Showing 15001 words to 18000 words out of 28936 words

Chapter 6 - Amani 3Hausa Novels by Takori Kabara .pdf

take kewa, da bege haka,
kai har ma da mararin gani, dan adam kenan mai saurin manta baya.
Gaskiya ne da aka ce (no condition is permanent). Gaskiyar Balewa da ta taba
cewa ta taka a sannu akan wannan bawan Allah bata san inda rana zata fadi
ba.
A wannan lokacin Hamida ta fado mata a rai, hakika bata kyauta ba,
tun zuwan ta bata kira Hamida ba, akawari bai ce haka ba, gashi zata so ta
bata labarin abubuwa da yawa da suka faru da ita dinnan a bayan rabuwar
su din nan, masu dadi da marassa dadin, koda yake masu dadin kamar
haduwar ta da Maman ta da dawowar Mukhy cikin nasa iyayen su suka fi
yawa cikin labarin da zata baiwa Balewa, to amma wace irin fassara Balewa
kan ta zata yi mata in ta ce mata yau gata dumu-dumu cikin kewar ‘Dirty
Human Being?’ Cikin mararin ganin ‘Smart Ass’ da begen sumumu-kasau? In
reality, Hamidah ta fi kowa gaya mata ta taka a hankali a kan Mukhy, ta ji
tsoron kaddara, ta rage kiyayyar ta ga Mukhy, har ce mata ta taba yi bata san
inda rana zata fadi ba, yau ga rana ta fadi da ita a gabas! Inda wanda ya san
kin da ta yi wa Mukhtar da tijarar data zuba masa don wai yana matsayin
yaron baban ta babu kamar Hamidah Balewa, ina ma dai da a ce Hamida
zata zo har Diffa, ta ga yadda rayuwa ta yi kuli-kulin kubra da ita, iyakaci dai
tayi mata dariya da shegantakar da bata san karshen su ba.
Anyway, ya kamata ta kira Balewa, ta labarta mata duk abubuwan da
suka faru a bayan ta, don abokin kuka ba’a boye masa mutuwa, shakiyanci ne
dai ta san zata yi mata har sai ta gaji ta bari don kan ta.
Amani ta kira wayar Hamida, cikin sa’a ba jimawa layin ya shiga, duk
da ba koyaushe suke amun network mai kyau na yin kira Nigeria ba, saboda
rashin kyawun network na yankin su. Hamida ta daga da hamzari, tana fadin.
“Sahibah, ke ce kuwa a kan layin? In da alkawari ruwa baya dafa kifi ba, kin
makale a Saliyo, kin manta da ni Bestien ki? Anya alkawari ya ce haka?”

Amani tayi ajiyar zuciya ta ce “da farko dai zan fara da baki hakuri
Bestie, ki yi hakuri Hamdy, na shiga harkalla mai yawan gaske data sa ban
samu damar kiran ki ba, sai yanzu da na samu nutsuwa.
Kawata I have a lot to gist you with, muhimmi a ciki, ina mai farin
cikin shaida miki cewa na hadu da Mama na Haj. Jal’an a Saliyo, har an
mayar da auren ta da Mahaifi na mun taho tare da ita, ki taya ni hango irin
farin cikin dana ke ciki a sanadin hakan, amma a halin yanzu bama Katsina
muna can yankin Diffa”.
Da tsananin mamaki Hamida ta ce “Sahibah Diffa kuma? Wajen wa?
Inane haka?” Amani ta nisa tana fadin “Bestie, wato labarin nan mai yawa ne,
mai matukar ban al’ajabi, har ma da ban tsoro a cikin sa, na so a ce ga ni ga
ki ne, in kwantar da kai a kafadun ki in yi kukan nadama, in kuma yi dariyar
farin ciki as well, amma dai in takaice miki, na kwashi kashi na a hannun
nadama, na kuma nade tabarmar kunya ta na yi gammo da ita a kai na.
Abinda kika dade kina tunasar dani cewa in taka a sannu, kada watarana in
zo ina nadama ya tabbata.
Ashe Mukhtar da nake rainawa dan sarkin Diffa ne, mai jiran gadon
sarautar gidan su, da daya kwal da Sarki Issouffou ya mallaka, wanda inda
an bi ta nasabar da nake masa gori ne, ba zai aure ni ba.
Diffa na daya daga cikin manyan biranen kasar Nijar, sannan kuma
ashe dan uwana ne na jini, dan Yayar mahaifiya ta ne Haj. Aisata, wadda ke
aure a can tun da jimawa”.
Hamida ta yi kabbara, ta sake yi, ji ta yi kamar ta shigo cikin wayar ta
tadda Amani sabida zaquwa ga abinda take ji, ta ce “ki bari Sahibah, bana so,
bana son irin wannan zolayar kamar ta hikaya” Amani ta yi rantsuwa tace
“babu zancen wasa a cikin magana ta. Ashe duk jini na na yiwa wannan
tijarar, yau gani dumu-dumu cikin kogin nadama da wani sabon yanayi
Sahibah, wanda nake so ki fidda ni a duhun sa”.
Ta dan yi shiru, domin ita kan tabtana jin kunyar abinda zata fada,
“kewar Mukhtar nake Hamdy, son ganin sa nake, matukar son ya sake
kusanta ta na ke, sabida baya gari yanzu haka, ya kai Alhaji Burkina Faso
tun satin da ya wuce” ta tusa kanta cikin filo rike da wayar tana cewa “na
shiga uku Balewa, don ji nake abinda nake fada kamar sabo nake, amma
gaskiyar abinda ke zuciya ta kenan, mararin ganin sa da dawowar sa daga
Burkina Faso nake yi kamar in yi tsuntsuwa in cimmasa.
Me yasa a da bana jin hakan ban da kiyayyar sa?
Hamida bana so ya kasance sai da ya taka wani matsayi ne hakan ta
faru da ni, don ban san fassarar da shi kan sa da al’ummar da ke zagaye da
mu zasu yi min ba!”

Hamida ta yi kabbara ta sake yi, sannan ta fadi ta yi wa Allah sujjadah
a dakin ta, ko babu komai ya karbi addua’r da ta dade tana yiwa aminiyar ta,
yau matsalolin ta sun warware ta kowanne bangare, jin abubuwan da take
fada mata take kamar almara ko tatsuniya, tace “Amani (sunan da ba kasafai
take kiran ta da shi ba), are you sure duk wadannan abubuwan da kike
gayamin daga bakin ki suke fitowa?”
Amani sai ta soma share hawaye cikin karaya da tsoron kada ya
zamanto Balewa ce farkon wadda zata karyata ta, ta ce “what are friends for?
Shi yasa na gaya miki. Shi ya ce tuba na na karya ne, kada kema ki ce haka
don Allah, in na boye miki ai bazan boyewa Allah ba cewa na yi nadama,
Allah ya ga zuciya ta tayi wani irin damuwa da shi yanzu”, ta share hawayen
ta sannan ta ce,
“amma wa zan gayawa ya yarda da ni in ba ke ba?
Ko cigiyar sa nayi cikin kuskure Baba Sahura mahaukaciya take maida
ni, shin dan adam baya taba iya gyara kuskuren sa ne a karbi tuban sa?
Don na tabbata in kowa zai yarda dani banda shi Mukhtar din, sabida
wata bakar magana dana gaya masa cikin kuskure da ya kasa mantawa”, da
sauri Hamida ta ce “kada ki gaya min, na san zaki aikata, ni na yarda da ke in
kowa bazai yarda da ke cewa kina son Mukhtar ba Sahibah, ni na yarda kina
son sa ba tun yau ba, wauta ce ta hanaki ganewa tun can kin damu da Mukhy,
kin damu da duk wani takun sa a rayuwa ta hanyar yawan yin maganar sa
with utmost hatred, and too much hatred ‘so’ ne yake kawo shi. Haka yawan
yin zancen mutum.
Don haka ‘yar uwa bamu makara ba zamu samo kan Yaya Mukhy din
mu, ke dai ki tabbatar kin canza din da gaske kuma da zuciya daya, ki kuma
tabbatar masa da canjin naki ta hanyar nagartattun halaye sababbi da zaki
yafa yanzo, ki koyi bayyana soyayyar dake zuciyar ki a gaban sa da ladabi da
biyayya, Sahibah ki nuna kulawa koda zai miki wata fassarar, to na dan
lokaci ne, don na tabbata “Mukhtar na son ki”.
Da sauri Amani ta damke wayar ta sosai a kunnen ta, hawayen farin
cikin kalaman Balewa ya tsirgo mata ta ce “da gaske kike Hamida Mukhtar
yana so na? Kuma zai cigaba da son nawa bayan duk abubuwan batanci da
tozarci da na yi masa? Zai cigaba da son nawa bayan ya dawo cikin gatan sa,
ba zai fassara ni da wata fassarar ta daban ba? Hamida har ce masa na yi
yana kama da….. Astagfirullah bana so in maimaita don na koyi sakawa
harshe na linzami”.
Maganar ta yi wa Hamida gingiringin, amma ta san Amani neman
wanda zai kwantar mata da hankali ta a ke yanzu, shi yasa har ta neme ta,
tana neman mai bata support da assurance na cewa in ta gyara kurakuran ta

za’a yafe mata, tunda ta ce ta koyi sarrafa harshen ta ta hanyar yin furuci mai
kyau ga kowa, ance matar na tuba bata rasa miji.
Hamida tayi ajiyar zuciya. Sun tattauna ‘extensively’ kuma ‘heart to
heart’ yadda ya kamata aminai na kwarai su magantu, a kan wata mas’ala
data sha kan dayan su. Hamida ta gaya mata cewa har abada Mukhtar ba zai
guje ta ba, ta gaya mata dalilan ta; inda tace bayan soyayya ta jini akwai
soyayya gangariya a zuciyar sa a kan ta. Sannan ta gaya mata wasu
maganganu na sirri na yadda zata nunawa Mukhtar cewa da gaske ta canza
da zarar sun tare a gidan su.
Amani da Hamida yau sun raba dare suna tattaunawa kuma Hamida ta
taya ta murnar duk abubuwan da suka faru din. Kuma ta ce zata zo har
dakin ta a Diffa watarana idan Allah ya nufa.
Tun daga ranar dokin ta ga son dawowar Mukhy ya karu, har
practicing/rehersing yadda zata yi masa sannu da dawowa take yi, da irin
kallon da zata ke masa mai nuna kunya da ladabi ba irin na baya ba da take
ware idanuwa ta zuba masa harara, yadda dai Hamida ta gaya mata, ya zama
duk dare da tunanin Mukhtar ta ke iya barci, ta kuma gan shi cikin mafarkin
ta, a yanayin da take kwadayin ganin nasu.
Ummami bata san hakan ba ita, domin ta koma fara yi wa dan ta yakin
neman soyayya, a fakaice (kamfen). Daga ranar data fara koyar da Amani
karatu, in suka yi karatun addini suka gaji don ko wajen Mai bata zuwa sosai
yanzu kullum tana like da Amani, don ta fahimci itama irin Mukhy ce ba
soyayyar uwa ta tashi, gara ita ta samu ta uban shi kuwa fa?
A kokarin ta na son kara cusa soyayyar tilon dan ta a zuciyar ‘yar uwar
sa kuma matar sa, tunda ta ji yaa ce bata son sa duk da ta musanta hakan, sai
ta ga bari tayi amfani da damar wajen fayyacewa Aman tarihin Mukhy
wataila hakan yasa ta tausaya masa a matsayin ta na ‘yar uwar sa, tausayi da
fahimta ta sani suna tasiri sosai wajen kimsa SO. Don haka rannan bayan sun
gama karatu na addini da Karin Al’qur’ani da take mata kullum sai Ummami
ta sako zancen Mukhtar.

Tace “Aminatu kin san labarin mijin ki Maina?”
Cikin jin ‘yar kunyar gaske da ta fara samun muhalli a tare da Amani
yanzu, ko da yake in bata kunyar kowa tana kunyar Ummami, ta sunkuyar
da kai, a lokacin tana taje ma Ummami dogon gashin kan ta da furfura ta
soma samun muhalli, Ummami ta ce ta raba shi gida biyu ta yi mata tufka
biyu ta gaji da shi a tsefe, mai kitson ta ta yi tafiya. Amani ta ce.
“A’ah Ummami, ni dai kawai na tashi na gan shi karkashin kulawar
Alhaji na, ban san inda ya samo shi ba kuma ban taba tambayar Daddy ba

don bama jituwa ni da Yaya Mukhy ko kankani, shi baya son hali na nima
bana son nasa, shi yasa kika ji yana cewa wai bana son sa!”.
Ta karasa fadi cikin karamar murya mai nuna kunyar idon uwa, amma
gara ta gaya mata gaskiya a kan ta ci gaba da rikon ta a ran ta a kan bata son
Mukhy, ba uwar da zata so a ce dan ta na auren macen da bata son sa sai dai
ta yi kawaici, idan mai kawaicin ce irin Ummami kenan. Ummami ta gyada kai ta ce “wato Amani, a duniyar Subhana ina
tsananin tausayin Mukhtar Amani, shi yasa nake so kema ki tausaya masa, ki
bashi soyayya wadda ban bashi ba, ki jiyar da shi dadin da mata hudu zasu
jiyar da shi a lokaci daya, ki kuma kula da shi da rayuwar sa yadda nake
kokari akan mahaifin sa ba don bai da wasu matan ba.
Ummami ta nisa, sannan ta cigaba da cewa “kin ga yadda ya bar gida
duk gatan shi a shekarun balaga, a shekarun da ya dace a ce yana kusa da
mahaifin sa a fadar sa yana koyar da shi sha’anin mulki, amma ya zabi ya tafi
uwa duniya sabida rashin samun kulawar iyaye. A hakan ma don baki san
irin rayuwar da yayi tare da ‘ya’yan bayi, a kuma sassan bayi ba”.
Idanun ta ya ciko da hawaye ta ce “shi da ni sai dai leke daga nesa, ban
taba goya shi a baya na ba, duk hakan bai isa ba aka zo aka bi shi da mugun
asiri wai “kurciya” ya kara yin nesa da gida, kuma Baban sa bai damu ba ya
cigaba da gudanar da harkokin mulkin sa rai kwance hankali kwance. A kan idanuna babu irin gatan da bai yi wa ‘yan uwan sa mata Sayluba
da Sa’adiyya ba. Tun ba lokacin auren su ba. ya zaba musu mazaje na fita
tsara ya kuma yi musu auren gata.
Kema kin san kafin uwa ta jure wannan kin san akwai wuya, meye
laifin Maina don kawai ya zo a namiji? Amma haka na jure don farantawa
miji na bisa ra’ayin sa, ban taba kalubalantar sa ba tunda aka ce abinda
babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba. Kullum jakadiya ta kawo min shi don in shayar da shi, nuna mata nake
bana so, in ta isheni da roko sai in karbe shi, amma kuryar daki nake tafiya
da shi ina shayar da shi ina kallon shi ina kuka. Ya kan kura min ido kamar
yana tambaya ta dalilin mu na yi masa haka….??? Ummami ta share hawayen da suka kawo a idon ta, itama Amani zuwa
lokacin nata idon ya ciko da kwallah, ta cigaba da cewa “na san yana leken
mu a shigifar sarki ko wajen hutawar sa da yamma a yawancin lokuta, wanda
ba komai ke kawo shi ba sai bond din nan na soyayyar iyaye, wannan yasa na
ke yawan zuwa wajen da Mai yake hutawar yammaci, dan mu yi sallar la’asar
tare, in mun idar in yanke masa akaifa ko in taya shi hira yana daga zaune
bida karagar sa ina daga kasan kafafun sa cikin ladabi mai yawa, ba don
komai ba sai don in ya zo leken namu nima ina samun damar ganin sa a sace.

Ranar da aka ce min ya gudu ni na san dalilin sa, na kuma yarda da
hujjar sa, tunda bamu taba zama da shi mun masa bayani, wanda zai gamsu
da hujjar mu ba, don haka duk abinda zuciyar sa ta gaya masa ko ta fassara
masa a kan mu a wancan lokacin a wurin sa shine dai dai. Suma na dinga yi
ba tare da kowa ya san dalili ba, ana zuba min ruwa ina farfadowa. Daga
ranar kuma ban kara sallah na tashi ban yi masa doguwar addu’a ba, kan
cewa duk inda ya shiga Allah ya zama gatan sa, ya kare mun shi da karewar
sa da kiyayewar sa, ya kuma kula da shi. Domin na yarda kulawar Ubangiji
tafi tamu ta iyaye, kuma itace ta kawo Mukhtar yau inda yake.
Ya yi rashin duk wata soyayya ta iyaye a kuruciyar sa, ina jin damuwa
idan na tuna hakan. Da wannan nake rokon ki, a kan ki dubi girman Allah ki
kula min da Mukhtar kin ji AMINA! Ko da a kasan ran ki babu soyayyar…”.
Amani sai ta saka kukan data ke rikewa tun dazu a bakin ta, kuka mai
sauti sosai, ta rasa abinda zata ce da Ummami wanda zai sa ta gamsu ba ta
kin Mukhy yanzu, it’s true Mukhy had a traumatic childhood, and he deserve
happiness a yanzu. Matsalar ta da shi ‘riko’. Ya ki sakin ran sa da ita su mori
auren da kuruciyar su sai tsananin rikon ta da laifukan na baya da ya bari
suka yiwa ran sa kaka-gida. Ko yayi kokarin sakin ran sa da jikin sa da ita
wani time din, rikon dake zuciyar sa sai ya hana shi. Bayan rayuwar
bakidayan ta sai ana ma juna afuwa, saboda rashin tsayin ta da rashin tabbas
din ta. ‘Life is very short and transient’. Amma ai Allah ya san ta yi nadama,
wadda ba lallai wanda ya santa a baya ya karba ba, za’a ce ne don ta gan shi
da gata ne a yanzu.
Don haka ta hadiye duk wani tunani a ran ta, nadamar ta da damuwar
ta a kan Mukhy bata iya ta cewa Ummami komai ba, sai sheshshekar kuka
take tana hadawa da ajiyar zuciya.
Ummami ta ce “to yanzu meye abin kuka daga magana? Ni labara
kawai na baki don ki tausaya masa. Ba don in saka ki kuka ba. Koda yake
Jal’an ma haka take da saurin kuka, da abinda ya isa a yiwa kuka da wanda
bai isa ba duk abin kuka ne a wurin ta tana karama, kin yi gado. Ni dai na
baki amanar Mukhtar don dai gashi ya dawo gare mu ne, amma rayuwar sa
zata fi yawa tare da ke, ke ce silar duk wani farin ciki da zai iya samu ko
akasin sa, domin sai kin faranta masa daga gida ne zai fito cikin jama’ar sa
cikin annashuwa, ya ji dadin tafiyar da al’ummar sa da mulkin gidan su da
tarin responsibilities din talakawa da ke kan sa, tun da dai kin ga shi Maina
ne wato (Mai jiran gado)”.
Da zata iya da ta gayawa Ummami cewa ta daina bata amanar
MUKHY don Allah, don ita Uwar sa ce kuma bata san halin sa ba, amma shi
ma ai takadarin kan sa ne na gani kashe ni,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login