Showing 72001 words to 75000 words out of 82745 words
sweet, Hajiya tace “tafi dinning Kihada tea kisha tea ki kinji” gyadamata kai tayi tamike tsaye
ahankali tawuce feet nata Abee yabi da kallo kaman jini zasu fito wani iri yaji yanda kowa ke
ganin kafan nata zai dinga sata tana saka safa, zama tayi a dinning tahada tea awani big cup
tafara sha abinta sukuma yan falon sai hira suke, kowa na falon yay mamakin yanda Abee
yazauna yanajin hiran dudda baya cewa komi but zaman kadai dayayi zai nunamaka yanajin
dadin hiran.
Saida tagama shan tea danshi tasha sosai bataci egg da chips ba sabida yanda cikinta ya
cushe, kitchen tawuce ta wanke cup datai amfani dashi ta ijiye sannan tafito tawuce sama tana
tafiya ahankali tana kama karfen bene dan cikinta yafara ciwo daga cin abinci, tana shiga
dakinta Hijabin tacire ta ijiye kan gado tareda tsugunnawa anan kasa tadaura kanta saman
gado tarike maranta kaman wacce ke nakuda, jin cikin yafara usulin ciwo kaman zai kasheta
yasa ahankali tafara. “Wayyoooo cikina Gwaggoooo” saikuma tafashe da kuka ahankali ko
kadan batada dauriyan ciwo tun tana yarinyar kodan sabida yanda ko bigewa tayi Gwaggo
tadinga riritata kenan yasa oho amman dai batada dauriya ko kadan.
Bude kofan dakinta akai ahankali hakan yasa dasauri tadago kanta tareda juyowa takalli kofan
da rinannun idanunta Abee ne yana tsaye jikin kofan yazuba hannunshi a aljihu yana kallonta,
kokarin mikewa tsaye tayi ahankali tana dafa jikin gado ahankali sannan tajuyo tadan kalleshi
tana yarfe hannu, anatse yace “kinsha maganin ki?” Girgizamai kai tayi ahankali tana goge
fuskanta da bayan hannunta, anatse yace “dauko maganin kizo nan” gyadamai kai tayi tajuya
ahankali tafara tafiya dan magungunan nakan mirror, wani kalan dauke kai Abee yayi daga
kallonta dayakeyi, daukan ledan maganin tayi tajuyo ahankali tazo dan nesadashi ta tsaya
tareda mikamai ledan sai alokacin yajuyo ledan yasa hannu Ya karba batare daya kalli fuskanta
ba yace “ba’ashan magani da ruwa ko” dasauri tajuya wani bottle water na sabo tadauko tajuyo
tadawo tasake tsayawa nesa dashi, dago idanunshi yayi yazubamata hakan yasa dasauri
hannunta har rawa yake tashiga kokarin bude goran ruwan amman takasa dan ba karfi,
hannunshi yamika mata alamun tabashi hakan yasa ta mikamai goran da sauri karba yayi
murdawa daya yabude mata goran sannan yabata karba tayi ahankali takurbi ruwan
magungunan daya ballo yabata a hannu kaman zatai kuka babu yanda ta iya ta watsa maganin
bakinta tahadiye tana tabe fuska takai ruwan bakinta tashiga kwalkwala kusan rabin goran
tasha sannan tasauke goran mika mata ledan magungunan yayi ahankali tasa hannu ta amsa
yajuya saikuma ya tsaya chak batare daya juyowaba hakan yasa ta kalleshi, anatse yace “stop
wearing irin rigunan nan agidana!” Yana maganan yawuce turo baki tayi tareda maida kofan
tarufe murya chan kasa tace “nima kayan gabaki daya sun isheni” tai maganan tana komawa
gado kwanciya tayi tana juye juye dan cikin ciwo yake mata ahankali yafara lafamata ahaka
bacci yay awon gaba da ita.
Wuraren 1 tafarka ita kanta har mamakin baccin datakeyi take, Gwaggo tagani adakin tana
karkada magunguna ganin ta tashi zaune yasa Gwaggo ta washe baki tace “sauko kizo kigani
Lulu nadafa miki kaza da tantabara” hararan Gwaggo tayi tawuce ta tafi bayi, Gwaggo tace “wai
baraki daina fushi dani ba Iyyee Lulu sabida namiki Auren gata, jibi yanda yan uwan mijinki keji
dani, kinsan nawa abokanenshi suka bani, dukansu dubu Hansin Hansin fa, Mujittafa Hamsin,
Haruna Hansin, saikuma dan sandan nan Abdul hansin, ai wlh kinyi saa kinzo katon gida ga
jama’a aciki kuma kowa na sonki ni Allah ma makirin dan iskan nan daya batamuku suna
Albarka dan abinda yayi yazame miki alkhairi” tana maganan wayanta yashiga ringing wayan ta
kalla tace “ai nasan ubanki ne kome zakayi baran dawo gidanka gidan wahala ba, dana dinga
rokonka ka kaini ka kaini ne ina ba saida nakira surukina ba da Allah yabani number shi da kyar
ba oho saikuma kayi” tana maganan ta ijiye wayan tacigaba da abinda takeyi, fitowa Lujain tayi
daure da towel taje gaban wardrobe nata ta shirya tsaf takara komawa bayi ta ijiye wannan
towel din tadauko sabo blue ta daura tazo tazauna kusada Gwaggo data ijiyemata kula
agabanta, bude kulan tayi tana turobaki sanan tashiga cin naman Kazan dana tantabara da
Gwaggo tamata farfesu dudda farfesun magani ne amman bala’in dadi, tass ta cinye ta ijiye
kasusuwa koba komi tayi kewan Gwaggon ta wani ruwa Gwaggo tabata na sayuwa tace “sha
wannan babu daci ko kadan kaman ruwa ne” dandanawa tayi jin babu daci yasa ta shanye tace
“Gwaggo me shi”? Wani Leda Gwaggo ta ijiye tace “ba’a fadima yara meshi, anjima zakisha
wayan nan su Abida sunce na gaisheki ” wani kalan murmushi tayi tace “Gwaggo ai tare zamu
koma ko”? Dan kallonta Gwaggo tayi saikuma tai kaman bataji ba, Ahankali Lujain tace
“Gwaggo bana iya bacci agidan nan, ban sansu ba, bansaba dasu ba, Gwaggo kuraba auren
Mandawari zai aureni” wani kalan dakuwa Gwaggo tamata tace “wlh idan kina kiramini sunan
wani namiji kina matan aure saina makeki Lulu” kaman Lujain zatai kuka tace “toni nagaya
muku ina sonshi ne, ni wlh Mandawari na nakes……..” empty farantin roban gaban Gwaggo
data gama kwashe magungunan ciki ta dauka ta rapka mata akai tace “rufamini baki” wani
kalan ihu Lujain tayi gabaki dayama ta manta ba a gidansu takeba dan haka take agida idan
Gwaggo ta bugeta Aiko ranan tashiga uku saita lallasheta da kyar sannan zatai shiru, wani
kalan mikewa tsaye tayi da towel din tana kuka sosai amugun shagwabe tabude kofan dakin
tafita Gwaggo data bitada idanu tace “aisai kiyi fitsararriya” daidai tana fitowa tana kukan ta
kama kanta da Gwaggo tabugama plate daidai Abee nashigowa saman ita ko kadan batama
luradashi ba, tundagakai zuwa kafa yabita da kallo yadan tsaya yay jim kaman yajuya yakoma
falo saikuma yacigaba da tahowa ko kadan bataji sahun takalminshi ba as usual kamshin
turarenshi kadai yagayamata yana wajen hadiye kukan tayi tass sannan tadago kanta kaman
munafuka tana sauke hannayen kasa, hada idanu sukayi dawani kalan sauri tajuya zata bude
kofan dakin tashiga yace “come here” dawowa tayi ahankali kanta akasa tashiga wasa da
yatsunta dan she’s so restless, “what happen”? Taji Abee yamata tambayan muryanshi
ataushashe, dago kanta tayi takalleshi saikuma ta kwabe fuska kaman zatai kuka taredakai
hannunta saman kanta inda Gwaggo tabugama plate tace “Gwaggo ne tadakeni tabugamin
plate akai” kanda ta taba yabi da kallo ga wajen har datti datti na abinda ke plate din ke wajen,
kaman baraiyi magana ba saikuma ashanyaye yace “what did you do tadakeki?”.EPISODE 4️⃣0️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Dago manyan idanunta tayi ta kalleshi yanda ya tsareta da idanu yasa takai bayan hannunta
tagoge fuskan nata tass murya chan kasa tace “sabida nace zan bita idan zata koma gidan mu”
tunda take maganan lips nata da kumatu yake kallo, dauke kai yayi yace “jeki cemata nace
takara miki” dasauri tadago idanunta takallai, wani mugun kallo yamata yace “tunda bakijin
magana, what did I tell you about this thing” yay maganan yana pointing towel na jikinta da
hannu, dasauri ta tura kofan dakin tashiga tareda maida kofan yarufe girgiza kai kawai Abee
yayi yawuce yatafi dakinshi.
Tunda Gwaggo tashigo gidan gidan yakara wani kalan dadi da annashuwa Baba yay kiran
dubiyan nan Gwaggo taki dauka wai ita barata komaba saitagama hutun datazoyi agidan nan
koda wasa kuma babu wanda yataba muna ta isheshi koyagaji da ita saima dawowa datayi
kaman itace asalin Gwaggon gidan. Kullum dare Gwaggo saita kadata dakin Abee dakin Anty Binta take zuwa ta kwanta dan Anty
Binta ta tafi gidanta babu kowa adakin, ita rabon datasa Abee a idanu tun ranan Sunday dan
Hamza ne ke kaita school yanzu, hakama Mandawari abin bakaramin damunta yayi ba bata
ganinshi gashi babu halin taje koda kofar gidansu ne dan ba fita takeba.
Yau juma’a Baba cire kunya yayi shida Hadi sukazo har gidan bayan magrib awaje suka tsaya
dan gani sukayi Gwaggo batasan abin kunya ba tazo gidan da jikanta ke aure ta tare tun ranan
asabar haryau juma’a kwananta shidda kenan haba mana ai bai daceba.
Abee na masallaci Abdallah yazo yakirashi baiwani jimaba yafito tareda Abdallah har zuwa
wajen su Baba cikeda girmamawa Abee ya gaidasu, Baba shima cikin mutunci yace “Imrana
dan Allah kuyakuri da halin Gwaggo wlh fitinace da ita haba tazo ta tare taki tafiya” dan
murmushi Abee yayi yace “bakomi bismillan ku” dasauri Baba yace “ai muna nan munriga
munsa maigadi yakirata ta fito mutafi” danjim Abee yayi dan baisan mezaice ba, ahankali yace
“dan Allah ku barta duk randa takeso saita dawo” dasauri Hadi yace “Bakasan Gwaggo bane
Imrana bazata taba dawowa ba”……..
Sosai Gwaggo tafashe da kuka afalo kowa na falon lallashinta yake tanuna kanta tace “ni su
Hadi kema bakinciki sabida nazo gidan jikata nahuta shine harda zuwa har kofar gida amaidani
gida karfi da yaji ko….” Bude kofa Abee yayi yashigo Gwaggo takallai tana sharce hawaye tace
“Imrana sunki tafiya sunce saisun tafi dani ko”? Dan shiru yayi yakalli yanda Gwaggo ke kuka
dakuma Lujain dake gefenta ahankali yace “eh” saikuma yawuce sama baiwani dade saman ba
yafito da bandir yan 1k guda biyu a hannunshi yazo har gaban Hajiya yabata alamun tabama
Gwaggo, murmushi Hajiya tayi tabama tace “Gwaggo gashi Imrana yace abaki” ganin kudade
mikakku farare fes yasa duk wani kuka da Gwaggo take ya tsaya tace “wayyo Allah na dubu
dari biyu, Imrana nagode nagode Allah maka albarka ubangiji Allah yakawo ciki da goyo
tsakaninka da Lujain bari natafi” tamike tana tura kudin lalita duka yan dakin murmushi sukayi,
tashi Lujain tayi kaman zata bita tace “Gwag……” wani kallo da Abee yamata yasa dagudu ta
juya tai stairs tana kuka Gwaggo tace “aisai kiyi tunda bakida hankali ne da aurenki zan tafi
dake jama’a saduwan Alheri” duk rako Gwaggo sukayi har compund ta tafi Abee kuma yakoma
masallaci.
Sosai Lujain tai kuka jitayi zuciyanta yamata nauyi da zafi Kwanan nan da Gwaggo kenan
gabaki daya ta manta menene bakin ciki ko fushi har damuwan Mandawari ta manta dashi
amman daga tafiyan Gwaggo saitaji komi yamata duhu sosai ahaka bacci yay awon gaba da
ita.
Tun wajajen 3:30 tafarka tabude idanunta hakanan kawai gabanta sai faduwa yake abin namata
kaman ma zazzabi zazzabi takeji, saukowa kasa tayi ahankali tareda daura kanta akan gado
hawayene yazubo mata she’s soooo sad and she’s hungry again, all abinda takeso shine
taganta agidansu.
Bude kofa Abee yayi 4 dot yafito sai kanshi yake yau Jallabiya ce ajikinshi fara da hula akanshi
kofan Lujain ya kalla saiya karasa wajen anatse yabude kofan dago kanta tayi takalleshi suka
hada idanu kafinma yamata magana ta mikeda sauri tawuce bayi dan haushin shi takeji daya
hanata bin Gwaggon ta jiya dan jim yayi ya tsaya kaman mai tunanin wani abu saikuma yajawo
kofan yarufe yawuce yatada su Abdallah yasauka kasa yajirasu suka fice tare zuwa masallaci.
Dayake yau asabar yadade amasallacin sai wajajen 7:00 nasafe yafito tareda Baba Liman
dawasu jama’a na masallacin duk sun tsaya gaban masallaci suna magana kan Solar da Abee
yasayoma masallacin daza’a fara aikin yau kaman an jefo mutun kawai wani saurayi suka gani
agabansu ya tsaya yana sanye da jean da Riga bakake yasaka bakin facing cap da nose mask
da bakin glasses dudda sunada yawa amman Abee yake facing, daya daga cikinsu yace
“kaikuma Malam lafiya haka”? Tsugunnawa yayi agabansu ahankali tareda saka hannu yazare
facing cap din kanshi, sannan yasa hannu yazaro shades din ya ijiye sanan yacire nose mask
din ahankali ya ijiye kasa kafin gently yadago jajayen idanunshi dasuka kumbura suntum yakalli
Abee dake kallonshi, dasauri jama’an wajen suka nunashi sukace “bakaine mutumin dayama
Alhaji Imrana shairi ba ai munga hotonka a news” gyadamusu kai yayi ahankali sannan yahade
hannayenshi yana kallon Abee dake kallonshi kuri saikuma kaman wanda ya haukace ya kwala
uban kara cikin harshen turenci yace “mutanen estate din nan kufito dan Allah, gani nan nine
nama Alhaji Imrana shairi nakuma kawo kaina da kaina” daidai lokacin Mandawari yafito daga
cikin gidanshi zai tafi gudu chak ya tsaya yana kallon gaban masallacin da jama’a suka taru
harda masu gadikan anguwan dakuma mutumin hakan yasa yakarasa wajen daidai Ibro shima
yana karasawa wajen dan fitowanshi daga gidanshi kenan yazo zai shiga gidansu yaji muryan
mutumin hakan yasa yashiga kiran Hamza, kallon duka mutanen dake kallonshi kuri yayi
mutanen kuma suka cicciro wayoyinsu ana video yakalli Abee yace “dan girman Allah
kayafemini wlh wlh bantaba sani hakkin wani abune mai girma ba sai bayan namuku kazafin
nan kaida wannan innocent yarinyar” yay shiru dasauri Hamza yashiga kiran Uncle Abdul Police
shikuma Ibro yashiga kiran Uncle Musty, cikin wani kalan yanayi na tsantsan nadama yace “tun
bayan nai editing video nasaka a yanar gizo nakasa samin kwanciyan hankali dudda nai
deleting amman a banza dan yarigaada ya yada duniya, bana iya bacci, banda sukuni banda
natsuwa, kirjina da kaina wani kalan nauyi sukemin kaman an dauramini tankin ruwa akansu,
tundaga ranan dana watsa video nan idanun nan nawa basu kara runtsawa da sunann bacci ba
wlh wlh da wannan azaban gwara nakawo kaina ankaini gidan yari, nazone nafara rokonka da
yarinyar gafara kafin nakai kaina dakaina police station dan Allah dan girman Allah kuyafemini,
jama’a kutayani rokon gafara” yay magananan yana kallon kowa na wajen saikuma ya shiga
babbaka kuka sosai kana ganinshi kasan babu peace arayuwanshi, ko’ina najikinshi rawa yake
yace “wlh wlh koda wasa ba fasikanci sukayi ba nine na maida abin yazama haka da editing na
computer, wlh nine nan na shirya komi nahada wlh wlh shairin shaidan ne da ruwan ido da son
abin duniya yakaini na aikata abinda nayima Ogana mutumin daya bani aiki nake samu naciyar
da yan uwana tasanadiyanshi shine nama haka dan Allah kuyakuri” kallon Baba Liman Abee
yayi yace “Baba bari nashiga gida” gyadamai kai Baba Liman yayi hakan yasa yajuya zai wuce
karaf mutumin yakama kafarshi tareda kwanciya akasa awajen flat yana kuka sosai yace “dan
girman Allah ka yafeni kona samu na rufe idanuna yau ko baccin minti biyu ne nayi dan darajan
Allah, wlh wlh bazan karaba shairin shaidan ne nasan nabata maka suna nabatama yarinyar
suna kuyafeni” wani kalan murmushi Mandawari yayi ya gyara tsayuwa he’s enjoying the show
koba komi yanzu ai zai sakin mai babe dinshi, daidai lokacin motan polisawa har guda uku suka
shigo estate din suna jiniya, Abdul da Musty ne suka fito daga wani jeep na Musty, some police
abayansu Abdul yace “you are under arrest for defamation of character, for threat, i advice you
to keep quiet cus anything you say or do will be use against you in the court of law, kuyi
arresting nashi” kara kankame kafan Abee yayi yana ihu sosai ihun da ko’ina na anguwan na
amsawa mata har lekowa suke daga gidaje suna kallon abinda kefaruwa sai video ake,
bambareshi akayi daga kafan Abee aka dagoshi sama Musty baiyi wata wata ba abunku da
soja yabashi two sided mari at a spot yace “dan Shegiya zakaci ubanka yau” dasauri polisawan
dasuka dagoshi suka sakeshi ganin Musty soja ya mareshi, wani kalan kwashemai kafafu Musty
yayi yazube awajen kanshi yay wani kalan mugun buguwa zai kara kaimai duka Abee yakama
hannunshi gam hakan yasa cikin fushi Musty yace “ku barni natafi dashi gad-room a barrack
gobe nakawo muku shi police station wlh ko amafarki your generation to generation to more
generation bazasu taba tunanin batama wani sunaba sabida yanda zan dispilaka kai kasan
sunan wane kabata kasan waye Imran kuwa? Did you know how many lives Imran ya chanza
including mine how dare you” azuciye Musty ya yunkura zai kara kaimai duka amman yakasa
sabida yanda Abee yamai riko mai kyau, kaman jira yan anguwan suke sukace “ai wlh mumishi
duka kafin atafi dashi, jungle justice in his life bazai kara tunanin yada abun kazafi ba yana
batawa mutane suna babban mutum haka dakeda manyan yara” hannu Hamza yashiga
gyarawa shida Ibro zasu sa hannu a lallasashi wani kallo Abee yamusu yace “ku wuce gida” ba
musu duk suka juya batare da sunji dadi ba sukai gida, Abee yakalli Abdul yace “kutafi dashi
Abdul nobody should touch him again” yay maganan yana kallon mutanen dake shirin dukanshi,
bada go ahead Abdul yayi aka wuce dashi mota Abdul yabisu Abee yakalli Musty da ranshi ke
bace yana kallonsu yace “let’s go” sannan yasakeshi, sai alokacin Musty ya iya motsi dan Abee
akwai karfi, binshi Musty yayi suka wuce Mandawari yabisu da kallo wani kalan mugun kishin
Abee yake kaman ba gobe duk ta yanda ya kalli Abee Abee yafishi in any way, what did he do
how did he earned this much respect daga jama’a? Shi dudda yana footballer one of the best
yadawo anguwan nan babu maibi takanshi saidai masu gadi ne ma ke tambayanshi for selfie,
what’s so special about this man da ake sonshi sama dashi mai about 400M followers a just IG,
har neman Abee yayi a social media amman yaga he’s not on any of those social media
platform, wani kalan kishin Abee yake dabazai iya misiltawa ba baitaba haduwa da mutumin
dayaji existence nashi poses as a threat to him ba sai Abee, yarasa sukuni, yanda Abee yake
nuna baimasan dashi ba is what is killing him more, yaso bayan yama Abee maganganun nan
Abee ya nemi bala’i dashi ko yasa acireshi daga community kokuma wani abu dazai bashi liver
yay bura’uba dashi amman no baimasan ko yana rayeba.
EPISODE 4️⃣1️⃣
Falo suka shiga a tsaye sukaga su Hajiya da Ibro da Hamza da Abdallah da Maman Aneesarh