Showing 15001 words to 18000 words out of 23992 words
Chapter 6 - Rayuwar Raihana Part 4 chapter D end book Complete Hausa Novel By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf
Tun daga wannan ranar da Ibrahim ya nunawa Rayhanah, ita wani bangare ce na rayuwarsa
da ba zai iya rayuwa ba ita ba, fushinta a kansa zai iya gurbata rayuwarsa. Rayhanah ba ta
sake yin irin wautar da ta yi a baya ba, ba ta sake takurawa Ibrahim a kan ‘yammata ko wayarsa
da mutane ba. Ita duk mai son Ibrahim ma duk kyanta da matsayin da take takama da shi ko na iyayenta
tausayi take ba ta. Annabi (S.A.W) ya ce,
“Imanin dayan ku baya cika har sai ya sowa dan’uwansa Musulmi abin da yake sowa kansa”.
Ta yarda ta amince Ibraheem abin so ne, ba kowacce mace mara aure ce za ta iya dauke ido
a kansa ba, don haka ta kama addu’a ta kama Ibrahim, ta kuma hada da kau da kai daga
mu’amalarsa da kowa.
Illa kullum tunaninta shine hanyoyin da za ta bi ta kara kyautata aurenta, ta kara martabarta a
idanunsa. Tunda ita din dai da ba kyakkyawar ba, ba ‘yar kowan-kowa ba, ita Allah ya kashe
ya baiwa.
Already Ibrahim ya gama duk abin da zai yi a Chicago, amma ganin cikin Rayhanah ya shiga
wata tara sai ya bari sai ta haihu don su jewa Daddy da tsarabar da za ta gigita shi, don ko kusa
bai taba gaya masa Rayhanah na da ciki ba.
Shi Daddyn ne dai yake faman tambaya sai ya yi dariya ya ce,
“A ci gaba da addu’a Daddy”.
A dai-dai lokacin EDD dinta ya cika, don haka bai cika yin nisa da gida ba, haka ko tafiya
yake on the street waya suke, sai idan driving yake. Shima din earpiece na jikinsa, da ta yi kira
zai sauka gefen titi ya amsa.
Ranar litinin, bayan gajeruwar nakuda ta haifi diyarta mace mai kyau, abin mamaki mai
matukar kama da Mami, duk da cewa kalar iyayenta ce (choculate) har sun fi ta haske. A labour
- room na asibitin (Illinois).
Ibrahim da shi aka karbi haihuwar, kuma sai da aka sake dinketa kamar kwarya (kamar
yadda yake fadi).
Shi da kansa ya goge jaririyar da olive oil (Zaitun), ya nadeta cikin shawul ya rungume yana
yi mata huduba da kalmar shahada cikin kunnuwanta, ya dura mata zam-zam, ya tauna dabino
(ajwa) ya sa mata a baki, sannan ne ya bari Nurses suka karbeta suka yi ta wanke ta.
Ashe har da dattin ciki ya kara mata baki, da aka gama wanke ta sai ta koma kamar Abida.
Rayhanah da ta dubi yarinyar da Ibrahim ya dora mata a kan cinyarta sai da ta tsorata…..
Yarinya kamar Abida ce ta haife ta, cleft din Ibrahim a kasan habarta, ga beauty point din
Mami.
Sai ta ji hawaye na diga daga idanunta suna sauka a fuskar jaririyar da ta tabbatar Mami da
Abida ba za su karbeta a matsayin jininsu ba, duk da cewa dasu take kama, saboda daga jikinta
da suke gani kaskantacciya sauran cuta ta fito. Sai ta yi wani tunanin da ya sanyaya mata
zuciya, tunanin cewa, “ Jawahir za ta goya ta, Aziza za ta dauke ta.”
Rayhanah ji ta yi hankalinta ya dugunzuma ya yi gida Nigeria, gara ayi wacce za ayi
tsakaninta da Mami wannan boyayyen aure ya isheta, ba za ta yarda Mami ta sheganta mata
‘ya ba, tunda ba ta san da auren ba.
Babban takaicinta a kullum idan ta tuno tozarcin da Mami ta yi mata sanda take zargin Daddy
da nemanta.
A wancan lokacin ba ta dau al’amarin da zafi ba saboda rayuwarta dake reto a gidan iyayen
rikon nata, amma yanzu da ta samu nutsuwa da karin hankali ta yadda ba karamin tozarci da
wulakanci Mami ta yi mata ba. Mutumin da yake makwafin mahaifi agareta.
Ta dauki ‘yar sosai a jikinta, tana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta ji hanci da ido, da dan
bakinta mai kyau kamar Dr. Asma’u Mansur Takai….
Sai ji ta yi Ibraheem ya rungumesu ta baya.
Dukkansu rufe idanunsu suka yi ruf, daga su har jaririyar, a sakamakon shigowar wata
sabuwar kauna da soyayya mai girman da baya misaltuwa da ta kara shigewa cikin zukatan
kowannensu.
Tsayin minti biyar sannan Ibrahim ya karbi Babyn daga hannunta yana kallo yana murmushi,
ya ce,
“Mami na ce….. sunanta NANA ASMA’U!’
Cikin karaji Rayhanah ta ce,
“Ban yarda ba, sai in ita da kanta ta amince a kira ta Asma’un…..”
Idanun Ibrahim suka yi mici-mici yana kallon ta da mamakin dalilin wannan ANGER haka a
kan sunan mahaifiyarsa. To sunan Mamin ne ba ta so ko Mamin ce ba ta so?
Ko kuma me take nufi da sai idan ita da kanta ta yarda a kira yarinyar Asma’u?
Bai gama tunanin da yake yi ba sai gani ya yi Rayhanah ta goye ‘yarta da tawul din da take
kunshe ciki, ta yi lullubinta yadda ta saba ba tare da tunanin cewa a asibiti take ba, kuma
likitanta bai sallameta ba ta doshi kofa.
Ibraheem tsayawa ya yi yana kallon ta ya daskare a tsaye kamar statue (mutum-mutumi). Bai
ankara ba har ta kai kofa, sai ya yi azama da sassarfa ya cimmata ya damko hannunta.
A rikice ya ce, “Rayhanah ina za ki je? Tafiya za ki yi ki barni Rayhanah? Me na yi miki? Ko
ko ba ki yi farin ciki da kyautar da Allah ya bamu bane? Ko don na ce zan sawa ‘yata sunan
mahaifiyata? Above all ma ina za ki je ne?”
Hawaye na kwarara a kan fuskarta ta ce,
‘TAKAI!”
“Takai???”
Ya fada cikin sigar tambaya.
“To wajen wa?”
Ya sake fadi a gigice. Ba tareda ya jira amsar farko ba. Ta kai tafukanta ta rufe fuskarta ta
soma shesshekar kuka kafin ta ce,
“Wajen Inna Juma da Inna Zinaru”.
Wannan lokacin Ibrahim ya fara fusata.
“Saboda na ce zan sawa ‘yata suna Asma’u? Ko don tsuntsun soyayyata ya tashi don kin
haihu dani?”
Ba ta ce komai ba, sai girgiza kai take tana kuka.
“Zinarun ta ci uwata….. ta ci ubanta! Ke idan kina da hankali har za ki sakota cikin wadanda
za ki yi tinkaho da su? To amma ba da wannan jaririyar da ke bayan ki ba ko?”
Ta fiddo ido jike da hawaye ta ce,
“Ai ita zan kai can, sai ni in dawo”.
“........Da yake kutumar uban Zinaru ne ya yi cikinta ko? Sakko min ‘yata!”
Ya mika mata hannu. Shi kansa baisan sanda wannan ashariyar da bai taba yi ba koda wasa
ta sulmiyo daga bakin sa ba. Cikin kuka mai fitowa tun daga karkashin zuciya ta ce,
“Idan sama da kasa za ta hadu, ba zan baka ‘yata ba ka kaiwa Mami....….”
Ai ba ta idasa rufe bakinta ba ta ji saukar marin da ya tafi da jinta da ganinta na wucin gadi,
har sai da ta ga wuta da gilmawar taurari, kafin ta farfado ya sake shimfida mata wani, ya fizgo
yarinyar dake bayanta, wadda a take ta soma canyara kukan da ya ratsa har cikin kwakwalwar
Ibrahim…..
Rayhanah na durkushe tana regaining consciousness. Ta rasa a duniya take ko a lahira.
Ibrahim ya kara da cewa,
“Idan don lasisin da na baki na soyayyata a gareki ne yasa za ki wulakanta min UWA, to kin
yi kadan Rayhanah! Son ya ci uwatar! Soyayyar ta ci abu kazan.....ubanta. Ki gaida mutanen
TAKAI”.
Ya raba ta gefenta ya wuce rungume da ‘yarsa, wadda har zuwa lokacin ba ta daina tsala ihu
ba.
Wata Nurse ce dake bangaren Nursery, wai ita Regina ta karbi jaririyar daga hannunsa ta
sanya mata kan feeding bottle a bakinta (nipple), sai ta yi shiru. Ta mika masa ita tana tambaya.
“Where is her Mum?”
Sai ya wuceta zuwa motarsa bai bata amsa ba.
Ya bude motar ya shiga ya zauna ya bude tawul din ya rufeta sosai ya kwantar da ita a
kusurwar kujerar baya, ya dinga jan motar a hankali kamar mai tafiya akan kwai kada ya
jijjigata.
In ka kalle su shi da jaririyar sai sunyi bala’in baka tausayi. Idanun shi sun kada sunyi jawur
amma ba hawaye yake ba. Bakin ciki ne da fushi mai tsanani, yana mamakin halayen mata.
Kai ka so su, ka kaunace su da zuciyarka daya, ka so nasu har fiye da yadda kake son naka,
amma ba za su saka maka da komai ba sai raini ga mahaifiyarka, wadda itace silar komai na
zamowarka in existence har kayi girma da balagar da suka samu suka aura suke mora, ba don
komai ba sai don saboda sun sameka a hannu.
To Allah wadaran soyayya! Shi ya sanya bai taba yiwa kansa sha’awar auren soyayya ba da
farko saboda gudun irin wannan fiffikar.
Ga wadda yake murna da halayenta, dabi’unta da ginin da suka soma yiwa rayuwarsu, ta
nuna masa itama bata da bambanci da sauran mata.
Har ya iso gida tunanin da yake ta yi kenan.
*****
[12/30/2019, 20:24] Takori: Sanda Rayhanah ta samu dawowa hayyacinta daga gigitattun
marin Ibrahim sai ta mike tsaye hajijiya na dibarta. Dai-dai lokacin likitanta da Nurse suka shigo,
cikin mamakin abinda ya kawo ta bakin kofa haka ko hutawa ba ta gama yi ba.
Haka suka sata gaba da lallami da ban baki har ta hakura ta koma gadonta ta kwanta. Suka
ci gaba da abin da ya kawo su, suka bata magungunanta ta sha suka sanyata ruwan zafi suna
ci gaba da kula da ita, kulawa ta musamman albarkacin Dr. Ibraheem.
Likitan ya tambayi babyn, tana kuka ta ce Babanta ya tafi da ita. Cikin mamaki suka ce
“Ina?”
Ta ce, “Ba ta sani ba”.
Sai kuka.
A take Dr. Aziz, Musulmin Lebanon ya kira wayar Dr. Ibraheem, magana suka yi mai kama da
jayayya. A karshe ta tsinci maganar Dr. Aziz inda yake cewa.
“Wannan Issue dinku ne kai da iyalinka babu ruwan baiwar Allah, kada ka kwareta ka kawo ta
uwarta ta shayar da ita ko in kai maganar kotu wallahi”.
A wajen Bature yaro ya fi komai muhimmanci, kuma gwamnati na da ikon raba Da da
iyayensa idan irin haka ta faru, ko in an ga za su cutar da rayuwar yaron musamman kasar
Amurka da Ingila.
Ba ta dai ji me Ibrahim din ya ce ba, Dr. Aziz ya ci gaba da bincikar lafiyarta. Ya yi
rubuce-rubuce cikin file dinta, sannan ya iso gabanta a hankali ya ce,
“Ko mene ne ya hadaki da Dr. Ibrahim ki kwantar da kai ki amshi laifin, ki karbi jaririyarki ki
shayar da ita kin ji? Babu abin da take bukata a halin yanzu sai ke da dumin jikinki, idan fa har
kina son soyayyar uwa da Da ta kasance tsakaninku, kar ki bari a rabaku, kin ji?”
Tana share hawaye ta daga masa kai. Ya ce ta zo ya kaita gida in ji Ibraheem.
Ba ta da zabi in ba komawa gidan ba, jiki ba karfi babu passport ina za ta je? Sai dai ita ma ta
yi fushi da Ibrahim a kan marin da ya yi mata, fushi irin wanda ba ta taba yinsa a kan kowa ba,
including MAMI.
Shine ya danna bell a flat dinsu, Ibraheem ya bude daga shi sai farar singilet da wandon
wanka gajere, ya bata hanya ta wuce inda ta jiyo babyn nata tsala kuka. Tsikar jikinta ta tashi
gaba daya ta saurara don jin daga inda kukan ke fitowa, master bed room ne.
Ba ta bi ta kan wani Ibraheem ba ta je ta sunkuto ‘yarta ta fito. Dr. Aziz na nan falo tare da
Ibraheem suna ta ragargazar Turanci kamar an bude CNN. Da alama mukabala suke yi, Dr.
Aziz na tausarsa.
Ta zo za ta wuce dakinta ya ce,
“Come here Rayhanah”.
Tana matukar ganin kimarsa kasancewarsa consultant na gynecology din Illinois baki daya,
kuma aboki ne na jiki ga Ibrahim, domin tare suka yi karatu duk da suna fanni daban-daban.
Ya mika hannu ya ce,
“Bani ita”.
Tana share hawaye ta mika masa, Ibrahim ya yi kicin-kicin ko kallon ta ya ki yi.
Dr. Aziz ya ce,
“Durkusa ki ba shi hakuri”.
Sai ba ta yi musu ba ta durkusa din.
“Ka yi hakuri Ya Himu, bai kamata ka yi hanzarin yanke hukunci a kaina ba, ba tare da ka
tambayeni dalilina ba.
Na san abinda baka sani ba. Mami ba ta sona, shi yasa Daddy yake boye mata aurenmu.
To kuma ga zuri’a ta soma taruwa ina so Mami ta sani…. ina tsoron..,. ina tsoron… kada ta ce
ba za ta amshe ta a matsayin jika ba…. tunda ba ta san da aurenmu ba”.
Cikin harshen Hausa take yin maganar cikin kuka da karkarwar murya, kada Dr. Aziz ya
fahimta.
“Wannan statement da kika fada wai bata son ki, kamar ya ya ba ta son ki, ban gane mata
ba? Wane irin so kike so ta yi miki bayan wanda ta yi miki tun kina Rahanen ki?
Da bakina mun yi fada da Mami a kanki, da na ce ban yarda da zamanku tare da su Abida
ba. Cewa ta yi ita babu ruwanta, Da na kowa ne, za ta rike ki tsakaninta da Allah.
Sannan don yanzu na ce zan sawa ‘yata sunanta ki nemi wulakanta min ita Rayhanah? Sam,
ba zan dauka ba wallahi. Ki yi mana duk zabin da kika gama dama, a shirye nake da karbar duk
hukuncin da kika yanke. Sunan ‘yata Asma’u, Rayhanah ki yi duk abin da za ki yi….”
Ganin cewa ba ta da hujjar da za ta kare kanta a kan wannan bayani na Ibrahim a kan
mahaifiyarsa, sai ta bi shawarar Dr. Aziz wanda ke ta daga mata kai da kada mata ido alamar ta
dauki laifin, sai ta kama kafarsa….
“Na yi kuskure Ya Himu, don Allah ka yi hakuri….”
Ta ci gaba da rera masa kuka mai nuna MARAICIN ta.
“Ba ni da uwa, bani da uba, bani da komai sai kai da Baba Dacta, sai ‘yar da Allah ya bamu
yau din nan. Idan ka rabani da ita ka ki ni saboda kuskurena ina za ni? Ibrahim ina zan sa
kaina???”.
Ta kwantar da kai a kan gwiwoyinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Ga mamakinta sai Ibrahim ya mika hannu ya dago habarta yana share mata hawayen da
‘yan yatsunsa zara-zara guda biyu. Sai Dr. Aziz ya yi gyaran murya don su san da zamansa a
falon, domin ga dukkan alamu suna bukatar fiye da hakan wajen lallashin junansu.
Rayhanah ta mike ta zauna kusa da Ibrahim, ya mika hannu ya sarkafo kugunta. Dr. Aziz ya
ce,
“Kin iya breast feeding?”
Ta girgiza kai cikin jin kunya wato “A’ah”.
Sai ya hau nuna mata,
“Haka za ki rike ta, ki dago ta haka…. Ki sanya nipple din a tsakanin yatsunki biyu, sai ki sa
mata a baki. Amma ki dinga yi da lura kada ki toshe mata hanci.
Idan ta sha da yawa sai ki dagata ki dora a nan…. (ya nuna mata) har sai ta yi gyatsa”.
Rayhanah ta daga kai. To ungota yi in gani. Ta karbi ‘yar, amma don kunya sai ta yi