Showing 15001 words to 18000 words out of 25000 words

Chapter 6 - Rayuwar Raihana Part 3 By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

Ai da azama ya fito ya bude kofofin da ya kukkule ya zari mukullin mota ya yi asibitin da yake
gudu don ya gayawa Daddy ba zai zauna gida daya da mutanen boye ba. In ba zai barshi ya
zauna kusa da uwarsa ba to zai koma inda ya fito.
Daddy yana seminar-room da likitocin bangarensa gaba daya wadanda suke karkashinsa,
meeting suke yi mai muhimmanci a kan sabuwar cutar da ta iso Nigeria ‘Ebola’.
Ibraheem ya fado dakin tattaunawar babu ko sallama, kwarai a firgice yake kira yake
“Daddy-Daddy.....”
Gaba daya likitocin sama da talatin suka maida hankalinsu da idanunsu gare shi. Ba ta tasu
yake ba sai da ya isa jikin mahaifinsa ya rungumeshi jikinsa yana kyarma yana fadin
“Wallahi ba zan koma gidan nan ba, in ba auren za ka bani ba to zan koma Chicago, I’m
exetremely perplexed.......”
[12/26/2019, 13:19] Takori: Hannunsa Dr. Mansur ya kama sannan ya manna shi a jikinsa ya
dauki excuse suka fito yana jaye da hannunsa yana yi masa magana cikin lallashi.
“Kwantar da hankalinka gaya min me ya faru?Ka ji Ibrahimu?”
Ya rungume shi sosai a jikinsa don ya samu nutsuwa, yana jin yadda yake sauke numfashi
da sauri. Sai da ya nutsu ya ce, “Muje kawai Daddy ka gani da idonka”.
Daddy ya ce, “Ba zai yiwu ba, baka ganin meeting muke yi”.
Ya ce, “To bari in jiraka a ofis dinka ka je ku gama”.
Ya ce, “Alright”.
Mintuna arba’in Dr. Mansur ya yi kamin ya dawo. Shi ya karbi tukin suka nufo Farm Center,
Ibraheem ya kame bakinsa ya yi shiru. Daddy ne ya bude gidan da kansa don Ibraheem
baya-baya yake yi.
Ya kama hannun Daddy zuwa bedroom din ya shiga nuna masa.
“Ka gani, ka gani....... akwai spirit a cikin gidan nan”.
Yana nuna masa kan mudubin, ya kuma ja shi ya kai shi toilet yana nuna masa su (Pad) har
da guntun sabulu dasu maclean din da aka yi amfani da rabi. Ga jakunkuna da takalma ga su
brazier, sannan ya ja shi kicin ya kai shi ya yi ta nuna masa, da gaske a rikice yake kamar
yadda ya ce dinne...... “He is perplexed.....”
Sai a lokacin Daddy ya soma fahimtar me ke faruwa, me Ibraheem ke son ganar da shi?
Dariya ce ta kulle masa ciki yana ta kokarin hadiyeta a cikinsa.
Ibraheem ya ce,
“Na taba tambayarka wace ce Jumah, ka nuna min wata tsohuwa. Ni kuma tabbas na yi
magana da wata yarinya mai suna Juma duk da na san sunan tsofaffi ne, amma wallahi Daddy
ni da (fresh girl) na yi magana. Ina jin aljana ke son aure na. I cannot live in this house
anymore...... sai ranar da Allah ya bani iyali........”

Yadda yake maganar ya bala’in baiwa Dr. Mansur tausayi. Ya ji wani abu ya motsa a
zuciyarsa, ya kamo Ibrahim ya jingina a jikinsa.
“Wace ce ita Juma din?”
“Nurse din ofishinka”.
“Ce maka ta yi a ofishina take? Yaushe akai hakan?”
Ibraheem ya ce, “Wayarka na kira ta dauka, bayan nan ma mun kara magana, har ta
tambaye ni wai don Allah nine Ibraheem? Kafin in ba ta amsa wayarta ta mutu. Kuma wallahi da
layinka Daddy”.
Sai a nan Daddy ya gano komai, ya tuna randa ya manta wayarsa a gidan. Ya gane
Rayhanah ce ta amsa mishi waya ta ce sunanta Juma, kuma ya ga received calls na Ibrahim
amma bai bi ta kansu ba.
Sai ya ce da Ibraheem,
“One minute...”.
Ya shigatoilet din Rayhana ya yi dariya ya koshi sannan ya fito. Ibraheem ya kulu ya
kumbura, don ya gane Daddy abin dariya ya dauki abin. Ganin yanayin da yaron ke ciki sai ya
zama serious.
“Kwantar da hankalinka Ibraheem...... ba wata ba ce mai suna Juman, RAYHANAH ce
MATARKA!!!”
******




Ya dago fararen idanunshi da sauri ya dubi mahaifinsa. Babu alamar wasa a tare da shi. Ya ci
gaba da cewa,
​“Ko da yake a da ne take matarka, amma na dade da yanke shawarar raba auren zan yi,
tunda baka yi na’am da zabina ba, ka mai dani ba komai ba a idanun Rayhanah da kakarta
Juma”.
Wannan karon da firgici ya dubi Daddy....... “Kakar tata ce Juman?”
Daddy ya daga kai. “Wannan kuma dakin da ta zauna ne shakara guda tana dakon auren
ka”.
Ya kara kallon Daddyn sosai,
“Me yasa ka yanke shawarar raba auren Daddy? Da bakina ban ce maka bana so ba”.
“Kana so ka wulakanta ni? Rimi-rimi muka yi magana, ka ce da amincewarka in aura maka
wadda zuciyata ta amince da ita, baka da zabi a auren fari.
Cikin girma da mutunci da bacin ran mutane masu yawa aka yi auren nan, na dauko yarinya
na kawo ta gidanka ni da Yaya Abdulkadir cikin mutunci da mutuntawa.
Tun daga ranar Ibraheem baka kara nemana ba, idan na neme ka baka amfani da layin.
Yarinya na ta hakuri har kakarta ta damu, ta nemi da a raba auren.
Amma Rayhanah ta zabi ta rabu da kakarta har abada ta ci gaba da dakon aurenka har
karshen rayuwarta. Koda har abada bazata ganka ba.
Ba don kai ba, ba don ta sanka ba, ba don tana sonka ba sai saboda darajata. Karewa ma da
Khalipha ne zai aure ta uwarku ta wargaza lamarin.

Wai ni mai DA, wanda nake da yakinin na isa da shi, kuma shi mai share min hawaye ne a
kowane lokaci na bukata, na baka auren Rayhanah don dama can kai na fi yiwa sha’awarta
saboda na san za ku zauna lafiya tunda halayya da dabi’unku daya.
Ibraheem da me na tsira a wannan gatan da na yi maka? Sai kunya da na sha da yake da
neman yadda zan yi in rage mata rayuwar kadaicin duk da bai dameta ba sai kakarta. Don haka
me ya yi zafi?
Rayhanah ba rasa mijin aure ta yi ba. Ban ba ta wannan damar bane, da ka ga dama ka zo
ko sau daya baka taba tambayata lafiyar matarka ba, kana jira sai na tallata maka ita. Na kasa
ta a fai-fai na ce Ibraheem dauki?
To ka yi kadan, uwarku ta yi kadan. Ungo wannan.......” Ya ciro takarda a gaban kwat dinsa ya
zaro biron dake makale jikinsa ya mika masa,
“Yankewa Rayhanah igiyar auren nan ko guda daya ce ta huta”.
Idanun Ibraheem suka cicciko da kwallah.
“Daddy kada mu yi haka...... kada mu yi haka...... saurareni ka ji uzirina tukunnah....”
“Zan saurare ka kadai bayan ka rubutawa Rayhanah saki ko guda daya. Wane uziri ke
gareka? Ni ka ga tafiyata, kada ka sake ka zo min gida in ba takardar Rayha ka kawo min ba,
babu gardin da zai zauna min a gida, ‘ya’yana sun girma kuma duk mata ne. A toh! Allah ya
bamu alkhairi”. Ya juya ya fita yana kara fadin,
“In ma aljanar ce za ta aure ka ku yi ta auren, kai ta ga ka yi mata, tunda tuzuru ne, sama da
shekara talatin babu mai kiranka saurayi, ba Khalipha mai iyali abin burgewa ba”.
******




Juyi yake a matsakaicin gadon, lullube cikin zanin atamfar Rayhanah. Sai yanzu ya gane
turaren ba wani bane ‘Makhmariyyah wa lamsa nectar’ ne wanda ake durawa a wani kanti a
Jiddah. Shima Sapna ce ta gaya masa wata rana yana rungume da ita yake tambayarta wane
irin turare ne mai sanyi da kwantar da hankali ta shafa a tufafinta haka? Me yasa take amfani da abubuwa irin na Sapna?Is it a coincidence or what? (Arashi ne ko
minene?) Ta san abubuwan da yasa yake son Sapna har da ire-iren wadannan abubuwan?
Gayun Sapna cool ne and cooly ba na tashin hankali ba. She's a designer baby.
Tukunna ma, wace ce Rayhanah? Shi fa ya san wannan sunan, amma ya manta inda ya san
shi. Ko Daddy zai tsire shi, ba zai taba yin sakin nan ba, ko ba don ji da ya yi ita ce Juman da ya
so a murya ba, sai wannan furuci da ta yi na cewa za ta jira shi da aurensa har abada saboda
Daddy. Koda har abada bazata ganshi ba. Ba don komai ba sai don cewa duk mai darajja
Daddy abin so ne da girmamawa a gare shi.
Shima zai koyawa zuciyarsa bajinta, zai sota zai zauna da ita har abada saboda Daddy ko da
a fili (a zahiri) ba ta yi masa ba. In yaso nan gaba sai ya je ya auro Sapna ya kara idan tana da
rakin da ba za ta iya dauke shi a shimfidarta ba.
Ya tara bukata mai yawa ga duk macen da tai kasadar aurensa, shekarunsa talatin da uku
bai taba sanin ‘ya mace ba. Ya killace kansa ne (insha Allahu) only ga matar aurensa, wadda

yake fatan ta zama itace tubalin iyalinsa.
Ya kuma yarda ya baiwa Rayhanah da bai sani ba wannan babban matsayin tunda zabin
Daddy ce. Addu’a yake har a fili Allah yasa RAYHANAH ba irin wadannan ‘yan lagwai-lagwai
din bane kamar tsada irin matar Yaya Khalipha.
Bakar mace yake so ‘yar’uwarsa fully Nigerian. Ba kyale-kyalen gashi da farar fata ba. Shi
kadai kuma ya koma yiwa kansa dariya duk da yana cikin tension din da Daddy ya hada masa
wai ya rubuta saki. Abin da ya ba shi dariyar shine tambayar da zuciyarsa ta yi masa.
“Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki? Tun ba a ga matar ba an ga kyau ko muninta, an
ga yankan bakinta har an fara kissima yadda ake son ta a shimfida? Man! Kwanciyar aure ba ita
ce kawai abin kissimawa a cikin aure ba, akwai wasu abubuwa masu muhimmanci ko da a ce
basu kaita muhimmanci ba, to suma suna da nasu. Shakuwa da juna, kusancin zuciya da zuciya, soyayya, tausayi da jin kai a tsakanin
ma’aurata, fahimtar juna, nuna kulawa da bakin cikin ko farin cikin juna, planning a kan tarbiyyar
‘ya’ya da yanayin yadda ta dauki addininta da yadda take gudanar da ibadarta.
Idan ta dauki nauyinka yadda kake so a shimfida, ta kuma rasa wadannan qualities din she’s
not enough wallahi auren ba zai dore ba.
Ga kuma kasancewar dan adam tara yake bai cika goma ba, da wuya a samu wadda ta hada
dukkan wadannan din, a wurin Ibraheem idan irin haka ta faru to saki ba shine solution ba.
Dubo wata wadda ba ta da wancan take da wannan ka hadasu, sai rayuwa ta fahimta da
soyayya ta dore. Tunanin Himu kenan har barci mai karfi ya dauke shi, mafarkin yadda zai ga
Rayhanah yake, saboda yasa abin a ransa.
*******








Da asubah bayan ya yi sallah a masallacin dake kusa da gidansa wajejen karfe shida na
safe, ya zauna ya shiryawa Daddy (text msg) na ban hakuri da neman afuwa. A ciki yace da
Daddyn
“Aurensa da Rayhanah na har ranar busa kaho ne. Ya yi hakuri ya yafe masa ba zai iya ko da
kwatanta abin da ya umarce shi ba, ya ba shi RAYHANAH....... akwai uzurin da ya janyo bai
neme shi a waya ba shima ya kasa samunsa.
​Ya rufe wayar ne kwata-kwata a dalilin jinya mai tsaho da ya yi a SanFrancisco, ya
tambayi Mami ita ai ya gaya mata. Ya kare da cewa,

“Daddy I’m sorry........ Luv u Dad!”

Shima fitowar shi kenan daga masallacin asibitin wayar dake aljihunsa ta sanar da shi
shigowar sakon. Ya dauko ya karanta, sai jikinsa ya yi sanyi. Amma bai ba shi amsa ba.

Mota ya dauka ya nufo gida da yake aikin kwana ya yi. A farfajiyar gidan ya cimma motar
Ibraheem, jikinsa ya kara yin sanyi da ya shigo falo ya ganshi zaune cikin kujera yatsunshi
goma cikin sumar kanshi kansa a sunkuye. Kayan jikinsa na barci ne.
Duk sallamar da Daddyn ya yi bai ji ba, ya yi nisa cikin tunani mai zurfi, kawai so yake ya ga
wannan Rayhanah da ta tokare masa a kahon zuci. Yasa hannu ya mikar da dansa tsaye,
sannan ya rungume shi.
“Jeka dauko passport ayi biza in sadaka ga Rayhaanah, amma don Allah Ibraheem ka rike
min Rayhana amana, domin amanar Allah ce a hannuna. Idan ba ta yi maka ba, ka bani ‘yata
kar ka wulakanta min ita yadda uwarku ta wulakantata......!!!”
Hannu ya kai ya toshe bakin Daddyn don ganin yana so ya tuno tsohon bacin ran da Mami ta
dasa mishi.
“Past is past Daddy........ just the present!”
Dacta Mansur ya girgiza kai, wato ya yarda da shi. Ibraheem a dan nauyaye da nauyin
harshe ya ce,
“A ina Rayhanah take?”
Daddy ya ce,
“Informatics - Singapore”.
Fiddo idon da Ibrahim ya yi ya baiwa Dr. Mansur dariya.
“Ita da wa Daddy? Da aurena?”
Daddy ya ce,
“Ita da budurwarka Juma, da kuke soyayya a waya”.
“Kasa tsage in shige!”.
In ji Ibraheem........ sai ya rufe fuskarsa da tafukansa. Wai ya ji kunya kenan. Dacta ya wuce
ciki yana dariyar Ibraheem.
Idan yana tare da Dr. Mansur (mahaifinsa) bai san sanda yake mai da kansa kamar yaron
goye ba. And the Dad likes it..... shi har gobe Ibrahim da Khalipha hangosu yake suna ‘yan
digwui-digwui a Al-Muntada da Al-Falah (Children Islamic Schools) a Birtaniya.
Sanda yake kama hannun daya, Asma’u ta kama daya su tsallaka titi. Su shigar dasu
makaranta.
Don haka shi har gobe yaran goye ne a idanunsa baya sakar musu ragamar rayuwarsu sai a
bisa hanya madaidaiciya, ba kuma takura musu yake ba, tsaka-tsaki. Ayi raha lokacin raha, ayi
discipline in sun karkace, sannan ayi musu abin da suke so
[12/26/2019, 21:08] Takori: *****


HADUWAR AMARYAR DA ANGON!

Cikin jirgin ‘Turkish Airlines’ da sukeciki, bairin tunanin da Ibraheem Mansur Takai bai yi ba,
ya gaza ko da kurbar dan jusin dake cike da kananan kankara da suka mishi a dan kofin su dan
kankani dake hannunshi.
Wace ce wannan Rayhanan? Ya take? Wace irin tarba za ta yi masa? Shima wace iri ya dace
ya yi mata? Zai so ta? Zai iya ba ta matsayin mata a gare shi? Zai iya hada rayuwarsa har
abada da yarinyar da bai sani ba bai taba gani ba? Bai taba yin wata mu’amala da ita ba balle

ya san kamanninta ko halayenta?
Tunaninnikan da suka addabi kwakwalwar Ibraheem kenan, yayin da a bangaren mahaifinsa
Dr. Mansur Takai, babu abin da ya dame shi, daga ya sha jus sai ya bude shafukan jaridar
‘Daily Tribune’ dake hannunsa, in yaso ya yafito ma’aikatan jirgin su zo su ba shi abinda yake
bukata da yake a first class seats suke. Lokaci-lokaci ya kan saci kallon Ibrahim ta gefen idonsa, sarai ya san tunaninnikan da ke
damunsa, amma bai ce masa komai ba, bai ma nuna ya san halin da yake ciki ba.
A lokacin da aka ba da order a daura belt jirgi zai sauka a ‘Changi-Airport’,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login