Showing 24001 words to 27000 words out of 82745 words

Chapter 9 - Sakon So Complete Hausa Novels by M Shakur .pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

226

trending na babansu, Zainab data tafi daga ita har mijinta sun dawo,
kofar gidansu yacika kaman anyi mutuwa dayan anguwa babu wanda baya sonshi a anguwan
dukansu sun karyata guards na estate dinsu sun hana ko reporter daya ya shiga saida su Musty
suka fara gaisawa da mutanen waje sukace shairi akamai sannan suka shiga ciki bayan babban
Liman na anguwan wanda yake matsayin ubansu yabisu zuwa cikin gida duk suka zazzauna a
falo idanun kausar yay jajir taci kuka harta gaji na Abdallah ma haka amman shi baiyi kuka ba.



Hajiya kafin suyi magana tace “ina yake”? Musty yace “ai kinsan Imran da taurin kai yace aiki
yake sai 4 yake tashi daga aiki munbarshi achan danko jawoshi zamuyi da karfi bazai tahoba
amman Ibro da Hamza na chan tareda shi karki damu” tagumi Hajiya tayi Anty Binta ta bubbuga
mata baya yace “dan Allah Hajiya kada kidamu kanki” anatse Hajiya tace “Meya faru Musty”?
Ahankali yabasu labarin daga farko har karshe tsaf da yanda iyayen yarinyar sukazo da abinda
sukayi kowa yay tsit adakin na kusan minti biyar sannan Hajiya tai breaking shiru takalli Liman
tace “Liman kaine kake matsayin mahaifin yaron nan yakake ganin za’ayi”? Ahankali Liman
yace “shi aure rufin asiri ne kuma sutura ne ga mumini, gabaki dayan mu nan munsan Imran
bazai taba iya aikata wannan abuba abinda nakeso kuduba anan shine ayar dake tattare da
abin nan inhar Allah ya shiryamai wannan kaddaran to da dalili, saikuma abu nabiyu shine inhar
akabar zancen nan haka shikenan yabata ma ita yarinyar dashi Imran suna nan da gobe zakuji
wasu sabbin labarai da kazafi da sauransu natashi indai mutane ne, saikuma sana’arshi da
kampaninshi zai jijjiga that is idan hukuma bata shigo bama ta rufe company gabadaya ba,
amman yanzu duk idan kuka ijiye sauran hujjojin nan kuka dauki hujjan farko dana kawo
kaddaran suce Allah yaga dama yakuma tsara musu ita ahakan dan haka ayarda da auren
amusu auren amusu auren asanara duniya su daman ma’aurata ne dan killace mutuncinsu
hakan kadaine za’ayi ya wankesu shikuma yaron kubashi dududu satin nan dakanshi zai kawo
kafanshi yanemi gafara zan nunamai ayar Allah ba wasa bane sannan Allah sarki ne tsarkakke
Al Azza Wajal! Dan haka mu amince da abinda sukace mu kalli maraicin yarinyar”, dan hawaye
Hajja ta share tace “nasan bazai taba yarda yay aure nan ba, babu abinda Abee ya tsana
kaman aure, amman yau zan nunamai nine mahaifiyarshi, zan iya komi dan kare mutuncinshi
aduniyan nan” sallama Liman yamusu yatafi sukuma kowa yay zugum falo saida aka kira
la’asar ne ma su Musty suka tuna ko azahar basuyibasuka wuce.



Biyar daidai on the dot Hamza da Ibro suka shigo office din yana zaune akan kujeran su kallo
daya yamusu yadauke kai anatse Ibro yace “Yaya Imran is 5 mutafi gida” dago idanunshi yayi
yakalleshi ahankali Ibro yasauke kanshi kasa dan gabaki dayansu babu mai iya jure idanun Ya
Imran akansu kwarjininshi is way to much, kaman daga sama yace “yaushe nida ku muka fara
barin office tare?” Da sauri dukansu suka dagakai suka kalleshi karamin Mac book dinshi da
yan kananun abubuwanshi yashiga hadawa batare daya kallesu ba babu alamun wasa akan
voice nashi yace “ku kama gabanku” daidai yatashi daga kan chair din tareda daukan Car key

nashi laptop dinshi a hannunshi yafito wuce su yayi duk suna tsaye suna kallonshi yabude kofa
yafice dasauri suka fito Ibro ya tsaya yana kulle office din ganin yayi hanyar dazai kaishi main
entrance suda sukeso yabi ta kofan baya dan reporters har yanzu na main entrance yasa aguje
suka bishi yana jinsu amman ko juyowa baiyiba yakallesu anatse yake tafiya one after another
kaman mai sarauta har zuwa gate din suma security nashi daga gaban entrance din ganin Oga
yasa sukaji kaman sucemai yajuya yakoma ta dayan exit din amman shakka da tsoro
yahanasu, budemai kofa sukayi yafice reporters na ganinshi suka taso aguje ana binshi kowa
da kalan tambayan dayake watsamai koransu security nashi suka dingayi suka rike hannu suka
taresu shikuma yay wajen motanshi yabude laptop dinshi ya ijiye a dayan sit na gaban sannan
yashiga yarufe kofa yatada motan yafice, su Hamza ma suka shiga motocin su suka mar mishi
baya.

Agaban estate nasu wasu reporter yagani but anhanasu shiga dayake motarshi tinted ne
basusan shibane aka budemai gate yashige abinshi yan jama’a yagani akofar gidansu ciki
harda Arif dolenshi ya tsaya akofar gidansu yasauke glass batare daya sakko daga motan ba,
chaaa jama’an anguwa sukamai akai suna Allah kyauta Alhaji duk mai nufinka da shairi Allah ya
maida musu Liman yamana bayanin komi Allah natare dakai kuma zamu nunama mutumin ayar
Allah ba abin wasa bane wlh saiyazo harnan anguwan dakanshi yabada hakuri dan murmushi
yamusu yace “nagode” hakan yasa suka watse saura Arif kadai da idanunshi sukai jaa yataho
wajen motan ahankali zubamai idanu Abee yayi kaman babu wani abu yace “what are you
doing here kabar Amarya”? Kasa magana Arif yayi but kana ganin hankalinshi kasan atashe
yake, dan murmushi Abee yamai kadan yace “wuce ka koma gidanka” gyadamai kai Arif yayi
ahankali babu musu yakoma yashiga motarshi shikuma Abee yatada motanshi aka budemai
gate yashiga cikin gidansu.

You can read EPISODE 13 a IGEPISODE 1️⃣3️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Parking yayi awajen parking nacikin gidan, yakai kusan 5min zaune acikin motan ya jinginar da
kanshi tareda lumshe idanu sannan yatashi yabude kofan motan yafito ahankali da Maigadin

yafaracin karo da shima idanunshi yay ja sai kallon Abee yake kaman yauya fara ganinshi,
dauke kanshi Abee yayi, laptop dinshi ya dauka yamaida kofan motan yarufe sannan yay cikin
gidan da sallama chan kasa yabude kofan Babban falonsu yashiga kowa na zaune falon harda
Zainab dayasan takoma gidanta kaman gidan da akai mutuwa duk suna kallonshi ga Hajiya ita
tabuga tagumi itama kallonshi take, ahankali yace “ina wuni Hajiya” batare daya jira amsanta ba
yawuce stairs dasaurinshi dan baimason wani magana yana zuwa yabude dakinshi yashiga ciki,
zama yayi ahankali bakin kujeranshi yacire takalminshi da safan kafanshi kafin yatashi yamike
tsaye ahankali yake tafiya zuwa bakin gado gently ya kwanta akan gadon tareda fuzar da ajiyan
zuciya ya lumshe ido ahankali yanajin kaman zazzabi na neman kamashi, knocking kofarshi da
akayi yasa ya runtse idanunshi da karfi yabudesu ahankali batare dayay magana ba, muryan
Kausar yaji ahankali tace “Abee” tashi zaune yayi da sauri yakalli kofan anatse yace “come in”
bude kofan dakin akayi Kausar yagani tareda Abdallah idanunsu sunyi jaa suna tsaye gaban
dakin duk suna kallonshi dawasu kalan disturbing eyes, wani abu yaji ya tsayamai azuciya
amman yadaure batare da wani abu yanuna akan fuskanshi yace “kushigo” Kausar tafara
shigowa da gudu tana zuwa batai wata wata ba kneeling tayi akasan gaban gadon gabanshi
kawai tafada jikinshi tasa kanta akirjin ta rungumeshi ta kulle hannayenta ta bayanshi ta
kankameshi sosai tawani kalan fashe da kuka duk duniyan nan batada abinda takeso kaman
babanta, ahankali Abdallah da Abee ke kallo yanajin yanda Kausar ke kuka ajikinshi yakaraso
wajen shima zama yayi akusa da mahaifin nashi agefen gado gently yadaura kanshi kan
kafadan Babanshi batare dayace komiba, saukan dumin hawayenshi Abee yaji kan kafadarshi
tunda abin nan yafaru sai yanzu ne Abee yaji kawai he’s completely heartbroken sabida yanda
yaranshi suke kuka ajikinshi, Kausar ita wannan daman ta iya kuka but Abdallah rabon dayaga
kukan Abdallah tunda mahaifiyarshi da yayyinshi suka rasu, shiru yayi jikinshi yayi wani kalan
sanyi baimasan wane zai lallasa cikinsu ba, baisan mezai gayamusu ba, all he knows is yau
shine reason behind his children tears, kusan 10min kuka suke ajikinshi hakan yasa yasauke
ijiyan zuciya Abdallah yafara dago kanshi da hannunshi yace “mehaka kakeyi Abdallah Men
don’t cry” dago fuskan Kausar yayi daga jikinshi dake kuka sosai hannunshi yakai yasharemata
hawaye yadanyi murmushi tareda jan mata hanci yace “kinsan bansan kuka ko” girgizamai kai
tayi cikin wani kalan sheshekan kuka tace “mekamusu akeson abata maka suna Abee, me
Babana yamusu? Why you Abee”? Kifa kanta tayi akan kafanshi tahau kuka sosai gwanin ban
tausayi, dagota Abee yayi idanunshi sunyi ja yakalleta dan murmushi yakakalo yakalli Abdallah
dake kallonshi yama rasa abinda zaice musu kawai rungumesu duka yayi akirjinshi duk suka
kankameshi kaman yanda he was holding them so tight, bayansu ya bubbuga anatse calmly
trying to soothe them yace “everything is going to be fine I promise” yay shiru jin haryanzu
hawayen su na zuba ajikinsu yace “if you two wants to break me kucigaba da kukan nan”
kaman yabasu pills din tsayarda kukan sukayi hakan yasa yadago kansu murmushi yamusu
yahada hannayensu biyu yakai bakinshi yamusu peck ahankali yace “you two are Abee’s
strength if you break I break, so I want you to be my strength not my weakness kunji, everything
is going to be fine I promise” gyadamai kai sukayi ahankali, murmushi yayi yaciro handkerchief
a aljihunshi fuskan Abdallah yafara gogewa tass sannan yashare na Kausar shima tass
ahankali yace “jeki kawomin abinci I am hungry” dasauri ta tashi tana gyadamai kai tafice daga
dakin hakan yasa Abee yakalli Abdallah yace “mesa zaka biyema Kausar kuyita kuka idan
tanayi bakasan kaine zaka lallasheta ba”? Gydama Abee kai yayi, Abee yay shiru yana

kallonshi saikuma chan yace “how many lectures kai missing yau?” Ahankali yace “all” cikeda
rashin nuna jin dadi Abee yace “kar hakan yasake faruwa” gyadamai kai Abdallah yayi daidai
Kausar takawo abinci fried rice a tray da flask na shayin shi zama yayi ahankali akasa sannan
yakalli Abdallah dake kan gado yace “sauko” debo abincin yayi yakai bakin Abdallah yace “haa”
dan yasan dukansu biyun basuci abinci ba tsaf yay feeding nasu yasha shayi sannan yasa suka
tafi shikuma yashiga bayi dan yay wanka yayi shirin zuwa masallaci magrib.


Shiryawa yayi cikin wani sky blue soft yadi mai kyau dinkin jumper da wandonshi iya idon sahu,
hula yasaka sai uban kanshi yake yazura takalmi yafito daga daki afalo yaga su Hajiya da
sauran yaran Hamza Abdallah da Ibro na ganinshi suka mike dan zuwa masallaci yakalli su
Binta yace “salat” ahankali tace “eh duk yanzu zamu tashi Yaya” suka wuce suka fita, saida
akayi isha’i yazauna yakarasa addu’o’in shi mikewa yayi zai tashi Baba Liman yace “Imrana
biyoni” ahankali Abee yabi bayan Baba Liman daya daukeshi amatsayin uba har zuwa waje
gaban wata Babban jeep da kallo daya yamata yasan motan Musty ne, bayan motan
yabudemai yajuya yana kallonshi yace “shiga” dan jimm yayi ganin Musty da Harun ne agaban
, Baba Liman yace “koban isa bane Imrana” babu musu yataho ahankali yashiga bayan motan
Liman yashiga sannan yarufo kofan motan Musty yaja motan.



Suna kaiwa kofar gidan da Gwaggo tamusu kwatance ga mamakinshi motan Ibro da Abdul
yagani akofar gidan, Hajiya, Anty Binta, sai Hamza da Ibro duk suna tsaitsaye da alamu su
kawai ake jira, kofa Baba Liman yabude yafito yakalli Abee dake zaune yace “fito” ahankali
Abee yafito daidai Baba yabude gate yafito sabida sallama da akace anayi dashi daman suna
expecting nasu hakan yasa yagaisa da kowa yace “bismillan ku”.


Falon Baba aka kaisu duk aka zazzauna kujerun ciki basu dauki kowa ba hakan yasa duk suka
zazzauna akasa daga Hajiya sai Baba Liman ne akan kujera da Gwaggo datake zaune har
yanzu kayan dazu ne ajikinta sai Mama da Baba, su Samira na dakinsu duk sun zauna jingine
da kofa dan suji ne za’ace, yanda Gwaggo kebin kowa da kallo kasan daidai take da kowa Baba
na shirin magana tadagamai hannu tace “dakata Malam ai ba kai kabasu adreshin gidan nan
bako dan haka wajena sukazo” Takalli Musty tace “kun yarda da sharadin nawa”? kafin Musty
yay magana Baba Liman yay gyaran murya hakan yasa akai shiru adakin taron yabude da
addu’a sannan yace “na farko dai nine ke matsayin mahaifi ga dukan yaran nan, marigayi
mahaifinsu babban abokinane, dukanmu munzo nan ne mukara jajantawa sannan mubaku
hakuri kan abinda yafaru wanan abin kaddaran, sannan na tunatar damu cewa mu musulmaine
hakkine akanmu na murufawa juna asiri, sannan kusani cewa abin nan dayafaru tun kafin
dukanmu nan muzo duniya aka rubuta hakan zai faru a Lawhun Mahfuz dan haka” yakalli
Hajiya da ahankali tace “nine mahaifiyar Imrana, amatsayina na mahaifiyarshi na yarda da
zancen Auren nan!” Wani kalan dagokai Abee yayi yakalli Hajiya dan baitaba sanin abinda suka
yankeba kenan shifa yadauka sunzo ayi sulhu sunada hakuri ne but what is it yake fadi haka

wani kalan rawa hannuwanshi suka fara gently Musty yadaura hannunshi saman hannayenshi
dake rawa yarike hakan yasa yadago ifanunshi yakalli Musty da idanu yamai alamu da karyay
magana ya kunyata iyayenshi, ahankali Hajiya tace “Imrana soja ne, yanadaga cikin manyan
sojojin da Nigeria ta tura su yaki yan kungiyan bamaiyi dasuka addabi Nigeria dasaka
bamabamai shekaru 13 kenan dasuka wuce, shine sojan dayaci nasaran kashe asalin Ogansu
gabaki daya hakan yajawo mishi makiya har akazo har gidanshi aka kashemai mata da yara
biyu sauran yara biyun ma da baa kasheba dan yaranshi hudu Allah ya tsirar dasu ne sabida
sunzo gidana su kwana, tun lokacin bai kara aure ba, d’ana kamili ne adali kuma yarone da
amana dayarike addininshi da gaskiya, ni nasan Imrana bazai tabayin abinda aka ce yayi ba
amman tunda haka kaddaran tajuyo wayemu dazamuja da ikon Allah mun yarda adaura Auren
Allah yasa hakane mafi alkhairi” washe baki Gwaggo tayi tace “Alhamdulillah Alhamdulillah”
takalli Baba dake kallonta tace “ka tsareni da idanu waye zai rikemana diya amana inba mutum
haka daya samu kyakkyawan shaida ba takanas takano wannan tsohon limamun yabiyoshi
harnan shima yamishi shaidan kirki, dazu nan nan su Abdulhadi damuka bincike suka dawo
suka ce duka yan anguwansu sun bada shaidan kirki idan baka aurama jikata mutum hakaba
kamili Babba mai hankali wazaka auramawa Iyyee” Ahankali Baba yakalli Baba Liman yace
“bismillah Liman adaura” wani kalan mugun ciwon kai Abee yaji yanaji idanunshi namai wasu
kalan duhu Misty yarikeshi gam batare da kowa yay noticing ba, agabanshi yana zaune yana
kallon kowa aka daura aure tsakaninshi da Lujain akan sadaki dubu dari biyu da friends dinshi
Musty Harun da Abdul suka biya take yanke in cash, Gwaggo tace “jedakina Hadi ka kwaso
goro” dasauri Hajiya tace “Muma muntaho dashi tashi ku kwaso Hamza da Ibro” tashi sukayi
nan da nan suka fara shigo da carton carton na goro da sweet ana kawowa falon Abee na
mamakin lokacin da duk aka sayo abubuwa haka but yasan aikin Hajiya dasu Musty ne shiru
kowa na dakin yayi banda Gwaggo data tashi tana bare kwalin sweet da Goro tana kakkasawa
kana ganinta kasan ita kadaine ke farinciki da wannan auren.

Dan gyaran murya Abdul yayi yakalli Gwaggo yace “Kaka mu bangaren police muna bukatan
video da statement naku dazaku bayar amatsayin shaida cewa sudin mata da miji ne sabida
duniya tagani hakan zai siliencing kowa kafin ayi tracking yaron shima muna kan hakan” dasauri
Gwaggo ta ijiye kwalin tace “to fara dani” kunna video yayi yace “Kaka waye Imarana” washe
baki tace “mijin jikata ne, jikata matarshi ce” yama su Baba dasu Baffa sannan yama Hajiya tace
“Lujain Matar d’ana ne” saida yagama sannan yay murmushi yamaida wayan aljihu yazauna
dakin aka karayin shiru anatse Liman yace “Alhamdulillah yanzu an daura aure Imrana Lujain
matarka ce yanzu sai magana tagaba aahhh yaushe zata tare”? Gamgam Musty yarike hannun
Abee dayaji na rawa sosai, Baba na shirin magana Gwaggo tace “zakudan bamu kwanaki
mudan shirya, tunda yau litinin ranan asabar idan Allah yakaimu mahaifinta dakanshi zai kaita
dakinta ko”? Gyadamata kai Baba yayi yace “in sha Allah” Gwaggo tai murmushi tace “yanzu
ma dan tai bacci ne dana turota ta gaisheku tunda nake bantaba ganin Lulu tai irin kukan datayi
yauba har muka dawo gida har magrib kuka yarinyar nan take Allah dai yasaka muku dagakai
Imrana har Matar taka Lujain, kutashi kutafi gida shima yaje yahuta Allah kadai yasan yanda
zuciyanshi ke tafarfasa Dan mutum kamili dashi wani gantalalle chan Ya batamaka suna ana
kiranka da fasiki, Allah ubangiji ya saka muku yakuma bimuku hakkin ku, yanzu fa anxama daya
zamu hadu mu kare mutunci yaranmu ne murufa musu asiri, kai dan nan idan akwai wani video

dakakeso nayi kuma kazo zan maka In har hakan zai kawo saukin lamarin nan” dan murmushi
Abdul yayi, Baba Liman yatashi hakan yasa Gwaggo da kowa na dakin suka tashi gaggaisawa
akayi Gwaggo da Hajiya sukai sallama sannnan har waje suka rakasu suka tafi.
EPISODE 1️⃣4️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Gwaggo kotakan su Baba batabi ba bangarenta takoma tana shiga tamaida kofan dakinta tarufe
tasaka sakata ta ijiye kwalin sweet da goron data shigo dashi akasa sannan tawuce uwardakan
tana kallon fuskan Lujain dake kwance kan gado daure dawani farin towel kanta babu dankwali
idanunta sun kumbura sosai da fuskanta ma, karasawa gaban gadon Gwaggo tayi tazauna
ahankali tana kallon fuskanta murya chan kasa tace “bantaba sanin kankanin abu na faruwa ba
dazai kawo wani rayuwanka wanda hakan yake kaman aya agareka ne sai akanki Lulu, ninafi
kowa sanin yanda kikeson wannan gantalallen dan kwallon Mandawari, yau agabana kika fasa
zunzurutun asusunki kika kaima wanan kuran kudin Samira dan kawai ta aramiki waya ki kalli
dan daudun mesaka hakorin makka, ni tsabagen yanda nama tsani yaron da kullum kike
nunamini awaya idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login