Showing 24001 words to 27000 words out of 41790 words
Chapter 9 - Fyade Book 2 Complete Hausa Novels by Aisha Maman Teddy.pdf
don Na samu labarin Nawaaz na Son ki ba da sai
nayi ƙasaƙasa dake . Tsayawa A'isha tayi tana juya maganan Jimmalo " badon Nawaaz na Son
ki ba da sai nayi ƙasaƙasa dake.” Nawaaz kuma ? Abun da tace kenan tana ɗago idanun ta
wanda nan taga Tuni Jimmalo ta bace da ganin ta . Hummmm ....Wani irin numfashi ta sauke
kamin ta juya tana rage Ƙarfin Gas din zuwa can ƙasa tana Gyara Rigar Aikin ta tare da fitowa
tana nufar part ɗin Hajiya Kubrah . Tun a falon take ganin Sauyi daga Ma'aikatan don kowa bin
ta yake da kallon da ta kasa fahimta . Mtswww Tsaki taja masu tana nufar rest Room inda take
jin magannn Su Hajiya Lubnah wacce bata taɓa Sanin ta ba.
Mom me zaku yi da Wannan wayar bulalan haka ?. Aslaam ne yayi maganan yana kallon su
Mum Kubrah wacce take ta hamdala da zuwan su , don burin ta bai wuce ta tijara A'isha Farida
a gaban kowa ba . Juyawa tayi tana kallon Jimmalo tare da cewa " Oya yanzu a tara mun duka
ma'aikatan Gidan nan mata da maza. Cikin Sauri Jimmalo ta miƙe tana cewa “ Tom An gama
yanzu Ranki Yadaɗe . Aaaryaan kuwa dake gyefe su kallon Bulalan baiyi ba bare har ya
tambayi na menene . Suna cikin Haka ne A'isha Farida ta shigo Resting Room ɗin nata . Cikin
zummar ta don ita bata san mene ake shirya mata ba kai tsaye ta nufi Wurin tana zubewa a
gaban su . Ɗago ido tayi tana kallon Hajiya Kubrah tare da cewa “ Barka da warhaka Hajiya ” .
Ban za Hajiya Kubrah tayi mata sai cabe baki da tayi tana cewa “ Sauke idon ki ƙasa.” Da'alama
baki da kunya da Tarbiyya kina kallo na ido cikin ido ke ga shahararriya ko ” .
Sunkuyar da kan ta Ƙasa A'isha Farida tayi yayin da Aslaam yake kallon Mum yana shirin
magana ,shi kuwa Aaaryaan har a lokacin idon sa baya akan su yanda kasan baiji da ganin
komai . Kiyi Haƙuri Don Allah. Banza Tayi ma A'isha tana kauda kan ta , Nan A'isha ta juya tana
kallon Momy Lubnah wacce tun shigowar A'isha Farida idon ta ke akan ta har a wannan lokacin
. Ganin kallon da take mata yasa A'isha jin tsammm duk ta damu a sanyaye tace "Hajiya Barka
da Zuwa . Kamin ta ji na bakin Hajiya Lubna ce Mom Kubrah tace " Tashi mu je biyo baya na .
A hankali ta miƙe tana bin bayan Hajiya Kubrah wanda Nan Itama Mom Lubnah ta biyo bayan
su . Benene na biyu ta ga sun hau na cikin Gidan . Inda taga Sun nufa can bangaren da idan
mutum ya tsaya zai hango komai na farfajiyar Gidan . Hannun ta Hajiya Kubrah ta danka tare
da nufa da ita Wurin zaf³ Don a tunanin A'isha Kila fadawa da ita Wurin zata yi . A dai dai kariyar
da ya tare suka tsaya ....nan taga Mutane sun fi Mutum Ɗari mata da maza . Wani irin Mari
Hajiya Kubrah ta wanke Fuskar A'isha da shi tana cewa kalli can.! Kalli mutanen nan duka nace
.”
Dafe Kuncin ta A'isha tayi idanun ta na fara fidda zafafan Ƙwallah masu ɗumi da Raɗaɗi . Hajiya
me nayi ?. Uban ki kika yi mun." Alama Hajiya Lubnah tayi da Hannu tana miƙa ma wata Yar
Aikin su Hannu ita kuma tana bata Mick tare da fara magana cikin izza da giyar kuɗi ta fara
cewa " Kunga Wannan Yarinyar da kuke Gani Abun da zamiyi mata a yanzu ya zama
makowacce Yar Aiki izina , Ki tsaya a matsayin ki na yar Aiki kaman yanda muka aje ki kar ki
kuskura Kice kin kyatare iyakar ki . Numfasawa Momyn Nawaaz tayi tana cigaba da cewa "
Wannan Yarinya da kuke Gani Ta shiga ta fita Wurin son Ganin ta tarwatsa mana kan Yaran mu
. Nawaaz da Aslaam , ke har Wa ne da zaki da Yaran mu su so ki wai har suyi yunkurin son
Auren ki , har da Faɗa duka a kanki . Don haka wannan bulalace da zamu zane ta iya fanshe
Haushin da ta bamu zamu zane ta a gaban kowa ne don wanda yake hari da kokarin yin irin
Abun da tayi ya zama masa izina ....Bani Bulalan cewan Hajiya Kubrah tana faɗin Nine zan fara
zane ta nayi mata Hukuncin da ya dace ”.
**
Gyara Ɗaurin Zanin ta take na atampha mai dai dai kudin dan talaka . Daura kallabin ta tayi
tana saka Mayafin ta Cofee brown Wanda ya shiga da Atamphan nata ... Mama Lantana kenan
kun san da da Akwai son Kwalliya Sam bata son kazanta . A'a Hajiya Lantana Kin ganki kuwa?
Kodai Wani bazawarin aka yi mana kamu ?. Inna Hansai tayi maganan tana Murmushi ganin
yanda Mama tayi kiba tayi kyau sosai . Wai kin ganki kuwa Wallahi kullum Dada kiba kike yi
abun ki , Anya zaki shiga adaidaita kuwa.? . Gyara Mayafin Mama Lantana tayi tare da cewa "
To dama a kullum Damuwa ta Shine Aisha Ta , Naga ta girma ta mallaki Hankalin ta yanzu
kuma Alhamdulillah yarinya na ta zama budurwa kin ga mai yayi saura , sauran ƙarike ne. Ehm
Gaskiya fa , Allah Alhamdulillah . Yanzu kuma ina kika nufa ne da Hantsin nan ? Ko zaki leka
Resturent ɗin ki ne .? . A'a Mama Lantana tayi maganan tana Girgiza kai ,kamin ta cigaba da
cewa " Yau na tashi ne ina Ƙwaɗayin son Ganin nayi ido biyu da ɗiyata ,don haka daga nan sai
Gidan Aikatau ɗin A'isha Farida ta . A'a To bari mu tafi tare mana ,Nima na matsu naga Farida
Kusan kwana nawa ?” . A tare suka fito daga Gidan Mama Lantana tana saka mawa Kofa
Ƙwaɗo tare da gangarowa wajen layi .
**
Ɓangaren Su Aaryan kuwa suna zaune ne suka ga Nawaaz ya shigo wurin sam baya ko kallon
Gaban sa . Kai lafiyan kuwa? Aaryaan yayi masa maganan yana bin sa da Kallo . A'isha...! Ya
furta sunan tare da nufar Stairs da Sauri yana wuce su . Ganin hakan yasa Aslaam da Aaryan
Saurin bin bayan sa , Don sai a yanzu suka fahimci Tabbas Su Hajiya Lubnah Da Akwai Abin da
suke shirin yi ne wanda su basu kawo ba . Shi kuwa Nawaaz shigowar sa Gidan ne Ganin
yanda Ma'aikatan suka taru a wuri ɗaya ko wa idon sa na akan bene hawa na farko yasa shi
shima kallon Wurin ,anan ne Yaga Abin da su Mommy ke shirin Aikata ma A'isha Farida .
Wannan yasa shi isowa cikin hanzari .
Ɗaga Bulalan Hajiya Kubrah tayi tana shirin saukewa a jikin Farida Wanda cikin Sauri Aaaryaan
da basu san da zuwan su ba ya riƙe Bulalan ta bayan ta . Mommy meye wannan meye Haka?
Me kuke kokarin yi ne . Yah Aaaryaan Abun da Mommy ke kokarin yi shine dai dai ...! Suka ji
Muryar Yusraht daga Bayan su tana tsaye tare da harɗe Hannayen ta biyu , Idanun ta cikin
Black shadow . Nawaaz ne cikin ɓacin Rai yace " You're Stupid , Baki da Tunani.! Hannun ta
tasa tana sauke bakar gilashin fuskar ta kana ta tako zuwa inda suke ,kaman mai shirin magana
kawai su dai sun ga ta rarumi A'isha ne ta shaƙe ta tana duka . Kuka A'isha Farida tasaka mai
ban tausayi wanda cikin zafin Rai Aslaam ya ƙwace A'isha daga Hannun Yusraht , Shi kuwa
tsananin Haushi sam Nawaaz bai San lokacin da ya koɗa ma fuskar ta wani irin Mari ba ,
Wanda lokaci guda shatin yatsunsa suka bayyana a Kuncinta .
Wurin ne da mai'akatan yayi tajin² na tsoro da mamakin Wannan Al'amari ,ita ko Yaya Maryamu
farin ciki tayi Ganin yanda Nawaaz ya wanke fuskar Yusrah da Mari . Innalillahi wainna ilaihir
raji'un shine kalmar da Hajiya Lubna tayi . Nawaaz yau kaine ka Mari Ƙanwar ka yar uwar ka ta
jini akan bare , Wacce baka san Asalin ta ba , talaka kaskantacciya yar Aikin ku ?. And SO
What mom? . Ina Son A'isha kuma na shirya na Rabu da kowa don na zauna da ita ,ita kadai a
rayuwa ta .
Tafa Hannu Hajiya Kubrah ta hauyi na salallami kana tace “ Wannan Abin da suke yi yaran nan
akan wannan karfan ba haka kurum bane , i have Already told you that, Yanzu kin gani da
idanun ki ko? Sihiri ne . Bayan Aslaam A'isha Tayi tana cigaba da Kukan ta cikin tsananin tashin
hankali,tun da take bata taɓa Ganin musiba irin na yau ba a rayuwar ta . Ba kuma ta taba yarda
Naawaaz Son ta yake ba , ta dauki hakan a matsayin suna so ne suyi lalata da ita kaman yanda
Aaaryaan yayi mata cin mutunci .
Juyawa Hajiya Kubrah tayi a fusace tana cewa " Kaima Aslaam naji naka Labarin cewa kana
Son A'isha Farida wanda duka baku isa ba ,ko don kin isan shine zaku tsaya har ku mun
katanga na kasa dukan A'isha ?. To bani Wuri kamin yanzu Ranka ya ɓaci.? Kallon ta Aslaam
ya tsaya yi yana ƙoƙarin bata hakuri ta fizgo A'isha dake bayan shi tana Wurgar da ita gyefe . A
cikin ku naga Wanda zai hanani dukan A'isha Farida.! Juyawa tayi tana kallon Aaaryan tare da
cewa " Bani Bulalan Hannun ka? . Kasa miƙa mata Bulalan yayi ya tsaya yana kallon ta ....oh ko
kaima Son ta kake yi?. Shiru yayi yana kallon Hajiya Kubrah , kamin ta kuma cewa cike da
Tsawa " Idan son ta kai ma kake yi to ka riƙe Bulalan ku gani ba zan bige ta ba A wurin nan.
Kallon A'isha Farida yayi suna yin ido Hudu gaba ɗaya ta gama ficewa a hayyacin ta , hular kan
ta sun wurgar mata , Ga kan ta babu kitso gaba ɗaya gashin ta ya gama rufe mata fuska .
Girgiza masa kai tayi tana narke masa Alamun kar ya bata Bulalan ,Amma kawai sai yaji Mom
ta fixge Bulalan A hannun sa tana dagawa tare da shirin Sauke Bulalan a jikin A'isha .
Kubrah Don Allah idan ke kin cika cikakkiyar mara mutunci ki bigi A'isha Farida bance ki dakata
ba don Uwar ki da Ubanki .! Wani irin Yamm Wurin yayi jin wata murya ta daban . Gaba daya
hankula ya dawo kan Mama Lantana da Inna Hansai wanda shigowar su kenan suka ga
Wannan Abun dake faruwa . A'isha ne tayi saurin furta " Maaama cikin tsananin kuka tana nufar
wurin tare da shirin fadawa don ta isa inda take . A'isha Dakata .! Muryar Mama ya kuma katse
ta , Wanda Hajiya Lubna mutuwar tsaye tayi.... Ita ko Kubrah Wasu irin ƙwallah ne na tashin
hankali ya ciko Ƙwarmin idanun ta . Idan kin haifu ki taba mun Ɗiyata , na rantse ba zaki zaune
Bulalan ba sai na shigar Miki biyu masu kyau , idan ke daya kike yi mata kenan . Cikin tashin
Hankali Hajiya Kubrah ta kalli sojojin dake a kasar tana cewa " ku daura kun bindiga a kan ta ku
har be mun ita yanzu nan ....! Wani irin ihu A'isha Farida ta saki tare da nufar Varrier ɗin tana
Faɗawa b tare da tayi tunanin a ina zata sauka ba ......Momyn Nawaaz ne tayi saurin cewa "
Inalillalahi wai'inna ilaihir raji'un......"
#MAMANTEDDY
[5/21, 8:50 AM] my number: *️FƳAƊE...!️*
#Love
#Sympathetic
#Romantic&
#Erotic
#Story.
***21***
*Don darajar Allah kar ki karanta mun littafi idan kin san baki biyani ba*
*Littafin fƴaɗe na kuɗi ne ban yarda Wanda bai biya ba ya karanta Don Allah...Masu buƙatar
book din Regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special ₦1500 via 6037312299 Mohammed
A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.*
WRITTEN BY:MAMAN_TEDDY
Bin sa Da kallo Naawaaz yayi ganin yanda ya ƙara gudun moton ma da yazo Dab dashi Alamun
baya buƙatar wata magana tsakanin su . Shiru Naawaaz yayi a zuciyar sa yana Tunanin Ai Dole
Aaaryaan Kishi yake taya Momyn shi Kubrah . Yana Wannan tunanin ne Moton Nawaaz yazo
Dab da shi yana cewa " Ya dai shigo Mu wuce da Sauri . Da kuma Sauri Nawaaz ya nufi moton
yana Shigewa tare da cewa " Yanzu mu nufi Hanyar da masu Adaidaita suke ne , kila mu same
su anan . Aslaam ne ya kalli Naawaaz yana cewa " Eh Hakan kuwa ya kamata . Bayan sunyi
nisa ne suka hangi moton Aaaryaan can da yayi parking ya mararraba ko zaman mai yake yi
Basu sani ba dai . Aslaam ne yace " Bari mu nufi Gurin Aaaryaan muji shi mafitar sa ....yana
ƙoƙarin Reverse ne Naawaaz yayi saurin dakatar dashi da cewa " Aiko Lallai Kana SO ya sauke
Haushin sa akan ka ne , don ko mene Aaryaan yayi maka kaga ai kai ka ja ma kanka .
Cikin Rashin fahimtar magannn Nawaaz din Aslaam yace " Kaman ya kenan ?. Au Kai baka
gane ba ?, To kishin Momy Kubrah yake yi , Tun da shima a iya sani na bai taɓa Sanin Daddy
yana da Wata matan bayan Mommy ba . Shiru Aslaam yayi yana shan Jinin jikin shi kamin yace
" Duka Wannan maganan ma da muke is waste of time , mu tafi kawai lokaci na tafiya kar mu ki
yin nasarar ganin su . Idan A'isha ta tafi ban san ina zan ganta ba , kuma hakan zai jawo mun
naƙasu ga Rayuwa ta . Saboda ina mahaukacin Son ta.... Wani irin Kallo Naawaaz ya yi masa
lokaci guda Abin na neman zama masu rikici . Allah ko to ai bakai kadai ke son ta ba Nima Ai
Son ta na keyi...! Wani irin kallo Aslaam shima yayi ma Nawaaz sai kuma ya numfasa ba tare
da yace komai ba ya cigaba da Driving ɗin bai kuma kallon Naawaaz ba .
**
Ɓangaren Aaryaan kuwa Securities din layin manya mutum uku ya kira , Wanda yana cikin
moton shi suka iso... fitowa yayi don dama tun a waya da ya kira su ya faɗa masu aikin da zasu
yi masa shine cire duk wasu CCTV Camera na tun daga Farkon layin har zuwa karshen ta . Su
bincika masa abun Hawan da suka hau da kuma Numbern Abin Hawan . Koda suka isa Nan
take suka fara Aikin su yana tsaye yana kallon komai , da mai amfani da na'uran Computer
shima yana nashi ....Minti goma suka Gano adaidaita ne yazo wucewa daga Wajen layin
,Numbern Adaidaitan suka ɗauka kamin su fara bincike . A takaice Awa biyu tsakani aka Gano
Inda Mai Adaidaitan yake , Yayin da Sam Aaaryaan bai tsaya Wani dogon zance ba yabi bayan
mai Adaidaitan.
**
Ɓangaren Hajiya Kubrah kuwa yi tayi tamkar zata zauce , cikin Rufewar kai da kullewar
Ƙwaƙwalwa ta daga Waya tana sanar da Daddy duk Abin da ya faru sai dai bata faɗa masa
Maganan ta Da Aaryaann ya ji ba . Wani irin kabbara Daddy yayi da Hamdala yana godiya ga
Ubangiji . Tun da Hadiza tana cikin Garin Abuja inshallah neman ta ba zai gagare niba yanzu
gani Nan dawowa . Mutuwan Tsaye Kubrah tayi tasa kasa datse kirar sai shi da kan shi yayi
hakan . Tana tsaye ne kirar Hajiya Rahmatu ya shigo mata inda cikin hanzari ta daga tana cewa
" Rahmatu komai ya ɓaci . Aaaryan duka yaji maganan da nake faɗa Miki . Kuma yanzu Alh
Abdu Kareem wani irin farin ciki yake yi dana faɗa masa Ganin Hadiza da mukayi , farin cikin da
rabon da yayi tun ranan da ya Fahimci Hadiza na dauke da juna biyun shi wato tana dauke da
cikin Aaaryaan , A yau wannan daukin da farin cikin na gani . Rahmatu Zan iya komai kar a bari
Hadiza ta dawo Gidan nan , daga zarar ta dawo duka wani shiri Na ya lalace . Na tsani matar
nan A rayuwa ta . Ki kashe ko nawa ne kije wurin wannan bokon da shi yayi aikin kar ta ta shiga
duniya ,a yanzu ma Ya kuma kar fa suyi nasarar Ganin ta . Yanzu kuwa Hajiya Kubrah ai kin
san shi aikin shi da kin fada masa da Kinga biyan buƙata yanzu zan nufa jejin silaja .
**
Zama A'isha Farida tayi tana numfasawa tare da kallon Inna Hansai da kuma Mama Lantana .
Mama Ban gane ba wai da Gaske Ke matar Daddy Marshal Abdu ne , mahaifin Aaaryaan?.
Rintse Ido Mama Lantana tayi kamin tace " A'isha Haka ne , Amma bana Son Wannan
maganan da kike yi .! Yanzu a gobe zamu bar Garin nan don bana son ido biyu da kowa na
cikin wannan a hali ko dangi . Mama me yasa to?. Kawai saboda Bayyanar su gare Ni ,
Bayyanar wani tsohon sirri ne wanda ya shafi Ni dake , Sannan bana Son haka ta faru . Cikin
Rashin Fahimtar zancen na mama Lantana A'isha Farida ta kuma cewa " Amma Mama ina so ki
Zauna tare da mijin ki ne yasa ke bakya so .? Shiru Mama Lantana tayi kamin tace " Kina SO ki
ga bacin Raina kenan?. Girgiza Kai A'isha tayi cikin sauri Alamun A'a .Tom tashi ki dauki buta
maza kiyi Alwala sai kizo kiyi Sallah , Sannan ki ci Abinci .
To Mama Amma Aaryaan Ai ba Ɗan Hajiya Kubrah bane? . Sakin cazbihan hannun Mama
Lantana tayi da Sauri tana kallon A'isha Farida tare da