Showing 3001 words to 6000 words out of 23627 words
Chapter 2 - MAI DAKI (4) Book Complete By Hafsat C Sodangi.docx
sakar zuci.
Ni kaina.nasan komawata gidan Ishak ba mai
yiwuwa ba ne, 1dan ba dole ya zama mun ba.
Haka an a yanzu da na samu aka lallaba
Babana ya hakura ya bar ni na komna
Makaranta wani abu yazo yayi sanadin da
damar ta subuce min ba zan so ba.
Hakan kuwa yana nufin da Babana ya ji
labarin zuwan Ishak, to zai dauki mataki, ne
kawai a kai.
Ilai ko ba a cika sati guda ba wannan karon
sai gashi ya dawo, abinda ya tabbatar mun da
maganar Umma da tace fuskata ya gani.
Na shiga dakin Umma tana kara gyaran
gadonta na ce, "Umma Ishak ne yazo.
Ta ce, To menene kuma nawa a ciki? Na ce,
eh dama na zo ne na gaya miki."
Ba ta ce mun komai ba, na juyo na kamo
hanyar fita waje. Yana hango ni ya saki
mumushi.
21
Al'amarin Ishak har mamaki yake bani,
idan na tuna irin zaman da muka yi da shia
matsayin mata da miji.
Uhum, wasu mazan ma dai sai a bar su,
basa taba sanin darajar matarsu a lokacin da
take zaune a gidansu har suyi tunanin ya
kamata su mutuntata don ta ji dadi.
Har sai ta subuce musu kuma sai su zo suna
ta faman kame-kame. Muna gama gaisawa na
ce mishi amma dai ya kamata ka san wannan
zuwan da ka ke yi ba shi da ka'ida.
Don kuwa idan har Babana ya ji labari ka
san ba zai ji dadi ba."
Ya dan yi murmushi har sautin murmushin
nashi ya bayyana, ya ce, "Eh ai babu wata
matsala, don kuwa Kawu ne zai zo jibi a kan
maganar saboda a yi komai nan ba da dadewa
ba.
Ba karamin bugun zuciyata maganar Ishak
tayi ba. Na dago kaina cikin mamaki da niyyar
nayi mishi magana.
Sai kawai yaci gaba.
22
"Kada ki samu damuwar komai, don kuwa
na dauka wannan auren da ki ka yi wata gada
ce ta halal ta mun ke don ki sake zama matata.
Ina so ki san har a yanzu ina sonki, na
rantse miki kuma na kasa yin wani auren ne
saboda kullum addu'ata bata wuce na ki dawo
gidana mu ci gaba da zamanmu ba cikin jin
dadi da kwanciyar hankali.
Kuma kema nasan kina sona, natsala ce dai
muka samu tare kuma da kaddara da
tsautsayi."
Takaicin Ishak ya kama ni, naji kamar na
shake shi na gana mishi azaba ko na samu na
huce,
Tun da ya fara magana shi nake kallo har
yayi shiru sannan nace ba addu'arka ce ta
karbu aurena da Ahmad ya mutu ba.
Don kuwa ba sakina yayi bisa son rai da
wulakanci ba, irin yadda kayi mun.
Sannan ban taba sanin cewa tunaninka zai
baka ni din zan kashe aure don na dawo
gidanka ba.
23
Ina so ka san babu tsautsayin da zai sani yin
hakan a yanzu. Nayi wani auren naji yadda ake
ji.
Na shaki iskar 'yanci da mutunci. Mijina ya
kula dani ya bani lokacinsa bai taba fita ya bar
ni ya dawo mun da tsakiyar dare ba.
Wani abu bai taba hada ni da shi ya zage ni
ya zagi talaucin iyayena ba. Ban taba yi mishi
wani kuskure ya wulakantani ya gana min
azabar duka irin yadda ka rinka yi mun a
gidanka ba.
Amma kai fa duk wadannan abubuwan a
gidanka suka same ni. Kana ganin kenan zan
sake dawowa gidanka da har ka ke karambanin
turo magabatanka gidanmu?
Jikinshi a sanyaye ya ce, "Haba Hauwa'u,
ina ce duk wadannan abubuwan sun faru ne
bisa kuskure kuma sun riga sun wuce.
Na ce, "Eh na sani sun riga sun wuce, amma
wucewar ba yana nufin zan sake tsoma kaina
cikin fitina ba ne.
Kayi hakuri amma ni har na fara shirye
shiryen komawa Makaranta."
24
Ya ce, "To amma Hauwa'u ai nayi miki
alkawura da yawa a baya da nake burin ganin
na cika miki su a ciki har da komawarki
Makaranta.
Na kuma yarda da kura-kuraina, na kuma
yarda zan gyara.
Na ce, Eh babu damuwa idan ka gyara nan
gaba, amma ni kam kayi hakuri.
Kaje kayi aurenka don kaima ka saukakewa
kanka damuwa."
Ishak bai yarda da abinda na gaya mishi ba,
don kuwa sai da ya turo magabatanshi.
Ba karamin godiya nayi wa Allah ba da ya
taimake ni na yiwa Umma bayanin komai a
ranar da Ishak din yazo.
Babana kuma ya gaya mishi shi a yanzu ba
zai tursasa mun auren kowa ba.
Idan mun sasanta a tsakaninmu to shi kenan
shi ba shi da matsala duk wanda aka yi.
Ban kara tsayawa sauraron Ishak ba idan
yazo, yazo har ya gaji. Kullum kuma yazo ya
aiko a kira ni hakuri nake ba shi na ce mishi ba
zan samu fita ba.
25
To ya dan kwana biyu yanzu bai zo ba.
Wani lokaci sai na ce ina ma da Ahmad ne ya
dawo?
Zan iya hakura na juya mishi baya haka
kuwa duk da matsalar mahaifiyarshi da
ya' yanshi? Zuciyata har yanzu shi take so.
Dan saukin abin ma shi ne, na hakura abin
kuma ya rage damuna.
Na kara fuskantar al'amuran karatuna
gadan-gadan har muka fara zana jarrabawa ban
fuskanci wani tsanani mai yawa ba.
Sakamako ya fito nayi nasara sosai, don a
yawan shekarun da nayi bana karatu ban yi
zaton zan samu result mai kyau haka ba.
WAEC na samu credit biyar, sai NECO na
samu shidda kuma a darussa masu
muhimmanci.
Kasancewar na ubuta har da JAMB sai
abin yazo mun kusan lokaci daya, don kuwa
JAMB din ma babu laifi an bani (Education
English).
Ranar murna a wajen Babana ba a cewa
komai, to ballantana kuma Yaya Auwalu.
26
Yana fama da asibitin matarshi saboda
laulayin da take yi, amma ba ya gajiya da tawa
dawainiyar.
Kullum kuma muka dan zauna zai gaya
mun ban da yawan yin kawaye saboda yadda
ake maganar 'yanmatan Jami'a.
Watanni uku ne kawai bayan nan sai gashi
har mun yi registration mun fara halattar aj
don daukar darasi.
Da iyakacin karfina na dage nake karatuna
saboda a yanzu shi ne abinda na tasa a gaba
don ganin bukatata ta biya.
A cikin sati guda da fara zuwana kuwa
tsakanina da kowa a ajin to gaisuwa ce ta
mutunci.
Ban ma ba da fuska ba saboda irin suturun
da nake amfani da su na mutunci wanda yasa
ake zaton ina da aure.
Na yarda da gargadin da Yaya Auwalu yayi
min, don kuwa a yan kwanakin fara zuwa
Makaranta da nayi naga yadda wasu 'yanmatan
suke ballagazar da kawunansu.
Wai su ga hadaddu wayayyu, kaga budurwa
takai ta kawo amma tana yawo da 'yar
27
fingilalliyar riga da matsattsen siket har ana
ganin shatan pant dinta.
Sannan babu gyale na mutunci ko hijabi,
kuma wai yar Musulma abin abin bakin ciki.
Yaya Auwalu dogayen hijabaí ya dunka
mun masu kyau har guda shida kala daban-
daban, ya ce gudunmawarshi kenan.
Ganin irin abinda ake yi na holewa ga
wadansu ni kuwa ban yi wannan wayewar ba
kuma bana fata sai akwai nake wucewa library
idan an yi break ko kuma na shiga cafë idan ina
da assignment din da zan yi.
A gida kuwa har Umma sai ta kara tattalina.
A duk sanda na dawo zan zo na samu abincina
kammale cikin food flask da dan abin sha.
Haka ma Baba Ladi duk da sanin da tayi
ana ajiye mun abinci itama duk abinda taci sai
ta ajiye mun nawa.
A yanzu bani da matsalar komai tafiyar da
al'amurana kuma nake yi cikin jin dadi, duk
wani nauyi ya sauka a Zuciyata.
Ban taba tuna Abulkhairi naji fargaba ko
rashin dadi ba don nasan yana hannu mai kyau.
28
Yaya mutuniyar kirki ce da ta san girma da
mutuncin kowa, da ace haka kaninta yake, to
da al'amarinshi yayi dadi.
Ina zaune na tasa abincin da aka aiko mun
daga gidan Yaya Auwalu a gaba zan fara ci.
Itama Samahatu kullum sai ta zubo min
abinci na daban duk da na gida da take aikowa
a babban food flask wanda wani lokaci ko
abincin dare ba ma yi saboda yawanshi.
Sannan ga laulayin ciki da ya tasata a gaba,
hakan ne yasa idan na dawo na samu nata shi
nake ci.
Idan kuma naci shi to shi kenan na koshi
saboda ni dama ba mai cin abinci ba ce.
Baba Ladi ta leka gefen gadonta ta jawo
kwano lafiyayyen kwadon zogale ne a ciki, ta
miko mun.
Na dan yi murmushi saboda nasan duk tana
yi ne don ta birge ni, ta nuna mun tana sona.
Hakan kuma kan sa naji dadi a raina.
Na ce, Baba Ladi Babanmu yana kawo miki
zogale ne saboda matsalarki.
Likita ne ya ce ki rinka cin zogale sosai
saboda yana magani, amma idan aka kawo
29
miki maimakon ki zauna ki ci ya ishe ki sai ki
raba biyu ki ajiye mun rabi, ni din da lafiyata
kalau.
Ta ce, eh nasan lafiyarki kalau ci ki kara
lafiyar 'yar nan ai ni tausayinki nake ji ke da ki
ka saba cin dadi a gidan mazan da ki ka aura.
Ke dai ina miki addu'a Allah ya kawo miki
wanda za ki huta fiye da su. Nayi dariya na ce
"Haba Baba Ladi, ai wannan addu'ar taki bata
yi ba.
Cewa za ki yi Allah ya kawo mun wanda
zan zauna lafiya a gidan shi zama na din-din-
din wanda zai yi hakuri da halayyata da
dabi' una masu kyau da marasa kyau.
Ni a ganina wannan shi ne mafi alkairi a
gare ni.
Na mike gidan Yaya Auwalu na nufa don
duba matarshi. Ina rike da kwanon da Umma
ta bani na kunun tsamiya da ta dama mata
saboda ganewan da tayi bata cin abinci ya
zauna mata.
Nayi sallama a bakin kofar na shiga. A
kwance na sameta shame-shamc a kasa.
30
Cikin sauri ta gyara zama tana daura
dankwalinta, na ajiye mata kunun ina gaya
mata sakon Umma tana dan murmushi cikin jin
nauyi.
Ban saurare ta ba kicin dinta na shiga na
dauko kofi na tsiyaya mata na mika mata ta
kar6a.
A raina ina tunanin mu'amalla mai sauki
irin wacce ke tsakanin matar Yaya Auwalu da
sirikarta Umma.
Ban jima a gidan ba na fito bayan na gaya
mata zan zo gobe nayi mata kitso, saboda kanta
dake tsefe.
Ina tafe ina tunanin rayuwar da nayi a
gidan Ahmad da mahaifiyarshi, da kuma shi
kanshi.
Da mahaifiyarshi dai kowa ya sani babu
sauki amma da shi wata irin rayuwa da
kowacce mata zata yi mafarkin samu.
Yanzu kuma ko ina zan fada sai Allah, don
kuwa a yanzu ko kwanakin baya da ya kira ni
gaisuwa kawai muka yi ya dan tambaye ni
abubuwa.
31
Saboda jin labarin komawata Makaranta da
yay1, da alama shima ya hakura. Kirana kawai
yake yi saboda mutunci.
Nasiba ita ce kadai yarinyar da nake
mu'amalla da ita a makaranta.
Jininmu ya hadu ne ba don halinmu yazo
daya ba. Nasiba 'yar gaye ce sosai
Irin yan gayun nan da basa kunyar
gayensu. Wadanda yafa gyale ko saka hijabi
bai dame su ba, yar gata ce sosai daga irin
Suturun da take sakawa na fahimci hakan.
Duk da irin bambancin da ke tsakaninmu
muna iin dadin mu'amallar mu don kuwa tana
da matukar kamun kai ba kadan ba.
Mu'amalla ta da ita ya sanya ni na kara jin
dadin karatuna, don kuwa komai tare muke yin
shi.
Amma har da irin sabon da muka yi da juna
ban san komai game da ita ba, kamar yadda ita
ma bata san komai game da ni ba.
Ta dai tambaye ni yarana na ce daya, don
haka ita kallon matar aure take yi mun.
32
Karatu sosai muke yi ba tare da wani wasa
ko kuma yaudarar kai ba, har aka zo rubuta
Jarrabawa.
Bayan yan gwaje-gwajen da aka yi mana
wanda tun daga nan muka fara ganin irin
kokarin mu da kuma ta inda zamu yi gyara.
A komnai kusan muna tafe ne da Nasiba sai
dai a wasu darussan ta fini haka nima a wasu
na fita.
A duk inda dayanmu kuma yafi daya, to a
nan zai rinka koyar da dan uwanshi.
Hakan yayi matukar taimakon mu ba kadan
ba.
Ranar da zamu fara jarrabawa kuwa har
Babana sai da na gayawa, ya taya ni da addu'a
ya kuma jaddada mun a kullum shi din cikin yi
mun addu'a yake.
Zai kuma kara a kan ta da. Na ce to na gode
Baba. Cikin sauki muka yi jarrabawarmu muka
gama ba tare da mun fuskanci wani tsanani ba.
An kuma ce wai Juma'a mai kyau daga
Laraba ake ganeta.
33
Muna rike da hannun juna ranar da muka yi
hutu zamu rabu, Nasiba ta ce amma dai kin san
ba ki da kirki ko?
Cikin murmushi na ce,"Na sani mana
Nasiba."
Ta yamutsa fuska tana kallona, ta ce
"Amsar da za ki ba ni kenan don wulakanci?
Na ce, "To ai kin ga ke ce ki ka fada kin ga
kuma na san ba za ki yi mun karya ba.
Ta ce, "To tunda muke da ke ba ki taba
tunanin ya kamata ki tambaye ni ta inda
gidanmu yake ba, ballantana in saka ran wata
rana zan ganki.
Kullum haduwar Makaranta rabuwar
Makaranta. Ni kuwa a yanzu din nan da nake
ko da ban taba zuwa gidanku ba har kalan
fentin shi na sani. Don kuwa komai yana cikin
zuciyata."
Nan take naji kunyar Nasiba ta kama ni, don
kuwa nasan gaskiyarta kawai ta fada.
Na saka hannu a cikin jakata na dauko biro
da 'yar takarda na ce "Kiyi hakuri Nasiba nayi
kuskure, amma rubuta mun a nan."
34
Ta watso mun wata zabgegiyar harara
sannan tayi tafiyarta ta bar ni a tsaye a wurin.
Sai da nayi wanka naci abinci na wartsake
gajiyata sannan na dauko wayata na rubutawa
Nasiba don gajeren text message.
Kiyi hakuri kawata ban kyauta ba, amma ki
saurare ni zan ba ki surprise.
Miss you so much.
Ranar da aka wayi gari satinmu biyu da
hutu ranar Samahatu ta haifo santalelen yaro.
Ina rike da yaron a hannuna bayan an
sallamo su daga asibiti sun dawo gida bakina
ya ki ufuwa saboda murna.
Shi kuwa Yaya Auwalu sai kaiwa da
kawowa yake yi. Iyayen Samahatu sun so su
dauketa ba a yardan musu ba.
Don haka kullum Inna Hadiza ce mai zuwa.
tayi mata wanka ta yi wa jariri.
Kwanaki uku da yin haihuwar sai ga
Nasiba. Duk da na sanar da ita maganar
haihuwan ban yi zaton zata zo ba.
Rungume juna muka yi cikin murna. Wurin
Umma na fara kaita suka gaisa, na kaita wurin
35
Baba Ladi, sannan na shigar da ita asalin
dakina.
Na ajiye mata abubuwan ci da na sha muna
yar hira tana ta dan kalle-kallenta sannan ta
kalle ni cikin mamaki.
"Yanzun nan Hauwa'u dama ba ki da aure
amma ba ki taba gaya mun ba? Gaskiya ke ba
mutuniyar kirki ba ce."
Na ce, "To kiyi hakuri a yadda dama naso
ki gane kenan. Tayi tsaki ta dauki kunun
ayarta ta fara sha.
Muna 'yar hirarmu tana ciye-ciyenta na
abubuwan da na ajiye mata. Ta ce, "Amma
gaskiya kina da zurfin ciki, koda yake ba zan
ga laifinki ba.
Don kuwa mutanen yanzu ba abin yarda ba
ne, balle kaje kana bude musu sirrinka.
Bayani na yi wa Nasiba na komai game da
ni, zamana a gidan Ishak da kuma Ahmad da
yadda aka yi auren ya mutu.
Tayi shiru jimawa kadan ta ce "Gaskiya
maganin matsalar kenan komawan da ki ka yi
makaranta. Sai ayi ta addu'ar samun salihin
miji a gaba da za ki yi zamanki lafiya da shi."
36
Na ce,"Addu'ata kenan nima."
Zukekiyar riga mai kyau da sabulai hadi da
turmin atamfa 'yar Ingila Nasiba ta bai wa
Samahatu da na kaita ta yi mata barka.
Umma ma tsaraba tayi mata sosai, dangin
kuka, kubewa busassa, daddawa da su citta.
Sannan ta kulle mata yajin daddawan
maijego duka ta ce, ta kai wa mahaifiyarta ta
kuma yi murna sosai.
Babu wanda bai yaba da nutsuwar Nasiba
ba a gidanmu. Munyi shagalin suna sosai da
sosai, yaro ya ci suna Abdurrahman saboda
darajar sunan. Hutunmu ya kare cikin
kankanin lokaci saboda dadin shi da múka ji.
Shiri sosai na sake yi don himmar fuskantar
zangon karatu na biyu, wato second semester a
makaranta.
Duk wani abu da nasan zai taimake ni,
kuma a tanade shi. Sammako nayi saboda
dokin da nake yi na tafi makaranta, duk da
sanin da nayi cewa a yau din rana ce da aka
bude mafi akasarin dalibai ba su zo ba.
Haka nan Malaman ma wasu ba a satin suke
fara shiga aji ba Kan gurin da na saba zama ni
37
da Nasiba naje na karkabe mana na zauna tare
da jawo wani littafi na turanci don ya dan debe
min kewa suna (Jane Eyre) ina karantawa.
Lokaci ya tafi ba kadan ba jifa-jifa kuma ina
dagowa don amsa gaisuwar abokan karatuna
da suke ta shigowa ajin.
Na kalli agogon da ke daure a hannuna don
ganin lokaci saboda ganewan da nayi lokaci ya
tafi.
Karfe takwas ne har da rabi amma Nasiba
bata zo ba. Na dauko wayata kenan da nufin na
kirata sai ga Mallam ya shigo.
Mallam Zakariyya shi ne Malamin da yake
daukanmu GNS wacce madda ce da ta zama
wajibi akan kowanne dalibi na makarantar.
Koda kuwa me ka ke karantawa sanin halin shi
da nayi ne yasa na mayar da wayar na ajiye. Ya
isa gaban allo yana rike da marker a hannunshi
ya rubuta test a jikin allon.
Gabana yayi mummunan faduwa na juya
don kallon sauran 'yan tsirarun ajin suma sai
zazzare idanu suke yi alamar bani kadai ba ce a
cikin rudani.
38
Sai dai babu wanda ya tanka. Ya rubuta
tambayoyin shi yaja gefe yana nade da
hannayenshi a kirji yayin da yake binmu da
kallo.