Showing 21001 words to 24000 words out of 28936 words
Chapter 8 - Amani 3Hausa Novels by Takori Kabara .pdf
gado daya. Tsakanin farin
ciki ko akasin sa, bai san wane ne yake nukurkusar sa a kasan ran sa ba, a
can wani sako na zuciyar sa yayi kewar ta, a wadannan sati biyun da bai
sanya ta a ido ba kuma bai ji muryar ta ba, duk da yake busy da kula da
Alhaji, amma kullum sai Alhaji ya masa zancen ta, mai nuna yay aye mat aba
don halin ta ba, mai nuna tsanannin kaunar da shimahaifin nata yake yi
mata, wanda ke sawa ya kara mannata a zuciyar sa shima ko ya ki Allah balle
yana son ta, albarkar Alhaji sai son yake ninkuwa kullum. Amma ba don ita
ba, ba kuma don halin ta ba, sai don an jarrabce shi da son ta da kaunar ta
tun kafin haka, (no matter how worse her behaviours are).
A haka suka yi sallama shi da Ummami, yana jin kan sa kamar wani
sabon mutum yau da ya mallaki matar aure a cikin gidan sa, kuma yar
Alhajin sa, Amani Tafisu da zuciyar sa ke matukar so fisabilillah, ya shiga
ratsa falillukan Ummami ya wuce zuwa sassan nasu, dogarai na faduwa suna
gaida shi a duk kofar da ya wuce.
Tunda Ummami ta ajiye ta a bakin gado bata sauya wajen zama ba,
dan irin kukan nan na amare babu shi a idon Amani Faskari, idanun
kemadagas, kamar soyayyar gyada marau-marau, amma damuwa da
taraddadin haduwa da Mukhy yau, ta mayar dasu yan kanana, data gaji da
lullubin ta sauke shi saman kafadun ta, ta daga kai tana kallon irin wannan
dukiya da aka zuba musu a wannan daki don su biyu rak, ta dade a zaune
tana godiya wa sarki Allah akan komai ma, musamman a kan iyayen ta da
suka koma auren su, sai kuma ta tuna bata yi sallahr isha ba, don haka ta
tashi da sauri ta shiga inda take tunanin toilet ne, don yanzu bata wasa da
lokacin sallah ko kadan sabida nasihun Ummami.
Ta idar da sallahr tana addua ta ji motsin shigar sa dakin da ke kallon
nata.
Kamar ta je, kamar kada ta je, ta tunawa kan ta cewa ita fa amarya ce
no matter how, Mukhtar shi ya kamata ya zo inda take duk mulkin sa.
Don haka ta daure ta cigaba da zama akan dardumar da tayi sallah,
daga baya tun tana addua a kan Allah ya gyara mata halayen ta da kowa ke
kuka da su, har barci ya dauke ta a kan sallayar.
Mukhtar na nasa dakin har washegari yana barcin gajiya, haka kawai
zuciyar sa bata amince ya je ga Amani ba, ko ya so hakan zuciyar ta ki
amincewa, haka kawai ya koyi juriya daga shiga alamarin ta.
Basu suka hadu cikin gida ba sai da safe a falon sa na farko, ta fito cikin
sassaukar shiga ta atamfa Holland, ta yi daurin kai dai-dai misali ba irin
daurin ta na baya da ta saba yi ba wato Ture ka ga Tsiya yau daurin Amani
kan sa ya russuna, kamar yadda zuciyar ta ta russuna, musamman da ta ga
sun kwana gida daya da Mukhy amma ko da wasa bai neme ta ba. Jikin ta
duk ya yi laasar ya jikakken tsumma.
Mukhtar na kwance cikin kujerar zaman mutum daya a falon nasa ta
shigo ba tare da ta san yana ciki ba, don ta duba abinda suka shirya musu na
Karin kumallo, ya yi wata irin kwanciya kamar mai barci amma a zahiri ba
barcin yake ba, yana tuna maganar da suka yi da Mai ne, na cewa Mai Diffa
yana so ya karbi sarautar Diffa tun yanzu, sabida shi tsufa ya cimmasa
abubuwa da yawa baya iyawa yanzu, sabida rashin karfin jiki.
Ya tuna amsar da ya baiwa Mai a lokacin.
Allah ya taimaki Mai Diffa, ina rokon a bari zuwa gaba kadan, tunda
Allah ya hore maka lafiya da koshin lafiya da abinda lafiya zata amfana, ina
so in kara samun nutsuwar da zan kara fuskantar yadda shaanin mulkin
yake daga gare ka.
Takun sawun Tafisu da kamshin turaren ta ne ya ankarar da shi isowar
ta, a daidai kafafun Mukhy Amani ta zauna, har yanzu gajiyar tafiya bata
sake shi ba, shiyasa yake ta kwanciya tun jiya ya kasa fita yau, ya bita da
kallo tana zama a daidai kafafun nasa, har ta zauna fuskar ta ba yabo ba
fallasa sai damuwa da kulawa, ga dukkan mamakin Mukhtar sai cewa ta yi.
An dawo lafiya Ya Mukhy?
Sai kuma ta tuna zaman da Ummami ta ce irin shi zata dinga yi in tana
gaban Maina, ai kuwa ta gyara zaman nata da irin zaman Ummami din,
kamar zata shige cikin jikin sa russunawa da kulawa kamar baiwa a gaban
Sarki, shi dai Mukhy kallon ta yake daga kwance yana cewa cikin ran sa
wannan canjin nata ba na kalau bane, don ganin abun yake banbarakwai, wai
namiji da suna Hajara.
Haka nan dai ya daure ya amsa mata (with straight face), sai kuma ta
ce masa ka ci abinci? I mean breakfast? Ya dan kalle ta da wutsiyar ido
yana mamaki, sai ya biye mata da yadda ta zo, ya ce aah ban ci ba tukunna,
wani abu ne ya faru? Tashi na kenan daga barcin da na koma bayan sallahr
asubahi, shine na zo nan nake hutawa, kafin lokacin fita ta ya yi.
Mukhtar yayi bayani, don ya kasa gane inda ta dosa da sabon canjin,
yafi sawa a ran sa wani abun take so shiyasa, don bai saba da concern din da
yake gani yau daga gareta ba. Amani ta karya kai, Allah ya taimaki Maina to
ai ga abincin can sun shirya shi tun dazu a kan dining-table, Maina ko zaka
taso mu je mu karya tare?
Mukhtar ya kasa hadiye mamakin sa har ma da dariyar sa, ya ce
Amani ce kuwa?
Don hatta lafuzzan ta da wani irin taushi da rangwada suke fito masa.
Tayi murmushin jan hankalin miji, sannan ta ce ko a kawo maka
abincin nan ne Ya Mukhy? Idan ba ka son tashi daga nan din?. Sai ya ce
umh kawai, ya koma yadda ta zo ta same shi a kwance, ya sake maida
hankalin sa kan wayar sa, don ya kasa gasgata abunda yake gani daga gare ta
dinnan. Maiyuwuwa gizo idaun sa ke masa.
Amani sai ta tashi ta tafi ta kawo abincin daya bayan daya, ta shimfida
ledar cin abinci a gaban sa, ta hau hadawa Mukhy black tea mai kamshin
kanimfari da citta, don Ummami ta ce mata lallai su duka su dinga yawan
shan kaninfari, tana cewa ni bana shan tea da madara fa, ban sani ba ko kai
ma haka?
Mukhy ya tashi zaune sosai, sannan ya harde hannuwa a kirji, ya kuma
harde kafafun sa, ya zuba mata kyawawan idanun sa, ya sake cewa umh,
kawai, yana ta mamaki dai, don still ya kasa yarda ita ce, sai ta mika masa
kofin shayin da ta kammala juyawa da Zuma maimakon sugar, ta bashi cikin
girmamawa.
Mukhtar sai ya karba, ba tare da ya ce komai ba, ya kuma kai bakin sa
ya kurba, kamshin kanimfarin ya masa dadi a makoshi, bai ce aah ba, amma
bai yi wata kwakkwarar magana ba har yanzu.
Amani ta cigaba da zama a yanda take, abin ki da rashin sabo da
kyakkyawar muamalar data ke son assasawa, duk ta kasa sakewa da zaman
da tayi din, shi kuma ya cigaba da sipping shayin sa ko a jikin sa. Ganin ya
karba ba tare da ya gwale ta ba har yana sha, sai ta samu karfin guiwar zuba
masa farfesun naman kaza, ta sa spoon a ciki ta mika masa.
Ya karba again, ya soma shan romon da cokali, yana yi yana daga ido
yana kallon ta, ta kara da zuba masa chips and fried egg wanda ya ji albasa
da koren tattasai, ta sake mika masa, ya karba babu musu, don yana jin
yunwar sosai, rabon shi da abinci tun jiya, amma kuma babu magana a
tsakanin su sannan babu nagode.
Ta zauna ta cigaba da latsa wayar hannun ta wanda chatting ne suke yi
da Balewa, ta ce Bestie, Im done with step one, but he seemed careless da
kokari na. Balewa ta turo mata Emoji na jinjina da kwanji, ta ce, dont
worry, keep up the good work, saura kwashe kwanukan da ya gama cin
abinci, ki tabbatar rigar ta zazzago gaba kuma a saitin idanun sa kin masa
flashing.
Dariya ce ta kama Amani ta yi yar sheshshekar dariya ba shiri, ta ce
Balewa ba dama! Sai da Mukhtar ya dago daga cin abincin sa ya dube ta,
ke da wa Hajjaju? Ya tambaya cike da tsegumi, don kuwa Amani ba mutum
ce mai yawan fara ba balle a je ga dariya a iya sanin da ya yi mata. Yau kuwa sai fara take kamar gonar auduga. Yanzu kuma har da
kyakyatawa.
Ya Mukhy ni da Balewa ne.
Oh I see! Ki ce Your role model!. Ta yi murmushi, domin bata yarda
da abinda yace din ba, hakika da aboki yana maida abokin sa role model din
sa, da tuni Balewa ta dade da zame mata role model tuntuni ba sai yanzu ba
da duniya da kan ta ke koya mata hankali. Domin iyakar hankali da sanin ya
kamata, mutunci da sanin ciwon kai da rikon addini suna tattare da
HAMIDAH HASHIM BALEWA, ita din ce a baya bata yarda ta yi copying
halaye da dabiun Hamida Balewa ba, don a nata tunanin, a sanda take kan
ganiyar ta it ace wayayya Balewa bata waye ba, shi yasa take yin simple life
duk da kasancewar ta yar gata, kuma a nata ganin simplicity din Hamida
yayi yawa, zai sa kowa ya raina ta.
Sai yanzu ne ta san Balewa ce wayayya ba ita ba. Ita shirme da kidifiri
da girman kan banza kawai ta sani, ta kuma kware a kai.
Mukhy ya ci ya koshi, ta tashi don ta kwashe plates da bowl din
farfesun, ta yi yadda Balewa ta ce ta yi, kuma cikin saa Mukhtar dagowar sa
kenan idon sa ya fada kai, ba zato ta ji ya mike shima, zata tafi da kwanukan
sai ya dan rungumo ta ta baya, ya ce. Na gode da kulawar nan, nagode da dan canjin nan dana gani,
honestly I cant resist it!.
Sannan ya dora karan hancin sa saman gashin kan ta yana rike da ita
daga bayan ta, ya mannota sosai zuwa jikin sa, yana sunsuna gashin ta yana
cusa dogon karan hancin sa a ciki, wanda hakan ya sa dankwalin Amani ya
sabule ya fadi kasa ta baya. Gabadaya gashin da ya shag yara ya zubo bisa kafadun ta. Ya Ilahee!
in ji Mukhy. Yadda Mukhtar ya shiga goga tsinin karan hancin sa cikin
gashin kan ta ya haifar mata da yar rudewa, daburcewa da bakuwar kasala,
duk ta san cewa ita ta tsokano shi, hakan yasa kwanukan dake rike a hannun
ta subucewa suka zube a kasa, da na tangaran ne ba abinda zai hana su
fashewa su yanke su sabida yadda suka subuce daga rikon ta ba zaton ta,
amma hakan bai sa Mukhy fasa abinda yake yi ba, ta fahimci bat un yau ba,
babu kamshin da Mukhy yake matukar so a jikin ta irin kamshin tsakiyar
gashin kan ta, wanda ya fahimci turaren gashi na musamman ne take amfani
da shi a cikin gashin ta, wanda iyayen ta Jalan da Aisata dake bata shi kadai
suka san sirrin da ke cikin sa.
Kamshin gashin nan ya tsokano abubuwa da yawa da yake ta kokarin
dannewa tun dazu, kuma dai dama ko ta ina aka je aka dawo Mukhtar ya san
yayi kewar Tafisu, ba ita kadai ba har tsiwar tata, kidifiri da rashin kunyar
duk ya yi kewa yadda ba ya zato, a kwanaki goma sha hudun da ya yi a
Burkina Faso.
Sai kawai ya jirkito Amani bakidaya ta fado masa ya soma kissing din
ta gently, wani abu data tabbatar ya matukar kwarewa a kai fiye da komai
watau gentle kiss, duk ta kara daburcewa kafin kisses din Mukkhy ya soma
shigar ta yadda ya kamata. Gangar jikin ta kuma ta soma responding.
Tafiya ta soma yin tafiya, Mukhtar na kara birkita Amani da duk wani
nauI na romancing na miji ga matar da yake matukar so, yana kara sanya
mata son amsa kiran sa ta koina da sumbar nan tasa mai shiga rai, a kowacce
gaba mai bukatar hakan a jikin ta, wannan karon ma kamar wadancan
karon, Amani ta gama sakarwa Mukhy komai, da dukkan zuciyar ta da
sahalewar ruhin ta, gabban jikin ta sun gama nuna amincewar ta, ta shirya
welcoming din sa (as a husband), har addua take a ran ta koma meye zai faru
ya faru a yau, kuma a yanzu. Zata jure, in dai hakan zai faranta ran Mukhy
ya daina rikon ta a ran sa ya bari su zauna lafiya.
Lokaci daya Mukhtar ya tuna Amani fa ba wai son shi take yi ba har
yanzu, kada yar canzawar nan da ta yi ya rudar da shi ga sanin ainahin
wacece Amanin sa, Tafisu wadda tafi sauran mata tinkaho, yanzu haka tana
da dalilin ta na wannan dan canjin da ya gani a tare da ita. Maiyuwuwa wani
abun take so yayi mata, amma a sanin da yayi mata, Amani bata da kirki,
kuma bata kirki domin Allah. Sai tana neman wata alfarma a gare ka.
And he will not be selfish anan, duk inda ya kai da son ta, da son
kasancewa tare da ita don bayyana wannan son da tabbatar da shi, yafi karfin
yayi auratayya da macen da baya ran ta kwata-kwata, bata kuma yi masa irin
son da yake yi mata, sai dai ta amince da shi bisa dole don ba yadda zata yi da
auren sa, tunda iyaye suka hada shi bisa karfin ikon su a kanta kuma sun fi
karfin ta. A yanzu kam baya jin akwai abunda ba zai iya hakura da shi ya
zauna lafiya ba a rayuwar sa, ya hakura da iyayen sa ma shekaru sha biyar,
kuma ya rayu da numfashin sa balle soyayyar mace, alhalin yana karkashin
gatan sa?
Amani sai gani tayi Mukhtar ya sake ta ya ja da baya cikin mutuwar
jiki, yatsun sa ya saka cikin tarin sumar kan sa, ya ce Im so sorry for that, I
know you dont love me Amani, and I will not force you to love me or to sleep
with me, because I will not be selfish! In na yi hakan na so kai na. Ya dauki dankwalin ta da ya sabule ya dora mata saman kujera, yana
fadin Sorry for making you to regret this again, I just couldnt resist your
changes for today, I like this new you. Ina ma wannan sabuwar Amani tawa ta
dore! Ya sumbaci goshin ta ya ce by Allah! You will be the death of me
Amani, je ki kada ki sa in kasa controlling kai na kuma, in yi abinda zai zo ya
dame ni, kema ya dame ki, tunda har gobe na kwana da sanin ba kya so na.
Dole aka yi miki a kai na. Na rasa me yasa? Komai na kudurta a raina don tsira da mutunci na
daga fitinar ki, in kika zo gaba na sai kin san yadda kika yi kika rusa min shi.
Amani, why? Why are you playing with my heart? Me yasa bazaki bar ni in
zauna lafiya ba? Ko don kin ga bani da juriya a wannan bangaren Im very
fragile? Kullum sai kin san yadda kika yi kika tsokano ni wato ko? Do you
know how Im suffering after touching you? Na rasa ko ke wace irin mai halin
hawainiya ce, yau ki zama fari gobe baki. Kasancewar kin san ni mutum ne
mai son a kyautata min, a kuma yi min ladabi shiyasa kika bullo min ta nan
ba don kina so na ba?
Na bi ladabin ki da gudu na tattake ba takalmi a kafa ta in dai da shi
zaki yaudare ni yau Amani!
Ya sake ta ya kama hanyar ficewa daga falon, ta karfin hali da bin
karfin zuciya da kuma bravity na son kiyaye pride irin nasa domin hakika
yanayin da fuskar ta ya koma yayi tsananin bashi tausayi, ya bar Amani a
wani yanayi na rashin jin dadi da takurar zuciya wanda har a fuskar ta ya
nuna nadama, ta cigaba da tsayuwa a wurin kamar an kafe ta. Kafin kuka
mai tsananin karfi na nadama da dana sani ya kwace mata.
Ta riga ta san it will not be easy for him and for her, ya yarda da ita, ya
amince da tuban ta farat daya, amma bata zaci har haka ya rike abun a ran
sa ba. Duk kuwa da cewa ta san yana da riko.
Haka ta wuni sukuku a cikin gidan ta, cikin rashin jin dadin abinda ya
faru tsakanin su ranar, it made her whole day black! At the same time, ta
wuni tana takaicin dandani haukacin nan da Mukhtar ke yawan yi mata. Sai
ta sakankance yau zata zama matar sa sai kawai ya fasa, yana nufin, this is his
punishment a gare ta ko me? Ko ya fahimci tana son sa ne yanzu, tun kafin ta
bayyana hakan da bakin ta gare shi, shi yasa yake faman yi mata dandani
haukaci wanda yafi ramuwar gayya ci mata rai?
Bayan wannan dan romance din na Mukhy da ya hana Amani barci
daren yau bakidaya, tunda ya fita lokacin bata kara ganin sa ba sai washegari
da safe a sassan Ummami. Don sanda ya dawo gidan ta riga ta yi barci, kuma
bai yarda ya kwana a dakin ta ba. ya dai leko ya gan ganta tana barci ya wuce
dakin sa.
Ta shiga kenan