Showing 12001 words to 15000 words out of 23179 words

Chapter 5 - The Sexy Boss Book 3 Hausa Novel By Maman Teddy.pdf


Wani irin kallo ta watsa mashi ,idon ta na ciko da ƙwallah , sai hawaye sharrrrrr³ , ganin yanda
Take xubda hawayen taana sauke ajiyar zuciya , wannan ya nunar she shi ,ko a juya tayi kuka
har ta gode Allah. Ya Umair Me yasa ba zaka sauya ba? Abun da take faɗi kenan a zuciyar ta a
sarari kuma jifan shi take da kallon dake nuna tsantsan tsana da ƙiyayyya . Ina Son ki ,kuma
kema dole ki Soni.! Yayi maganan yana takowa zuwa inda take . Wannan shine maganan da
kayi mun tun da fari . Amma kuma kai yaci ace ka ƙaryata kan ka ,tun da ba na Son Ka har
yanzu . Kallon ta yayi yana sa hannayen sa biyu tare da tallabo kuncin ta ,idon ta ya ƙura ma
ido yana kallon ta .kamin yace " Ƙarya kike ga So na nan ina gani a idon ki .! Umaima kina

Sona, Bama So kaɗai ba...Fuzgar kan ta tayi daga garesa tana cewa " A haka zan So ka? Ka
kasance mazinaci, Mashayi , wanda har duniya an yi maka shaidar Shaye² .na haɗa zuri'a da
kai me ƴaƴan da zamu haifa idan suka tashi zamu ce masu ?. Nan da nan fa.....maganan nata
ne ya sarƙe tana sakin kuka tare da sa taffan ta tana rufe bakin ta . Sorry Yah Umair , baxan
Zauna da kai ba . Ban san mene zan faɗawa yara na ,baxaka sauya ba . Ba zaka daina
abubuwan da kake yi ba . Nan a gidan muna zaune da Momy muke gani a news ake watsa
labaran ka , na tayatar da ka amsa a ƙwalɓe , da kuma lalata sunan Ƴan uwan ka likitoci ... Ni
dai a'a ya Umair ka sauya tukuna .


Jah baya yayi yana kallon yanda take xubda hawaye , a hankali yake motsa hannun sa , Jikin
sa gaba ɗaya yayi sanyi , a Rayuwar sa abu ɗaya ya tsana shine ya bude ido yaga Umaima a
cikin wannan hali ... Umaima wannan wani irin magana kike ? Hajiya Turai tayi maganan cike da
rashin jin dadin maganganun ta , a ganin ta kar Umair ya fusata abubuwa su dagule .

Kamin Umaima tayi magana ne , ta ji Muryar Umair yana cewa " Momy zanyi magana da
matata. Saurin ware idanun ta Umaima tayi ,Kana tace " Me kake nufi to??. Kamin yyi magana
ne Hajiya Turai tayi saurin cewa ' A'a bari na baku wuri . Momy babu inda zaki je , Kasan
wacece wannan kuwa?. Na sani , yayi maganan yana kallon idanun ta . Haɗa ido sukayi nan ya
daga mata gira yana cewa " Yass nasani Yayar Umman ki ce ,wacce take uwa gare ki. To ka
sani kake wannan maganganun ? To babu inda zata je . A'a bari dai na fita. Cikin Muryar Kuka
Umaima ne ta kuma kwatse shi da cewa " A'a Momy babu inda zaki . Kamin ta rufe baki ita dai
taji ya rungume ta ne yana haɗe bakin sa da nata , wani irin hot kissing yakeyi mata , wanda
jikin Umaima ne ya hau rawa so take ta ƙwace kan ta daga gare shi ,amma ya rungume ta
ƙammm a tare da shi . Juyawa Hajiya Turai tayi da sauri tana fichewa daga ɗakin. Tafe take
tana sambatun da bata sani ba tana cewa ' Oh Ni Turai Ni naga Zamani?? Shi yasa yace na
basu wuri , wannan tacewa da mai yayi kama???. Naam Hajiya magana kike yi?? Muryar ƴar
Aikin ta taji ,wannan yasata farga ashe a sarari take maganan . A'a zubaida ba dake nake ba.
Wuce yar aikin tayi cikin sauri tana nufa falon ta. Itako Zubaida da ido ta rakata a zuciyar ta tana
cewa " Yau Hajiya Lafiya kuwa ?.



Kusan mintuna biyu da sakanni suka ɗebe yana tsotsan bakin ta ,kana ya shagala ƙwarai ya
saki jikin sa a natse yana Kissing ɗin labɓan ta tayi saurin janye kan ta tana yin baya , tare da
cewa " A'a Umair... Shiiiii yayi saurin sa yatsar sa a laɓban ta ,hannun sa ɗaya ya riƙo nata , bin
sa da kallo take tare da cigaba da xubda hawaye . A hankali taga ya sa gwiwowin sa a ƙasa
yana kallon ta cikin Muryar karaya da ladabtawa tamkar yana gaban na gaba dashi .Umaima
faɗa mun abubuwan da kike so na daina daga yau nayi miki alƙawarin dai nasu. Na bar shan
barasa ,na bar shan sigari ,haka na daina Sex da kowacce mace sai ke kadai mata na... faɗa
mun abubuwan da kike kuma son na daina yin su zan daina badon komai ba saboda ke...!

Aƙwai supliment masu ƙyau da inganci babu illa ,muna sayar da na breast da kuma na hip up.
Aƙwai na ƙiba , da kuma na hasken fata mai ƙyau ba na bliching ba. Ga masu buƙatar ƙarin
bayani You can chart me up .

*MMN TEDDY*
*08081202932*
*Littafin the sexxy boss na kuɗi ,duk wanda ya karanta bai biyani ba ALLAH ya isa.! Regular
group₦300... VIP group₦500...SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank
ko ki turo da MTN card ta wannan Numbobi 08081202932*




***



_Kuyi manage da posting yau , wallahi mun koma school ,next week kuma zamu yi resuming
work, kunga yanzu sai kuna haƙuri da posting babu yawa,Amma a hakan zan rinƙa ƙoƙarin yi
mana sau biyu , ko zuwa can dare zana rinƙa maku night update in Sha ALLAH.!_


"Kallon sa Umaima ta tsaya yi kaman maitantaman wani abu na daban kamin cikin sanyin
murya tace " Ni ai ba tawa rayuwar ka gyara ba naka ne?. Idan ka daina duk abubuwan da ka
faɗi zaka daina alhmdllh shine Abun da zana ce. A matsayin ki nawa kenan a guri na? Yayi
maganan yana zuba mata lulun idanun sa . Shiru tayi tana murza ƴan yatsun ta kana daga
bisani tace" Ai ni kasan daiii...Pls Umaima ki yafe mun , wallahi tun bayan rabuwa na dake na
daina mu'amala da kowacce ƴa mace. Kawai dai abun da nasan ina cigaba da aika tawa shine
shan barasa na . Kuma daga yau na daina . Bana komai yanzu ki sa na bar wannan duk abun
da kika san ina yi. Pls Umaima ki zauna dani Muyi rayuwa mu haife yaran mu masu kama
dake. Kunya ne ya kamata saurin ƙasa tayi da idanun ta da kallon sa tana murmushi , hannun
ta ya kama yana miƙewa daga tgurfanan da yayi gaban ta . Murmushi shima yake wanda rabon
da yayi irin wannan sanyayyar murmushi ya manta . Kallon sa tayi cikin sauri tana zame hannun
ta , tare da cewa " Kar Momy ta shigo ta gan mu ...Aaa ke ba mata na bace ba? Ai wuri ta
bamu. Saurin fiddo da idanun ta tayi waje na mmkin tare da jin nauyin furucin nasa ,kana ta juya
da sauri tana ficewa daga Bedroom din . Murmushi Umair yayi yana sa hannayen sa sama tare
da godiya ga ALLAH da ya nuna masa mafarkin sa a zahiri , hamdala yayi yana biyo bayan ta .
A dirning Area ya tadda Hajiya Turai da Umaima da ta amshe ta aikin tana taya ta hidimar haɗin
karin kumallo .


A'a Umair Har ka fito?. Hajiya Turai tayi maganan cike da fara'a . Saurin kallon Ta Umaima tayi

kana ta juya suna haɗa ido da Umair . Ɗaga mata gira yayi yana murmushi ,bai damu da Hajiya
Turai dake gaban sa ba. Saurin kauda kan ta Umaima tayi tana cigaba da gyara zaman wani
babban bowl dake akan Dirning table ɗin . Hajiya Turai ne ta cigaba da cewa " Ai baka tafi ba ,
don yanzu nake haɗa maka break nasan bakayi ba a gida ka fito . Murmushi yayi yana cewa '
Momy sauri nake yi yanzu haka zan wuce Lagos ne wani aikin ujula ya kamani ,shi yasa nazo
nayi sallama da Matana . Eyyaaa kuma bata faɗa mun wai tafiya zaka yi ba. Cewan Hajiya
Turai tana juyawa tare da kallon Umaima da itama batasan wai tafiya zaiyi zuwa wani wurin ba
.


Murmushi yayi har hushiryar sa na bayyana kana yace "itama ai taki tsayawa ta saurari abun da
ya kawo Ni ,guduwa ma tayi ta bar Ni kaɗai . Murmushin yaƙe Hajiya Turai tayi kana tace " To ai
shikenan Allah ya kaiku lafiya . Ammm Momy don ALLAH kimun wani ƙoƙari mana kamin dawo.
Kallon Sa Hjy Turai tayi cike da mmkin yanda ya tausasa lafazin sa kana tace " Ƙoƙarin mene
ne Umair??.


Don ALLAH Momy kisan yanda za'a yi kamin na dawo a maida Umaima gida na , Ni nayi
magana da Ammie ko a gida na nan Abuja zan zauna na hakura da zaman Lagos ɗin . Ki
shawo kan Daddy ya amince . Murmushi Hajiya Turai tayi tana ƙara faɗaɗa Fara'a kana tace "
In Sha Allah Umair zaka dawo ,ko Umaima bata tare ba ,tana gab. Thknyou . Yayi maganan
tare da Kallon gyefen da Umaima take ita dai tayi shiru tana faɗawa tunanin rayuwar su idan ya
kasance daga ita sai Umair ɗin ..wani irin gwagwatuwa zatayi a hannun sa .


Zo ki mun rakiya.! Taji Muryar sa ya katse ta , amm...Tsayawa tayi tana kame kame don tana
tsoron bin sa , bata san me kuma zai mata a farfajiyar gidan ba a gaban ma'aikata , don bai ji
kunyar Hajiya Turai ba , inaga kuma sauran ma'aikata da baya ganin su a bakin bakin komai .
Hajiya Turai ne ta katse su da cewa " Aaaa Umaima raka sa mana ? Mijin ki kuma zai wuce kin
kasa masa Rakiya . Ɗago da idanun ta tayi kawai sai ƙwallah ya ciko idanun ta suna dab da
zubowa . Saurin cewa Umair yayi " A'a mom ta bar shi kawai sai na dawo.! Yana maganan ya
fice daga falon . Bin ta da Kallo Hajiya Turai tayi ,kamin tace " Meke damunki ne Umaima??.
Shiru Umaima tayi tana sada kan ta ƙasa ,tare da cewa " Ba komai . Ohk kina ji ,nasan ba Son
Umair kike ba , ki sa a Ranki zaman da zaki yi dashi na ɗan lokaci ne ba mai ɗorewa ba Kinji
Baby na.! Murmushi Umaima tayi tana jan kujera tare da cewa " Mom Bara na fara breakfast .
Alright . Abun da Hajiya Turai tace kenan tana juyawa tare da nufar Kitchen. cookies Ta fara
kaiwa bakin ta , amma sam bata jin daɗin abincin nata ,wannan yasa Umaima turewa gyefe
tana ɗaukar tea cup tare da sa spoon tana juyawa , shiru tayi tana tunanin abubuwa da yawa
dangane da Hajiya Turai akan Umair . Me yasa Momy bata Son Ya Umair da alheri? Me yayi
mata ne?? Dole ina Son sani. Sauke ajiyar zuciya tayi tare da kai cup din bakin ta tana shan tea
ɗin kaɗan tare da saukewa . Tun da na sauya Ya Umair itama in Sha ALLAH zan sauya Momy
ta koma tamkar sauran iyaye mata masu fatan alheri da kowa , bazan iya cutar da Umair ba ,
Saboda Ni kaina nasan ina Son sa a zuciya ta ,tun ban san So ba nake Son ya Umair , har

daga ƙarshe na yarda da cewa Zuciyata ta kamu da Son Umair . ALHMDLLH da sauyin da
Allah yayi mun ina sake godiya. Wayar ta ce tayi ƙara dubawa tayi kirar Fa'iza ne kusan sau
goma sha Ciki har dana Fahad.


Mikewa Tayi daga dirning Area tana nufar Bedroom din ta . A hankali ta fara shafa wayar nata
tare da fara kirar Numbern Fa'iza . ringing ɗaya biyu ta ɗauka . Umaima kina ina ne??? Me ya
faru?? Umaima ta katse ta da wannan tambayar . Tun jiya Fahad yake neman ki da mutanen sa
har gidan mu sun zo . Yanzu dai haka in taƙaice maki Yana hanyar zuwa Abuja ,wai zai kira ki
idan ya iso.! Ƙirjin Umaima ne ya buga dam... shi Fahad ɗin ? Eh mana.!



*ANTY MMN TEDDY*
Tun da Umaima tayi shiru bata kuma cewa komai ba sai Fa'iza ce dake ta faɗin " Hello kina jina
Umaima...Shurun da taji ne yasa ta katse kirar yayin da ita Kuma Umaima ta Juya tana jefar da
Wayar Ɓarayi guda . Dafe kan ta tayi gami da kuncin ta tana maganganun sa dana Sauran
Abokanan sa na dawo mata " Wannan da kuke gani Budurwar Fahad ce a wannan makarantan
kar wanda yayi kuskuren... Umaima..! Muryar Hajiya Turai ne ya katse ta , wanda bata san ma
ta shigo ba , gigif tayi tana buɗe idanun ta tare da amsa ta da" Na'am . Kallon ta tayi tana ƙare
mata kallo baki ɗaya kana tace " Kina lafiya kuwa?. Murmushin yaƙe Umaima tayi mata don ta
nuna mata babu komai nan tace " Momy komai lafiya , Waya muka gama yi yanzu da Fa'iza
,tayi mun maganan school shine hankali na ya karkata gare ta . Shiru Hajiya Turai tayi kamin ta
dafa Umaima tana cewa " Kin san dai me Umair yace dake ko??. Maganan makarantar nan a
barta , saboda Umair juyayye ne . Kallon Hajiya Turai Umaima tayi cikin ɗan damuwa Umaima
tace " To Momy kuɗin da Kuka kashe mun fa ? Duka a barshi ?? . Eh ki barshi ... To shikenan
Momy . Amma ina Son Na je gida na gaida su Umma na. Ai wannan me sauƙi ne . Ki kirya ina
so Anjima kaɗan ki raka Ni ,zanje mall Nayi siyayya na dawo . To Umaima tace da ita kamin
Hajiya Turai ta fice ita kuma tana komawa tare da bin lafiyar gadon tana ƙwantawa a hankali
tare da tunanin abubuwa , ita dai har ga ALLAH bata jin Zata iya rabuwa da karatun ta akan
zancen Umair. Wannan ma fa ɗan rainin hankali ne , ban da rainin wayo da tunani har ya manta
abubuwan da yayi mun a baya tun yanzu ya fara sharaɗɗa mun wasu zancen wofi ?. Taɓ to
yanzu ina ga yaganni a cikin gidan sa abin ai sai inda ya kai kuma.
***

Kaman yanda Umaima tace zata taho gida , hakan ya faru , a tunanin Hajiya Turai gidan ne
kawai a zuciyar ta , bata san zuciyar ta tunanin makaranta bane. Don tana komawa A washe
gari ta shirya tsaf tayi na makaranta . Rayuwarta kawai take yi , don ita sam ta fara mantawa da
Umair a ƙwana biyu ,sai dai wani abu ɗaya da yake sakata tunawa dashi shine ,duk idan Fahad
yazo gareta ko ya jata zuwa wani wuri babu wanda take tunawa face Umair , a haka ta cigaba
da rayuwar ta . Wanda duk shige da ficen ta har dawowan ta Umair ya sani . Bai tada hankalin
sa ba ,sai da yaji labarin Fahad. Wannan yasa shi kirar Ammie Hankali tashe yana tambayar ta
da izinin waye Umaima ta koma Makaranta??. Ammie da taji abun nashi yayi ƙamari ne yasa ta

cewa " Au Har Makarantar ka kashe mata ne Tun yanzu yanzu ??. Sai a sannnan ya tuna da
basu yi maganan da ita ba , wannan yasa shi datse kirar cikin sauri yana kirar Hajiya Turai .


Salallami Hajiya Turai ta ɗauyi tana faɗin Umaima ce ta koma makarantar?? Bari zan kirata
yanzu . Gida fa tace zata koma ,tana Son ganin Umman ta. No Mom Kar ki kirata Bari zan
dawo.! Zaaakk kamin Hajiya Turai tayi maganan ne taji ya katse kirar . Cikin sauri ta fara
lalaubar lambar Umaima amma baya shiga . Kaiwa da komowa take tana faɗin " Umaima wai
me take nema da zafi ne akan wannan karatun nata?? (Kuji mun Rainin hankali ma) .Haka
Ta cigaba da kirayen wayann ta amma amsan daya ne Wato Is not reachable at the moment .

***

Fa'iza ce ta taɓo Umaima tana ce mata a hankali " Fahad ya shigo . Saurin ɗagowa daga
rubutun da take yi tayi , tana kallon Fahad da yake kurɗaawa ya iso har zuwa inda take , ba tare
da yayi duba ga lecturer ɗin tasu ba.


A gaban su ya tsaya yana kallon Umaima wacce itama shi take kallo . Yau me ake maku? .
Kallon Fa'iza tayi kamin tayi masa magana yana juya yana kallon Whiteboard din da lecturer Ke
gyefe . Ohk taso mu tafi sai na koya maki . Miƙewa Umaima tayi tana kallon ɗaliban da lecturer
a ido ido ,amma da mamakin ta sai ji tayi lecturer tace " Dr Fahad Hala dai wannan itace Surikar
shiyasa kake cika zaƙewa da yawa?. Dariya Ɗaliban suka yi har da shima Fahad ɗin kana ya
rike da jakar Umaima suka fuche daga hall ɗin . Mayafin Abayar ta ta gyara tana kallon gyefen
ta , wani irin yanayi ne taji ya kamata , tsoro ne ko meye taji yana kai kawo a zuciyar ta . Bin filin
wurin tayi da kallo , ganin motoci ne wanda dama suka zama ana aje su a wurin don gaban hall
ɗin tasu fili ne sosai da ake aje kowani irin abun hawa .ji tayi gaban ta na faɗi. Wanda ya sata ja
ta tsaya . Saurin kallon ta Fahad yayi tare da cewa " Menene?? Meke faruwa??. Cikin rawar
murya ta kalle shi tana cewa" Ina ji a jiki na kamar Ya Umair yana wurin nan??. Kallon ta yayi
kamin yace " Waye shi??...Kamin ta bashi amsa ne taji Ƙamshin sa ya durar ma ko ina na wurin
. Can ɗan nesa ta kalla , ganin sa tayi ya fito daga cikin moton sa , wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login