Showing 6001 words to 9000 words out of 23627 words
Chapter 3 - MAI DAKI (4) Book Complete By Hafsat C Sodangi.docx
/>
Na yago takarda na rubuta suna, course
(madda), department da kuma matriculation
no, nayi gaggawan rubuta abinda na sani daidai
gwargwado.
Sannan na jawo wata takardar duk da
faduwar gaban da nake yi baisa na fasa abinda
nayi niyya ba.
Nasiba na rubutama duk kuwa da sanin
halin shi da nayi. Muna gamawa ya karba
sannan yayi mana dan karatun da zai yi mana
ya fita.
Ban ko tsaya jiran wani darasin ba, fitowa
nayi daga makaranta na wuce gidan su Nasiba.
Babban gida ne sosai irin na masu kudin da,
sai dai gini ne na bulo amma sashe-sashe.
A yadda Nasiba kuma ta gaya mun to a
gidan nasu kaf dinshi ita ce 'yar autansu.
Matan Babanta hudu ne don haka Yayu ne
da ita maza da mata masu yawan gaske.
39
Wani yaro ne ya shigar dani har dakin
Nasiba kamar yadda nayi zato kuwa bata jin
dadi ne.
Bata yi zaton ganina ba sai dai taji jiki don
gaba daya ta zube. Ta kokarta ta wartsake har
ta karya saboda lokacin da naje bata ko karya
ba.
Tayi wanka sannan ta kai ni wurin
mahaifiyarta. Maman Nasiba Hajiya Tani
dattijuwa ce sosai, don kuwa zata kai shekaru
sittin da biyar zuwa saba'in amma kuma das da
ita.
Da karfinta babu wani alamar da zai nuna
cewa shekaru sun hau mata ka.
Na durkusa ina gaisheta tana amsawa cikin
fara'arta. Yayinda Nasiba take gabatar mata da
ni. Ta tambaye ni karatu da iyayena na bata
amsar komai lafiya.
Ban wani zauna ba na mike da nufin tafiya,
Hajiyar Nasiba tayi mun alheri sosai, na fito
bayan na jaddadawa Nasiba lallai tayi kokarin
zuwa makaranta gobe saboda tsoratar da nayi
da abinda Mallam Zakariyya yayi mana.
40
Ta kuma yarda don kuwa a washegari har
sai da ta riga ni. Karatu ya kankama sosai don
kuwa muna cikin sati na uku ne a cikin wannan
zangon.
Muna zaune a a friends joinrt inda mafi
akasarin lokaci idan anyi break sannan ba mu
da abin yi a wurin muke zama.
Hira muke yi cikin nishadi da wasu daga
cikin 'yanmatan makarantar mu.
Kowa yana nashi korafin ne a kan yadda
yanmatan Jami'a suke bai wa Malamai
kawunansu, wanda kuma hakan shi ne ke kara
lalata mana al'amura.
Yake rage mana mutunci suke kuma ganin
mu a araha banza. Wani yaro ne ya iso wurin
da alamar gajiya a tare da shi.
Watakila saboda sassarfar da yayi don
isowa wurin da muke zaune.
"Hauwa'u kije in ji Mallam Zakariyya."
Abinda ya fada kenan, a lokacin da ya gama
gaishemnu.
Gaba dayanmu muka zuba mishi idanu
saboda yadda abin yazo mana kwatsam. Take
alamar tsoro ya bayyana a idona, sai dai kafin
41
na samu damar tambayar shi har Nasiba ta riga
ni.
"Lafiya yake nemanta?"
Abinda ta ce mishi kenan, sai dai a
maimakon ya bata amsa dariya yayi ya ce.
"Ka ji Malama Nasiba, ana tambayar
tsakanin Malamin Jami'a ne da kuma
dalibarsa.
Juyawa yayi ya yi tafiyarshi, bayan ya ce
yana fa jiran ki don kada ya ce ban fada miki
ba."
Da ni da Nasiba muka mike don zuwa kiran
Mallam Zakariyya, ni dai gabana sai faduwa
yake yi abinda yasa shi kirana.
Don kuwa ni ban ma san ya sanni ba, haka
nan ban tuna wani laifi da nayi mishi ba.
Har muka isa kofar ofishin nashi babu
wanda ya tankawa wani a tsakaninmu. Na taba
kofar a hankali naji an ce shigo.
Nayi kyakkyawar sallamata bayan na
karanta addu'o'in neman tsari.
"Ina wuni Mallam?"
42
Yana zaune a kan kujerar ofishin nashi yana
duba wata zungureriyar takarda mai dauke da
zanen map (Taswira).
Sai da ya gama nadeta sannan ya samu
daman amsa mun gaisuwar da nayi mishi, ya
dago kanshi yana kallona tare da dan
Jujjuyawa a kan kujerar tashi.
"A gwajin farko da nayi muku na ranar da
aka dawo daga hutu akwai karin takarda daya
da ta hau kan adadin yawan daliban da ke ajin
a wannan ranar.
A iyakacin binciken da nayi sai na fahimci
kece ki ka rubutawa kawarki saboda rashin
tarbiyya da sanin ka idar neman ilimi.
Don haka zan yi amfani da ke don ki
zamanwa sauran daliban ajinku darasi a kan
ganganci irin wannan koda kuma a nan gaba
wani zai yi kuskuren yi to ba zai zama a kaina
ba.
Don kuwa ni mutum ne mai bin komai nawa
bisa tsara da bin ka'ida. Fita ki bani wuri."
Na fito jikina a sanyaye na samu Nasiba a
tsaye a waje tana jirana saboda kin shiga da
tayi.
43
Ta ce, "Lafiya dai ko? Na ce, "Lafiya
kalau. Ban yi niyyar gaya mata abinda ya faru
ba, don kada tayi tunanin ita ce sanadi.
Duk kuwa da rokona da tayi tayi, har taj1
haushi ta kyale ni.
Babu iin tunanin da ban yi ba a kan
matakin da Mallam Zakariyya yake nufin
dauka a kaina.
Shin zai sa ni na maimaita maddar ne ko
kuwa yaya? Maimaita madda irin wannan mai
matukar muhimmanci ba karamin abu ba ne.
Ya zama dole na je na ba shi hakuri.
Washegari sanin da nayi muna da shi da
safe yasa nayi sammakon tafiya. Sai da ya
gama da mu ya fita sannan na mike na bishi
don nayi mishi magana.
Ina shiga ofis din nashi ya dago kai ya kalle
ni fuskarshi a murtuke.
"Yaya lafiya dai ko?"
Na ce, "Eh lafiya Mallam."
Ya ce, "To na kira ki ne?" Yayi tambayar
cikin daga hannayenshi alamar jaddada
tambayar tashi.
44
Na ce, "A'a Mallam don Allah nazo ne don
na baka hakuri bisa kuskuren..."
Kan na karasa sai kawai naji ya ce "fitar
mun a office."
Sum-sum na wuce na fita na dawo aji jikina
kamar an bi gabobina an bubbuge su.
Na samu Nasiba a ajin bata ce mun komai
ba, nima ban ce mata ba, ita dai da alama fushi
tayi don kuwa taga lokacin da na bi bayan
Mallam Zakariyya.
"Wai me ki ke nufi ne da wannan
wulakancin da ki ke yi mun? ina binki ina
tambayarki abu kina wani daddaure rai kina
bata fuska?"
Na kalleta na ce, "Ba fa daure rai nake yi
ba." Ta tabe baki ta ce, "Kya dai ji da shi, ni
nasan Mallam Zakariyya ba zai kira ki don ya
nemi lalacewa da ke ba.
Don kowa ya shaide shi a makarantar nan.
Ni nasan da abinda ya faru amma kiyi mun
bayani kin ki, ai kuma sai kiyi ta yi."
Haka na wuni sukuku babu lakka a jikina.
Da na dawo gida ma Umma sai da ta gane. Ita
kam nayi mata bayanin komai.
45
Ta ce, "To ai sai kiyi hakuri kawai ki roki
Allah ya sassauta fushin nashi idan kuma ya
saki kin maimaita ma ai shi kenan tunda ba
karatun ba ne gaba daya za a fadi ko?
Idan badi tazo da rai sai ki sake rubutawa ai,
shekara kwana ne ga mai rai. Allah kuma yasa
hakan ya fiye miki alheri."
To na dan ji dadin bayanin Umma, wanda
hakan yayi matukar sani na dan wartsake.
Duk da sanin tsakanina da Mallam
Zakariyya da nayi bai sa na daina halattar
darasin shi ba.
E Haka nan na kara dagewa sosai da sosai ba
ma akan darasin shi ba kawai har a kan saura.
Kamar yadda ya saba na bayar da test ba
tare da anyi zato ba yau ma haka yayi daidai
gwargwado, kuma na amsa tare da yin bayani
filla-filla.
Kwanaki biyu bayan nan ya aiko da
takardar yin gwajin, abin mamakin shi ne,
mutum biyu ne suka ci, sha takwas a ajin gaba
dayanshi, daga wani yaro namiji sai ni a mata.
Nade takardar nayi na cusa a jakata saboda
zagaye ni da aka yi don tabbatarwa yayin da
46
wadanda abin ya basu haushi suka fara haba!
Ai dama biri yayi kama da mutum.
Don kuwa ai yanzu bini-bini sai ka ganta a
office dinshi.
Nasiba ta kalle ni, bayan mun fito ta ce, "Ni
me ke tsakaninki da Mallam Zakariyya ne?
wannan shi ne karo na uku da nake tambayarki.
Kuma ba zan sake ba daga wannan karon."
Na dan yi murmushi nayi mata bayanin duk
abinda ya faru, har zuwa yau.
Ta ce, Ikon Allah, to Allah dai yasa ba
yayi miki makin ba ne kawai."
Na ce, "Nima tsoron da nake ta ji kenan."
Nayi iyakacin taka tsan-tsan kan al'amurana
da sauran Malamai gaba daya, ba ma Mallam
Zakariyya shi kadai ba.
Har aka yi jarrabawarmu ta wannan karon
wacce da ni da Nasiba muke sa rai da
kyakkyawan sakamakon.
Rayuwata tana tafiya mun yadda ya kamata.
Na cire komai cikin raina. Ahmad, Ishak da
danshi duka burina kullum na ga na kammala
karatuna ne.
47
Na karbi sakamakona cikin nasára na tafi
bautar kasa sannan na zama Malamar makaranta.
Burina kenan, to amma anya hakan zai yiwu
kuwa? Har a yanzu ina da wajen shekaru biyu
ne a gaba kafin na gama makaranta.
Amma ban taba sauraron wani da sunan
yazo zance wurina ba, don gudun samun
matsala a wurin 1yayena.
To suma kuma har yanzu ba su ce mun
komai ba. A yanzu hutunmu ya kare mun shiga
shekara ta uku ne.
Zan iya cewa a ajinmu gaba daya babu
mace da ta fini fice da hazaka, don haka
Malamai gaba daya sun sanni don hazakata.
Wayewar garin yau Asabar ce, don haka
duk kokarina na ganin na gama ayyukana ne
da wuri na tafi gidan Yaya Auwalu wuni.
Sai dai kan na kai ga gamawa Babana ya
shigo gidan.
"Idan kin gama ayyukanki kizo ki same ni."
Na ce,To. Ba tare da wata fargaba ba.
Na kammala cikin sauri na samu Babana
kamar yadda ya umurce ni.
48
Ina shiga dakin na kara nutsuwa saboda
ganewar da nayi neman da yake yi mun mai
muhimmanci ne.
Umma tana zaune a can gefe da alama kuma
wata maganar suke yi.
Na durkusa a gefe na ce, "Gani Baba. Ya
ce, "Zama za ki yi da kyau."
Na gyara zaman da nayi ta hanyar zama a
kan tabarmar da ke shimfide a tsakar dakin.
"Na kira ki ne saboda a ganin da nake miki
a yanzu to ya kamata ace kina da cikakken
hankali da kuma tunanin irin na manya.
Haka nan ko baya ga haka addini ya baki
yanci na kanki, a duk lokacin da wata bukata
ko hukunci da ya dangance ki kai tsaye.
Kuma ko da nake uba wato Mahaifi a gare
ki, nayi miki alkawari zan yi iyakacin kokarina
don ganin ban tauyeki na tilasta miki wani abu
ba.
Akwai wasu mutane da suka zo suka same
ni kan na basu izini na neman aurenki, kamar
kimanin watanni biyu kenan, ban yardar musu
ba ne a wannan lokacin saboda kokarin da nayi
49
na ganin nayi kyakkyawan bincike a kan shi
mutumin.
A iyakacin abinda naji na kuma gani a
game dashi ban samu wani mugun abu ko
mummunan abu ba.
Mutum ne na gari abinda mutane suka fada
kenan a game da shi.
To a jiya da daddare sai ga wani aiken ya
sake yi duk dai akan maganar ne na kuma
yardar musu amma hakan ba yana nufin
maganar aure ya tabbata ba ne.
Don ba zan tilasta miki ba, don kuwa a
shekaru uku zuwa hudun da kika yi a gida
banga wani laifi ko mugun abu da ki ka yi ba.
Wanda zai sa na tilasta ki yin aure a wannan
lokacin ba. Amma duk da haka ina so ki san
shi aure hijabi ne a wurin 'ya mace, shi ne ke
kara mata martaba, kima da kuma mutunci.
Shiru nayi cikin wani irin yanayi da
zurfaffen tunani. Abin da ban taba zaton zai zo
mun a yanzu ba kenan, wato maganar aure.
Wandakuma hakan yana daga cikin
manyan dalilan da suka hana ni sauraron kowa
50
Menene zai biyo baya kenan a yanzu
Tunanina ya dawo a daidai lokacin da naji
Babana yana cewa zai zo a cikin kwanakin nan
don ku daidaita.
Na ce, "A'a Baba ba sai ya zo ba ma, idan
yayi maka shi kenan."
Babana ya ji dadin maganar da nayi ba
kadan ba, amma duk da haka sai ya ce "A'a ai
zuwan nashi yana da kyau, don ku san juna."
Na tashi na dawo dakina jikina a sanyaye.
Sanya mun albarkar da Babana yayi ta yi bai sa
na wartsake ba.
Baba Ladi ta kalle ni ta ce, "O' oh maganar
auren ne ta mayar da ke haka? Ko gidan Yaya
Auwalun da nayi niyyar zuwa kasawa nayi.
Aikin da na zaba yi na gida kuwa Umma ko
saurarona a kai bata yi ba.
Al'amuran baya sai suka fara dawo mun.
"To shi kenan shi kuma wannan auren idan
nayi shi menene zai zamo nashi matsalar? Don
kuwa a yanzu sai na fahimci cewa babu wata
mata da take zaune a dakin mijinta ba tare da
tayi hakuri da wasu matsaloli ba sai dai kawai
na wasu yafi na wasu.
51
Haka nan na wasu yayi sanadin mutuwar
aurensu yayinda na wasu kuma ake ta ci gaba
da fafatawa.
Ba hakuri ko rashin hakuri ba ne yake kashe
wa mata aure, sai dai kawai kowacce mace da
nata kaddarar.
Don kuwa sai kaga wata matar masifaffiya
ta fitini kowa dangi da shi kanshi mijin ba
dadinta ya ji ba. Amma auren na nan ana zaune
a haka saboda kaddarar ta ba ta aure-aure ba
ce.
Haka nan wasu matan kuma sai ka same su
masu matukar hakuri, amma wasu 'yan dalilai
da ba su kai sun kawo ba sun zamo dalilin
rabuwar nasu auren.
Ni kam a kafin zuwan wannan rana fatana
daban, haka nan hankalina a kwance yake.
Haka nan nayi kyau na sake murjewa na zama
cikakkiyar mace.
Wanda kana ganina ka san ina da
watacciyar nutsuwa da kwanciyar hankali.
To amma tunda Babana yayi mun wannan
maganar sai naji gabana ya fadi, don maganar
aure a yanzu yana tsoratar da ni.
52
A take sai na fahimci dai wato ita 'ya mace
da zarar ta gima ta kai munzalin aure sai ta
shiga cikin wani yanayi.
Idan tayi auren matsaloli idan bata yi ba ma
hankalinta ba kwanciya yayi ba.
Don kuwa ita a lokacin burinta bai wuce na
auren ba, haka nan mutanen gari ba barinta za
su yi da zantuttuka ba.
Tsawon daren nan ban runtsa ba tunani
kawai barkatai a cikin raina.
Baba Ladi da bata barci mai nisa saboda
kusur-kusur dinta da kuma sabo da tashin
nafilar dare har tayi ta gama idona biyu, ban
kuma tashi ba saboda ina hutun sallah.
Sai dai duk da haka kwana nayi addu'o'i
ciki da bakina da kuma zuciyata.
Ban samu na runtsa ba sai bayan da aka yi
sallar asubah. Wajen karfe takwas da kwata na
tashi na fito tsakar gida da nufin nayi wanka na
kama ayyukana, sai na samu Umma ta gama.
Na nemi wurina zauna ina karyawa ita kuma
Umma tana tankade garin alkama da zata yi
tuwo dashi sai kawai ga sallama.
"Wai ana sallama da Hauwa'u."
53
Cikin sauri na dago kai na kalli yaron,
sannan na kalli Umma. Tankadenta take yi ko
kallona bata yi ba.
Da wannan irin safiyar kuma kira haka ko
karyawa ban yi ba. Sai dai duk da abinda na
fada ban fasa tashi ba.
Don kuwa ba sai an ce mun ga mai kiran ba,
mutumin da Babana yayi mun magana a kanshi
ne.
After dress na dauko na dora a kan riga da
wando na material da ke jikina na mutsuka
hoda don ko hodar ban shafa ba da na fito
wanka.
Na dosa hanyar fita kofar gida sai dai a
daidai nan ne naji wani irin mummunan
faduwar gaba take na fara jero addu'o'i ina
maimaitawa.
Ina kuma fata duk wanda zan gani yayi mun
a cikin raina kada na samu matsala ya kuma
zamo mai alkhairi a gare ni.
Don kuwa bana fata a kan maganar aurena
Babana ya sake bacin rai.
Na isa daidai inda yake tsaye ya jingina da
mota. Daga bayanshi na fito.
54
Don haka na dan kare mishi kallo. Dogo ne
dan siriri yana kuma sanye da kaftani masu
ruwan kasa.
"Salamu alaikum! "
Nayi mnishi sallama daidai na karasa inda
yake, me zan gani? Amsawar da zai yi tare da
juyowa sai kawai muka yi ido hudu da Mallam
Zakariyya.
Shi kanshi ya gane kaduwar da nayi da na
ganshi. Murmushi yayi abinda ban taba sanin
ya iya ba.
"Malama Hauwa'u kina nan lafiya ko?"
Kasa amsawa nayi saboda yanayin da na
shiga. Haka nan ko gaishe shi na kasa yi.
"Nasan kin yi mamakin ganina ba kuma
komai yasa nayi hakan ba sai dai don ganin da
nayi miki na cikakkiyar ya mai tarbiyya.
Wacce nasana kowanne yana y1 zata
zamanto mai bin umurnin iyayenta.
Ban tuntube ki na nemi ra'ayinki ba duk
kuwa da cewa idan na bukaci hakan mai sauki
ne a wurina, to sai na guji wasu abubuwa da ka
iya biyo baya. Ina fata za ki gafarce ni.
55
Ganin ban ce mishi komai ba, ba ni kuma da
niyya, sai kawai ya ci gaba.
"Ina da mata da 'ya'ya hudu, mata biyu
maza biyu. Ina kuma fata zamu samu fahimtar
juna ba tare da wata matsala ba?
Zan ba ki dan lokaci domin kiyi shawara,
don haka zan dawo a cikin sati mai kamawa."
Na ce, "A'a ba ma sai nayi shawara ba."
Ya gyara tsayuwarshi ya ce, "To menene
ra'ayinki?"
Na ce, "A gaskiya ni bani da niyyar yin aure
a yanzu saboda karatu nake, duk kuma abinda
zai shiga tsakanina da karatuna bana sonshi."
Ya dan yi murmushi kadan ya ce, "A'a ke
dai idan kina da wata matsalar kawai ki fadi,
amma ba wannan ba don kuwa ni kema kin san
ba zan hana ki karatu ba.
A matsayin da nake na Malaminki, kuma
nutsuwarki da na gani yasa nay1 takakka na
biyo ki.
To kuma