Showing 15001 words to 18000 words out of 19701 words

Chapter 6 - WATA KARUWA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

107

shafeshi saidai naji a gurin
Hanisa gatanan dake itan aminiyarsa ce to yanzu wani lbr jiya da daddare take bani iyayensa
sun matsa masa sai ya fitar da matar aure kuma ni yayimin alƙawarin aure so fahimtar da nayi
kamar ba da gaske yakeson aurena ba Ni kuma aurensa nakeso da gaske"



Murmushi Mal Wada yayi ya ɗauko ƙasar sa da yake bugu da ita yayi zanensa ya shafe ya sake

yin wani ya kuma shafewa saida ya zana sau bakwai yana shafewa sannan ya ɗago duk ya
haɗa zuffa ya zubawa Aneesah da kanta ke ƙasa tana chat ido tsayin lkc Hasina tace “Mal ka
kafeta da ido bakace komai ba" jinjina kai yayi yace “Wato Hasina lamarin akwai ƙura a cikinsa
tabbas a baya kinso samun guri a zuciyar Abdul-Ahad Amma fah yanzu a halin da ake ciki
kwata² babuke a lissafinsa hasali ma ko zancenki baya ƙauna ke in taƙaice Miki ma matarsa ta
gabata gareshi....."
Wata zabura Hasina tayi tace “Innanillahi nashiga uku na lalace Mal kayima Allah kayi wani abu
wlh da gaske nakeson Abdu bazan taɓa yarda ya kufcemin ba wlh Mal har kisa zan iyayi akan
Abdu...." Ɗagowa Aneesah tayi da sauri idanunta cike da hawaye ta dubi malamin gabanta na
faɗuwa tace “Yanzu kai bakada yanda zakayi Mal don cikar burin ƴar'uwata?" Sunkuyar da
kansa yayi yace “Muna da damar yin addu'a ne da roƙon Allah kusanto da nesa tazo kusa
amma bamuda ikon rusa ƙaddara bare canzata Hanisa wannan abun saidai kuje kuyi addu'a ku
rungumeshi a yanda yazo kunyi sakaci yanzu haka an ɗaurawa Abdu Aure da....." Shiru Mal
Wada yayi ba Hasina ba hatta Hanisa faɗin an ɗaurawa Abdu Aure saida yasa jinin jikinta
daskarewa zuciyarta tayi wata muguwar bugawa data sanyata dafe ƙirjinta ta lumshe idonta
tare da cije leɓenta ta latse kiran da yakeyi mata tun zuwansu gurin tama kashe wayarta
gabaɗaya.
Maimakon ya kasance Hasina za'a riƙo jiri ne ya ɗebi Hanisa saida Hasina tayi saurin riƙe ta
tana kuka tace “kada ki faɗi ki nakasa kijamin ciwo biyu Aneey tabbas Abdu ya cuceni ya
yaudareni ashe dama haka akeji wlh tallahi sai yasan ya yaudareni saina fitineshi na hanashi
kwanciyar hankali da matarsa"..............
•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU✨
MASU HASKAWA* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari
Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA'AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu
cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba'a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000


•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi'u. GTbank_


Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ ```Sai munjiku Masoyan Amana....ShareShareAnd ShareHabibties
Allah ka barmu da masu sonmu```♡♡



*OUM HAIRAN*
[12/6, 4:45 PM] +234 706 301 1585: *WATA KARUWA*



*OUM HAIRAN*




*PAGE NINE*


*WARNING❌*
_Only matured ahead idan kika zageni ban yafe ba domin banyi littafina don ƴammata ba
idan kinga zaki iya go ahead._

Mal Wada ne yace “Komai fah yana tafiya ne bisa bigiran ƙaddara kiyi hƙr kada kiyi abinda zai
dameki zaki samu canjin daya fisa alkhairi"kallon Mal Wada tayi da sauri tace yanzu har akwai
wanda yafimin Abdu alkhairi a duniyar nan? Ina mal babu wlh bazaa sameshi ba saboda haka
ko a hannun wa zuciyarsa take saina ƙwatota" Jinjina mata kai kawai yayi suka fice dukkansu babu ɗaya dake cikin hayyaci napep suka hau
suka tafi gda babu me cewa wani har sukaje gdan suna shiga Hanisa ta ɗauki buta ta nufi bayi,
tana shiga ta buɗe wayarta kiransa ya shigo ta katse ko kaɗan bata sha'awar ɗaga wayar to
shima ganin taƙi ɗaga wayar tasa ya turo mata test yana cewa “Wyf kinƙi ɗaga wayata ko ki
nemi mijinki kiji lfyrsa.
Wani Gwauron numfashi ta sauke yace “Na sauka lfy ina cikin ƙoshinta kefa?" Shiru ta sake yi
masa yayi murmushi yace “bazakice komai ba?" Fasali ta ajiye tace “Alfarma zan roƙa a gurinka
don Allah ka fita a rayuwata kwata² bazan iya baka haɗin kai mu cutar da ƴar'uwata ba"
murmushi yayi yace “ko?" Da ƙarfin gwiwa tace masa “Eh" dariya sosai yayi yace “Ranar biyan
bukata rai ba bakin komai yake ba inji ƙuda Ni inada zaɓi kuma bazan taɓa bari saboda farin
cikin wani na rusa nawa ba"




Ƙit ya kashe wayar daya samu aka ɗaga masa daƙyar taja numfashi tace “sai kayi ai" gama
abinda zatayi tayi ta fito daga bayin ta nufi ɗakinsu baba ya shigo da sallamarsa ta amsa masa
tare da durƙusawa ta gaisheshi ya amsa yana cewa “Aneesatu na ina kikaje ne yau gdan shiru
ko ɗakin nawa ma ba'a gyatta min ba" dariya tayi tace “ina sauri na manta Baba bari nayi sallar
la'asar nazo na gyara maka am Baba nace kamar magungunan ka sun ƙare ko?" Jinjina kai yayi
yace “sun kare Aneesah an ɗauki adashin ne?" Murmushi tayi tace “Aa Baba kawai dai na
samu wasu manyan kuɗaɗe ne shine nakeso idan zai yiwu na kaika asibiti a gwadaka agani
idan jinin ya sauka itama sugar ta sauka sai a rubuta maka samfurin wasu magungunan"
Zubanta ido yayi yace “Aneesah ina kika samu manyan kuɗaɗe?" Gabanta ne ya faɗi tayi saurin
cewa “Lah Allah Baba ba abinda kake tunani bane wani saurayin Yaya Hasina Abdu shine zaiyi
tafiya so sai yabani wasu kuɗaɗe yace mu kula da kanmu bayason tallanmu harma yace idan
yaje ya dawo zaizo ku gaisa ƙilan ma yazo maka da mgnr auren Yaya Hasinan"



Jinjina kai yayi yace “shikenan Aneesatu tabara yayi miki albarka ya tsare gabanki da bayanki
yayi miki tsari da dukkan abin ƙi bari na shiga ciki" amsawa tayi da Amin ya shiga ciki ita kuma
ta shige ɗakinsu tayi salla ta zuba masa abinci takai masa dama ita kaɗai ce a gdan ta damu da
cikin mahaifin nasu lkcn da yaje yana kishingiɗe ta ajiye masa ta gyara ɗakin ta fito sukayi
kiciɓis da Hasina ta fito a ɗaki tace “ina zaki Yaya?" Kallonta tayi hawaye ya zubo mata tace
“Haba Hanisa meye yasa Abdu ya zaɓi wulakantani ne tun safe nake kiran wayarsa yaƙi
ɗagawa na tura masa test not reply nayi masa mgn ta whattsAp shima yaƙi buɗewa"
Daƙyar Hanisa ta haɗiye wani yawu me ɗaci tace “To yanzu da kika fito a fusace haka ina zaki?"

Gaba tayi tanacewa “Waya zanje na nemo na kirashi" murmushi tayi tace “Kina son kina
zubarwa da kanki ƙima Yaya mgn ta girman Allah Abdu baya sonki tunda kikaga yana miki haka
da nice ke da tuni ma na manta da babins.....



Dakatar da ita tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tace “bansan ke mahaukaciya bace sai yau to ta
yaya zan cireshi a raina ta yaya zan fara faɗa min ta ina ake farawa Hanisa" gaba tayi ta barta a
gurin ta biyo bayanta tace “kiramin shi ta wayarki" shiru tayi kamar bazata kirashi ba ta kuma
cewa mgn fah nakeyi miki Aneey ki kiramin Abdu ta wayarki" Badon ranta naso ba ta kirasa bugu ɗaya biyu ana uku ya ɗaga yace “Ya akayi Wyf ajiyar
zuciya ta sauke tace “Yaya Hasina keson mgn dakai"



Murmushi yayi yace “Ok haɗani da ita" miƙa mata tayi ta karɓa ta ƙara a kunnenta memakon
tayi mgn kawai sai ta fashe da kuka shima yayi shiru baice mata komi ba saida tayi me isarta
sannan tace “yanzu Abdu irin adalcin ka kenan ashe dama rayuwa zata iyayin juyin da zaka
watsar dani Abdu meye yasa ka kasa sona saboda Allah ne nasani ni na fara sonka nice na
nace maka amma ko babu komi ya kamata ace zuwa yanzun na samu gurbi a zuciyarka Abdu
wa ka aura ka watsar da narkon dakon soyayyata Abdu wace tafini matsayi da daraja a gurinka
har kakejin bazaka iya rayuwa da ni ba ita zaka iya da ita wacece ita Abdu ya sunanta a wanne
gari take?"
Numfashi yaja da har Aneesah dake gefe saida tajishi bata zaci zaiyi mgn ba taji yace “Kinga
Hasina tsakaninki da Allah yaushe na taɓa yi miki alƙawarin aure? Tunda nake bantaɓa yima
mace alƙawarin kaina ba domin banji a raina na haɗu da macen da zan iya saita rayuwata da
tata ba sai cikin watanni takwas ɗin nan banci mutumcinki ba kuma ko ba so bazanci
mutumcinki ba Hasina saboda har yanzun kinada sauran ƙima a idanuna dalilin kin kasance
sanadi na samun abinda na daɗe ina farauta Hasina ƙanwarki Aneesah itace cikon farin cikina
itace zaɓina da ita naji zan iya rayuwa in ƙare miki zance ma har na gabatar da ita ga Parents
ɗina dukkansu sunyi na'am da zaɓina harma sun aminc......"




Wata ƙara Hasina ta saki tare da sakin wayar ta dafe kanta tana faɗin Innanillahi wa Innah
Ilaihirraji'un Wayyoh Allah na ni Hasina na shiga uku na lalace lallai na yarda Aneesah ke micijin
ƙaiƙayi ce wato duk wannan abinda nakeyi kallo na kikeyi ashe kece babbar yar iska....." Da
sauri Hanisa ta katseta da cewa “Haba Yaya meyasa kike wannan kalamin me nayi miki?" Wata
damƙa takai mata ta shaƙeta ta haɗata da bango tana dukanta ta ko ina tana kuka tana cewa
“Wlh baki isaba Hanisa kinyi kaɗan kici amanata nabarki" kokowa sukeyi sosai Hayaniyar
Hasina ce ta fito da Mama da Baba Suka ishe su sunata faman kokowa Hasina na dukan
Hanisa ita kuma ta kasa ramawa sai kuka takeyi da ƙoƙarin ƙwatar kanta.

Daƙyar aka rabasu Hasina ta zube a gurin taci gaba da kukanta me ciwo Hanisa ma kukan take
ta kwanta a jikin Baba tana cewa “Bantaɓa jin a raina wannan ranar zatazo da idanun ƴar uwata
zai rufe ta kasa tsayawa ta saurareni ba tunda muka taso irin wannan ranar da za'a shiga
tsakaninmu bata taɓa riskarmu ba sai yau kuma akan namiji Yaya meye Abdu da zaki zaɓi cutar
dani akansa meye ya faɗa miki da zaki kasa tsayawa ki saurareni har kika iya yanke hukunci da
kalaminsa......"



Sake zaburowa Hasina tayi tace “Na rantse da Allah akan Abdu ko rana ɗaya mukazo duniya
saina kasheki maci amana azzaluma mayaudariya maci amanar ƴan'uwantaka kullum na
tambayeki tsakaninki da Abdu sai kicemin Abota ashe rusheni kikeyi kina kafa kanki tabbas kin
shammaceni Aneesah kuma nima zan shammaceki kamar yanda kika rusamin farin ciki nima
saina tarwatsa naki".




Murmushi Hanisa tayi tace “ni kuma inada burin har gobe ki samu farin ciki koda zan rasa nawa
kije ki rayu da Abdu Hasina bantabajin a raina zan rayu dashi ba domin bantaɓa yi masa kallon
masoyi ba bakuma zanyi masa ba badon bai isaba a'a saidon farin cikinki ya samu"
Baba ne yace “Wai meye yake faruwa?" Sai yanzu hawaye ya zubowa Hanisa tace “babu
ruwanku Baba kawai dai idan hukuncin da zan yanke yayi maku ƙunci ku yafemin zanyi ne don
cikar farin cikin ƴar uwata inason ta rayu cikin farin ciki ne yasa na ɗauki wannan matakin"
sulalewa tayi tayi ɗaki ta zauna gefen katifarsu ta haɗe kai da gwiwa ta rushe da kuka me gunji
a tsakar gdan tana jiyo Muryar Hasina tanata bala'i tana faɗawa Mama abinda yake faruwa
memakon ta tattarasu tayi musu nasiha kawai saita biyewa Hasina suka rinƙa ɗebewa Hanisa
albarka kukanta ya ƙara ƙarfi ta dauko mayafinta da wayarta da ATM ɗin ta ta fito idanunta na
tsiyayar da hawaye ta tsaya tace “Koda kike cewa na munafurceki na ɓoye miki wani abu Ni
kaina bansan meke zuciyar Abdul-Ahad ba sai jiya kuma ban ɗauki abin da muhimmancin da
zanji zan iya faɗa miki ba kiyi hƙr Yaya insha Allahu daga yau bazaki ƙara ganina ba harsai
burinki ya cika" tana faɗin haka ta juya zata fice Mama tace “Eh aje wannan abin kunyar
baza'ayishi a gdana ba banda tsabar iskanci ma tayaya hakan zata faru sun gama lole junansu
da Yayarki sannan saboda ke watsattsiya ce ya dawo gurinki ki karɓesa sai aje wannan dai yafi
ƙarfin ki aje abawa wasu suci shidai wannan na Hasina ne zanyi maganin ɗan iska"........


•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU✨
MASU HASKAWA* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari
Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_

_*AUREN SHA'AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu
cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba'a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000


•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi'u. GTbank_


Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ ```Sai munjiku Masoyan Amana....ShareShareAnd ShareHabibties
Allah ka barmu da masu sonmu```♡♡



*OUM HAIRAN*
[12/6, 4:45 PM] +234 706 301 1585: *WATA KARUWA*

*OUM HAIRAN*




*LAST FREE PAGE TEN*




*WARNING❌*
_Only matured ahead idan kika zageni ban yafe ba domin banyi littafina don ƴammata ba
idan kinga zaki iya go ahead._



_Nayi warning akan littafina wasu ƴaƴan Ramatun Awaki sun samu damar Write-up akansa
saboda nace under so baku isa nayi muku bayani dan ku gane ba domin tun a baya ma
banyi muku ba bare yanzun._
_Abu na ƙarshe shine na gama free page na book ɗin nan daga PAGE TEN idan kika karanta
na gaba dashi ban yafe ba idan kinaso kici gaba da samunsa ki karanta ki fahimta cikin aminci,
zaki iya tuntuɓata ta whattsAp number na 09013718241 ko kuma kibi hanyoyin dake ƙarshen
page ɗin_


Juyowa tayi ta kalli Mama tace “Ba karuwanci na tafi ba zan matsa ne na baku guri har zuwa
lkcn da burinku zai cika ni nasan bantaɓa cutar dake ba Yaya a cikin hayyacina amma idan kin
kasance kina kallo na da wani abu saɓanin abinda ke zuciyata kiyi hƙr Allah ya sadamu da
alkhairi" Ficewa tayi daga gdan da sauri ta nufi titin unguwar tasu cikin Sa'a har tabar unguwar bata
haɗu da wani idon sani ba tana tafe ne cikin fitar hayyaci gabaɗaya duniyar tayi mata ƙunci lkc
zuwa lkc hawaye nabin kuncinta ƙuncinta yana ƙaruwa tayi tafiya me tsayin gaske a ƙafa tama
manta da ana hawa wani abu abin hawa kamar daga sama taji ana mata horn ta matsa da sauri
daga titin motar tayi parking me motar ya fito ya tsaya a gabanta yana ƙare mata kallo kaucewa
tayi ta kuma bin hanya zata tafi yayi saurin riƙo mayafinta yace “Ƙarfe 11:15pm ƴammata ya
kamata ace kina kwance cikin ɗakinki ko ɗakin mamanki bama wannan ba na wutto wata
unguwa naga wani tsoho yanata kuka yana tare mutane yana nuna musu hotonki yana
tambayar ina kike"
Hawaye ne ya zubo mata ta juya zata tafi yace “kiyiwa Allah ki tsaya naji inason taimakonki ne"
kawar dakai tayi tace “bana buƙata" ta juya tayi gaba bai ƙyaleta ba saida yaga ta tsaya ta
saurareshi yace “Kizo na kaiki gdana ki kwana da safe sai ki fito yanzu dare yayi akwai risk zaki
iya faɗawa hannun ɓata gari"

Nacin da yasa shine kawai yasa ta yanke shawarar binsa tana shirin shiga motar wata arniyar
mota tazo ta giftasu a guje har ta shiga taga yayo ribbors yayi horn wannan tasa me motar yaƙi
shiga ya tsaya don ganin waye ke a cikin motar meye ya tsayar dashi, saida gaban Hanisa ya
faɗi ganin Abdul-Ahad ya fito a cikin motar ya tsaya wasu mutane sun fito a motar dake bin
bayansa sun russuna da girmamawa sunyi masa mgn ya ɗaga musu hannu ya taka a hankali
ya isa ga motar da Hanisa ke ciki ya sunkuya ya riƙo hannunta ya kamota ya fito da ita ya dube
mutumin ya basa hannu suka gaisa yace “Tnks good Jamal naji daɗi daka taimakeni batayi nisa
ba mu ƙara sa" tsayawa tayi tana kallonsu da mamaki hawaye nabin idanunta yaja hannunta ta
janye yace “Ina zaku kaini" kallonta sosai Abdu yayi yace “Aneey dare yayi kizo na mayar dake
gda da safe mayi mgn"




Fir taƙi shiga motar ganin zata ɓata masa lkc ne yasashi ɗaukarta cak ya nufi motar da ita ya
sanyata ya shiga ciki yana shirin tada motar ta riƙe hannunsa da ta zame ƙasan motar tace
“Don Allah ka barni na tafi nayi alƙawarin bazan ƙara komawa gdanmu ba harsai burin Yaya
Hasina ya cika" murmushi yayi ya tada motarsa yaja da gudu yabar gurin ta kuma rushewa da
kuka.
Kai tsaye gdan daya kaita kwanaki can ya kuma nufa yayi parking ya fita ya buɗe mata alama
ya gani na bazata fito ba ya sake ɗagota cak tanata kiciniyar ƙwacewa yaƙi bata dama saida ya
shiga wani babban parlour ya direta ta miƙe da sauri ya riƙota ta fusge tana kuka yace “Kina
ban mamaki Wyf nifa banga abinda akayi ba da zaki zaɓi barin gda akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login