Showing 6001 words to 9000 words out of 28936 words
Chapter 3 - Amani 3Hausa Novels by Takori Kabara .pdf
Musamman da aka tabbatar min ka bar Farisa baa san
inda ka shiga ba kuma. Har gobe a kan treatment nake, mahaifiyar ka kuwa
ka gan ta yanzu bata gani sai da Gilashi, sabida yawan kukan tafiyar ka
Maina.
In mun yi kuskure cikin abinda muka aikata muna rokon Allah ya yafe
mana, kai ma ka yafe mana. Sannan madallah da jin cewa kayi aure, lokaci ya
yi da zan bayyana ka ga duniya.
Zan maka bikin aure irin wanda baa taba yin irin sa a masarautar
Diffa ba, zan gayyato duk sarakunan jamhuriyyyar Nijar, in gabatar da kai
gare su, sannan zan baka sarautar Diffa tun ina raye. Kafin nan zan maka
nadin sarautar Mainan Diffa ka fara zama a fada tare da ni don ka koyi
shaanin mulki na lokaci mai tsaho.
Duk wadannan abubuwa da ke faruwa yau, Mukhtar couldnt believe
them, don ya dauka mafarki yake yi, ire-iren mafarkan da dan adam in yana
yin ba ya so ya farka, yana rokon Allah da dai ya farka daga wannan
mafarkin, gara ya zarce a cikin niimar sa, wato ya karasa mutuwa a cikin
dadin sa
..
***** ***** *****
WASHEGARIN RANAR
Da wayewar gari, Sarki Issouffou Massaoudou ya aiko a tafi da su
Alhaji cikin masarauta, yasa aka kai su dakin da yake ganawa da manyan
bakin sa, sannan aka shirya musu karin kumallo tare da Sarki da Ummami.
Wanda ya kai su shigifar ya ce su jira kadan, Mai Diffa na zuwa tare da
Mowa.
A lokacin Mukhtar na can yana ramuwar barcin gajiya bai ko tashi ba,
don kwanan zaune suka yi da iyayen sa, tun bayan da suka dawo masallaci
sallar asubahi aka bude masa wata shigifa da ke kusa da na mahaifin sa, yake
barci har zuwa lokacin, barci na kwanciyar hankali irin wanda bai taba samu
ba.
Su Jalan sun nutsu suna kallon sarautar Allah, domin ko a cikin
masarautun Nijar Diffa na sahun farko, komai na masarautar mai ban
shaawa ne da ban mamaki kuma irin ancient dinnan amma aka zamanantar
da shi, suna kalle kalle suna jiran isowar Mai Diffa da Maidakin sa, wadda
suka ji an kira Ummami (Mowa).
Can suka jiyo takun sa ya durkako inda suke. Cikin taku na haiba da
kamala. Yana shigowa duk suka mike domin girmamawa. Haske da kwarjinin
addinin Musulunci ya bayyana sosai a tare da farin balaraben dattijon. A
nitse ya zauna a kujerar da ita kadai ce kujerar mulki a dakin, wanda yafi
dacewa a kira shi palace, ba jimawa da zaman sa sai wata kofar ta kara
budewa. Doguwar matar cikin kyakkyawar laffaya da farin gilashi a idanun
ta, ta shigo, ita kadai ba tare da kowa ya rako ta ba.
Ta nemi guri gefen maigidan ta ta zauna kasan kafafun sa, fuskar su fal
annuri da maraba dasu. Kafin kowannen su ya ce komai aka ji Mamma Jalan
ta tsinke da salati ta ce Yaya AISATA!
A firgice Ummami ta juyo, jin muryar kanwar ta, Jalan. Da gudu
Jalan ta sheka ta isa gareta ta rungume ta. Sai kuma ta saka kukan farin ciki.
Da kyar Aisata ta banbarota daga jikin ta. Ta ce Jalan, ke ce koko ido na
ne? Aah ke zan tambaya da gaske ke ce? Kuma Mukhtar dan ki ne kenan?
Aisata (burst into tears) tace ban taba gaya miki cewa na haihu ba, sabida
bamu kara haduwa ba tun rabuwar mu sai aike ne a tsakanin mu, sabida a
kaida matan gidannan basa fita, ko asibiti bama zuwa saidai likita mace ta zo
har daki ta duba mu, sannan da matsalolin da suka biyo bayan haihuwar tasa,
da muka fara waya dake bayan kin yi aure na biyu kenan, ni ban san meyasa
na kasa gaya miki ina da Da ba, kodayake bana maganar sa sam, balle irin
wannan a muhimmiyar magana ta hada mu da wani nawa ta waya, daga baya
kuma bama tare dashi ma, daidai lokacin rasuwar Abbu sanda na aiko dan
aike na wajen ku, aike na na farko gida Kenema, lokacin Maina ya riga ya
gudu.
Me ya kai ki Najeriya yanzu? Na dauka kun rabu da mijin ki na can
tun su Abbu na raye, har kin yi wani auren da Lukman kin samu yara? Daga
baya kika gaya min a waya ya rasu, ta ina kika hadu da yan Najeriya bayan
na san kina Kenema? Suka rungume juna ana ta mamakin wannan ikon Allah, Jalan ta gaya
mata Alh. Usman shine mijin ta na fari wanda aka aura mata a kasar
Katsina, suka rabu bayan ta haihu, itama rabon ta da yar tun lokacin, sai
yanzu da kaddara ta sake hada su. Ta nuna mata Amani dake ta sakin fitsari
a kai-a kai daga zaune ta cikin wandon ta a lokacin, sabida yadda ta kara
firgicewa da alamarin Ubangiji, wato Mukhy Yayan ta ne na jini kuma?!
Bayan nadamar data sha jiya bata ko gama fita daga cikin ta ba, yau ga
gagarumar nadamar data fi ta jiya ta kara samun ta. Jalan ta nunowa Aisata
ita da hannun ta manuni.
Kin gan ta itace yar da na haifa na baro a Najeriya sunan ta Amina,
sai da girman ta na gan ta, kuma ita ce matar Mukhtar a halin yanzu, domin
a hannun mahaifin ta ya zauna a gidan su duk tsayin wannan lokacin.
Ummami sai ta mikawa Amani dukkan hannuwan ta tana hawaye tana
fadin Ya ki nan diya ta, ta kaina! Amma Amani ta kasa tashi sabida yadda
ta jika jikin ta da fitsari a zaune, sai da Sahura ta ciccibata, ta isa ga Aysata,
ita kuma ta saka dukkan hannuwa ta rungume ta a ciki, tana fadin dukkan
godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, mai rahma mai jin kai, mai yawan
hikima ga rayuwar bayin sa.
Sai lokacin Sarki yayi gyaran murya ya ce hakika Ubangiji mai hikima
ne, madallah da ku, madallah da kariman mutane irin ku, masu mayar da
dan kowa nasu.
Ya dubi Daddyn Amani yana murmushi ya ce yadda ka rike min
Mukhtar da amana ba tareda ka san komai a kan sa ba, haka nake fatan in
rike Amina daga nan har karshen rayuwar mu, ko da bata kasance yar uwar
sa ba. Allah ya saka maka da alkhairi ya kuma baka lafiya. Sai ga Mukhtar ya shigo dakin daga shi sai farar jallabiyya kal da
bakar hular larabawa a kan sa, kallo ya koma gare shi suna mamakin yadda
cikin kwana daya tal ya canza ya koma tamkar ba shi ba, yayi kyau, yayi wani
irin fresh tamkar balaraben Madina. Kamar da ka latsa shi jini zai yi
tsartuwa. Nan aka gaya masa ko me ke akwai, wato Jalan kanwar Ummami
ne ta jini, uwa daya uba daya.
Mukhtar sai kamar bai yi wani mamaki ba, cewa yayi ai ni naso in
gane hakan tuntuni, kawai ban san komai akan Ummami bane ko dangin ta,
wanda zai karfafa zargin nawa, amma tabbas na ga alamu, tun sanda na ga
cindo Ummami a hannun ta da wasu attributes da dama, sannan jiki na ya
bani, son da na samu kaina ina ma Mamma, kamar na Ummami ne,
musamman da ita ta sake da ni sosai ba kamar Ummami ba cikin yan
kwanakin da nayi tare da ita.
Nan aka shiga mayar da zance, aka dauko tarihi tun daga farkon sa,
tarihin masarautar Diffa da yadda kakan sa Sultan Oumarou ya bada
sarautar ga dan sa Sultan Massaoudou tun yana raye, bayan rasuwar sa Sarki
Issouffou ya gaji sarautar daga hannun mahahifin sa Sarki Massaoudou. Ya
ce sun kasance su masu karancin haihuwa ne a jinin su, shiyasa suke
aure-aure daga kasashen Africa daban daban daga kyawawan matan Africa,
wadanda suke saye suna sa-daka dasu (concubines) basu cika maida su matan
aure ba.
Ya ce amma ita tunda aka kawo ta gaban mahaifiya ta ta ganta da
tabon sujjadah a goshin ta, sannan aka gaya mata daga Saliyo take sai tace
aure zaa daura mana bata yarda in yi sa-daka da ita ba.
Marigayiya mahaifiya ta tace matan Saliyo mata ne na musamman,
daban suke a halitta da sauran matan Africa, Allah yayi musu baiwa ta auren
manyan mutane, tace sanda zata kwace Mowar Diffa daga hannun Ummu
Aymana, bazan sani ba. Sarki yayi murmushi yace and thats exactly what happened today,
Aisata Mowar Diffa! Kafin ita ina da matan aure guda biyu, uwargida Ummu
Aymana yar sarkin Zinder tana da ya daya; Sayluba. Sai Tarha diyar sarkin
Agadaz wadda itama na samu haihuwar diya mace da ita. Sai aka daura
mana aure na Sunnah da Aisata, na bata dakin mace ta uku a gidan sarautar
Diffa.
Kasancewar duk matan da ake kawomin matsayin sa-daka nake basu,
wannan ya tada hankalin mata na; Ummu Aymana da Tarha. Musamman da
ya kasance har zuwa lokacin babu wadda ta samu haihuwar Maina cikin su.
Suka daga hankalin su a kan Ummami nima suka daga min, sanda ta samu
cikin Mukhtar kuwa ina wuta su saka ta, aka hanamu aure ta hanyar saka
min tsanar ta a shimfida, aka saka mata warin gaba, aka saka mata kurarraji
kai matsaloli marassa dadin ji iri-iri a dalilin wannan ciki kamar ba zai kai
labari ba.
Don daga baya ko dokin haihuwar tata na daina. Na koma ganin abinda
zata haifa min din a matsayin matsala.
Sai malaman fada ne suka saka ta gaba da addua don kowa yana so
Diffa ta samu Maina, basa so sarautar ta bar gida na, don ina da yan uwa a
raye, amma ni ko a jiki na. Uwargida na da bakin ta ta gayamin cewa muddin
Aisata ta haifi Da namiji sai ta salwantar da rayuwar sa, na kuma san zata
iya, a yadda ta cika zuciyar ta da burin ita zata haifa mun Maina.
Sai bayan an haife shi an kawo min shi hannu na zuciyata ta cika da
kaunar sa, gashi cikin yan uwa na ma da suke da yara maza basu so na samu
Maina ba, sun so ya kasance na mutu babu magaji don sarautar Diffa ta
koma hannun yayan su. Don haka na san ta koina Mukhtar yana cikin
hadarin makiya musamman da ya kasance kamar an tsaga kara ni da shi a
kamanni. Sai na shiga tunanin ta hanyar da zan bi in kare rayuwar sa.
Nan na zaunar da Aysata, na ce wannan yaro kin haife shi dai ko? To
ki godewa Allah komin runtsi sunan sa dan ki, amma ki nema masa kariya ta
hanyar rashin nuna kauna da kulawa a gare shi.
Ta yi min kallon rashin fahimta nan na wayar mata da kai, na ce mata
na barshi karkashin kulawar bayin mahaifi na na tun tali-tali, wadanda nima
gadar su nayi a gun mahaifa na saboda amanar su, wato Katchalla sarkin
fada da Jakadiyar dana bata. Na ce ta runtse idon ta daga kan yaron nan, ta
bar shi ya rayu a hannnun su. Zasu kula da shi kamar yadda zasu kula da
yayan su amma rayuwa irin ta yayan su.
Da yake Aysata mai fahimta ce, mai kuma bani hadin kai akan duk
abinda na zo mata da shi sai ta yarda. Amma ta roke ni in bar ta ta shayar da
shi ko a boye ne, ko na tsayin shekara daya ne, na amince mata. Don na san
muhimmancin nonon uwa, kuma inaso ya tsotso irin kwakwalwarta da
kyawawan dabiun ta.
A takaice wannan ne dalilin da yasa muka yi wa Mukhtar rainon da
muka yi masa, yau gashi Allah ya raya shi yadda nake fata, duk wani da ya
nufe shi da sharri na tabbata ya ga abun sa a kwaryar shan sa, domin koda
aka gaya min kurciya aka yi masa daga baya ni ban damu ba, na bar shi ya je
ya koyi rayuwa har zuwa lokacin da ni da kai na nasa malaman fada suka
karya sihirin, tun a daren ne kuma aka gaya min Ummu Aymana ta fita daga
gidan nan, ta tafi har Zinder a kafa, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai
hankali ba, ta dai koma kamar tababbiya, kuma kalamanta kullum.
Mainan Diffa dana yi wa kurciya zai dawo yanzu ya karbi Diffa.
A halin yanzu tana can hannun iyayen ta ana mata magani amma tace
bazata dawo gida na ba in dai Mukhtar na cikin sa.
Don haka a jiya na datse igiyar aure na da ita na aikawa mahaifin ta
sarkin Zinder. Diyar da muka haifa nida ita (Sayluba) na dade da aurar da ita
a Tahoa, tana da yaya basu fi uku ba itama ta gado rashin yawan haihuwa ta,
sai kanwar ta yar wajen Tarha (Saadiyya) itama tana aure a kasar Guinea
kusa da Liberia ga Amabasadan Nijar a Guinea.
Bayan Aisata ta haifi Mukhtar shiru shiru babu karin haihuwa a gida
na, sai na kara aure da Balqissa, wadda aka kawo min ita daga kasar
Abidjan. Har yau itama bata haihu ba, Mukhtar mai bakin baya ka hana ni
samun ko yaya matan ne sabida alhakin ka Ubangiji ya hana ni
.. Ya karasa fadi cikin zolayar Mukhtar. Sai da kowa a wajen yayi dariya
Ummami ta ce kada ka damu MAI DIFFA! Ba da jimawa ba in sha Allah
diyata Aminatu zata cika maka gida da yaya. Jalan ta ce ni nafi so a kara
mishi da sadakoki yadda yaran zasu fi saurin taruwa dariya kowa yayi,
amma banda Amani da Mukhtar, wadanda duk suka bi suka daddaure fuska,
kuma kowanne yaki yarda ya kalli inda dan uwan sa yake. A zuciyar ta cewa
take ta Allah ba taki ba Mamma.
Ga dukkan jin dadin ta sai Ummami tace in har ba ya zama (Mai) din
Diffa ba (Sarkin Diffa) babu mai bashi sa-daka a halin yanzu. Yanzun Maina
ne kawai, ku bar su su mori kurucciyar su don Allah.
Sai Amani ta hau addua a cikin ran ta;
Ya Allah kasa kada a taba baiwa Mukhtar sarautar gidan su, Allah ka
kara nisan kwanan mahaifin sa, yayi ta zama a muhallin sa na Mainan Diffa.
(Ta manta Sarki ya ce tun da ran sa zai baiwa Mukhtar kujerar sa).
Sarki yayi umarni da su Jalan su koma bangaren Ummami da zama
har Amani. Gobe-goben nan zaa saka tubulin ginin bangaren matar Maina.
Ya kuma ce a yau dinnan zai soma aika takardar gayyata zuwa ga
sarakunan jamhuriyyar Nijar, wato gayyatar bikin auren Maina da nadin
sarautar sa ta (MAINAN DIFFA).
**** ****** ******
MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU
(MAINAN DIFFA)
B
aka jin komai sai tashin bushe-bushen algaita da kade kaden ganguna irin na
masautar Diffa, a yau Asabar, wadda ta kasance ranar bikin auren Maina da
nadin sarautar sa.
Cikin wadanda suka halarci wannan kasaitaccen biki har da Yayar shi
gimbiya Sayluba daga Tahoa, mai bi mata da yake tana Guinea, bata samu
zuwa ba don tayi nisa sosai, mahaifin ta ya aika mata kan ta zo ga dan uwan
ta Maina ya dawo gida, ta ce sai ta haihu zata zo daga baya, tana cikin watan
aifuwa.
Tunda aka soma shagulgulan bikin nan wanda zaa kwashe kwana
bakwai ana yi Amani bata saka Mukhy a idon ta ba ko daga nesa, rabon ta da
shi tun washegarin zuwan su Diffa, wato ranar da suka gana da iyayen sa,
yana can cikin sarakuna abokan Baban sa da yayayen su saannin sa,
wadanda iyayen ke kokarin kulla abota da zumunci mai karfi tsakanin yayan
nasu, kamar yadda nasu iyayen suka yi masu.
Ba iya masarautun Nijar kadai Sarki ya gayyato ba har daga
bangarorin masarautun Songhai, Mali, Gao, da Kanem-Bornu. Haka ya
gayyato aminin sa Sarkin Burkina-Faso, wuri yayi wuri, taro yayi taro sai
Rakuma ake kayarwa ana gashewa ana kyafewa. Abinci kuwa duk iya diban
ka haka zaka gaji da diba ka bari.
Umami tasa an yi wa Amani kwalliya irin tasu, da kaya na shudin karen
miski da sarkokin zinare har a hancin ta, an dorata akan kujerar Mowar
Diffa, wato kujerar da Ummami take zama a kai koyaushe, abin gwanin ban
shaawa, shagalin sai wanda ya gani. Kwana bakwai aka kwashe ana wadannan shagulgulan na ban
mamakia Al-Imaraat Al-Diffa, an nadawa Mukhtar rawanin sarautar jiran
gadon mahaifin sa Mainan Diffa, wato dan sarki mai jiran gado.
**** **** ****
MATAR MAINA
“
Kuma shikenan don ya zama Maina ganin sa ma ya zama jan aiki? Amani ta
tambayi Baba Sahura babu ko kunya, koda yake dama kunyar ta mata
karanci ai, ranar da suka cika sati biyu a Diffa bata sanya Mukhtar a idanun
ta ba. Kai ko daga nesa bata hango shi ba. Don ko yana son magana da
Ummami baya shigowa sassan ta, don ma kada ya hadu da Amani, can a
turakar Mai Diffa suke haduwa da mahaifiyar tasa su yi duk maganar da
zasu yi.
Baba Sahura ta bantari farin goro sal, sannan ta fashe da wata
shashashar dariya, ta dubi Amani tana mamakin rashin kunyar ta, wai yau ta
murje ido tana cigiyar Mukhy a gicciye da idanu, ta ce,
ki na so ki gan shi fa kika ce? To kewar sa kike ko yaya abin yake? A
dan yimin bayani?
Baba Sahura bana son irin wannan rainin hankalin naki, daga
magana sai kimin wata fassara daban, na