Showing 18001 words to 21000 words out of 82745 words

Chapter 7 - Sakon So Complete Hausa Novels by M Shakur .pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

218

dumfarota tacigaba da cin abincinta
gabanta na faduwa ganinsu su kusan shidda amman bata nunaba Princess na karasowa

gabanta batai wata wata ba duka kayayyakin abincinta tawani barar dasu dayasa Lujain tamike
tsaye dasauri tana kallon Princess da some much anger tace “mehaka princess”? Wani mugun
kallo princess tamata tanuna kanta tace “kinganni Miss Chubby, kinga Lily we can proudly say
eh munji muna chokes dasauran su but I can assure you this muba yan iska bane, our vaginity
is intact unlike you dakin saba har kin iya moan” wani kallan kallo Lujain tamusu tace “me akace
miki nayi I don’t understand ni kike kira da yar iska”? Wani murmushi princess tayi Lily ta tofar
da miyau agefe tace “you disgust me Lujain you look so innocent babu wanda zai miki kallon
karuwa sabida yanda kika kware a pretending” Lujain zatai magana Princess tace “kola play the
video for her” dasauri Lujain takalli Kola dake danna wayanshi yana chewing cingum abaki
kaman dan daudu saiga muryan Lujain tace “wayyooooo, Hmmm, Hmmm, hmmmm” hmmm
hmmm din was repeating babu kakkautawa da karan buga kofa babu wani baligi mai hankali da
zaiji da bazaice Iskanci akeba, Kola da abokinshi sukahau dariya Kola yace “Ashedai Fatty
bombom tasan dadi kizo muyi dake I promise zan saya miki 5 shawarma da chocolates goma
expensive ones ba irin na yan 500 din nan da kike zuwa dashi school ba” dukansu sukahau
dariya princess tace “karuwa kawai mai gindin roba” baki Lujain tabude zatai magana kawai taji
saukan drinks masu sanyi ana tsiyaya mata akai har zuwa jikinta princess tace “bari mu miki
wankan tsarki da drinks” daidai nan Principal tashigo class din dakusan all the school teachers
biyeda ita abaya.
EPISODE


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Zaro idanu Principal tayi ganin yanda suka watsa mata drinks sun mata wanka sun bata mata
jiki gabaki daya tace “what in God’s name is this Kola and co?” Da sauri duk suka wurgad da
gorunan kasa, Principal tace “to disciplinary office now!” dasauri suka fita sannan takalli Lujain
wani irin kallo da Lujain takasa fassarawa koname tace “come with me” ahankali ta tsugunna ta
dauki jakanta dake tsiyaya da drink ta kakkabe jikinta tabi bayan principal faran safan kafanta
har tusan ruwa yake sabida yanda drinks suka jikashi teachers nasu na kallonta wani kalan
kallo tawucesu ahankali suka rufamata baya suna fitowa taga student an taruuuu kawai kallonta
akeyi kaman yau aka fara ganinta a school din aka wuce da ita saikuma chan taji student na

murmuring “God forbid, ewwww wasu na cewa na karuwa” har zuwa office na principal suka
shiga principal ta zauna akan wani kujera tanuna mata wani waje teachers kuma suka fita,
anatse principal din na kallonta tace “a ina kikasan Alhaji Imran”? Zaro idanu tayi tace “na’am
waye Alhaji Imran”? Dan to be honest bamata gane kan maganan ba, ahankali Principal tace
“mai company ceramic, at first da aka fara fadamini awaya I thought maybe forcing naki yayi he
took advantage of you but after watching the video…….” Principal tai shiru daga gani kasan
maganan namata nauyi tace “after watching the video I understood komi yafaru ne with your
consent dan is so obvious, ni baran wani iya cewa komiba dan you have your rights as an adult
data wuce 18yrs you are 19, keba minor bace, all I will say is have this” tamika mata wani
takarda ahankali Lujain tasa hannu takarba ganin letter na susupension yasa dasauri takalli
principal din, Principal tace “I believe guardians naki are on their way right now tun dazu muka
kirasu wata tsohuwa da farko damuka kira mukaji, hakan yasa muka dauki second number
wanda yacemana shine mahaifinki yana hanya” shiru Lujain tayi kawai tana kallon letter ita she
don’t even know what’s happening.


Suna parking Gwaggo data gama rudewa tace “Ya ubangiji kasa ba ciwon yarinyar nan bane
yatashi ba Wanan damai makarantan takirani gabaki daya” fitowa Baba yayi tareda Mama
dasukai gaba daidai lokacin wayan Baba yahau ringing anatse yace “eh muna makarantan
yanzu, tom saikun karaso” dasauri Gwaggo tace “waye?” Ahankali yace “Abdulhadi da Yusufa
ne” fashewa da kuka Gwaggo tayi tace “kafadamin gaskiya kodai Lujain dina tamutu ne wanan
dahar ka kira kannenka suzo nan iyye kafadamin gaskiya” ja idanun Baba sukayi yakalli Mama
yace “kujirani anan bari na shiga” Gwaggo na kuka sosai tace “wlh kafanka kafana kaida
matanka damai makarantan kunki fadamin abinda ke faruwa saikuma kuhanani shiga wlh saina
shiga” dan jim Baba yayi yana kallonta saikuma yace “muje” dasauri Gwaggo tabishi tana goge
hawayenta da bakin zaninta data warware har zuwa principal office suka shiga, ganin Lujain
zaune nata kallon takardan da aka bata yasa ta taho dagudu tana shafa fuskanta tana bude
mata idanu tabude bakinta tana kallon da duba harshenta danta gane ko rashin lafiya take tace
“Alhamdulillah babu abinda yasameki yarnan Iyyee Alhamdulillah wayyo Allah zuciyata kubani
ruwa Insha” dasauri principal tabata ruwan gora budewa Gwaggo tayi ta kwankwade tass
sannan ta zauna Baba batare daya kalli Lujain ba yace “gamu principal” ahankali tace “ba
babanki takardan Lujain” ahankali Lujain tamikama Baba takardan fuskanta yakalla da jikinta
daya baci da drinks da jakanta dahar lokacin na diddigan ruwa sannan yasa hannunshi ya amsa
ya karanta yakalli principal din harzaiyi magana saikuma yatashi tareda kama hannun Lujain
yace “muje” tashi principal din tayi tace “kuyakuri sir bazan iya barin yarinyar ku tacigaba da
karatu anan makarantan nan ba she is a bad influence zata batamini sauran dalibai kuya kuri
babu abinda zan iya” sai alokacin Baba yakalleta yace “akwai abubuwa da yawa da zaki iya na
farko shine kare hakkinta jibi yanda akama y’ata wanka da drinks sabida kunga batada kani ko
Yaya amakaranta kobaki koreta bama nixan cireta daga makarantan, inaso kisan abu daya,
akwai Allah! Sannan zai wanke mini diyata agaban kowa muna nan zakusan you all have
wronged her” yaja hannun Lujain dasauri suka fita tashi Gwaggo tayi tana kallon Mama tace “ke
Maman su Samira me akace tayi ne kifadamin” chak Mama ta tsaya kaman jira take tace
“yarinyan dakike mana tunkaho da ita kina fifitata kan nawa yaran video dinta dawani kato

dasukaje excursion akafaninshi na yawo a yanar gizo suna fasikanci sun shiga bayi yana
dugurguzanta diyarki na ihun dadi” wani kalan zaro idanu Gwaggo tayi tace “mene shairin kine
dai ko” wayanta Mama taciro anan office an principal takunnama Gwaggo video tundaga lokaci
da Abee ke kokarin kwance belt har zuwa lokacin daya shiga bayi ga muryan Lujain nan dako
amarfi tasani tai ihu wayyooo saikuma uhmmm Uhmm uhmmm saikuma chan aka nuno Laujain
tafito corridor tana gyara riganta tajuya dasauri ta tafi tunda Gwaggo take bata tabajin tashin
hankali hakaba baya tayi zata sume dasauri Mama ta tarota tace “ni kada ki sumemin yace
dagangan na nuna miki inason kashemai uwa mutafi” takama hannun Gwaggo tanaja suka fita
awaje taga duka yaranta da Yusuf da Abdulhadi dukansu suna sanye da manyan kaya sai
Yayanta sunyi jugum suna kallon Lujain da idanunta sunyi ja ganin Gwaggo tafito anriketa yasa
tai wajen Gwaggo da sauri saiga hawaye, zaunawa Gwaggo tayi akasa tana zaunar da Lujain
bata damu da yan makaranta ba tanuna kanta tace “Lulu tun kina cikin kwalban asibiti nake
rainanki nasanki ciki da bai nasan halinki tsaf amman bansan ki da Iskanci ba kifadamin gaskiya
meyamiki kike ihu” zaro idanu tayi dukta rude tace “waye? Wani ihu Gwaggo”? Wani kalan
fizgota Baba yayi cikin ihu kaman zai mareta yace “ranan dakukaje excursion me mutumin nan
yamiki abayi kike ihu”? Jikinta har rawa yake ganin Baba na shirin dukanta tafashe da kuka tace
“wlh babu komi Baba” Baba Abdulhadi yace “to ubanme aka miki kike ihu”? Cikin kuka sosai
tace “Baffa wlh naje bayi na kalli video wan nan dan kwallon Mandawari ne awaya” kusan
dukansu atare sukace “a ina kika sami waya”? Cikin kuka sosai tace “wajen Ya Samira na ara
bayan nabiyata da kudin asusu na” Baba yace “saime yafaru”? Cikin kuka sosai tace “ina zaune
kan masai nasa earpiece a kunne kawai naga mutum yashigo yana kokarin cire wando”
dukansu sukace “Meya miki kike ihu” jikinta har bari yake tana haki tace “wlh babu abinda
yamin tsoro naji nadauka aljani ne saisa nadinga ihu na manne jikin kofa shine yamin ihu yace
nafita nace ban iya bude kofaba shine yace na matsa yabudemin na fice yay min ball da jaka da
wayan Ya Samira harta fashe na kawasa na tafi shikenan” kaman jira Mama take tace “wlh wlh
karya kike ke yanzu ki kalli tsabaragen idanun Babanki da Baffan ki kina karya, kifadi gaskiya
tun yaushe kika fara iskanci eh? Daman naga gabobin jikinki sai kara habbaka suke waya
koyamiki? Wayake matseki? A ina kika sanshi dahar kuka hadu abayi yaushe kika dawo Yar
iska mayyan maza Lujain”? Wani kalan fashewa da kuka sosai Lujain tayi tama kasa magana
sabida yanda kukan yafi karfinta jin maganganun Mama, tashi Gwaggo tayi tana kakkabe
jikinta takalli Baba tace “ku kaini kampanin yanzun nan” kallonta sukayi duka cikeda bala’i tace
“ku kaini kampanin nan Kona tare abin hawa nakai kaina, koya mata wani abu kobai mataba bai
isa tasanadin shi a batamin sunan diya ba a yanar gizo duniya tagama ganinta, wlh wlh yau sai
anyita an kare” Baffa Abdulhadi yakalli Baba yace “Baba dole dama muje muganshi idan ma
za’a kai kara hukuma ne asan nayi kumuje” Ahankali Baba yabude motarshi suna suka bude
tasu aka shiga har akakai company nan kuka Lujain takeyi sai yanzu tagane abinda yasa su
Princess suka kirata har karuwa dudda bata kallo video ba suna kaiwa company reporters
dasuka gani agaban kampanin sunfi hamsin saukowa akayi Gwaggo takama hannunta suka
wuce ciki ganin ana musu hoto mayafin jikinta tayaye tayafama Lujain dake kuka tarike
hannunta sukai wajen shiga taresu security yayi Gwaggo da idanunta sukai jajir tace “na rantse
maka da ubangiji zan tube nai dambe dakai awajen nan kace bazamu shiga ba, dan ubanka
Mudi da Uwarka Safara’u idan akai kokarin batama jikanka suna bazakayi abinda yafi haka ba
budemin kofa kona fasa” girgiza mata kai yayi yace “Mama Oga yace ba shiga ba fita bakiga

yan jarida sun cika nan ba” cikin ihu Gwaggo tace “yo ina ruwana shi yasan Meyayi ai” jin yanda
Gwaggo ke ihu Hamza da idanunshi sukai jajir yazo wajen daga ciki ganin student din
makarantan nan da aka lullube da mayafi tana kuka sosai from yanda jikinta ke bari ga
wayanda ke tareda ita dazai iya cewa iyayenta ne yasa ahankali yace “kushigo” bude musu
kofa akayi Gwaggo taja hannun Lujain suka shiga ciki, waje yanuna musu awajen yace “ku
zauna bari naje na sanar” cikin ihu Gwaggo da idanubta sun juya tace “nabaka minti biyu” stairs
yayi karo yaci da Ibro da shima idanunshi sunyi jajir yana kallon su Gwaggo da yarinyan dake
sanye da uniform da aka lullube da gyale ahankali Hamza yace “I think is the girls family ka kira
Uncle Musty” gyadamai kai yayi yace “yama iso he’s trying to come inside” daidai lokacin
wayanshi yahau ringing dasauri Hamza yace “Hajiya ko” gyadamai kai yayi ahankali, hawaye ne
yakawo idanun Hamza dan he’s a very soft person yace “kana tunanin tasani” gyadamai kai
yayi yace “kaima kasan that’s the only answer to yanda taketa kiranmu tun dazu clean those
tears if our workers saw that kanason suyi tunanin Ya Imran zai iya aikata abin ne” girgixamai
kai tayi daidai lokacin Musty na sanye da kayan sojoji da Haruna dakuma wani babban
abokinsu police man su uku suka taho ganinsu yasa Musty yace “calm down you all Ya Imran
din”? Ahankali Ibro yace “yana office working as if nothing is happening amman nasan deep
down he’s hurting bama wanan ba Uncle Musty I believe the girl’s parent are here gasuchan”
yanunasu ahankali Uncle yace “Innalillahi wa innailaihi raji’un! Allahumma ajirni fi musibati”
yakalli hannu da police man yace “kuje ku kutaho dasu lemme see him” yana maganan yawuce
sama su Hamza suka bishi ahankali yabude kofan office din Abee, kallo daya Abee yamai
yacigaba da aikin dayakeyi bazaka iya gane takamaiman reaction dake kan fuskanshi ba
karasawa gaban table din Musty yayi ahankali yace “the girl’s parents are here” chack ya tsayar
da typing din dayakeyi batare daya kalli Musty ba, anatse Musty yace “nace su Harun su taho
dasu nan we need to speak to them and show them, but maisa baka fadamin komi ba eh Imran”
dago idanunshi Abee yayi yama Musty wani kallo yace “me kake so nagaya maka takamaimai
nace maka wani anonymous number sent me a text demanding 100M and this company’s
document koyay releasing video tarayyana da wata da I know nothing about!”?

Knocking kofan akayi kallon Abee Mustafa yayi yace “gasunan” sanan yajuya yace “bude musu
kofa Hamza” juyawa Hamza yayi ahankali yabude kofan Haruna da Police nan mai suna Abdul
ne suka shigo sai Gwaggo data rike hannun Lujain gam dake lullube suka shigo tana hura hanci
sai Baba dasu Baffa da Yayan Lujain sai Mama wuri harun yanuna musu kan dogon setin
kujerun office din zazzamansukayi Gwaggo ta zaunar da Lujain da sheshekan kukanta kawai
ketashi acikin office din itakuma Gwaggo tabi kowa na office din da kallo tace “nifa ba zama
takawoni ba waye mutum dayaja sunan diyata yabaci aduniya ina mai kampanin?” Ahankali
Abee da kanshi ke kasa yadago kanshi gently yazubama Gwaggo idanunshi da hakanan kawai
taji magana ya makale abakinta.
SAKON SO


M SHAKUR ✍

Abu daya zan fadamuku gareku masucin hakki na, da masu daukan book dina suna sawa a site
dinsu, damasu sawa a YouTube, da dukma wata ko wani mai amfani da book dina yana kudi
without consulting me wlh wlh ban yafeba kuma bazaku taba ganin cigaba ba dan hakkin wani
kukeci, kome zakuyi da rubutu na contact me first! 07012181461


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuna kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da
Episode biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



EPISODE 1️⃣
~Masjid Ibn Taymiyah~
Aka rubuta ajikin babban masallacin dake cike makil da jama’a kowa yaci manyan kaya
manyan shaddoji da kanagani kasan daurin aure ake shirinyi, wani matashin saurayine ke
sanye da manyan kaya dakuma babban Riga na shadda datasha aiki yana tsaye daga ta wajen
masallacin yana kallon agogon hannunshi da alamu lokaci yake dubawa chan kuma yadago
kanshi yana leken kan titin da masallacin ke kai, tabashi akayi daga baya dayasa dasauri ya
waigo wani matashin saurayine yatabashi shima yana sanye da manyan kaya yasha hula kube,
cikeda damuwa yace “he’s 20minutes late Arif kazo mutafi koda na’ibin limamum masallacin
nanne ya karba maka Auren, duk an taru mutum daya ake jira haba mana is not cool”
girgizamai kai wanda aka kirada Arif yayi yace “I know he will come let’s just give him some
time, Uncle Hamma is just…..” dasauri abokin yace “sociopath” wani mugun kallo Arif yamai
zaiyi magana daidai wata Babban jeep na parking abangaren masallacin dayadan sami space
na parking, wani kalan walwala ne ya bayyana akan fuskan Arif baisan lokacin dayabar abokin
nashi yafice daga cikin premises na masallacin dasauri ba dudda jama’a na kwalamai kira ta
ko’ina suna ango ango baibi takansu ba yay wajen motan dayake nan bamaka ganin kowa na
ciki sabida tinted glass ne duka kuma arufe, ahankali yasa hannunshi batare daya jiraba yabude
gaban motan bangaren mazaunin direba tareda tsugunnawa har kasa cikeda girmamawa
batare dayama kalli fuskan mutumin dake cikin motanba yace “barka da zuwa Uncle Imran”
wani magidancin mutum ne zaune cikin motan da akalla zaiyi 48/49yrs yana sanye dawani soft
milk yadi daya haska bakar fatanshi dake bala’in sheki tsabagen hutu.

Yanada cikan gashin gemu sosai gasunan baki sidik masu tsayi kadan dawasu sirarren saje
dakenan a kwance suma lublub, ga cikan gashin gira dakuma suman kai dudda lafiyayyan
hulan minister na kanshi hakan bazaisa kagane cewa yanada cikan sumaba, yanada wasu
kalan kananun yet manyan idanu idan ya zubamaka su idanba ka natsu ka kalleshi ba zaka
dauka idanun nashi a lumshe suke amman abude suke ras kwayan idanun farare fat, hancinshi
dogone sosai kuma siriri sai lips dinshi dakenan jazur, kallo daya yama Arif dake tsugunne
kanshi akasa babu wani murmushi ko fara’a akan fuskanshi sannan kuma babu wani bacinrai
ko wani yanayi akan fuskanshi saima fuskanshi dake nan adake dake lullube dawani kalan
warm rahama akai, kaman baiso yay magana yace “Arif” wani kalan murmushi Arif din yasaki
cike da mugun girmamawa yace “na’am Uncle Imran” tareda dago kanshi yadan kalleshi
saikuma yasake sauke kan nashi kasa dasauri baitaba ganin mutumin dake tattare dawani
kalan mugun kwarjini dakuma haiba irin na Uncle Imran ba, duk yanda kakai ga bushewar
idanunka baka iya kallon tsabaragen idanun Uncle Imran kamai, Ahankali kaman baiso yay
magana cikeda wannan natsuwan yace “get up kayanka will get dirty” tashi Arif yayi babu
gardama still kanshi na kasa hakan yasa anatse ya sauko daga cikin motan yafito ya tsaya
kusada Arif duk tsayin Arif akafadar Uncle Imran yake dan Uncle Imran giant ne sosai, dudda
babba ne shi ya manyanta amman jikinshi da gabobinshi gabaki daya atsaye suke tsaf kana
ganinshi kaga wanda yake gyara jikinshi ta hanyar cin lafiyayen abinci dakuma excercise, yana
sanye da babban riga dake kyalli da wandonshi daya tsayamai a daidai idanun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login