Showing 18001 words to 21000 words out of 28936 words

Chapter 7 - Amani 3Hausa Novels by Takori Kabara .pdf

wanda baya bari ko da wasa a

taka shi, ko a danne hakkin sa da ya rataya a wuyan mutane. Sai ya kwaci
abinsa ko ta karfi ne.
Kamar misali in tayi masa kwauron gaisuwa kasancewar shi mutum ne
mai so a bashi girman da ya cancanta, da son kowacce mace ta kasance da
halaye da dabi’u na kwarai na girmama miji kwatankwacin irin na Ummamin
sa, to fa ba zai hakura ba sai ya nemi gaisuwar nan ko ta karfin tsiya ne da
bakin sa, haka in tayi masa rashin kunyar nata mai lasisi, Mukhy ramawa
yake yi babu jinkiri babu bata lokaci, wani lokacin da mai zafin da yafi nata
zafi, wanda sai ta kwana tana hadidiye bakar maganar sa.
Amma tayi ‘relating’ da labarin da Ummami ta bata na kuruciyar
Mukhy, sai ta ga cewa ita kam, duk da babu Jal’an, kuruciya ta gata da ‘yanci
kuma mai dadi ta yi, har ma da jin dadin tafi kowa gatan uba, he really
deserves happiness ko yaya ne a rayuwar girman sa ta yanzu, kamar yadda
mahaifiyar sa ta ce. Kuma ba daga kowa wannan farin cikin zai fara samuwa
gare shi ba sai daga cikin gidan sa, wato daga hannun ita matar sa.
Can cikin kanta ta jiyo sassanyar muryar Ummami, kasancewar ta yi
nisa a tunani.
“Kin min alkawarin kula da Mukhtar da bashi soyayya da farin ciki a
rayuwar girman sa AMINA? Ni kuma in kika yi min hakan, na yi miki
alkawarin ba dai kiyi kuka akan Da namiji ba, zan tabbatar na zame miki
garkuwa a wurin sa, daga duk mai son shiga gaban ki. Fata na kawai shine
Mukhtar ya samu kwanciyar hankali a rayuwar girman sa, wadda bai samu
ko kadan a kuruciyar sa ba.
Ni da ke, babu hijabin surukuta ko yaya a tsakanin mu, sakamakon
cewa ke din ‘ya ta ce ta halali, wadda ko babu Mukhy a tsakanin mu zamu
kashe mu rufe tare, ba tare da ko Jal’an data yi nakudar ki ta ji ba. Hakika
Allah Subhana na so na da kwanciyar hankali a tsufa na, wanda ban samu a
kuruciya ta ba cikin gidannan, shiyassa ya bani ke wato ya sallado min ke a
matsayin suruka ba tare da dabara ta ba, ke da kika kasance ‘ya ta halali a
gare ni, bai yi min suruka da wata daga waje ba, wadda zata sa Mukhtar ya
sha wuya a hannun ta, don kawai yana son ta, shi yassa na bude miki ciki na
yau mu fahimci juna mu tallafawa juna ta hanyar bashi kulawa a farin ciki ni
da ke, ki sa a ran ki ni na haife ki ba Jal’an ba”.
Amani ta share ‘yan kananan hawayen da suke ta tsatstsafo mata a
kowanne furuci na Ummami, wadanda ta san ba na komai bane na tausayin
Mukhy da Mahaifiyar sa ne, duk Ummami ta gama kasha mata jiki da kuzari.
A hankali ta gyadawa Ummami kai, wato ta yi wannan alkawarin, na kula da
Mukhtar, da sanya shi farin ciki da bashi soyayya.
Kuma har cikin ranta ta yi din, domin jikin ta yayi wani irin sanyi, ta yi
lakwas kamar jikaakken tsumma, jijiyoyin rashin kunya, na girman kai, na

alfahari dana dolonci suka shiga tssitstsinkewa suna farkewa da kan su,
hankali da nutsuwa har ma da tsoron Allah ya soma ratsa Amani a
kusufa-kusufa daban-daban na kwakwalwar ta.
Ta gamawa Ummami kitson cikin matsanancin mutuwar jiki, kuma
dare ya yi, don haka ta ce mata zata je ta kwanta, kan ta na sarawa sabida
kukan data yi mai tsanani.
Kuyangin ta da aka bata su suka raka ta har dakin barcin ta, don har
zuwa lokacin suna can suna jiran ta a inda suka saba zama su jira ta in ta zo
gun Ummami, da suka dawo bangaren ta daya daga cikinsu ta hada mata ‘tea’
mai kamshin na’na’a bisa umarnin ta, ta sha a gefen gadon ta, sannan ta kawo
mata Panadol ta hadiya, suka yi mata duk abubuwan da suke yi mata kafin ta
kwanta kamar kashe kayan wuta, kunna A/C da kunna mata karatun
Al’qurani a radion bakin gadon ta cikin kira’ar Mahmoud Khalil bisa
umarnin Ummami, na kullum su kunna mata in zata kwanta daga kanan
surori don ta kara iyawa da gyara karatun sallahr ta. Tahira da Sugra kenan,
wadanda su tafi sanyawa aiki da ja a jikin ta cikin hadiman nata guda biyar
da Sarki yasa aka bata tun zuwan ta, sauran biyun suna kula da girki da
kitchen din ta ne, daya kuma sharar bangaren ta da goge-goge da wankin
toilets, ta zabi Sugra daTahira su dinga zama a jikin ta ne don su ba yara bane
kamar sauran ukun, suna da hankali da nutsuwa, kuma suna da aure har da
yara. Ko’ina zata shiga cikin gidan suna tare da ita.
Tahira da Sugra suna bada baya, bayan sun mata light off da sai da
safe, sun bar mata dim light shudiya, kukan ta cigaba da yi, mara sauti, da
alama dai Amani Faskari, most at times, finds pleasure and comfort in crying,
tana yi tana yin wannan kukan ne don tausayin Mukhy tana ‘comparing’
rayuwar sa da nata. Sai ta ga cewa, ratar gatan da ta samu da wanda ya samu
mai tsananin girma da fadi ne. bama za’a kwatanta ba. Da gaske kamar
yadda Ummami tace ne Mukhtar yana bukatar kulawar su su duka yanzu,
amma ta yaya? Ta ina zata fara tata kulawar? Ko ta yi kokarin hakan ba zai
bata dama ba, saboda ya rike ta da yawa a ran sa.
Wata zuciyar ta ce da Amani “Ai kema Amani mace ce, ko da ake cewa
kin rako mata! Ki yi tunanin hanyoyin dadadawa mutum, musamman mijin
auren ka, ta yadda zai ji dadi, ya manta da laifukan ka komai girman su, ya
sakar maka fuska da zuciyar sa gabadaya koda baya so, albarkacin kulawar
ka gare shi. Tunda an ce ‘zuciya na son mai kyautata mata’.
Sai ki hada da abubuwan da Balewa ta koyar da ke na kissa mai kyau ta
waya, da kuma naki ‘yan dabarun da bazaki rasa ba, da wadanda Ummami
ma ta koyar da ke na tafiyar da Saraki.
Daddyn ta ya fado mata a rai shima zai iya taimakawa wajen sayo mata
yardarm Mukhy a yanzu, ta tuna tun tafiyar Daddy basu yi way aba sai ta

dauko wayar ta, ta kuwa same shi online a kan whtsp. Sai ta yi masa kira ta
cikin whtsp call.
Yana dagawa ya ce “Tafisu! Me kike yi har yanzu baki yi barci ba?”
Amani ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce “yanzu nake shiri ai Daddy,
so nake in tambaye ka yaya jikin ka? Kuma Yaya Mukhy yana lafiya?”
Dadi mai yawa ya kama Alhaji, y ace “na samu lafiya sosai Uwata,
kuma ina iya mikewa ma yanzu, Mukhtar sai dai in ce Allah ya saka shi a
aljannah y araba shi da iyayen shi lafiya, ko ke da na Haifa iyakar abinda
zaki yi min kenan a rayuwa. Uwa in har baki bi Mukhtar sau da kafa ba wallahi sai Allah yayi mana
hisabi ni da ke, na hore ki da ki bi shi ki nemi aljannar ki babu ruwa na dake
duk ranar da Mukhtar ya kawo min karar ki”.
Amani ta saki kukan da ke cin ran ta, ta ce “Daddy! Kuna ta dora min
abinda yafi karfi na, bayan ba daga gareni bane matsalar yanzu, na riga na
gane kuskure na, shine dai ya ki ya yarda da ni ya kuma saki zuciyar sa da ni.
Hakika na yi kuskure, ina so na gyara in zai bani dama, ka roke shi ya karbi
tuba na ya kuma bani damar gyarawa. Na yi alkawarin canzawa daga yadda
kowa ya sanni dinnan, amma hakan ba zai yiwu ba sai ya yarda da ni”.
“Yardar miji kuma yardar Allah ba! In sha Allahu Mukhtar zai karbi
tuban ki musamman in kin ajiye girman kai. Nima kuma zan taimaka wajen
ganar da shi halayen ki ba laifin ki bane, nawa ne. Musamman a yanzu da
muke da lokaci ni da shi kullum muna tare barci kadai ke raba mu. Ina rokon Allah yayi wa rayuwar ku albarka bakidayan ku, ya kuma
albarkaci auren ku da zuri’ar da zamu yi alfahari da ita mai yawa mai
albarka”.
Ta tambayi Maman ta yace ta yi barci tun dazu.
Sun dade suna hira irin tasu ta Tafisu da Daddyn ta.

Washegarin ranar, a darussan su na yau, ita da Ummami, har yadda
uwargida ke zama a gaban Sarki sai da Ummami ta koyawa Amani, da
yanayin yin magana da Sarakuna cikin kankan da harshe da tausasa furuci,
da hadawa da kirari na kambamawa da nuna soyayya. Wani abun har sai Amani ta rufe ido don kunya. Da gaske Ummami ta
janye hijabin surukuta bakidayan sa. Tasaka na malunta.

***** ***** *****

BAKIN BURKINA FASO

R
anar da su Mukhy suka dawo Diffa daga Burkina Faso ana zabga wani irin
ruwan sama kamar da bakin kwarya har da kankara. Labari ya isko su cewa
Maina ya dawo lafiya tare da jama’ar sa, suna fada wajen Mai Diffa.
Tsakanin Mukhtar da Alhaji bata san wa tafi dokin gani ba, don an ce
da su Alhaji na tafiya yanzu a kan kafafun sa. Wannan ya kusa saka ta
shekawa da gudu don ta cimma Daddy har fadar sarki.
Don haka ta roki Ummami Allah Annabi tana son zuwa masaukin su
Alhaji. Ummami tasa kuyangin ta wato Sugra da Tahira suka raka ta har
inda aka sauki su Alhajin, da gudu ta karasa shiga dakin tana kwarara kiran
sunan Alhaji “Daddy, Daddy na!” Alhajin kuwa ta fara yin tozali da shi yana tsaye a kan kafafun sa yana
waya da Matawalle da ke Katsina, da gudu Amani ta karasa ta rungume shi,
tana kukan farin ciki, da godiyar Allah. Mamma ce ta hau ta da fada tana
cewa ta yi masa a hankali, bashi da kwari, jiya ba yau bace, kuma da da
yanzu ba daya bane a gareta ita kan ta, ta daina wannan haukan da take yi a
jikin Alhaji. Ita matar gida ce yanzu
Ta dube su duk sun murje sun yi gwanin kyau, tsufa duk ya bace, Alhaji
yayi kiba yayi haske, ta hau dariya ta ce “ai kawai Mamma ki ce ‘honeymoon’
kika tafi kai Alhaji Burkina Faso ba jinya ba, wannan irin murjewa haka?”
Jal’an uwar saurin hannu nan da nan ta kai mata duka. Amani ta goce
tana tana ta dariya, Jal’an na fadin “na ga alama kin maida ni sa’ar wasan ki,
ni kike cewa na je honeymoon?” Alhaji ya kammala wayar da yake yi ya rufe
yasa a aljihu, yace “Ya ki nan Uwa ta, kyale ta”, sannan ya hau Jal’an da fada,
“ni tunda nake ban taba ganin Uwa mai saurin dukan Da irin ki ba, to in bata
yi wasa da ke ba da wa zata yi? ‘Yar guda daya ita kenan Allah ya bani bazaki
taya ni tattalin ta ba don ke kina da wasu ko?”
Amani tayi dariya ta ce “a’ah Daddy, daina mata fada haka, kada ta yi
zuciya taki yi min wasu kannen, biyu sun min kadan”. Duk suka fashe da
dariya har Mamman. Alhaji ya ce ta tashi ta koma cikin gida haka, don mai
Martaba ya ce masa an gama ginin su, an saka komai, yau za’a kai ta
bangaren ta kafin wucewar su gida Katsina. Su kuma in sha Allahu gobe zasu
wuce Nigeria.
Tuni jikin Amani ya mutu, ‘yar far’ar data shigo da ita ta koma ciki,
aure da rabuwa da iyaye ba wasa bane ba kuma sauki gare shi ba, damuwa da
kewa suka bayyana a fuskar ta tun ma yanzu kenan, ta soma tunanin irin
kewar su da zata yi tun basu tafin ba, musammamn Alhaji. Zata soma kukan tun kafin gobe ta yi, Ummami ta aiko jakadiya tayi
kiran ta, don haka ta rike hannun Daddy tana hawaye ta rufa tafukan sa a
kan fuskar ta, ta ce “to yanzu Daddy ni da ku sai yaushe?” Kai tsaye Alh.

Usman yace “sai kin haihu zamu zo, in kin min aboki ko sabuwar amarya, ki
sa himma shekara mai zuwa sai ki gan mu gabadaya mun dawo radin suna,
har Balewa zamu dauko miki da su Laure, da Kamilu”.
Kunyar da bai san Amanin shi da ita ba ya gani ta zo ta lullube ta,
harda kare fuska da hannayen ta cikin jin kunyar Daddy yau.
Jakadiya da kuyangin ta suka maida Amani wajen Ummami, aka soma
shirya ta don wucewa nata bangaren, wanda ke can gefen dama na
masarautar Diffa. Da ka wuce sassan Sultan Issouffou Massaoudou.
An kawata ginin a zamanance, hakanan ya tafi da zubin sarautar “Al
Imaraat Al-Diffa” duk da haka. Daga ciki ne aka zuba abubuwa na zamani.

Bangaren Maina Mukhtar Bn Issouffou Massaoudou dake ciki “Al
Imaraat Al Diffa” wato masarautar Diffa, zan iya kwatanta shi da ‘Palace’ din
da babu kamar shi a duk cikin fadin masarautar, in ka cire sassan Sarkin
Diffa. An shirya musu dakunan barci har shidda, da shigifu (faluka) na
alfarma wadanda aka yi wa design da furnitures kala daban-daban, wasu an
yi musu zubin royal parlors, wasu kuwa English parlors ne, da kuma
Francaise. Jal’an na cikin hada kayan ta don gobe da asubah zasu kama hanya,
Mai ya basu driver wanda zai kai su har Katsina sannnan ya dawo, Jal’an ta
ki yarda su yi sallama da Amani ta ce da Ummami a wuce da ita gidan ta
kawai, ita bata son koke-koken banza na Amani, sannan duk wani abunda
uwa zata fada mata ta san Ummami ta gama gaya mata, don haka Ummami
tayi abunda ba’a taba yi ba a masarautar Diffa, inda tace da kan ta zata kai
Amani har dakin ta.

A daren Mukhtar yana tare da Mai, suna cin abinci a kwano guda, yana
masa hirar abubuwan da suka faru dasu a Burkina Faso da yadda aka
magance lalurar Alhaji Usman ta suga da shanyewar jiki ta hanyar maganin
gargajiya ziryan. Mai cikin gamsuwa da taimakon da aminin sa sarkin
Burkina Faso yayi masa ya ce da Mukhy, ya saka an warewa Alhaji Usman
Rakuma hamsin, a fara yi masa kiwon su anan cikin bargar Rakuman sa, in
kuma yana so a kai masa su Nijeriya ne duk zai iya sawa akai masa har can,
sannan ya bashi sittiru irin nashi na alfarma da rawanin sarautar Diffa
akwati guda, har da zoben azurfa mai matukar daraja.
Mukhy ya taya Alhaji godiya sai ya ce “Uwa ta fa? Me aka tanadar
mata? I mean ita me za’a bata?” (yana nufin Mamma Jal’an).
Mai ya ce ya bada ‘bracelet’ na zinare a bata, har Baba Idi ma ya samu
kyautar Rakuma goma daga Mai Diffa, Baba Sahura kuma Sarki yace

Ummami ta ce a nan shiyyar Amani zata zauna tare da ita har sai ta saba da
gidan da mutanen cikin sa koda zata koma Katsina. Duk da dai an bata
wadatattun kuyangi da masu hidimar ta. amma zaman Sahura zai mata
amfani. Mukhtar yana can suna wannan tattaunawar da mahaifin sa, ba tare da
ya sani ba Ummami da Baba Sahura suka kai masa Amani dakin ta, bai san
hakan ba don tun dawowar su bai nemi ganin Amani ba, kuma ko a hanya
basu hadu ba, tunda yayi alkawarin daina kebewa da ita sai ta yi hankali ta
kuma koyi son shi don radin kan ta, ya fahimci sai sun kebe ne take warware
masa lissafi, da haka yake so ya koyawa kan sa hakuri daga shiga lamarin ta
yanzu, ya fuskanci muhimman al’amuran da ke gaban shi na taimakawa
mahaifin sa kan sha’anin mulkin sadon sauke nauyin al’ummah dake kan su.
Don haka yayi gefe da Amani daga ran sa (for the mean time) na yana
so ta koyi son shi domin Allah ba don wasu material attachements, ko nasabar
da take goranta masa ba.
Daga wajen Mai, sai ya wuce suka yi sallama da su Daddy, yana jin
wata irin kewar Alhajin nasa, Mukhy har da hawaye ya yi, ya fiddo wayar shi
ya yi ma Alhaji hoto, yace “Alhaji duk tsayin lokacin nan wai ace bani da
hoton ka a waya ta”. Dariya Hon. Ya yi ya ce to gashinan ka samu, sai ka ajiye
in ka tuno ni ka dauko ka duba. Tunda ni da Uwa bama kama balle take tuna
maka ni, Jal’an da yake ta fini karfin jini ta kwace wannan”. Da kyar suka iya
rabuwa don dare ya fara yi, daga wajen su sai ya wuce sassan Ummami.
Ya same ta tana shirin kwanciya, sai ta ce “Maina tun dazu nake jiran
shigowar ka in kwanta don na gaji da yawa, hidima kan hidima yau na sha ta
har na gode Allah. Alhamdulillah tunda komai ya nabba’a yanzu yadda na
tsara” Mukhtar ya samu kujerar sofa din ta ya zauna, ya ce “ai ga ni yanzu,
Sweet Mum, me zaki bani Ummami na?”
Budar bakin Ummami sai cewa tayi.
“Amanar diya ta Amina mana!”.
“Maina ka sani daga yau zaka soma rayuwar manyantaka, ka kasance
mai hakuri da yi wa matar ka adalci da rangwame a kan duk wani ajizancin
ta, kai ne babba sama da ita, don haka babba juji, bayan kasancewar ta
matar ka ‘yar uwar ka ce, jinin ka ce, da ta fi karfin kowanne uzuri a wurin
ka”.
Haka Ummami ta zaunar da Mukhy wajen awa guda tana masa wata
irin nasiha mai ratsa zuciya, ta gaya masa ta kai masa Amani gidan sa yanzu
haka”.
Ya dan yi shiru na ‘yan sakanni, ya rasa a yanayin da yake ciki, finally,
shi da Amani yanzu! A gida daya, daki daya, kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login