Showing 1 words to 3000 words out of 9565 words
Chapter 1 - Rijiya Gaba Dubu Book 2 by Abdulaziz Sani Madakin Gini.pdf
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 1
Da isar saiyaru cikin gidan kurkukun bayan ya wuce kofofi goma sha daya sai ya wuce kai tsaye
izuwa dakin tuhuma yana ta murmushin mugunta,da isar sa kofar dakin sai masu gadin dakin
suka rusuna suka gaishe shi,ko kallon su bai yi ba ya daka musu tsawa yace Maza ku budemini
kofar da sauri na shiga,cikin hanzari daya daga cikin masu gadin yasa kuba ya bude kofar ya
kunna kai,ashe wadannan masu gadin duk na bogi ne acikin shigar kayan dakaru suna daga
cikin dakaru guda ashirin din da Imhal suka zaba domin su taimaka musu wajen samun nasarar
guduwa daga kurkukun.Da shigar saiyaru cikin dakin sai yayi arba da Zauwadu zaune akan
kujerar da aka saba dora masu laifi an daure hannayensa da kafafunsa da sarkoki ga badakare
daya a tsaye akansa yana dukansa da kulki har ya fasa masa baki da hanci jini na suba.koda
ganin haka sai saiyaru ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dubi badakaren yace dakata
haka yanzu kuma nine zanyi masa tawa azabar,ya kai Zauwadu kayi sani cewa yau ne ajalinka
zai tabbata a hannnuna tunda har ka karya dokata ka sake haddasa fada tsakanin
fursunoni,hakika yau gawrka rabon kifayen dake cikin teku ne.yana gama fadin haka sai ya
daga kulkinsa ya nufi Zauwadu da nufin ya buga masa a kansa,ba zato ba tsammani sai kawai
wannan badakaren dake tsaye ya shammaci saiyaru ya maka masa kulki akan kunnensa na
hagu,take saiyaru ya sulalae kasa sumamme.Koda saiyaru ya farfado sai ya tsinci kansa a
zaune akan kujera wacce ake dora fursunoni idan za a yi musu azaba an daure hannayensa da
kafafunsa ta baya,Imhal da Zauwadu na tsaye akansa sanye da kayan dakaru,shi dai Zauwadu
kayan saiyaru ya sanya sannan ya sanyawa saiyaru nasa na fursunoni.Koda saiyaru yaga haka
sai ya tuntsire da dariyar mugunta kuma ya turbune fuska yace kun bata lokacinku a banza
domin baku isa ku iya guduwa daga cikin gidan nan ba,nan gidan mutuwa ne gidan da babu
wani fursuna da ya isa ya tsira da rayuwarsa koda kun gudu sai an kamo ku an dawo daku idan
ma sanyin teku da halittun cikinsa basu hallaka ku ba.Koda gama fadin haka sai saiyaru yaci
gaba da kyalkyala dariyar mugunta,cikin fushi Zauwadu ya daga katon kulkin nan na saiyaru ya
maka masa shi a ka,take kan saiyaru ya fashe har kwakwalwarsa tayi fallatsi,koda suka ga
saiyaru ya mutu sai Imhal ya dubi Zauwadu yace to fa yanzu duk nasarar mu tana hannunka
duk yadda za a yi kada ka kuskura ka bari a gane cewa kai ba saiyaru banen,hatta muryarka
sai ka karyar da ita irin ta saiyaru tunda daman can kuna kama da juna a fuska da yanayin
jiki.Zauwadu ya risina ga Imhal yace yakai abokina kuma shugabana a wannan gida na darul
maut,ina mai tabbatar maka cewa baza a taba samun wata matsala ba daga gareni sai dai
daga sauran yan'uwanmu fursunoni guda ashirin wadanda muka janyo cikin wannan aiki,ni dai
alkawari daya nakeso kayi mini,koda jin haka sai mamaki ya kama Imhal yace wane alkawari
kakeso nayi maka?koda jin wannan tambaya sai Zauwadu ya sanya hannu acikin aljihunsa ya
dauko wata sarka ta dinare ya damkawa Imhal a hannunsa yace,Wannan sarka ce ta matata
wacce muke tsananin son juna fiye da hangen mai hange,a ranar da aka daura aurenmu da ita
acikin birnin kisra dakarun sarki Gurzalu suka zo su dubu uku suka rufeni da masifaffen duka
har sai da suka sumar dani,ina ji ina gani aka Rabani da amaryata SUHAILA aka sa mini sarka
a wuyana,hannayena da kafafuna aka tafi dani suhaila tana kuka da ihu.Wannan shine asalin
rabuwata da suhaila yau tsawon shekaru ashirin da bakwai kenan,suhaila na raye ko ta mutu
ban saniba.ina son duk sanda ka dawo cikin birnin kisra komai dadewa ka nemi suhaila a
unguwar Sharkas ka bata wannan sarka idan har na rasa rayuwata a kokarin guduwarmu daga
nan,idan kuma na tsira da rayuwata to zan karbi sarkata domin nayiwa suhaila alkawarin cewar
indai ina raye komai daren dadewa sai na dawo gareta ,amma idan ta ga an kawo mata
sarkarta to bana raye.Koda Zauwadu yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa,Al'amarin
da ya karya zuciyar Imhal kenan shima yaji ya kamu da tausayin Zauwadu har kwalla t acika
masa idanu,nan take dai suka fito daga cikin dakin tuhuma Imhal ya sanya sarkar suhaila a
cikin aljihunsa suka kullo kofar dakin ,masu gadin dakin mutum biyu suka rufa musu baya.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 2
Duk ta inda su Zauwadu suka zo wucewa sai ka ga ana gaishe su sabo da ana zaton saiyaru
ne,hatta muryar Zauwadu ta amsa gaisuwar sai ta zama iri daya sak da ta saiyaru,su kansu su
Imhal sai da suka cika da tsananin mamaki bisa yadda suka ji Zauwadu ya iya mayar da muryar
tasa haka,haka dai suka cigaba da tafiya har suka iso dakin da ake ajiye gawarwakin fursunonin
mutum hudu da suka mutu a sanadiyyar fadan da akayi a dakin cin abinci,kawai sai Zauwadu
ya bada umarni a debo gawarwakin a dora su akan amalanke domin a futar dasu gaba daya
daga gidan a watsa a teku,nan take kuwa dakaru suka cika wannan umarni daya bayan daya
fursunonin nan guda ashirin abokan aikin su Imhal suka dinga shigowa cikinsu suna take musu
baya.dama su duka sunyi shigar dakarun gidan kurkukun,haka dai su Imhal suka cigaba da
tafiya acikin kurkukun suna tura amalanken gawa ana bude musu kofofi,duk inda suka zo da
zarar anga saiyaru akan gaba sai kaga anbude musu kofa da sauri har suka shige ta cikin kofofi
goma sha biyu na kurkukun kuma duk kofar da suka fita sai an mai da ita an rufe.
Suna fitowa daga cikin kofa ta karshe sai suka yi arba da dandazon dakarun dake tsaron gidan
kurkukun,a gefe daya kuma ga jirgin ruwa da ma'aikatan kurkukun ke shiga idan zasu je karbo
abinci ko wani kaya acikin birnin kisra.Su dai masu gadin kurkukun dakaru ne kimanin guda
dubu arba'in,kuma ko yaushe acikin shirin yaki suke dauke da muggan makamai,koda suka yi
arba da juna tsakanin su Imhal da masu gadin sai aka tsaya ana kallon-kallo,in ba don ma
shugaban dakarun ya hango saiyaru akan gaba ba da tuni ya baiwa yaran nasa umarni su afka
musu.
Cikin karamar murya Imhal ya matso daf da Zauwadu yace dashi kada ka kuskura ka matsa
kusa da dakarun can,domin sai shugabansu ya gane cewa kai ba saiyaru bane,daga nan zaka
yi musu magana ka gaya musu cewa zamu tafi watsa gawar fursunoni ne teku.Koda jin wannan
umarni sai Zauwadu ya daga murya ya dubi shugaban dakaru yace ya kai Murwatu kayi sani
cewa yau an samu mutuwar fursunoni har guda hudu,sabo da haka ina son ku bani jirgi na zuba
su a ciki sai na isa tsakiyar teku sannan na zubar dasu domin na tabbatar da cewa sun zama
abincin kifayen ruwa.Koda jin wannan batu sai Murwatu ya turbune fuska ya dakawa saiyaru
tsawa yace,Kai saiyaru sabo dame yau zaka zo mana da sauyin yanayin aiki? A aikin tarihin
gidan nan tsawon shekaru arba'in da kafuwarsa ba a taba yin hakan ba,duk fursunan da ya
mutu daga nan ake jefa gawarsa cikin tekun,idan baza ku iya jefa gawarwakin ba daga nan to fa
sai dai ku hakura ku koma da gawarwakin ku,duk wanda yayi wani yunkuri cikin ku kuwa zamu
far masa.
Koda jin wannan batu sai hankalin su Imhal ya dugunzuma ,suka rasa abinda ke musu dadi
domin ga dukkan alamu sun sha wahalar banza kenan bisa duk irin kokarin da sukayi suka
samu nasarar fitowa har kofar karshe ta gidan kurkukun DARUL MAUT.
Cikin tsananin damuwa da karayar zuciya Zauwadu ya dubi Imhal yace ya kai abokina yanzu
mene abin yi?Imhal yace Bamu da abin yi face mu yaki su Marwatu ko mu ko su!
Cikin firgici Zauwadu yace Baka da hankali ne,ta yaya mu ashirin da biyu zamu iya yakar
dakaru dubu arba'in?
Imhal yace bamu da wani zabi wanda ya wuce hakan,ko dai mu yake su ko kuma mu jefa
kanmu acikin tekun nan mu hallaka shine kadai gatan da zamu yiwa kanmu,ya kai abokina kai
sani cewa faduwar gaba asarar namiji ce,yau ne za muyi yaki da dukkan karfinmu na jiki da
karfin zukatanmu,ko mutuwa mukayi mun bar abin fadi.Ko kuwa ka zabi ka koma cikin darul
maut a cigaba dq gana maka azaba har ka mutu tunda kasan cewa ko kadan baza ayi mana
sassauci ba tunda mun kashe saiyaru?koda Zauwadu da sauran fursunonin suka ji wannan
batu sai nan take suka ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zukatan su.
AYI MIN AFUWA ZAN CI GABA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA3
Lokaci guda su duka suka daga kulakensu,sannan suka ruga izuwa kan dandazon dakarun
suna masu kurma uban ihu,ai kuwa suma wadan nan dakaru su dubu arba'in sai suka zare
takubban su suka ruga gare su.ana haduwa aka kacame da azababben yaki. a kofar gidan na
darul maut.Kaico hakika idan mutum yaga mutuwa muraran to fa sai inda karfinsa ya kare,duk
da cewar su Imhal yan kalilan ne a cikin wadannan dakaru sai gashi suna ragargazarsu don duk
inda suka sa gaban su sai dai kag maza na zubewa kasa alokacin da jini ke feshi da
fantsama,kuma ihun mazaje da karafkiyar karafa ta cika dodon kunne.Koda aka samu dakika
dari biyu ana wannan gumurzun sai labari ya sauya sabo da sarkin yawa yafi sarkin karfi,nan fa
dakaru suka fara samun nasarar saran jikin fursunonin nan,jikinsu na darewa suna ihu amma
sabo da naci gami da taurin rai sunki su fadi kasa,a hakan suke cigaba da yaki.Sai dai kaga
jikin fursuna yayi kaca-kaca da sara da suka tamkar yayi wanka a kogin jini amma shima bai
fasa ragargazar maza ba,wani lokaci ma har faduwa suke kasa sakamakon jiri dake dibarsu
amma sai kaga suna mikewa tsaye suna cigaba da yakin.
Koda shugaban dakarun ya ga ana ta ragargazar yaransa kuma ya kasa fahimtar bangaren
dake samun nasara a tsakanin mutum ashirin da biyu kacal da kuma mutum dubu arba'in sai ya
fusata ainun ya kutsa cikin fursunonin nan da karfin tsiya cikin tsananin kwarewar yaki ya dinga
fillewa fursunonin kawuna suna zubewa kasa matattu. Kafin Zauwadu da Imhal su ankara da abinda yake faruwa tuni ya kshe musu mutane goma sha
biyu ya zamana cewa saura goma kacal,koda Imhal ya juyo yaga gawarwakin jama'arsu a kasa
a lokacin da gaba daya jikinsa ya rine da jinin dakarun da ya kashe sai ya kwarara uban ihu ya
kara kaimi yana mai cigaba da sara da suka cikin tsananin zafin nama mara misaltuwa sai gashi
yana yiwa dakarun mummunar barna.
Shima Zauwadu da yaga Imhal ya kara zage damtse sai shima yayi koyi dashi suka haukace
suna ta daukar rayuka,Koda shugaban dakaru Murwatu yaga haka sai ya daka tsalle sama
kamar an cilla shi daga cikin kibiya ya dira a gaban Zauwadu ya tare shi suka ruguntsume da
azababben yaki. Wohoho! idan tsagwaron karfi ya hadu da kwarewa akwai tashin hankali,kai koda ga dan kallo
ma cikin firgici da tashin hankali zai iya kallon wannan gumurzun.Sai da Marwatu da Zauwadu
suka shafe dakiku masu yawa suna kaiwa juna mugayen hare-hare na sara da suka basu samu
nasarar komai ba. A wannan lokaci kuwa Imhal ya samu nasarar bazar da dakaru dubu ashirin a kas,ragowar
dubu ashirin din ma sun razana dashi ainun sun fara ja da baya duk da cewa wasun su ya
sassare su amma sabo da naci sun ki hakura dada yi masa kawanya suke domin suyi masa
rubdugu
A bangaren Marwatu da zauwadu kuwa,lokacin da suka fafata ainun suka ga babu wata nasara
sai suka ja da baya sukayi cirko-cirko suna haki da kallon juna kamar wadan su
zakaru,kowannensu na tunanin irin dabarar da zai sauya don ya samu nasara akan abokin
yakinsa.kamar hadin baki suka zare takubbansu suka daga sama lokaci guda suka rugu izuwa
kan juna suna kururuwa,koda ya rage saura bai fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka
tsalle sama suka kaiwa juna mummunan hari.Cikin sa'a Murwatu ya sokawa Zauwadu takobi a
kahon zuciyarsa,shi kuwa Zauwadu ya soka masa a gefen cikin sa,suka rikito kasa a matukar
galabaice jini na zuba a jikin su.
Zauwadu ya baje a kasa wanwar ya kasa tashi yana aman jini da karkarwar jiki,shi kuwa
Marwatu sai ya mike tsaye ya yage rigar jikinsa ya daure raunin cikin nasa don tsaida zubar jini.
TO AYI MUN AFUWA ZAN CIGABA IDAN NA HUTA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 4
Koda ya dubi Zauwadu yaga yana kakarin mutuwa kuma ya waiga yaga shima Imhal ya fara
gajiya ainun tsabar naci ne da tsananin juriya yasa yake cigaba da yakin sai ya bushe da
dariyar farin ciki ya dubi zauwadu yace Ai babu yadda za ayi ku samu nasarar guduwa daga
nan har ku tsira da rayuwarku,shekaru arba'in baya haka muke gadin gidan nan ku duka sai kun
zama gawa,saura Imhal shi kadai a tsaye shima kuma yanzun nan zan koma na gama dashi
kamar yadda na gama dakai.
Koda jin wannan batu sai hawayen bakin ciki ya zubowa zauwadu ya dubi gawarwakin 'yan
uwansu fursunoni dake kwance a kasa,kawai sai ya yunkura cikin matukar karfin hali ya bushe
da dariya ya dubi marwatu yace,Tabbas mutuwa zanyi amma ko ba komai na jagoranci
fursunoni mun karya alkadarin gidannan tunda gashi har mun samu nasarar fitowa daga cikinsa
alhali babu fursunan da ya taba fitowa,ko ba komai kai marwatu zan mutu na barka da tabon
yankan takobina a cikinka.
Gama fadin haka keda wuya sai suka ji karar bude kofofin kurkukun guda goma sha biyu gami
da gudun sawaye alamar cewa dakarun da ke cikin gidan sun faarga da mutuwar shugabansu
saiyaru wanda aka bar gawarsa a dakin tuhuma don haka fitowa za suyi waje su kawowa su
marwatu dauki. Koda Imhal ya jiyo sautin gudun dakarun daga cikin kurkukun sai ya zabura ya falfalo da
azababben gudu izuwa inda su marwatu suke ya buda dakarun nasa da karfin tsiya yana
saransu da banke su kai kace tamkar bai taba gajiya ba ko kuma a sannan kuma a sannanne
ma ya fara yakin. Kafin marwatu ya juya ya tari Imhal tuni Imhal ya dako tsalle a sama ya doki gadon
bayansa,sabo da karfin dukan sai da marwatu yayi tsalle sama ya bar kan tsuburin gaba daya
ya fada cikin tekun,koda ganin haka sai ragowar dakarun nasa gaba daya suka ruga zuwa
bakin tekun domin su ceto rayuwar marwatu. Damar da Imhal ya samu kenan ya sunkuya ya dauki zauwadu ya saba shi ae kafada ya ruga
da baya izuwa inda jirgin ruwa yake ya daka tsalle ya dirga acikin jirgin ruwan ya warbar da
zauwadu a ciki sannan yasa takobinsa ya sare igiyar da ta daure jirgin,aikuwa sai igiyar ruwa ta
kada jirgi sai gaba. a dai dai wannan lokaci ne dakarun cikin kurkukun suka karaso kofar gidan a guje suna da
yawa kuma a sannan ne aka tsamo marwatu daga cikin tekun aka dawo dashi kan tsibirin.
Koda marwatu ya kyalla ido ya hango su Imhal acikin jirgi nesa kadan da tsibirin sai ya kwarara
uban ihu yace A ruga a debo karnukan gidan,nan take kuwa aka je aka debo karnukan,Marwatu
da karnukan tare da wadansu dakaru kimanin mutum dari biyu suka shiga wani jirgin dabam
suka bi bayan jirgin Imhal. TO JAMA'A AYI MIN AFUWA IDAN NA HUTA ZAN CIGABA.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 5
Lokacin da Imhal yaga igiyar ruwa ta kada jirginsu yayi gaba sa ya dawo inda ya warbar da
Zauwadu ya iske shi yana ta kakarik mutuwa bai mutu ba,Imhal ya durkusa daf dashi ya kama
hannayensa ya rike a lokacin da hawaye ya zubo masa ya dube shi yace "Haba ya kai
abokina,sabo dame zaka tafi ka barni alhalin gashi mun sami nasarar guduwa daga kurkukun
darul maut?" koda jin wannan batu sai Zauwadu yayi kakin jini ya tofar sannan ya dubi Imhal
cikin karfin hali yace"ya kai abokina ina mai farin ciki da ya zamana cewa kai kadai ka tsira da
rayuwarka daga cikin mu ba don komai ba sai don nasan cewa ka samu damar da zaka cika
alkawarin dake tsakanin mu, duk ranar da ka riski matata suhailat ka bata labari irin rayuwar da
mukayi a cikin kurkukun darul maut da yadda ka zama babban abokina kuma masoyina alhalin
da farko mun kasance makiyan juna,ka sanar da ita yadda akayi muka samu nasarar guduwa
daga wannan masifaffen kurkuku har izuwa sanda ajalina ya riskeni,ya kai Imhal idan kayimin
haka ka gama yimin komai,kuma cikin kabarina zanyi bacci acikin kwanciyar hankali batare da
bakin ciki ko nadamar komai ba,sabo da ko ba komai matata tasan cewa na mutu a filin daga a
matsayin gwarzon jarumi,ka sani cewa ba wani laifi nayi baaka kawoni kurkukun darul maut
face kawai na hana dakarun sarki Gurzalu zalunci a watavrana sanda suka shigo cikin gari suka
kashe wani attajiri suka kwashe dukiyar gidansa kaf,suna shirin kashe iyalinsa ne na afka musu
na ragargaje su suka gudu,nan take na taimaki iyalan attajirin na kaisu tashar jirgin ruwa suka
hau jirgi suka bar garin gaba daya,tun daga wannan rana sarki Gurzalu ya dinga farauta ta ina
buya har izuwa ranar da tsautsayi yasa aka zo aka kamani ranar da na auri suhaila"
kodaZauwadu yazo nan a zancen sa sai yayi wa Imhal murmushin karshe sannan idanunsa
suka kafe gaba daya jikinsa ya sandare ya zama gawa.Koda ganin haka sai Imhal ya kwanta
akan gawar zauwadu ya rungumeta yana mai fashewa da matsanancin kukan bakin ciki kamar
ba zai taba dainawa ba, sai da Imhal yayi kuka har ya gaji barci ya dauke shi bai sai ba,a
lokacin da igiyar ruwa ta ci gqba da kada jirgin acikin teku yayi ta tafiya ba sassauci.
TO JAMA'A ZAN CIGABA IDAN NA HUTA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 6
Al'amarin su marwatu kuwa,wadan da suka hawo wani jirgin tare da mugayen karnuka kimanin
guda arba'in sai suka nemi jirgin su Imhal suka rasa a cikin tekun domin ya bace musu