Showing 21001 words to 23627 words out of 23627 words

Chapter 8 - MAI DAKI (4) Book Complete By Hafsat C Sodangi.docx

22 Jan 2026

25

/>
iyakacin karfina na yi ihu tare da salati.

Wuf nayi zan mike saboda firgitan da nayi da

radadin kunun a jikina, santsi ya debe ni na sake

zamewa na fadi warwas a kasa.

Gudun da Mallam yayi wajen rike ni bai sa

hakan ya taimake ni ba. Illahirin komai nawa sai

da ya dauke ya sake dawWowa saboda buguwar da

nayi,

Take ya dauko ruwan sanyin wurin ya sheka

mun ya kama kici-kicin tube min rigar da ke

jikina ta atamfa wacce Allah ya ufa asiri ta r

age karfin kunan da nayi.

123

"Sannu Hauwa'u." Ya fada a lokacin da ya

gama zame rigar a jikina. A gefen hannuna na

dama kunan ya tsaya kuma nan ma Allah ya

takaita babu yawa.

"Kiyi hakuri." Abinda ya fara gaya mun

kenan, sai dai kafin na ce wani abu ji nayi

tamfar ina fitsari saboda irin wannan abin yasa

take gabana ya fadi.

Ba sai an tsaya yi mun bayani ba, jini ne.

kukan da nake yi zatonshi na kunan da nayi ne,

don haka hakuri yake ta bani.

Sai dai ban ce mishi komai ba sai da yaga ya

dan fara gangarowa gefen tiles din da nake

zaune. Mikewa yayi yasa hannu ya ciccibe ni

cikin sauri yayi waje.

Inda yake ajiye mota bakin shi kuwa fadin

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un yake yi.

Tun kafin mu karasa asibitin na fahimci

wannan karon da bambanci, don kuwa ciwo ne

mai tsanani ya kama ni.

Ciwon ciki da bayana tamfar zai karye. Muna

isa aka tabbatar mana haihuwa zan yi. Mallam

ya kalli Likitan ya ce, haihuwa watan cikin

bakwai ne fa?

124

Ya ce, eh babu damuwa in dai da ranshi shi

kenan zamu san yanda muka yi da shi. Cikin

ikon Allah da taimakon Likitoci na haifi da wata

bakwai.

Yana fitowa kuwa ya fara zandara ihu alamar

da ke nuna yazo cikin koshin lafiya. Nose din da

ke wurin ta nuno mun shi na kalle shi hawaye na

bin kumatuna.

Ta dan yi murmushi ta ce, kada kankantarshi

ta dame ki, muhimmin abu shi ne lafiyar shi

kalau.

A ka gama kintsa ni tare da canza mun daki.

A lokacin ne kuma Mallam shima ya shigo. Ya

kama hannuna ya rike yana dan matsawa.

"Kiyi hakuri Hauwa'u. Na daga ido na kalle

shi take na hango fadawar da yayi ta farat daya

na dan yi murmushi don ganin kankalinshi ya

dan kwanta.

Na ce mishi, karfe nawa ne yanzu? Ya daga

hannunshi da agogo ke daure ya ce, biyu da

kwata, na ce har yanzu ba ka ci komai ba ko? Ya

ce, na ci zan yi magana ya ce, rufe idonki kiyi

barci ki huta.

Ban farka ba sai wajen bakwai na safiya.

Samahatu da Baba Ladi na gani a zaune. Nayi

125

murmushi muka gaisa suna tambayata jiki, na ce

da sauki.

Ban dade da farkawa ba Mallam ya shigo da

Baba Ladi sannan ya matso kusa dani yana

tambayata abinda zan ci.

Na ce, Haba 'yallabai ka bari su Samahatu za

su bani. Ya dan yi murmushi yana kara kallon

hannuna da kunan kenan ya dan tattashi, ya juya

ya fita.

Wata Nos ta dawo tare dashi da kayan

dressing na zauna a bakin gadon ta daye kunan

sannan tayi mun dressing.

A asibiti muka bar yaron saboda umurnin

Likita na a saka shi a kwalba (incubator) saboda

ba shi da girma sosai ga kuma rashin kwari.

Sai dai da gargadin kullum za a zo a tatsi

nono wanda za a rinka ba shi safe da yamma. Na

dawo gida sai dai babu Amina a ciki abinda na

lura kenan ban tambayi Mallam ita ba, shima

kuma bai ce mun komai ba.

Sai dai ya roki Umma da ta ba shi wacce zata

zauna da ni mai dan shekaru, don haka Inna

Hadiza tazo.

Jego mai matukar dadi nake yi don kuwa ta

ko ina ji da ni a ke yi. Ta bangarena da kuma

126

bangaren Mallam, don kuwa 'yan uwanshi sun

zo, Rannenshi da kuma Ranwar mahaifinshi.

A wurinsu kuma naji zancen sakin Amina. A

rayuwata babu abinda naki irin saki, ko ambaton

shi aka yi a kusa dani sai gabana ya fadi.

Kamar yadda Likita yayi umurni kullum

muke zuwa baiwa yaro nono. Idan naje kuma za

Su sani na gwada mishi don ya dan koyi tsotso.

Sai dai basa bari ayi ta bashi sosai saboda rashin

karfin mukamukinshi.

Sai na tatsa mai yawa a cikin wani abu a ajiye

shi ne za a rinka ba shi har yamma idan mun

koma. Cikin yardar Ubangiji kuma yaron yana

dan murmurewa a hankali yana kara gima

kadan-kadan.

Ranar da aka wayi gari kwana bakwai

Mallam ya nada wa yaro suna Zakariyya. Ni dai

mamaki ya kamani.

Na shiga dakin don kirana da yayi, na same

shi ya tsala kwalliyarshi cikin shadda 'yar asali,

fara yana murza hular da zai saka yana ganin isa

na ya ajiye ya jawo ni jikinshi.

Ya ce, Wata alfarma zan roka a wurin ya ce

wata alfarma zan roka a wurin ki na ce ta me

127

yallabai? Ya ce, ga Mallam nan na baki kiyi

hakuri ki canza mun suna.

Amma yadda ki ke gantsara mun Mallam din

nan wani ai sai yayi zaton idan ya tashi ganina a

zaure zai ganni a kan buzu.

Na ce, To shi kenan me ka ke so na ce maka?

Ya ce, ga sunaye nan da yawa ga Darling na

karka ce na gallà mishi harara na ce, eh ai dole

na ce maka darling don shi yafi maka dadi.

Ya kyalkyale da dariya saboda gane abinda

nake nufi ya ce, kai Hauwa'u kenan na ce,

Habibi zan ce shifa yayi maka ya dan limshe ido

ya fadi sunan.

Sannan ya ce, masoyina kenan ko ba daidai

ba ne da kalmar larabci na ce, eh haka ne yayi

mun. Har na juya zan dawo na ce, to amma ai

sunan Mallam suna ne mai daraja wanda ake

yiwa manyan mutane lakabi da shi kamar kai ai

na kira ka da shi ne saboda girmanka da darajar

da ka ke da shi a wajena. Ya ce. Haka ne

Habibati nayi murmushi na juya na dawo dakina

inda aka cika dankam ake shagalin sunan da ban

san iya adadin kudin da mai gidan ya kashe ba

duk kuwa da cewa yafi kowa sanin jaririn da ya

128

kashewa wannan kudin yana can asibiti kwance

cikin kwalbar Likita.

Cikin ikon Allah sai yaro yayi murmurewar

da su da kansu suka ba mu shi cikin sati biyu, sai

dai tare da gargadi mai yawa. Na yadda za a kula

dashi cikin dan kankanin lokaci sai na murje

nayi kibar da ta baiwa kowa mamaki.

To balle kuma jaririn da tamkar hura shi ake

yi. Yayi wayo babu mai ganin shi ya ce,

bakwaini aka haife shi. Taruwan da ayyukan

gida suka yi mun bai hana ni kara kula da mijina

ba tunda har yanzu kusan wata biyu Amina bata

dawo ba don ya ce ya hakura.

Da taimakon Sahura sai komai ya zamo mun

mai sauki, sannan shima da kanshi yasa a nemo

mun mai taya ni reno.

A wannan lokacin ne nake ganin na taba yin

amarci a rayuwata saboda kula da tattali da

tsantsar so da habibi yake nuna mun.

Sai na gane shi aure dai sa a ne idan Allah

yaga dama sai ya baka. Ba kuma yana nufin don

kayi aure ka fito ka sake yi ka fito shi kenan kai

baka da rabo ba.

Sai dai kowa yana da irin tashi kaddarar ni

tawa kaddarar ta zan yi wasu auren ne a baya

129

kafin wannan kaunar da nake yi wa mijina kuma

sai tasa na koyi wata dabara ta rokon Allah a

kullum nayi sallah shi ne ya karawa mijina sona

da kaunata.

Ya kwadaitar da shi zama da ni, ya bani ikon

kyautata mishi na zamo mace ta kwarai saliha a

gare sh1, ya kuma sa na zamo mata a gare shi a

Aljanna.

To kuma ya amsa don kuwa kullum kara sona

yake yi. Ban bar yaran Amina sun yi maraicin

uwa ba, don kuwa na tsaya tsayin daka wajen

ganin na wadatar da su.

Sai dai abu daya da na kula kawai shi ne, shi

da a koda yaushe uwarshi kawai yake bukata.

An wayi gari yau Asabar kasancewar Mallam

a gida yake bai hana ni baiwa yaran kulawata ba,

duk da hidimar shi da nake yi.

Sai da suka tafi makaranta sannan na shiga

dakin nashi. Waya yake yi ban dai san da wanda

yake yi ba, na ajiye mishi plate din dambun

naman da na kawo mishi.

Sannan na dauko ruwan juice din da nayi

mishi da yayi sanyi na ajiye. Shima ya ajiye

wayar yana murmushi ya ce "Hajiya tana

hanya."

130

Na ce "Amma shi ne bata fada ba." Ya ce, Eh

nima nayi waya da Karima ne take gaya mun

tayi niyyar yi mana kwatsam ne z ata zo ganin

yaro.

Wuf nayi na mike ya ce ina za ki? Na ce haba

yallabai ai banga ta zama ba."

Kafin isowar Hajiya har na kammala

muhimman abubuwan da zan yi, tuwo nayi mata

na alkama da kuma lafiyayyiyar miyar kuka nayi

mata farfesun kayan ciki da ya ji kayan kamshi

na kuma yi mata kunun zaki.

Gaba dayanmu muna zaune a gabanta har da

yaran, yayinda take rike da (Daddy, Junior

abinda yaran suke kiran shi kenan). Itama

mamakin girman yaron take yi.

Ta dan fadada murmushinta ta ce, gashi

kuma cikin yaran babu wanda yayi kama da shi

haka. Ta sanyawa yaran albarka gabaki dayansu.

Ta miko mun shi ta fara cin abincinta don

haka da ni da yaran muka basu wuri.

An dade kafin yazo yayi kirana na shiga

dakin na zauna a can gefe ta kalle ni ta ce, matso

nan Hauwa'u, na dan kara matsawa gab da ita ta

ce, bude hannun naki mu gani.

131

Na bude gefen hannuna da ke dauke da tabon

kunan, don kuwa ya dade da warkewa. Ta ce,

sannu kin ji, ki kuma kara hakuri.

A yadda mijinki ya yabe ki kin samu

kyakkyawar shaida amma kada hakan ya sanya

ki ki rudu. Ki kalli wadannan yaran guda hudu

ki yafewa uwarsu ki kuma san Ubangiji shi ne

ya kare ki daga sharrinta ba wayo ko dabararki

ba.

Ki kuma san shi ne a kullum zai ci gaba da

kare ki. Ballantana a ganin da nayi mata ta

canza ta yi da na sani. Da sabuwar kishiya ai

gara wacce ka san halinta.

Na umarci mijinki da yaje ya dawo da ita,

don haka ku dukkanku ku kara hakuri akan

wanda ku ke yi a dah.

Tunda zama ya hada ku tare kun haifa yara

kuma dolenku suyi zumunci tunda ubansu daya.

Na dawvo dakina na zauna tare da yarda da

abinda Hajiya ta ce. Ita kuma washegari da

sassafe ta tafi.

Sati daya cif bayan nan ya shigo dakin cikin

kwalliya ta manyan kaya sai kamshi yake yi ya

matso kan kujerar da nake zaune a kai ina baiwa

Daddy Junior nono.

132

Ya rike hannunshi yana wasa dashi. Zuwa

can yace na dauka zamu fahimci juna da ke

Hauwa'u, ina rokonki ki bani hadin kai da goyon

bayan da nake nema daga gare ki tunda kin sa ko

a da na hakura da zama da Amina to a yanzu zan

bi maganar mahaifiyata, don haka bana son wata

matsala daga gare ki. Ya mike ya tafi.

Wani irin abu na rinka ji mai daci a bakina

saboda Bacin rai wanda daga baya na gane kishi

ne. haka na wuni wannan abun yana

nukurkusata.

Nayi kuka har na gaji wato dai shi aure ba ka

samun yadda ka ke so. Kamar ni da nayi aure na

gamu da matsalar miji da uwar miji da

ya'yanshi, a yau kuma na gamu da na kishiya

wanda nake ganin kamar yafí wahalarwa saboda

shi a zuciya yake.

Idan kayi sa'a ka samu saliha mai tsoron

Allah sai abin yazo maka cikin sauki, idan kuwa

ka gamu da muguwa mara imani to ba saki ba sai

ta kashe ka. Ba komai ke sa hakan ba face dacin

da zuciya ke yi a kanta. Sai dai a yau na kudurci

aniyar kara wata addu'a a kan wacce na saba yi

a dah, ita ce ta neman tsari da kishiya da

sharrinta da kuma muguwar shawara.

133

Zan kuma baiwa mijina goyon bayan da yake

so, don kuwa na kuduri aniyar zan kyautata

mishi iyakacin iyawata.

Tashi nayi na fara kokarin shirya musu

abinci don nasan a yanzu kam suna gab da

isowa. Sannan na shirya yaran gaba daya tare da

sanar da su dawowan Mamansu.

Nima nayi kwalliya mai kayatarwa na gyara

yaro. Muka yi shar. Ba su iso ba sai bayan Isha'i.

Har daki na same ta nayi mata sannu ta amsa

cikin fara'a da sakin fuska take kuma na yarda ta

canza a kamanni koda kuwa bata canza a halaye

ba.

Don kuwa ta rame tayi bakikkirin. Na shiga

dakinshi da fara' ata nayi mishi sannu da zuwa

abinda ya ba shi mamaki yasa shi ya rinka bina

da kallo har dakinta na koma na kirata don muci

abinci.

Sannan yayi bayanan da zai yi wadanda nuni

ne kawai akan ba zai sake lamuntar raini ko

karya dokar shi a cikin gidanshi ba, haka nan

duk wacce ta sake hantara ko zagin wata to zata

bar mishi gidanshi ballantana a kai ga saka

hannu a jiki.

134

To a halin yanzu kam zaman yayi kyau, sai

na ce ma ba mu taba zama mai dadi irin wannan

ba. Ta 6angarena dai ina iyakacin kokarina

wajen ganin ban 6ata mata ba, haka nan ita ma

kokarinta kullum ta kyautata mun ne don ta

fahimci zafin barin gidan miji da ya'ya.

A kullum kuma za ka same ta tare da Daddy

Junior, don a wurinta ma yake wuni don kuwa

yan uwanshi basa yarda yayi nesa da su.

Shekara ta zagayo don haka na koma

makaranta a lokacin da Daddy yake da watanni

tara. Yayi kato dashi har yana kokarin yin tafiya

bani da matsala a game dashi.

Don kuwa a wurin Amina dama yake wuni

sai na dawo ne yake shan nono. Zamanmu

gwanin sha'awa mun zama tamfar yan uwan

juna, komai zamu yi tare muke yi.

Babu wani habaice-habaice ko bakar magana.

Mafi akasarin gidajen da zaka ga matan sun kasa

zaman lafiya daga mazajen ne a yanzu ne na

kara yarda da hakan.

Don kuwa mu a gidanmu da maigidan yayi

tsaye gashi abin ya tsaya. Sai na fahimci babu

wani abin da yafi auren jarumin namiji dadi a

rayuWa.

135

Ya tsaya ya tsare maka mutuncinka da

yancinka a waje a cikin gida kuma ya nuna

maka tamfar kai kadai ne saboda yanci da

kauna.

Na yarda cewa idan har kaga matsalar ka bata

kare ba, to ba ka daga hannu sama ka roki

Ubangiji ba ne, ko kuma ba ka yi Imani da cewa

yana amsawa ba.

Don kuwa a yau an wayi gari babu wata

addu'a da nayi na gayawa Allah damuwata ba

tare da ya biya mun bukatata ba. A watan da na

mika project dina na kammala karatun Jami' ata

a watanne kuma na haifi santaleliyar jaririyata ba

tare da wani matsala ba.

Na tuna abinda Babana ya gaya mun a ranar

da aurena da Ishak ya mutu, take na yarda cewa

addu'ar iyaye ga 'ya'yansu karbabbu ne don

kuwa ya amshi addu'ar Babana ya bani Mallam

Zakariyya.

Mutumin da nayi ta kokarin na bijirewa aura

sai gashi ya zamo mun mijin marainiya.

Na gode.

Hajiya iiafsat C. Sodangi

(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)

December, 2014

136

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login