Showing 6001 words to 9000 words out of 9565 words
Chapter 3 - Rijiya Gaba Dubu Book 2 by Abdulaziz Sani Madakin Gini.pdf
namu da hannu na domin ko sunan sa bana so naji an ambata
bare kuma na ganshi da idanu na".
To zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 15
Koda jin wannan batu sai Sarki Gurzalu ya bushe da dariya yana mai janye jikinsa daga cikin na
LAMIRAT sannan ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar ya dubeta cikin nutsuwa yace,yake 'yata
rabin jikina ki kara hakuri daga nan zuwa ranar da zamu hadu da wannan babban makiyi namu
a filin gasar JARUMTA ta misra, zaki ga yadda zanyi masa kisan gillah ta hanyar yi masa
mugayen sare-sare da takobi na,lallai sai na daddatsa shi kamar yadda ake daddatsa nama a
mahauta, yanzu zan sanar daku wani babban sirri Wanda baku sani ba ke da mahaifiyarki, Ku
sani cewa wannan jarumi Imhal Wanda nake so nayi gasar KAMBUN JARUMTA dashi ba wani
bane face Dan marigayi Sarki Imhal na kasar nan Wanda na kashe shi na hau karagar mulkin
da karfin tsiya,idan ban kashe wannan yaro yanzu ba nan gaba sai ya kashe ni ya karbi karagar
mulkin sa,duk naga wannan al'amari ne a cikin madubin tsafi na bisa bincike da nayi a jiya da
daddare. Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai hankalin Gimbiya lamirat da
mahaifiyarta ya dugunzuma ainun suka rasa abinda yake musu dadi,cikin alamun tsananin
damuwa lamirat tace,Ai kuwa tunda haka ne yanzun nan zan he kurkukun Darul maut na kashe
jarumi Imhal da hannu na in ba haka ba ina cikin zulumi da fargaba tunda nace Ka kashe
makashinka karfin ya samu damar kashe ka,Koda gama fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike
tsaye da nufin ta fice daga cikin turakar amma sai Sarki Gurzalu yayi wuf ya ruko hannun ta
yana murmushi ya dubeta yace,Haba yake 'yata ai kin sani cewa duk irin kiyayyarki da Imhal
bata kai tawa ba amma sai gashi nayi hakuri ina jiran lokaci ya cika Wanda ya dace da zan
kashe wannan yaro, kin sani cewa dake zanyi wannan tafiya izuwa birnin misra a gabanki zan
kashe wannan yaro, abinda nake so dake shine, lallai ki danne kiyayyarki ga Imhal a yayin
wannan tafiya tamu, kada ki kuskura ki sanar dashi cewa nine na kashe mahaifinsa da dukkan
zuri'arsa domin idan ya gano hakan burina na kashe shi a filin gasar JARUMTA ba zai cika
ba,Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai zuciyar Gimbiya lamirat tayi Dan sanyi ta dube
shi tace ,shikenan ya kai Abbana zan cigaba da hakuri har izuwa wannan rana amma fa ka sani
cewa ba zan iya danne zuciya ta ba akan nunawa Imhal kiyayya gami da cin zarafin sa da
azabtar dashi kafin mu isa birnin misra, Sarki Gurzalu yace A a bana son ki taba lafiyarsa domin
ina so ya murmure kafin mu isa can din ramar dake jikin sa ta bace kuma ya samu isasshiyar
lafiya don kada mutane suga cewar da nakasasshe zanyi wannan gasa, Koda jin wannan batu
sai Gimbiya lamirat ta ciza yatsanta cikin tsananin takaici domin ba haka taso ba,tabbas taci
buri ta kara azabtar da Imhal ainun bayan da ma ya Sha azabar RIJIYA GABA DUBU. wannan
shine abinda ya faru a gidan Sarki Gurzalu kafin cikar kwanaki goma Sha hudun da za a fito da
Imhal daga cikin kurkukun Darul maut.
To jama'a ayi min afuwa zan cigaba idan na dawo,jiya na dawo gida amma gobe zan sake
komawa ina fatan za ayi min uzuri.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 16
Al'amarin Jarumi Imhal kuwa bayan Angama yi masa wannan azaba ta kwanaki goma Sha
hudu da kayan masifun dake cikin RIJIYA GABA DUBU an fito dashi an kai shi gidan sarautar
sarki Gurzalu a matukar galabaice kuma a daddaure cikin sarka sai aka watsar da shi a cikin
rana yayi ta gasuwa a cikin harabar gidan sarautar har tsawon kimanin sa'a guda sannan sarki
Gurzalu tare da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT suka fito Daga cikin gidan sarautar a cikin gagarumar
shigar yaki gami da kimtsawar tafiya, tun daga nesa Gimbiya LAMIRAT ta kurawa Jarumi Imhal
idanu Wanda ke kwance a kasa magashiyan ya jike sharkaf da gumi yana faman nishi kamar
Wanda ransa zai fita. duka da cewar Imhal ya rame matuka amma surar jikinsa irin ta manyan
sadaukai tana nan kuma babu abinda ya taba lafiyar kyakkyawar fuskarsa, koda tayi arba dashi
a karon farko sai taji zuciyar ta ta buga da karfin gaske kuma ta kasa sanin dalilin haka, Yayin
da sarki Gurzalu da Gimbiya lamirat suka iso akan jarumi Imhal suka tsaya sai sarki gurzalu ya
sa kafarsa ya dunguri wani ciwo dake hakarkarin Imhal,Imhal yayi Dan ihu sakamakon mugun
zafin da ya ji, shi kuma sarki gurzalu sai ya dube shi ya bushe da dariya yace Ya kai yaro, ka
sani masu iya magana suna cewa, Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,Yau gashi ranar
yin gasar mu ta JARUMTA ta so kamar yadda na shaida maka, ko da gama fadin haka sai sarki
ya kirawo wadansu hadimansa yace, Ku dauki wannan fursunan kuje kuyi masa wanka kuma a
kirawo likita na yayi masa magani sannan a bashi kayan yaki yasa azo dashi bakin kafar gari
inda za muyi wannan tafiya tare dashi, Koda gama fadin haka sai wadannan hadimai suka
ciccibi Imhal suka tafi dashi dakaru kimanin guda dubu na kewaye da su don tabbatar da tsaro,
saboda kar Imhal yayi yunkurin guduwa duk da cewar yana daure cikin sarkoki, Bayan an tafi
da jarumi Imhal ne sarki gurzalu ya juyo ya dubi Gimbiya Lamirat yace, amma fa kin bani
mamaki, wai shin duk ina zafin zuciyar taki ya tafi ne alhalin ga babban makiyin namu a gabanki
amma ko dukan sa ba kiyi ba bare kiyi masa azaba ko wulakancin da kike furucin za kiyi masa,
koda jin wannan batu sai lamirat tayi dan guntun murmushi tace,ya kai Abbana na sani cewa
bana cin zalina ba ramamme ko nakasasshe, na fison na zalunci lafiyayyen mutum Wanda ko
yaya na taba shi zai ji mugun ciwo amma ba ragowar mutuwa ba,Koda jin haka sai sarki gurzalu
ya bushe da dariyar farin ciki yace Dakyau 'yata hakika barewa bata gudu danta yayi rarrafe,
lallai yanzu na gamsu cewar kin gaje ni kuma ko a bayan raina nasan zaki iya tafiyar da mulki
kamar yadda nake tafiyar da shi. to jama'a idan na huta zan cigaba.
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 17
Koda gama fadin hakan sai sarki ya kama hannun Gimbiya lamirat ya na ta suka tafi izuwa can
kofar gidan sarautar inda aka ajiye keken dokin da za su hau don tafiya birnin Misra kuma ga
dakaru masu yawan gaske sun kewaye keken dokin gaba da baya, kuibi-kuibi, wadanda zasu yi
musu rakiya, kamar yadda sarki gurzalu ya bayar da umarni haka akayi, wato sai da aka yiwa
Imhal wanka aka sa masa magani a jikin raunikansa sannan aka kawo abinci mai rai da lafiya
aka bashi yaci yasha ya koshi,daga nan kuma aka sanya masa kayan yaki a jikinsa, amma
maimakon a dama masa makami sai aka sake zuba masa sarkoki aka daure shi aka kawo shi
cikin tawagar sarki da zata tafi birnin misra, nan take aka sanya Imhal acikin wani akurki Wanda
dawakai ke Jansa aka kulleshi a ciki, sannan aka dunguma gaba daya aka fice daga cikin birnin
gaba daya.
Tsakanin birnin kisra da misra tafiya ce ta sa'a bakwai don haka fun safe aka fara wannan tafiya
ba a iso birnin kisra ba sai da rana ta take, kai tsaye tawagar sarki gurzalu ta nufi gidan sarautar
sarki Taiyara don haka sai ya shirya ya fito ya tare su cikin tsananin murna, nan take aka shigar
da Gimbiya lamirat da mahaifiyarta izuwa inda iyalan sarki Taiyara suke, shi kuwa jarumi Imhal
sai aka kai shi cikin wani daki mai kama da kurkuku aka kulleshi, Sarki gurzalu da sarki Taiyara
kuwa sai suka shige izuwa turakar sarki Taiyara inda suka zauna aka kawo musu abinci da aka
Sha har da giya suka ci suka Sha suka yi tatul suna ta kyalkyala dariya, daga can sai sarki
Taiyara ya numfasa ya dubi sarki gurzalu yace, Ya kai tsohon abokina jarumin jarumai na
wannan nahiyar, wai shin bana da wanne guzuri kazo mana da shi ne?ka sani cewa duk
shekara Kaine kake lashe gasar nan don haka babu sabon wani al'amari Wanda zai sa mu
samu kudade masu yawa tunda kowa ya San cewa kaine zakaran gasar, yayin da sarki taryan
yazo nan a zancen sa sai sarki gurzalu ya bushe da dariya sannan yace, Kwantar da hankalin
ka ya kai abokina kayi sani cewar nazo mana da wani gwarzon jarumi wanda zai burge yan
kallo kuma nine kadai zan iya gamawa da shi, kafin na kara dashi zan bashi dama yayi wasa
kamar sau shida, ina mai tabbatar maka da cewar a ranar da yayi wasan farko labarinsa zai
bazu a ko ina, kuma kashegarin da zai sake wasa sai filin gasar ya cika ya batse da yan kallo
don haka kafin ranar da zamu kafsa ni da shi ba kananan kudin shiga zamu samu ba.
to zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 18
Wannan karon har dukkanin sarakunan da ke nahiyar nan sai sun zo sun kalli wasan karshe,
domin suga yadda zata kaya, Yau baza ayi wasa ko guda daya ba sai gobe saboda ina son
jarumin nawa ya huta sosai ya samu karfin jikinsa, Koda sarki gurzalu yazo nan a zancen sa sai
sarki taryan ya bushe da dariya sannan yace, Ya kai abokina nifa duk wannan labarin da na
bani naji sane kamar tatsuniya, duk da cewar banga wannan jarumi ba da kazo dashi nasan
nawa jarumin sadauki Darwaz ya fishi komai da komai, don haka a goben da safe ina son
Darwaz da jarumin naka su kara.Koda jin wannan batu sai sarki gurzalu ya sake bushewa da
dariya yace Ai shikenan, dama masu salon magana sun ce sai an gwada akan San na kwarai.
Sarki Taryan yana da 'ya' guda daya wata kyakkyawar budurwa ta kwatance mai suna
Shumaira, Shumaira da Lamirat sun kasance kawayen juna tun suna yara kanana saboda
abotar dake tsananin iyayensu, don haka suma sun shaku ainun, Wani abin mamaki shine, ko
kadan ra'ayinsu baizo daya ba,domin ita Gimbiya Shumaira tana da tsananin tausayi, sabanin
lamirat wadda ta kasance Mara imani ga zalunci, hakan bata sa sun kasa shakuwa da kaunar
juna ba,amma suna yawan samun sabani domin ako yaushe Shumaira tana matsawa lamirat
akan ta daina zaluntar talakawa da masu rauni, wani lokacin ma idan suka samu sabani, sai su
kwana uku basa magana da juna,kuma su daina kwana a waje daya da con abinci tare. Gimbiya Shumaira na zaune a cikin turakar ta sai ga Gimbiya lamirat ta shigo, Koda ta dago kai
suka yi arba da juna sai Shumaira ta Mike zumbur! ta ruga gareta cikin tsananin farin ciki suka
rungume juna,Shumaira ta janye jikinta daga cikin nata suka fuskanci juna sannan tace,Ai tun
jiya nake zuba ido naga kun iso amma sai naji shiru tunda dai shekara ta zagayo, Lamirat tayi
murmushi tace Ai mun kara kwana daya ne akan lokacin da muka saba tasowa, saboda
wannan karon mun taho da wani gagarumin jarumi, wanda za a samu kudade da yawa a dalilin
sa,Koda jin wannan batu sai mamaki ya Kama Gimbiya Shumaira tace, Haba ya ke kawata
yanzu Ashe har za a iya samun wani jarumi wanda zai burge mutane a wannan nahiyar tamu
sama da mahaifina ki?Lamirat tayi murmushi tace,Ai bana nufin yafi mahaifina JARUMTA,
amma dai zai taka muhimmiyar rawa a wannan gasa da za ayi ta bana,kuma ina tabbatar miki
da cewar inba mahaifin nawa ba babu wanda zai iya kaishi kasa a wannan gasa, Shumaira ta
girgiza kai tace Yake kawata kin sani cewa ban taba zuwa kallon wannan gasa ba saboda ko
kadan bana son naga jini yana zuba, bana son naga ana kashe mutane a aikin banza, amma
wannan karon naji zuciyata tana son taga wannan bakon jarumi wanda kika zo mini da labarin
sa don haka indai zai yi wasa gobe zan fita filin gasar na kalle shi don kawai naga iyakar
jarumtakar tasa da kike kodawa, Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Gimbiya lamirat
saboda ta dade tana son ta dinga Jan Shumaira suna fita kallon wannan gasa tare amma taki
tsawon shekara da shekaru, Tabbas lamirat tayi mamaki da taji Yau dare daya Shumaira ta
amince zata fita kallon wannan gasa.
to jama'a sai na huta zan Dora
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 19
A daren wannan rana kuwa aka yi ta shela birni da kauye cewar sarki gurzalu yazo da wani
sabon gwarzon jarumi kuma ansa cacar kudi akan sa cewar duk jarumin da ya kai shi kasa za a
bashi dinare miliyan daya,kuma sannan zai yi wasan farko a gobe da safe tare da sadauki
Darwaz na birnin misra, Koda wannan labari ya bazu sai gari ya rude da kace nace ana
mamaki, attajirai kuwa suka yi ta shirya cacar kudi a tsananin su kowa na zabar gwaninsa a
tsananin jarumi Imhal da sadauki Darwaz, Jama'ar gari kuwa mata da maza yara da manya
kowa ya dinga dokin gari ya waye yaje ya biya kudin shiga filin gasa domin ya ga irin gumurzun
da za ayi tsananin wadannan manyan jarumai.
Kai! tun kafin ma gari ya waye filin gasar ya cika makil ya zamana cewar har akan katanga
mutane ne a zaune, duk inda mutum ya duba baya ganin komai sai kawunan bil'adama, babu
wani guri da yayi saura sai na sarakuna da manyan attajirai, sune kadai basu iso ba,sai kuma
jaruman da za suyi gasar, wato jarumi Imhal da sadauki Darwaz. Sadauki Darwaz wani narkeken katon mutum ne mai girman gaske wato mai kirar mutanen
farko, Darwaz ya kasance shahararren gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga,A ranar
da suka fara yin gasar kambun JARUMTA shi da sarki gurzalu, dakyar shi sarki gurzalu ya
samu nasarar kaishi kasa,don har sai da ya yanki sarki gurzalu sau biyu bayan sun shafe sa a
daya da rabi suna bakin yamutsi, daga wannan lokaci basu sake haduwa ba kawo I yanzu,
kuma har gobe ta ciki na ciki, domin kowannensu yayi matukar bakin ciki bisa yadda gumurzun
nasu ya kasance saboda sun Sha bakar wuya sun zubar da jini, wannan karon da sadauki
Darwaz yaji cewar jarumin da zai kafsa dashi, sarki gurzalu ne yazo dashi sai yaci mugun burin
daukar fansa a kansa ya kudurce a ransa cewar a gaban sarki gurzalu zai yiwa jarumin kisan
gillah. Sai da gari yayi haske sosai sannan jama'a suka ji anfara buga tambura ana busa algaita da
sarewa alamar cewa sarakuna zasu fito daga cikin gidan sarautar, nan take gaba daya jama'ar
dake filin gasar suka mimmike tsaye don girmamawa, Fadawan sarki taryan da manyan
attajiran kasar suka fara shigowa cikin filin gasar, sannan sai ga sarki taryan, sarki gurzalu,
Gimbiya lamirat da gimbiya Shumaira sun shigo,dakaru da kuyangi na take musu baya har suka
iso wajen da aka tanadar musu mai dauke da kujeru na alfarma,Koda jama'ar gari suka ga
Gimbiya Shumaira ta fito kallon wannan gasa sai suka cika da matukar mamaki, nan dai su
sarki taryan da su Shumaira suka isa mazauninsu suka zazzauna.
Al'amarin jarumi Imhal kuwa, tun a jiya bayan anyi masa wanka, ansa masa magani ajikin
raunikan jikinsa, kuma an bashi abinci na alfarma ya cika cikin sa sai ya nutsu sosai ya dawo
cikin hayyacinsa inda ya fada cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru a baya.
to jama'a zan cigaba idan na huta.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 20
Babu abinda ya fara fado masa a rai face irin tsananin azabar da aka gana masa a bakin
RIJIYA GABA DUBU ta tsawon kwana goma Sha hudu, A tsawon kwanakin azabar gobe tafi ta
jiya, haka akai ta azabtar dashi babu sassauci, azabar farko itace wadda kunamun nan suka fito
suka yi ta cizon sa,kashegari kuwa macizai ne suka fito suka yi ta saran sa,haka abin ya cigaba
da wakana, wata ran ya ga dodanni suyi ta dukansa suna tamola dashi. Koda jarumi Imhal ya
gama tuno wannan masifaffiyar wahala da ya Sha acikin RIJIYA GABA DUBU wacce ke cikin
kurkukun darul maut, sai ya takarkare ya kwarara uban ihu,Ihun nasa ya cika gidan sarautar
gaba daya, har sai da dakaru masu yawa suka rugo izuwa kofar dakin da yake,Koda suka leka
suka gan shi a kwance a kasa kuma a daure ga kofar dakin a kulle sai hankalin su ya kwanta,
sabo da dama can an gargade su matuka akan cewar kada su kuskura su bari ya tsere, idan
kuwa ya gudu a bakacin ransu su duka.
Gama tunani ke da wuya sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya fashe da matsanancin kuka, A
karshe ya kudiri aniyar cewa komai rintsi da tsanani sai ya jure duk irin bala in dake gaban sa
domin ya tsira da rayuwarsa, ya koma gidan kurkukun darul maut ya ruguje shi kuma ya kone
wannan RIJIYA ta gaba dubu domin a daina azabtar da al umma,Bayan nan kuma yayi
alkawarin cewar sai ya koma gidan Likiciya Zumaira domin ya dauke tsoho imzanu su gudu
izuwa wata nahiyar daban inda da sannu zai cigaba da bincike domin ya gano asalin iyayensa
da danginsa, haka dai Imhal yayi ta sakar zuci har dare ya raba bai sani ba sannan bacci ya
kawo masa mamayar ba zato,
Kashe gari kuwa da safe aka sake kawo masa abinci da abin Sha mai rai da lafiya ya kimtsa
cikin sa,sai bayan ya huta sosai sannan aka zo aka bude dakin aka fito dashi a daure cikin
sarkoki, aka nufi filin gasar JARUMTA dashi.
koda aka iso filin gasar da jarumi Imhal a daddaure cikin sarka, da jama'a suka yi arba dashi sai
filin gaba daya ya rude da shewa gami da tafi.
zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 21
Gimbiya lamirat da Shumaira na hango shi sai su duka suka mike tsaye, suka kura masa idanu
domin