Showing 12001 words to 15000 words out of 23627 words
Chapter 5 - MAI DAKI (4) Book Complete By Hafsat C Sodangi.docx
kasa sakin jiki
da irin mu'amallar Mallam da matarshi.
Na sani tare na same su amma da sai su
rinka bari idan bana nan suyi abinsu.
Gyara zamana nayi a kan kujera na rufe ido
nayi kamar ina barci ne. zuwa can naji ya kira
sunana.
Shiru nayi ban amsa ba. Amina ya kamata
kije ki kwanta dare fa ya fara yi, goma ta wuce.
Shiru tayi bata amsa ba zuwa can na dan ji
shishikar kuka shi kuma yana cewa menene
kuma? Me aka yi miki na kuka?
To darling yaya ba zan yi kuka ba don Allah
wai har an yi lokacin da ni zaka kore ni a
dakinka saboda ka matsu da wata ni kuma na
isheka ko?"
"Haba Amina, wannan wace irin magana ki
ke yi haka? Kina so ki tsokalo magana ne
kawai.
Idan kinga ba za ki tafi ba zauna mu kwana
duka a nan. Magana ta kare.
74
"Hauwa'u." Ya kara kirana. Shiru na sake
yi, sai da ya kara daga murya na amsa tare da
gyara zama ina kallonshi.
"Shiga daki ki kwanta." Abinda nake ta jira
kenan, don haka ban tsaya bata lokaci ba na
mike na nufi hanyar fita.
Ya ce, Ina za ki je? Na juyo ina kallonshi ga
daki nan shiga ki kwanta."
Wucewa nayi na shiga daya daga cikin
dakunan kwananshi biyu da ke falon.
Na gyara na kwanta sai dai ba barci nayi ba.
Haka nan sama-sama ina jiwo maganar ban dai
san me suke yi ba.
An kusa awa guda sai naga shigowar shi
ban dai motsa ba har da maganar da yayi mun
don ya gani ko nayi barci.
Washegari da asuba yana dawowa daga
sallah tun zuwa na ban taba lekawa ba.
Babba ne sosai don kuwa ya kai girman
daki, haka nan zagaye yake da tiles kasa da
jikin bango.
A gefen sink an saka kabinet bango zuwa
bango ga gas cooker freezer da na'urorin girki.
75
Ya kalle ni ina so ne za ki fara yin girki
daga safiyar yau tunda kinga ai Amina tayi
miki na kwanakin ukun da ki ka yi har gashi
tayi na jiya ko?
Na ce haka ne, don haka ina so ko shayi ne
ki hada a sha da rana sai a yi abinci na ce to.
Kamar yadda ya fada hakan nayi sai dai na
dada da soyayyen kwai tunda da biredi za a sha
shayin.
Yana tsaye yana saka links din rigarshi ni
kuma ina goge mishi takalman da zai sa
maganar makarantata tana cina a rai.
Amma gagara yi mishi maganar. Ya gama
shirin shi zai tafi ya ce, "Kiyi wa Amina
magana zata nuna miki komai na kayan
amfani."
Na ce, To. Har ya juya sai ya dawo "Kina
da magana ne? kamar nayi shiru sai na kasaa
na ce eh.
Ya ce, "To menene? Na ce, Ta game da
makarantana ne. Ya ce, Ban manta ba, sai da
nayi nufin kiyi sati biyu ne sai ranar Monday ki
fara zuwa.
76
Amma idan kinga hakan bai yi miki ba ki
shirya gobe ki fara zuwa.
Na dawo dakin nashi nayi mishi
kyakkyawan gyara na hada kayan wankin
dakin.
Sannan na nufi kicin don nasan dakina baya
bukatar gyara. Sai da na gama gyaran kicin din
sannan na fito na samu Amina a dakinta.
Tana can ciki, don haka a falo na tsaya nayi
sallama. Ta fito cikin murmushi.
"A'a, Amarya ta fito ko ai darling yayi mun
magana kan ya kamata na huta haka kema ki
shiga kicin din, shekaru bakwai ai ba sawa, ba
ne.
Kullum fa aikin kenan da safe kana kicin da
rana haka da daddare kuma baka huta ba. Ai
kin ga kwana biyu ai nima na kan samu barci.
Don jiya har ce mun yayi na kara dan nauyi
alamar nayi kiba."
Na ce, "Haka ne. Ya ce, Nazo wurin ki ki
nuna mun abubuwan amfani."
Ta fito ta shiga kicin din tana nuna mun
inda abubuwan suke. Ta juya ta fita na kasa
hassala komai don bacin rai.
77
Me take nufi da maganganun da tayi mun.
na dan kokarta na fara aikina.
Dafa duka nayi da taji hadin kayan lambu
da karas da hanta, sannan nayi lemon ginger na
hada duka na gama cikin kankanin lokaci.
Don haka nayi wanka na gyara jikina na
kammala komai a wajen shi kamar yadda aka
saba.
Ba a wani dade ba naji dawowarshi na mike
na shiga falon, amma har Amina ta riga ni ta
tsiyaya mishi lemon jinjar tana ba shi a kofi.
Raina ya sosu amma sai na shanye na
karasa tare da yi mishi barka da zuwa.
Na gyara zama ina zuba mishi abincin na
mika mishi ya karba ya fara ci, ita ma Aminan
tana ci tana magana.
Kaga cin abincin yan Jami'a, wannan
hade-hade ai dole yayi dadi ko ya ki don kuwa
zakin abinda ke ciki kawai ya isa.
Kamar yadda ban ce ba haka shima ya gama
cin abincin shi ya koma wurin aiki, nima na
tattara wurin sannan na fitO na samu yara sun
dawo.
78
Na basu abincin sannan na dora na dare,
tuwo nayi miyar kuka.
Ana gobe zan koma makaranta. Mallam ya
zauna damu a falon shi Amina Hauwa'u zata
koma Makaranta gobe.
Don haka ina so ki rinka yin abincin rana
kullum in yaso ita sai ta rinka yin na dare.
Bata musa ba haka nan ni ga wurina sauki
na samu, don haka shiri sosa nayi da sassafe
muka fita tare zuwa Makaranta.
Yan ajinmu kowa da abinda yake fada
akan canzawar da nayi, ballantana Nasiba da
ke ta bina da kallo.
Ta dai gaji ta ce, "Kai mu ma dai bari muyi
auren nan mu ji." Na ce, "Kyaji dai da shi."
Kullum da safe tare muke tafiya Makaranta
mu kuma dawo tare. Idan muka dawo kuma to
zan zo na samu Amina tayi abincinta na rana.
Don haka ni kuma idan na dan huta sai na
shiga kicin nayi na dare.
Ban taba sawa Amina ido a kan harkarta da
mijinta ba. Don kuwa ranar kwananta ina gama
cin abincina nake tashi na tafi dakina nayi
harkokin gabana.
79
Amma idan kwanana ne to sai ta kai sha
dayan dare, idan ba ce mata yayi zai kwanta
ba.
Haka nan idan ranar kwananta ne ko da
nake yin abincin dare to ita nake mikawa bana
cewa don nayi abincin sai na zuba mishi da
hannuna.
Ita kuwa ko ni ce nayi abinci ranar kwanana
to idan ban yi da gaske ba sai ta zuba ta mika
mishi, tana tambayarshi abubuwan da yake so.
Nayi ta kokarin daurewa akan abin, amma
ta kai ma daga shi har ita sun kure ni.
Don haka yau da na gama abinci kai musu
nayi falon na baiwa kowa a gidan nashi na
debo nawa na dawo dakina na zauna naci na
koshi.
Na dauko assignment din da nake dashi na
fara yi. Wajejen karfe tara sai gashi ya shigo
dakin ya nemi wuri kusa da ni ya zauna.
Lafiya ki ka dawo nan?"
Na ce, "Lafiya kalau, ina dai da abin yi ne."
Ya ce, "To ai da sai ki zo muje can kiyi
abinda za ki yin." Na ce, "Ai ina son nutsuwa
ne sosai."
80
"Kina so ki ce mun idan kina tare da ni ba
ki da nutsuwa?
Na ce, "Ni fa ba haka nake nufi ba, amma
ka duba ka gani fa lissafi ne kashi uku cikin
hudun aikin.
Haka dai ya hakura ya bar ni ya tafi.
Washegari kuwa naci abinci a falo sai dai
ban wani bata lokaci ba na mike na dawo
dakina.
Koda kwana ya juya kan Amina ma ban
tsaya ba ina gama cin abinci nake dawowa
dakina.
Idan ya tambaye ni na ce kasan jarrabawata
kusa ina da bukatar samun lokaci don karatu.
Sai dai ban sani ba ko abin ya fara gundurar
shi ne. da wurwuri na gama aikina na kammala
komai a yadda muka saba na dauko nawa na
dawo dakina na zauna.
Zan fara ci sai gashi ya shigo, "Tashi ki
wuce muje. 99 Na kalle shi sai dai ban musa
mishi ba don banga alamar zan iya yin hakan
ba.
81
Saboda yanayin da na gani a tare dashi
Muna shiga falon Amina tana zaune tayi baje-
baje ta sheka kwalliya sai kyalli take yi.
Ta kalle ni tayi 'yar dariya ta ce, "Hauwa 'u
kenan 'yar lelen darling to ke in banda abin ki
kin san darling ya saba cin abinci a nan don kin
yi girki.
Ki dauki naki kin tafi ai kin san ba zai sa ya
dauki nashi ya biki ba takamar ke ki ka yi.
Ban ce mata komai ba shima bai ce ba sai
dai maganar ta kara 6ata mun rai.
Nemi wuri ki zauna ban kuma yarda daga
yau ki kara daukan abincinki ki tafi wani wuri
kici ba.
Ban wani ci abincin ba, shima kuma hirar
yau ba wani sosai yake amsata ba tara da rabi
nayi na mike da nufin zuwa na kwanta.
Ya ce, Ina za ki na ce zan kwanta ya ce ga
dakinan na dan yi jim saboda ko kadan bana
jin dadin raina na ce ina so ne na yi
assignment.
Ya ce, Gobe kiyi. Dawowa nayi na wuce shi
na shiga dakin barcin shi ya kwanta
82
Bai shigo ba sai wajen goma da ashirin.
Daidai inda nasa kaina a filo yazo ya tsaya ya
kira sunana na amsa ya ce tashi ki zauna.
Menene damuwarki? Ya tambaye ni bayan
shima ya zauna a kan wani madaidaicin stool
muna fuskantar juna.
Na ce, Babu. Ya ce akwai gaya mun kawa
don na san kina da ita. Nayi shiru ban ce komai
ba.
Haba Hauwa'u idan nayi miki wani abu ki
fada mun don na gyara idan kuma wani ne sai
na dauki matakin da ya dace akai amma 1dan
ba ki fada mun ba wa za ki fada ma?
Ba zamana kike yi ba. Ba zan so na rinka
ganin ki cikin bacin rai ba abin kuma da ke
faruwa kenan kwana biyun nan maganganun da
yake yi mun su ne suka sani fara kuka saboda
nauyin da kirjina yayi mun.
Sai da nayi kukana na share hawaye sannan
ya ce "Kiyi hakuri amma ban san na bata miki
rai haka ba.
Ya mike ya dauko robar ruwan sanyi ya
miko mun, ban musa bà na karba na
83
kwalkwala na gyara zan kwanta tare da jan
bargo zan kwanta.
Yana zaune a inda yake ya ce "Idan ki ka y1
mun haka kin yi mun adalci? A hankali na ce
"Me nayi maka na rashin adalci?
Ya ce, "Ba ki sani ba? ya ce, Yaushe rabon
ki da kwana a dakin nan? Kin kusa kwana
goma.
Na kyale ki ne saboda bana son takura miki,
amma ke banga haka a tare da ke ba. A yanzu
kuma da na tirsasa ki kin ja bargo kin rufa.
Tashi kiyi min bayanin abinda ki ke so zan
yi miki, amma bana son ki rinka kokarin da
karfi sai kin tauye mun hakkina da ke kanki.
Danne tawa damuwar nayi na biya mishi
tashi bukatar. Zazzabin da na tashi dashi shi ne
yayi dalilin da muka kusa makara.
Duk da ban tsaya yin wani abu ba baya ga
shayin da na dafa.
Daidai lokacin da muka yi break sai ga
wayarshi. Na kalli Nasiba na ce, Ki raka ni
ofishin Mallam yana kirana.
84
Ta ce, A'a ke dai je ki nasan abinda kiran
yake nufi, sai kuma kawai ya ganni sokai-sokai
na rakaki.
Na juya na barta a friends joint na nufi
ofishin shi. Na samu dalibai da yawa anmma sai
na nemi wuri na zauna a can gefe saboda sanin
da nayi ofishin ba ya rabo da dalibai masuu
matsala.
Don shi ne Dean of students affairs, yana
sallamar na ciki ya kira sakatariyar shi ya ce
mata kada wani ya sake shigowa.
Sannan ya dawo ya ce Yaya jikin naki? Na
ce da sauki. To me zan kawo miki? Na ce,
ruwa kawai.
Ya miko mun ruwan sannan ya zauna a kan
doguwar kujerar da nake zaune a kai ya mannu
da jikina.
Na dan yi kokarin matsawa don kuwa
kunyar Mallam kan kama ni a irin wadannan
lokutan.
Shima matsowa ya sake yi na dan yi
murmushi ya ce, "A to kya yi dariya dai kema
me yasa ki ke guduna?
85
A hankali nayi magana na ce,"Bana
gudunka. Ya ce, "Kina yi mana koda yake na
fahimci laifi nayi miki shi yasa nake so ki gaya
mun laifin.
Na rasa yadda zan yi nayi mishi wata
magana. Kada kiji kunyar gaya mun
matsalarki.
Ganewan da nayi ba zan iya kaucewa ba
yasa na ce, Ni dai kawai na fi so na rinka zama
a dakina ne.
Ya ce, Zan bar ki ki rinka zama a dakinki
idan kin gaya mun dalili. Na ce, dalilin kenan
saboda karatuna.
Ya ce, Ban yarda ba, wannan ba dalili ba ne,
don haka ban yarda da zaman daki ba, tashi ki
bani madara a fridge.
Na mike na isa wurin fndge din na dauko
hade da tumblan na tsiyaya na mika mishi, ya
zuba mun ido yana kallona.
Na dan kawar da kaina gefe. Yasa hannu ya
riko hannuna da kofin gaba daya ya kai
bakinshi. Sai da ya shanye madarar sannan ya
sake hannuna na ajiye kofin.
86
Ya ce, Koyi hidimar mijinki. Ki kula da
abubuwan da yake so da dabi'unshi nunawa na
kusa dake cewa abinda yake yi baya baki
haushi.
Don za ki yi wanda yafi haka. Kina da kyau
kina da kuruciya, baya ga haka Allah yayi miki
wasu baiwa da kema ba ki san da su ba.
oUwa uba kuma mijinki yana sonki. Kada ki
bar wa wata mijinki saboda zafin kishi.
Kuma don kina jin haushin wani abu ba zai
sa na canza dabi'ata ta zama da ku ba a
kullum.
er Juyowa nayi na kalle shi saboda abubuwan
da yake fada. Ya ce, Eh matsalarki kenan ko ba
haka ba ne?
Na ce, Ni ba haka ba ne, na ce maka bani da
matsala. Ya dan yi dariya ya ce, To naji ba ki
da matsala.
Na mike da niyyar tafiya, don ganin lokaci
ya kure na break din mu, na dauki tumblan da
robar zan mayar, shima ya mike ya biyo ni.
Ina ajiyewa na juyo ya rike ni tare da
mannani jikin bango yasa hannu ya zare
hijabin da ke jikina.
87
Na dan fara kokarin yin magana amma bal
bar ni ba. Na fara kokarin zamewa ya dauke ni
ya ajiye ni a kan makeken teburin da ke
tsakiyar office din.
Da kyar naja jikina na koma kan kujerar da
na baro na kifa kaina. Na kasa komawa kusa da
shi na dauki hijabina. Na kuma kasa kallon shi.
Ya taso ya zauna kusa da ni tare da jawo ni
jikinshi nayi saurin cewa zan koma aji fa
kuma...ya ce, kuma me?
Kunya tana da kyau a addini, amma taki
tayi yawa Hauwa'u, ki daure ki dan rage
saboda ni ki taimake ni kema kuma ki taimaki
kanki.
Da na dawo na zauna sai na fahimci gaskiya
kawai ya gaya mun, kishi shi ne abinda yafi
kuntata min.
Don haka ya zama dole nayi koyi da
shawarar da ya bani. Shiri sosai nayi ranar da
na karbi girkina nayi kayatacciyar kwalliya.
Na shiga dakin shi na fitar da duk wani
abinda bai yi mun ba, na sake shimfidu na
feshe shi da turare.
88
Ina kammala abinci kuwa na hada komai
na zauna zan fara zuba abinci sai Amina ta
dauko plate din shi zata zuba mishi kamar
yadda ta saba.
Na mika hannu da niyyar karba, ta kalle ni
ai zan zuba mishi ne, na ce eh na sani amma ci
naki kawai na hutar da ke.
Ta dan tabe baki tare da cewa, ai shi kenan
na zuba mishi na mika mishi, sannan na zuba
mishi abin sha na ajiye a kusa da shi.
Sannan na zuba nawa na fara ci. Duk motsin
da zai yi idona na kanshi na kankane, don haka
yau ko doguwar hira ba ayi ba.
Tun ina yi ina dan jin kunyar abubuwa har
na zake, sai kuma na gane da gaske abinda ys
takura mun kenan.
Shirye-shiryen jarrabawarmu ya kankama
gadan-gadan, don kuwa a gobe ne ma zamu
fara.
Zama tsakanina da Amina ya canza gaba
daya, don kuwa sai na gaisheta sau uku kafin ta
amsa mun sau daya.
89
Ban kuma taba fasawa ba. Ko wurin cin
abinci muka hadu sai takai ta kawo ne magana
ke hada mu.
Idan bata ga dama ba kuwa ko nayi mata
bata amsawa. Ta daina shisshigin zuba mishi
abinci ranar girkina, ko shisshige mishi da take
yi.
Shirin jarrabawa ta bata hana ni hidima da
mijina ba, don kuwa a yanzu ne ma nake jina
na fara auren.
Na gama hada abinci a falo na fara zuba
mishi salad saboda azumin da yayi.
Ya fara ci na kai hannu zan dauki cokali sai
naga ta rike, na ce barı mana na gama zuba
mishi sai na baki.
Kan na ankara sai kawai naga ta fauce shi a
hannuna ta ce, To duk maitakarki sai na zuba
nawa, jarrababbiya kawai.
Bude baki nayi galala ina kallonta, shi kuma
cikin bacin rai ya ce, Yaya haka? Meye haka
kuma daga magana sai ki zage ta? To bana so.
Eh mana ai dole ka ce ba ka so sai kawai ta
fashe da kuka. Muna zaman zamanmu ka
dauko masifa ka kawo mun cikin gida.
90
Duk abubuwan da take yi mun kana gani ba
ka ce komai ba, saboda ba haka kawai ta barka
ba, da haka muke?
Ta shiga tsakaninmu ko kallon arziki baka
1ya yi mun sai idan bata nan har ta kai ma zata
wulakantani a gabanka, kuma ka goyi bayanta.