Showing 12001 words to 15000 words out of 18852 words
Chapter 5 - FYADE COMPLETE BOOK 1 HAUSA NOVELS BY MAMAN TEDDY.pdf
Ware ido kowa na Wurin yayi cikin mamakin raunin hankalin Wannan Yarinya . Wata ce mai
zafin Rai ta miƙe a zafafe don ta lura A'isha Farida zata ja masu sallama da kora gashi a gaban
Aminin Mai Companyn take wannan Aikin ,suma duk a tsorace yau suke , don daga mai
Companyn har abokin nasa Sir Aslaaam ba mutunci ne dasu ba . Duka iskancin da A'isha keyi
a idon sa . Amma kaman bai ga komai ba ,kallon ta kawai yake bai nuna ko in kula ba .
Amma ke wacce kalar Jakar Yarinya ce ? Cewan Gift Dake ƙara tighting belt ɗin ta . Juyowa
A'isha Farida tayi cikin Wani irin kallo don Har ga Allah bata san ba'a siyayyar Ɗaiɗai A
Company ba . Cike da Mamaki A'isha Farida tace " Ke Me nayi Miki zaki zage Ni ? Bani kika
zagaba Uwar ki wacce kika bari a gida kika zaga.! Wani irin yunkuri Gift tayi tana Shirin damƙo
Wuyar A'isha Farida wanda ko gyezau bata nuna tsoro ko ɗarrr Ba .wannan yasa Aslaam ƙara
Sakin baki yana mamakin wannan Wacce irin tsilalliyar Yarinya ce ,bin ƙirjin ta yayi da kallo
kamin ya kalli Fuskar ta ,mtswww Small Kid Yarinya ƙarama sai Rashin kunya abun da yace
kenan a zuciyar shi kamin ya dakatar da Gift yana cewa " A ba A'isha Farida Kayan taje dashi
zai biya . Juyowa A'isha tayi cike da mamaki kamin ta wangale baki tana cewa "Lahhh Wai na
tafi da kuɗin duka ? Ka saya mawa Mama ta Maggi ? Gyaɗa kan sa Yayi Alamun Eh don baya
cika dogon magana .Kai wai dama ya'yan masu kudi suna da kirki irin ka ? Na gode Yaya na ,
na gode halin ka ba iri ɗaya da Wannan Shegiyar Kafurar ba , baƙa ƙirin fuskar ta har duhu
yake tun kamin ta jita a wutan .....Shiiii Enough please.! Ya katse ta cikin hanzari jin tana shirin
cin ma Gift mutunci . Ya isa Ɗauka ki tafi . Ai gashi nan a hannu na ,A'isha tayi maganan tare da
juyawa tana kokarin ficewa daga Companyn . A'a Ai Duka Ƙwalin zaki dauka .
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe A'isha Duka Yaya na Zan dauka , Allah ya baka abun da kake
so na gode . Murmushi yayi har ta gama addu'an ta,ta fice daga reception din . Tare da barin
Companyn da Ƙwalin Maggi Star .
**
Abuja
3:20pm .
Tun da ta ƙara Wayar a kunnen ta take Sauraren maganan nasa da yake mata cike da baƙin
izza da Miskilanci . Numfasawa tayi tare da sauke Muryar ta tamkar Wanda take magana da
Yaron goye . Aaryaan Ka tabbata gobe zaka sauka a Nigeria?. Sai da ya dau kusan mintuna
uku sannan a takaice ya ba Hajiya Kubrah Amsa da Yeah ". Ok ya....Mum Ina Wani Aiki yanzu i
Will call you later. Take care of yourself Okay? . Datse Kirar yayi yana cigaba da Aikin sa ta
laptop . Dafe kan sa yayi yana tunanin abubuwa . Mum I'm very sorry for what I did . Baa
Son Raina bane bana Son zama tare dake , kawai Zuciya ta ce kullum take sakani nake nesa
dake wanda ban san dalilin hakan ba . Tun tasowa ta nake jin hakan har yanzu . Buhhh I'm
sorry mummy i love You. Maganan yake shi kaɗai Don yana keɓantacciyar Ɗakin sa na Nan
malesia . Tsintar kan sa yayi da kallon Hoton Hajiya Kubrah kamin ya rufe laptop ɗin sa yana
miƙewa tare da cewa " Inshallah A gobe zan sauka a gida nigeria . I know my mom will be very
happy. Ɓangaren Hajiya Kubrah kuwa tana sauke wayan Kallon Ƙanwar ta tayi Hajiya Leela
kamin tace "Hajja Leelah Abun fa na Aaryaan is worst ,zuciya na zata buga . Ina tsoro kar
yasan Gaskiya . Cikin Sauri Hajja Leelah ta dafa Hajiya Kubrah tana cewa ":Cool ur mind Mum
Aryaan . Kawai nafi ganin girma ne yazo masa Kin san kowa da kalon nasa girman ,wani zaiji
ya raba jikin sa dana iyayen sa ,wani kuma A lokacin yake daɗa ɗafa ma iyayen sa . Kar ki
manta Aryaan tun da ya kammala primary school ku ka tafi Abroad baku dawo nigeria ba sai da
ya kammala deegre ɗin shi na Farko . SO dole ba lallai ya kasance yana jin dadin zaman
Nigeria ba . Kinsan Rayuwar ya'yan Turawa ya sani , Su daga sun kai misali suke barin gidan
iyayen su su koma nasu .
Huhmmm Sauke ajiyar zuciya Hajiya Kubrah tayi kana tace " Ban san ya akayi Allah ya jarabe
Ni da Soyayyar Aryaan a zuciya ta ba , tamkar nice na kawo sa duniya , soyayyar da nake
masa Ko mahaifiyar sa bata masa irin sa ,don da tana masa Ni Nasan da yanzu ta ne meshi .
Leelah ce tayi saurin cewa " Kin manta mun mata farra'u tsakanin ita da mijin ta da Ɗan cikin
ta? Kin manta me mukayi ne? . Na sani Hajja Leelah amma me yasa Aikin ya ki tasiri akan
Aryaan ? Me yasa ? Na fara tunanin duka ƙarya ne Leelah . Hajiya Kubrah Wallahi ba ƙarya ,ki
duba fa kiga ke kike juya cikin gidan nan . Aaryaan ne dai kawai . Yanda yake nuna mun tamkar
ya zauna da mahaifiyar sa ta faɗa masa abubuwan da nayi mata , kuma Nasan fa bai san Ni
banice mahaifiyar sa ba . Ƙwallah ne ya fara sauka ma kuncinta tana saka taffan ta tare da
gogewa . Ba gobe bane yace zai dawo? A gobe Inshallah zan tafi Jigawa wurin mutumin nan na
sanar masa dawowar Aaryaan , Idan kin rufe ido kin sa masa a binci yaci to, idan kuma kin ƙi ke
kina tausayin Ɗan ki shikenan, Sai ma Yasan bakyece mahaifiyar shi ba zaki ga sauyi . To Hajja
Leelah ki amso wannan karon Abun is to much Wai Har Hajiya Lubna ta fini matsayi akai na ,
Yafi ganin ta da kima a kaina . Ya dauki Yusraht tamkar Ƙanwar sa ta jini . Ko da yake ai hakan
yake Amma mahaifiyar Yusraht Ƙanwar Mahaifin sa ne kaɗai , Alh Abdu Kareem me yasa yake
zama a can Gidan Fiye da gidan mahaifin sa ?. Kuyi hakuri Hajiya Kubrah Za'a yi maganin
komai , Wallh in so kike yi idan Aaryaan ko wani irin umarni kika basa kar ya kyatara ba zai yi
ba . Kawai ki bani daga yau zuwa gobe.
**
9:01pm .
A hankali take Gyara ƙwanciyar nata tare da Kallon Mum Lubna dake rufe ta da Blanket .
Yusraht Sleep well . Mumy Good Night. Juyawa Mom Lubna tayi zata fita taji Yusrah ta riƙo
Hannun ta , Wannan yasa ta juyowa tana kallon ɗiyar nata .! Mummy Wai me yasa tun tasowa
ta Baƙwa jituwa da Daddy? Kullum kaman akwai wani Abu a tsakani ku amma kuma ɓoye mana
, a tunani na a da don ina yarinya ce ki shiyasa kike ƙin faɗa mun , Amma mai yasa ba ki faɗa
mawa Ya Nawaaz ba ? Idan shi namiji ne ai Ɗan ki ne ,to Ni a yanzu na isa rufe ko wani irin sirri
ne dake tsakanin Iyayena , please Mummy ki faɗa mun a yanzu shekaru na ashirin da Huɗu na
cancanci Nasan damuwar ki dana Daddy . Wani irin bugawa zuciyar Hajiya Lubna yayi cikin
ƙaƙaro murmushin dole ta sa hannun ta tana haɗawa dana Yusrah , Yusraht babu komai
tsakanin mu me yasa kike Wannan tambayar , Kawai dai kin Daddyn ki ba mutum ne mai yawan
surutu ba shi yasa zaki ga Bama fira tsakanin mu . Amma mum ai muna fira idan muna a tare ,
Tsakanin ku ne nake ganin tamkar akwai wani Abu . Babu komai Yusrah ki yarda da abun da na
faɗa Miki . Shiru Yusrah tayi kana tace " Na yarda Momy good night . Rage hasken Fitilun Ɗakin
tayi kana ta fito tare da rufo ƙofan Bedroom ɗin nata .
**
Bayan A'isha Ta koma gida a lokacin iyayen Lauratu sun bar Gidan ,don haka babu kowa sai
masu ba Mama Lantana haƙuri . Anan ne A'isha take jin gorin da Laminde tayi ma mama
Lantana tare da cin mutunci wai ba'a san A salin su ba . Farin cikin Maggin da Ta samu kyauta
ne ya koma ciki . Ɗaki ta nufa ba tare da ta ce komai ba ,jikin ta yayi sanyi tausayin kansu ya
kamata . Zama A'isha tayi tana tunanin yanda Mama Lantana ke shiga Wani Hali duk idan ta
tambaye ta ina ne Asalin su . Wannan kuma yasata yanke hukuncin har abada ba zata kara
kuma tambayar ta komai ba . Wuraren Yammacin ne A'isha ta fito daga Dakin su . A Madafi ta
samu mama Lantana tana Aikin girkin yamma . Mama Sannu da Aiki . Cikin fara'a mama
Lantana ta juyo tana cewa " A'isha kin tashi barcin , Yau baki je islamiyya ba , Kina ta barci
yanzu nake shirin na tashe ki bakyau barcin yamma . Shiru Aisha tayi a tunanin Mama barci
nake yi kenan ? Tunanin Rayuwar mu nake yi . Kallon Fuskar mama Lantana tayi ganin yanda
ta nuna uwa duniya ba'a yi wani Abu ba ɗazu na rikici . A'isha ta lafiya tunanin me kike yi?
Abinci ne zaki ci? . Mama Lantana ta jero mata Wannan tambayoyin tana jirar Amsan A'isha
wanda gani tayi A'isha Farida ta rungume Ta tsam tana fashewa da kuka . Mama na amince mu
bar garin nan A yau zamu tafi ,zan je Aikatau ɗin , Ina so na zama Kaman saura masu gani da
idanun su a ko wani lokaci , ina so nan kusa na fidda ki cikin damuwar da muke ciki tun tuni . A
hankali Mama Lantana tasa Hannu tana Ɗago Fuskar A'isha . Murmushi tayi mata cike da son
kawar mata da damuwa . A'isha kwantar da hankalin ki ,bakina Son zaman nan ba ?. Mama A
yau zamu bar Garin nan mu tafi can , Kibar Inna Hansai ta sai gidan da komai kawai . Tana
Gama faɗin haka kamin ta ji na bakin Mama Lantana ta juya tana shigewa ɗakin ta don harhada
kayan su .
Cikin Sauri mama Lantana ta nufi Dakin don ta rarrashi A'isha ta bari sai zuwa Safe su nufi
Tasha su hau moto da kayan su a yammacin nan kuma ta samu dalallin gidan ya basu kudin .
Ɓangaren Aryaan kuwa da Hajiyoyin sa biyu Nahila da Bie-bie Tun bayan keorar sa da Mom
Kubrah tayi ya wancakalar dasu , a ranan babu mutum guda da ya iya Saduwa da ita da sunan
sex . A daddafe ya kwana yayin da Safe ya shirya tare dasu don su dawo gida nigeria daga nan
kowa tayi ta kanta. Sai kuma sun haɗu a ɗaya daga Gidajen sa na nigeria su cigaba daga inda
suka tsaya .
Malesia Airline 9:00am
Da misalin Wannan lokacin ne jirgin su ya ɗaga zuwa Gida nigeria sai dai muce Allah ya sauke
su lafiya .
**
NAAWAZ kuwa Tun da ya amfa Taskon Hajiyar sa ya faɗa hannu kwanan su uku sam taki barin
shi ya fito . Niko abun mamaki yake bani , banda jaraba da iskanci Allah ya rufa maku duk son
Iskancin kuyi aure mana ku huta . Amma duka sun gummaci su rinka biyan buƙatar su a
hannun matan banza da Wofi har da iyayen su . Suyi ta sukwanan yan banza . Yau jin Aminin
nasa yana Hanya kuma Ɗan Uwan sa cousin din sa Wato Aaryaan yasa shi tattarawa don dole
yana kimtsawa don ya dawo Abuja . Gentle Guy ƙyaƙyƙyawan matashi shi dama shigan sa bai
wuce track suit baya son kayan nauyi sam. Fuskar sa cikin baƙar tabarau yake Wanda yaƙara
ƙayatar da kyawun sa . A tsakiyar compound din gidan Hajiya Nafeesa take riƙe da hannun sa
,a bakin Moton sa sam taƙi rabuwa dashi . Hannun ta tasa tana Kamo Kaciyar sa tare da shafa
tana murzawa tare da kumshe ido tana masa Wani irin kallo . Zan yi kewar ka sosai . Tana
maganan tana cigaba da mutsikar Ƙatuwar Buran sa , tare da Karkaɗa Twins ɗin sa tana wani
lasar labɓan ta . I Will come back soon inshallah . I'll be waiting Nawaaz ,ka dawo da wuri don
Allah. Girgiza kan sa yayi yana sakar mata Murmushi don shi kan sa ya ji dadin mu'amalar tasu
in a just two days ta shayar dashi mamaki ,bai taba gani mace Harija data amsa sunan ba
kaman Hajiya Nafeesa . A haka daƙyar kaman ba zata bar sa ba ya fito gidan .
**
Kaman yanda Mama Lantana tace tun safe suka bar garin da komai nasu tare da Tarkatawa
zuwa Garin Abuja .wanda tun kamin su isa Da yake ita mai jama'a ce aka saya mata gida dan
dai dai karami . A daga Waje kuma wani babban Shago ne wanda zata rinƙa sana'ar Sayar da
Abincin ta kaman yanda ta saba . Da sauran rana Suka isa Abuja tun shigar su gidan A'isha ke
bin gidan da kallo a lokaci guda tunanin sa ya fara dawo mata Ƙwallah ne ya ciko idanun ta a
zuciyar ta cewa take " Shikenan Yanzu ba zan ƙara Ganin ka ba ? Amma kai kace mun zaka
dawo.! Kana ina ne ,kana ina ne ɓoyayyen Masoyi na?. A wannan rana a ɓoye ba tare da
Mama Lantana ta lura ba A'isha Farida tayi kuka iya kuka har ta gode Allah . A haka ta fara
sabuwar rayuwa a garin da Batasan Yaya yake ba. Satin su guda ta shiga Islamiyya , ana haka
kuma Inna Hansai ta taho ,anan ne take sanar da Mama cewa Hajiyar Gudan ta amince da
aikatau ɗin nata . Wannan yasa a washe Gari Inna Hansai ta dauki A'isha Farida da kayan ta
tana ma Mama Lantana sallama . Wannan shine rabuwar su ta farko tun da suke a rayuwa .
Kuka A'isha Farida take yi mama Lantana na kukan itama tare da rarrashin ta ,kana tayi mata
Alƙawarin rinka zuwa Tana dubata duk idan ta samu lokaci, rarrashin ta take yi tare da cewa "
Aikin wata shida ne Hajiyar ta Ɗauke ta .
Gidan Alh marshal Abdu Kareem Gida ne mai mahaukacin Girma ga ma'aikata kowa da aikin sa
, kuma uniform suke sakawa a dokan Hajiya Kubrah kenan don tace bata son tana ganin
tsummoki wannan yasata ko wani ma'aikacin ta yake saka uniform ,kalon na masu shara da
goge goge da ban ,na masu girki da ban . Tun da A'isha Farida ta fara Aiki a gidan Take ganin
tijara wanda bata taɓa ganin irin sa ba . Amma haka tasa hakurin da bata dashi don dole .
Yanda Hajiya Kubrah ke ma yan Aikin ta tamkar bayin ta . Har da Ma'aikata masu yi masu
massage ( Tausa) . Ke yanda take mulki ko sarauniyar Ingila Albarka .
5:pm .
Tun wuraren ƙarfe Uku na yammaci take kitchen ita da Adda Maryama , Itama mai girki ne
amma babbace tana da shekaru ba kaman A'isha Farida ba. Ihu take ji da Shashanci irin na
ya'yan Hutu yayan gata ,rabi da kwatan maganan su bata fahimta , ta dai fahimci turanci suke yi
,amma kuma American English Kuma ita bata iya ba wannan yasa bata mai da hankali don ta
saurara . Kee ke A'isha..! Taji Adda Maryamu ta kirata a hankali . Ɗago idanun ta tayi tana
kallon ta kamin tace me ya faru ? . Ki fita ki kai wannan Dinning room suna nan a falo Sir
Aaryaan fa ya dawo ,bakiji firar su ba gayi can , ki bi a hankali har ƙasa ki gaida su , basa da
kirki ,kuma har da Tsegalallun ƴammatan nan a wurin ,idan kin kammala sai ki masu magana
Kinji . To Adda Maryamu amma Ai Nasan shi zai kasance mai kirki ba kaman Mahaifiyar sa ba
Hajiya Kubrah .
Saurin kama baki Maryamu tayi tana cewa " Kee Wane ? Ai wannan ya fita kaman sama da
ƙasa ,ga rashin mutunci ga Miskilanci ke halin sa sai mun zauna . Hummm A'isha Farida tace
tare da Ɗaukar wani Basket dake dauke da different dishes . Nufo Falon tayi kan ta tsaye fuskar
ta a sake idanun ta a sama ita har ga Allah duk ta kosa tazo taga masu magana da American
English haka don bata fahimta . Wow .! Ta furta cikin sauri tare da nufar falon don ƙamshin
Turaren wurin yayi mata dadi sosai kaloli daban-daban alamu ya nuna mutane mabanbanta a
wurin .
Cikin sauri ta risina a daga tsakiyar falon tana kallon Hajiya Kubrah dake tsakiyar Falon . Hajiya
Sannu da Hutawa.! Duka a tare suka ɗago suna kallon ta jin Sanyayyar Muryar mai zaƙi da
daɗin saurara . Juya kai Hajiya Kubrah tayi tana cigaba da Shafa Kan Yusrah tare da cewa "
Yanzu ai kuka kuma ya ƙare tun da Cousin ɗin naki ya dawo ko?. Inda sabo A'isha ta fara
sabawa da wulaƙancin Hajiya Kubrah wannan yasata juyawa tana kallon ƙasa tare da cewa A'a
Aaa A'ammm Sannun ku da Izuwa .!
Saurin Miƙewa Yusraht suka ga tayi kaman wanda aka mitsina kece?? Tayi magana da ƙarfi
tana nuna A'isha Farida da Hannu . Ɗago kai A'isha tayi a lokaci guda ta tuno da Yusra da
kuma marin Yusra da tayi .wani irin tsoro ne ya kamata Wannan yasata saurin juyawa tana
kallon Gyefen ta Aslaam ta gani yana bin ta shima da kallo . Kai ne ka saya mun me tauraro
ko? Tayi maganan kamin ya bata amsa ta juya tana kallon ɓarayin sa INDA Nawaaz yake
Shima ita yake kallo ,tuno da rashin