ya sayo
da kudinsa ba. Ta koma daki ta dauko masa wayarsa ita ma ta dora a kan tebir din.
Ya shiga hamdala yana cewa, “Ashe a nan na barta, kai! Batan waya babu dadi, ba wayar ce
abin ji ba, al’amuran da suke ciki. Ke Rayhanatu jeki daki zan yi magana da Inna”.
Ta ce, “To Daddy”. Ta mike ta nufi bed room dinta.
Ya sha tambulan din ruwa mai sanyi, ya gyara zama ya ce,
“To Inna ke nake sauraro, laifin me mutuniyar taki ta yi miki haka har kika yi tunanin tafiya ki
barta?”
Inna ta share ido da gefen zaninta saboda tausayin Rayhanah, in iyayenta suna raye ai dole
za su yi wani abu a kan wannan zaman mara kan gado.
Ta ce, “Ita ce ta ce na tafi”.
“Raihan?”

Ya tambaya da mamaki.
“To a kan me?”
Ya sake dorawa ba tare da ya jira amsar ta farko ba.
Inna ta kwaso zance tiryan-tiryan ta shiga gaya masa yadda suka yi da Rayha da abubuwan
da ta fada akansa da aurenta da Ibrahim. Sai ga Dr. Mansur yana kuka amma ba mai sauti ba,
danshin idonsa kawai yake daukewa da hankicinsa.
Kaunar Rayhanah ce da kimarta suka karu a idanunsa,at the same time, Inna ta burge shi, ta
nuna masa a duniya akwai masu kaunar Rayhanah bayan shi. Kauna ba ta abin hannunta ba
ko don a rabi inuwar da take ciki, ingantacciyar rayuwa take nema mata, ba kwadayi da son
duniya ba. Muryar Dacta Mansur na rawa ya ce, “Don Allah don Annabi Inna ki kara hakuri komai ya zo
karshe insha Allahu. Ni na daura kuma ni zan kwance da yardar Ubangiji, zan bi Ibraheem har
inda yake in karbowa Rayha takardar ‘yanci. Amma kafin nan..........”
Ya zaro passport guda biyu ya mika mata.
“Kamar yadda na yi miki bayani shekaranjiya gobe zaku wuce kasar Singapore, Rayhanah za
ta dora karatunta ni kuma in wuce Chicago. Ba zan baroku ba sai na tabbatar Rayhanah ta
samu ‘yancin kanta, aure ko saki ayi karatu.
Abin da yasa har yanzu ban dau mataki ba akwai wsu matsaloli ne da nake warwarewa na
cikin gida, kuma alhamdulillahi na fara shawo kansu, ku kara hakuri Inna”.
Ta ce, “Ai shi kenan, Allah ya zaba abin da ya fi alkhairi. Sai dai ni kam ba zan iya zuwa kasar
da babu Allah babu Annabi ba idan ba Makka da Madina ba, don haka ni dai don Allah Alhaji
Likita ka cire ni daga wannan lamari naku na nasara ko na samu in cika da imani.
Yaya mace da igiyar aure a kanta za ta tsallake mijin ta cilla wata duniya daban wai karatu?
Kuma ba da izinin mijinta ba, ka duba lamarin nan da kyau Alhaji”.
Dariya ce ta kama Dr. Mansur ganin yadda Inna ta takarkare tana bayani tsakaninta da Allah.
Ya ce, “Inna zamani ya canza. Mata da miji duka fafutukar neman ilimi suke tunda Allah bai
iyakance ba, su taru su rufawa juna asiri. Don haka kada ki tauyi Rayhanah..... ba ki san tarin
baiwar da Allah ya yi mata ba.
Ni na gaya miki RAYHANAH na da future akwai wani nasibi da Allah ya yi mata wanda bai
yiwa sauran ‘ya’ya ba, wannan nasibi shine kwakwalwa, wanda jikina yake bani ba za ta kare
rayuwarta haka ba.
Hakan kuma ba zai faru ba sai da zuzzurfan ilimi wanda duniya ke damawa da shi,
musamman irin nata (computer).
Abin da za ki yiwa Rayhanah a yanzu shine addu’a da bata kauna da kwarin gwiwa irin
wanda Iya Bilki ta ba ta.
Wannan shine abin da za ki yi mata yanzu har Allah ya daidaita al’amarinta, nima ban
tsaurara ba, in Ibraheem ba shi da hujjar yanke sadarwa dani, ya yi ne don ba ya son zabina,
wallahi sai na raba auren ko a kotu ne. Ki kwantar da hankalin ki Inna”.
Inna ta ji dadi har cikin ranta. Ya kara da cewa, “Yanzu kada ki nuna mata kin gaya min
musabbabin fadanku, ki lallameta ki ce da ita baki kyauta ba, kuma kin gane ke kika yi laifi.
Ni zan wuce gida ku hada kayan da za ku bukata tun yanzu, gobe da daddare zamu tashi, ni
zan raka ku har Singapore, ba zan tafi ba sai Rayhanah ta soma shiga aji.
Daga nan sai in wuce neman Ibraheem, ki kwantar da hankalinki Inna, Allah yana ko’ina

kuma ko’ina kika yi ibada ko a birnin Sin ne ba Asiya ba (Asia) Allah zai karba. Idan babu ke
wane ne zai debewa Rayhanah kewar mijin? Wa zai dafa mata abinci kamin ta dawo? Waye zai
sadaukar da lokacinsa da rayuwarsa gareta idan ba ke ba? Kindly observe it........”
Murmushi ta yi ba don ta ji Turancin ba, sai don ya nuna mata ita mutum ce mai kima da wani
amfani ko yaya yake a RAYUWAR RAYHANAH duk da ba ta da abin da za ta bata ta wanke
dattinsu da su Zinaru suka goga a idon yarinyar ban da kauna ta fisabilillahi wanda shine
tsakaninta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login