Showing 39001 words to 42000 words out of 82745 words

Chapter 14 - Sakon So Complete Hausa Novels by M Shakur .pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

219

makaranta kika saka ba yau sai kikayi kaman ba
kanwata Lujain ba, bakiyi kaman Lulu Gwaggo ba daikika fito tsaf Lujainnnn, kidinga saka
kaya kinga yanda kikai kyau ne” kallon kanta Lujain tayi amadubi wani kalan murmushi tayi tace
“wlh nai kyau amman kinga harsun soma damuna kayan kaman na kwabe su cizona suke” Ya
Samira tace “ki kwabesu Baba ya kwabe ki” kyalkyacewa da dariya Lujain tayi sosai hakan yasa
Gwaggo ta daga labulen uwar dakan taleko tace “chakulkuli kike mata ne datake dariya
hak……” kasa karasa maganan Gwaggo tayi ganin yanda Lujain tayi kyau, Gwaggo batasan
lokacin data yafito su Abida ba tace “kuzo kuga kanwarku” dasauri suma duk sukazo kallonta
suka shigayi Lujain sai dariya take tace “nai kyau ko Gwaggo na”? Washe baki Gwaggo tayi
tace “kaman hurun ini Lulu ta” tabe baki Abida tayi takoma tazauna Habiba tace “kidinga sa
kaya haka jibeki saikika fito kaman mai hankali” hararanta Lujain tayi zatai magana Gwaggo
tace “barta da halinta yi maza kiyi isha’i gashichan an sallame a masallaci yanzun nan Babanki
zai kiraki” gyadama Gwaggo kai tayi tahau kan dadduma Gwaggo tasaki labulen taja su Abida
kitchen tabasu manya manyan jakunkunan da Allah kadai yasan meta hadama Lujain aciki tace
“su wuce sukai motan Baba” kaiwa sukayi suka dawo Abida tace “Baba yace kije waje”
gyadamusu kai Lujain data tashi daga kan dadduma tayi zata saka slippers Gwaggo tace “saka
takalmin da Baban naki Ya Aiko miki mana” sakawa tayi dan kuttubin kafanta yay kyau tayi da
cute white feet nata da long long nails dinnan kaman kasa abakinka kaitasha, tana murmushi
tawuce tafita lullubin lafayan na zamewa baya kyakkywan gashinta Ya bayyana gate tabude
tafita, Baba tagani da Baffan ta guda biyu awajen tsaye jikin mota dukansu tsayawa kallonta
sukayi ahankali tace “ina yininku” amsa mata sukayi Baba yazo gabanta ahankali yadaga
hannunshi yajawo Dan kwalin lafayanta gaba sannan yakama hannunta zuwa bayan motan
yasata aciki Baffa Abdullhadi yashiga maxaunin direba yusuf Ya zauna agaba Baba Ya zauna
abaya kusada ita sannan aka tada motar.


Murmushi tayi takalli hanya tace “Baba ina zamu”? Anatse Baba yace “gidan mijinki zamu
kaiki!”.
EPISODE 1️⃣7️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Don’t miss this book for anything dan yanzu aka fara



Wani kalan faduwa da gabanta yayi saida taji kanta yasara dum, hannunta Baba yakama yace
“namiki laifi da dama Lujain tun kina Yar kankanuwan ki, lokacin banda courage na kallonki ne
sabida banda abinda zan kuladake, wannan auren ma bawai dan Gwaggo tadage akai yasa na
yarda ba is because that’s the only right thing I can do for u, dakina karama I couldn’t do
anything but yanzu I can do anything to protect you, your image, I can do anything dan inga
society ya girmamaki, yakuma darajaki, nasan bakisan mutumin nan ba shima baisanki ba but
abu daya dana sani shine bazai cutarmini dake ba dan shima yanada kamarki kokuma nace
wacce tafiki agida, he’s a father so he can handle you, munyi bincike akanshi shaida daya bamu
samu akanshi na cewa mutumin banza bane dan haka inaso ki zama mai tsoron Allah ki manta
da komi kicigaba da rayuwanki amatsayin matarshi kinji” wani kalan kukane taji yana tasomata
amman kotari takasa tana tsoron Baba dako gardama batayi agabanshi Baba nada dukan yara
yasha dukanta dasu Samira ita kuma babu abinda take tsoro kaman duka yanzu wayau
Gwaggo dama tamata dasu Ya Samira, sai alokacin hawaye yazubo mata dasauri takai
hannunta ta share, amman ina bini bini saisu zubo ta share sunyi tafiya mai nisa sosan gaske
sannan sukakai wani mahaukacin estate dinsu bude musu gate akayi dan ansan da zuwansu
har gidansu Abee gateman yabude musu gate suka shiga yamaida gate yarufe yatafi ciki da
gudu duk suna zaune cikin motan Musty yafito shida Harun duk suna sanye da manyan kaya
sai Anty Binta da Matar Harun mai suna Amina sunci atampopi masu kyau sunsha aiki kana
ganinsu kama hadaddun mata masu kudi, bude mota su Baba sukayi sannan Baba yasa hannu
yafito da Lujain daga cikin mota, gently tasauke kafarta akan interlock na compund din wani
kalan sanyi taji yashigeta kaman zata sandare dan har hanjinta taji sanyin, ahankali Baba yaja
hannunta tsayawa tayi kikam dayasa Baba yajuyo yakalleta wani kalan fashewa tayi da kuka
tana girgizama Baba kai dan sai yanzu ta yarda wani wuri fa yakawota tace “dan Allah Baba
karka kaini wlh bansan su ba, Baba baran kara rashinji ba, ban kara zama ba dan kwali, ban

kara zama da towel, ban kara aran wayan Ya Samira wlh Baba zanmabar wajen Gwaggo
nadawo kwana adaki dasu Ya Samira amman dan Allah kada ka kaini ko’ina mukoma gidanmu”
Shi kanshi Baba sanyi jikinshi yayi baitaba kawowa cewa Lujain ce zata fara aure acikin duka
yaranshi ba, amman yadaure yay ta maza wani mugun kallo yamata yace “let’s go my friend
banson shirme” kafafuwanta har girgidi suke kaman maijin fitsari tabishi kanta akasa tana kuka
sosai duksu Anty Binta dasuke dan nesa dasu na kallonsu afuskansu kadai zaka gane suma
jikinsu yay sanyi jin maganganun Lujain, karasawa gabansu su Baba sukayi da fara’a aka gaisa
sannan sukace bismillan ku, Baba na rikeda ita suka shiga falon sake tirjewa tayi ajikin kofa
ganin mutane afalon cike kowa kuma su ake kallo, Hajiya da duka yaranta, sai Abdallah Kausar
da matan Ibro sai Abee dake zaune kan 3 sitter da Hajiya ke zaune kai dan anan ta umurce shi
da zama yana sanye da shadda anmai dinkin jumper da hula akanshi yay wani kalan kyau
kaman kasace shi kanshi na kasa dan shi kadaine adakin wanda ba kofan yake kallo ba, ganin
mutane na kallonsu gashi ta turjemai yasa Baba yajata da karfi but karfin dat is not obvious
shigowa Anty Binta da Amina sukayi suna ayiriririiiii kujerun dakenan empty su Baba suka
zauna da Lujain na kusadashi kanta akasa tana kuka sosai, cikeda dattaku Hajiya tai murmushi
tace “barkan ku da zuwa ah’ah amaryan tamu mai kuka ce kodai Alhaji kun tsunguleta a hanyan
zuwa ne” dan murmushi Baba yayi yace “munsameku lafiya Hajiya” murmushi tayi tace “lafiya
lau” cikeda dabara ta taba kafan Abee hakan yasa anatse yadago kanshi yakalli Baba ahankali
yace “ina yini” murmushi Baba yayi shima yace “Alhamdulillah Imrana” kayan ciye ciye aka
shiga cika gabansu dashi murmushi Baba yayi yace “Alhamdulillah sassannunku da aiki an
gode Allah amfana” mikewa tsaye yayi ahankali sannan yakama hannun Lujain da kanta ke
kasa tana kuka har lokacin yadagata yaja hannunta tana biyeda shi Dan murmushi Hajiya tayi
tamike tsaye ahankali tareda komawa gefe, gently Baba yazaunar da Lujain kusada Abee kuka
take ita bama gani takeba balle tasan meke faruwa hannunta da Baba kerike dashi yadauka
yakama na Abee da kanshi ke kasa yasa aciki dudda kukan da Lujain take but she was able to
understand hannunta baya cikin na Baba kuma, wani kalan warm serene cold taji akan hannun
Abee dake shiga cikin fatar hannunta, matse hannun Abee Baba yayi kan nata hakan yasa
Abee yarike hannunta gam addu’a Baba yatofa a hannayen nasu biyu da duka Ya rirrike yahada
sannan yakalli fuskan Imran dake kasa ahankali yace “Imrana” gently Abee yadago idanunshi
yadaura akan na Baba, ajiyan zuciya Baba yasauke dan Abee nada wani kalan kwarjini da
charisma da idan yakalleka dole kagani yace “ga diyata nan Lujain nabaka ita amana, bansanka
ba amman na yarda dakai zuciyata ta aminta dakai sama da yanda kake tunani, karikemini ita
amana daga yanzu rayuwanta komi nata na hannunta ne banda iko akanta saikai karike amana
kaji Imran” Abee jiyayi kanshi yamai nauyi ganin yanda Abee ke kallonshi amsa yake jira yasa
ya gyadamai kai batare dayay magana ba dan baijin zai iya magana ba, sakesu Baba yayi
yatashi yajuya yakalli Hajiya hannunshi yahade yace “Hajiya ke mahaifiyar muce nan gabaki
daya ga diyata nan nakawo muku marainiya ce tun kafin a haifeta mahaifiyarta tarasu, a hannun
mahaifiyata ta girma takuma tashi, Lujain goyon kakace, nasan zakuga abubuwa da dama na
shirme da rashin wayau dakuma rawan kai ina rokonki da idan batai daidai ba ki tsawata mata
dan kin isa ne, sannan ku dorata akan hanya mai kyau, Alhamdulillah nazo na ganku duka naji
dadi hankalina ya kwanta dan Lujain tabar family tane tazo tasami even a bigger family dan
haka kurikemini amana nan ta, tunda take aduniya yaune rana na farko da barata kwana tareda
kakarta ba kokuma agidansu ba ko tafiya bata tabayiba, dan Allah kuyi hakuri da ita sannan ku

dorata kan hanya madaidaiciya” wani kalan kuka Lujain take tafara kokarin cire hannunta daga
nacikin Abee kallon hannun nata dake cikin nashi Abee yayi saikuma yadauke kai batare daya
saketa ba dayaji takeson yayiba, ahankali Hajiya tace “na dauki amana in sha Allah bazamu
cutar da Lujain ba namaka wannan alkawarin” murmushi Baba yayi yace “to mungode mungode
bari mukoma gida saida safen ku” cikeda girmamawa Hajiya tace “Muma mungode saida safe
agaida kowa da kowa” tashi su Baffa sukayi Baba yajuya shima zai tafi jin da gaske Baba tafiya
zaiyi yabarta agidan nan wani kalan fizge hannunta Lujain tayi daga cikin na Abee ta tashi da
gudu ta kankame Baba tabaya tana kuka sosai har gyalenta na zamewa kasa lafiyayen
gashinta da aka kama da ribbon mai kyau ya bayyana cikin kuka sosai tace “Baba dan Allah
dan Allah kada katafi ka barni wlh ban sansu ba, wlh kuwa” bata damu da da karfi take
maganan ba tarike Baba gam cikin kuka tace “Baba wlh baran kara maka barna ba, Baba nace
baran kara aran wayan Ya Samira ba saika siyamini tawa Baba dan Allah kada kabarni anan”
tahowa su Baffa sukayi ganin yanda ta rirrike Baba tabaya yakasa motsi kaman zata karyashi
Baffa Hadi yace “ke cikashi” cikin kuka ta makemai kafada tace “dani zaku tafi Baffa” Musty
daduk suke kallon drama yay murmushi yakalli Anty Binta da Amina hakan yasa suka taho
wajen Anty Amina tace “yakuri Lujain ki barsu sutafi” wani kalan ihu tabuga da saida yasa for
the first time Abee yadago kanshi yadaura akanta, dudda he’s not seeing her face directly but
yaga yanda goshinta har zufa yake ketowa kuka harda majina ga gashinta da aka gyara
tsabagen yanda take jujjuyar da fuska abayan Baba harya hargitse babu lallashin duniya da
Anty Binta da Amina basuyiba har Hajiya tasa baki ina taki sakin Baba da Baba ta kular dashi
wani kalan tsawa yadaka mata Lujain! Yanda taji saukan tsawan saida ta sakeshi tai tangal
tangal tama fadi akasan tiles na wajen jikinta narawa sosai tana girgizama Baba kai, kowa na
falon su yake kallo jin yanda Baba yadaka mata tsawa, kaman Baba zai daketa yace “stand up
go back to your sit ki zauna” juyawa tayi da sauri tana rarrafe ta tashi yanda ta tashi takoma
tazauna zaka dauka mala’ikan mutuwa tagani, tahowa Baba yayi azuciye batasan lokacin datai
pulling hannun Abee ta kama hannun Abee gamgam ba ta boye fuskanta akafadanshi kaman
zata shide tace “Baba dan Allah kayakuri karka dokeni” yanda jikinta ke bari da yanda take
numfashi kaman zata shide Abee could hear it, yanda tarike hannun Abee gam tana boye
fuskanta abayanshi Musty yakalla daidai itama Anty Binta takalleshi kashe mata idanu yayi tayi
murmushi Baba zaiyi magana Hajiya tace “aaaa ina ake haka Alhaji? Har gidana zakazo ka
firgitamin diya sabida tayi kuka kan katafi da ita bata sanmu ba yo ai batai karyaba babu wanda
tasani anan, kataba ganin inda aka rabu da amarya lafiya dama ai sai sunyi yan koke koken
nan, karma kafadi abinda kakeson fadi dan nasan fada zaka mata” dan murmushi Baba yayi
akunyace yace “shikenan to Hajiya saida safen ku” anatse kowa yace “Allah bamu alkhairi” fita
sukayi hakan yasa ahankali tasaki hannun Abee sannan takoma gefe takifa kanta akafa tana
kuka sosai tashi Abee yayi yawuce sama Hajiya tabishi da kallo tashi Kausar itama tayi tawuce
fuuuu sama ahankali Hajiya tazauna kan kujeran daidai nan mai gadi yashigo dawasu
jakunkuna manya guda biyu yace “Hajiya ina za’a saka wayan nan” Hamza ta kalla tace “jeka
kaimata dakinta” gyadama Mamanshi kai kawai yayi yawuce sama ahankali Hajiya takai
hannunta tadaura saman bayan Lujain cikeda lallashi yace “kiyakuri kowace mace saitaji irin
abin nan dakikeji idan aka kawota gidan mijinta, amman zakigani nan da sati kin warware kin
daina tunanin gida ko” ta tambayi su Anty Binta dake tsaye akansu sukace “hakane” murmushi
Hajiya tayi tace “ku kaita dakinta Binta” Gyadamata kai Binta tayi dagata itada Amina sukayi

suka wuce da ita sama Mama takalli su Sajida da Zainab tace “ku kai abinci dakinta dan ba
lallai taci abinci ba” dan tabe baki sukayi saikuma suka tashi itadai Maman Aneesa na zaune
tana magana da yaran tace “Aneesarh takarasa maganin ta” gyadama Hajiya kai tayi takalli
Abdallah dayay shiru tace “kaikuma fa dakai shiru haka”? Dan murmushi yayi yace “bakomi ni
zuwa zanyi ma na kwanta inada lectures gobe” Maman Aneesarh tace “dole abama Abdallah
award din shine mai fara zuwa ya kwanta agidan nan kafin kowa” murmushi yayi yawuce
abinshi.
EPISODE 1️⃣8️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Zaunarda ita Anty Binta tayi akan gado itada Amina sosai take kuka tana kwabe baki kaman
yanda yara ke kuka Anty Binta dake kallonta da yanda takeyi kawai fadomata maganan mijinta
yadingayi a zuciya she looks so cute, cute sosai yanda takeyi gashi yanda takeda kiba da yaran
kumatunta keyi yayi soo adorable kaman kasaceta kagudu she looks kaman Yar baby Yar
yarinya hakanan kawai taji Allah yasanya mata son yarinyar azuciya and idan Abee zaizo
yasota she will be so soo happy wlh, zama Anty Binta tayi kusada ita tace “dan Allah ya isa
hakanan Lujain kiyakuri” makema Anty Binta kafada tayi tana tabe baki cikin kuka tace “ni
gidanmu zani wajen Gwaggo na” murmushi dukansu biyun sukayi Amina tace “to yanzu kidaina
kuka kinga tunda babanki yayi fushi yanzu baraki iya komawa ba kibari gobe saimu maidaki
gida” rage kukan tasomayi tana kallon Amina dake magana ahankali tace “da gaske zaku kaini
wajen Gwaggo na gobe”? Gyadamata kai daga Amina har Anty Binta sukayi atare daidai su
Sajida da Zainab na shigowa da kulolin abinci da tray na drinks suka bita da kallo kaman yanda
itama ke kallonsu still hawaye nafita daga idanunta amman ba kuka takeba gashin idanunta sun
jike sharkab, suna ijiyewa suka fita Anty Binta tace “zakici abinci? Ga abincin ki nan ankawo
miki” murya chan kasa tanabin abincin da kallo tace “tea zansha da bread” tashi Anty Binta tayi
tace “bari naje nakawo miki” daidai lokacin Sajida tashigo da flask da gwangwanin madara da
Milo da chokali da karamin mug da bread Anty Binta tace “yauwa ga kayan tea nan bari nahada
miki” karba tayi Sajida tawuce tafita Anty Binta nan da nan tahada mata tea akaramin cup
tadaura akaramin tray takawo mata saman gado tabata karba tayi ahankali tana kallon fuskan
Anty Binta saikuma takalli tea yanda yake tururi Anty Binta tace “oohh zafi bakishan tea

tafashashe haka”? Gyadamata kai tayi ahankali hakan yasa Anty Binta tashiga juya tea
ahankali take sauke ijiyan zuciyan kuka saida Anty Binta ta dandana tea jin zata iyasha yasa
tamika mata karba tayi takai bakinta ta dandana jitayi yafi na Gwaggo dadi kaman bada milon
da aka sabayi aka mata anan ba bread din Anty Binta ta dauka tana kokarin budewa taciro
mata slice Lujain tamika mata cup din ahankali tace “Anty akaramin” daga Anty Binta har Amina
kallonta sukayi ayanda kadai yarinyar take orobo Masha Allah sunsan bakaramin abinci takeci
ba da murmushi Anty Binta tamata shima tasha tareda bread cup uku tasha na tea sannan tace
takoshi yunkurin sauka tafara daga kan gadon har lokacin bata daina ijiyan zuciya na kuka ba
Anty Binta tace “ina zaki”? Kaman zatai kuka tace “wanka zanyi kayan nan na cizona” wanan
karan Amina saida dariya ya kufce mata Anty Binta kuma ta murmusa tace “to ga bathroom naki
nan kije kiyi” gyadamusu kai tayi tawuce ciki duk suka bita da kallo suna kallon uban tulin
gashinta kodan family su basuda gashine oho jitayi kaman ta deba ta sammata, tashi sukayi
Amina ta tayata daukan flask din itakuma Anty Binta tadau cup da tray suka fitada shi suka rufo
mata kofa, kowa har yashige dakinshi though bawai anyi bacci bane but babu wanda ke falo
ijiye komi sukai a kitchen suka fito Hajiya suka gani tsaye gaban dakinta dake nan kasa tace
“taci abincin kuwa”? Anty Binta tace “shayi kawai tasha Hajiya” kallon Amina Hajiya tayi tace “ke
ina mijin naki” dariya tayi tace “wlh Hajiya ni baraki kadani natafi yauba kwana zanyi sai gobe
zan koma” hararanta Hajiya tayi tace “ai shikenan, saida safenku” “saida safe Hajiya” har Hajiya
tashiga daki saikuma tajuyo daidai sun zauna a falo zasu kunna kallo Hajiya tace “Binta”
dasauri Binta tadaga kanta tace “naam Hajiya” cikeda damuwa tace “dan Allah kiduba mini Yar
mutane kafin ku kwanta dan nasan Imrana ba dubata zaiyi ba” murmushi Anty Binta tayi tace
“tom yanzu ma wanka tashiga Hajiya saisa muka dan zauna anan mubata wuri” gyadamusu kai
tayi tawuce ciki dan ita bata jure hawa benen nan sabida kafafu saitafi wata bata haura sama
ba.


Tadade tana kallon bayin komi daban da bayinsu dansu normal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login