Showing 12001 words to 15000 words out of 28936 words

Chapter 5 - Amani 3Hausa Novels by Takori Kabara .pdf

yadda
suka dauke ta a matsayin kyakkyawar al’ada, sai ta yi kasa da murya duk da
har zuwa lokacin jikin ta bari yake yi, ta ce. “Yaya Mukhy ina wuni?”
Bai amsa ba, don ko kyau ladabin bai mata ba, da yake bata saba ba,
sai ma cewa da yayi a dan tsawace. “Nace ina Ummami?”
Amma a kasan ran sa yana mamakin gaisuwar data yi masan, wadda ya
ji ta kamar daga sama, ko kuwa kamar wadda aka tursasa sai tayi, ta yi
gaisuwar ne ta hanyar kokarin danne girman kan ta, wanda har zuwa lokacin
akwai burbushin sa tare da ita, bai bar ta gabadaya ba, duk da ta yi wa kan ta
alkawarin dainawa,
“Ummami ta tai gun Mai” ta bashi amsa murya na rawa da irin hausar
gidan, “bata gun Mai” shima ya bata amsa, “to ina jin tana dakin Mammah”.
Karo na farko a rayuwar su, da Amani ta yi masa Magana cikin kwanciyar
jankali. Hakan yasa ya taso ya kara matsowa inda ta ke cikin son tabbatar da
canjin da aka samu a tare da ita, na gaske ne ko gizo idon sa ke mata? Ya ce
“na zo in gay mata ne zamu yi tafiya Burkina-Faso, zamu kai Alhaji wajen
mai magani, ko zamu jima, ban sani ba”.
Ga dukkan mamakin Mukhtar tashin hankali da tsantsar damuwa ne
suka bayyana a fuskar ta, ta ce “har wata kasa? Amma ai Daddy is doing well

a hakan da yake, not like before, tunda yana motsa komai nasa tafiya ce
kawai baya iyawa”.
Mukhy, ya kara matsowa jikin Amani yana jin dan sanyi a ransa na
canjawar ta, ya ce,
“Wa ya gaya miki tafiya ce kawai baya iyawa? Ai Mamma Jal’an bata
yi tsufan da zata yi zaman zuba ruwa a buta da da daga ruwan wanka da kika
zabar mata ba, kin gane?”
Kunya mai tsanani ta kama Amani ta harari Mukhy ba tare da ta sani
ba, hararar da ta kara kunna shi dama ba wai ya zama satisfied bane yana so
ko yaya ya sumbaci bakin nan nata na tsiwa kafin ya bar dakin, zuciya da ego
da pride din sa na hana shi, tasa kai zata wuce shi don bata son cigaba da
tsayuwa tare da Mukhy, kafafun ta rawa suke yi sakamakon kallon kurillar
da yake bin ta da shi, sai Mukhtar ya riko hannun ta tana kokarin wucewa ta
gaban sa.
“Na gaya miki zan yi tafiya, amma ba wani fatan alkhairi ba komai, me
ya kamata kice min ko ki bani?” “Allah ya kiyaye hanya” kawai zan ce. Ni me
nake da shi da zan baka Yaya Mukhy?” Ya ce “abunda zai mantar da ni
kalolin rashin kunyar ki, da kamanni na da shegu”. Ai Amani kamar jira take
sai ta saka kuka tana cewa.
“Allah ya gani ban san yaushe zaka bar maganar nan tabi ruwa ba
Yaya Mukhtar, wai shi dan adam ba zai taba yin subutar baki ya hadiye ya ce
ya mayar da su inda suka fito, a karbi tuban sa ba?”
Yace “in dai ke ce baki san tuba ba, tubanki shi ake kira tuban muzuru,
baya taba cika sharuddan tuba na addini, don ko bayan wannan din da kika
fada a Freetown, bayan mun dawo Katsina me kika ce min a dakin ki???
Wane cin mutuncin ne baki yi min ba ana I gobe zamu taho nan?”
Ta gane ya koma neman rikici kuma, ya saki layin soyayyar da ke
rinjayar sa da farko, tana kokarin cewa ta tuba tabi alah ta bi shi ‘ego’ din ta
na rinjayar ta, yana gaya mata kada Mukhtar ya ce don ta gan shi da
matsayin sa na yanzu ne ta bashi hakuri. Don haka ta hadiye bada hakurin data so yi a cikin zuciyar ta. Amma
hakika Amani tayi nadama mai yawa, just bata san hanyoyin da zata bi ta yi
expressing hakan wa mijin ya gamsu ba, da kuma yadda zata yi repenting
kura-kuran ta, amma ai darasin rayuwa da karatun ta nutsu da duniya ta
gama daukar sa ita kam! Da a ce tana da wayewa a sha’anin aure, da tuni ta
saukewa Mukhy hadda, musamman da ya kasance mai rauni wajen yawan
son (body contact) da ita. To bata da wannan ‘exposure’ din sai na iya rashin
kunya.
Cikin rikici irin nasa kuma ya sake riko ta, wannan karon bakin sa ya
hade da nata yana kissing, da wani irin zafin rai, kamar ta hakan ne zafin

sheganta shi din data yi zai fita daga zuciyar sa, shi kadai ya san irin pleasure
din yake samu daga irin wannan kiss din da yake yi wa bakin ta a karo na
biyu kenan bayan wanda ya faru a Saliyo, wanda yake jin zakin sa ya fi na
zuma, gardin sa ya fi na madara. Watakila kuma hakan ne kadai zai sa ya
samu rangwame a zuciyar sa da gangar jikin sa na tasirin soyayyar ta mai zafi
da ke damun sa, da kuma jin zafin maganar ta ta baya ta da yake yi akan
maganar ‘shege’, yawan sumbatar ta na sakawa ya manta duk wannan, wani
sako na zuciyar sa ya yarda cewa Amani masifa ce a gare shi.
Eh masifa fa, tunda maganganun ta na Saliyo kadai sun isa su sa ya
tsane ta, ya shata babban layi a tsakanin su amma ina! Kullum sai in bai gan
ta ba, yana iya jurewa rashin ganin ta na wani lokaci amma da zarar ya ganta
din shikkenan ya rasa duk wani control na kan sa. Ya cigaba da sakin zazzafan kiss din sa idanun sa a rufe, a kasan ran sa
yana rokon Allah ya canza masa Amani, (from evil to good, and from devilish
to saint), cikin wannna halin suka jiyo takun Ummami tana kokarin shigowa
don suna jiyo kirarin da bayin ta ke mata daga waje. Da sauri Amani ta hankade Mukhy, ya ce “ta baya ta rago bayan duk
kin gama tsotse mata Dan ta, na kan manta ke kanwata ce nake wannan aikin
zubar da girman da ke, in sha Allah ta yi kai, daga yau ba zan kara ba”. Ya
dauki wayar sa a kan sofa ya nufi kofar fita, ya bar Amani da budadden
bakin mamakin sa.
Mutum kamar mai iskokai, ya gama yamutsata yadda yake so har
dakin uwar ta, kuma ya bita da wannan maganar, wai itace ta tsotse shi, ta yi
dan murmushi tana cewa a ran ta “Mukhy-Mukhy case ne shi wallahi, ko
yaya ne dai, ni di kujera ce, dole a zo inda nake a zauna a kai na, duk da gorin
hali da ake yi min din!”.
Yana saka kai zai fita daga dakin Ummami na shigowa, sun kusa karo,
ya yi maza ya ja baya ya bata hanya, ta ce “to kai kana nan ashe, ana can ana
ta neman ka, duk sun fito kai suke jira zaku tafi airport” “Ummami ke na zo
nema ni, bamu yi sallama ba” “a’ah ka dai zo yin sallama da matar ka, to gani
me zaka bani?” Mukhy sai ya riko hannun Ummami, ya sumbaci saman
hannun nata ya ce “wannan sallamar zamu yi”. Kunya irin na rashin sabo ya
kama Ummami, amma ta yarda Mukhtar yayi rashin wannan soyayyar tata,
bata nadama, amma tana tausayawa faruwar hakan a tare da shi, yau gashi ai
Allah ya raya musu shi, ya zama magidanci cikin koshin lafiya.
Tabbas ka ki naka ne duniya ta so shi, amma mutanen duniyar ma ba
kowadanne ne irin Alhaji Usman Faskari ba. masu maida dan kowa nasu,
kodayake shima din sa’ar sa aka ci don a baya halin mutanen duniya gare shi.

Da wannan tunanin take so itama ta kwatanta, wajen rike masa tilon
‘yar sa da amana duk da cewa itama ‘yar ta ce. To Amani zata ci tudun
alfarma har biyu kenan a wurin su.
Ta dubi Amani dake ta sunkuye-sunkuyen kai, rashin gaskiya duk ya
bayyana a tare da ita, da kyar in Ummami bata ga abin da ta gani ba, ta ce,
“ina fatan kun yi sallama, zasu wuce Burkina-Faso ne”. Yace “Ummami
wace irin sallama ce tsakanina da ita? Baki san Amani bata so na bane?”
A firgice Amani ta dago ta kalle shi a tsorace, ya kuwa tsare ta da
kyawawan idanun sa ya ce “ko zaki ce karya nayi miki? Ba auren dole Alhaji
yayi miki ba? Ko in gaya mata me kika ce da ni a Freetown gidan Faytoory?”.
Idanun sa suka kada, suka kuma tsaya a kan ta, kamar yanzu ta fadi
maganar, ita dai ta shiga uku ta lalace da Mukhy a kan wannan maganar,
mana daya ya ki yafe ta. Amani ta hadiyi miyau da kyar, ta girgiza kai,
idanun ta fal hawaye, ga mamakin ta tafiyar da zai yi Burkina-Faso har
tsayin sati biyu shi ya fi damun ta da daga mata hankali a yanzu, ba wannan
tone-tonen nasa da neman rigimar tasa ba.
Ummami duk da maganar ta buge ta kuma bata yi mata dadi ba amma
ta waske, ta ce “ta yaya za’ayi hakan? Dole kanwa ta so Yayan ta” yace “banda
wannan Ummami, ita bata son kowa daga kan ta sai kan ta” da Amani ta ga
zai tona mata asiri a gun Ummamin dake ganin mutuncin ta, sai ta saki kukan
da dole zai dakatar da shi, kuka shiga yi riii-riii sosai, nan kuwa ba na komai
bane na damuwar tafiyar sa ne.
Ko har yaushe Mukhy ya soma samun matsuguni irin wannan a ran ta,
da har take jin damuwar tafiyar sa matuka gaya haka a kasan ran ta? ita kan
ta bata sani ba! Ummami ta hau shi da fadan girma, inda take cewa cikin
fada-fada “kada ya kara gaya mata wani abu da ya shafe su, tunda ita bai
shafe ta ba”.
Sannan ta hau lallashin Amani, tace “rabu da shi diya ta kin ji, gidan
zai bari ki samu ki huta sosai” Amani kamar ta cewa Ummami “ita so take ma
ta bi shi, babu wani hutu a nesantar ta shi sai karin damuwa da hakan zai
zame mata”, hakika yau ta samu kan ta a sabon yanayi, wato ta samu kan ta
da enjoying dan short kiss din da yayi mata fiercely (a zafafe) fiye da wanda
ya faru a gidan Mamma a Kenema, ita bata san ana soyayya cikin zafin rai ba
sai yau.
Memories din hakan, dana sumbatar da ya yiwa kirjin ta, ya like a
kasan ran ta, kamar har zuwa lokacin Mukhy sumbatar nata yake ke cigaba
da yi, don har zuwa lokacin tsigar jikin ta da Mukhtar yayi sanadin tashin ta
bai koma normal ba. Ya saci kallon ta, kamar ya karanci situation din da ya bar ta a ciki,
shima hakan take, ji yayi kamar ya ce da Mamma a tafi da ita su dan zauna

tare, amma sai kawai ya share, yayi wa Ummami sallama sannan ya bar dakin
ba tare da ya sake bi ta kan ta ba, yana so ya koma Mukhtar din sa na baya,
mai daurarriyar fuska, rashin walwala, da cin magani, amma ina! Idan yana
gaban Ummami yanzu, sai ya ji kan shi kamar yaron goye, farin ciki ya cika
zuciyar sa, rayuwar sa ta haskaka ta zama cikakkiya, soyayyar da bai samu a
kuruciyar sa ba ita yake samu yanzu wadda take yawan saka shi a nishadin
da yake sawa ya manta previous situation din nasa.
Wannan yanayin nasa na rashin walwala da bacin rai a yanzu ya zama
tarihi a tare da shi.
Ya gane hakan ne da ya ga har ya ga Amani duk da fushi da yake da ita
amma kuma ya kasa ignoring din ta, karshe sai gashi ya bige da sumbatar ta,
wanda ya jima da hana kan sa sake bari wani abu makamancin wannan ya
shiga tsakanin su, sabida abubuwan data faffada masa ana I gobe zasu taho
Diffa a dakin ta na gidan su sun kara kwaba waccan maganar ta farko.
Duk da cewa ya rama da mai zafi har fiye da nata tun a lokacin, daidai
da yadda yake so ya rama din, amma tsatsar maganganun har yanzu bata bar
ran sa ba.
Mukhtar, Alhaji, Mamma, Baba Idi da wadanda sarki ya wakilta su
raka su har mutum biyar, sun tashi a jirgin sama zuwa makwabtan su wato
Burkina Faso, ya zama sai ita da Ummami da Sahura da tarin bayi mata da
ke shige da fice suna ayyukan su a bangaren Ummami. Tunda Mukhy ya kira Ummami yace sun sauka lafiya bai kira Amani
ba, hakan yana cikin sababbin techniques da ya dauka don yana so ya koyawa
kan sa tolerance a kanta, ita kuma ya koya mata sanin darajar sa, har zuwa
lokacin da zata koyi son shi don radin kan ta, irin son da ya samu kan sa yana
yi mata, ba wai so na tursasawa ba ko na cin alfarma, ko don idanun iyayen
sa da take tunanin bashi da su a baya, ko na dangantakar jini da ke tsakanin
su.
Ummami tasa aka shirya musu zuwa wajen kishiyar ta wato Hajja
Tarha domin Amani ta gaishe ta, an musu karba ta musamman a sassan
Tarha ta kuma kira ‘yar ta Sa’adiyya dake Guinea a waya ta hada su suka
gaisa da Amani. Ummami ta yi haka ne don samar da sanayya tsakanin
Amani da ‘ya’yan Sarki guda biyu mata, wato Sayluba da kanwar ta Sa’adiya
kasancewar su ‘yan uwa biyu kacal da Maina ya mallaka a duniya. Kuma dai
dama tsakanin ta da Tarha babu muguwar gaba ta azo a gani sai kishi, wanda
ba’a iya kaucemawa, wannan sai Ummu Aymana, wadda Allah ya raba su a
yanzu.
Sayluba kuwa sun hadu tun a wajen bikin auren su data zo, har ta
koma Tahoa tun kafin a kammala bikin, halayen ‘ya’yan Sarki Issouffou mata

kwata-kwata bai yi kama dana iyayen su mata ba. Suna da saukin kai sosai da
son mahaifin su, don bai raga musu komai na soyayyar Uba ba.
Sannan tasa aka kai Amani gun amaryar Sarki ta yanzu wadda ita daga
Somaliya ya auro ta.
A daren Mukhy ya kira Mai Diffa, ya gaya masa in sha Allahu akwai
alamun nasara a maganin da akewa Alhaji, don haka Sarki ya gayawa
Ummami, inda ya ce ta gayawa Amani ta cigaba da yi wa mahaifin ta addu’ar
neman lafiya mai dorewa. **** **** ****

MALAMA BA SURUKA BA!
W
annan tafiyar da su Alhaji suka yi suka bar Amani tare da Ummami, shi ya
haifar da wata kyakkyawar shakuwa a tsakanin su, kuma Ummami ma
kamar kowa ta soma noticing rashin wadatar ilmin addini da rashin ingancin
dabi’un Amani, sakalcin ta, doloncin ta da sauran su. Amma ita ba kamar
Jal’an ba, bata duka bata hantara, sai tayi amfani da tafiyar su Mukhy
Burkina Faso ta ja Amani a jikin ta, babu tsawa, babu duka ta soma koyar da
ita muhimman abubuwa da ya kamata matar aure ta sani na addini, Ummami
tun daga alwalah, sunnoni da farillan sallah dana alwallah da wankan janaba
ta soma koya mata, domin ta sha mamaki da ta ce ta yi mata bayanin yadda
ake yi ta ga ta hau kame kame, ko kuma kai tsaye ta ce bata sani ba, ko ta ce
ta manta.
Sannnan hatta yadda akewa sarakuna magana cikin ladabi da kwantar
da murya sai da Ummami ta soma aikin koya mata, da yadda ake rayuwar
aure da masu mulki, wani abun Amani ta ji kunya, wani abun ta gode har
cikin ran ta. Ummami dai ta zamewa Amani malama ba suruka ba, shakuwar su ta
kai ga cewa Ummami ta fahimci akwai rashin jituwa da rashin kakkarfar
soyayya tsakanin Amani da Mukhtar, kuma auren hadin Alhaji ne ba wai su
suka hada kan su ba, amma ta fannin dan ta Mukhtar dai ta san ko makaho
ya shafa zai gane yana matukar son Amani a cikin idanun sa ma kadai, amma
abinda ya fada ranar da zai tafi, ya dan tsaya mata a rai, da ya ce Amani bata
son sa, auren dole Alhaji ya yi mata da shi, ta sunsuni akwai babbar matsala a
kan hakan a tsakanin su.
Ummami bata san cewa daga tafiyar Mukhtar zuwa yanzu an samu
positive improvement wato canji mai yawa ba, a tare da Amina-Amani. Ta
kasance cikin kewar Mukhtar, yadda bata zato, ba tare da ita kan ta ta san
cewa tana kewar tasa ke damun ta ba, gabadaya tayi sanyi, duk ta zama wata
irin shiru-shiru ba tsiwa, ba gayu ba cokala daurin kallabi. Mukhtar ya bar ta

da kewar sa mai yawa a ranar da zai tafi, in ta tuna memories na abinda ya
faru ranar da zai tafi kai mahaifin ta gidan magani, wato (sweet sensation) na
lokacin ya ki barin ran ta, taji tana so ma ya dawo, ko ganin sa ne ta yi daga
nesa, koda yake yace ba zai kara kiss ba, umh. Amma ita yanzu ne ma ta fara
so da sha’awar kiss din nan nasa, ta samu kan ta da son yayi maza ya dawo a
maimaita sumbar, ko da cikin cokali ne wato wadda bata kai ta tsayin
mintinan na ranar tafiyar sa ba.
A wannan lokacin da wannan tunanin ya zo mata, Amani sai da ta tura
kan ta cikin filo tana jin kunyar kan ta da kan ta, zuciya mai abun mamaki,
zuciya tsokar naman kirjin dan adam mai yawan dawurwura (rashin
tsugunawa a wuri guda), wai yau kuma Mukhtar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login