Showing 9001 words to 9565 words out of 9565 words
Chapter 4 - Rijiya Gaba Dubu Book 2 by Abdulaziz Sani Madakin Gini.pdf
a wannan rana kyawunsa da siffar jarumtakarsa sun bayyana a fili muraran,ita dai
Gimbiya Shumaira nan take taji ta kamu da tsananin kaunar sa,bata ma San sanda ta kama yin
murmushi ba a gareshi, ita kuwa Gimbiya lamirat sai kawai taji zuciyar ta taci gaba da bugawa
da karfi, bugawar da bata San dalilin ta ba,shin kiyayya ce ko soyayya ta janyo hakan? amsar
da ta kasa baiwa Kanta kenan.
Koda aka kawo jarumi Imhal tsakiyar filin gasar wanda sama da dakaru dubu dari ne suka
kewaye shi rike da makamai don tabbatar da tsaro harma da wadanda suka dana kibiyoyi akan
baka, kawai jira suke suga wani yayi ba dai dai ba yasha ruwan kibbau, aka kwancewa jarumi
Imhal dukkanin sarkokin da ke jikinsa sannan aka bashi takobi da garkuwa ya rike, nan fa Imhal
ya fara waige-waige da dube-dube domin ya ga abokin gwaninsa, amma bai ga kowa
ba,Alokacin ne sarki taryan ya bushe da dariyar mugunta ya dubi sarki gurzalu yace,Yanzu
wannan Dan jarumin ne lake tunanin zai iya karawa da gwarzo na abin alfahari na?Sarki
gurzalu yace,Ai a inda babu kasa nan ake gardamar kokawa, ina naka jarumin ya fito su kara
mu gani,Koda jin haka sai sarki taryan ya daga kai ya dubi wani barde,take barden ya daga
wata katuwar gudumar danko ya daki wani katon bandiri, karar bandirin ta cika birnin gaba daya
da amsa kuwwa, Faruwar hakan ke da wuya aka bude wata katuwar kofa, sai ga sadauki
Darwaz ya fito cikin shigar yaki rike da takobi da garkuwa, Tunda Imhal yazo duniya bai taba
ganin mutum mai tsananin tsawo, kauri, da murdewar jiki ba irin ta sadauki Darwaz, nan take
zuciyar Imhal ta karaya ya fara tunanin cewa, ai bazai iya ba da wannan katon domin da
sadauki Darwaz ya karaso ya tsaya daf da shi sai ya zama Dan mitsitsi akansa kamar an ajiye
dantsako a gaban shirwa, tun kafin a bayar da umarnin a fara gasar sai Darwaz yasa hannu
daya ya make Imhal, saboda karfin dukan sai da Imhal ya yi tsalle sama yaje ya gwaru da
karfen da aka kewaye filin gasar ya fado kasa Tim!yana aman jini,Koda Faruwar hakan sai filin
gasar ya rude da shewar jama'a, Attajiran da suka shiga cacar kudi da sadauki Darwaz suka
kama murna suna ihu da tsalle domin suna ganin cewar lallai jarumin sune zai lashe gasar su
kwashi tsabar kudi, shima sarki taryan sai ya kama kyalkyala dariyar mugunta, ita kuwa Gimbiya
Shumaira sai hankalin ta ya dugunzuma ta rude ainun ta kamu da tsananin tausayin Imhal, har
kwalla ta cika mata idanu.
Ba zato ba tsammani sai aka ga jarumi Imhal ya mike tsaye zumbur! ya ruga da gudu izuwa kan
sadauki Darwaz sun ruguntsume da azababben yaki suna masu kaiwa junan su SARA DA
SUKA cikin tsananin zafin nama da juriya da bajinta ta ban al'ajabi.
WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GASA TSAKANIN JARUMI IMHAL DA SADAUKI
DARWAZ? SHIN SARKI GURZALU ZAI SAMU NASARAR KASHE JARUMI IMHAL YA LASHE
GASAR KAMBUN JARUMTA? SHIN IMHAL ZAI CIKA BURINSA NA RUGUJE KURKUKUN
DARUL MAUT DA KONE RIJIYA GABA DUBU?YAUSHE NE IMHAL ZAI KOMA BIRNIN MISRA
YA SAKE SADUWA DA TSOHO IMZANU KUMA YA SAN 'YAR UWAR MAHAIFIYARSA
LIKICIYA MUZAIRA? Mu hadu a littafin RIJIYA GABA DUBU 3 don jin cigaban wannan
kasaitaccen labari.
to jama'a zan Dan huta kafin Ku jini a cikin na uku