Showing 12001 words to 15000 words out of 23992 words
Chapter 5 - Rayuwar Raihana Part 4 chapter D end book Complete Hausa Novel By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf
Ibrahim na dakin ganawa da (Chief Medical Director) na Illinois TH, tare da manyan likitocin
koda na duniya, tattaunawa ake yi a kan cutar (sars) tare da wakilan kungiyoyin AAPS, NAD,
AMA, da Alberta. Ibrahim ya mike yana magana ta cikin ‘yar na’urar daukaka sauti dake makale
jikin farar rigarsa ta likitoci, can karkashin rigar bakaken suit ne wuyanshi daure da bakin tie din
da Rahane ta daura masa.
A lokacin ita Rayhanah tana can ofishinsa tana tsimayinsa, ya hadata da typing din wani
record da yake son fitarwa a kan cutar ta sars, ba tare da sallama ba ko neman izinin sakatariya
ko danna knocking na neman izini, wata farar yarinya kyakkyawa (ko da yake ba za a kira ta
yarinya ba, domin a kalla tana da ashirin da takwas), ta murdo kofar ofishin ta shigo.
Kallon-Kallo ake tsakanin Rayhanah diyar Malam Rashidu Takai da diyar Ambasada Kabiru
Abubakar Dogon-Daji. Rahanen, glasses ne prada a idanunta mai duhu wanda ya boye kwayar
idonta. Tana sanye cikin traditional attire dinta atamfa ‘yar Holland koriya shar, yafe da mayafin
da ya shiga da adon atamfar wato yellow, a kafafunta takalmi ne mai tsayin dunduniya sosai
(heel shoe) shima yellow, babu kwalliyar komai a fuskarta sai ruwan hodar mary-kay sai
lebbanta dake kyallin lip-balm mai danko.
Ita ma Sapnan ba wata kwalliya ta yi ba amma kallo daya za ka yi mata ka kirata da sunaye
uku; ‘yar gata, ‘yar hutu, yar gayu.
Shadda ce getzner dinkin Senegal a jikinta dark pink wadda ba a cika zare da yawa wajen yin
sirfaninta ba, wanda aka yi shi da zare light pink, haka dan shara-shara gyalen da ta zarga a
wuyanta shima light pink din ne, sai babbar jaka ta mata baka mahadin takalmi flat baki da ke
kafarta samfurin (gucci).
Haka suka ci gaba da kallon juna kowacce ba ta yi magana ba, amma ta soma huci, hancina
sun bubbude kowanne tsiron gashi ya mike sai Allah ya jeho Ibrahim gabanin a fara baiwa
hammata iska.
Mara gaskiya an ce ko a ruwa jibi yake, Ibrahim rikicewa ya yi. Amma da yake namiji ne
lab-coat din jikinshi ya soma kokarin cirewa yana fadin
“A’a, Sapna, wata sabon gani”.
Ta mai da budadden hancin nata a kansa kamar ta feso shi daga cikin hancin don takaici.
Me wannan bakar yarinyar ta fita da har ya zabeta a kanta? Tsakaninta da Ibraheem sai
ALLAH YA ISA! Domin ya gama wulakantata……
Rahane ta mike tsaye wanda ya baiwa Sapna damar ganin matashin cikin dake jikinta har ya
soma turowa gaba sosai. Sai Sapna ta cire takalminta ta rufe Ibrahim da duka da hannu da
kuma takalmanta…..
“Mugu….. azzalumi…. maci amana, tsakanina da kai sai ALLAH YA ISA! Na gode Allah da
ban taba baka budurcina ba balle in yi nadamar haduwa da kai….. I hate you Ibraheem….!!!”
Ta zubar da takalman ta fashe da kuka ta durkushe a gabansa tana ta yi. Daga karshe ta
mike ta yi kofa da gudu ta fita, ga mamakin Rayhanah sai Ibrahim ya bita, amma ba da gudu ba
sai sassarfa.
Rayhanah ba ta iya tukin mota ba, wannan dalilin ne yasa ta tsimayen Ibrahim, banda haka
da tuni ta ja motar ta tafi in ya so ya debo da sayyadarsa ko masoyiyar tashi ta kai shi gida.
Daga inda take tsaye jikin motar mijin nata tana hangosu ta cikin gilashinta, Sapna ta bude
mota ta shige shi kuma ya zauna a gefen mai zaman banza ya danne totur din motar da
kafafunsa yadda ba za ta iya jan motar ba, ya kuma dafe sitiyarin da hannayensa yana yi mata
magana, da alama cikin lallashi. Sai ta ji wani bakin ciki ya turnike mata zuciya ba ta ankara ba sai da hawaye suka zubo. Sai
kawai ta hau tafiya ta fita daga harabar Illinois TH tana bin gefen titi a hankali ba ta san inda
take jefa kafarta ba.
Da gudu motar Sapna ta zo ta wuce ta, tabbas ba don a kasar da ba’a laifi a kwana lafiya
bane da ta kwasheta da motar.
Jin tahowar motar Ibraheem ta yi a bayanta yana ta horn yana binta sannu-sannu, amma ko
kallon shi ta ki yi, ba ta ko son ganinsa ya yi duhu a zuciyarta, ya yi muni a idanunta.
Maimakon ta tsaya ma hanzari ta kara yi, dole ya kashe motar a gefen titi ya kara da gudu ya
cimmata ya rike hannunta a lokacin da ita kuma ta rufe idonta gam, sai kawai ya daddage ya
sureta tana fiffizgewa tana komai ya sata a motar ya rufe kofofinta da lock, glasan motar dama
ko guduma aka rotsa musu ba za su fashe ba saboda ingancinta. A haka ya ja motar suka nufi gida.
*****
Lallashin duniya Ibrahim ya yi, ban bakin duniya ya yi shi, Rayhanah ta ki saukowa. Ta yanke
duk wata kyakkyawar mu’amala dake tsakaninsu, ta kaurace masa a shimfida, ta kaurace masa
a ido biyu. Ko falo ta daina fitowa balle ta rakashi wani wuri.
Cikin ma dake like jikinta da za ta iya da ta ciro masa abinsa ta bashi, in yaso ya kaiwa
Sapnar. To ba ta da ikon wannan, wanda take da iko da shi, ta hana.
Duk da ta san cewa zai iya jure komai amma ban da wannan Hausar (a raba daki). Ba ta yi
karya ba, idan ta ce Ibraheem ya rame, ya rage fita.
Wani sashi na zuciyar da soyayya ta mamaya na neman fizgarta su sako mata tausayi,
musamman da ta soma saukowa. Ba ta da saurin fushi amma idan ta yin, ba ta sauka da wuri.
Ibrahim a falo yake kwana tsayin kwanaki goma sha hudu (sati biyu).
Ba rufe daki take yi ba, cewa ta yi muddin ya shigo mata daki wallahi zai nemeta ya rasa a
Chicago.
“Idan wannan shine kishi Rayhanah, ashe kuwa dole a cika jahannama da mata. To ni
wannan ai lasisi kika bani idan ni dan iskan ne ma in je in ci gaba da iskanci na. Kina tunanin
wannan rashin hankali da rashin zurfafa tunanin naki, shi zai raba namiji mai kuruciya kamana
da mata a America? Kin yi kuskure. Idan kin manta ne bari in tuna miki, ba ni kika fara so ba, Khalipha ne. Kaddarar Allah ce ta
wanzar da aurenmu ba tare da mun san juna ba.
Ni kuwa Rayhanah na so ki ne tun kina RAHANE.....Na so ki ba tare da na ganki a fili ba, na
so ki again daga jin muryarki zuciyata ta gaya min uwar ‘ya’yana ce wannan duk da ban ganta
ba.
Da na ganki a fili a matsayin matata babu abin da ya canza daga soyayyar da nake yimiki, sai
ma abin da ya karu. Duk da nasan ke din ba ni kika fara so ba. Rayhanah duk baki duba
wannan ba, sai don wata ta ce tana sona, alhalin na barta ne saboda ke?
Ai idan baki gode min ba, to a kalla ki cire takunkumin da kika sanya a tsakaninmu. Hakurina
ya gaza ba zan iya jurewa ba….!!!”
Tsaye yake a bakin kofarta a sanda yake yi mata wannan maganar. Ya tokare hannunsa da
kofar. Tana kwance ta yi shiru tana jinsa amma ba ta ce komai ba, ba ta juyo ba ma balle ya ga
fuskarta. Har ya san cewa maganganun sa sunyi tasiri a gareta ko basu yi ba. Sai ya girgiza kai,
ya fita ya bar mata dakin. Abu daya yake tattali yanzu a duniyar nan (cikin Rayhanah). Wannan ne dalilin da yasa bai
fiya takura mata ba, don sau biyu tana yin barin ciki dan sati uku. Wannan ne aka samu ya
zauna da taimako da dabarun likitoci.
Ibraheem ya rasa yadda zai yi da ita ta birkice ta hautsine masa gaba daya. Bai taba ganin
kishi irin na Rayhanah ba. Tun yana binta yana lallami har ya gaji ya rabu da ita, ya kuma koma
zagayawa wajen Sapna ta bayan fage.
A sabuwar tarbar da Sapna ta yiwa Ibraheem cikin rayuwarta, a shirye take da ta mallaka
masa kanta in dai zai aure ta. Bai yi hakan ba, cewa yake da ita a yawancin lokuta.
“Idan kin bani kan naki yanzun Sapna, idan muka yi auren kuma me za ki bani???”
Rayhanah da kanta ta soma noticing Ibraheem ya canza, ya daina zama a gidan sam-sam, in
kuma da dare ne to cinye daren yake yana waya, kamar yadda ya ce ta ba shi lasisin iskanci,
iskancin sa kuwa yake ta yi abinsa har a office kullum suna tare da Sapna kamar tip da taya.
Idan ta saurari hirar da yake yi da dare duka da Sapna ne. Wata irin hira marar dadin ji
da tada hankali agareta.
Sai fushin ya sauka, hankalinta ya yi mugun tashi, ta soma kokarin repenting
gundumemen kuskurenta.
Amma duk ta inda tayi tunanin bullowa Ibraheem baya bata fuska. Mata da yawa
muna wannan kuskuren, a lokacinda miji yake binmu da lallashi da kokarin amsa laifinsa, a
lokacin ne shekarar girman kanmu ke kamawa.
*****
[12/30/2019, 14:40] Takori: BAYAN WATA DAYA
1/Sha’aban
Wannan rana bakar rana ce ga Sapna da shi kansa Ibraheem din watakila. A yau ne za su
bar kasar Amurka a dalilin sauyin aiki da aka yiwa mahaifinta Ambasada Kabiru Abubakar
Dogon-Daji zuwa kasar Djibouti. Kuma da yake ta kammala karatunta mahaifinta ya sata a gaba
suka tafi yana gaya mata wannan Dr. Ibrahim din da ta likewa ba karamin raina mata wayo ya yi
ba, dan taking advantage ne ba aurenta zai yi ba.
So ba hauka bane, ko lambarta ta kasar Djibouti ta ba shi sai ya tsine mata albarka.
Addu’ar Rayhanah ce kawai Allah ya amsa amma ba isarta ba. Tashi take cikin dare ta yi
sallar nafila raka’a biyu, cikin sujjadarta ta karanta
“Ya hibbu na hum ka-hibbullahi (kafa bakwai). Qad shagafahaa hubbah (sau bakwai). Sai ta
ce,
“Yaa Allah ka mallaka min soyayyar Ibrahim dan Mansur da Asma’u. Ka kare min shi daga
zina da neman maza, da duk ayyukan sabo dake da alaka dasu. Ka juyo da hankalinsa gareni
ka ragemin kishin da nake da shi a kansa.
Yaa Allah ka bani soyayya da kaunar dake cikin zuciyarsa baki dayanta, ka dora shi a kan
hanya madaidaiciya ta neman halali, ka cire haramun daga aljihunsa.
Yaa Allah ka ba shi ikon ciyar damu (ni da abin da ke cikina) da tufatar damu da shayar damu
da halal. Ya Allah ka zama jagoran sa, ka rabani da abinda ke ciki na lafiya.”
Wannan ita ce adduar da Rayhanah ta dukufa tana yi dare da rana a cikin satittika hudun da
suka biyo baya, wadanda suka yi dai-dai da cikar cikin jikinta watanni shida.
Kasancewarta doguwa kuma cikin fari, kallon farko ba za ka ga cikin ba, musamman in riga
da zani ne a jikinta, sai in ta sanya doguwar riga.
Yau kwanan su Sapna uku da barin America. Idan ya ce bai yi kewarta ba ya yi karya. Ya
rage gantalin, dama wuraren shakatawa suke zuwa, ko bakin ruwa (beaches) su ci su sha, suyi
kazamiyar soyayyarsu.
Don haka yau da ya kasance a gida wuni guda zur, ko kofar gida bai leka ba, ita kanta
Rayhanah haushinta yake ji. Yana ta tsimayen wayar Sapna amma har ta cika sati da komawa
Djibouti ba ta kira shi ko sau daya ba.
Ita kuma wannan muguwar ta cikin gida ga yadda take, ba ta da niyyar ko ranar daina
muguntar ta.
Iyaka tunanin da ta yi na hanyar da za ta bi ta nuna ta karbi laifinta ba ta samu ba. Sai ta hau
zirga-zirga daga kicin zuwa bed room, ta yi kyau cikin (Layered-mini-Dress) duk da cikin ya turo
sosai, amma ko kallon ta ya ki yi.
Ya yi rigingine da waya a hannu yana faman hira da wata daban, tunda ba Sapna.
Rayhanah ta ga idan ta bari Ibraheem ya ci gaba da cusa mata bakin ciki a kan ‘yammatan
kan titi ta fadi babu nauyi, kuma zuciyarta za ta buga. Sai ta yi zaman ‘yan bori a gabansa ta
daddage ta fasa masa kuka mai gigitarwa.
Iyakar tsorata Ibraheem ya tsorata, wayar hannunsa bai san inda ya jefa ta ba. Don ya dauka
nakuda ce ta zo mata da ciki wata shida. Ya kama ta ya kankame yana kira.
“Mene ne Rayhanah? Haihuwar ce?”
Ture shi ta dinga yi da iya karfinta..
“Ka rabu dani, in ma mutuwa zan yi in mutum mana ina ruwanka? Tunda ‘yan iska sun sa ka
juya min baya, to ka mai dani inda ka dauko ni…..”
Dariya ce sosai ta kama Ibraheem da ya fahimci musabbabin wannan ihun da ya kada masa
‘ya’yan hanji, yasa shi cikin tashin hankalin, kada a haife masa bakwaini a tsakar daki.
Ya ce, “To ga bayan na dawo miki da shi, zo ki hau!”
Ya juyo mata bayan, ya yi durkuso a gabanta…..
“Zo ki hau Rayhanah, na daina juya miki shi. Zo ki hau ki riga baby hawa, don ban tashi juya
miki baya ba ma sai ranar da Allah ya fito da Da na ko ‘yata duniya Rayhanah, muddin baki
daina kokarin azabtar dani da kishinki na shirme ba, wanda ba irin na su Nana Aisha ba.
Kishi ne na halaka da daukar hakki Rayhanah, duk abinda zai munana lahirar ki bana sonki
da shi Rayhanah, kuma ba zan zama sanadi ba.
A da, na san Rahane mai yiwa mutane uziri ce, uzri sau saba’in, kafin ta kama su da yi mata
laifi, tunda ‘no body is perfect, except our Almighty…..!!!”
Jikin Rahane ya yi matukar nauyi, idonta ta dago a hankali ta kalli mijin nata, shima idonsa a
kanta. Sai dai gab yake da ya fidda hawaye.
“Zo ki hau…..”
Ya zube a kasa ya bata bayan. Da gudu ta runtuma ta rungume shi ta bayan, tana fadi cikin
kuka,
“Ka yafe min Yaa Himu? Zan kasance cikin tababbu, butulu masu manta alkhairi da rashin
godiyar Ubangiji idan baka yafe min ba IBRAHEEM…....”
Juyowa ya yi ya kama ta, fuskar mai cike da kwarjini da kamala, kunshe da murmushi mai
kayatarwa yana kada kai.
“Zan yafe miki only in kin hau bayan nan na goya ki, kafin na goya ‘ya’yan Ibrahim!!!”.
Sai ta dane shi, ya mike kamar bai dauki komai ba sabida rashin nauyinta, ya nufi master
bedroom dinsu.
Tana tuno kalaman Daddy ne a wannan lokacin…..
“Ibraheem is a nice person… Allah ba kwarzantashi nake yi ba Rayhanatu… wata rana ke da
kanki za ki gaya min hakan….
Lokacin da zai sunkuya yana yi muku doki sukutum ke da yaranku…..”
“Ba ka yi karya ba Daddy… bayan kasancewarsa nice, honest ne, kind ne, brave ne, sweet
ne, jarumi ne kuma sadauki a fannin nuna soyayyah!!!”
*****