Showing 15001 words to 18000 words out of 23179 words

Chapter 6 - The Sexy Boss Book 3 Hausa Novel By Maman Teddy.pdf

guard É—in sa ne ya biyo
bayan sa , ammma sai kuma taga ya ja ya tsaya , shi Kadai Umair É—in na takowa zuwa inda
suke . Jikin ta ne ya hau rawa karrr³ , hannun ta tasa tana ƙoƙarin Amsan jakarta , amma sai
Fahad ya riƙe jakar yana mata wani irin kallo na rashin fahimta .

Ƙari kowa zuwa inda suke Umair yayi ba tare da ya sauke bakar gilashin sa ba , fuskar sa a
murtike take haka girar sa da yake a haÉ—e , sam baya tsammanin zai iya duba da inda Fahad
yake tsaye , wanda ko ba'a ce masa ba ,yasan shine wanda Umaima take kokarin hada
soyayyar shi da nata . Taho mu tafi.! Shine Abun da Umair yace da ita yana miƙa mata hannun
sa . Idon ta na ya raina fata ganin Yanda Fahad duk da ya san waye Umair a kallon Farko
,yasan matsayin sa a yau Nigeria ,amma kun san So me sanya ido ya makance ka faÉ—a ko wani
halaka , cikin wani irin murya yace " Me yasa zata bika ? Kaine wane??.

Wani irin murmushi Umair yayi yana kallon Fahad kana ya juya yana kallon Umaima dake ce
masa" Yaya na ne??. Taho mu wuce.! Kallon Fahad yayi kamin yace " To duk wannan ɓarin jikin
na mene? Kawai saboda ya kasance Yayan ki??. Kiiiiii...! Umair ya daka masu uban tsawa .
Wanda yasa Umaima saurin rabuwa da Fahad tana barin masa jakar ta nufo inda Umair yake ,
Hannun sa ta rike Muryar ta na rawa tace " Yi haƙuri muje don ALLAH. Wani irin kallo yabi
Fahad dashi kana ya riƙe hannun Umaima da ta riƙe gammm don tsoron abin da zai iya biyo
baya . Saurin nufar motocin sa tayi . Yayin da securities din sa suka yi saurin buÉ—e masa moton
Umaima ne ta fara shigewa kana ya shigo .


Hankalin Umaima gaba É—aya ya gama tashi , hawaye ne suka fara zubo mata , kawai sai ta fara
kuka a hankali tana kauda kan ta izuwa kallon ɓarayin window side . Duk da ransa a ɓace yake
amma kukan ta ji yake na fi komai taba masa zuciya . Laptop É—in da yake operating don har
yasa a binciko masa waye Fahad ? Waye uban sa? baya Son sanin meye tsakanin sa da
Umaima?? Don shi ba ma kawo kmane ya Gani da idanun sa . Rufe Laptop din Yayi yana sa
hannun sa tare da rungumo ta jikin sa . Sam bata ki ba , don gaba É—aya hankalin ta da natsuwar
ta ta rasa shi a lokaci guda . Shafa bayan ta yake a hankali alamun rarrashi duk da shima baiƙi
ya samu mai rarrashin zuciyar tasa ba a halin yanzu . Sorry I'm verry Sorry dear , Na taɓa maki
bugun zuciyar ki , na raba ku a lokacin da baki So ba ko??. Saurin É—agowa tayi tana kallon sa ,
sai kuma ta kauda kan ta zuwa ƙasa tana kallon dogayen yatsun sa . Hannun ta tasa tana
É—aurawa saman nasa tare da kamasu tana haÉ—ewa da nata , Wasu marayun hawaye ne suka
fara sauko ma kuncin ta wanda suka fi na baya , a hankali ta buÉ—e baki zata masa magana
,Amma sai zame hannun sa ɗaya yayi yana daurawa a saman laɓɓan sa . alamun baya Son jin
wani Magana daga gare ta. Tsayawa tayi tana kallon sa na yan daƙiƙu yayin da shi kuma ya
juya kan sa gyefe yana kauda kallon sa daga gareta .


Sakin kuka tayi a hankali , gani tayi ya juye mata ,ya koma mata tamkar ranan da ta fara ganin
sa a rayuwar ta .

Ƙara rushewa tayi da wani irin kuka tare da juya kan ta itama gyefe tana fara tunanin rayuwar ta
da Umair a yanzu?? Tabbas tasan zaman gidan sa dole? Amma kuma bata san da wani irin
salo a yanzu zasuyi rayuwar tasu ba . Momy don ALLAH ki fahimce Ni a rabani da Ya Umair
wallahi mugu ne.! Juyowa yayi yana kallon ta , wanda ya sata saurin rufe bakin ta don maganan
Zuci ne ya fito sarari ba tare da ta sani ba ... Hawaye ne ya cigaba da ƙwaranya mata . Tana
kallon sa yayin da shima ita yake kallo , kallo É—aya yayi mata ya fahimci duk wani abu dake cikin
zuciyar ta . Tsoron ƙwana dani kike?? Ko kuwa tsoron Sex dani kike? This time around , Komai
nawa kisani ya sha banban da ta da . Ki shirya amsan ko wani irin hukunci daga gare Ni . Kin
san meye?? Kamin na taho nan , Wurin Baba na fara zuwa , Kar ki tunanin guduwa ta ko wani
Faraga ba zaki samu dama ba, Kin san meya sa?? Hajiya Turai.! Wani irin kallo Umaima take
masa , me take So dake dani?? Bana ce ba , don bazance ban san komai ba , na sani...!!!!
Saurin girgiza kan ta Umaima tayi wasu irin hawaye na mata ambaliya , A'a Ya Umair babu

....ba babu Komai .! Motsa bakin sa yana alamu zayyi magana kawai sai yaji tasa hannun ta
duka cikin ruÉ—ewa da tashin hankali ta faÉ—a jikin sa tana rufe bakin nasa , kuka take sosai har
idon ta na kumbura saboda zuban ƙwallah ...!




*Littafin the sexy boss na kudi ne , don ALLAH kar ki karanta idan baki biya Ni ba.. Regular
group₦300 vip group₦300 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko
katin MTN ta wannan Numbobi 08081202932*
*Littafin THE SEXXY BOSS na kudi ne , Regular group ₦300 VIP group₦500 SPC ₦1000 via
6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko MTN card ta wannan number 08081202932*


Yanda yake take kukan ne yayi matuƙar karya masa zuciya ,duk da dama Soyayyar nata ta
samu gurmi ta musamman a zuciyar ta ,hannun sa yasa yana ƙara haɗawa da nata a hankali ya
furta " Ba haka bane Umaima? Ai haka yake , Ni nasani ko baki faÉ—a mun ba, nasan Momy
Tana Son Aure na dake ne saboda ta cimma wani buri nata , sannan matsalar ma abun dake
daÉ—a sa ma zuciya ta damuwa shine ke.! Yayi maganan yana lumshe lulun idanun sa tare da
cijan laɓɓan sa na ƙasa . Cike da wauta Umaima ta riƙe hannun sa , Ya Umair kayi haƙuri ,
Momy zata sauya , amma wallahi a karon farkon nan dana taho gidan ka ba ita ta turo Ni ba ,
Kawai Ni ne nazo kaji Yah Umair...ware manyan idanun sa yayi yana zuba su akan fuskar ta
kana yace " Kinji matsalar, Umaima kece.., Baki taɓa ce mun kina Sona ba , ko alama kin san
ya zuciya ta take ji kuwa?? Sauƙin ta ɗaya idan na kalli cikin idanun ki anan kaɗai nake ganin
Soyayayya ta , ga shi nan , anan ne kaɗai Bakya iya ɓoyemun . Sada kan ta ƙasa tayi tana yin
shiru , jin Muryar sa tayi yana cewa " FaÉ—i mun duk abun dake kike so ,Zana baki Umaima ,
KuÉ—i??? Kallon shi tayi saurin yi , a zuciyar ta tana cewa" oho a inda ya aje Ni kenan,so kuÉ—i tun
da sanadin kudi komai ya faru tsakani na dashi . I love You ,ina Son naga na kasance dake har
abadan abada . Faɗa mun ko nawa ne zan baki tun daga kan dala biliyan zuwa sama . Ƙurrr
yaga tayi masa da ido , tana kallon shi ƙwallah na taruwa a saman ƙwarmin idon ta .


Girar sa ya gyara mata ,alamun ita yake sauraro . Shi dai Umair baiyi aune ba yaji Taji Dunkule
hannun ta ne tana haɗa yatsun ta tare da bugun cikin sa . Ashhh. Ya saki ƙara don yaji zafin
bugun nata . Dari ya ta sheƙe dashi tana yin baya , har da kama ƙwallah na mugun ta . I luv
you.! Ya furta yana kallon ta , kallon idanun sa tayi kana ta saki murmushi tana cewa " Dama
ashe Soja yana jin zafi idan an bige sa??. kamin yayi magana ne ta kuma cewa " Ina Son zama
dakai Ya Umair, Ka san menene?? Shiru yayi mata bai ce mata komai ba sai dai idanun sa dake
akan ta ,alamun yana sauraren ta . Ƙwallah ne ya fara gangaro mata , hannun ta tasa tana
gogewa kamin ta motsa laɓɓan ta tana mai cewa "Aduk lokacin dana zauna Ni kaɗai bana
tunawa da kai a zuciyata . Amma a duk lokacin da wani É—a namiji yayi rabe Ni ,sai naji wutar
Soyayyar ka a zuciyata. A da baya na É—auka Wauta ce , kuma nayi kokarin hana zuciya ta
faɗawa soyayyar ka ,amma ta gagara . Ina Son ka ya Umair...Ta ƙare maganan tana riƙo

hannun sa . Hannun sa ya ware mata alamun taje garesa . Da sauri ta faÉ—a jikin sa tana jan
shashsheƙa . Ina ji kaman Soyayya ta tafi taka?. Hannun sa yasa yana rufe bakin ta , kamin
yace " Kar ki ƙara faɗin haka ba daidai bane , Ni dana zabi na bar komai na sa boda ke , na
daina Kula kowacce mace ,amma ke Baga shi ba.

Shiru yayi da faÉ—in maganan don ji yayi zuciyar tasa na masa wani irin harbawa tuno da Fahad.
Ɗago da kan ta tayi ba tare da ta tashi da jikin sa ba tace " Amma fa har yanzu Ban haƙura da
kyeta mun mutunci na da kayi ba ,babu imani bare tausaya wa . I'm verry Sorry dear . Maƙale
kafaÉ—a Tayi tana mai da kanta tare da lafewa jikin sa . A haka sam ta mance da wai a mota take
, don mota ne suke cikin ta wanda ta amshi sunan ta , baka ko jin hayaniyar sauran abun hawa
,yanda kasan tana inner room din ta . Tafiya ce mai tsawo suke yi , wanda ganin ba zai iya
komawa Abuja a mota ba yasa shi sawa a taho masa da jirgin yawo Helikwafta .


Ji tayi yana taɓa fuskar ta a hankali yana maida ita tare da ƙwantar da ita . Saurin buɗe ido tayi
tana kallon gyefen da gyefen ta , wanda taga pilot Yana ƙoƙarin tada jirgin . Har ya dauke ta
daga moton bata sani ba don barci ya É—auke ta a jikin sa. Saurin kallon sa tayi cike da mamaki
tace " Yah Umair Ina Zamu je?? . Ta ƙare maganan tana kuma juyawa tare da ganin Jirgin na
sama dasu . Juyowan da zata yi da fuskar ta ne ya haÉ—e da nashi , haÉ—e bakin shi yayi da nata
yana tsotsan harshen ta a sukune yana sa hannun sa tare da shafa gadon bayan ta , kasa
motsi tayi don ji tayi gaba daya ya sakar mata da duk wani laka nata . Kusan mintuna biyar suka
debe a haka kana ya zare bakin sa daga nata tana jan dogon ajiyar zuciya tare da sauke
numfashi a hankali . Murmushi ya sakar mata wanda har hushiryar sa na bayyana kana cikin
Muryar sa ta ingarman namji soja tsayayye , ya furta " Abuja nan da 1 hour Zamu sauka . Cox
naga kinyi gaji da yawa. Bin sa tayi da kallo , cike da mmki kana ta komawa ta kwanta tana yin
shiru , first a Rayuwar ta na duniya wai yau itace a jirgi . Ohh Umaimatuwa kenan😂 .

Kusan 50mins taji jirgin na ƙasa a hankali har ya ida sauka ,wannan ya alamta mata cewan sun
fa iso . Hannun ta ya kama yana kallon ta cikin murya mai kama da rarrashi yace " Zaki iya
sauka? Ko na...a'a zan iya ,ta katse shi cikin sauri tana miƙewa tashi daga jikin shi . A hankali ta
sauko shima yana bin bayan ta . Hannun sa yasa yana rungumo ƙugunta tare da manna ta da
jikin shi , kallon sa tayi tana Son raba jikin ta da nashi ,ganin ta a wani gida na daban ,ga kuma
securities da sauran masu tsaron gidan da bata san ina ne ba . Ji tayi duk a takure rungume tan
da yayi da jikin sa . Shi kam bai ganin yayi wani abu . Nufar wani apartment suka yi , wanda sai
a sannan a hankali cikin sanyin Muryar ta tace " Ya Umair ina ne nan? Ai ba gidan Daddy bane
nan . Hannun sa yasa yana kama subu subun kumatun ta ,yana murmushi tare da cewa " Calm
down my Swt Ccbr . Wani kallo ta watsa masa na ita yake zolaya . Dariya yayi yana cewa" Our
Swt House . Nan zamuyu rayuwa Ni dake , with ur kids , nasan they will come verry soon
inshallah . Murmushi Tayi cike da jin kunya tayi kasa da kan ta ,don taga yana mata kallon kasa
kasa. Wanda duk sai taji yarrrr. Nufan Wani falo Sukayi da babu komai sai glsses da suka
kewaye ko ina . Gani tayi kamin su karasa basu danna ko ina ba wurin ya bude kaman hanyar
kofa , suna shiga ya koma ya rufe , Ohhh wato da Ƙamshin jikin mutane yake aiki kenan.?

Kallon ta Umair yayi kamin yace " Me kika ce??. Saurin dawara tayi don bata san maganan ciki
ya fito sarari ba ,tace " A'a ban ce komai ba. Ohk taho mu shiga daga ciki yayi maganan yana
kai hannun sa gareta . Saurin ja baya tayi tare da cewa " A'a Su Ammie fa basu san zaka kawo
Ni ba. Huuuuu Sauke numfashi yayi tare da furxarwa yana kai hannun sa tare da shafa sumar
kan sa.. tun da sun hana Ni mata na ,basai na kawo ki nan muyi amarcin kwana É—aya ba ,idan
kin koma sun gan ki da juna biyu sai Kice nawa ne sai su dawo mun dake dole ,daganan mu tafi
honey moon da suka.....Ya Umair.!!! Ta kira sunan sa cikin tsoro da É—aga murya na mamakin
furucin sa gare ta ........





*MMN TEDDY*
*Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne , Regular group₦300 VIP group ₦500 SPC ₦1000 via
6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,ko katin MTN ta wannan number
08081202932...idan kuma ki ka karanta baki biyani ba keda ALLAH*


Tare da ja baya kaman taga Abun tsoro , A hankali ta furta " Don Allah Ya Umair ka maidani
gidan Daddy , Don Allah na roƙeka Pls ya Umair. Yanda tayi maganan ya kusa saka sa dariya
amma sai ya mai da dariyar sa ciki yana mata kallon da ta rasa gane manufar sa . Kinji fa Wai
Yaya...Ni kike kira Da Yaya a matsayi na na mijin ki , Kina ji Pls Mah wife ki bani dama just na
kwana ɗaya , zan miki wani Abu mai daɗi da aƙwana ɗaya zaki sauya mun wannan sunan da
kike kirana irin yanda su Fareesat ke kirana dashi kema a matsayin na Matana ace kina kira na
dashi?? Kai kaiii ina ina ina??? Ya maimaita maganan kusan sau uku . Cikin sauri cike da
tsoron sa kar yayi mata abun da take tsoro tayi saurin matsawa kusa dashi tana cewa " Zan
sauya To , Wallahi zan sauya faÉ—a mun wani Sunan kake So ,Amma Ni dai don Allah ka
maidani gida Ya Umair ". Shikenan ta maimaita ". Yayi maganan tare da kallon Gyefen Window
Glass É—in dake Kusa dashi. Kwana Biyu zamuyi ina koyar dake daga bisani sai na dauke ki na
maida ki wurin Su Momy ya ƙare maganan tare da juyawa yana shirin tafiya , da gudu ta bi
bayan sa tana sa hannun ta tare da maƙalewa a bayan sa tana sa hannayen ta duka biyun tana
rungume sa ƙaammm , Cak ya ja ya tsaya ji yayi wani abu mai kamar shocking na kama tun
daga ƙafafun sa yana circulating blood nashi har zuwa kan sa . Lumshe ido yayi yana jin tamkar
suyi ta tsayuwa a haka kar ta cika shi , har sukai Wani yammacin a haka a tare . Cikin dadÉ—an
Muryar ta wanda Fareesa ke cewa " Shine kaÉ—ai mai daÉ—i a tare da Umaima bayan shi ita bata
ga Abun da Yah Umair ya nace ya kuma maƙale mata ba . A Hankali yaji Muryar ta tana furta "
I'm sorry My champ . Ba zan sake ba ,wannan yayi maka ko a sauya?. Lumshe lulun idanun sa
yayi yana ware su . Wow'. Shine kalmar da ya furta , kamin yayi magana ne tayi saurin cika shi
tana juyowa tare da fuskantar sa .


Hakan yayi ko? To mu tafi gida. Habawa my Bul bul , ki bari mana ki ci abinci ki shirya a gidan

mijin ki ... Juyawa tayi tana bin kanta da kallo a tsakankanin glsses É—in dake gaban su da bayan
su . Haɗe girar sama da ƙasa tayi tana cuno baki , a sarari ta furta ,tabbas kuwa naci sunana
Bul-bul gani nan can ƙasan ka , ga kuma kiba mai muni . Buɗe baki yayi dariyar da yayi ta
danne ta ya kuɓce masa , haushi ne ya kamata , saurin juyawa tayi tana kallon sa kamin ta kai
hannun ta tana riko nasa , meye na kauda kai kuma Yallaɓai.? Fuskance Ni kayi dariyar ka
,nima zan rama ai . Ayya Sorry My Swt Ccbr . Au ka ƙara ko?? Kace swt Tomato Mana kawai .
Tayi maganan tana juya masa baya tare da sa hannayen ta tana naɗewa a ƙirjin ta . Ji tayi ya
É—aga ta cak yana sama da ita .wayyo Umma na sauke ni , Please Yah Umair Ka sauke ni ,juyi
da ita yake yi bai tsaya ya saurare ta ba , sai dariya da yake mata ,wannan yasata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login