Showing 3001 words to 6000 words out of 23992 words

Chapter 2 - Rayuwar Raihana Part 4 chapter D end book Complete Hausa Novel By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf


karatunsa baisan cewa Daddy na ganin sa ba.
Tana kuma iya tuna ranar da Abida ta kifa mata pampas na kashin Aziza a fuska ya zo ya
gani bai ce komi ba, bai nuna komi ba, bai wa Abida koda fada ba. Sai YAYA KHALIFA ne yayi
hakan.
Tun zuwanta gidansu kafin ya bar gidan, kalma wannan koda ta gaisuwa ce bata taba
hadasu ba. Tun daga lokacin ta bawa Himu matsayin wani mutum mara kirki.
Don haka ne fuskar da ya karbeta da ita a Singapore ta bata mamaki kwarai, ta kuma
sanyata cikin shakku, akan tunaninta na baya a kansa.
A ranar da ya ganta matsayin matarshi a ranar ya hada jikinsa da nata, ya yi mata sumba mai
tsayawa a zuci, ba tare da ta yi wani abu don ta ja hankalinsa ba. Ba za ka taba yin hakan ga
macen da kake kyankyami ko baka so ba.
Wannan ya nuna cewa Ibrahim ya karbeta a matsayin mata ba don kyale-kyalenta ko wani
abu special data ke da shi ba.
Wannan tunanin da ta yi yanzun, sai ta ji haushin nasa da take ji na rabata da Informatics
yana decreasing a hankali cikin zuciyarta. Zuciyarta ta ci gaba da yin sanyi, jikinta ya yi la’asar.
Ta samu kanta da mikewa don cika umarninsa. Ba don tsoron kuli-kulin kubrar da yace zai yi
da ita ba.
A’ah, sai don wani kima da daraja har ma da martaba da ya kara a idaniyarta. Yanzu ma
taunar gefen gyalenta take cike da tunani da bege mai yawa dake mamayar ta.

Duka kofofin guda hudu dake cikin babban falo a rufe suke da mukulli, sai daki daya wanda
ya fito daga cikinsa kenan, kuma can ta ga kayanta a kan gadon dakin.
Cikin nauyin ido da nauyin zuciya Rayhanah ta daga ido tana karewa cikin dakin Ibrahim
kallo. Daki ne sosai irin na manyan proffessionals din Amurka, babu tarkace ko kankani.
Komai yana ma’adanarsa, na’urori da yawa bata san na menene ba duk da sunfi kama da
computer ta san ba duka ne computer ba, sassanyan kamshi ke tashi na room fresh din
rasp-berry.
Dakin da dumi yake sosai, na’urar dumama daki na aiki. Tun ganin ta dashi a Singapore taji
tana so ta san menene sirrin gayun Ibraheem? Don ita dai a kafatanin rayuwarta bata taba
ganin mutum irinsa ba (mind blower!).
Ashe amsarta tana toilet da ta rage kayan jikinta ta shiga don yin wanka.

Abubuwan da ta gani a kan cabinet din bandakin tunda take a Singapore ba ta taba gani ba
ko a shaguna. Hatta macleans din da yake amfani da shi daban ne, kayan aski da after shave
designer din harrods, inner wears da towels a jere cikin wata cabinet din.Bath foam, bath gel da
exfoliating gels kala-kala duka designers. Kayan gyaran akaifa daban, na gashi su ma daban
(Argan).
Rayhanah sai ta zama ‘yar kauye fitik! Ta kuma samu amsarta da wurwuri. Ba komai ne sirrin
haiba da kamalar Ibrahim ba tsafta ce, amma mai tsada.
Sai ta ce a ranta,
“Matarshi ta more”.
Zuciyarta ta jefo mata tambaya a take,
“To wace ce matar tasa in ba ke ba?”
Ta kyabe baki ita kadai abin dariya, a fili ta ce,
“A’a, ni a suwa? Ba ya ce hudu zai auro ba? Kuma na sani ciki har da ‘yar gayun nan
‘yar’uwarshi Nabilah, ni ai ta ladan noma ce, matar shige ce, matar shige kuwa ai bata da wata
daraja”.
Abin da take fade kenan a fili ita kadai, tana ninkaya tana sullube jikinta da kumfar ‘Cien’ cikin
jacuzzi.
Ta dauki mintuna masu tsayi tana yin wankan cikin ruwan dumi mai dadi da kamshi, ta wanke
gashin kanta da shampoos din Ibrahim wato Argan, sai taji sun russuna daga karfinsu
(steamed) tayi brush yadda ta saba, ta dauro alwala ta dauro tawul ta fito gashin kanta na digar
ruwa. Sauri ta yi ta zura Pakistan rowan Kwaiduwar kwai masu kyau a jikinta (beig), cikin Jakarta ta
ciro mataji tana sharce kakkarfan gashin kanta domin bai dauko da drayer ba cikin kayan da ya
kwaso mata.
Da sallama ya turo kofar, ya dan kalle ta ya rausayar da kai wato ya ji dadi ta bi umarninshi,
don ya dauka ba za ta yin ba.
“Uwargida Rahane...... budurwar Yaya Khalipha, irin wannan daukar wanka haka?”
Ko kula shi bata yi ba, don ta soma sikewa da zancen Yaya Khalipha da yake yi mata kamar
bai yarda da ita ba, saboda sun so juna ita da Khalipha, wanda ita yanzu in ba ya kira sunanshi
bama ba ta tuno shi.
Ta ci gaba da tazar kakkarfan gashinta, sai ya iso gareta ya kai hannu yana duba gashin nata

baya ko fita jikin kumb saboda karfinsa. Ibrahim shiru ya yi, amma wadannan natural features
na Rayhanah na kara ribatar zuciyarsa.
Ta yarda cewa ita baka ce cikakkiyar Nigerian, ba ta kokarin canza launin fata ko canza
launin gashi, sai dai ta tsaftacesu. Tsoron Ibrahim da take ji a Singapore ya ragu sosai tunda bai
sake attempting abin da take jiwa tsoron nasa a kai ba.
Yanzu ma bai kai hannu gareta ba, gashin nata kadai ya taba, ya juya ya fita kicin ya jero
masu kayan ciye ciye da ya shigo dasu a tray da kansa ya dauko, su burger da pizza da kayan
McDonald’s da fresh milk ya shigo da shi har bed-room din ya aje a gefe.
“Kinga malama daina tazar nan zan ci abinci, kada ki jefa min gashi a ciki”.
Sai ta kame gashin ta daure da ribbon ba ta ce komi ba. Sai ya ji dan tausayi ya kama shi,
saboda tunda suka zo bai yi mata magana ta dadin rai ba, alhalin ya rabota da wadanda ke sata
farin ciki suna tarairayarta (Daddy da Inna).
Yana kuma sane da cewa cikin bacin rai da kawa-zucin karatun ta da ya rabota da shi take.
Yayi sanyi gabadaya yace a hankali,
“Rayhanah idan ba za ki daina yi min abubuwan da kike yi min din nan ba, ba zamu shirya
ba. Kin kama bakinki kin dinke, ina ta magana ba za ki amsa ni ba.
Rayhanah ko a dawo lafiya baki ce min ba, dazu da zan fita, baki tambaye ni ina ne dakin ki
ba, na dawo ko sannu da zuwa baki ce min ba. Kina jin yunwa ba za ki gaya min ba.
Ba sai kin yi hakan za ki nuna min cewa Khalipha kike so ba ni ba….”
Bai kai karshen maganarsa ba sai ga hawaye sun biyo kuncinta…… bai damu ba ya ci gaba
da fadin.
“Ba dama in fadi Khalipha sai ki sa min kuka, idan shi kika aura za ki yi mishi wannan
shakulatin bangaron da ni kike mini? Ko ko don ni lika miki aka yi?
Kina bakin ciki an raba ki da farin Balarabe an daura miki baki a kafa.... to dai ai gara ni sau
dubu da wannan bakar fuskar taki da kike min rowarta.
In don dan kiss din da nake roka ne a wajenki na bari, na zo inda zan samu a bagas, ba sai
na biki ina lallashi ba.
Kin ga mukulli nan, dauki ki tattara koma tsani ki kama hanyar dakin ki wancan dake kallon
nawa, ranar da kika shirya karbata a mijin aurenki, sai ki zo nan inda nake….. have your way
out…..!!!”
Ya fadi da dan daga murya yana nuna mata kofa. Ta sulale a kan kafafunta tana kuka sosai
ba ta fitan ba. Sai ya ja wani mugun tsaki ya mike ya yi fatali da abincin nasa ya suri mukullin
mota ya yi waje.
Tana jin tashin motarsa daga inda take, sai ta ji zuciyarta kamar ta fashe. Ta yi kukanta mai
isarta, babu mai lallashi babu wanda ya san tana yi. Fitar hawayenta a ganinta shi ne hukunta
zuciyarta da ta ki yin farin ciki da Ibraheem a matsayin miji. Amma kuma take KISHINSA!.
Abincin da ya tankwabar ta bi ta tsittsince ta yi kokari ta ci amma ta kasa. Rabon ta da abinci
tun a cikin jirgi, da ta tabbatar ba za ta iya ci din ba, tunda wanda ya sayo da kudinsa bakin
cikinta yasa ya kasa ci bai ci ba, ya fita yana mai fushi da ita.
Ya kasa ganeta ne, ita ba ta da yawan magana, yawancin abubuwa ma in ya fadi mata ba ta
san amsar da za ta ba shi bane, shi yasa take yin shiru.
Shima kuma da yana Kano ai haka yake, ba ta san yaushe ya koyi son surutu ba, abu kadan
ya ce Khalipha wanda dare daya ta nemi gurbin da ta saka shi a ciki a zuciyarta ta rasa. Ya

shafe kamar ba a yi shi ba (Son).
Me yasa yake yi mata duka wadannan tuhume-tuhumen marasa amfani a gareshi? Abin da
ya wuce, ya wuce a zuciyar Rayhanah……..
Har wata shukar ta dasu, tana so ta fidda rassa, ta yi sabuwar yabanya. Wannan bishiyar
kuma ba wata ba ce illa dan tsiron da Allah ya dasa tsakanin mace da mijinta na sunna, ba irin
na saurayi da budurwa ba.
Idan ya ci gaba da zarginta a kan Khalipha babu shakka yana daukar alhakin ta, ina ruwansa
da abin da ya gabata a wata rayuwa can da ta shude wadda ba shi da hurumi a ciki? Abin
haushin ma wai a kan Yayansa ciki daya.
Rayhanah ba ta san cewa da matacce ma mai sonka na kishi balle rayayye. Karfin kishin miji
a kan matarsa na da nasaba da adadin soyayyarsa gareta. Don haka ita ma ta yi fushin, ta
tattara inata-inata da mukullin da ya jefar mata ta yi dakin da ya batan.
Ta so ne ta shirya kayanta cikin cupboard amma ta kasa. Yunwa ta ci karfinta, damuwa da
fushin nasa ya fi nata fushin. Sai ta kasa hassala komai ta yi tagumi a gefen lafiyayyen gadonta
ta rasa abin da ke mata dadi.
Dakin kawai take kallo da kayatuwar zamanancinsa. A yau ne Rayhanah ta taba sha’awar
Allah ya ba ta ‘ya’ya, ko ba komai su din sanyin zuciya ne a lokacin da ubansu ya hutsance,
sannan abebaden debe kewa ne.
Har agogon bango ya buga karfe goma sha biyun dare a Chicago ba ta ji shigowar motar
Ibrahim ba.
Sai ta fara sana’ar tata wato (kuka) har da addu’ar Allah ya sanyaya zuciyar IBRAHEEM. Har
da jan Ayar “qul yaa Naaru kuuni Bardan wa Salamun alaa Ibrahimu...”
Me ke faruwa da ita ne haka a kan Ya Himu? Da fushinsa ya tafi da dukkan farin cikinta?
Walwalarta da bukatun rayuwarta ta dan Adam (barci da abinci).
Wadannan alamu ne na wani mutum da ka damu da shi matuka. Ibrahim ya zo ya yi
karan-tsaye a rayuwarta da zuciyarta. Ta yadda har bacin ransa ya tafi da sukunin zuciyarta da
kuzarin gangar jikinta gaba daya.
Dungurgur Rayhanah ke zaune, duk iya sata irin ta barci ya kasa sace Rayhanah. A kan
idonta lokacin sallar asubahi ya yi, ta yi sai ta ci gaba da zama a inda ta yi sallar, a lokacin ne
barci mai nauyi ya dauke ta.
Ba ta farka ba sai a dalilin tashin kira’a daga redio dake fitowa daga falo, wannan ya tabbatar
mata Ibrahim din ya dawo. Kuma da gaske yake sai ranar da ta shirya karbarshi a matsayin miji
zai sauko daga fushinsa tunda ga shi bai kwana gidan ba, ya dawo kuma bai nemi inda take ba.
Yaushe ce wannan ranar? Me za ta yi din ya nuna ta karbe shin? Ita tun ranar da ta san
Ibrahim aka aura mata ta karbi yin Allah, babu komai cikin zuciyarta a yanzu sai so da kauna
irin na mace da mijin da suka yi aure bisa tubalin soyayya.
To shirin da yake nufi din ne ba ta gane ba, in dai hira ce da surutu ba ta iya su ba, ta san
kuma shima din bai iya ba, banda yanzu da bakinshi ya bude. Mai zai hana suyi zamansu
yadda Allah ya haliccesu? Su yi magana a inda hakan ya zamo dole, kuma mai muhimmanci?
Tunanin Rayhanah kenan. *****
[12/28/2019, 19:06] Takori: Toilet din dake makale da dakinta ta shiga hajijiya na dibarta
saboda yunwa wadda ta haifar mata da ciwon kai. Wanka ta yi a daddafe, ta yi brush ta kuskure

da listerine, sannan ta fito.
Kayan da ta dauka riga da wando ne suit na mata masu kauri da dogon hannu maroon
kala, ‘yan gidan ‘george’. Ta bi ta feshe ilahirin gabobi da kusurwoyin jikinta da deo-spray din
rexona, ta cakuda da turarenta na din-din-din (Makhmariyyah wa lamsa nectar), ta tausasa
labbanta da vaseline din avon ta murda kofa ta fito falon.
Yana kwance ruf da ciki a doguwar kujera, exercise wears ne a jikinsa. Da alama ya yi
exercise din ne ya gaji yake hutawa. Ta karasa ta zauna a kujerar gefensa kanta a kasa ta yi
shiru.
Ya ji bude kofarta da fitowarta amma bai juyo ba, don ya san ba wani abu za ta ce masa ba,
shima bai san me zai ce mata ba.
Amma ga mamakinsa sai ya ji ta zauna a kasan kujerar da yake kwance muryarta na dan
rawa ta ce,
“Don Allah don Annabi ka yi hakuri Ya Himu, Allah ni ban san abin da zan dinga ce maka
bane shi yasa nake yin shirun..”
Ya yi shiru bai tanka mata ba. Sai ta sake cewa cikin damuwa ta gaske,
“Ka gaya min abinda kake so in dinga gaya maka din, sai in gaya maka…”
Bai juyo ba amma dariya ce ta kama shi, a kalla ta nuna ba ta da wani ra’ayi nata na kashin
kanta sai nasa.
Ya mike gaba daya ya zauna sosai a kujerar ya mike santala-santalan kafafunsa a kan
tebirin gilashi, ga alama ya yi matukar yin sabo da irin wannan zaman.
Ya dube ta a hankali ta sadda kai tana share hawaye ya ce,
“Yaa Ladif! Ke kam baki da aiki sai kuka kamar matar mamaci? To ai kinga abin da bana so
din kenan, kukan.
Rayhanah ya za ayi na ga farin ciki da walwala a fuskarki? Bayan Daddy ya ce min kina hira
har da dariya, ko duk a cikin rashin son nawa ne Rayhanah? Me zan yi ki saki jiki dani ki daina
sani a gaba kina min kukan nan?”
A hankali amma da alamar fusata cikin consonants and vowels din sentence din da zai fito
daga bakinta tace,
“Ka daina tuhumata a kan Yaya Khalipha!”.
“Saboda kada in taso miki da son da kike masa?”
“Ka ga abin da bana so din kenan”.
“Sai in yi shiru, ni ina aurenki kina tunanin wani can?”
“Ni na ce maka ina tunanin sa?”
Ta fada muryar na kara yin rawa.
“Kada ki yi min kukan saurara….. dago ido ki dube ni…..”
Ta kasa dagowar sai da ya sake maimaitawa a dan zafafe.
Cike da nauyi, da tsoro da firgita ta daga idanunta a hankali ta dube shi.

Abin da ta gani cikin idanun Ibraheem din suna da yawa, ga kishi, ga rikici, ga neman rigima,
ga neman tada zaune tsaye….. sannan ga so da kauna mai yawa….. so yake ayi ta rikici kada
a daina ba shi da alamun saukowa idan ba a fadi yadda yake so ba.
Sai ta mike ta yi dakinta da sauri-sauri da gudu-gudu don zuciyarta da gangar jikinta ba za su

iya jure rikicin nasa ba. Shine bai son a zauna lafiya sai dai ya yi ta tone-tone kamar kaza, to ita
ina yake so ta jefa ranta?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login