Showing 3001 words to 6000 words out of 9565 words
Chapter 2 - Rijiya Gaba Dubu Book 2 by Abdulaziz Sani Madakin Gini.pdf
sakamakon iskar da ta ie kadawa mai karfin gaske ce gami da hazon da ake yi mai duhun
gaske,amma sai suka cigaba da tuka jirgin nasu a haka,sai da suka kwana uku suna tafiya a
cikin teku sannan suka iso bakin gaba a wata sakaliyar safiya,ai kuwa suna isowa suka yi kicibis
da jrgin su Imhal a gefen tekun,cikin hanzari murwatu yasa aka saki wadan nan karnuka suka
ruga izuwa cikin jirgin Imhal suna nemansa suna shinshine-shinshine,A lokacin ne murwatu da
dakarunsa suka iso gaban jirgin suka caje cikinsa kaf amma basu ga Imhal ba sai alamar jinin
zauwadu da ya zuba a kasa wanda har ya bushe,Kawai sai marwatu ya dago kai ya dubi
dakarunsa yace Duk yanda akayi Imhal yana nan cikin dajin nan bai yi nisa ba amma abokinsa
zauwadu ya mutu domin babu mutumin da zai zubar da jini mai yawa haka ya rayu,yanzuzamu
bazama cikin wannan daji duk inda Imhal yake sai mun riske shi mun kashe shi,sai na cire
kansa na tafi dashi izuwa darul maut domin sauran fursunonin gaba daya su gani ya zama
gargadi a gare su don kada wani yace zai kara yunkurin gudu anan gaba,kuma nasan cewa sai
sarki Gurzalu ya daukaka ni ya bani dukiya mai yawan gaske sakamakon wannan gagarumin
aiki da zanyi kai inda hali ma a araye nake so na kamo Imhal domin na mayar dashi cikin darul
maut mu sake tsare shi sabo da sarki ya fi son su sake haduwa a gasar jarumtaka wacce za ayi
a birnin misra nan da cikar kwana goma sha daya,maza ku saki karnukan nan subi sawun Imhal
domin suna iya jin kamshin mutum komai tazarar da ya basu kuma suna da karfin gudun da bai
isa ya tsere musu ba.Koda jin wannan umarni sai dakarun dake rike da karnukan suka sake su
suka sake rugawa izuwa cikin dajin suna masu haushi da falfala azababben gudu su marwatu
suka bi bayan karnukan da gudu.Marwatu na cikin yin gudu sai raunin da ke gefen cikinsa ya
motsa yaji wani azababben zafi da zugi ya shige shi,bai san sanda ya fadi a kasa ba,nan da na
dakaru suka yanyame shi,koda ya kwaye rigarsa sai yaga ashe dinkin raunin ne ya farke,cikin
tsananin takaici marwatu ya kwarara uban ihu ya dubi dakarun yace Maza ku tafi farautar Imhal
kada ku dawo nan sai tare dashi,nan take kuwa suka bi bayan karnukansu da gudu shi kuwa
marwatu sai ya bude jakar guzurinsa ya dauko zare da allura gami da garin magani domin ya
sake gyara rauninsa.
Al,amarin Imhal kuwa,a ranar da jirgin ya kawo shi gabar teku sai ya dauko gawar zauwadu ya
fito da ita daga cikin jirgin ya nausa da ita izuwa cikin daji,sai da yayi tafiya mai nisa ya iso
gaban wani katon dutse sannan ya sauke gawar ya haka kabari ya binne ta.A sannan ne ya
kurawa kabarin idanu yana tuno duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninsa da zauwadu a
cikin darul maut,kawai sai hawaye ya fara zubo masa,yana cikin wannan hali ne ya jiyo sautin
haushin karnukan nan na darul maut,da yake yasan irin haushin nasu kuma ya san tsananin
gudunsu da irin mugun horon da aka basu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,kawai sai ya
mike tsaye zumbur! ya falfala da azababben gudu izuwa cikin dajin.
Imhal ya dage iya karfinsa da iyawarsa har yana tashi sama yana shallake duwatsu da
karyayyun bishiyoyi da suka fadi kasa amma koda ya waigo sai ya hango wadan nan karnukan
suna neman cimmasa sai kawai ya kara kaimin gudun,Ba zato ba tsammani sai yaga wani
katon rami mai tsananin zurfi a gabansa,kafin ya iya sarrafa kansa ya cije sai karfin gudun nasa
ya rinjaye shi ya fada cikin ramin yana mai kurma uban ihu.
TO AYI MIN AFUWA IDAN NA HUTA ZAN CIGABA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 7
Sa'ar da yayi kawai kawai kasan ramin cibiya ce ta ruwan teku amma yana tsunduma a cikin
ruwan sai kansa ya bugu da wani dutse ya sume.
Su kuwa karnukan suna isowa bakin ramin sukayi tirjiya suka fara haushi,sautin haushin nasu
ya cika dajin gaba daya,wanda hakan ne ya janyo hankalin dakarun Marwatu suka rugo sashin
da suke jin haushin cikin matsanancin gudu,suna cikin gudun ne suka hango karnukan sun
kewaye wani rami suna ta haushi,don haka suka kara azama don nufar inda ramin yake. Lokacin da dakarun marwatu suka iso bakin ramin wanda Imhal ya fada sai suka iske karnuka a
tsaye a wajen suna ta haushi sai suka leka kasan ramin,ai kuwa sai suka hango Imhal a
kwance akan ruwa kuma ruwan yana tafiya dashi ko motsi bayayi kamar gawa.
Cikin gaggawa wasu daga cikinsu suka gangara kasan ramin suka shiga cikin ruwan suka
tsamo Imhal,suna fitowa dashi sai suka ga yana numfashi don haka sai suka yi sauri suka
turmushe shi suka daure hannayensa da kafafunsa da sarkoki sabo da sun san cewa in har ya
farfado baza su iya kamashi ba.
Nan take suka daure shi suka kai shi can inda Marwatu yake zaune,da zuwan su suka iske
Marwatu a kishingide ya gama dinke raunin dake cikinsa ya saka magani,koda Marwatu yaga
dakarunsa sun dawo dauke da Imhal a daure cikin sarka sai ya kamu da tsananin farin ciki
mara misaltuwa ya mike tsaye zumbur!ya kwarara uban ihu irin wanda manyan barade ke yi
afilin yaki yayinda suka samu nasara akan abokin gabar su,kawai sai yasa aka warbar da Imhal
gefe daya a kasa aka kyale shi har sai da ya farfado daga suman da yayi.
Koda Imhal ya bude idon sa yayi arbuna da marwatu zaune a gabansa yana yi masa
murmushin mugunta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya yunkura da nufin ya gudu amma
sai ya kasa sakamakon sarkokin da suka daure kafafuwansa da hannayensa
AYIMIN AFUWA ZAN CIGABA
TO AYIMIN AFUWA ZA CIGABA IDAN NA HUTA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA8
Nan take yaji wani irin bakin ciki ya lullube shi,ya ayyana a ransa cewar da ma ya mutu a
kokarin wannan guduwa da yayi daga kurkukun Darul maut da ya fiye masa alheri.
Kawai sai yaji marwatu ya bushe da dariyar mugunta yana mai nuna shi da yatsa,daga can sai
marwatu ya fara yiwa kansa kirari yana cewa Nine sa gudu maganin ki gudu,kuma nine sarkin
darul maut mai RIJIYA GABA DUBU,ya kai wannan takadarin jarumi,kayi Sani cewa inda ba
muyi nasarar kamoka ba da sai Na kashe kaina sabo da Kaine kadai jarumin da ya karya
alkadarina,ya sami nasarar guduwa daga kurkukun darul maut Wanda Na shafe shekara da
shekaru INA gadinsa,ban taba samun rauni ba a rayuwata sai wannan karon don haka idan
muka koma darul maut sai Na dandana maka azabar da bantaba dandanawa wani fursuna ba
sai Na shigar da kai RIJIYA ta azaba mai GABA DUBU.Koda gama fadin haka sai marwatu ya
mike tsaye yaje inda jarumi Imhal yake zaune ya shammace shi ya gabza masa wawan naushi
a fuska ,nan take Imhal ya sulale a kasa sumamme.
lokacin da Imhal ya farfado sai ya tsinci kansa a cikin jirgin ruwa ga marwatu da dakarunsa sun
kewaye shi,yana daga kansa sama ya dubi gabas sai ya hango kurkukun Darul maut a nesa da
su kadan,jirgin Na tafiya acikin teku,al'amarin da ya jefa Imhal acikin bakin ciki kenan a cikin
zuciyarsa yace Yanzu mene ne amfanin wannan yunkurin guduwar da nayi?wai shin menene
dalilin da yasa bai kashe kansa ba ya huta da wannan bakin ciki?yana cikin wannan tunanin
zuci ne jirgin nasu ya I so kofar kurkukun Darul maut,nan take aka tsaida jirgi ya tsaya cak!
sannan dakaru suka kama Imhal suka tashe shi tsaye aka fitar dashi daga cikin jirgin ,shi kuwa
marwatu bai fita daga cikin jirgin ruwan ba sai ya dubi dakarun da suke rike da Imhal yace dasu
Kada Ku kaishi bangaren dakin fursunoni Ku kaishi dakin RIJIYA GABA DUBU Ku daure shi a
jikin bango da sarkoki Ku barshi a haka,kuma kada a bashi ruwa ko abinci har sai Na dawo,
Zanci GABA in Na huta
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA9
Na tafi gidan Sarki domin inyi masa albishir bisa nasarar kamo Imhal da mukayi,koda gama
fadin haka sai marwatu ya juya ya umarci masu tukin jirgin da su juya akalar jirgin su nufi cikin
gari,ba tare da gardamar komai ba kuwa suka bi umarninsa suka juya jirgin suka kama hanya
akan ruwa. Su kuwa dakaru sai suka shigar da jarumi Imhal cikin kurkukun,suna shigewa aka mai da kofar
Gidan aka rufe,tayi kara mai karfi tamkar an kulle kofar birnin gaba daya,yayin da aka zo
wucewa da jarumi Imhal ta bangaren dakunan fursunoni suka kyalla I do suka hango shi sai
suka kama ihu da shewa suna yi masa tafi da jinjina sabo da kasancewarshi fursuna Na farko
da ya taba samun nasarar guduwa kuma ya tsira da rayuwarsa.Koda fursunoni suka ga an nufi
dakin RIJIYA GABA DUBU da Imhal sai gaba dayan su jikin su yayi sanyi suka kamu da
tsananin tausayinsa,ba komaine ya haddasa hakan ba face sanin cewar duk mutumin da aka
shigar dashi cikin
ayya frnds ayimin afuwa wlh fefar littafin ta tsakiya banganta ba amma bari nayi wani postn din
Na cigaba yanzu
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 11
Koda Imhal yazo nan a zancensa sa aljani Sautil makatur ya bushe da dariyar mugunta a karo
Na biyu yace, Sai kayi kokari ka fita daga nan din cikin hayyacinka yadda zaka iya bude
idanunka ka kalli maharbi Imzanu. Koda gama fadin haka sai aljani Sautil makatur ya bace bat
tamkar bai taba wanzuwa ba acikin dakin,nan fa Imhal yaci gaba da jin tsananin zogi da radadin
Harbin da kunamun nan suke masa har ya dinga jin kamar ya yanke duk wadan nan kurajen na
jikinsa wadan da suka duri ruwa, gashi kuma a wannan lokacin yunwa da kishirwa sun addabe
shi sai birgima yake yi a kasa yana mutsu- mutsu,kai komai rashin tausayin mutum idan yaga
Imhal acikin wannan hali dole ya tausaya masa, haka dai Imhal ya kasance acikin wannan hali
har sai da dare ya raba sannan aka bude kofar dakin RIJIYA GABA DUBU aka shigo aka baiwa
Imhal wani irin ruwa mai tururin zafi acikin kwarya,Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da
suka ce, Wanda yake cikin ruwa ko takobi aka mika masa kamawa zai yi, domin ana mikawa
Imhal wannan ruwa a lokacin da yake fama da kishi sai kawai ya karbi kwaryar ya kafa a
bakinsa ya fara kwankada duk da cewar ruwan yana kona masa harshe kuma yana mugun war
I sannan bashi da dadin dandano,shi dai kawai burinsa ya jika makogwaronsa ya kawar da
kishirwar da ta addabe shi. Hakika rashin Sani yafi dare duhu! Inda Imhal yasan abinda sai biyo
baya da bazai sha wannan ruwan ba,gwara ya gwammace kishirwa ta zama ajalinsa domin
yana gama shan ruwan da kamar dakika daya sai cikinsa ya murde matuka ya kama ciwo yaji
kamar ana daddatsa hanjin cikinsa,bai San sanda yaci gaba da birgima ba a kasa yana rusa
ihu,idanunsa kuwa suka kumburo sukayi bulu-bulu kamar zasu fado kasa.
Ayi min afuwa zanci gaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 12
Kurajen dake jikinsa kuwa sai suka cigaba da tsananin zogi suna kara kumbura, Daga can
kuma sai Kurajen suka dinga fashewa da Kansu suna zubar da jini gami da wani irin mugunyar
ruwa mai doyi, nan take kurajen Na gama fashewa gaba daya sai ya sume, bai sake farfadowa
ba sai da sanyin asuba ya buga.A sannan ne aka sake bude kofar dakin aka kawo masa abinci
loma daya da ruwa mukurwa uku acikin wani Dan karamin kofin kasa, Haka dai aka cigaba da
ganawa Imhal azaba kullum, daga cikin azabobin da aka tanada na cikin RIJIYA GABA DUBU,
har tsawon kwana goma sha hudu ya zamana cewa ya rame matuka ya lalace kuma ko ina a
jikinsa duk ciwuka ne babu kyan gani,hatta fuskarsa ma sai da tayi muni amma duk wannan
tsananin azaba da yunwar da ake yi masa horo da su bash sa ya mutu ba.
A Ranar kwana na goma sha hudu ne da sassafe aka bude dakin RIJIYA GABA DUBU aka fito
da jarumi Imhal a cikin matukar galabaice tamkar an dauko tsumma domin ko kadan babu
kuzari a jikinsa da kyar ma yake iya taka sawayensa, da yawa daga cikin fursunonin Gidan ma
da aka zo za a wuce dashi ta gabansu kasa shaida shi suka yi saboda yadda kamanninsa suka
sauya da kuma yadda ya rame matuka, Koda fursunoni suka shaida shi sai suka kamu da
tsananin tausayinsa harma wasu suka zubar masa da hawaye, nan dai aka fitar da Imhal daga
cikin kurkukun gaba daya aka saka shi acikin jirgin ruwa a daddaure cikin sarkoki, kai kace wani
katon goggon biri aka kamo, kuma suma dakaru DUBU ne suka kewaye shi acikin jirgin ruwan
don kada yayi wani yunkuri na guduwa, nan take aka nufi Gidan sarautar birnin kisra da wannan
jirgin ruwan,Wannan shine abinda ya faru da jarumi Imhal bayan ya gudu daga kurkukun Darul
maut an kamo shi ansake dawo da shi.
Al'amarin shugaban dakarun kurkukun Darul maut kuwa, wato sadauki Marwatu, lokacin da
yaga sun dawo da jarumi Imhal kurkukun cikin nasara sai ya tafi izuwa gidan Sarki Gurzalu
yana mai tsananin farin ciki.
tayi min afuwa zan cigaba idan Na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 13
Da Isar sa gidan sarautar kuwa aka yi masa iso a wajen Sarki, take Sarki yayi masa izini ya
shiga har cikin turakarsa inda ya iske shi tare da matarsa Muzaina a zaune acikin farin ciki da
nishadi suna ciye-ciye da shaye-shaye, da isowar Marwatu kusa da kujerar da su Sarki suke
zaune sai ya zube kasa kamar zai yi masa sujada ya kwashi gaisuwa sannan ya dago kai da
nufin yayi bayani amma sai Sarki Gurzalu ya daga masa hannu yana mai yi masa muni da yayi
shiru,Sarki Gurzalu ya mike tsaye ya tako har gaban Marwatu ya kama kafadun sa ya tashe shi
tsaye sannan ya dube shi fuskarsa cike da annuri yace, ya kai Marwatu kayi sani cewa a iya
tsawon aikin da kake yi mini a kurkukun Darul maut baka taba yi mini aiki mai kyau ba kamar
wannan na kamo jarumi Imhal, domin inda ya samu nasarar tserewa da ya karya alkadarinmu
gaba daya,kuma da ya rusa tarihin da mahaifina ya kafa akan kurkukun Darul maut, tabbas
sakamakon da zai biyo bayanka shine mutuwa, to amma yanzu da ka samu nasarar kamo shi
na baka kyautar dinare dubu dari biyar gami da nayi mata da maza guda dubu, sannan kuma
na baka gidan gona ta na birnin Saihur, Koda Marwatu yaji wannan bushara sai ya dimauce ya
sake zubewa kasa yana sumbatar kafar Sarki yana mai yin godiya, Sarki Gurzalu ya bushe da
dariyar murna yace, Tashi ka tafi abinka ya kai Marwatu, domin ka kamo min zakin da idan ya
balle daga daji zai iya hallakani ya kawar da dukkan zuri'ata ta yanzu, Nan take Marwatu yayi
sallama da Sarki ya mike tsaye da nufin ya juya ya fita,sai matar Sarki Gurzalu ta kirawo
sunansa ya waigo sannan ta dube shi tace, Ya kai Marwatu kayi sani cewa nayi maka matukar
farin ciki matuka da kasa aka kai wannan babban makiyi namu dakin RIJIYA GABA DUBU na
kurkukun Darul maut, lallai acigaba da yi masa azabobin cikin RIJIYA GABA DUBU har tsawon
kwanaki goma sha hudun nan kafin as tafi da shi birnin misra inda Sarki zai kashe shi a gaban
miliyoyin jama'a a lokacin GASAR JARUMTA, Koda Muzaina tazo nan a zancen ta sai Marwatu
ya risina yace,Angama ya shugabata sannan ya juya ya fice daga cikin turakar.
zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 14
Faruwar hakan ke da wuya sai ga wata tsaleliyar budurwa ta kunno kai cikin turakar, Hakika
wannan budurwa ta cika dari a fagen kyau domin sau tari idan ta fito cikin gari bata wucewa
tabar mutane lafiya dole sai kaga hadari na faruwa, domin Wanda ke kan jaki ko doki zai
bangaje masu tafiya a kasa bai sani ba,wadanda ke dauke da kaya a Kansu zasu saki kayan su
zube bash sani ba,Kai bama maza ba hatta 'yan uwanta mata idan suka yi arba da ita sai kaga
sun Wangame baki suna dalalar da yawu basu sani ba,sabo da tsabar kyawunta da burgesu da
take yi,Ba wata bace wannan budurwa face Gimbiya LAMIRAT 'ya guda daya JAL! a wajen
Sarki Gurzalu, A duniya babu abinda Sarki Gurzalu yake so dama da Gimbiya LAMIRAT, ba don
komai yake tsananin sonta ba sai saboda halayenta sun zo iri daya da NASA,wato ko kadan
lamirat bata son talakawa kuma sannan bata da imani da tausayi ko kadan,Laifi kankani bawa
ko baiwa za su yi mata tasa a gaba musu azaba mai tsanani ko kuma tasa a sare musu
hannaye, idan ma ranta ya baci sosai da kanta zata zare takobi ta sare musu kai,Gimbiya
lamirat ta gado mahaifinta Sarki Gurzalu a tsananin Mark da iya yaki sannan tana taba samun
tsananta gaba akan makiyi, domin idan tasa shi a gaba sai taga bayansa, Bisa wannan dalili ne
take yiwa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai na birnin matukar kwarjini suke tsoron tunkararta da
batun soyayya ko aure, Ita da Kanta Gimbiya lamirat ta dauke alkawarin baza ta auri wani
namiji ba face Wanda ya fita bata,karfin damtse kuma ya cinye gasar jarumtaka ta nahiyar akan
mahaifinta tunda mahaifinta shine ke rike da kambun gasar sama da shekaru ashirin ankasa
samun Wanda zai karbe daga hannunsa.
Lokacin da Gimbiya LAMIRAT ta shigo cikin turakar Sarki Gurzalu ta iske shi tare da
mahaifiyarta Muzainat a zaune cikin farin ciki bayan taba fitar sadauki Marwatu sai ta karasa
garesu cikin tsananin murna ta fada kan kirjin Sarki Gurzalu ta rungume shi tana mai cewa, Ya
kai Abbana ina mai tayaka murna da aka samu nasarar kamo wannan babban makiyin namu
bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut kayi sani cewa naso ace ka bani dama naje har Darul
maut na kashe wannan makiyi